Monday, February 25, 2013

Amsoshin Wasikun Masu Karatu (2)

Wannan shi ne kashi na biyu na "Amsoshin Wasikun Masu Karatu."  Kamar sauran lokutan baya, ban hada da wadanda na amsa su ba. Akwai wadanda aka aiko ta Imel, su ma na amsa su, don haka ban sako su cikin wadanda na amsa a wannan mako ba. Kamar yadda sanarwa ta gabata a makon jiya, a halin yanzu na loda dukkan kasidun da suka gabata a shekarar 2012, duk mai so sai ya shiga Mudawwanan da ke shafukanmu, kamar yadda aka saba. Na gode.

…………………………………………………………..

Baban Sadik, Allah ya saka maka da alheri da fadakarwar da kake yi wa al'umma.   Da fatar Allah ya barmu tare, amin.  Daga Nasiru Sani Gusau, Jihar Zamfara.

Ina godiya matuka Malam Nasiru, Allah saka maka kaima da alheri, ya kuma ji kan mahaifa. Na gode da addu'ar da ka min, Allah bar zumunci, amin.

Fatan alhairi a gare mu, kuma da fatan kana lafiya kamar yadda nake lafiya.  Baban Sadiq, shin, zan iya tura sakon Imel ta hanyar tsarin 'MMS' ga wanda nake son tura wa, alhali ban bude Imel ba? Na gode. Prince Babani Yola

Da farko dai tukun, duk wayar da ke da tsarin aika sako ta hanyar MMS, to, lallai kana iya aikawa da sakon Imel ta hanyar da ta ake yin hakan, ba sai ta hanyar MMS ba.  Bayan haka, ana iya aikawa da sakonnin hotuna ne ko bayanan tes ta hanyar MMS, amma ba sakon Imel ba.  Ma'ana, tsarin aika sako ta Imel wani tsari ne mai dauke da nasa ka'idojin aika sako na musamman.  Shi yasa idan ka bukaci aika sakon Imel ta wayarka, muddin tana dauke da wadannan ka'idoji, nan take za ta kaika inda masarrafar Imel take in akwai.  Don haka, ba a aika sakon Imel ta hanyar MMS, sai ta tsarin Imel, domin dukkansu (da Imel da MMS) suna amfani ne da Intanet wajen daukan sako daga wayar da aka aika su zuwa wata waya ko kwamfutar da ke dauke da adireshin da aka aika.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik bai manta da roko na ba na tura min laccar da ka gabatar a katsina. Na gode!

Wa alaikumus salaam, lallai kam na tura maka. Ina kyautata zaton ka samu sakon tuni.  Allah sa mu dace, amin.

Assalaamu alaikum Baban Sadik. Don Allah, tsakanin uwa da uba wa yaro yafi gado wajen siffa.  Saboda mafi yawan mutune sun fi debo kamannin iyayensu mata da dabiunsu.  Za ka ga uba fari tas amma in matarsa baka ce sai aga mafi yawan yayansa bakake.  Haka nan za a ga mutum baki kirin amma in matarsa fara ce sai aga mafi yawan 'ya'yansa farare.  Daga Mahfuz Tasiu Kano

A gaida Mahfooz, sannu da kokari.  Wannan tsokaci ne kan abin da ka lura dashi.  Amma na yi bayani iya gwargwado a kasidun da suka gabata kan wannan al'mari, da hujjoji na hadisai da kuma bayanan masana kimiyyar halitta na zamani cewa, tsakanin Uba da Uwa akwai nau'ukan dabi'un halitta da suke raba wa 'ya'yansu.  Domin 'ya'ya sukan yi kamaiceceniya da dayan iyayensu ne sanadiyyar rinjiyar dabi'a da siffar halitta da kowanne cikin iyayensu nasu keyi.  Misali, idan dabi'ar halittar Uba (Paternal Genes) a bangaren launin jiki sun fi na Uwa karfi (wato yana da "Dominant Trait"), 'ya'yansa za su yi kama da shi a wannan bangaren.  Sannan idan uwar tana da rinjayen dabi'ar halitta a bangaren saurin fushi, to, ana iya samun wasu 'ya'yan su zama masu masu saurin fushi, ko da kuwa sunyi kama da mahaifinsu wajen launin jiki. Sannan  Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya nuna cewa lallai idan maniyyin namiji ya zama a saman na macen (ko ya rigayi nata, ya zama a sama), to dan da za a samu ta sanadiyyar wannan haduwa zai yi kama da mahaifinsa ne. A takaice dai kamaiceceniya ta fuska ko launin fatar jiki, ba ita ce kadai kamaiceceniya ba, akwai dabi'un zuci, da tsawon jiki, da girma ko sirantakar gabobin jiki, da launin gashin kai, da tsarin hakora, da tsarin fadi ko sirantakar yatsu da dai sauransu, wanda idan aka yi la'akari dasu, za a ga ko da 'ya'ya sun biyo Uwarsu a launi, ta wani bangaren bai hana suyi kama da mahaifinsu, idan aka yi la'akari da wadancan dalilai.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq ya aiki?  Don Allah ka kara taimaka mini da wani adireshin gidan yanar sadarwa na Muslunci, wanda zan rika aika tambaya ana bani amsa da hausa.  Kwanaki ka bani na www.islama-qa.com to, sai dai ina son na harshen Hausa ne.  Da fatan babu matsala nagode.  Usman Muazu Funtua, Katsina State

Wa alaikumus salam, Malam Usman bark aka dai.  Kamar yadda kace, wanda na baka kwanakin bayan na harshen Turanci ne, ma'ana da harshen Turanci ake aika tambaya, haka ma cikin harshen Turanci ake amsawa. Wannan shafi da na baka dai shi ne shafi mafi shahara a Intanet kan abin da ya shafi aikawa da karbar amsar fatawowi kan al'amuran Musulunci.  A gaskiya a halin yanzu dai ban san wani shafi karbabbe, cikin harshen Hausa, wanda ke karba da kuma amsa tambayoyi kan sha'anin Musulunci ba.  Wannan ne ma yasa na baka wannan din.  Tabbas  akwai wasu shafukan yanar sadarwa na wasu kungiyoyi inda malamansu ke amsa tambayoyi, amma ba wai musamman aka gina shafukan don amsa tambayoyi ba.  Amma idan kana da shafi a Dandalin Facebook, kana iya neman duk malamin da hankalinka ya kwanta dashi, ka shiga shafinsa don aika tambayarka, za a baka amsa.  Akwai malamai da dama 'yan Najeriya, shahararru, kuma Hausawa, masu shafuka a Dandalin Facebook.  Kuma muddin ka aika tambaya za su amsa maka in Allah yaso.  Allah sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik, don Allah yaya zan mayar da shafin Facebook di na ya zama dandali? Kuma wane ne Harun Yahya, da gudunmawarsa a kimiyance? Abul-waraqat Ayagi.

Dubun gaisuwa ga Abul Waraqaat. Dangane da abin da ya shafi canza shafin Facebook ya koma Dandali, sai dai ka bude Dandali na musamman, wanda shafin ke bayar da damar budewa, wato "Group" ko "Page."  Galibin shahararrun malamai da shugabanninmu na siyasa suna da shafuka ko Dandali na musamman a shafin Facebook.  Idan kana bukata ba sai ka canza shafinka ba, wanda zai zama mai wahala a gareka, kana iya bude Dandali na Musamman. Idan ka shiga shafinka, ka gangara kasa daga bangaren hagu, za ka ga inda aka rubuta "Create a Group,"  kana shiga za ka ga yadda ake budewa, babu wahala.

Dangane da Harun Yahya kuma, wani shahararren mai bincike ne kan fannin halitta a musulunce, da bambance-bambancen da ke tsakanin mahangar Kur'ani da mahangar Malaman kimiyyar karnoni biyar zuwa yau.  Asalin sunansa shi ne Adnan Oktar, kuma an haife shi ne a birnin Ankara na kasar Turkiyya cikin shekarar 1956, yana da shekaru 57 kenan a duniya yanzu. Ya yi karatunsa gaba daya a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, inda ya karanta fannin Falsafa. Adnan Oktar mutum ne mai sha'awa kan binciken malaman kimiyya musamman na wannan zamani, tare da gwama fahimtarsu da wanda ke cikin Kur'ani ko Hadisai ingantattu.  Littafin farko da ya fara fitarwa shi ne "The Atlas of Creation," wanda babban kundi ne kan bayanan da suka shafi halittu, da tsarin halittarsu, da hotunansu, da kuma mu'jizar Allah da ke cikin halittatarsu.  Bayan  wannan akwai rubuce-rubuce da yawa da ya yi daga baya, duk a kan fannin kimiyyar halittu ne da sama da kasa da duwatsu da kuma sararin samaniya.  A halin yanzu yana da gidan rediyo na musamman inda yake tattaunawa kan asalin halitta, da kuma shafukan yanar gizo masu dauke da dukkan rubuce-rubucensa.

Ya yi suna a kasashen Yamma, saboda yada rubuce-rubucensa da yake yi a duk sadda aka buga. Yakan aika su kyauta ga shahararrun masana kimiyya, da jami'o'n kasasashen turai da Amurka baki daya.  Duk da cewa galibinsu ba su yaba abin da yake yi ko yake rubutawa, amma hakan dai ya yi tasiri wajen jawo hankalin turawa da dama kan ayoyin Kur'ani da ke bayani kan halitta baki daya.  Ga duk mai son karin bayani kan rayuwarsa da rubuce-rubucensa, ana iya samu a shafinsa na yanar gizo da ke: www.harunyahya.com. Da fatan an gamsu.


Amsoshin Wasikun Masu Karatu (1)


A yau ga mu dauke da wasu daga cikin wasikunku. Wadanda na amsa a lokacin da aka turo, na goge su.  Wadanda ke nan a yanzu su ne wadanda ban samu amsa su ba sadda masu sakonnin suka aiko. Akwai wadanda aka aiko ta akwatin Imel, su ma wadannan duk na amsa su.  Sai kuma wadanda suka kira don neman karin bayani. Kada a mance, idan an tashi aiko sako, a rika hadawa da adireshi. Kuma ga dukkan masu sha'awan kasidun da suka bayyana a shafin nan cikin shekarar da ta gabata, a halin yanzu na loda su gaba daya cikin shafukanmu da ke Intanet.  Idan kasidun Kimiyyar Sadarwa ne zalla, a je shafin da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com  idan kuma na sauran fannin ilmin kimiyya ne zalla, sai aje wannan shafin: http://kimiyyah.blogspot.com Da fatan za a dace.

…………………………………………………..

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alheri tare da daukacin musulmai. Don Allah ina so kayi min bayani a kan "Hacking." Wassalam, ka huta lafiya. Muhammad U. Bala, daga unguwar Kofar Ruwa "B" karamar hukumar Dala, jihar Kano. 08069367793

Wa alaikumus salam Malam Muhammad, da fatan kana lafiya. Ina godiya da addu'arka. A baya bayanai sun gabata masu tsawo kan kalmar "Hacking" da "Hackers", wato dandatsanci kenan, ko aikin fasakwaurin kwamfuta.  Abin da wannan kalam ke nufi shi ne tsarin amfani da kwarewar ilmin kwamfuta wajen aiwatar da wasu ayyuka na amfani ne ko cutarwa.  Kalma ce mai harshe biyu wajen ma'ana.  Asali ana amfani da ita ne ga 'yan dandatsa, matasa ko kwararru masu amfani da kwarewarsu wajen aiwatar da ta'adanci ta hanyar kwamfuta da Intanet; ko sace bayanan sirri, ko yada kwayoyin cutar kwamfuta, ko leken asirin abin da mutane ko ma'aikatan hukumomi ke yi.  Amma da tafiya tayi nisa, sai aka canza wa kalmar ma'ana, inda a galibi ake amfani da kalmar da manufar kwarewa wajen sarrafa kwamfuta da aiki da ita.  Duk wanda aka kira shi da "Hacker" kuma ana daukansa a matsayin kwararre ne wanda ya san makaman amfani da sarrafa  kwamfuta.  A yayin da ake amfani da kalmar "Cracking" ko "Crackers" wajen nufin masu aiwatar da ta'addanci. Duk da wannan canji dai har yanzu akan yi amfani da kalmar ne wajen nufin masu aiwatar da ta'addanci ta hanyar kwamfuta da Intanet.  Da fatan ka gamsu.

Baban sadiq sannu da aiki, Allah ya kara basira kuma ya raya mana sadik.  Daga Lauwali Ja'afar mai nema ga Allah, dan (Niger), Malali, Kaduna.

Lauwali barka dai, ina godiya matuka da addu'arka, kaima Allah kara maka basira, ya kuma ba ka wadatuwa wajen nema ga Allah, da'iman. Amin.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, kuma na dauki dogon lokaci ina karanta shafin nan naka. Ba abin  da za mu ce sai dai Allah ya saka maka da alheri.  Mutane suna karuwa sosai da abin da kake rubutawa a duk mako.  Ina son yin amfani da wannan dama don neman fahimta; me yasa idan mutum ya aika sako a daga wasu wayoyi kamar Nokia, za ka iya zuwa wani wuri ka ga kwafin sakon da ka aika  ko ka tura, amma a Tecno ba haka abin yake ba?  A huta lafiya.  Suna na Usman, ina cikin Lafiyan Barebari: 08135433503

Wa alaikumus salam, ina godiya matuka da wannan sako. Kamar yadda kace, ana dai iya kokarin wajen fadakarwa kamar yadda ya sauwaka. Allah sa mu dace, amin.  Dangane da tambayarka, abin da ke faruwa shi ne, a Tecno din ma akwai inda za ka je ka ga sakon, sai in ba a saita wayar a haka ba.  A ka'ida, kowace waya tana taskance sakonni na kira da sakonnin tes da ake aikawa daga gare ta zuwa wasu wayoyi ko layukan, amma da sharadin idan an saita wayar don gudanar da wannan aiki.  Don haka akwai alamar ba a saita wayar don ta rika taskance sakonnin da aka aika daga gare ta ba shi yasa.  Idan kana bukata sai ka "Menu", ka shiga "Message", sai ka gangara "Settings," ka shiga inda aka ce "Save Sent Messages," sai ka matsa "Yes" ko wani abu makamancin hakan.  Daga nan duk sadda ka aika sakon tes, wayar za ta taskance masa su, don komawa gare su a duk sadda kake so.  Da fatan an gamsu.

Salamun alaikum  Baban Sadik, har yanzu ban gaji da tambayarka ba dai!  Ka ba ni cikakken bayani a kan Bermuda triangle.   Dangana Musa Azare

Wa alaikumus salam, Malam Dangane, bayanai kan Tsibirin Bamuda sun gabata a wannan shafi. Mun rubuta ko gabatar da kasidu sama da shafuka 12 kan asali da yadda wannan tsibiri yake, da irin abubuwan da suka faru, da ra'ayoyin masana kan haka, da kuma rubuce-rubucen da aka yi akai. Idan kana bukatar wadannan kasidu, ko dai kaje shafinmu na Intanet da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com ko http://kimiyyah.blogspot.com, ko kuma ka turo adireshin Imel sai in tunkudo maka kasidar gaba dayanta ka dabba'a don karantawa.  Da fatan ka gamsu.

Fatan alheri a gare ka. Fatana Allah ya kara maka daukaka, da hakuri da mu. Malam Imail di na ne ya samu matsala, na shiga sai aka ce mini: "Where Did U Meet U Spouse?" -  Ali Jauro

Godiya nake da addu'a Malam Aliyu. Abin da ke faruwa shi ne, watakila ka saba shiga akwatin Imel dinka ne ta hanyar wata waya ta musamman, amma sai ka samu canji.  Duk sadda ka zo shiga da wata wayar daban, ko ta hanyar kwamfuta, masarrafar za ta gane cewa ba ta hanyar da ka saba shiga bane ka shiga, ma'ana kamar ba kai bane, wani ne ke kokarin shiga akwatin naka da karfi. Don haka sai a nemi tantancewa, ta hanyar aiko maka da tambayar da ka amsa sadda kake bude akwatin Imel din.  Wannan shi ne abin da ya faru.  Don haka, sai ka rubutu musu amsar da ka sa a sadda kake bude Imel din.  In kuwa ba haka kayi ba, to zai yi wahala su baka daman shiga.  Da fatan ka gamsu.

Salam, don Allah ka taimaka min da hanyar da zan gyara shafina na Facebook a Privacy kamar yadda ka gaya min, domin na shiga amma na kasa fahintar yadda zan gyara, kuma har yanzu ana yi min satar fage a shafin nawa.  Da fatan za ka turo min ta layi na. Na gode daga Aminu Garba Dirimin Sambo Kano

Wa alaikumus salam, Malam Aminu ka gafarce ni, domin na riga na goge tes din da ka aiko a waya ta, sai wanda na taskance a kwamfuta di na.  Abin da nake tunani shi ne, ko dai ka taba ba wani kalmomin izinin shiganka (Password), ko kuma 'Yan Dandatsa, wato "Hackers" sun shiga shafin naka. Wannan ba wani bakon abu bane.  Don haka, idan ta waya kake shiga, da zarar ka shiga shafin sai ka gangara kasa inda aka rubuta "Settings" ka shiga, a nan za ka ga dukkan zabe-zaben da ke ciki masu taimakawa wajen kariya.  Idan damuwanka shi ne wasu suna iya yin rubutu a shafinka, ko bangon shafinka, wato "Wall" kenan, ina iya cewa wannan ba wata damuwa bace.  Amma idan kana son hana hakan.  In har wannan ne matsalarka, to a gaskiya ba wata matsala bace kamar yadda kake riyawa.  Amma idan kana samun sauye-sauye ne a shafinka wadanda har ga Allah ka san ba kai bane kayi su, sannan bai kamata a ce wani ya yi su ba kai ba, to, shawarar da zan bayar kawai ita ce, ka kulle shafin (Deactivate), sannan ko bude wani daban, sabo.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, gaskiya muna jin dadin wayar mana da kai da kake. Malam ina da wata mastala da take damu na kullum.  Idan zan taba rediyo sai ta buge ni da sinadaran lantarki, ko in zan kunna na'urar DVD ma haka ne.  Amma da wani zai taba ba zai samu wannan matsala ba.  Kuma ko da rediyon na aiki da batir ne, idan na taba karfin lantarkin na iya ja na.   Abin yana damuna.  Meye mafita? Na gode. Daga mai son shawararka a kullum; M. Adamu shushaina, Dikko, Jahar Naija.

Wa alaikumus salam, Malam Adamu. Ina godiya da addu'o'inku. Allah saka da alheri, amin.  Dangane da wannan matsala na jan sinadaran maganadisun lantarki da kake samu kan duk abin da ka taba, zan so ba da shawaran ganin likita ko wani kwararre kan harkar wutar lantarki.  Musamman ganin cewa idan kai ka taba  kana samun matsala, amma duk wanda ya taba ba ya samun ja daga sinadaran maganadisun lantarki.  Amma kafin nan, abin da na sani sh ne, akwai hanyoyin gudanuwar maganadisu/wutar lantarki guda biyu. Na farko shi ne ta yin amfani da wayoyi, don daukan wutar lantarki daga wani  wuri zuwa wani, ko daga wata na'ura zuwa wata, ko daga wani bangare zuwa wani bangare.  Wannan shi ake kira "Current Electricity."  A daya bangaren kuma akwai tsarin gudanuwar wutar lantarki sanadiyyar haduwar abubuwa biyu masu akasin dabi'a (tsakanin mahallin namiji – Positive – da mace – Negative).  Wannan yanayi shi ne wanda muhalli ke samar da shi.  Ma'ana, a duk inda dan adam ke rayuwa ana samun wannan tsarin gudanuwar lantarki.  Yana samuwa a jikin abubuwan daki, kan mota, ko a jikin tufafi, a tsakanin kayayyakin lantarki, kamar yadda kake samu. 

Bayan haka, yanayin jan wutar lantarki sanadiyyar taba kayayyakin lantarki kamar rediyo a misali, yana samuwa ne sanadiyyar maganadisun lantarkin da babbar masarrafar rediyo ko talabijin ke bazawa zuwa sauran bangarorin rediyon, ko da kuwa a kashe take.  Wannan babbar masarrafa ita ake kira "Capacitor", wanda ita ce ke gudanar da wutar lantarki a tsakanin rediyon a sadda take kunne. Da zarar an kashe, wannan yanayin lantarki ba ya gushewa, sai a hankali.  Don haka, da zarar hannu ya taba, nan take ragowar wannan sinadaran lantarki zai tunkude shi gefe.  Abin da ke haifar da hakan kuwa shi ne ragowar karfin lantarkin da wannan masarrafar lantarki ta taskance, kafin ya bi iska.  Hakan nan akan samu sinadaran lantarki a jikin tufafi mai kaushi musamman, da jikin mota, ko cikin daki, ko a tsakanin gashin kan mutum, muddin wadannan abubuwa suka yi kacibis da wani abu da ke dauke da sinadararan lantarki da ke samuwa a muhalli.  Wannan tsarin samar da sinadaran lantarki shi ke kira "Static Electricity."  Don haka, idan a cikin daki ne, kana iya bude tagogin dakin, ko kayi amfani da na'urar dumama daki (Heater) don kore wannan yanayi na lantarki.  Da fatan ka gamsu.

Baban Sadik, Rabbi yai sakamako da aljanna.  Na dade ban bude akwatin Imel di na ba, na sa kalmar shiga (Password) sai ta aka ce mini: "Wrong password." Kuma da shi nake shiga shafin Facebook.  Abul Waraqaat

Malam Rabi'u Isa barka ka dai.  Wannan ke nuna cewa lallai ka mance kalmar shiganka ne.  Don haka a kasa za ka ga inda aka ce: "Forgot Your Password?"  ka matsa, za a kaika inda za samu bayani kan yadda za ka warware matsalar. Da fatan an gamsu.

Salam, fatan alheri. Wallahi duk lokacin da zan shiga Shafin Facebook, sai a ce min dole sai na sa Confirmation Mail, kuma Gmail ya ki budewa.  Ya zan yi?  Sako daga Yahuza Idris, Hotoron Arewa

Abin da wannan ke nunawa shi ne, baka shiga shafinka ta hanyar da ka saba shiga ba, kamar yadda nayi bayanai makamancin wannan a sama.  Don haka, sai ka nemi kalmar shigan Gmail dinka, tunda da adireshin Imel ka bude shafin ba da lambar waya ba, ka je akwatin Imel din, akwai sako mai dauke da "Kalmar Tantancewa" (Confirmation Code) da suke aikawa a duk sadda aka bude shafin Facebook.  Wadannan kalmomi su za ka dauko ka saka, sai a baka damar shiga.  Da fatan an gamsu.

Wednesday, February 13, 2013

Katsina 2013: Rayuwar Matasa a Dandalin Abota na Intanet


Wannan ita ce kasidar da na gabatar a taron TSANGAYAR ALHERI na shekara shekara, wanda aka yi a makera Motel da ke hanyar Daura a Katsina birnin Dikko.  Duk da cewa a baya na gabatar da wasu daga cikin abubuwan da ke kasidar, amma da yawa daga cikin al’amuran da ta kunsa baki ne ga mai karatu. A sha karatu lafiya.


Wata Sabuwar Duniya

Ray Lam dai wani matashi ne a birnin Vancouver na jihar British Colombia da ke Æ™asar Kanada; ya gama jami'a, ya kuma yi ayyuka sosai wajen ganin ci gaban rayuwarsa.  Ganin haka tasa yayi tunanin shiga siyasa don kawo sauyi a mazaÉ“arsa. Nan take ya kama kamfe, jama'a suka ta zagaye shi: "Sai ka yi…sai ka yi…sai ka yi," kamar dai yadda ake wa 'yan siyasanmu a yau.  Ya shahara sosai har abokan hamayyarsa suka fara neman yadda za su kayar da shi, amma abu ya ci tura.  Sai ta hanyar Dandalin Facebook suka ci nasara.  Yana da shafi inda yake kamfe a dandalin, wanda ke cike da hotunansa na zamanin samartaka.  Daga ciki akwai waÉ—anda ya É—auka yana dafe da Æ™irjin budurwarsa a gidan rawa ana holewa, da kuma waÉ—anda ya dauka masu bayyana al'aurarsa. Nan take suka É—auko waÉ—annan hotuna suka ta rabawa; ana mannawa a wurare. Wannan ya rage masa shahara, da cewa ashe É—an iska ne, har yana bayyana tsaraicinsa ga duniya.  Wannan bai kamata ya zama shugaba ba.  Wannan ya tilasta masa fita daga jerin 'yan takara, abokan hamayyarsa suka samu nasara a kansa.  Babban dalili shi ne katoÉ“arar da yayi wajen É—ora hotunansa marasa kyau, masu nuna rayuwarsa ta baya, wanda hakan ya kai shi ya baro[1].

Jama'a, ina mana barka da shigowa wata sabuwar duniya a cikin wannan duniya tamu, wadda har yanzu bamu gama sanin haÆ™iÆ™aninta ba.  Duniya ce mai cike da annashuwa, da raha, da sauÆ™in rayuwa, da sauÆ™in mu'amala, da sauÆ™in sadarwa, da sauÆ™in yin abota, da hanyoyin samun faÉ—akarwa, da hanyoyin gabatar da faÉ—akarwa, da sauran hanyoyin gabatar da harkokin rayuwa a wani tsari mai kama da haÆ™iÆ™a.  Kai, ba kama bane, rayuwar haÆ™iÆ™a ce, sai dai a wani irin yanayi mai cike da mamaki, irin wanda ke wautar da fahimtar É—an adam.  Domin  a yayin da wannan sabuwar duniya ta mu ke bamu waÉ—ancan hanyoyi na farin ciki da annashuwa da bayaninsu ya gabata, har wa yau dai ita ce ke cike da abubuwan mamaki na baÆ™in ciki, da damuwa, da shagwaÉ“a, da ruÉ—i mara iyaka, da wasu munanan halaye masu jefa mutum cikin irin halin da matashi Ray Lam ya samu kansa a ciki, kamar yadda kuka ji a farko.

Wannan duniya dai ba wata bace illa sabuwar duniyar da ci gaba a fannin kimiyyar sadarwa da fasahar sarrafa bayanai ya tsunduma mu ciki tsundum, daidai gab da Æ™arshen karnin da ya gabata.  Wannan ita ce sabuwar duniyar tsarin sadarwa ta Intanet, wadda a farkon lamari ta faro da 'yan kwamfutocin da basu shige É—ari ba, amma a halin yanzu akwai sama da biliyan uku masu É—auke da bayanai da muke aikawa a tsakaninmu.  Samuwar fasahar Intanet da yadda bunÆ™asarta ya kasance abu ne mai cike da mamaki ga duk wanda ya san asalin lamarin, amma bai kai irin mamakin da ke É—auke da sabuwar duniyar da ta tsiro a cikinta bayan 'yan shekaru Æ™asa da goma da suka shige ba.  Wannan duniya dai Jama'a, ita ce duniyar gamewar mu'amala a mahallin sadarwa. Daga kowace nahiyar duniya a yau jama'a sun game, sun zama É—aya; suna samun sanayya a tsakaninsu.  Wannan ta kai ga samun natsuwa, da kuma ruÉ—uwa, inda aka wayi gari jama'a suka sake; komai na rayuwarsu ma suna iya bayyana shi; cikin rubutu ne, ko hotuna ne, ko zane ne, ko murya ne, ko kuma hoton bidiyo ne mai motsi.  Ba abin da ya shafe su.  Wannan shi ne irin ruÉ—in da ya jefa matashi Ray Lam cikin halin da ya samu kansa.  Ta yaya wannan sabuwar duniya ta tsiro daga mahallin giza-gizanin sadarwa ta duniya?

Samuwar Dandalin Abota a Intanet

Tsarin samar da bayanai a Intanet ya kasu kashi biyu.  Tsarin farko shi ne tsohon tsari; watau hanyar samar da bayanai ta gidan yanar sadarwa.  Wannan shi ne tsohon yayi, kuma shi ne abin da a farkon zamanin mu’amala da fasahar Intanet ya shahara.  Da tafiya tayi nisa, harkar kasuwanci ta fara haÉ“aka a duniyar Intanet, sai ‘yan kasuwa suka shiga binciken sanin hanyoyi ko irin buÆ™atun  da masu sayen hajojinsu a Intanet ke da su ko suke bi.  Wannan ta sa aka fara Æ™irÆ™irar gidajen yanar sadarwa ko mudawwanai masu baiwa mai ziyara a gidan yanar sadarwa damar faÉ—in albarkacin bakinsa kan hajar ko abin da yake so ko yake sha’awa.  A É—aya gefen kuma sai ga manyan gidajen yanar sadarwa – irin su Yahoo!, da MSN, da Google - sun Æ™irÆ™iro hanyoyin da masu ziyara ke haÉ—uwa suna tattaunawa kan buÆ™atunsu na rayuwa, da É—anÉ—anonsu kan rayuwa, da abubuwan da suke buÆ™ata, da dai sauran abubuwan da suka shafe su.  Hakan kuwa ya samu ne ta hanyar Majalisun Tattaunawa da Zaurukan Hira (wato Cyber Communities – ko “Ƙauyukan Intanet”), waÉ—anda kuma suka haÉ—a da Groups, da Internet Chat Rooms, da Communities, da kuma Bulletin Board ko Forums.  A waÉ—annan wurare, masu karatu da masu ziyara da masu saye da sayarwa ne ke tattaunawa a tsakaninsu kan buÆ™atunsu da É—anÉ—anonsu.  Kuma wannan tsari, a harshen Kimiyyar Sadarwa ta Zamani, shi ake kira User Content; wato tsarin samar da bayanai ta hanyar mai ziyara.  Samuwar wannan tsari ne har wa yau, ya haifar da samuwar ire-iren dandamalin abota da ake dasu a Intanet a yau, irin su Facebook, da NetLog, da JHoos, da LinkedIn da dai sauran makamantansu.  WaÉ—annan su ake kira Social Networking Sites[2].

A mahangar Kimiyyar Sadarwar Zamani, idan aka ce “Social Network” ana nufin dandalin shaÆ™atawa ne da yin abota.  Wuri ne ko kace “Dandali” ne da ke haÉ—a mutane daga wurare daban-daban, masu launi daban-daban, masu harshe daban-daban, daga wurare daban-daban, masu matsayi daban-daban, masu matakin ilimi daban-daban, kuma masu manufofi daban-daban.  HaÉ—uwar waÉ—annan mutane a “mahalli É—aya” shi ke samar da wani dandali buÉ—aÉ—É—e, mai kafofi daban-daban, inda kowa ke zaÉ“an abokin hulÉ—arsa ta hanyar masarrafa ko manhajar kwamfuta da aka Æ™irÆ™ira a irin wannan dandali. Kafin mu yi nisa, yana da kyau masu sauraro su san cewa wannan dandali ba wani abu bane illa wani gidan yanar sadarwa ne na musamman da wasu ko wani kamfani ko mutum ya samar don wannan manufa.  Manufar a farko ita ce samar da muhallin da mutane za su tattauna da juna ta hanyar yin abota da yaÉ—a ra’ayoyinsu kan wasu abubuwa da suke sha’awa.  Wannan manufar asali kenan.  Amma a yau wannan manufa ta canza nesa ba kusa ba.  Akwai manufar kasuwanci, da yada manufa ta siyasa ko addini, da samar da hanyoyin bincike kan É—anÉ—anon mutane dake dandalin[3].

Bunƙasar Dandalin Abota a Intanet

Samuwa da yaÉ—uwa da bunÆ™asar dandalin abota a Intanet ya kashe wa zauruka da majalisun tattaunawa kasuwa, duk da cewa har yanzu akwai su.  Dalilan bunÆ™asa da haÉ“akansu kuwa ba nesa suke ba.  Abu na farko shi ne ingantuwar hanyoyin gina manhajar sadarwa tsakanin gidan yanar sadarwa zuwa wani gidan.  Sai yaÉ—uwar na'urorin sadarwa masu É—auke da Æ™a'idar sadarwar Intanet (Internet Protocols) irin su wayoyin salula da dukkan nau'ukansu (kamar su iPhone, da iPad, da iPod, da BlackBerry, da Samsung Galaxy Note da sauransu).  Abu na uku shi ne sauÆ™in hanyoyin rajista a waÉ—annan dandalin abota.  A yayin da ake buÆ™atar dole sai ka kai shekaru 18 kafin ka iya mallakar akwatin Imel, a wajen rajistar mallakan shafi a dandalin abota ana buÆ™atar shekaru 13 ne kacal.  Abu na hudu shi ne bunÆ™asar hanyoyin kasuwanci da nau'ukansu a giza-gizan sadarwa ta Intanet. Abu na biyar shi ne sauÆ™in mu'amala da waÉ—annan shafuka suke tattare dashi.  Duk rashin karatunka kana iya sarrafa su iya gwargwado.   Sai abu na shida, wato ingantuwar tsarin sadarwar fasahar Intanet a Æ™asashe masu tasowa, musamman nahiyar Afirka, da Gabas-ta-tsakiya, da Gabashin Asiya da kuma Kudancin Amurka.

Wannan bunÆ™asa yana da ban al'ajabi matuka.  Domin ba matasa kadai ya game ba, har da manya, da tsofaffi, da kuma kananan yara.  Ba 'yan birni kadai abin ya shafa ba, har da 'yan karkara, da makiyaya. Kai, lamarin ma ya hada da nakasassu ta É“angaren gani da ji; duk ba a barsu a baya ba.  Shahararru daga cikin dandalin abota da aka fi shawagi a cikinsu dai su ne: Dandalin Facebook, da Dandalin Twitter, da Dandalin Instagram, da Dandalin Pinterest, da kuma Dandalin Google+.  WaÉ—annan dandamali dai ana ji da su a Æ™asashen duniya, saboda tasirinsu wajen kame zukatan masu mu'amala da su.  Abin ya wuce hankali da sanin ya-kamata.

Dandalin Facebook, wanda ya faro daga É—aliban jami'a zuwa 'yan sakandare shekaru 8 da suka gabata, a yanzu yana da mambobi masu rajista a duniya sama da biliyan 1.2!   Mutum miliyan 4 ne suka "so" jawabin nasara da shugaba Obama ya rubuta a shafinsa na Facebook.  Kashi 25 cikin masu amfani da shafin Facebook basu damu da wata kariya ba.  A duk wata a Æ™alla mutum miliyan 800 ne ke shiga Dandalin Facebook.  Mutum miliyan 488 ne kuma ke mu'amala da shafin Facebook ta wayar salula. Sama da kashi 23 kan shiga shafinsu na Facebook sau biyar a duk yini.  A Æ™alla akan shigar da hotuna sama da miliyan 250 a duk rana.  Zuwa Æ™arshen shekarar 2012, an saurari waÆ™oÆ™in da tazarar lokacinsu ya kai tsawon shekaru 210,000 a Dandalin Facebook.  Kashi 80 cikin 100 na masu neman hajojin kasuwanci sun fi son samunsu ta hanyar Dandalin Facebook.  Kashi 43 cikin masu mu'amala da shafukan Facebook maza ne, a yayin da sauran kashi 57 É—in duk mata ne[4].

A É“angaren Dandalin Twitter ma haka lamarin yake.  A tsawon kwanakin shekara ta 2012, duk rana masu mu'amala da Dandalin Twitter kan aika sakonni miliyan 175.  Ya zuwa yanzu tun bayan buÉ—e shafin Twitter, an samu saÆ™onni sama da biliyan 163.  Jawabin nasarar shugaba Obama ne yafi kowane saÆ™o yawan tallatawa, yayin da aka tallata shi (retweeted) sau miliyan 800!  Lokacin zaÉ“en Æ™asar Amurka da ya gabata an aika da saÆ™onnin da suka danganci zaÉ“e wajen biliyan 31.7!  Cikin masu amfani da fasahar Intanet gaba É—aya, kashi 32 na amfani da masarrafar Twitter.  A tsawon kwanakin shekarar 2012, a duk rana an samu masu rajista a Æ™alla miliyan É—aya.  Shafin da jama'a suka fi bi a Dandalin Twitter shi ne na shahararriyar mawaÆ™iya Lady Gaga, inda ta wayi gari da masu binta sama da miliyan 31. Shafin kamfanin da jama'a suka fi bi a dandalin twitter kuma shi ne na Youtube, inda ya samu masu bi sama da miliyan 19.  Kashi 50 cikin É—ari na masu mu'amala da Dandalin Twitter na yin haka ne ta hanyar wayar salula.   Kai jama'a, in taÆ™aice muku zancen, a Dandalin Twitter a duk sakwan guda, sai an samu masu rajista mutum 11[5].

Idan muka koma É“angaren Dandalin Google+, wanda bai jima da bayyana ba, za mu ga abin mamaki nan ma. Shafin, wanda gwarazan masana harkar manhajar kwamfuta sama da 500 ne suka gina shi, ya zuÆ™i dala na gugan dala wajen miliyan 585!  A duk rana jama'a kan matsa alamar Google+1 sau biliyan 5!  Cikin kashi 100 na kamfanonin da suka fi yawan dukiya a duniya, kashi 48 na da shafi a Dandalin Google+.  A duk rana mutane sama da 625,000 ne ke amfani da shafin Google+.  Cikin mutum miliyan 400 da suka mallaki shafi a Dandalin Google+, kashi 27 ne masu aure, sauran duk  tuzurai ne; marasa aure.  Cikin wannan adadi har wa yau, kashi 68 maza ne, sauran kashi 32 mata ne.  Kashi 60 cikin 100 na mamabobin Dandalin Google+ kan shiga shafinsu a duk yini[6].

Wannan Æ™ididdiga mai kama da almara, kaÉ—an ne daga cikin abubuwan mamaki da waÉ—annan shafukan abota suke É—auke dasu.  Goma daga cikin mafiya yawansu su ne: Facebook (biliyan 1.2), sai Twitter (miliyan 500), sai Qzone (miliyan 480), sai Google+ (miliyan 400), sai kuma SinaWeibo (miliyan 300).  Sauran sun haÉ—a da: LinkedIn (miliyan 160), da Orkut (miliyan 100), da NetLog (miliyan 95), da hi5 (miliyan 80), sai kuma dandalin MySpace, wanda tuni ya mace (miliyan 30)[7]. 

Idan muka dawo nahiyar Afirka, Æ™asashen da suka fi mu'amala da Dandalin Facebook su ne: Misra (miliyan 12.1), da Najeriya (miliyan 6.7), da Afirka ta kudu (miliyan 6.4), da Maroko (miliyan 5), sai kuma Aljeriya (miliyan 4).  A É“angaren dandalin twitter kuma, Æ™asar Afirka ta kudu ce a gaba, da yawan saÆ™onni sama da miliyan 5 a shekarar 2011.  Sai Æ™asar Kenya da saÆ™onni sama da miliyan 2.  Sai kuma Æ™asarmu ta gado Najeriya, mai saÆ™onni sama da miliyan 1.6.  A nahiyar Afirka, kashi 57 na saÆ™onnin Twitter da ake aikawa duk ta hanyar wayar salula ne.  Kashi 60 cikin masu amfani da Dandalin kuma duk matasa ne 'yan shekaru 20 - 29.  Ƙididdiga kuma ya tabbatar da cewa duk masu rajista a Dandalin Twitter, suna da rajista a Dandalin Facebook, da Youtube, da Google+, da kuma LinkedIn.  A duniya gaba É—aya, kashi 23 cikin masu mu'amala da shafukan abota a duk rana matasa ne[8]. Kuma kamar yadda bayanai suka gabata, matasa sun fi shawagi a Dandalin Facebook, saboda keÉ“antattun siffofin da ya keÉ“anta dasu.  Don haka, sauran bayanan da ke tafe kan tsarin mu'amalar matasanmu a dandalin abota na Intanet, za su taÆ™aita ne kan wannan dandali.

Sana'ar Matasanmu a Dandalin Facebook

A bayyane yake cewa akwai matasanmu da yawa a Dandalin Facebook; tsakanin 'yan mata da samari, da tsofaffi da zawarawa, da gwagware da tuzurai, duk sun yi rajista kuma suna sada zumunci iya gwargwado.  Babban abin da ya sawwaÆ™e yaÉ—uwarsu a wannan dandali kuwa dalilai ne guda biyu.  Abu na farko shi ne samuwar wayar salula a hannun jama'a, wanda ya game gari da duniya baki É—aya.    Abu na biyu shi ne sauÆ™in mu'amala.  Shafin facebook yana da sauÆ™in mu'amala.  Wannan yasa duk wanda ya shiga sau É—aya sau biyu, ba ya buÆ™atar wani darasi kuma.  Cikin amfanin da matasanmu ke samu a Dandalin Facebook akwai sadarwa, da yin abota, da samar da sanayya mai amfani da amfanarwa, da fahimtar rayuwa ta hanyar kallon yadda wasu ke tafiyar da rayuwarsu a duniyar da suke[9].  Akwai kuma samartaka tsakanin 'yan mata da samari, da koyon addini, da siyasa, da raha, da faÉ—akarwa, da kuma sambatu. 

A É—aya É“angaren kuma, akwai majalisu da matasanmu suka kafa masu amfani sosai.  Akwai zaurukan tattaunawa na musamman masu amfani su ma.  Akwai kuma shafukan gwaraza da suka buÉ—e don koyi dasu ko karantarwarsu.  Akwai zaurukan zumunta na musamman.  Wasu daga cikinsu sun haÉ—a da: Zauren Sahabban Manzon Allah (7,608), da Dandalin Marubuta (7,292), da Tsangayar Alheri (4,570), da Dandalin Ilmantarwa da Nishandantarwa (1,614), da Dandalin Tsaraba daga Mimbarorin Jumu'a (1,392), sai Dandalin Tambayoyin Musulunci (273).  Sauran sun haÉ—a da: Dandalin Zauren Sunna (2,845), da Dandalin Buhariyya Zalla (10,293), da Dandalin Siyasa (5,283), da Dandalin Iyantama (13,377), sai kuma Dandalin Dariya (8,801).  A É“anganren shafukan gwaraza kuma akwai shafin Dakta Sheikh Mansur Sakkwato (5,707), da shafin Marigayi Sheikh Ja'afar (23,670), sai Zaure na musamman mai take: Zauren Malam Ja'afar (10,454)[10].  Dukkan wannan adadi, tsakure ne cikin daruruwan shafuka da zaurukan da matasanmu suka buÉ—e kuma suke aiwatar da sadarwa a tsakaninsu a wannan Dandali. 

A É—aya É“angaren kuma, wannan dandali ya baiwa matasanmu wata sabuwar hanyar faÉ—akarwa da karantarwa da tunatarwa da kuma gayyata.  Wanann tsari ya samar da wata hanya ta gayyatar biki, ko suna, ko taro, ko duk wani sha'ani nay au da kullum.  A É“angaren siyasa ma haka abin yake; kowa na bayyana ra'ayinsa yadda yake so, ba tare da tsangama ba.   WaÉ—annan kaÉ—an ne cikin amfanonin da matasa ke samu a wannan dandali.

Manyan Ƙalubale

A duk inda aka ce samari da 'yan mata sun haÉ—u, a yanayin da ba a ganin juna, a yanayi mai jefa hankali da zuciya wata nahiyar nishaÉ—i mai girma, to, dole a samu 'yar karkata.  Domin tatsuniyar Gizo, kamar yadda muka sani, ba ta wuce ƘoÆ™i.  Daga cikin manyan Æ™alubalen da ke fuskantar matasanmu a wannan dandali shi ne na rashin alÆ™ibla a galibin lokuta, musamman a shafukansu.  Wannan ke sa a kashe lokaci ana lilo a shafin Facebook amma in ban da sambatu ba abin da ake yi.  A É—aya É“angaren kuma muna yawan ruÉ—uwa da hotunan 'yan mata.  WaÉ—anda suka fi yawan abokai a shafukansu su ne mata, a duk faÉ—in Dandalin Facebook.  Dalilin hakan kuwa ba sai na gaya muku ba.  Su kansu 'yan matan sun fahimci haka.  Wasu daga cikinsu kan loda hotunan da ba nasu ba, musamman idan ba kyawawa bane su.  Idan ka ga irin yabon da samari ke yi kan hotunan 'yan mata, kare bazai ci kalaman ba. 

Ƙalubale na gaba shi ne rashin kiyaye sirri.  Kowa da irin tsarinsa a rayuwa, amma   wannan ba ya nufin komai na rayuwarka sai ka bayyana wa jama'a a shafinka.  Kada mu mance lamarin marigayiya Cynthia, wacce wasu samari suka ruÉ—a a shekarar da ta gabata, a Æ™arshe suka mata fyaÉ—e, suka kuma kashe ta bayan sun gayyace ta birni Ikko, tun daga jahar Nasarawa.  Da yawa mukan rubuta sirrin rayuwarmu, mu loda hotunan sirri a shafinmu, da duk abin da ya shafe mu, ba tare da tunanin cewa wani na iya dauka ya sarrafa su don wata mummunar manufa ba.  Bayan haka, mu faÉ—aka; akwai jami'an leken asiri na gwamnati da na É“arayi, masu neman inda rauni ko sakaci yake, don tattaro bayanai kafin su aiwatar da aikinsu, mummuna ne ko mai kyau.  Galibin lokuta har wa yau mukan sanar da duniya jujjuyawarmu a shafinmu.  Wanann akwai kuskure a ciki, iya gwargwadon matsayinmu a rayuwa.  Da yawa cikin ta'addancin da ake aikatawa a zamanin yau, tsakanin Æ™asashen turai da namu, masu yin hakan na samun bayanan ne ta hanyar Dandalin Facebook.

Daga cikin Æ™alubale da ke fuskantar matasanmu a Dandalin Facebook akwai matsalar yaudara da Æ™arya wajen bayyana asali da tarihi a shafi.  Wannan matsala ce mai girma. Da yawa cikinmu kan rubuta cewa mun yi makaranta a Æ™asa kaza, ko mu mazauna Æ™asa kaza ne, alhali wataÆ™ila ko Æ™waryar jiharmu bamu taÉ“a bari zuwa wata jiha ba.  Wasu kuma mazaje ne, amma sai su buÉ—e shafi na musamman da sunan mata, da hotunan mata, har da lambar waya na bogi.  Duk wannan bai kamaci mutum natsattse mai dattako ba.  Su ma 'yan mata suna da nasu.  Yaudara cikin zance da yaudara cikin hotuna.  Wasu kan loda hotuna masu motsa tsimin namiji, don su ji me za a ce.  Duk wannan bai kamata ba.  Manyan dalilan da ke haddasa su su ne: sakakkiyar 'yanci, da rashin tarbiyya, da yawan ruÉ—uwa da Æ™yale-Æ™yale, da kuma rigima wajen latse-latse.  Da yawa cikin mutane a wasu Æ™asashe sun rasa rayuwarsu, wasu sun rasa dukiyarsu, wasu sun rasa mutumci da darajarsu, wasu kujeru da mulkinsu, duk ta sanadiyyar latse-latse marasa kan-gado a shafin Facebook.  WaÉ—annan kaÉ—an ne daga cikin Æ™alubale da ke fuskantar matasanmu kan abin da ya shafi mu'amala da juna a Dandalin Facebook.

Hanyoyin Gyara

Ga dukkan alamu wannan tsari na rayuwa a Dandalin Abota dake Intanet wani abu ne da ya zo, kuma akwai tabbacin ya samu gindin zama musamman a zukatan matasa.  In kuwa haka ne, to dole a kullum a nemi hanyoyin gyara cikin tafiyar, tunda tafiya ce doguwa.  Bayan doguwar nazari da bincike kan irin nau'ukan wauta, da sakaci, da ganganci, da gidadanci, da tumasanci, da Æ™auyanci da ke faruwa a Dandalin Facebook, tashar talabijin hukumar Kanada mai suna CBC, cikin wani shirinta na musamman mai take: Facebook Follies, ta nemi shawarar Mista Graham Cluly, É—aya daga cikin manyan ma'aIkatan kamfanin SOPHOS, kuma shahararre a hanyoyin kariyar bayanai da tsarin sadarwa a kwamfuta da Intanet, dangane da hanyoyin da jama'a za su bi wajen samun natsuwa a Dandalin Facebook, sai ya fara da cewa: "Facebook ba kyauta bane, domin sun fi ka riba ma, duk da cewa kana ganin kyauta kake komai a ciki, ba ka biyan kuÉ—i.  To, amma ya kamata mutane su san cewa, duk abin da ka latsa a shafin Facebook, ko ka rubuta a shafinka ko a shafin wani, ko ka "so" (like), ko duk wani hoto da ka loda ko bidiyo, duk kuÉ—i ne a gare su.  A taÆ™aice ma dai, kai ne hajar da masu shafin Facebook ke tallatawa."

Graham Cluly ya ci gaba da cewa: "Ya kamata kuma mu san cewa, duk abin da ka rubuta shi a shafin Facebook, ko wani hoto da ka loda a shafin, to, ka rasa shi kenan har abada.  Domin ba ka da wani iko a kansa. Wani na iya É—aukawa yayi duk abin da yake so a kai."   Abin da wannan batu ke nufi shi ne, in dai kana da wani abu da ka san sirri ne na rayuwarka; hoto ne, bayanai ne, Æ™asida ce, bidiyo ne, sauti ne, to kada ka loda a shafin Intanet.  Domin kamar ka kai kasuwa ne ka ajiye, duk wanda ya masa, zai iya tayawa.  Shi yasa a gaba Cluly ya ci gada da cewa: "Muddin ka san ba za ka iya zuwa tsakiyar kasuwar garinku ka É—aga murya kana gaya wa jama'a sirrin rayuwarka ba, to ko kaÉ—an kada ka rubuta ko loda su a shafin Facebook.  Duk abin da ka san ba ka son kowa ya sani, kada ka rubuta shi a shafin Facebook."  Wannan saÆ™on a fili yake, ba ya buÆ™atar sharhi.

Dangane da abin da ya shafi yin amfani da shafin Facebook wajen aikata miyagun ayyuka da laifuka kuwa, Graham Cluly yace: "Dandalin Facebook ne shafin miyagun laifuka da ayyukan yanar gizo da yafi saurin haÉ“aka a duniya yanzu.  Akwai satar bayanan sirri, da yaÉ—a Æ™wayoyin cutar kwamfuta, da aikata miyagun ayyuka da laifuka da ake yi a Dandalin Facebook fiye da kowane irin shafi a duniya.  Idan kana son zuwa babbar matattarar 'yan ta'addar yanar sadarwar duniya a yanzu, to ka je Dandalin Facebook."  Wani mai sharhi kan harkokin sadarwar Intanet ya sanar da Umar Shehu 'Yan Leman, wakilin BBC Hausa dake Legas, cewa: "Mu'amala a shafin Facebook lalube a cikin duhu. Baka san abu ba bai sanka ba.  Ba ka ganshi ba bai ganka ba."  Wannan shi ne haÆ™iÆ™anin gaskiya wanda babu tantama  a cikinsa.

Kammalawa

A Æ™arshe, rayuwar matasanmu a Dandalin Facebook abu ne da yazo, kuma za a É—auki tsawon lokaci yana tare damu.  Abin da ya rage kawai shi ne neman hanyoyin gyara É—abi'u, da tarbiyyan kai, da manufa Æ™aƙƙarfa, da kiyaye sirri, da kaffa-kaffa da miyagun abokai, da kamewa daga sha'awa mara kangado, da kuma tsantsene.  WaÉ—annan su ne manyan guzurori da suka kamata duk wani mai shawagi a duniyar Intanet na zamanin yau ya riÆ™e su, don samun isa masauÆ™i lafiya lau.  Allah Ya mana jagora, amin.


[1] Cikin shiri na musamman da gidan talabijin CBC ya shirya, mai take: Facebook Follies, cikin shekarar 2012
[2] Dandalin Facebook a Mahangar Binciken Ilmi, Abdullahi Salihu Abubakar, Abuja, 2011
[3] Dubi marji'in sama.
[4] 100 Fascinating Social Media Statistics and Figures From 2012: Brian Honigman, 2012
[5] Dubi marji'in da ke sama.
[6] 100 Fascinating Social Media Statistics and Figures from 2012: Brian Honigman, 2012
[7] List of Social Networking Websites: Wikipedia – http://en.wikipedia.org  
[8] Social Networking Statistics: Statistics Brain, http://www.statisticsbrain.com/social-networking-statistics
[9] Rayuwar Matasanmu a Dandalin Facebook: Abdullahi Salihu Abubakar, Abuja, 2012
[10] Wannan adadin alkaluma na tattaro su ne daga Dandalin Facebook, ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu, 2013, da misalin karfe 6 na yamma.