Friday, June 22, 2007

Rariyar Lilo da Tsallake-Tsallake (Web Browser) #2

Siffofin Internet Explorer 6.0

Hausawa suka ce alkawari kaya ne. Idan mai karatu bai mance ba, makonni biyu da suka gabata ne muka fara koro bayanai kan Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake watau Web Browser, a turance. Mun fadi ma’ana da kuma tarihin yadda wannan manhaja mai muhimmanci ya fara bayyana. Daga karshe, bayan mun gabatar da sunayen wasu daga ciki, muka sanar da mai karatu cewa wadanda suka fi shahara a halin yanzu su ne: Internet Explorer (na kamfanin Microsoft), Firefox (na kamfanin Mozilla), da kuma Netscape Navigator (na kamfanin Netscape). Daga karshe kuma muka yi alkawarin cewa a mako mai zuwa za mu kawo bayanai kan siffofin Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake na kamfanin Microsoft, watau Microsof Internet Explorer 6, tun da ita ce ta fi shahara a wannan bangaren da muke. Bamu samu yin hakan ba cikin makon da ya gabata saboda wasu dalilai da suka sha karfi na. da fatan za a gafarce ni.

Da zaran ka budo wannan masarrafa ta Internet Explorer wacce ka saba amfani da ita, za ka samu a kalla bangarori shida ne, wadanda ke taimaka ma dukkan mai amfani da ita. Wadannan bangarori dai su ne: Title Bar, Menu Bar, Tool Bar, Address Bar, Display Page, da kuma Process Bar. Wadannan bangarori dukkansu kowanne aikinsa daban ne da na dan uwansa; kamar yadda maginin Rariyar ya gina ko tsara su. Kuma duk da yake a wuri daya suke, wani a saman wani, kowannensu manhaja ne mai zaman kansa a can cikin tumbin kwamfutar da kake amfani da ita. Duk lokacin da ka kira daya daga cikinsu, sai kwamfuta ta zakulo maka shi cikin kiftawa da bisimilla, don ya gabatar maka da aikin da kake bukata, sannan ya koma mazauninsa. A halin yanzu ga bayanin kowanne daga cikinsu, a fayyace:

Title Bar

Wannan shine shudin layi ko gurun da ke saman shafin masarrafan gaba daya. An kuma kira shi da wannan suna ne saboda shine ke bayyana maka sunan masarrafa, da kuma sunan shafin gidan yanan sadarwan da kake ciki. Da zaran ka budo shafin gidan yanan sadarwa da Internet Explorer, kana daga kanka sama daga hannun hagu, zaka ga an rubuta “Yahoo! – Microsoft Internet Explorer”, idan gidan yanan sadarwan Yahoo! ka shiga, misali. Idan kuma ka dubi can kuryan dama, zaka samu wasu alamu guda uku, wadanda ke taimaka kara fadin shafin da kake ciki, ko rage zuwa kasa, don budo wani shafi, ko kuma ma ka rufe shafin gaba daya. Na farko ne zai taimaka ma sauko da shafin kasa (minimize), na biye da shi kuma ya taimaka maka kara fadin shafin (maximize), shi kuma na karshen aikinsa shine rufe shafin gaba daya (close). Har way au, idan kana bukatan kara fadin shafin, zaka iya yi ba tare ka je “minimize” ba, a a, sai kawai ka saman Title Bar din sau biyu a lokaci daya (double-click). Shafin zai karu gaba daya, iya fadinsa na asali. Wannan aikin Title Bar kenan.

Menu Bar

Shi kuma Menu Bar shine layin da ke kasan Title Bar, yana daga cikin bangarori masu muhimmanci ga duk mai amfani da masarrafan lilo da tsallake-tsallake. Menu Bar na dauke ne da hanyoyi guda bakwai da zasu taimaka maka aiwatar da wasu ayyuka masu muhimmanci yayin da kake yawace-yawacenka a gidajen yanan sadarwa ta Intanet. Wadannan bangarori ko hanyoyi sune: File (mai dauke da hanyoyin budo wani sabon shafi, ko binciko bayanan da ka ajiye cikin kwamfutarka don loda su a shafin yana, ko adana wasu bayanan da ka samo daga Intanet, zuwa kwamfutarka, ko kuma ya taimaka maka buga - print – bayanan da ka samo masu muhimmanci), Edit (mai taimaka wajen yanko wani bayani da ka gani zuwa kwamfutarka, ko kwafo shafin gaba daya), View (wanda zai kai inda zaka iya kara yawan makaman aikin da ke Tool Bar, ko kuma taimaka maka wajen ganin fasahan da aka gina shafin da kake ciki da shi, watau View Source), Favourites (wanda zai taimaka maka wajen adana adireshin shafin yanan da kake ciki, idan ya kayatar da kai, ko kuma yadda zaka tsara wasu adiresan da ka adana a baya), Tools (zai taimaka maka wajen tsara saitin kwakwalwan rariyarka. Yana daga cikin bangarori masu muhimmanci a masarrafan lilo da tsallake-tsallake. Zaka samu inda zaka tsara makale-makalen da ke tattare da wannan masarrafa, masu taimaka mata aiwatar da wasu ayyuka – Manage Add-ons- sai kuma inda zaka je don tsara yadda masarrafan zata rinka budo maka shafukan yanan gizo, da irin gidajen yanan da zata rinka shiga. Akwai kuma inda ma zaka iya shigar da gidan yanan sadarwan da baka son a rinka ganinsu a kwamfutar gaba daya. Duk wadannan zaka iya gabatar da su ne a Internet Options, mai dauke da bangarorin: General, Security, Privacy, Content, Connections, Programs, Advanced.), sai Help (mai dauke da hanyoyin samun taimako kan dukkan matsalar da ka samu a yayin da kake amfani da wannan masarrafa ta Internet Explorer. Dukkan wadannan hanyoyi, zasu riskar da kai ne zuwa jerin bayanai kan irin aikin da kake so masarrafar tayi maka. Da ka matsa, zasu budo jerin bayanai, sai ka zabi abinda kake so. Shi yasa ake kiran su da suna Menu, kamar yadda zaka je gidan abinci, a kawo maka jerin sunayen abincin da ake dasu, sai ka zabi wanda kake so a kawo maka. Bangare na karshe a Menu kuma wata alama ce da ke can kuryan hannun dama, mai kama da kwallon taswiran duniya (Global Map), ko kuma mai dauke da tutar kamfanin Microsoft. Shi wannan tambari alama ne da ke nuna maka cewa akwai siginar Intanet a yayin da ka budo ko kake yawo a gidan yanan sadarwa, ko kuma babu. Idan ka ga yana jujjuyawa ba kakkautawa, to alama ne da ke nuna cewa akwai Intanet. Amma idan ka ganshi a tsaye cak, to da matsala.

Tool Bar

Wannan shine bangaren da ke dauke da almun da zasu aiwatar maka da wasu ayyuka na gaggawa, ba tare da sai ka je Menu Bar ba. Alamun na dauke ne da sunan nau’in aikin da kowannensu ke yi. Tool Bar na kasan Menu Bar ne. daga hagu zuwa dama, zaka fara cin karo da alamar kibiyar da tayi hagu, an kuma rubuta Back daura da ita. Zai taimaka maka ne wajen dawowa baya daga inda kake, a shafin yanar gizo. Sai kibiyar da yayi gaba, don taimaka komawa shafin da ka fito, idan ka yi baya da farko. Sai alamar Stop, wacce za ta dakatar da masarrafa, idan da farko ka bata umarnin nemo maka wani shafi. Sai Refresh, wacce idan ka ga alamar “Page Cannot Be Displayed”, ita zaka matsa, don ta farfado maka da shafin da kake nema. Sai Home, wacce zaka isar da kai asalin adireshin da aka dabi’antar da masarrafan ka a kai (a Internet Options ake wannan). Da dai sauran alamun da ke wajen, wanda zaka samu kowanne da sunansa ko aikin da zai maka.

Address Bar

Wannan a fili yake; shine farin layin da ke kasa da Tool Bar, kuma aikinsa shine ya zakulo maka gidan yanan sadarwan da kake bukata, ta hanyar shigar masa da adireshin gidan yanar. Idan baka shigar da adireshin daidai ba, bazai gyara maka ba, don bai san manufarka ba. Afuwan da zai iya maka kawai shine ya taimaka maka wajen shigar da haruffan http:// idan ya zama www.yahoo.com kawai ka shigar, a misali. A gaba dashi zaka samu wasu rariyoyin likau da aka tanada maka, wadanda zaka iya matsa su a zarce da kai gidan yanan kai tsaye.

Display Page

Shafin masarrafan kenan, inda zai rinka budo maka dukkan shafin yanar da kake so, idan ka shigar da adireshin daidai kenan. Idan baka shigar da adireshin daidai ba, za t ace maka: Page Cannot Be Displayed. Za kuma ta iya nuna maka wannan alama idan ya zama siginar Intanet ta dauke daga kan kwamfutar da kake kai, saboda tsananin ruwan sama da ake tafkawa, ko kuma tsananin hazo ko yawan masu lilo a inda kake, ko kuma wayar da ke sadar da kai da uwar garke (server) ta cire.

Process Bar

Shi kuma Process Bar shine layin da ke kasan shafin gaba daya. Shima ba zaman banza yake a wajen ba, a a, yana da nasa ayyukan da yake yi, ko ka kula shi ko baka kula shi ba. Ayyukansa muhimmai guda hudu su ne; ya sanar da kai cewa ya gama budo maka shafin da kake nema, ta hanyar “done” da zaka gani a rubuce, ko ya sanar da kai cewa yana kan lalubo maka shafin da kake nema, ta hanyar “connecting to . . . .” da zaka gani a rubuce; ko sanar da kai cewa sauran kadan shafin da kake nema ya gama budowa, ta hanyar “4 items remaining”, da zaka gani a rubuce, a misali. Wazifansa na karshe kuma shine ya sanar da kai cewa akwai siginar Intanet a kwamfutarka ko babu, ta hanyar tambarin taswiran duniya da zaka gani, kamar yadda yake a Menu Bar. Idan ka ga ba ya juyawa, to da matsala. Wadannan su ne siffofin Microsoft Internet Explorer 6.0. Sai dai a wasu lokuta, zaka samu wasu layuka a kasan Address Bar, masu dauke da wasu karikitai wajen taimaka maka gabatar da wasu ayyuka daban, kamar yadda mai karatu zai gani a hoton masarrafan da muka gabatar a sama. Ire-iren wadannan makale-makale ana kiransu Add-ons, ko kuma Plug-ins, a turancin kwamfuta.

Add-Ons/Plug-Ins

Wadannan karikitai su ma manhajoji ne ko masarrafa, masu taimaka ma Rariyar Lilo gabatar da wasu ayyuka, kamar su budo jakunkunan bayanan da aka tsara da wasu manhajojin da kwamfutarka bata zo da su ba, irin su PDF (Portable Document Format) dsr. Har wa yau, su kan taimaka maka wajen sarrafa jakunkuna masu sauti (audio files), da jakunkuna masu dauke da hotuna masu motsi (video files) da dai sauran ayyuka. Wasu kuma su kan taimaka maka ne wajen tattaro maka bayanai ko labaran duniya a takaice (RSS Feeds), don ka samu isa garesu ba tare da kaje gidan yanar sadarwan ba. Wannan tasa manyan gidajen yanar sadarwa irinsu Yahoo! da Google suka kirkiro abinda suke kira Tool Bar (Yahoo! Tool Bar/Google Tool Bar). A wannan sandan manhaja da suka kirikiro, zaka samu manhajoji da dama da zasu taimaka maka gabatar da ayyuka masu muhimmanci, ciki har da nemo bayanai ta hanyar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine). Galibin wadannan manhajo ana samunsu ne a gidajen yanan sadarwa masu bayar da su kyauta. Shahararriya daga cikinsu ita ce Download.com (http://www.download.com). A ciki zaka samu manhajoji muhimmai da zasu taimaka maka gabatar da ayyuka da dama.

Kammalawa

Daga karshe, yana da kyau mai karatu ya budo Microsoft Internet Explorer yin nazari kan dukkan ababen da aka sanar da shi, duk da yake galibin manhajojin da zaka iya dirowa (downloading) da su, na bukatar a ce kwamfutar taka ce. Shi ilimi wani abu ne da saninsa ke da muhimmanci, ko da kuwa watakil mutum ba zai aikata shi ba, musamman kan harkokin rayuwa. Za mu dakata a nan, sai zuwa wani lokaci in Allah. Ina mika gaisuwata ga dukkan masu karatu, Allah Ya bar zumunci tsakaninmu, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent,

Garki II – Abuja.

080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

Friday, June 8, 2007

Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake (Web Browser) #1

Mabudin Kunnuwa

Ga duk wadanda suka saurari shirin Amsoshin Tambayoyinku na sashen Hausa na Muryar Jamus, cikin karshen makon da ya gabata, na tabbata sun ji yadda Malam Mohammad Hashim Gumel ya kwararo ingantattu, saukaka kuma kayatattun bayanai kan yadde ake sanya ma na’urar kwamfuta babban manhajanta (Operating System) ko kara inganta mata shi (Upgrading), musamman ma kan abinda ya shafi yin “hijira” daga tsohon manhajan Windows XP, zuwa sabon manhajan Windows Vista na kamfanin Microsoft Corp. Idan masu karatu basu mance ba, Malam Hashim Gumel dai shine mai gidan yanar sadarwan Gumel.com, watau gidan yanar sadarwan da muka kawo bayanai a kanta cikin makon da ya gabata. Kwararre ne kan harkan kwamfuta da manhajojinta. Ganin cewa dukkan abinda mai lilo da tsallake-tsallake ke yi a kan kwanfuta, na ta’allaka ne da ruhi ko wannann babban manhaja na ta, na ga ya dace mu ajiye masarrafan da muke amfani da ita wajen shiga yanar gizo ko Intanet, a gabanmu, don karantar tsarinta, da kuma yadda take sadar da mu gidajen yanan sadarwan da muke ziyarta a kullum. Wannan masarrafa kuwa ita ce Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake, ko kuma ka ce: Web Browser, ko Browser, a turance.

Ma’ana da Asali

Kalmar “browse” dai a turance na nufin budowa, ba tare da bin ka’idan “daya-bayan-daya” ko “gaba-da-baya” ba. Ma’ana, daga wannan bigire, ka cilla can, ka dawo nan, ka tsallaka can; kamar dai yadda Malam Biri ke yi a saman bishiyoyin kurmi. Idan kuma aka ce “browser, ana nufin abinda ke budowa ko binciko wani abu a wannan tsarin. Wannan a turancin yau da kullum kenan, na gama-gari. A bangaren ilimin kwamfuta kuwa, idan aka ce “Browser”, ba komai ake nufi ba illa wata masarrafa ko manhaja (Software/Program) da ake amfani da ita wajen budo shafukan yanan sadarwa ta Intanet. Duk wanda ke shiga giza-gizan sadarwa ta Intanet a yanzu,yana yi ne ta amfani da wannan fasaha ko manhaja. Amma kafin wannan lokaci ko zamani, ana amfani ne da masarrafar Gopher, wacce ke taimaka ma masu shiga gidan yanan sadarwa ta hanyar rariyar likau kadai, watau Hypertext Links ko Menu Links. A wannan tsari, tsagwaron bayanai kadai ake iya shiga da kuma yawo a ciki; babu hotuna balle sauti. Har wa yau, dukkan shafukan da masarrafan Gopher ke iya budowa, babu launi; daga farin shafi sai bakin rubutu. Kuma wadanda su ka fi kowa amfani da Intanet a wancan lokaci su ne Jami’o’i da kuma cibiyoyin binciken kimiyya da fasaha.

Haka abin ya kasance har zuwa wajen shekarar 1993, lokacin da Baban Intanet, watau Farfesa Tim Barnes-Lee, ya kirkiro ka’idar World Wide Web (www), watau ka’idar giza-gizan sadarwa ta duniya, wacce ta bayar da daman shiga wani shafin daga wani, a ko ina uwar garken take a duniya. Bayyanar wannan ka’ida ke da wuya sai masarrafar Gopher ta zama tsohuwar yayi, domin a yanzu an samu shafuka masu launi, da hotuna masu motsi da marasa motsi da kuma sauti, wanda ke bukatar wasu manhajoji masu kwazo wajen budowa ko sarrafa su. Don haka aka samu wasu kwararrun masana kimiyyar kwamfuta da lissafi suka kirkiro abinda a yanzu muke kira Masarrafar Lilo da Tsallake-tsallake, ko Web Browser, a turance. A lokacin aka samu kwararan rariyar lilo da tsallake-tsallake guda biyu. Wacce ta fara bayyana ita ce Microsoft Internet Explorer 3.0, wacce Bill Gates, tsohon shugaban Microsoft ya kirkira. Daga nan aka samu Netscape Navigator, wacce Mc Andreessen, shugaban kamfanin Netscape shi ma ya kirkiro. Wadannan rariyoyin lilo da tsallake-tsallake guda biyu ne suka kara ma fasahar Intanet shahara a duniya gaba daya. Sanadiyyar su ne aka samu bunkasar harkar kasuwanci ta Intanet a manyan kasashen turai. Gidajen yanar sadarwa na tallace-tallace suka yawaita, suka bunkasa kamar wutar daji. Wannan ya faru ne saboda irin tsarin da suke dashi mai kayatarwa wajen iya budo shafukan yanar gizo masu launi da sauti da kuma hotuna masu motsi da ma marasa motsi. Wannan yanayi shi ake kira The Dot Com Boom, a turance. Daga nan kuma masana fasahar kimiyya suka kara zage damtse wajen kirkiro wasu rariyoyin lilon, irinsu Mozilla, Opera, Kameleon, Surfit, ACE, da dai sauransu. A kalla daga lokacin da aka fara kirkiran wadannan hanyoyin lilo da tsallake-tsallake zuwa yau, an samu rariyoyin lilo sama da dari uku da aka kirkiro. Wasu an daina amfani dasu, saboda rashin shahara ko kuma sauyin yanayi. Misali, an daina amfani da Mozilla a yanzu. A madadinta ne aka kirkiro Firefox (http://www.mozilla.com). An kuma daina amfani da Opera gaba daya.

A halin yanzu wadanda suka fi shahara su ne: Internet Explorer na kamfanin Microsoft (http://www.microsoft.com). Da Netscape Navigator na kamfanin Netscape (http://www.netscape.com). Sai kuma Firefox na kamfanin Mozilla (http://www.mozilla.com). Ita Internet Explorer nau’i-nau’i ce; akwai ta farko, watau Internet Explorer 3.0, daga nan aka samu Internet Explorer 4.0, sai 5.0, sai 6.0, wacce ke kan gama yayinta a halin yanzu, saboda kirkiran Internet Explorer 7.0 da kamfanin yayi, kuma aka fara amfani da ita yanzu. Wannan sauye-sauye na faruwa ne saboda canjin yanayi da ake samu wajen bunkasar hanyoyin sadarwa da kuma tsaron da ake son masu amfani su samu wajen amfani da wannan rariya, idan sun tashi aiwatar da saye da sayarwan da suke yi a gidajen yanar sadarwa. Ita Netscape ta shahara kamar dai Internet Explorer, amma a yanzu kwarjinita ya fara kasa, saboda kalubale da tsoffin kamfanonin fasahar Intanet ke samu a yanzu. Har yanzu ana amfani da ita kam, amma masu amfani da Firefox, ta biyu a shahara bayan Internet Explorer, sun haura masu amfani da Netscape yanzu.

Galibin wadannan masarrafa ana samunsu ne ta hanyoyin gidajen yanar sadarwansu, kyuata. Sai dai idan ka je neman Internet Explorer da ke gidan yanar sadarwan Microsoft, za a bukaci ka yi “gwaji”, don a gane ko babban manhajan kwamfutarka ingantacciya ce, ko a a. Idan ka haye wannan gwaji, sai ka diro (download) da masarrafa, ka mika (run) ma kwamfutarka don ka fara amfani da shi. Idan kuma sabuwar kwamfuta ce ka saya, to daman ta kan zo dashi, ba sai ka saya ba kenan. Dukkan wadannan rariyoyin tsallake-tsallake amfaninsu daya ne, sai dai ‘yan kananan siffofin da suka banbanta su wajen tafiyar da ayyukansu na budo shafukan yanan sadarwa. Idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, zamu kawo kashi na biyu, inda zamu dubi siffofin rariyar lilo da tsallake-tsallake na kamfanin Microsoft, watau Internet Explorer 6.0, wacce galibin mutane ke amfani da ita, da kuma wasu siffofin da suka kebance ta, da rariyar lilon kamfanin Mozilla, watau Firefox. A dakace mu!

………………………………………………………………………………………………

Sabuwar Mudawwana

Malam Hamisu Musa Isa da ke Sheka, Kano, ya bude tasa Mudawwanar mai taken Hikimata, kuma za a same ta a http://bahaushensabonkarni.blogspot.com. Sai a garzaya don karuwa da wannan hikima tasa.

………………………………………………………………………………………………

Wasikun Masu Karatu:

Ga wasu daga cikin wasikun masu karatu nan da suka aiko a lokuta daban-daban. Da dama daga ciki na bayar da amsarsu. Ban kuma kawo sakonnin Imel ba, saboda karancin wuri. Mun gode, Allah Ya saka da alheri, amin.

“…bayan gaisuwa tare fa fatar kana lafiya Allah Yasa haka amin. Dalilin rubuto maka wannan sako shine, ni ma’abocin karanta jaridar Aminiya ne kowane sati, kuma filinka na Kimiyya da Fasaha yana daya daga cikin filayen da nake karantawa kwarai da gaske. Saboda haka nake tambaya kan yadda mutum zai bude adireshin Imel da kuma inda ake zuwa a bude. Ka aiko min cikakken bayani a wannan lambar da na aiko maka da wannan sako. Ka huta lafiya.”

Abdullahi Mohammad Argungu, 080 23578938

“Wallahi ina murna da irin tambihin da kake mana kan Intanet. Kuma ina fatan ka taimaka mani da abinda ya dace a zaure na: http://groups.yahoo.com/group/musulmai

Daga 080 30819598

Assalaamu Alaikum (Baban Sadiq), ina son in shiga Intanet ta wayar hannu, amma ban san yadda zan yi ba. Ina neman taimako a gunka, kan yadda zan yi.”

Mohammad Abbas Lafiya, 080 36647666

“Mal. Abdullahi naji dadin write up dinka a kan Gmail, kuma zan yi sign in, in kara samun gogewa akan IT. God Bless”

Abdullahi Azare, 080 36305226

“Salam, yanzu na gama kammala karanta bayananka a Aminiya na 4 ga wata, kan Mudawwana #2. A gaskiya na sake ilmantuwa.”

Shehu Mustapha Chaji, 080 44191221

“Salam, ina fatan kana lafiya. Na rubuto ne don gaisuwa kawai. Da fatan komai yana tafiya daidai. Na ga gaisuwarka a jaridar Aminiya na makon jiya. Mun gode.”

Muntaka Abdul-Hadi Zaria, 080 36397682

Salam, ina karanta shafinka a jaridar Aminiya, kuma yana kayatar da mu. Ina labarin Gamji Chatroom? Muna bukatar sanin inda aka kwana.”

Salisu Hashim Fagge, 08054361950

“As salaamu Alaikum, Mal. Abdullahi muna jin dadin bayananka, musamman bayani kan gidan (yanar) Kanoonline da kayi. Allah Ya kara basira, amin.”

Sanusi Sani Dala, Suleja, 080 36800241

Wadannan su ne wasu daga cikin sakonninku, kuma muna godiya. Allah Ya bar zumunci, Ya kuma amfanar da mu abinda muke koyo, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent,

Garki II – Abuja.

080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

Tuesday, June 5, 2007

Ziyartan Gidajen Yanar Sadarwa #3

GUMEL.COM (http://www.gumel.com)

Cikin yawace-yawacen da muke yi a gidajen yanar sadarwa a matsayin ziyara, a yau zamu bakonci Zauren Gumel.com ne; gidan yanar sadarwa ta farko da aka fara dorawa a giza-gizan sadarwa ta duniya. Kafin mu ci gaba, zan so sanar da masu karatu cewa wannan ita ce makala ta karshe a wannan silsila da muka dauko na ziyara. Zuwa mako mai zuwa zamu juya akala zuwa wani bangaren kuma, don dada fadada sanayyarmu ga hanyoyin sadarwa ta zamani, in Allah Ya yarda.

Gidan Yanar, Kacokan

Wannan gidan yanar sadarwa ta Gumel.com, ginanniyar gida ne da aka gino daga kwarangwal (template) din manhajar gina gidan yanar sadarwa ta Dreamweaver, wanda kamfani da gidan yanar Macromedia (
http://www.macromedia.com) ta kirkira. Duk da yake kamfanin Adobe (http://www.adobe.com) ta saye wannan manhaja na Dreamweaver, har yanzu akan masa lakabi da sunan kamfanin Macromedia din. To da daya daga cikin kwarangwal dinsa ne aka gino gidan yanar. Kuma shi ma maginin yayi amfani ne da fasahar Java Script wajen kawata hotuna da haruffan da ke dakunan gidan yanar gaba daya. Duk tambarin da ka matsa da dan manunin kwamfutarka (mouse pointer), zaka ga ya canza, ko kuma ya motsa zuwa wani abu daban. Har wa yau, maginin yayi amfani da gajeren fasahan tsara hafuffa da kasidu a dakin gidan yanar sadarwa, watau Cascading Style Sheets, ko CSS a takaice. Da zaran ka shigo zauren gidan yanar, zaka fara cin karo ne da wani babban tambari (Banner) a saman zauren, mai dauke da hotunan Hausawa a zaune a tabarma. A bangaren dama kuma wata baiwar Allah ce cikin lullubi irin na matan Hausawa. A tsakiya ga wani babban tambarin GUMEL, wanda aka masa dogarawa da sunayen wasu daga cikin biranen kasan Hausa; Kano, Zaria, Maiduguri, Abuja. Ga alama dai wannan tambari na kwance ne a kan wani taswira (map) mai dauke da sunayen garuruwan Hausa. Kasa da wannan tambari kuma zaka ci karo da matakalan shiga sauran dakunan gidan gaba daya, watau Navigational Links. Daga nan sai maginin ya raba gidan zuwa bangarori uku, kamar irin tsarin da maginin Kanoonline yayi; bangaren tsakiya, sai hagu da kuma dama. Bangaren tsakiyan a rabe yake daga kwance. Hakan ya bayar da daman sake raba bangaren zuwa kashi uku, sama da kasa.

Abinda ke Ciki

Kamar sauran gidajen yanar sadarwa a Intanet, gidan yanar Gumel.com na dauke ne da bayanai na sauti da hotuna masu motsi da marasa motsi da kuma tarin bayanai (texts). A tsagin hagu na zauren gidan yanar, zaka samu mashigi ne zuwa wasu dakuna da gidajen yanar sadarwa. A sama akwai rariyar likau zuwa Majalisar Hira (Chat Room) na Gumel.com, wanda ba a gama ginawa ko ba. Kasa dashi kuma sai rariyar likau zuwa gidajen yanar sadarwa na wasu mujallu da jaridun Nijeriya irinsu: African News, Daily Trust, Daily Independent, Daily Champion, Guardian, This Day, Vanguard, The Sun, Punch, Triumph, da Nigerian Tribune. Kasa da wadannan kuma sai kafofin da zasu riskar da kai majalisun tattaunawa na Finafinan_Hausa (wanda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya kirkira kuma Malam Magaji Galadima ke shugabanta), da kuma na Gamji.com. A bangaren tsakiya kuma a sama, zaka cin ma BARKA DA ZUWA GUMEL, wanda aka rubuta da manyan haruffa. Kasa dashi kuma zaka ci karo da rariya guda uku, masu dauke da hotuna, da zasu sadar da kai in da za ka samu bayanai kan Kasar Hausa da Tarihinta, da Wakokin Hausa da kuma Littafan Hausa. tsagin da ke biye da wannan kuma zai riskar da kai ne zuwa bangaren Koyon Hausa, da bangaren Tallace-tallace, sai kuma shafin da zai kai ka gidajen rediyon Hausa, irinsu BBC Hausa, da Muryar Amurka (Voice of America), da Jamus (Deustchewelle) sai kuma Sashen Hausa na Rediyon Kasar Sin (China Radion International). Sai bangaren karshe, wanda zai sake riskar da kai ne zuwa Sashen Littafan Hausa da Giajen Rediyo da kuma Wakokin Hausa. A wadannan bangarori, zaka samu wakoki ne na zube, irin wakokin su Marigayi Mamman Shata da sauransu. Har way au, akwai wasu shafukan daban, wadanda basu cikin jerin wadanda na zayyana. Idan mai karatu ya koma kasan tambarin gidan yanar gaba daya, zai ga Shafin Farko, Trihin Hausa, Ma’aikatanmu, Wakokin Hausa, Bayaninmu, Saduwa Da Mu. Wadannan, a takaice, su ne aubuwan da ke cikin wannan gidan yanar sadarwa.

Manufa

Manufar kafa wannan gida a bayyane yake; ilimantar da duniya kan kasar Hausa, musamman ma kasar Gumel (ko Lautai, kamar yadda mai gidan ya kira garin) da masarautar Gumel din gaba daya. Sai manufa ta biyu, wanda it ace koyar da harshen Hausa. wannan shafi ba a gama gina shi ko ba. Alal hakika idan ka shiga wannan gida, zaka amfana da abubuwa da dama, daga littafai zuwa kasidu da wakoki. Don haka wannan ke nuna cewa babban manufar assasa wannan gida shine ilmantar da duniya kan kasar Hausa. Na tabbata wannan na daga cikin abinda tasa aka gina gidan da harshe biyu; Husa da Turancin Ingilishi.

Uban Gidan Yanar (Webmaster)

Mai wannan gidan yanan sadarwa shine Malam Muhammad Hashim Gumel, dan kasar Gumel ne, kamar yadda ya nuna a fili; daga sunan gidan yanar zuwa dukkan abinda ke ciki. Mutum ne mai sha’awar tarihi da al’adu, kuma a halin yanzu yana zaune ne a kasar Amurka. Ya dade a can, a gaskiya. Kuma shine wanda ya fara gina gidan yanan sadarwa da harshen hausa a giza-gizan sadarwa ta duniya (a iya sani na), kafin zuwan su Dandali da Kanoonline. Shi yake tafiyar da wannan gidan yanar sadarwa tare da wani bawan Allah mai suna Abba Dauda Abba. Allah Ya saka musu da alheri, amin.

Shawarwari

Yana da kyau a yi kokarin hanzarta karasa gina Zauren Hira (Chat Room), wannan na daga cikin abinda ke kara ma gidan yanan sadarwa shahara da yawan maziyarta. Sai kuma wasu ‘yan kurakuran rubutu (typographical errors) da nai ta cin karo dasu cikin shafuka daban-daban. Misali, a shafin Tarihin Hausawa, an rubuta “arewacin Nijeriya” da “arewancin Nijeriya”, watau an kara harafin “n”, wanda bai kamata a shigar ba. Bayan haka, akwai matsalar lahaja (dialect); misali, an yi amfani da kalmar “tarishi”, maimakon “tarihi”, kamar yadda yake a daidaitacciyar Hausa. Allah sa mu dace gaba daya, amin.

Kammalawa

Daga karshe, za mu dakata a nan, sai wani mako in Allah Ya kai mu. Kamar yadda na sanar, mako mai zuwa za mu koma wani banganren, don fadada fahimtarmu kan hanyoyin fasahar sadarwa ta zamani. Kada a mance a kai ziyara zuwa Mudawwanarmu da ke:
http://fasahar-intanet.blogspot.com.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent
Garki II – Abuja.
080 34592444
fasaha2007@yahoo.com
http://babansadiq.blogspot.com