Friday, March 14, 2008

Fasahar Sadarwa ta "Infra-Red"

Gabatarwa

A yau mun dawo don ci gaba da bayani kan tsarin sadarwa ta wayar iska, inda zamu yi bayani kan wani tsari, makamancin tsarin da ya gabata na Bluetooth. Wannan tsari shine tsarin sadarwa ta amfani da fasahar sadarwa ta Infra-red. Kamar tsarin sadarwa ta Bluetooth, Infra-red ya kunshi tsarin sadarwa ne daga wani kayan fasahar sadarwa zuwa wani, amma a iya tazaran da bai kai na Bluetooth ba. A yau zamu ji tarihin wannan tsari ; yaushe ya samu, me da me ake yi dashi, yaya tsarin ke kasancewa, wasu irin kayayyakin fasahar sadarwa ne ke amfani dashi, kuma me ye alakar da ke tsakanin fasahar sadarwa ta Bluetooth, da na Infra-red ? Idan mai karatu na tare damu, duk zai samu wadannan bayanai cikin yardan Ubangiji. A biyo mu :

Ma’ana da Tarihin Infra-red

Kalmar Infra-red, kalma ce mai dauke da bangarori biyu ; bangaren farko shine Infra ; na biyun kuma Red. Wannan tasa a galibin wurare zaka ga ana sanya alamar ‘dash’ a tsakani, watau a rubuta Infra-Red, maimakon Infrared, kamar yadda muka saba fada da rubutawa a lokaci guda. Ko a cikin kamus din turanci da galibin manyan littafan kimiyyar fasahar sadarwa ta zamani, sukan raba kalmomin da alamar da ke nuna cewa bangare biyu take kumshe dashi. To me wannan kalma ke nufi ? Bangaren farko watau Infra, kalma ce da aka tsakuro daga harshen Latin, kuma yana nufin “kasa da” wani abu, a misali. Shi kuma bangare na biyu, watau Red, kalma ce ta turanci, wacce ke nufin “launi ja”. Kenan, abinda Kalmar Infrared ke nufi shine: kasa da launi ja! Wannan fassara ce ta zahiri. Amma a fasahance idan aka ce Infra-red, ana nufin hanyar sadarwa ta zamani wacce ke amfani da makamashin harske kasa da launin ja, mai dumi, da ke taimakawa wajen sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa na zamani. An kuma siffata wannan nau’in haske ne da Infra, saboda kwayan ido baya iya tsinkayarsa. Ba kamar sauran nau’in haske irin na rana da muke tsinkaya har mu ji ya ishe mu ba. An gano tasirin wannan yanayi ko makamashin haske ne shekaru dari biyu da suka gabata, inda aka lura da cewa akwai wani tasiri mai amfani da ke taimakawa wajen gano abubuwa da dama ; daga aikawa da sauti zuwa gano darajar yanayi ; daga gano cututtuka zuwa aikawa da sakonni ; daga daukan hoto zuwa magance cututtuka, duk ta amfani da haske da ke samuwa a wannan sararin samaniya da Allah Ya hore mana !

Asali da Bunkasar Makamashin Infra-red

Tsarin gudun haske da maimaituwar sa da ke samuwa a sararin samaniya, watau Electromagnetic Wave, na da bangarori biyar ko shida, kuma kowanne daga cikin su na da nashi aiki wajen taimaka ma dan Adam yin wani abu da zai amfane shi (idan ya binciko kenan ko gane hakan), ko kuma iya cutar dashi, idan ya shantake yaki bincikan tasirin wannan haske dake darsuwa a muhallin sa a kullum. Banganren farko shine tsarin haske mai dumi na lantarki mai takaitaccen maimaituwa, amma mai cin dogon zango wajen aikawa da sako na sauti. Wannan shi ake kira Radio Waves, kuma dashi ne ake iya aikawa da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin da kuma shi ne har wa yau, ake amfani wajen gina na’urar hangen nesa da ke dukkan filayen jirgin sama, watau Radars. Yana daukan dogon zango, amma yana da takaitaccen maimaituwa, watau Frequency rate. Sai kuma mai biye masa, watau tsarin haske mai tattare da dumi, mai taimakawa wajen dafe-dafe, kuma da wannan tsari ake amfani wajen tsara na’urar dumama abinci da sauran kayayyakin makulashe,watau Microwaves. Sai kuma na uku, wanda haske ne da ke tattare da dumi da kuma launi, amma kamar sauran tsarin hasken da suka gabata, dan Adam ba ya iya ganinsu da idon sa; kasa suke da ganin sa, sai dai kawai ya ji su. Wannan shine tsarin hasken da ake kira Infra-red, kuma ana amfani dashi wajen yin abubuwa da dama, ciki hard a aikawa da sakonni a tsakanin kayayyakin sadarwa na zamani. Sai tsarin haske na gaba shine wanda ya kumshi launuka bakwai da ake dasu a Bakan Gizo, watau Rainbow (Red, Orange, Blue, Yellow, Green, Indigo & Violet). Wannan nau’in haske shine hakikan haske da muke samu daga rana amma wanda ke riskan mu a wannan duniya da muke ciki; tataccen haske kenan, watau Visible Light. Bayan wannan sai kuma nau’in haske mai tsanani da ke samuwa daga rana; gundarin hasken kenan, wanda ke fitowa kai tsaye daga rana. Ba halittar da zata iya jure masa. Wannan shi ake kira Ultraviolet Light, kuma yana da saurin maimaituwa wajen isa ga abinda ya hasko, mai cin gajeren zango. Idan ya fito daga rana, akwai dabaka-dabaka da Allah Yai masa a sararin samaniya da ke tace shi, ya takaita mana haske da zafin sa zuwa nau’in hasken da muke iya rayuwa cikin sa. Sai kuma hasken na’urar bincike ko hango cututtuka da ke jikin dan Adam ko halittu, watau X-Ray Machine. Wannan nau’in haske ne da ke cin gajeren zango, mai saurin maimaituwa don ya darkake duk abinda aka haska shi gareshi. Da shi ake hasko illolin da ke damun mu galibi a asibitocin mu; dashi ake hango jarirai da lura da halin da suke ciki. Wadannan, a takaice, su ne tsarin gudun haske da maimaituwansa da muke mu’amala dasu a sararin wannan duniya da muke ciki. Kada mu shagala, bayani muke kan tsarin fasahar sadarwa ta Infra-red.

An fara amfani da wannan nau’in sadarwa ne a kayayyakin fasahar sadarwa cikin shekarar 1994, amma kafin nan, ana amfani dashi ne wajen kera na’uran hangen nesa, da wajen magance cututtuka da kuma daukan hotuna daga sararin samaniya. Haka ma na’urar Remote Control da muke amfani da ita wajen sarrafa akwatin talabijin mu, duk da makamashin Infra-red aka gina ta. A takaice ma dai, bayanai sun nuna cewa an yi amfani da makamashin Infra-red cikin yake-yaken da aka yi ta gwabzawa a yakin duniya na biyu. Hukumar da ta kirkiro wannan tsari a kayan fasahar sadarwa kuma ita ce Infra-red Development Association (IrDA). A halin yanzu an shigar da nau’in fasahar Infra-red cikin kayayyakin fasahar sadarwa irin su wayar salula; kana iya aikawa da sakonnin lambobin waya da katittika daga wayar ka zuwa wayar abokin ka; kana iya aikawa da hotanni, da kuma jakunkunan sauti na wakoki ko karatuttuka da sauran bayanai. Haka ma an shigar da wannan nau’in sadarwa cikin na’urar daukan hoto ta zamani (Digital Camera). Bayan ka dauki hotuna, kana iya aikawa da su ta wannan hanya; kana iya aikawa dasu cikin kwamfutar ka, ko kuma na’urar sawwara hotuna ko bayanai, watau Scannin Machine, don ta bugo maka su waje ka gani. Haka na’urar sawwara hotuna daga maaddan su ta asali zuwa bayanai na haske, watau Scannin Machine, tana dauke da wannan fasaha, kuma kana iya shirya alaka tsakanin ta da kwamfutarka, don aika mata da hotuna ko bayanai ta sawwara maka su nan take.. Har way au, akwai wannan fasahar sadarwa cikin kusan dukkan kwamfuta ta zamani, kuma zaka iya hada alakar sadarwa tsakaninsu.

Tsarin Sadarwa

Sabanin fasahar Bluetooth, sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da makamashin Infra-red ya sha banban. Ba a bukatar doguwar tazarar da ta gota taku uku, ko kuma mita guda, watau 1meter. Wannan shi yayi daidai da digiri talatin (30 Degrees). Har way au, fasahar Infra-red na iya aiwatar da sadarwa ne idan ya zama babu wani shamaki komai kankantar sa tsakanin kayayyakin sadarwa biyu. Idan akwai shamaki, ko da na kaurin yadin riga ne, sadarwa bat a yiwuwa. Amma sabanin yadda muka dauka, cewa sai an hada wayar salula jiki-jiki kafin a iya aikawa da sako ta Infra-red, ba haka abin yake ba. Idan an yi haka ba komai, amma ba ka’ida bace cewa dole sai ta haka za a iya sadarwa. Har way au, fasahar sadarwa ta Infra-red ta dara Bluetooth a wurare da dama; baka bukatar sai ka nemi abokin huldan ka ta hanyar barbaran wayar salularsa, a a. Da zaran ya kunna tasa shikenan. Amma Bluetooth dole ne ka bata lokaci wajen neman abokin hulda da kuma barbaran wayar sa. Haka na’urar Infra-red ta fi gaugawa wajen sadar da bayanai, wannan tasa zaka iya aikawa da bayanai masu mizani mai yawa cikin kankanin lokaci, sabanin Bluetooth uwar saibi da nawa; duk kwaskwariman da ake ta mata shekara-shekara. Wannan ya faru ne saboda ka’idar da ke taimaka ma Infra-red sadarwa, watau Very Fast Infra-red Protocol (VIFR Protocol) ta shallake wacce ke isar ma Bluetooth, nesa ba kusa ba. A daya bangaren kuma, wannan bai sa Bluetoth ta gaza ba kwata-kwata; sadarwa ta Bluetooth ba ta bukatar dole sai masu sadarwa na tsaye cif, ba motsi. Kana iya kunna Bluetooth dinka, ka sanya cikin aljihu, ka ci gaba da harkokin ka alhali wani na karban sako daga gareka. Haka fasahar Bluetooth ba ta saurara ma wani shamaki; ko da shamaki ko babu, kana iya aiwatar da sadarwa kai tsaye. Ka ga kowa da nashi maziyyar kenan. A cewan masana ci gaban fasahar sadarwa ta zamani, zai yi wahala wani ya doke wani daga kasuwa. Domin kowanne cikin su na da nashi siffa wacce abokin mukabalar sa ba shi da ita. A takaice dai kowanne na da fagen sa, kuma zasu ci gaba da habbaka lokaci-lokaci, iya gwargwadon yadda bincike ko mu’amala da su ya kama.

Kammalawa

A halin yanzu na san masu karatu sun fahimci tsarin da wadannan kebantattun hanyoyin sadarwa ke bi wajen aikawa da kuma karban sakonni. A mako mai zuwa za mu kawo bayanai, daya na bin daya, kan babban cutar da ke damun masu rike da kwamfutoci a duniya, musamman cikin wannan zamani da muke ciki. Idan akwai sakonnin neman karin bayani a rubuto ta 0803459244, ko kuma a aiko da sakon Imel kai tsaye ta fasaha2007@yahoo.com. Idan ba a gaji da lilo da giza-gizan sadarwa ta Intanet ba, a iya kai mana ziyara a Mudawwanar da muka bude ma wannan shafi da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com. A ci gaba da kasancewa tare da mu.

Tuesday, March 4, 2008

Fasahar Sadarwa ta "Bluetooth" (2)

Matashiya

A makon jiya mun yi tattaki ne zuwa dakin bincike don tsamo bayanai da suka shafi ma’ana, asali, tarihi da kuma bunkasar fasahar sadarwa ta Bluetooth, in da a karshe muka karkare da cewa wannan fahasar sadarwa ta bunkasa ne saboda tasirin ta wajen sawwake aikawa da sakonni daban-daban ta hanya mafi sauki, ba sai an yi ta hakilon jona wayoyi a jikin kayayyakin sadarwa ba. A yau zamu ci gaba da bayani kan nau’ukan kayayyakin da ke dauke da wannan tsarin sadarwa mai kwarjini, da kuma tsarin aikawa da sakonni ta amfani da wannan sabuwar fasaha. Idan hali yayi, za mu zurfafa bayani kan abinda ya shafi “ka’idojin sadarwa” (Communication Protocols) da kuma zangunan da ke sawwake wannan tsarin sadarwa, a fasahance, watau Protocol Layers. A biyo mu:

Kayayyakin Sadarwa Masu “Bluetooth”

A farkon al’amari galibin mu mun dauka wannan fasahar sadarwa ta Bluetooth na dauke ne cikin wayoyin salula kadai. Amma ga duk wanda ya karanta kasidar mu ta makon jiya, ya san cewa akwai kayayyakin fasahar sadarwa da dama da ke dauke da wannan fasaha a halin yanzu. Duk da cewa wayar salula ce nau’in farko wajen samun wannan fasaha a shekarar 2001. To akwai ta cikin wayar salula, ‘yar madaidaiciya, ba yar karama ba. Na tabbata nan da wasu ‘ya lokuta ko shekaru, za a fara shigar da ita cikin kananan wayoyin salula. Idan ka samu wayar salula nau’in Nokia, SonyErricsson, Motorola, da dai sauran su, duk suna dauke da wannan hanyar sadarwa ta Bluetooth. Bayan wayoyin salula, sai kuma kwamfuta, manya da kanana, wadanda ake kerawa a wannan zamani, duk suna dauke da wannan fasaha. Idan ka samu kwamfutar tafi-da-gidan ka, watau Laptop, zaka samu tana dauke da nau’in sadarwa ta wayar iska, watau Wireless Network, wanda ke sawwake mata saduwa da ‘yar uwanta ba tare da an jona mata wayar kebul ba, zaka kuma samu tana dauke da wannan fasaha ta Bluetooth. Don haka, zaka iya aikawa da jakan bayani na sauti (sound files), ko haruffa (text files) ko kuma hotunan majigi (video files). Haka na’urar sauraron wakoki watau MP3 Player, irin ta zamani, duk akwai masu dauke da fasahar Bluetooth. Galibin mutane masu irin wannan na’ura na iya aikawa da wakoki zuwa dukkan wata kwamfuta ko wayar salula mai dauke da wannan fasaha ta Bluetooth. Haka radiyoyin mota irin na zamani su ma yanzu, galibi suna dauke da wannan fasaha. Idan radiyon na kunne, za ka iya aikawa da waken da ake bugawa daga rediyon zuwa ga wayar salular da ke dauke da wannan fasaha, kai tsaye, ba tare da matsala ba. Haka idan kana da na’urar sauraron wake irin ta kunne, watau Headset, galibi su ma suna dauke da wannan fasahar sadarwa. Kana iya aikawa da wakoki daga nan zuwa kowace irin fasahar sadarwa ta zamani da ke dauke da fasahar Bluetooth. Bayan haka, akwai nau’rar daukan hoto irin na zamani, watau Digital Camera, duk su ma sun samu shiga duniyar Bluetooth. Idan ka dauki hotuna, baka bukatar sai ka jona ma kwamfutar ka wayoyi kafin aikawa da hotunan cikin kwamfutar. Kawai sai dai ka kunna na’urar, don aikawa da su kai tsaye ba tare da matsala ba.

Idan muka koma kan na’urar kwamfuta ta kan tebur (Desktop) milsali, tana dauke da hanyar aikawa da sakonni ta Universal Serial Bus, wanda ake kira USB Port. Wannan hanya na dauke ne da ka’idar mu’amala da kwamfuta, kuma hakan na faruwa ne ta hanya makamanciyar ta ; ma’ana, akwai hanyoyin aikawa da sakonni masu irin wannan nau’i, irin su Flash Drive. A halin yanzu akwai irin wadannan kayayyaki da aka tsara su don baiwa kwamfutar da bata da wannan fasaha ta Bluetooth ginanne a cikinka, daman aikawa ko karban bayanai a wannan tsari na sadarwa. Ana kiran su Bluetooth USB Devices. Ba a kwamfuta kadai ba, duk wani kayan fasahar sadarwa mai dauke da irin wannan nau’i na aikawa da karban bayanai, zaka iya lika shi a jiki, don aikawa da karban bayanai. Har wa yau, ta amfani da na’urar buga bayanai na kwamfuta, watau Computer Printer, za ka iya ba ta umarni don buga maka bayanai da ke dauke cikin wayar salular ka mai dauke da fasahar Bluetooth. Haka idan kwamfutar ka na dauke da wannan fasaha, ba ka bukatar sai ka jona na’urar buga bayanai (Printer) da kwamfutarka, a a, sai ka kunna Bluetooth din ka kawai, ka aika da shafukan da kake son a buga maka su cikin sauki. A karshe, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya, cikin shekarar 2007 ne aka kirkiri akwatin talabijin mai dauke da wannan fasaha ta Bluetooth. Abinda wannan ke nufi shine, za ka iya aikawa da shirye-shiryen da ake yi a cikin talabijin dinka, kai tsaye zuwa cikin kwamfutarka ko wayar salularka, idan har tana da mizanin da zai iya daukan bayanan. A karshen wannan shekarar ne har wa yau, aka kirkiri na’ur lasifika ta sauraron FM a cikin mota, mai dauke da wannan fasaha. Wannan na’ura ana kiranta MotoRokr T505 Bluetooth In-Car Speakerphone Digital FM Transmitter. Dankari! Ta amfani da wannan na’urar jin rediyon FM, kana iya karban kiran da aka yi maka ta wayar salular ka, muddin mai kiran ka na dauke da fahasar Bluetooth a wayar sa. Da zaran ya kira ka, maimakon wayar salular ka ta amsa, sai wannan na’ura ta lasisfika ta kashe kanta na wucin gadi, ta fara kara. Zaka iya amsa kira ta lasifikar, da zaran ka gama sai ta ci gaba da watso maka shiri ko waken da kake ji kafin wannan lokaci. Wannan na’ura akan sayar da ita ne a farashin da bai wuce dalar Amurka dari da arba’in ($140.00) ba, wajen naira dubu goma sha takwas kenan nairan Nijeriya. Kamfanin sadarwa ta Motorola ce ta kirkiri wannan na’ura, amma nan da wasu ‘yan lokuta, za a samu irin sa daga kamfanoni irin su Jabra, Nokia Corporation da Parrot. Wadannan, a halin yanzu su ne galibi kuma shahararrun kayayyakin fasahar sadarwa da ke dauke da wannan fasahar aikawa da sakonni ta Bluetooth. To sai me?

Tsarin Aikawa da Sakonni ta “Bluetooth”

Kafin mu yi bayani dangane da tsarin da kayayyakin fasahar sadarwa ke bi wajen aikawa da sakonni ta amfani da na’urar Bluetooth, zai dace mu dubi kadan cikin ka’idojin da ke sawwake wannan sadarwa a farkon lamari. Idan mai karatu bai mance ba, mun sha kawo bayanai kan ka’idojin sadarwa a wannan shafi, kuma muka nuna cewa yardaddun ka’idoji ne da dukkan masu fada-a-ji a wannan fanni suka amince da su wajen sadarwa. Wadannan ka’idoji da aka yarda dasu, su ake shigarwa cikin kayayyakin fasahar sadarwa a fasahance, yayin da ake kera su, don ya zama akwai “fahimtar-juna” a tsakanin su, idan aka tashi hada su alaka da ‘yan uwansu masu wannan sifa ginanniya. Idan muna son fahimtar wannan cikin sauki, mu dubi tsarin kai-komo cikin gari, a mota. Duk mai tuka mota a cikin biranen mu a yau, ya san cewa, da zaran yazo wajen danja ya ga an nuna masa launi ja, to dole ne a gareshi ya tsaya. Idan launin ja ta dauke, aka nuna masa koriyar launi, to sai ya ci gaba da tafiya. Wannan ka’ida, sananniya ce wajen duk masu tukin motoci da ma masu tafiya a kafa. To amma idan babu danja saboda daukewar wutar lantarki, sai duk wajen ya cakude, mutane su kasa fahimtar junansu; kowa so yake ace shi zai wuce ba dan uwansa ba. Don me ? Don babu tsari, kuma babu ka’ida a tsakanin direbobi a yayin da aka rasa sananniyar ka’ida ; kowa ra’ayin sa yake bi.

Akwai ka’idoji masu dama da suka shafi wannan tsarin sadarwa ta Bluetooth, amma guda hudu kawai za mu kawo, don su ne masu siffata mana mafi karancin tsarin da ake bukata kafin hada alaka a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da Bluetooth. Da farko dai, wannan fasahar sadarwa na amfani ne da tsarin aikawa da sakonnin ta siginar rediyo, watau Radio Frequency Waves (RFW), wanda a iliman fasahar aikawa da sakonni ta zamani ake ma lakabi da Spread Spectrum. Wannan tsari na Spread Spectrum shine tsarin da ke aikawa da sakonni ta hanyar nemo siginar rediyo mai alaka da abokin huldan sa, daga mafi karancin zango, sai ya yalwata siginar zuwa zango mafi fadi don sawwake hanyar sadarwan. Wannan tsari na dauke da manyan ka’idoji guda hudu da ke sawwake wannan sadarwa ; akwai Baseband Protocol (BP), watau ka’idar da ke haddasawa ko kuma samar da siginar rediyo (Radio Frequency Waves) don tabbatar da yanayin sadarwa a lokacin da mai son sadarwa ke bukata. Hakan kuma na faruwa ne daga lokacin da ka kunna na’urar Bluetooth da ke jikin wayar salular ka, don nemo abokin hulda da ke da wannan tsari a waya ko abin sadarwan sa. Sai kuma Link Manager Protocol (LMP), wanda ke yin aikin sa da zaran Baseband Protocol ya gama nashi aikin. Shi Link Manager Protocol aikin sa shine haifar da sadarwa a tsakanin wayar salula da wata wayar ko fasaha mai dauke da Bluetooth, don tabbatar da tsarin sadarwan. Wannan ka’ida ce har wa yau ke tabbatar da tsaro ga jakar bayanai da ake son aikawa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwan biyu. Daga nan kuma sai ka’ida ta gaba, watau Logical Link Control & Adaptation Protocol (L2CAP), wacce ke kacalcala bayanan da ake son aikawa daga wayar da ake son aikawa da su, zuwa irin yanayin da suka dace a aika dasu. Idan masu karatu basu mance ba, wannan aiki shi kwamfuta ke yi a zangon Presentation Layer, kamar yadda bayani ya gabata a kasidar Tsarin Aikawa da Sakonni a Tsakanin Kwamfutoci (2). Za a kacalcala bayanan ne, don sawwake tsarin aikawa dasu. Da zaran sun isa masaukin su a daya bangaren, akwai ka’idar da za ta gyatta su zuwa yanayin su na asali. Har wa yau, wannan ka’ida ce ke tabbatar da samun yanayin aikawa da sako mai inganci. Sai kuma ka’ida ta karshe, watau Service Discovery Protocol (SDP), wacce ke zakulo maka dukkan wata wayar salula da ke dauke da fasahar Bluetooth da zaran ka nemo, ta kuna nuna maka sunan da mai wayar ya bata ko kamfanin da ta kirkiri fasahar ta bata. Wannan ka’ida ce ke hada alakar idan ka zabi wacce kake son aika mata. Misali idan akwai wayoyin salula guda biyar masu kunne da Bluetooth din su a yayin da kake neman abokin huldan ka, zaka ga dukkan su, da sunayen su, sai ka zabi wacce kake son hulda da ita. Idan ka zaba, wannan ka’ida ce ke yiwo maka barbaran wacce kake nema, kai tsaye. Wadannan, a takaice, su ne shahararrun ka’idojin aikawa da kuma karban sakonni ta hanyar sadarwa ta Bluetooth, a fasahan ce. A yanzu ga yadda yanayin ke kasancewa, a zahirance.

Aikawa da Sakonni

To kamar dai yadda muka saba ne, idan kana son aikawa da sako ta Bluetooth, abu na farko shine “neman” wayar salular da kake son aika mata da sakon. Wannan shi ake kira Searching, a turancin fasahar sadarwa. Da zaran ka yi wannan, ka’idar da ke lura da wannan aiki zata nemo maka wadanda ta hararo maka su, kai tsaye. Dole ya zama suna tazaran da bai wuce taku talatin ba (30 Feets) ko mita goma (10 Meters) daga inda kake. In sun wuce wannan tazara, ba za ka taba hararo su ba. Idan aka hararo maka su, zaka samu bayanan da suke dauke dasu, ko kuma sunayen da masu su suka basu. Da zaran ka nemo wayar da kake son hulda da ita, sai ta sanar da mai wayar cewa ana neman sa, idan ya amince, ta hanyar matsa Accept”. Idan ya matsa, sai wayar ka ta nemo ka’idojin da suka dace tabi wajen aika sakon, ta kuma lika ma wannan waya da ta barbaro alamar da zata sheda ta wajen aika mata da sakon. Daga nan, sai kuma ta kara binciko cikin wancan wayar, don tabbatar da dacewa da wannan alama da ta lika mata. A ka’ida, dukkan wayar salula ko kayan fasahar sadarwan da take iya saduwa da wata ta wayar iska, na dauke ne da suna da ke cikin rukunin lambobi, wanda ta kebanta dasu. To idan wayar ka ta nemo sunan wannan waya da take son saduwa da ita, ta tabbatar da sunan ta, sai ta bata suna na musamman, sannan sai ta nemo kogo (Port) mafi sauki da zata iya aikawa da sakon, ba tare da mishkila ba. Da zaran ta nemo, sai ta fara Barbara, don sheida ma wancan wayar salula, cewa ‘gani nan tafe’. Idan aka amsa mata, sai ta fara aikawa, kai tsaye. Idan ta gama aikawa, sai ta rufe wannan hanya, tare da yanayin sadarwan. Ita kuma wacce ake barbara, da zaran sakon neman alfarma ya zo mata, sai ta taimaka wajen nemo ka’idar da za ta yi wannan aiki na karban sako. In ta nemo, sai kuma ta zabi kogon (Port) da zai karbi wannan sako, don shigar mata. Da zaran ta gama wannan aiki, sai ta fara sauraron sakon. Da zaran an turo, sai ta karba, kai tsaye. Idan sakon ya shigo kogon da aka tanada masa kafin zuwa, sai ita wannan waya da ta karba, ta rufe kofofin da ta bude da farko, don cika sadarwa. Duk wannan na faruwa ne lokacin da bai wuce dakiku ashirin ba. Illa kawai aikawa da sakon ne ya danganta da yawan mizanin sakon ; idan mai yawa ne, zai dan dau lokaci. Idan kuma kadan ne, nan da nan sai a gama. Wannan tsari na aikawa, a yayin da ake aikawa din, shi ake kira Pairing, ko kuma Point to Point Communication (ko P2P, a lafazin ilimin aikawa da sako ta zamani).

Kammalawa

A karshe, za mu dakata a nan, kuma da fatan an gamsu da wannan takaitaccen bayani mai rikitarwa. Idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, zamu kawo bayani makamancin wannan dangane da fasahar sadarwa ta Infra-Red, wacce ta gabaci zuwan Bluetooth. Na samu sakonnin tambayoyi kan alakar da ke tsakanin Bluetooth da Infra-Red, duk mu yi hakuri. Bayanai na nan tafe. Idan akwai neman Karin bayani, sai a rubuto ta 08034592444, ko kuma a aiko sakon Imel ta fasaha2007@yahoo.com. Haka ma ana iya ziyartan Mudawwanar da ke dauke da dukkan kasidun da ke bayyana a wannan shafi, a http://fasahar-intanet.blogspot.com. Ina mika sakon gaisuwa ta ga masu karatu, musamman masu aiko sakonni ta text ko Imel ko kuma bugo waya. A dai ci gaba da kasancewa tare da mu.