Tuesday, July 1, 2008

Wace Wayar Salula Ta Fi Fitar da Tururin Haske?

Cikin makon da ya gabata ne masu karatu suka karanta bayanai kan irin jita-jitan da ke ta yawo a duniya kan samuwar illolin da ke tattare da tururin da ke fitowa daga kowace wayar salula, da zarar ka fara Magana da abokin maganarka. Duk da cewa galibin masana basu samu tabbataccen tabbaci ba kan alakar da ke tsakanin wannan tururin haske (ionized radiation) da ke fitowa daga wayar salula da kuma cututtuka irinsu sankara (cancer) da rashin tagomashi wajen haihuwa ba, wasu cikinsu sun yarda cewa akwai wannan tururi kuma bazai tafi haka banza ba. Ko dai alakar na bayyana ne bayan tsawon lokaci (sama da shekaru goma) ko kuma ta wata hanya dabam. Wannan tasa gidan yanar sadarwa na CNET (http://www.cnet.com) yayi wani bincike kan wayoyin salular da suka fi fitar da wannan tururin haske a yayin da ake Magana. Wannan tururi, kafin mu ci gaba, yana fitowa ne sanadiyyar alakar sadarwa da ke tsakanin wayar salula da kuma cibiyar yanayin sadarwa ta kamfanin. Wannan alaka shi ke haifar da abinda ake kira Radio Frequency Waves, wanda kuma a nasa bangaren, ke haifar da tururin haske daga wayar da yake sadar da sakon da ya dauko daga cibiyar sadarwar.

Sakamakon da wannan gidan yanar sadarwa ya fitar na nuna cewa akwai wayoyin salula guda goma, a kalla, da suka fi kowanne karancin fitar da wannan tururi, da kuma wasu goma wadanda su suka fi kowace irin waya yawan fitar da tururin. Goman farko sune: kirar LG KG800 na kamfanin LG, da kirar Motorola Razr V3x da Motorola Razr2 V8, na kamfanin Motorola. Sai kirar Nokia 9300 da Nokia N90 da kuma Nokia 7390. Sauran sun hada da kirar Samsung SGH-G800, da SGH-A707 da SGHT809, sai kuma kirar Samsung SGH-E910. Binciken ya nuna cewa wadannan wayoyin salula basu fitar da tururin haske daga cikinsu fiye da kima. Amma goman da ke tafe, sunyi kaurin suna wajen fitar wannan tururi. Wadannan kuwa sune: kirar Motorola V195s, da Slvr L6, da Slvr L2, da Motorola i335, da Motorola Deluxe ic902, sai kuma Motorola W385. Sai kuma kirar RIM BlackBerry Curve 8330 (ta kamfanin sadarwa na Sprint), da RIM BlackBerry Curve 8330 (ta kamfanin Verizon). Sauran sune: kirar T-Mobile Shadow (HTC) da kuma Samsung Sync SGH-CA17. Wadannan, a daya bangaren, su suka fi kowace yawan fitar da tururi daga garesu. A karshe, masu binciken dai sunyi amfani ne da wayoyin salular da ke kan ganiyarsu, ba wadanda kamfanoni suke daina kera su ba. Sakamakon wannan bincike dai na nuna cewa galibin wayoyin salula kirar Nokia na cikin wayoyi masu inganci, masu karancin tururi a yayin da ake amfani dasu.

Labaran Mako

An Samu Alamar Dausayi a Duniyar Mirrik (http://www.bbc.co.uk/news): Binciken da kumbon Phoenix ya kai zuwa duniyar Mirrik (Mars) cikin makonnin da suka gabata na nuwa cewa akwai alamun dausayin kankara a wannan duniya, wanda hakan, a cewar kwararru, alama ce da ke nuna cewa dan Adam zai iya rayuwa a can. Wannan ziyara ta bincike da kumbon Phoenix ya kai zuwa Mirrik cikin watan Afrailu, ziyara ce ta musamman, wadda ta samu goyon bayan masu bincike kan sararin samaniya na kasar Jafan. Masu binciken da ke cikin wannan kumbo sun tafi ne da wani mutum-mutumi (robotic) mai kafafu da hannaye, wanda kuma shine ya kankaro nau’in kasar da ke can duniyar Mirrik, tare da daukan hoton muhalli da kuma ramukan da ya karto wannan kasa. Cikin burbushin nau’in kasar da ya debo ne masana suka samu alamar dausayi mai farin launi. Bayan wasu kwanaki, sai wannan dausayi ya bace daga nau’in kasar da aka debo. “Wannan”, a cewar Dakta Peter Smith, masani kan harkar falaki da sararin samaniya, “alama ce da ke nuna cewa kankara ce, ba wai gishiri, ba”, sabanin yadda wasu masana suke cewa da farkon gano wannan dausayi.

Duk da cewa binciken baya da aka yi a wannan duniya ya tabbatar da samuwar wannan dausayi mai dauke da kankara, babban manufar ziyarar Phoenix ita ce tabbatar da ko dan Adam na iya rayuwa a wannan nahiya ta duniya. Wannan mutum-mutumi dai ya dakatar da aikin tono kasar ne a yayin da daya daga cikin hannayensa ya ci karo da wani tsauri mai tsanani a yayin da yake aikin tonon. Tuni dai mazu wannan ziyara suka sauko wannan duniya tamu lafiya kalau, kuma ana can ana ci gaba da bincike kan nau’ukan kasa da kuma hotunan da kumbon Phoenix ya dauko, don samun tabbacin rayuwar dan Adam a wannan duniya ta Mirrik.

An Harba Kumbon Binciken Yanayi Zuwa Cikin Falaki (http://www.bbc.co.uk/news): Cikin makon da ya gabata ne Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta kasar Amurka, watau NASA, ta harba wani kumbo zuwa falakin wannan duniya don yin bincike na musamman kan yanayin da manyan tekunan duniya ke gudanuwa. Kumbon, mai suna Jason-2 Satellite, ya bar wannan duniya tamu ne safiyar Jumma’a, daidai karfe bakwai da minti arba’in da shida, ta hanyar roket mai suna Delta-2. Wannan bincike ne na hadin guiwa tsakanin kasar Amurka da kasar Faransa, inda ake son gano yanayin manyan tekunan duniya. Ana sa ran sakamakon wannan bincike zai taimaka wa hukumomin da ke lura da yanayi a duniya, ta hanyar samun bayanai masu gamsarwa kan hasashen yanayi a kullum. A lokacin ziyararsa, kumbon Jason-2 zai dauki hoton kusan kashi casa’in da biyar na dukkan manyan tekunan duniya, da karfin gudun ruwa da kuma jihar da galibin tekunan duniya ke bi. Don tantance yadda yanayi zai rika kasancewa a kullum. Jason-2 zai rika aiko da ire-iren wadannan hotuna da yake dauka ne a dukkan kwanaki goma, a yayin da yake yawo cikin falaki. A halin yanzu dai akwai kumbon Jason-1 da ke kai komo cikin falaki don irin wannan aiki. Da zarar ya isa cikin falaki, Jason-2 zai taya shi, inda zasu rika yawo tare, a tazarar da bata wuce na dakiku sittin ba.

Wasu Samari ‘Yan Dandatsa Sun Shiga Hannu (http://news.google.com): Wasu samari biyu a kwalejin Tesoro da ke Orange County a jihar Kalifoniya, sun shiga hannu. An gurfanar da Omar Khan dan shekara shatakwas, da Tanvir Singh shi ma dan shekara shatakwas ne a kotun koli da ke birnin Orange County na jihar Kalifoniya da ke Amurka. A cewar masu gabatar da kara, Omar Khan, wanda dalibi ne a wannan kwaleji, na fuskantar dauri ne sanadiyyar aikin dandatsanci da yayi wa kwamfutocin makarantar, a kokarinsa na canza darajar karatunsa. Khan, a cewar kuliya, ya aikata laifuka sittin da tara sanadiyyar wannan dandatsanci da yayi. Idan kuma ta sameshi da laifi karara, Omar Khan na fuskantar barazanar zaman gidan yari na tsawon shekaru talatin da takwas. A halin yanzu an bayar da belinsa kan dalar Amurka dubu hamsin ($50,000).

A nasa bangaren, Tanvir Singh na fuskantar tuhuma kan cin amanar kasa, da satan bayanai da canza su da kuma dukkan wani laifi da ya shafi yin amfani da kwamfuta wajen aikata ta’addanci. Wannan tuhuma ya biyo bayan kama shi da aka yi ne lokacin da ya samu shiga cikin kwamfutocin makarantar, ta hanyar satar kalmomin iznin shigar malaminsu, tare da kuma dasa manhajar leken asiri (spyware) a kwamfutar malamin (wacce ke jone kan gajeren zangon sadarwar makarantar), don samun damar ganin sakamakon karatunsa ta karshe, inda ya caccanza wasu daga darajojin “C” da “D” da “F”, zuwa darajar “A”, tare da na wasu abokanansa goma shabiyu. Bayan laifin shiga kwamfutar makarantar ba tare da izni ba da kotun ke tuhumarsa, har wa yau ta tuhumeshi da laifin satowa da kuma canza bayanan sirri, tare da bata kwamfutar ta hanyar dasa manhajar kwayar cutar kwamfuta da leken asiri. Sabanin abokinsa Khan, Singh na fuskantar barazanar dauri ne na tsawon shekaru uku.

Har way au, ana tuhumar dukkan samarin biyu da hada wajen tsara hanyar shiga gajeren zangon kwamfutar makarantar, wanda hakan zai basu damar yin yadda suke so da dukkan bayanan da ke cikin uwar garken makarantar gaba daya, musamman abinda ya shafi satar takardun jarrabawan da ba a riga aka rubuta sub a. Sheda a kan haka shine sakonnin wayar salula (text messages) da aka samu a wayoyin kowannensu, masu nuna alaka da abinda ke faruwa. A halin yanzu an daga wannan shari’a zuwa watan Yuli.

Kamfanin Yahoo! Ya Fadada Rumbun Imel Dinsa (http://news.zdnet.com): Kamfanin Yahoo! ya kara fadada rumbun Imel dinsa don baiwa masu bukatar rajistar akwatin Imel damar yi ba tare da matsala ba. Kafin wannan lokaci, manhajar Imel ta takaita ne da uwar garken “yahoo.com” kadai. Duk mai bude akwatin Imel da wannan uwar garke (mail server) yake mu’amala. Wannan tasa a karshe da wahala ka samu irin sunar da ke kake so, sai wanda uwar garken ta zaba maka. Idan ba wadanda suka bude adireshin Imel shekaru biyar da suka gabata ba, zaka samu sunayen adireshinsu na hadawa ne da lambobi (gamagari143@yahoo.com, a misali). Hakan bai rasa nasaba da yawan jama’a da suka yi rajista tsawon lokaci, kuma a ka’idar adireshin Imel, dole kowane adireshi ko suna ya zama shi kadai. Ba a samun sunaye biyu masu kama da juna. A halin yanzu akwai sunayen adireshin Imel sama da miliyan dari biyu da sittin da masu amfani da wannan uwar garke suka kirkira ko bude. Wannan ya tilasta wa hukumomin Yahoo! fadada wannan rumbu don baiwa masu rajista damar yin rajista da irin sunan da suke bukata ba wanda aka tilasta musu ba. Kamfanin ya kara wasu iyayen garke biyu; ymail.com, da kuma rocketmail.com. Rocketmail dai, idan ba a manta ba, tsohuwar manhajar Imel ce da kamfanin yahoo ya saya a shekarun baya, wacce a halin yanzu yake son yin amfani da ita don rajistar masu bude akwatin Imel.

Gidan yanar sadarwa na Yahoo! na cikin tsoffin gidajen yanar sadarwa masu dauke da manhajar Imel na kudi da na kyauta. Kamfanin ya shahara wajen harkar Imel, inda a halin yanzu ya bullo da tsarin shigar da manhajar Imel cikin wayoyin salula irin Blackberry da sauran makamantansu.

Wai Amfani Da Wayar Salula Na Tattare da Cutarwa?

Yaduwar hanyar sadarwa ta wayar salula a duniya ta haddasa jita-jita a tsakanin masu mu’amala da wannan sassaukar hanyar sadarwa. Wannan jita-jita wacce ta shafi irin illolin da ke dauke da wayar salula ko rashinsu, bata tsaya ko takaitu da kasashe masu tasowa ba kadai, hatta a kasashen da suka ci gaba, inda aka kirkiri wannan fasaha, ana samun wannan jita-jita. Kai kusan ma dai ta fi yaduwa ma a can wajensu. Wannan tasa wasu cibiyoyin bincike na asibitoci da wasu jami’o’in da ke wadannan kasashe suka shiga dakunan bincike don gano ko akwai alaka tabbatacciya tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma lafiyar dan Adam, musamman samuwar cutar sankara, ko cancer a turance. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa ba wai cutar sankara kadai ba, akwai jita-jita da dama da ke yawo cewa mutumin da ke yawaita amfani da wayar salula na tsawon lokaci, yana iya zama bakarare, watau ya kasa haihuwa, saboda rashin tagomashin da maniyyinsa zai samu sanadiyyar hakan. To meye hakikanin gaskiyar wadannan jita-jita da ke yawo?

Yaduwar hanyar sadarwa ta wayar salula a duniya ta haddasa jita-jita a tsakanin masu mu’amala da wannan sassaukar hanyar sadarwa. Wannan jita-jita wacce ta shafi irin illolin da ke dauke da wayar salula ko rashinsu, bata tsaya ko takaitu da kasashe masu tasowa ba kadai, hatta a kasashen da suka ci gaba, inda aka kirkiri wannan fasaha, ana samun wannan jita-jita. Kai kusan ma dai ta fi yaduwa ma a can wajensu. Wannan tasa wasu cibiyoyin bincike na asibitoci da wasu jami’o’in da ke wadannan kasashe suka shiga dakunan bincike don gano ko akwai alaka tabbatacciya tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma lafiyar dan Adam, musamman samuwar cutar sankara, ko cancer a turance. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa ba wai cutar sankara kadai ba, akwai jita-jita da dama da ke yawo cewa mutumin da ke yawaita amfani da wayar salula na tsawon lokaci, yana iya zama bakarare, watau ya kasa haihuwa, saboda rashin tagomashin da maniyyinsa zai samu sanadiyyar hakan. To meye hakikanin gaskiyar wadannan jita-jita da ke yawo?


Dangane da abinda ya shafi rashin haihuwa sanadiyyar amfani da wayar salula na tsawon shekaru ko lokaci, wani gidan yanar sadarwa na kwararru kan harkar haihuwa da abinda ke haddasa ko rage samuwarsa, mai suna Reproductive Biomedicine Online, ya tabbatar da cewa babu wata alaka ko hujja tabbatacciya da ke nuna hakan, ko kadan. Wannan tabbaci ya biyo bayan wani bincike ne da wani asibitin haihuwa dake kasar Amurka yayi cikin watan Janairun da ya gabata, cewa ana iya samun raunin kwayar halitta dake cikin maniyyin namiji da ka iya rage masa karfin haihuwa, idan ya dauki tsawon shekaru yana amfani da wayar salula. Sakamakon wannan bincike ya ta’allake ne da nazarin da asibitin yayi kan wasu mazaje dari uku da sittin da daya, wanda ke nuna raguwar karfin maniyyin wadannan mazaje, sanadiyyar tsawon lokacin da suka dauka suna mu’amala da wayar salula a rayuwarsu. Har wa yau, akwai bincike da wata cibiya ta yi kan wasu beraye na tsawon makonni goma shatakwas, inda a kullum ake dumama su cikin tururin walkiyar dake fitowa daga cikin wayar salula a yayin da ake amsawa ko yin Magana da wanda aka kira, na tsawon sa’o’i shida. Sakamakon wannan bincike, Kaman wanda ya gabace shi, shi ma ya nuna samuwar raguwar inganci ko tagomashin maniyyin wadannan beraye daidai wannan lokaci. Wannan tasa masu binciken suka kulla alaka a tsakanin yawaita amfani da wayar salula da kuma raguwar tagomashin kwayoyin haihuwan da ke cikin maniyyin namiji. Sai dai, a nata bangaren, cibiyar magungunan haihuwa mai suna Reproductive Biomedicine Online tace ba lalai bane wannan alaka ta zama tabbatacciya. Idan ma akwai alakar, to bata kai wani matsayin da za ta zama abin damuwa ba. Maimakon haka ma, tsananin gurbatar yanayi (pollution) da yawan shan taba sigari sun fi hadari wajen haddasa rashin haihuwa fiye da hadarin lazimtar amfani da wayar salula.

A daya bangaren kuma, kwararru kan cutar sankara, musamman wacce ta shafi kwakwalwa, ra’ayoyin su sun sha bamban kan samuwar alaka tsakanin amfani da wayar salula da kuma samuwar cutar a kwakwalwar mai yi. Akwai nau’ukan cutar sankara guda biyu da ake danganta samuwarsu ga yawan amfani da wayar salula. Wannan jita-jita, a cewar kwararru, ya samo asali ne sanadiyyar tururin hasken da ke fitowa a yayin da mai amfani da wayar salula ke yi, wanda kuma ke shigewa kai tsaya zuwa kwakwalwarsa. Hakan, a cewar wasu masu binciken alaka, kan haddasa samuwar wani curin tsokar nama a kwakwalwar mutum. Wannan curin tsoka kuma da zarar ta bunkasa, sai ta haddasa samuwar nau’ukan ciwon sankara, watau cancer, iri biyu. Nau’i na farko ita wacce ke samuwa ta dalilin curin tsoka da ke tsirowa a kwakwalwa, wacce idan ta bunkasa, tana iya takura wa muhallin da jijiyoyin kwakwalwa suke, har ta toshe su, ta hana su sakewa. Wannan, inji masanan, a karshe, yana haifar da toshewar hanyoyin numfashi da dan Adam ke amfani dasu wajen tafiyar da rayuwarsa. Wannan nau’in sankara ita ake kira Glioma tumor. Sai nau’i na biyu, wacce ke samuwa a mahadar da ke tsakanin kunne da kwakwalwa, wacce ake wa lakabi da Acoustic neuroma tumor. Duk da cewa wannan nau’in bata da hadari sosai, amma tana iya haddasa rashin sukuni idan ta bunkasa ita ma. Wannan tasa Hukumar Cutar Sankara ta kasar Amurka, watau American Cancer Society ta bayar da sanarwar cewa, akwai tabbacin alaka tsakanin wannan cuta ta sankara da yawan amfani da wayar salula.

Amma a nata bangaren, Hukumar Abinci da Magunguna ta kasar bata yarda da galibin sakamakon wadannan bincike ba. Domin, ta la’akari da bincike nau’i uku da aka gabatar kan haka tun shekarar 2000, babu wani abin damuwa kan kamuwa da cutar sankara don an dauki tsawon lokaci ana amfani da wayar salula. Wannan shine ra’ayin Kungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Wayar Iska, watau CTIA-Wireless Association. Wannan kungiya tace “dangane da binciken da aka gabatar a baya, akwai tabbacin babu wata hadari da wayar salula ka iya haifarwa ga lafiyar masu amfani da ita.”

Wannan takaddama da ake ta tafkawa dai ta samu ne sanadiyyar rashin wata tabbatacciyar ka’ida ko mataki da masu binciken ke amfani da su don gane alaka a tsakanin yawan amfani da wayar salula da kuma cutar sankara, a misali. A yayin da wasu ke amfani da shekaru uku wajen gane tasiri, wasu sun ce za a iya samun alaka ne idan yawan amfani da wayar salula ya kai tsawon shekaru goma. Wasu binciken da aka gabatar a kasashe irin su Isra’ila da Siwidin na nuna cewa akwai alaka. Wadanda aka gabatar a wasu kasashe kuma na nuna babu alaka. Wannan tasa da dama cikin masana ke ganin hanya mafi sauki ita ce mutum ya kiyaye ka’idojin amfani da wayar salula. Hakan na cikin abinda wasu masana cutukan kwakwalwa da Larry King yayi hira dasu cikin watan Mayu a shirinsa mai suna Larry King Live, suke ganin dacewarsa; suka ce in ma akwai, a kalla mutum ya samu kariya. Idan kuma babu alaka, to daman abinda ake so kenan. Daga cikin hanyoyin akwai yin amfani da na’urar jin Magana ta kunne, watau Ear Piece, ko kuma sanya wayar a tsarin Speaker Phone, lokacin da kake amsa waya ko kiran wani. Wannan zai sa ka tsira daga tururin hasken da ke fitowa daga jikin wayar; maimakon ya zarce zuwa kwakwalwarka, sai ya bi iska. Domin rigakafi, inji Hausawa, ya fi magani.

Labaran Mako


Sagey Brian Zai Kai Ziyara Zuwa Sararin Samaniya (http://www.upi.com): Sagey Brian, daya cikin shugabannin kamfanin Google Inc. ya biya zunzurutun kudi dala miliyan biyar ($5m), wajen naira miliyan dari shida da hamsin kenan, don siyan tikitin kumbon kai ziyara a sararin samaniya don yawon shakatawa. Kamfanin Space Adventures da ke Virginia a kasar Amurka ya tabbatar da hakan cikin makon da ya gabata. Kamfanin yace duk da wannan kudi da ya biya, ba dole bane sai Brian yayi wannan tafiya, yana iya sayar da tikitin ga wani mai bukata kafin lokacin tafiyar. Har wa yau, yace wannan kashin farko kenan cikin kudaden da zai biya, ba wai duka ya biya ba. A nasa bangaren, Brian, wanda ya nuna farin cikinsa don samun wannan dama na kai ziyara zuwa sararin samaniya, ya sanar da cewa yana cikin masu sha’awan ganin wannan harka ta safarar mutane zuwa sararin samaniya ta habaka. Daga shekarar 2001 zuwa yanzu, kamfanin safarar masu kai ziyara sararin samaniya na kasar Rasha ta hanyar kumbo, ya kai mutane biyar don shawagi a sararin samaniya. Kuma a kalla kudin tikiti daya ya kai dalar Amurka miliyan ashirin, kwatankwacin naira biliyan biyu da miliyan dari shida da hamsin kenan.

Sagey Brian dai, tare da Andrew Page ne suka kafa kamfani da gidan yanar sadarwar manhajar matambayi-ba-ya-bata ta Google (www.google.com) cikin shekarar 1998. A halin yanzu kamfanin na gaba wajen samun kudaden shiga cikin jerin kamfanonin sadarwa, a duk shekara, inda aka kiyasta ya samu ribar dalar Amurka biliyan goma cikin shekarar 2006. Brian da Page dai na cikin matasan masu kudi a kasar Amurka.

Hukumar NASA ta Cilla Kumbon Bincike Cikin Falaki (http://www.nytimes.com): Hukumar habaka bincike cikin sararin samaniya da dukkan falakin wannan duniya, watau NASA, ta cilla wani kumbo zuwa falaki, don lura da kuma yin nazari kan wasu manyan buraguzan haske masu kai-komo cikin falaki ko hanyoyin taurarin da ke sararin wannan duniya tamu. Wannan kumbo, wanda hukumar ta aika ranar laraba, 12 ga watan Yuni, yana dauke ne da wani madubin hangen nesa na musamman watau telescope, wanda zai dauki hoton wadannan nau’ukan haske da ke haddasuwa kuma suna bacewa cikin kankanin lokaci. Bayan sa’a daya da rabi kumbon da ke dauke da wannan madubin hangen nesa ya isa muhallinsa a sararin samaniya, inda ya cilla madubin cikin falaki, bayan tafiyar mil 350 daga sararin wannan duniya tamu. Wannan shiri dai yaci a kalla dalar Amurka miliyan dari shida da casa’in ($690,000,000.00), kuma binciken hadin guiwa ne tsakanin hukumar NASA da kuma hukumar Makamashi ta Amurka, masu kokarin gano nau’in makamashin da ke cikin wannan haske.

Kafin wannan shekara, binciken baya da aka yi kan wadannan ire-iren hasken da ke darsuwa a cikin hanyoyin taurari ko falaki da a turance ake kira gamma-rays, ya nuna cewa wadannan nau’uka na haske na cillowa ne daga wasu ramuka ko koguna masu duhu, kuma ba su bayyana a sararin wannan samaniya tamu, balle a gansu. Wannan ya sa dole a je inda suke darsuwa, don yin nazari kansu. Nau’in hasken gamma-ray dai, shine matakin haske mafi kaifi da saurin maimaituwa wajen darkake abinda ya dosa a muhallinsa. Wasu daga cikin nau’ukan hasken dai sun hada da wankakken hasken rana da muke mu’amala dashi a wannan duniya tamu, da gundarin hasken rana wanda ke fitowa kai tsaye daga ranar, sai hasken da ke game duniya mara zafi. Daga cikin su har wa yau, akwai hasken da ke kasa da gani ko idon dan Adam, mai taimakawa wajen sadarwa ko dafa abinci, irin su hasken Microwave, da kuma makamashin Infra-red.

Sanarwa

Hukumar makarantar koyon ilimin kwamfuta da sassanta, watau NIIT, ta fara raba fom don yin jarabawar shiga da ake sa ran rubutawa cikin watan gobe, watau Yuli. Ga duk mai bukatar rubuta jarabawar, yana iya zuwa reshen Zenith International Bank da ke biranen kasar nan, don karban fom din. Kyauta ake bayarwa, ba ko sisin kwabo. Idan ka cike fom din ka mayar musu dashi, ko kuma ka kai reshen makarantar da ke Kaduna ko Kano ko Ibadan ko Legas ko kuma Abuja, idan a nan kake. idan lokacin rubuta jarabawar yayi, zasu aiko maka da adireshin inda zaka je don rubutawa. Ka’idar su ita ce, idan ka samu martaba ta karshe, watau “A++”, za a zaftare maka sama da dubu dari biyu cikin kudin da zaka biya. Idan ka samu “A” ko “B+”, za a rage maka kasa da haka, har dai iya kwazonka. Ga duk mai sha’awa, yaje reshen Zenith Bank ko kuma reshen makarantar, a daya daga cikin biranen da aka zayyana a sama.

Abdullahi Salihu Abubakar

08034592444; fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com