Wednesday, January 28, 2009

Tsarin Bincike da Neman Bayanai a Intanet

Gabatarwa

Duk wanda ya karanta tarihi  da kuma asalin fasahar Intanet, zai ga cewa asalin manufar da ta haddasa bunkasa da kwarjinin wannan fasaha ita ce manufar yada ilimi da samunsa cikin sauki.  Wannan manufa kuwa ita ce kan gaba har a yanzu.  Domin haka ne galibin masu bincike suke karade duniyar Intanet don samun abin dogaro wajen bincikensu - daga dalibai zuwa malamai; daga masu bincike zuwa masu neman karin ilimi; daga ‘yan kasuwa zuwa masu binciken sanin ingancin hajojin da suke bukatar saye.  Har wa yau, idan kana neman babban dalilin da yake haddasa karancin masu bincike a dakunan karatu, musamman a kasashe masu tasowa, za ka ga cewa fasahar Intanet ce.  Domin muddin bayanai kake nema masu nasaba da kuma alaka da abin da kake bincike, cikin lokaci da kuma yanayi mai sauki, to ka je farfajiyar Intanet.  Wannan ba ya nufin cewa fasahar Intanet kadai mai bincike zai dogara da ita wajen bincikensa.  Domin akwai abubuwa da dama da ba lallai bane ya same su.  Sai dai kuma, kamar yadda duk wani mai bincike ya sani ne, duk bayanan da za su zama madogara a gareshi wajen bincikensa suna dauke ne da wasu siffofi masu muhimmanci; kamar nasaba, da saukin samu, da alaka da kuma tsari.  A bayyane yake cewa fasahar Intanet a yau duk ta kumshi bayanai masu wadannan siffofi, komai kankantar bayanan kuwa.  In kuwa haka ne, kenan mai karatu ko binciken ilimi bai da wadatuwa da fasahar Intanet a yayin da yake bincikensa.  Ga duk wani mai binciken ilimi ta hanyar fasahar Intanet, dole ne ya kiyaye wasu ka’idoji ko matakai  da za su taimaka masa kai wa ga nasara.  Domin kuwa wani muhalli ne mai dauke da nau’ukan bayanai fiye da tunanin mai bincike.  Wannan shi ke nufin cewa dole ne duk wani mai binciken ilimi a wannan muhalli ya samu wasu ka’idoji da za su taimaka masa samun abinda yake nema.  In kuwa ba haka ba, to sai ya bace.  Ire-iren wadannan matakai ko ka’idoji sun hada da:

Ingancin Bayanai

Abin da duk wani mai bincike ke so a farkon lamari shine ya samu bayanai ingantattu da za su taimaka masa samun kyakkyawan natija a bincikensa.  Domin a Intanet akwai bayanai nau’uka dabam-dadan, wadanda wasu suka rubuta su da manufofo dabam-daban, har wa yau.  Idan kana bincike ne a kan amfanin wani abu ko muhimmancin wani abu, za ka samu bayanai kan haka, sannan da bayanai masu akasin hakan.  Akwai hanyoyi guda biyu da duk mai bincike zai bi don tabbatar da ingancin bayanan da yake son dauka a yayin da yake aikin bincikensa.  Hanyar farko ita ce: ka tabbatar da marubucin kasidar ko makalar da ka samu.  Wa ya rubuta?  Dole ne ka tabbatar da wanda ya rubuta kasidar ko makalar.  Domin wannan zai ba ka damar ambaton madogaranka a karashen binciken da kayi.  Bayan nan, ka tabbata ka san wani kan fannin da kake son gabatar da bincike a kai.  Hakan zai dada taimaka maka wajen fahimtar manufar marubucin.  Hanya ta biyu ita ce: ka tabbata cewa marubucin ya ambaci madogaransa a ciki ko karshen kasidar.  Wannan ma zai taimaka sosai wajen fadada bincike.  Idan cikin wasu littafai ne ya tsamo bayanan, hakan zai sa ka neme su misali, don fadadawa. 

Abu na karshe kan abin da ya shafi ingancin bayanai, shine muhallin da ka samu bayanai ko kasidar.  Ba kowane gidan yanar sadarwa zaka je don neman bayanai ba.  Ba kuma kowanne cikin sakamakon binciken da aka turo maka ke dauke da ingantaccen bayanin da kake nema ba.  Dole ne ka nemi muhallin da ke da alaka da fannin bincikenka, don samun natija mai kyau.  Misali, kana neman bayanai ne ko kasidu akan hanyoyin da ke haddasa hauhawan farashin kayayyakin masarufi a cikin al’umma (Causes of Inflation in an economy).  Dole ne ka doshi gidajen yanar sadarwar da ke da alaka da fannin tattalin arzikin kasa ko hada-hadar kasuwanci.  Bayan nan, wasu cikin gidajen yanar sadarwar da ake samun bayanai ingantattu sun hada da: rubutattun kasidun da ake samu daga gidajen yanar sadarwar jaridu da mujallu, da makarantu ko jami’o’i da kuma hukumomin da fannin ya shafe su.  Haka kuma, ana samun kasidu masu inganci a gidajen yanar sadarwar malaman jami’a ko kwararru kan fannonin da me bincike ke neman bayanai kan su.  In da hali, mai karatu ya kiyaye kansa daga tsamo bayanai daga mudawwanai zalla, watau Blogs.  Domin galibin bayanan da ke ire-iren wadannan mudawwanai, ko dai na tallace-tallace ne, ko kuma suna dauke ne da tsantsar son zuciya; ma’ana, zallar ra’ayin marubucinsu, wanda ba lallai bane ya fadi hujjojinsa ba a ciki.  Tabbas a kan samu bayanai ingantattu a wasu mudawwanan, amma da dama duk hauragiya ne a cikinsu.  A takaice dai, kada ka takaita kanka da su; duk da cewa hakan ya danganci irin bayanan da kake nema ne a bincikenka.

Nasabar Bayanai

Abu na biyu da duk mai bincike ya kamata ya kiyaye shine, alakar da ke tsakanin bayanan da ya samu, da kuma binciken da yake yi.  Kada ka rudu da taken kasida ko makala kadai.  Ka karanta sadararorin da ke ciki, don tantance alakar da ke akwai da maudu’in da kake bincike a kai.   Idan kuwa ba haka ba, sai ka tara bayanai marasa amfani, wadanda kuma ba za su baka natijar bincike mai kyau ba.  Bayan nan, cikin abin da zai taimaka maka sanin alakar da ke tsakanin kasidar da ka samu da kuma bangaren da kake bincike akwai sanin yaushe aka rubuta kasidar?  Ta yiwu kana neman bayanai ne kan dalilan da suka haddasa rushewar tattalin arzikin kasa a duniya cikin shekarar 2008.  Da ka yi tambaya sai aka turo maka kasidu masu taken: “dalilan rushewar tattalin arzikin kasa a duniya” kadai, babu shekara a cikin taken shekarar.  Kana ganin haka kai kuma, sai ka budo kasidar, ba tare da karanta kadan cikin mukaddimar ba, ka dinga loda wa kwamfutarka don taskancewa.  Sai kaje gida sai kawai ka ga ashe kasidar na Magana ne kan dalilan rushewar tattalin azikin kasa a duniya cikin shekarar 1930, watau gamammiyar matsalar farko da tattalin arzikin kasashen duniya ya fara samu.  Ka ga dai ga shi taken kasidar daya ne, kuma kan matsala daya, amma alakar shekara ko lokacin faruwa ta raba su.  Wanann kuma ke nuna cewa wannan kasidar ba  za ta maka cikakkiyar amfani ba cikin binciken da kake yi. Abu  na karshe da ya kamata mai binciken ilimi ta hanyar Fasahar Intanet ya kiyaye shi ne yin amfani da kalmomi masu siffatawa ko kwatanta abin da yake so.  Bayan haka, dole ne mai bincike ya san cewa da wahala ya samu wata kasida rubutacciya mai take da tsari da kuma zubin rubutu irin wanda yake bincike a kai.  Domin galibin abin da kowa ya sani ne cewa amfanin bincike shine zuwa ko samar da wani abu sabo, wanda wani bai irinsa ko makamancinsa ba.  Don haka dole ne ka yi amfani da Kalmar da za ta siffata wa manhajar neman bayanai irin nau’in bayanan da kake so.  Sannan kuma ka sani, ba wai taken kasidar da kake rubutawa kadai zaka rubuta wajen neman bayanai ba, a a.  Dole ne ka kacalcala kasidar da kake bincike a kai zuwa mataki-mataki ko sashe-sashe.  Ka kuma ayyana irin nau’in bayanan da kake so a kowane mataki, watau Outlines kenan.  Wannan zai sawwake maka samun bayanai masu nasaba da kasidar, ya kuma sawwake maka tsarin rubutun a yayin da ka tashi rubutawa.  Misali, sai malaminka a makaranta ya baka aikin gida da ka rubuta kasida mai shafi goma, kan dalilan da ke haddasa yawan hadarurruka a kan titunan Nijeriya (Causes of Road Accidents in Nigeria).  Idan ka tashi bincike, za ka nemo bayanai ne kan tsarin kare hadarruka a Nijeria, da kuma hukumomin da ke lura da hakan a Nijeriya, sannan, a karshe, ka kawo bayanai kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka a kan titunan kasar.  Wannan ke nuna cewa ba kalma daya kawai za ka yi amfani da ita ba wajen binciken bayanan da kake nema.  Kana bukatar kalmomi a kalla uku zuwa hudu, kamar haka: (1) System of road safety in Nigeria, (2) Road safety regulators in Nigeria, (3) Causes of Road Accidents in Nigeria.  Idan ka bi wannan tsari kai kanka za ka san cewa ka samu sauki, kuma rubutun ba zai maka wahala ba.  A karshe kuma, duk wanda ya karanta ya san cewa lallai ka fahimci abinda ake son ka da rubutawa.  Bayan haka, sai abu na karshe:

Ina Zan Je?

Kamar yadda bayanai suka gabata kan tsarin gidajen yanar sadarwa, duk wani bayani na kasida ko makala da za ka ci karo dashi, yana dauke ne a wani gidan yanar sadarwa.  Sai dai kuma, zai yi wahala a ce ka san dukkan gidajen yanar sadarwar da ke dauke da bayanan da kake son mu’amala da su a lokacin bincikenka.  Wannan tasa dole ka nemi hanya mafi sauki da zai taro maka dukkan wani abin da kake bukata ko hanyar samunsa.  Daga cikin wadannan hanyoyi akwai yin amfani da manhajar Matambayi Ba Ya Bata, watau Search Engine kenan.  Wannan manhaja na samuwa ne a gidajen yanar sadarwar Google, ko Yahoo!, ko kuma MSN, a takaice.  Idan ma hotuna kake nema ko bayanan da suka shafi sauti ko hotuna masu motsi, watau bidiyo kenan, duk za ka samu.  Gidan yanar sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da suka fi shahara su hada da na kamfanin Google, wanda ke www.google.com.  Sai kuma gidan yanar sadarwa na kamfanin Yahoo!, da ke samuwa a www.yahoo.com.  Idan kana son fadadawa, sai ka kara da na kamfanin Microsoft, watau MSN, shi kuma za ka samu shafinsa ne a www.msn.com.  Dukkan wadannan gidajen yanar sadarwa ne masu amfani da wata manhaja da ke yawo rariya-rariya a giza-gizan sadarwa ta duniya, don taskance dukkan gurabun samun bayanai na hotuna ko sauti ko kuma rubutattun kasidu da makaloli.  Idan manhajar ta tattaro su, sai ta taskance su a cikin kwamfutocin da ke dauke da gidan yanar sadarwar.  Duk sa’adda mai neman bayanai ya “tambaya”, sai a turo masa bayanan – da sunan take, da takaitaccen bayani da kuma rariyar da za ta kai shi inda kasidar ko hoton yake tsibe.   

Haka idan bayanan da suka kunshi hotuna masu motsi kake nema, watau bidiyo, kana iya ziyartar gidajen yanar sadarwa irin su: Youtube da ke www.youtube.com,  ko kaje Google Video da ke http://video.google.com, ko Yahoo! Video, wanda ke samuwa a http://video.yahoo.com.  Idan kana son fadadawa har wa yau, akwai gidajen yanar sadarwa masu rubutattun kasidu kan fannonin ilimi da dama, irin su How Stuff Works, wanda gidan yanar sadarwa ne mai dauke da rubutattun kasidu masu kwatanta maka yadda ake gudanar da abubuwa da dama, a aikace – daga kan ilimin kwamfuta zuwa yadda ake dafa abinci kala-kala, a misali.  Idan kana son sanin yadda mota ke aiki, akwai.  Idan kana son sanin yadda kwamfuta ke aiki, akwai.  Idan kana son sanin yadda tauraron dan Adam ke shawagi, akwai.  Kai a takaice dai, idan ka shiga wannan gidan yanar sadarwa, akwai abubuwa da dama da ba za ka so a ce ka wuce su ba tare da ka duba ba. Wannan ba karamar dama bace da za ta taimaka maka wajen rubutu.  Har wa yau, akwai gidajen yanar sadarwa masu dauke da rubutattun kasidu na ilimi kan fannonin rayuwa, masu tsawo wadanda aka rubuta su don amfanin masu bincike ko karantarwa, birjik.  Shararriyar cikinsu ita ce:  EssayWorld, wacce shafinta ke samuwa a www.essayworld.com.  A wannan gidan yanar sadarwa, akwai kasidu sama da dubu talatin wadanda musamman aka rubuta su don taimaka wa dalibai masu karatu a dukkan matakan ilimi.  Da zarar ka shiga gidan yanar sadarwar, sai ka matsa alamar “essay” da ke sama a hannun hadu.  Idan shafi ya budo, sai ka shigar da taken kasidar da kake so ko kuma taken binciken da kake son yi, a wani fili da aka tanada maka a kasa, daidai inda aka rubuta: “Search for Essays in the Essayworld Database”.  Kana matsa enter, za a budo maka tarin kasidun da suka shafi abinda kake nema; ka zabi na zaba. Wannan kadan ne cikin alfanun da ke tattare da wannan fasaha ta Intanet wajen taimaka wa mai bincike a kowane fanni ne na ilimi.

Kammalawa

Fasahar Intanet duniya ce makamanciyar wacce muke rayuwa ciki, amma a wani irin tsari da kimtsi da ya sha bamban da wannan duniyar tamu da zahiri.  Duk abin da kake bukata na bayanai kan wani nau’in ilimi a duniya, in Allah Ya yarda kuwa za ka same shi.  A wani lokacin kyauta, a wani lokacin kuma sai ka biya taro da kwabonka.  Duk da haka, samuwar fasahar Intanet a wannan zamani da muke ciki ya samar da dama ga dalibai zuwa har malamansu, wajen fadada binciken ilimi da kuma sanayya kan wannan duniya ta mu da irin al’ummar da ke makare cikinta.  Duk da yake yin hakan ba ya samuwa ta dadi ba tare da mai bincike ya san wasu ka’idoji ko matakan da zasu sawwake masa binciken ba.  Dole ya kiyaye ingancin bayanan da zai ci karo dasu yayin da yake nema; ya kuma fahimci alakar da ke tsakanin bayanan da kuma fannin bincikensa.  Idan ya san wannan, abu na karshe da ya rage masa shine yin amfani da kalmomin da zasu nemo masa abin da yake so, a muhallin da ya dace da wannan fannin da yake bincike a ciki.  Da wannan, sai mai bincike ya tsinci dame a kala.

Kasuwar Manhajar "Windows Vista" Na Kara Dusashewa!

Tun bayyanar babban manhajar kwamfutar kamfanin Microsoft Corp mai suna Windows Vista watanni kusan goma sha daya da suka gabata, har yanzu haskenta sai kara dusashewa yake yi a fuskar masu amfani da kwamfuta; tsakanin kamfanoni da kuma daidaikun mutane.  Idan ba a mance ba babban manhajar kwamfuta ta Windows dai ita ce mafi shahara a kasuwannin manhajar kwamfutoci a duniya, tun farkon bayyanar nau’in Windows 3.1 da kamfanin Microsoft Corp yayi shekaru goma sha bakwai da suka gabata.  Hakan na damfare da tsarin sauki ne da kamfanin ke amfani da ita wajen gina wannan babbar manhaja, wanda sanadiyyar hakan miliyoyin mutane suka iya amfani da kwmfuta cikin sauki ta hanyar tsarin Graphical

 User Interface, ko GUI a takaice.  Shi kuma kamfanin yayi ta cika aljihunsa da biliyoyin daloli, inda a karshe ya zama kamfani mafi kasaita wajen shahara da ciniki a duniya.  Shekara guda kafin fitowar nau’in Windows Vista, mutane sun yi ta Allah-Allah da fitowarta.  A tunaninsu Vista

 za ta fito ne da cikakken tagomashi kamar sauran nau’ukan Windows da suka gabata, musamman Windows XP, wacce har yanzu ke cin kasuwarta babu kakkautawa.  Fitowarta ke da wuya sai kowa yayi turus, kamar an tara masa yashi a kofar gida!

Babban abin da mutane suka fara ruduwa da shi a jikin Windows Vista shine tarin kyale-kyalen da ta zo dasu; daga hotuna zuwa shafukan manhajoji masu kayatarwa da shashantar da idon mai mu’amala da kwamfutar.  To amma kamfanin Microsoft Corp ya mance cewa galibin masu mu’amala da kwamfuta yanzu musamman kamfanoni, ba damuwarsu bane kyale-kyale.  Abin da aka fi damuwa da shi yanzu shine tagomashi, watau ingancin manhajar da ke sarrafa kwamfutar, da aminci da gaggawar aiwatar da aiyuka da dai sauransu.  Dukkan wadannan, idan mai karatu ya dubi Vista, bata zo dasu ta dadi ba.  Wannan yasa galibi suka juya wa wannan manhaja baya.  Wasu manyan kamfanonin suka ce baza su juya zuwa Vista ba sai bayan ‘yan shekaru, lokacin da ake tunanin kamfanin Microsoft Corp ya kara wa manhajar inganci da tagomashi. Wasu kuma, suka ce atafaufau, ba su ba manhajar Windows Vista; sun tsaya kan nau’in Windows XP, idan an fito da wata manhajar bayan Vista, sa dubi dacewar yin hakan ko rashinsa.  Wasu kuma, ‘yan zafi, suka daina amfani da manhajar Windows ma gaba daya, suka koma sauran nau’uka irin su Linux ko kuma Mac OX.

Matsalan farko da galibi ke ta kuka kansa shine yawan saibi.  Idan ka baiwa manhajar Windows Vista umarnin budo maka wani shafi ko wata jakar adana bayananka da ke kwamfutar, sai ta gama yanga sannan ta biya maka bukata.  Musamman idan kana yawo a shafukan yanar sadarwa ta duniya, watau Intanet.  Sai ya zama ita ce ke baka umarni, wajen ganin damar bin umarninka, ba kai ba.  Wannan tasa wasu ke mata kirari, cewa: Windows Vista kyakkyawar budurwa ce mai yanga”.  Wannan matasala na yawan saibi na cikin abinda ya sad a dama suka daina amfani da wannan manhaja ta Windows Vista gaba daya, duk da kyale-kyalen da take tare dasu.  Wannan saibi har wa yau, shi ne ke haddasa mata yawan sumewa cikin kankanin lokaci, watau Hanging.  Ko kuma yawan sandarar maka da masarrafan da kake amfani dasu ba tare da izininka ba.  Haka kawai sai ka nemi ruhinsu ka rasa.  Ka matsa, amma ba motsi.  Wannan shi ake kira Crashing, kuma ba abinda yafi bata wa mai amfani da kwamuta rai irin wannan lamari; kana ji kana gani, ka kasa sarrafa abin da ke karkashin ikonka.  Su kuma masu amfani da kwamfuta sun fi so su ji komai zam-zam, musamman dai kamfanoni da ke bukatar aiyukansu a lokacin da suke so.

Bayan wannan, daga cikin illolin Windows Vista akwai yawan cin makamashin kwamfutarka, watau System Resources.  Kowace manhajar kwamfuta na amfani da karfin makamashin da ke tare da gangar-jikin kwamfutar ne, wanda shi ne misalin injin da ke baiwa mota karfin tunkudawa zuwa gaba ko baya.  Da zarar ka  kunna kwamfutarka, sai babbar manhajar ta rarraba wa dukkan karikitan da ke tafiyar da ruhin kwamfutar iya makamashin da suke bukata.  Ragowar makamashin kuma sai ta adana maka su; da zarar ka bude wata masarrafa za ka yi amfani da ita, sai babbar manhajar ta yanko mata iya makamashin da take bukata don tafiyar da aikin da kake son yi da masarrafar.  To amma saboda yanayi da kuma tsarin ginin manhajar Windows Vista, sai ya zama da zarar ka kunna, sai ta kwashe kusan dukkan makamashin kwamfutar, ta rarraba wa ‘yan kananan masarrafan da ke taimaka mata rayuwa (watau processes), kai kuma ka ji da kanka.  Wannan tasa idan ka budo wata manhajar don yin wani aiki, sai kwamfutar ta fara saibi, domin karancin makamashi da take fama dashi.  Daga nan sai ta sume a tsaye, ba tare da ka sani ba.  In ta dama ne za ta aiko maka da sakon cewa: “This System is not responding”.  Hatta kashewa ma baka iya yi, domin ba abinda ke jin umarninka balle ya karbi umarnin.  Sai dai ka kashe ta karfi da yaji, sannan ka sake kunnawa.

Idan kuma ka tsira daga sharrin cinye makamashi mai haddasa mummunar saibi don kafcecen ma’adanar kwamfuta da kake da shi, to wata matsalar da baka tsira daga gare ta ba ita ce matsalar rashin kyakkyawar muhallin dasa wasu manhajoji.  Abin so ne ga dukkan wanda ya mallaki kwamfuta ya ga ya samu damar dasa wasu manhajoji musamman irin su masarrafan sauraron karatun Kur’ani ko koyon karatu ko na rubutu da karatu da zane-zane.  Babban matsalar Windows Vista shine rashin kyakkyawar muhalli da zai sawwake maka yin hakan, musamman a farkon fitowarta.  Wannan shi ake kira “Software incompatibility” a turancin ilimin kwamfuta.  Misali, ba dukkan mai amfani da Windows Vista ke iya sanya manhajar Alim a cikin kwamfutarsa  ba, saboda wannan matsalar.  Wannan matsala na faruwa ne saboda rashin manhajoji ko “jami’ai” masu sawwake yin hakan.  Duk da cewa kamfanin Microsoft ya fitar da nau’in Vista na daya, watau Windows Vista Service Pack 1, wanda sanadiyyar hakan aka samu dan daidaito na a-zo-a-gani, har yanzu da sauran rina a kaba.  Akwai sauran burbushin saibi tare da wannan manhaja.  Wannan a tabbace yake kamar yadda wani kamfanin binciken ingancin kwamfuta yayi kwanakin baya  Kamfanin ya nuna cewa har yanzu babbar manhajar Windows Vista na kasa da Windows XP wajen saibi da kashi arba’in.  Wannan babban aibu ne ga kamfanin Microsoft Corp, domin hatta kamfanin Intel Corp, wanda abokin huldan Microsoft ne tun shekaru da dama, inda yake kera masarrafai masu tafiyar da ruhin kwamfuta, watau Micro-chip ko Processors, wadanda kuma galibi da su ake gwajin tasirin babbar manhajar a kwamfutoci, yaki ya juya kwamfutocinsa zuwa manhajar Windows Vista.  An kididdige cewa wannan kamfani na Intel Corp ya mallaki kwamfutoci wajen dubu tamanin a kamfaninsa, amma duk da haka, tare da kusancinsa da kamfanin Microsoft Corp, yaki.  Dalilinsa kuwa shine, har yanzu bai gamsu da ingancin wannan manhaja ko ba.  Ba kamfanin Intel Corp kadai ba, akwai kamfanoni ko mutane da dama, kwararru kan harkar kwamfuta, sun ki komawa ko juyawa zuwa nahiyar Windows Vista, sun doge da tsohuwar Windows XP dinsu, asirinsu a rufe.

Ganin wannan bakin jini da babbar manhajar ke kara yi, duk kuwa da kokarin da kamfanin yake ta yi na tallace-tallace da kara wa manhajar kuzari, sai Microsoft Corp ya sanar da cewa zuwa karshen shekarar 2008 da farkon shekarar 2009, zai daina sayar da babbar manhajar Windows XP.  Ga masu amfani da wannan manhaja kuma, za su ci gaba da samun tallafi ne zuwa shekarar 2010.  Da zarar an wuce wannan shekara, to kai da Windows XP kuma sai dai ka yi ta bilinbituwa idan ka shiga matsala; domin kamfanin zai daina bayar da tallafi tare da daina sayar da manhajar ma gaba daya.  Wannan barazana ce don yanke wa wasu kin juyawa zuwa Windows Vista hanzari idan suka ki amfani da manhajar.  Su san cewa akwai iya lokacin da aka diba mata, don daina sayarwa ko bayar da tallafi.  Kamfanin yayi wannan sanarwa ne cikin shekarar 2008 don cin ma manufar kado kan masu kyamar Vista.  Amma wannan barazana bata biyan kudin sabulu ba.

Ranar 18 ga watan Agustan 2008, gidan yanar sanar sadarwa na Computer World ya hakaito binciken da wani kamfanin fasahar sadarwa yayi mai nuna cewa, duk da barazanar da kamfanin Microsoft Corp ke yi na daina sayarwa tare da bayar da tallafi ga manhajar Windows XP, kashi talatin da biyar cikin dari na kwamfutocin da aka saye su tsakanin watan Janairun 2008 zuwa watan Yuni, masu dauke da babbar manhajar Windows Vista, an canza musu manhaja zuwa Windows XP!  Kamfanin yace ya gano hakan ne daga binciken da ya gudanar kan kwamfutocin tafi-da-gidanka da na kan tebur wajen guda dubu uku, inda kashi 35% suka tabbatar da cewa asalin manhajar da suka sayi kwamfutocinsu da ita Vista ce, amma daga suka kai wa kananan dilolin kwamfuta don a mayar musu zuwa manhajar Windows XP, ko kuma su da kansu suka goge manhajar Vista da ke dauke cikin kwamfutar, don sanya Windows XP.  Wannan har wa yau ya tilasta wa manyan kamfanonin kwamfuta irin su Hewlett-Packard (HP), da Dell Incorp., bin wannan tafarki.  A yanzu suna da tsarin da ke baiwa mai sayen sabuwar kwamfuta damar canza manhajar da ke ciki (wanda Windows Vista ce) zuwa Windows XP.  Wannan sabon tsari, a cewar wadannan diloli, dama ce kamfanin Microsoft ya basu don ganin karkatan mutane zuwa manhajar Windows XP. 

Ganin yawan karkatan mutane da dogewarsu kan Windows XP tasa kamfanin Microsoft Corp a ya sake daga lokacin da ya haddade a baya, don janye tsohuwar manhajar Windows XP, wacce har yanzu tauraronta ke haskakawa babu kakkautawa.  Cikin sanarwar da ya fitar ranar 22 ga watan Disambar 2008, kamfanin Microsoft Corp yace ya janye sanarwarsa ta farko wacce a ciki yake bayyana cewa zai janye lasisin manhajar Windows XP daga kasuwa daga ranar 31 ga watan Janairun 2009.  Kamfanin ya sanar da cewa saboda wasu dalilai, ya daga wannan lokaci zuwa karshen watan Mayu na shekarar da ake ciki, don baiwa kananan dilolin kwamfuta damar saya da kuma sayar da lasisin da suke ajiye dasu a shagunansu.  Manyan diloli ko kamfanonin kwamfuta masu rakaba babbar manhajar kwamfuta tare da sabbin kwamfutocinsu irin su Hewlett-Packard (HP) da Dell, misali, su ma an basu damar ci gaba da sayar da tsohuwar manhajar Windows XP har zuwa karshen watan Yuli na wannan shekara.  Duk wannan dai alamu ne da ke nuna cewa lallai kamfanin Microsoft Corp ya fahimci irin dogewar da jama’a suke yi wajen rashin amincewa da sabuwar manhajarsa uwar kyale-kyale da saibi.  Kuma har yanzu jama’a basu daina warwason Windows XP ba a kasuwa; wadanda suka sayi Windows Vista kuma sai kwam-baya suke yi, don neman sauki da inganci.  Kididdigan baya—bayan nan da aka yi cikin watan Nuwambar 2008 ya nuna cewa, a yayin da manhajar Windows Vista ke rike da kashi 20.5% na yawan masu saye, ita kuma manhajar Windows XP na rike ne da kashi 66.3% a kasuwar babbar manhajar kwamfuta a kasashen yamma.   Babban abin da ya jawo wa Windows Vista wannan rashin farin jini kuwa shine yawan saibi mai haddasa wa kwamfutocin mutane sumewar da basu shirya ba.  Kuma har wa yau, shi ne ke kara sanya haskenta dusashewa a sahun manyan manhajojin kwamfuta a duniya.