Tuesday, January 3, 2012

Tsaraba Daga Kano...


Ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu ne na halarci babban taron sabuwar shekara
na kungiyar Tsangayar Alheri da ke Dandalin Facebook. An gayyace na gabatar da 
kasida ta musamman kan Bunkasar Fasahar Sadarwar Zamani a Najeriya: Kalubale da Ci Gaba. A sha karatu lafiya.

.......................................................
BUNKASAR FASAHAR SADARWAR ZAMANI A NAJERIYA: KALUBALE DA HANYOYIN CI GABA




Gabatarwa

Shekaru 22 da suka gabata a Najeriya, kalmomi irinsu Nokia, da Samsung, da Internet, da Email, da SMS, duk ba abubuwa bane sanannu a kwakwalen mutane, balle harsunansu.  Ba wai ga gama-garin jama'a ba kadai, hatta a harshen masana a jami'o'i da sauran cibiyoyin ilmi wadannan kalmomi basu shahara ba.  Faruwan hakan ba ya nufin wadannan kalmomi ko sunaye baki ne a duniya baki daya, a'a, sai don rashin isarsu gare mu ne, sanadiyyar halin da kasar ke ciki na rashin bunkasar fannin kimiyya da fasahar sadarwar tarho da abin da ya shafi na'urorin sadarwa da sarrafa bayanai, irinsu kwamfuta, da wayoyin salula, da fasahar Intanet.  Duk da cewa akwai hukumar lura da harkar sadarwa ta Gwamnatin Tarayya, wacce ita ce kadai ke da alhakin bayar da lambobin wayoyin tarho tare da yin rajistarsu ga masu bukata, wannan bai sa an samu bunkasar wannan fanni mai matukar muhimmanci da tasiri ga al'ummar kasar ba, sai bayan bude kafar zuba jari da aka yi a 'yan shekarun baya.

Kafin wannan lokaci, layukan tarho da hukumar gwamnati ke bayarwa basu wuce 500,000 ba, a kasa mai dauke da al'umma sama da miliyan dari!  Bayan haka, duk da karancinsu, babu yanayin sadarwa mai inganci a kasar.  Ba komai ya kawo haka sai don na'urorin sadarwar na amfani ne da tsohon tsarin sadarwa, watau Analogue, sannan ga gagarumin matsalar rashin wutar lantarki da kasar ke fama da shi.  A bangaren na'urorin sadarwa irinsu kwamfuta kuwa, sai ofishin kamfanonin kasashen waje masu zaman kansu da ke kasar, da wasu 'yan daidaikun shagunan buga bayanai ake samunsu.  Hatta a makarantun kasar nan kwamfuta ba ta shahara ba sosai, balle tsarin amfani da su a hukumomin gwamnatin jiha ko na tarayya.  Galibi ana amfani ne da keken rubutu, watau Typewriter irin na kamfanin IBM, (IBM Digital Typewriter), sai kadan daga cikin kwamfutoci kanana na kamfanin IBM masu amfani da tsohuwar manhajar kwamfuta ta kamfanin Microsoft mai suna MS-DOS, ko Disk Operating System a warware. Dangane da abin da ya shafi fasahar Intanet da Imel kuwa, babu wanda ya sansu, in ka kebe 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, irinsu Amurka da Ingila da sauran kasashen Turai.

To amma a yanzu lamari ya canza; Najeriya ta shiga sahun kasashe masu ta'ammali da bayanai nau'uka daban-daban, ta hanyoyi daban-daban, a yanayi daban-daban.  Daga birane da maraya zuwa kauyuka da rugage, duk jama'a na iya aikawa ko karban sakonnin murya, ko tes, ko ta'ammali da fasahar Intanet ta hanyoyi daban-daban. Wannan kasida za ta duba wannan ci gaba ne da aka samu, da dalilansu, da nau'ukan fa'idojin da 'yan Najeriya suke samu ta wannan hanya, da kuma kalubale ko matsalolin da suke fuskanta.  A karshe kuma ta duba hanyoyin da hukuma ko jama'a a matsayinsu na al'umma za su bi wajen shawo kan wadannan matsaloli, don samun ci gaba mai alfanu.

Bunkasar Fasahar Sadarwa a Duniya

Fasahar sadarwar zamani ko Information Communication Technologies (ICTs) a harshen turanci, tsari ne na aiwatar da sadarwa mai inganci da fa'ida, ta amfani da kayayyakin sadarwar zamani – irinsu kwamfuta, da wayoyin salula, da tauraron dan adam, da na'urorin sadarwar zamani – ta hanyoyin sadarwar zamani – kamar  su fasahar Intanet, da Imel, da sakonnin tes, da shirye-shiryen talabijin masu inganci da dai sauransu.  Wannan alaka da ke tsakanin kayayyakin sadarwa da hanyoyin sadarwar na kulluwa ne da taimakon wasu ka'idojin kimiyyar sadarwar zamani, irinsu IP Address, da WAP, da POP3, da IMAP, da SMTP da dai sauran ka'idoji makamantansu. Wannan tsari ne ya hade duniya zuwa wata dunkulalliyar unguwa saboda gamewarsa, da tasirinsa, da kuma saurin yaduwarsa.

Daga cikin mutum biliyan 7 da ke rayuwa a wannan duniya a yau, alkaluman bayanai sun nuna sama da biliyan 2 na amfani da fasahar Intanet.  Daga cikin wannan adadi, kashi 45 duk matasa ne 'yan kasa da shekaru 25[1].  Har wa yau an samu karuwan masu ta'ammali da fasahar Intanet a kasashe masu tasowa daga kashi 44 a shekarar 2006 zuwa kashi 62 a shekarar 2011.  A wadannan kasashe, bayanai sun nuna cewa matasa sun fi tsofaffi kashe lokacinsu wajen mu'amala da fasahar Intanet. Daga cikin adadin nan har wa yau, kashi 30 duk 'yan kasa da shekaru 25 ne.   Daga shekarar 2000 zuwa 2011 an samu karuwar masu amfani da fasahar Intanet a nahiyar Afirka da kashi 2,527.  Domin a shekarar 2000 mutum miliyan 4.5 ne kacal ke ta'ammali da fasahar, amma shekaru goma bayan wancan adadi, a yau ana da mutum miliyan 118.6 masu shawagi a giza-gizan sadarwa daga nahiyar Afirka[2].  Akwai hasshen cewa idan gwamnatoci a nahiyar Afirka suka shigar da tsarin sadarwar zamani a makarantun firamare da sakandare da jami'o'i, za a samu karin matsa masu shawagi a giza-gizan sadarwar duniya sama da biliyan daya[3].

Idan muka karkato zuwa Najeriya kuwa, za mu ga an samu ci gaba a wannan bangare sosai.  Domin shekaru goma da suka gabata adadin masu ta'ammali da fasahar Intanet a kasar duk bai shige mutum 200,000 ba.  Amma a yau, daga cikin mutum miliyan 118.6 da ke kutsawa giza-gizan sadarwa ta Intanet a nahiyar Afirka, miliyan 44 duk daga Najeriya suka fito.  Wannan shi ne adadi mafi yawa da kaso mafi girma a nahiyar.  Najeriya ce ta daya a yawan masu amfani da Intanet a nahiyar Afirka. Dangane da abin da ya shafi masu shawagi a Dandalin abota na Facebook kuwa, daga cikin mutum miliyan 710.7 da suka yi rajista a duniya, mutum miliyan 30.6 daga nahiyar Afirka suke, a yayin da Najeriya ta zo na uku a yawan masu rajista da miliyan 3.4, bayan kasashen Misra, da Afirka ta kudu da suka shallake ta[4].

Daga cikin abin da ya dada taimakawa wajen karuwar adadin masu ta'ammali da fasahar Intanet a Najeriya da sauran kasashen Afirka akwai samuwar wayoyin salula da yaduwarsu.  Domin a yanzu akwai layukan wayoyin salula masu rai a duniya wajen biliyan 6.  Wannan adadi ya samu ne sanadiyyar karuwar masu amfani da wannan tsari a kasashe masu tasowa da kashi 79.  Daga cikin abin da ya dada taimakawa wajen wannan kari a wadannan kasashe, akwai saukin farashin wayoyin salula sanadiyyar yawaita, da samun nau'uka daban-daban[5].  Domin a shekarar 2007 kadai an samu karuwan masu amfani da wayoyin salula wajen miliyan 65.  A shekarar 2008 wannan adadi ya haura zuwa miliyan 250[6].  A halin yanzu akwai masu rajistan layin wayar salula sama da miliyan 90 a Najeriya[7].

Ba wai kira kadai jama'a ke aiwatarwa da wayar salula ba, akwai ta'ammali da fasahar Intanet, da rubutawa tare da aika sakonnin tes.  A yini guda kacal, mutanen birnin Bejin na kasar Sin sun taba aikawa da sakonnin tes sama da biliyan daya.  A jajibirin bikin shigan sabon shekarar 2008 kuwa, alkaluman bayanai sun tabbatar cewa sakonnin tes wajen biliyan 43 ne suka sauya hannu a tsakanin al'ummar duniya.  Daga cikin wannan adadi, sakonnin tes biliyan daya daga kasar Indiya ne, a yayin da aka samu mutum miliyan 50 na kasar Filifin masu wayar salula suka aika sakonnin tes wajen biliyan 1.39[8]. A bincken da ta gudanar a wani shiri na musamman, talabijin kasar Kanada mai suna CBC, ta tabbatar da cewa a kowane yini a kalla jama'a kan aika sakonnin tes wajen biliyan biyu[9]. A karshe dai, adadin sakonnin tes da ake aikawa a duniya ya kusan haura biliyan dubu bakawai, tun daga ranar da wani matashi dan shekaru 22 mai suna Neil Papworth ya fara aikawa da sakon tes daga kwamfutarsa zuwa wayar salular abokinsa mai suna Richard Jarvis, a ranar 3 ga watan Disamba, shekarar 1992[10]. Su kansu masu kera wayoyin salula ba a barsu a baya ba.  Domin daga cikin wayoyin salula sama da biliyan 1.3 da aka turo kasuwa a shekar 2010, kamfanin Nokia kadai yana da miliyan 453, biye da kamfanin Samsung mai miliyan 280, sai kamfanin LG mai miliyan 116.  Daga cikin wancan adadi har wa yau akwai miliyan 51 da kamfanin ZTE ya turo, da miliyan 48 daga kamfanin Research in Motion (RIM) da ke kera wayoyi nau'in Blackberry, sai kuma ragowan miliyan 437 da wasu kamfanoni suka turo kasuwa[11].

Yaduwar fasahar sakonnin tes da ke jikin wayoyin salula ko kadan bai kashe wa fasahar Imel tagomashi da habaka ba. Domin adadin masu mu'amala da fasahar Imel musamman a kasahen da suka ci gaba ya haura sosai. Bayan samuwar wannan tsari a kwamfuta, akwai shi a jikin wayoyin salula. Don haka fasahar Imel na ci ne daga akushi biyu.

Bayanan da suka gabata duk suna mana ishara ne ga irin halin da duniya ke ciki na dunkulewa ta bangaren gamayya da sadarwa. Domin a yau kusan duk abin da ba a tunanin za a iya aiwatar da sadarwa da shi, sai ka ga ana yi.  Bayan sadarwa da ke yiwuwa tsakanin shahararrun kayayyakin fasahar sadarwa irinsu kwamfuta da wayar salula, a yanzu ana aiwatar da sadarwa tsakanin kwamfuta da talabijin, tsakanin kwamfuta da na'urar dumama abinci, tsakanin wayar salula da na'urar sauraren wakoki, tsakanin wayar salula da talabijin, har wa yau, na san masu sauraro za su yi mamakin jin cewa hatta agogon da ake daurawa a hannu duk ana aiwatar da sadarwa ta hanyarsa.  Daga cikin fasahohin sadarwar da suka yi ruwa suka tsaki wajen aiwatar da hakan kuwa akwai fasahar Bluetooth, da fasahar tauraron dan adam masu aiwatar da sadarwa, musamman fasahar GPS na kasar Amurka, da fasahar GLONASS na kasar Rasha, da fasahar Galileo mai dauke da tauraron dan adam 24 da kasashen Turai suka cilla sararin samaniya, sai wadanda kasar Sin ta harba 'yan kwanakin baya, don killace kanta da wannan tsari na sadarwa mai inganci. Bayan wadannan, akwai taurarin dan adam masu cilla shirye-shiryen kafafen talabijin (Satellite Channels) sama da 300 a sararin samaniya suna shawagi.  Sannan ga babban tauraron dan adam na giza-gizan sadarwar duniya ta Intanet mai suna SAT3.

Bunkasar Fasahar Sadarwa a Najeriya

Kafin isowar fasahar Intanet kasar nan, fasahar Imel ta gabace ta. Wannan ya faru ne saboda duk da cewa dukkansu su fasahohi ne na sadarwa da a galibin lokuta suke zama wuri daya, amma kowanne ka'idar gudanuwarsa sun sha bamban da na dan uwansa.  A shekarar 1990 ne jami'ar Mc Master da ke kasar Kanada ta jona jami'ar Ilorin na jihar Kwara da hanyar sadarwa ta Imel.  Daga jami'ar Ilorin kana iya aikawa da sakonnin Imel zuwa kasashen duniya. To amma mutum nawa ma ya san abin da wannan fasaha take nufi balle alfanun da ke tattare da ita?  Don haka ba wanda ya san ana yi, wai kunu a makwabta. Zuwa shekarar 1993 sai gwamnatin tarayya, ta hanyar hukumar sadarwa ta jona kasar da babbar tafarkin sadarwar fasahar Imel, watau Post Office Protocol 3 (POP3), wadda babbar hanya ce mai dauke da ka'idar sadarwar aikawa da karban sakonnin Imel, daga Najeriya zuwa kasar Amurka.  Sai dai wannan ka'ida an jona ta ne da Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke Legas, watau Yabatech.  Har zuwa wannan lokaci dai fasahar Intanet bata leko kasar nan ba, sai shekarar 1997, sanadiyyar wani kamfanin mai da ya bude reshensa a Kaduna da Fatakwal.  Wannan kamfani ya mallaki kwamfutoci, kuma suna dauke da fasahar Intanet, ta amfani da makalutun sadarwa, watau Internet Modem.  Daga nan ne kadai ake iya mu'amala da fasahar Intanet a dukkan fadin kasar nan[12].

Zuwa shekarar 1998 sai aka fara samun kamfanonin sadarwar Intanet masu zaman kansu.  Kamfanin farko shi ne Hyperia, wanda ya bude ofishi a Kaduna, kuma yake jona kwamfutoci da fasahar Intanet ta hanyar makalutun sadarwar tarho, watau Dial-up kenan.  Daga nan sai hukumar gwamnatin tarayya watau NITEL ta bude kafar bayar da lasisin bude ire-iren wadannan kamfanoni da kuma mashakatar tsallake-tsallake, watau Cyber Café, a shekarar 1999.  A shekarar ne ta bayar da lasisi wajen 40 ga masu bukata, amma galibinsu a biranen Legas ne da Kaduna.  A wannan shekarar ne dai fasahar Intanet ta samu isowa Kano birnin dabo, kuma akwai tabbacin cewa ta sanadiyyar wannan kanfani ne mai suna Hyperia[13]. Daga nan aka samu masu bude wuraren mu'amala da fasahar Intanet a manyan biranen kasar nan, irinsu Legas, da Kaduna, da Kano, da Jas, da Abuja, da Fatakwal da sauransu.

A daidai wannan lokaci fannin sadarwar tarho bai bunkasa ba. Domin layukan tarho duk na gida ne (Land Lines), kuma babu yanayin sadarwa mai inganci.  Duk da cewa akwai kamfanin sadarwar wayar tarho na Intercellular da ke aiwatar da sadarwa ta wayar iska, amma fannin bai bunkasa ba sai cikin shekarar 2000, sadda gwamnatin tarayya ta bude kafar zuba jari a fannin.  Daga nan ne aka samu kamfanonin sadarwar tarho da muke dasu a yanzu.  A halin yanzu, kamar yadda bayanai suka nuna a baya, akwai layukan tarho masu rai sama da miliyan 90 a kasar nan.  Wannan adadi ya dada taimakawa wajen yaduwar sauran fasahohin sadarwa musamman fasahar Intanet, da fasahar Imel, da fasahar Infra-red, da fasahar Bluetooth da dai sauran makamantansu.  Ba wannan kadai ba, an samu bunkasar tsari da ingancin sadarwa a bangaren fasahar tauraron dan adam. Wannan yayi sanadiyyar habaka wannan fanni mai muhimmanci da tasiri, inda a yanzu kusan galibin jama'an da ke birane da kauyuka sun mallaki wayar tarho. Sanayya kan kwamfuta ya karu, haka ma'adanan bayanai irinsu Flash Drive, da Memory Card, da Hard Disk, da nau'ukan faya-fayan CD da DVD duk sun zama 'yan gari a idon jama'a.

Dalilan Yaduwar Fasahar Sadarwar Zamani

Kayayyakin fasahar sadarwar zamani suna da saurin yaduwa cikin jama'a. Daga cikin dalilan da ke haddasa haka akwai saukin mu'amala; ko baka iya karatu ba kana iya sarrafa wayar salula misali, ta hanyar aiwatar da kira, da amsa kira da dai sauransu. Ba wayar salula kadai ba, duk galibin kayayyaki da hanyoyin fasahar sadarwa haka suke.  Kuma tunda galibin dabi'ar dan adam ta fi karkata zuwa ga sauki, sai hakan ya basu saurin yaduwa a kasashen duniya. Abu na biyu shi ne saukin farashi.  A farkon bayyanar wayar salula Najeriya suna da dan karen tsada. Amma ta dalilin yawaitansu a kasuwa daga kamfanoni daban-daban, an samu saukin farashi, wanda hakan ya bayu zuwa ga shahararsu a tsakanin jama'a.  Sannan samun na'uka daban-daban ma ya kara musu yaduwa.  Domin kowane irin matsayi kake, ko wane irin dandano kake dashi, akwai irin waya da ta dace da kai.  Sai tsarin zumunci a tsakanin kayayyakin sadarwa, watau Network Convergence.  A yanzu kana iya aiwatar da sadarwa tsakanin kwamfuta da wayar salula, ta hanyar sakonnin tes, ko Imel, ko aikawa da hotuna masu motsi, ko daskararru.  Dukkan wannan shi ma ya taimaka wajen yaduwar fasahar sadarwa a duniya baki daya.  A daya bangaren kuma akwai bunkasar binciken ilmi kan hanyoyin sadarwa a duniya.  Dukkan abin da wayar salula za ta iya aiwatarwa, ko kwamfuta, ko wani tsari da wani hanyar sadarwa ke amfani dashi wajen aiwatar da sadarwa, duk hakan ya samu ne sanadiyyar binciken ilmi da malamai ke yi a jami'o'i da kamfanonin sadarwa a warwatse a duniya.  Sannan akwai samuwar hanyoyin sadarwa masu inganci, ta amfani da fasahar tauraron dan adam, wanda wannan ya dada taimakawa wajen samun yanayin sadarwar tarho mai inganci a duniya.  Hatta a Najeriya an samu ci gaba a wannan fanni, idan muka kwatanta da yadda yanayin yake a farkon bayyanar wannan tsari.

Idan muka koma bangaren fasahar Intanet za mu ga cewa ta fi dukkan sauran hanyoyin sadarwa shahara da tasiri a tsakanin jama'a.  Hakan ya faru ne sanadiyyar wasu dunkulallun dalilai guda uku[14]; dalilin farko ya riga ya gabata, watau saukin mu'amala. Sai dalili na biyu, watau game duniya.  Duk inda kake kana iya mu'amala da fasahar Intanet muddin ka mallaki na'urar da za ta baka daman hakan.  Kana iya shiga ta kowace kafa, ka fita ta kafar da kake so, sannan a lokacin da kake so; babu kaidi.  Dalili na karshe shi ne, dangane da abin da ta kunsa, fasahar Intanet wata jakar magori ce; duk abin da kake nema yana ciki.  Daga warakar jahilci zuwa warakar lafiyar jiki, duk akwai. Daga sana'a zuwa neman aiki, duk akwai. Daga zumunci zuwa nazarin ilmi, duk akwai.  Haka idan ka koma bangaren nau'in hanyoyin sadarwa – daga talabijin, zuwa tsarin wayar tarho, da rediyo, da tasoshin tauraron dan adam – duk akwai su a cikin Intanet.  Intanet jakar magori ce, duk abin da kake nema akwai a cikin Intanet. Dukkan wadannan sifofi da dabi'u na cikin abin da suka haddasa yaduwa da bunkasar harkar sadarwar zamani a duniya baki daya.
Abu na karshe da ya dada taimakawa wajen yaduwar wadannan hanyoyi da kayayyakin sadarwa a duniya akwai ingancin ka'idojin kimiyyar sadarwa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke taimakawa wajen samarwa.  A bangaren Intanet akwai kungiyar Internet Corporation for Assigned Names and Numbers (ICANN) wacce ke da alhakin samar da adireshin gidajen yanar sadarwa a Intanet. Sai  kungiyar Internet Engineering Task Force (IETF) wacce ke da alhakin samar da ka'idojin da fasahar Intanet ke gudanuwa a kansu a cikin kwamfuta, irinsu IP Address da sauransu.  Sannan akwai kungiyar World Wide Web Consortium (www3) wacce ke da alhakin samar da ka'idojin habbaka shafuka da gidajen yanar sadarwa da tsarin isa gare su cikin sauki, a kwamfuta ne ko a wayar salula.  A bangaren sadarwar wayar tarho kuma akwai kungiyar International Telecommunication Union (ITU).  Ita kuma aikinta shi ne habbaka tsari da yanayin sadarwar tarho a duniya baki daya.  Bayan wadannan akwai wasu kungiyoyin kuma a bangaren kerawa da tsara na'urorin sadarwa da lantarki.  Dukkan wadannan sun taimaka gaya wajen samar da inganci, da shahara, da kuma gamewa ga kayayyaki da hanyoyin fasahar sadarwar zamani.

Fa'idojin Fasahar Sadarwa Ga Al'ummar Najeriya

Kamar sauran al'ummomin da ke wasu kasashe, al'ummar Najeriya na amfana da kyawawan tasirin fasahar sadarwar zamani, wanda kuma wannan ya dada taimakawa wajen inganta zamantakewa a tsakaninsu.  Abu na farko shi ne fa'idar sadarwa, abin da a baya ya ta'azzara, sanadiyyar rashin yaduwar hanyar sadarwa da rashin ingancin yanayinsa.  Sadarwa a yanzu abu ne mai sauki; ba wai a tsakanin al'ummar kasar kadai ba, hatta zuwa wasu kasashe duk dan Najeriya na iya aiwatar da sadarwa.  Domin a halin yanzu tsarin fasahar sadarwar tarho ya game duniya. Kashi 90 cikin 100 na kasashen duniya duk suna aiwatar da sadarwa a tsakaninsu.  Wannan tsari ya taimaka har wa yau wajen neman bayanai da nazarin ilmi.  Ta hanyar Intanet samun bayanai ya sawwaka.  Kana iya gabatar da binciken ilmi, ka tantance bayanan da kake so, ka rubuta abin da kake son rubutawa ba tare da ka je dakin karatu ba a jami'arku; duk ta albarkacin Intanet.  Har wa yau ta wadannan hanyoyin sadarwa harkokin da'awan addini musamman na Musulunci sun habaka. Daga wayar salula zuwa kwamfuta, duk kana iya samun bayanan shiriya kan addini, kana iya aika fatawa, zuwa ga wani malami da ke wata uwa duniya, ya aiko maka da amsa nan take ba tare da bata lokaci ba. 

A daya bangaren kuma akwai tsarin karatu da karantarwa, akwai tsarin neman magani ko waraka na bangaren lafiya, duk ta hanyar Intanet. Akwai hanyoyin neman aiki, da hanyoyin sana'o'i daban-daban duk ta Intanet.  Daga gidanka kana iya yada manufofinka ta hanyar Intanet ko wayar salula, kamar yadda 'yan siyasa ke yi a lokutan zabe.  Kana iya mu'amala da hukumomin gwamnati; musamman makarantu.  Domin a yanzu galibin makarantun gaba da sakandare da ke Najeriya duk sun mallaki shafin Intanet, inda za ka je ka nemi bayani kan makarantar, da yadda ake daukan dalibai, sannan kana iya yin rajista a matsayinka na sabo ko tsohon dalibi, duk ta wannan kafa.  Bayan dukkan wadannan, kana iya yankan tikitin jirgi a Najeriya ta hanyar Intanet. 
A bangaren wayar salula an samu ayyukan yi musamman ga masu gyara wayar salula, da masu sayar da su, da masu sayar da katin waya, an kuma samu ayyukan yi ta bangaren kamfanonin sadarwa da ke da rajista a kasar.  Har wa yau, fasahar Intanet ta samar da aikin yi ga masu mashakatar lilo da tsallake-tsallake, watau Cyber Café.  Sannan hukumar tarayya ta samu kudaden shiga ta hanyar haraji da take karba daga wadannan kamfanonin sadarwa, da kuma kudaden lasisi masu dimbin yawa da a baya ta karba.  Wannan, kadan ne daga cikin fa'idojin da fasahar sadarwar zamani ke samarwa ga al'umma.

Kalubale da Matsaloli Ga Al'umma

A daya bangaren kuma, yaduwar hanyoyin sadarwar zamani na da nasa aibun ko kalubale, musamman ga matasa; ganin cewa su suka fi yawan mu'amala da shi a kullum.  Abu na farko dai shi ne yawaitan bayanai a lokaci guda, a kuma muhalli guda.  Wannan tsari, wanda tsohon Shubaban kamfanin Microsoft watau Bill Gates, ya kira Information Overload, abu ne mai cutarwa sosai.  Domin idan ba kana da mizanin tantancewa ba, sai ka rasa wanne za ka dauka.  Abu na biyu shi ne: wadannan hanyoyi da kayayyakin sadarwa suna yin mummunar tasiri a kan kwakwalwa da tunanin dan adam, kamar yadda suke da tasiri a kan dangantakarsa da 'yan uwansa ko abokanansa, da tasiri kan lafiyarsa, da tasiri kan lokacinsa, da kuma tasiri kan manufofinsa – musamman idan ya kamu da ciwon shakuwa dasu.  Wannan kan kai shi ga shiga wani hali da rayuwa cikin kawalwalniya, da gaugawar zuci ko ci-da-zuci, da kuma dawwamammiyar kadaici.

Daga cikin kayayyaki da hanyoyin sadarwar da aka fi samun wadannan matsaloli dai akwai kwamfuta, wacce ke dauke da fasahar Intanet, da wayar salula, da kuma wasu masarrafan sadarwa da ke dandalin abota irinsu Facebook, da MySpace, da NetLog, da Twitter, da sauran majalisun tattaunawa na Intanet irinsu Yahoogroups, da Googlegroups da sauran makamantansu. 

A ire-iren wadannan majalisu da dandamali, akwai matsaloli masu dama da suka hada da: cin mutuncin addini (musamman Musulunci), da leken asiri saboda rashin sirri da ke tattare da su, da yawan gulma da hirar banza, da haifar da tsana da hassada, da samar da gajiya da damuwa, da haifar da kashe-kashe da ta'addanci ga mutunci, da batsa da ashararanci, da yawan shagala da shagaltarwa, da kuma uwa uba munanan akidu da al'adu.  Wadannan dunkulallun matsaloli ne da galibin matasa musamman basu cika damuwa da su ba a yayin da suke ta'ammali da wadannan masarrafai. Matasa kan kashe lokacinsu a dandalin Facebook musamman, suna hirar banza mara alfanu; ka ji mutum na cewa "yanzu na tashi daga bacci," ko "bacci nake ji," ko "abu kaza nake ci," ko "wance ta bata min rai…" da dai sauran shirme marasa amfani.  Maimakon fasahar Intanet ta taimaka mana wajen amfani da kwakwalenmu mu fa'idantu da alherin da ke ciki, sai mu buge da shashanci.

A daya bangaren kuma, wayar salula na da nata matsalolin.  Da farko dai wayar salula taskar ajiya ce.  Wayar salula kundin tarihi ce.  Wayar salula na'urar sauraran sauti ne.  Wayar salula kafar mu'amala da fasahar Intanet ce.  Sannan kana iya amfana da ita wajen aikawa da sakonnin tes masu fa'ida.  To amma mutum nawa ke haka daga cikin matasa?  Da yawa daga cikinmu kan kwana muna hira da 'yan matanmu ne ko samarinmu.  Mun dauka kamfanin MTN ko Etisalat da ke bayar da wannan dama, wawaye ne.  Da yawa daga cikinmu wayoyin salularmu na dauke ne da hotunan 'yan mata da samari.  Da hotunan bidiyo na batsa ko na raha da shashanci.  Da sakonnin tes na soyayya zalla ko na raha da shashanci. Da kuma masarrafai masu shagaltarwa irinsu Facebook, da 2go; masu dauke kaso mafi tsoka na lokutanmu a rayuwa.  Da wayar salula muke satar amsa a makarantu.  Galibi idan kaji dalibi ko daliba na cewa "ance an ga wata," ko "muna jiran ganin wata ne," to, za ka samu tana jiran a turo mata satar amsa ne a wayarta. Amma ko kadan ta kasa amfana da wayar salularta wajen taskance darasin malami. Ta kasa amfani da masarrafar 2go da ke cikin waya wajen tattaunawa da sauran dalibai 'yan uwanta kan darussan da aka karantar da su.

Abu na gaba shi ne rashin tantance ingancin bayanai da ke Intanet ko wadanda ake turo mana a waya.  Da zarar lokutan azumin Ramalana sun shigo, za ka ji sakonni na ta shiga wayarka daga wajen 'yan uwa da abokan arziki.  Sau tari wasu daga cikin hadisan da ake turo su ba ingantattu bane ko kadan.  Musamman wadanda ake turowa kan falalar watan Rajab, da falalar wanda ya sanar da wani shigan watan Ramalana.  Har wa yau, akwai matsala wajen yadda muke ciro bayanai masu alaka da shari'a daga Intanet.  Domin kuwa ba kowa bane yake da mizanin tantance ingantacce daga mai rauni.  Wannan ba karamin kalubale bane a gare mu matasa.

A daya bangaren kuma, duk da habbaka da bunkasar wannan fanni a Najeriya, har yanzu muna fama da matsalar rashin ingancin tsarin sadarwar Intanet da rashin yanayin sadarwar wayar salula.  Wannan ke sa mu kasa amfana da katin da muke sa wa wayoyinmu, musamman ga wadanda suke karkara. Shi yasa kuma har wa yau, za ka ga mutum daya da wayoyin salula guda uku rikis a hannunsa, ko ka ganshi da wayar salula mai amfani da layuka uku, duk saboda tsoron rashin tabbacin da ke tattare da yanayin sadarwar kamfanonin waya ne.  Idan akwai ingancin sadarwa, duk ba ka bukatar daukan wayoyi ko layuka sama da guda daya.

Bayan dukkan wadannan, akwai matsalar tsaro.  Domin sata ya koma kan wayoyin salula da kwamfutoci yanzu.  Galibin lokuta da zarar barayi sun tsare mutane ba abin da suke kwacewa a farko sai wayoyinsu.  Haka idan mota aka gani da jakar kwamfuta ko wayar salula, nan take ana iya fasa gilashin motar a dauke.  Wannan kalubale ne ga hukuma.

Hanyoyin Gyara da Ci Gaba

Wajibi ne ga matasanmu su koyi ladabin mu'amala da wadannan kayayyaki da fasahar sadarwar zamani.  Abu na farko da ya kamata su sani shi ne, wadanda suka kirkiri wadannan kayayyakin fasaha, duk da 'yancin da muke ganin yana tare dasu kayayyakin, dabi'arsu da akidarsu da addininsu sun sha bamban da namu.  Don haka wajibi ne mu koyi tarbiyya wajen ta'ammali da lokaci, da ta'ammali da manufa.  Domin idan ka kasa tantance manufarka a yayin mu'amala da wadannan abubuwa, shi zai sa komai ka gani ka shagaltu da shi.  Idan haka ta faru kuwa, za ka zama kamar yaro a kantin alawa.  Abu na gaba shi ne tarbiyyar dabi'a da zuciya.  Ma'ana, mu zama masu kiyayewa cikin abubuwan da muke yi a wadannan wurare.  Idan al'amura sun cushe maka, dole ne ka zama mai neman shawara, musamman kan nau'ukan bayanan da aka aiko maka ta waya ko ta Imel ko ka karanta a shafukan Intanet masu alaka da shari'a.  Idan ba ka da mizanin tantancewa, ka nemi shawara wajen kwararru.

Har wa yau, ka zama mai manufa a dukkan abin da kake yi. Wannan zai sa ka ribaci lokacinka, da lafiyarka, da kwarewarka, da kuma ilminka.  A daya bangaren kuma, wajibi ne ga iyaye su rika lura da 'ya'yansu, su koya musu tarbiyya, ta yadda ko da ba su kusa da su, za su kiyaye, su lazimci abin da yake daidai.

A karshe, yana da kyau Gwamnatin tarayya da na jihohi su kara kaimi wajen tabbatar da samuwar ingantacciyar hanyar sadarwa ta amfani da fasahar tauraron adam.  Sannan su karfafi hukumomin da ke da alhakin bunkasa wannan fanni, tare da samar da wutar lantarki mai inganci a kasa baki daya, don dada sauke farashin sadarwa.  Sannan ta samar da tsaro ga jama'a da dukiyoyinsu, ta hanyar karfafa tsarin rajistan layukan waya, a karshe kuma ta samar da Babbar Rumbun Babayanai na kasa, watau National Database, don samar da kyakkyawan shugabanci a kasa baki daya.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a tabbace yake cewa yanzu ne muka fara cin gajiyar wannan fanni na fasahar sadarwar zamani.  Da zarar hukuma ta taimaka wajen samar da muhalli mai kyau, al'amura da zau dada inganta, a samu karin ci gaba.


[1] The World in 2011: ICT Facts and Figures – www.itu.int
[2] World Internet Users and Population Statistics, March 2011 – www.internetworldstats.com
[3] The World in 2011: ICT Facts and Figures – www.itu.int
[4] Facebook Users in the World, 2011 Q2 - www.internetworldstats.com
[5] The World in 2011: ICT Facts and Figures – www.itu.int
[6] African Telecommunication/ICT Indicators 2008: At a Crossroads – www.itu.int
[7] Nigeria Mobile Market: Overview, Statistics, & Forecasts – www.budde.com.au
[8] ICT Statistics Newslog: SMS -  www.itu.int
[9] Are We Digital Dummies? –  www.cbc.co.ca/doczone
[12] Malam Magaji Galadima, Kaduna, Najeriya.
[13] Fasahar Intanet a Sawwake: Abdullahi Salihu Abubakar, 2009, Abuja, Najeriya.
[14] The Death of Distance: Frances Cairncross, Harvard University Press, 2000. Shafi na 95-98