Thursday, January 15, 2009

Labaran Mako

NIGCOMSAT-1 Ya Samu Matsala Cikin Falaki

Tauraron dan Adam da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta harba cikin falaki shekara da wasu watanni da suka gabata mai suna NIGCOMSAT-1, ya samu matsala a halin shawaginsa cikin falaki. Hukumar da ke lura da tauraron, watau Nigerian Communication Satellite, ta bayyana haka cikin makon da ya gabata. Hukumar tace ta gane hakan ne sanadiyyar yakewar sadarwa tsakanin tauraron na NIGCOMSAT-1, da kuma cibiyar da ke lura da shawaginsa a falaki, wanda hakan ke nuna cewa ya daina aiki sanadiyyar wasu matsaloli da ya ci karo dasu a cikin falakin da yake sulmiya. Wannan, a cewar Hukumar, “shi yasa aka dakatar dashi.”

A farkon al’amari dai akwai jita-jita da ake ta yadawa cewa tauraron ya bace ne, ba a ma san inda yake ba cikin falaki. Wannan tasa jama’a suka yi ta mamakin wannan zance mara kan-gado: “ta yaya za a ce ya bace, bayan harba shi aka yi, kuma ana lura dashi?”, a cewar wani bawan Allah mai suna Malam Murtala Baba Aminu Kalgo. Amma daga baya sai Hukumar ta tabbatar da cewa ba bacewa yayi ba, ya samu matsala ne da fika-fikansa masu taskance masa makamashin hasken rana, watau solar panels, wanda hakan ke taimaka masa wajen cajin batirin da yake dauke da shi. Wannan tasa injinsa ya tsaya, don batirin yayi rauni, baya iya juya injin da ke gudanar da tauraron gaba daya. Ga al’ada kowane tauraron dan Adam na da hanyoyin samun wutar lantarki ne kashi biyu; akwai batir mai taimaka masa yin rayuwa cikin dare ko duk lokacin da wannan duniya tamu tayi masa shamaki daga hasken rana, da kuma fika-fikai biyu masu kallon rana. Aikinsu shine taskance makamashin hasken rana, wanda tauraron ke amfani dashi kai tsaye, tare da taimaka wa batirin yin caji lokacin yini.

A karshe dai Hukumar ta baiwa kamfanonin da wannan matsala ta shafa hakuri, da kuma cewa kada su damu, za a sada su da wani kamfanin da zai ci gaba da basu bayanan da suke bukata, kafin gwamnatin Nijeriya ta samu wani tauraron daga kamfanin da ya kera NIGCOMSAT-1. Wannan ke nuna cewa NIGCOMSAT-1 ya kwanta dama kenan. Hakan ya haddasa kace-nace a tsakanin ‘yan Nijeriya masu lura da abinda ke kai ya kawo. Shin wannan na nufin cibiyar da ke lura da wannan tauraro ba ta ganin shawagin da yake yi kenan a aikace cikin falaki, sai dai kawai ta samu sakonni daga gareshi? Kenan ba don sun kasa samun sakonni daga tauraron ba, da shikenan, sai ya zama sharar cikin falaki (space junk), ba wanda ya damu. Amma sai dai kuma sabanin yadda mutane ke zato, bah aka lamarin yake ba. Kamfanin da ke lura da wannan tauraro dai ta dakatar dashi cikin falaki, cikin wani irin yanayin da kanikawansa zasu iya duba shi don gano cikakken dalilin da ya haddasa masa wannan tsayawa cikin kankanin lokacin.

Gwamnatin Nijeriya dai ta mallaki tauraron NIGCOMSAT-1 ne cikin shekarar 2007 ta hannun wani kamfanin sadarwa na kasar SIN (China), a kan kudin da kimarsa ta kai Naira Biliyon Arba’in (N40B). Manufar mallakar wannan tauraro shine don taskance bayanan da suka shafi yanayi (Weather Forecast), da kuma taimaka wa kamfanonin sadarwa wajen yada bayanai. Har wa yau, akwai gidajen rediyo na FM da ke amfani da wannann tauraro wajen yada shirye-shiryensu. Wadannan kamfanonin sadarwa na biyan gwamnatin tarayya kudaden wannan aiki ne a duk farkon watanni hudu. Yanzu haka akwai kamfanonin da suka biya kudi ba tare da sun amfana da ko harafi guda ba, sai tauraron ya kwanta dama. Wannan tasa dole a hada su da kamfanin da zai basu bayanan da suke bukata, kafin a samu wani tauraron dabam.

Tasirin Fasahar Intanet Kan Nasarar Barack Obama

Gagarumar nasarar da Mr. Barack Obamaclip_image002 ya samu a zaben shugaban kasa da aka gabatar a Amurka makonni biyu da suka gabata ya samu tagomashi ne daga tasirin hanyar sadarwa ta Intanet da yayi amfani da ita wajen kamfen da kuma neman agaji daga ‘yan kasa da ke ciki har wajen kasar Amurka. Wani kididdiga da wani gidan yanar sadarwa ya fitar kwanaki biyu bayan zaben, ya nuna cewa kashi sittin cikin dari na tallafin kudi (donations) da Mr. Barack Obama ya samu duk ta hanyar Intanet ne. Kuma duk da cewa Mr. John McCain, abokin hamayyarsa ne ya fara amfani da wannan hanya ta Intanet wajen yin kamfen, amma Mr. Barack Obama ya shallake shi nesa ba kusa ba, inda bayan yayi tasiri a zukatan masu shawagi a Intanet ‘yan kasar Amurka (da ma wasu kasashe), ya kuma ci gaba, inda ya samu karbuwa har gidan yanar sadarwarsa ya zama wani dandalin bayar da tallafi da gudummuwar kudi.

Bayan gidan yanar sadarwar da ya gina don gabatar da kamfen, wanda ke http://www.barackobama.com, wadanda suka dada taimakawa su ne gidajen yanar sadarwar magoya bayansa, wadanda tasirinsu ya fi na gidan yanar sadarwarsa. “Shine ya fara amfani da sabbin hanyoyin yada manufofi wajen neman magoya baya, ya kuma nemi goyon bayan wasu sabbin kungiyoyi, sannan ya sauya tsarin yadda ake yakin neman zabe a Amurka”, inji Mr. Simon Rosenberg, tsohon shugaban kungiyar yakin neman zaben Mr. Bill Clinton a shekarar 1992. A yayin da wasu ke kokarin sanin manufofi da kuma tsare-tsaren Mr. Barack Obama ta hanyar gidan yanar da ya tanada a Intanet, dubunnan magoya bayansa, ‘yan a-mutun-Obama, suna can sun kirkiri gidajen yanar sadarwa don taimaka masa yin hakan, tare da shirya tarurrukan neman agaji da tallafin kudi ta hanyar wadannan gidajen yanar sadarwa. An kirkiri a kalla kungiyoyi sama da dubu talatin da uku ta wadannan gidajen yanar sadarwa. Kuma an kiyasta cewa Mr. Barack Obama ya samu tallafin kudi daga magoya bayansa, wadanda suka bayar da tallafinsu ta hanyar katin adashin bankinsu (watau Credit card) a gidan yanar, sama da dalar Amurka miliyan dari shida ($600M) – wajen naira biliyan saba’in da daya da miliyan dari hudu kenan (=N=71.4B)! Wannan zunzurutun kudade an same su ne daga mutane miliyan uku – tsakanin kwabo da taro da sisi da sule. A tarihin siyasar Amurka, babu wanda ya taba kashe kudi wajen yakin neman zabe irin Mr. Barack Obama. Domin a yayin da abokin hamayyarsa Mr. John McCain ya kashe dalar Amurka miliyan dari tara da ‘yan kai, Mr. Barack Obama ya kashe dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari shida da arba’in ($1,640M) - . Kusan dukkan wadannan kudade tallafi ne daga magoya baya.

Bayan hanyar sadarwa ta Intanet da Obama yayi amfani da ita, miliyoyin magoya bayansa da aka ribato ta wannan hanya sun yi amfani da hanyar tarho, musamman wayar salula, wajen nemo masa magoya baya a sauran jihohi; daga ‘yan uwa zuwa abokan arziki. Har wa yau, shi kansa Mr. Obama yayi amfani da tsarin gajeren sakon wayar salula, watau SMS, wajen aikawa da sakonni ga magoya bayansa. Duk wanda ke son a rika aiko masa da sako, sai ya aika da kalmar “hope” zuwa wasu lambobi da aka bayar, don a taskance lambar wayarsa. Wannan ya sa Mr. Barack ya samu karbuwar da ba a samu wanda ya samu irin sa ba a siyar Amurka. Ya samu gagarumar nasarar da ba a samu wanda ya samu irinsa ba, sannan sanadiyyarsa, an samu fitowar masu jefa kuri’a, inda kashi tamanin cikin dari suka fito don jefa kuri’arsu, wanda ba a taba samun irin sa ba tun shekaru dari da suka gabata. Don haka kwana daya da samun nasarar Mr. Obama, jaridu sun yi karanci a birnin Washington, inda aka yi ta warwasonsu kamar kosai. Wasu su kwashi biyar, wasu shida, wasu goma. Kai wasu ma dauri guda suke son a sayar musu. Wannan tasa sai da kamfanonin sayar da jaridu suka kafa doka, cewa duk wanda ya zo saya, kwara daya za a sayar masa, don wasu ma su samu. Wasu kamfanonin sai da suka kara buga wasu kwafe. Misali, jaridar The Washington Times ta kara buga kwafe dubu sittin, don wadanda ta buga sun yi karanci. Duk dai wannan, kamar yadda mai karatu ya sani, saboda shaharar Mr. Obama ne; kowa na son ya samu tarihi a gidansa; wasu ma su ce don jikokin su su taso ne su gani.

Kamfanin Sadarwa na Etisalat Ya Iso Birnin Abuja

Idan ba a mance ba, cikin shekarar 2006 ne gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa Obasanjo, ta baiwa kamfanin Etisalat lasisin fara hada-hadar sadarwar wayar salula nau’in GSM a Nijeriya gaba daya. Wannan lasisi ya fito ne daga Hukumar Bunkasa Harkar Sadarwa ta kasa, watau National Communications Commission (NCC), wacce ke da alhakin sanya farashi da kuma ka’idojin da duk wani kamfanin sadarwa zai biya ko bi, don samun gabatar da harkar sadarwa a Nijeriya.

Bayan lasisin da aka baiwa kamfanin a shekarar 2006, ya dau tsawon shekara daya da rabi yana ta tsare-tsaren kafuwa don fara tafiyar da harkokinsa a kasar; ta hanyar kafa cibiyoyin sadarwa masu dauke da na’urorin sadarwarsa, da mallakar ofishi a wurare irin su Legas da ma wasu manyan biranen kasan. Bayan haka, kamfanin yayi ta maza wajen biyan kafafen yada labarai don tallata hajojinsa kafin wannan lokaci. Har wa yau, kamfanin bai tsaya a nan ba, yayi amfani da kafar hanyar sadarwa ta Intanet, watau ta hanyar gidan yanar sadarwarsa da ke http://www.etisalat.com.ng, don soyar da hajojinsa ga masu sha’awar hulda dashi, ta hanyar yin tayin kyautar lamba ta musamman (special number) ga duk wanda ke so.

Yadda abin yake shine, za ka shiga gidan yanar sadarwar ne a adireshin da ke http://www.etisalat.com.ng, sai kaje kai tsaye zuwa shafin da ke maka wannan tayi, wanda ke zauren gidan yanar (Homepage), ka shigar da lambar da kake amfani da ita a yanzu a wayar salularka. Sai ka matsa alamar “send”, wacce za ta cillo maka wasu lambobi guda biyar nan take, da ake son ka shigar cikin shafin da ka aika da lambarka. Kana gama shigarwa, sai ka matsa alamar “confirm”, wacce a karon karshe za ta aiko maka da lambar da kamfanin ya tanada maka ta musamman. Za a zaftare lambobi ukun farko ne na lambarka, sai a bar maka sauran. Misali, idan kana da lamba kamar haka 080-247-88040, sai su baka lamba makamanciyarta, kamar haka 080-987-88040. A cikin sakon, akwai wasu lambobi guda bakwai, watau pass cord, wadanda ake son ka taskance a cikin wayarka. Da zarar kamfanin ya fara aiki (kamar yadda ya fara yanzu), sai kaje ofishinsu ka nuna musu lambar da aka tanada maka, tare da wadannan lambobi na pass cord. Da zarar ka je, zasu karbi lambobin, su shigar cikin kwamfutarsu, don tabbatar da cewa lallai haka ne. Sai su baka katin SIM din kamfanin. Idan ka samu lamba ta wannan hanya, kamfanin zai rika baka kyautar dakiku dari uku (30 seconds), ko mintuna biyar a kowace rana, kyauta; ka buga zuwa duk jihar da kake so a Nijeriya. Sannan kana da damar zaban garuruwa goma da kake son a rika maka sauki yayin da ka buga waya zuwa wadannan wurare. Wannan tsari na zaban garin da kake son a maka saukin caji, shi suke kira Home Zone.

Wannan kamfani na Etisalat dai babban kamfanin sadarwa ne na wayar salula da ke da rassa a kasashe sama da goma sha-hudu a Gabas-ta-Tsakiya. Daga cikinsu akwai irinsu Saudiyya da Kuwait da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa, watau United Arab Emirates. Kamfanin ya fara aiki ne a birnin tarayyar Abuja cikin makonni uku da suka gabata, kuma katin SIM dinsa naira dari biyu ne. Da zarar ka saya ka sanya, kana iya amfani dashi a dukkan kasar da kamfanin ke aiki. Kana iya mu’amala da fasahar Intanet muddin wayar salularka ta mallaki fasahar yin hakan, ka aika ko karbi sakonnin text. Haka idan ka kashe wayarka, duk wanda ya bugo alhalin wayar na kashe, za a sanar dashi halin da wayar ke ciki, sannan da zarar ka kunna, za a aiko maka da sakon text cewa “wane . . .ko kuma lamba kaza da kaza sun bugo lokacin da wayarka ke kashe”. Idan kana son ganin lambarka kai tsaye daga wayar salularka, akwai lambobin da za ka matsa, sai lambar ta bayyana nan take. Wannan duk kyauta ne! Bayan wannan, kamfanin na da wasu hajojin sadarwa masu kayatarwa da babu wani kamfanin sadarwa mai irinsa a nan Nijeriya. Kuma farashin cajinsa kusan daya ne da na kamfanin MTN, amma ya sha bamban da kamfanin MTN wajen yawaitan hajoji masu sawwake farashi ko kuma masu kayatarwa, wadanda kyauta zaka same su ba tare da ka kashe kwabonka ba.

Ko shakka babu, bayyanar kamfanin Etisalat a sahun kamfanoni masu hada-hadar harkar sadarwa a Nijeriya zai kara haddasa saukin farashin caji da wasu kamfanonin ke yi mara misali, ya kuma sa wasu hajojin su samu inganci. Misali, sanin kowa ne cewa daya daga cikin babbar matsalar da kamfanonin sadarwar wayar salula ke addabar masu mu’amala dasu itace rashin ingancin yanayin sadarwa, watau Network Service. Duk wanda yayi amfani da tsarin sadarwa ta Etisalat, zai samu bambanci nesa ba kusa ba. Duk da yake ta haka kowane kamfani ya faro, amma daga baya idan rumbun bayanansa suka cika da lambobi, sai a fara samun matsala. Sai dai, galibin masu amfani da layin Etisalat a kasashe irin su Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman birnin Dubai, sun shaida cewa lallai yanayin sadarwar kamfanin na da inganci da aminci. Amma, kamar yadda muka sani ne, komai na Nijeriya ya sha bamban da sauran kasashe.

Fatanmu dai shine jama’a su samu ingantacciyar yanayin sadarwa, da farashi mai sauki da kuma mu’amala mai kyau daga wajen ma’aikatan kamfanin Etisalat; ba ayi ta cika maka kunne da kade-kade ba duk sadda ka bukaci a warware maka wata matsala. Barka da zuwa Nijeriya, ITTISAALAAT!

BUNKASA HARSHE DA AL’UMMAR HAUSAWA: DAGA ADABI ZUWA KIMIYYA DA FASAHAR SADARWA TA ZAMANI (4)

Hanyoyin Bunkasa Ilimin Kimiyya da Fasaha

Bayan takaitattun bayanai kan irin matsalolin da ke addabar ci gaban rubuce-rubucen ilimi musamman na kimiyya da fasahar sadarwa cikin harshen Hausa, a yau za mu kawo kadan cikin hanyoyin da idan muka dabbaka su, za mu samu ci gaba in Allah Ya yarda. Akwai hanyoyin warware wannan matsala da dama, amma za mu takaitu kan muhimmai daga cikin su ne kawai. Hanya ta farko ita ce ta hanyar yawaita rubuce-rubuce kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere. Idan nace yawaita rubuce-rubuce, mai karatu ya daina tunanin rubuce-rubuce daga “kwararrun marubuta” kadai, kamar yadda abin yake a yanzu. A a, ina nufin duk wani mutum da Allah ya sawwake masa kwarewa a fannin kere-kere ko kimiyya da fasahar sadarwa; ko da kuwa ba ya ji ko iya rubutu da harshen Turanci ko Hausan boko. Idan mai gyaran mota ne kai, ka yi kokari ka rubuta wa al’umma irin hanyoyin da kake bi wajen wannan aiki, da irin nau’ukan matsalolin da motoci ke fuskanta, musamman ma wadanda ka ke iya gyarawa. Idan likita ne kai, kai wa Allah ka taimaki al’umma wajen rubuta wani abu cikin harshen Hausa; nau’ukan cututtuka ne ko yadda ake tiyata, duk wanda Allah Ya hore maka, ka rubuta. Idan kwararre ne kai a fannin hada magungunan zamani (pharmacist), ka rubuta mana bayanai kan matakan da kamfanonin da ke hada magungunan da muke ta sha, suke bi wajen yin hakan. Idan sunayen saiwowi ko ganyayyakin ne baka sani ba a Hausance, akwai wadanda za su taimaka maka da bayanai. Na tuna, shekaru kusan sittin da suka gabata, lokacin da Likita Bergery ya tashi rubuta Kamus din Hausa da Turanci a nan kasar, sai da yayi kusan shekaru biyar suna kai-komo da wasu bayin Allah masana sunayen ganyayyaki da itatuwa a kasar Hausa. Aikinsu kawai shine su rika gaya masa sunan itacen ko ganyen ko ciyawar, shi kuma yana rubutawa da Hausa. Haka idan Allah Ya sawwake maka iya gyaran babur, duk ka agaza wa al’umma wajen taskance bayanan yadda kake aikinka. Idan malamin makaranta ne kai da Allah Ya hore wa sanayya kan fannin lissafi, ka rubuta littafi guda kan yadda ake lissafi cikin harshen Hausa, da yadda ake warware dukkan matsalolin da suka shafi darussan da kake karantarwa. Idan manomi ne kai, na zamani ko na gargajiya, duk kana iya taimakawa. Haka idan mai gyaran kwamfuta ne ko wayar salula, ka rubuta littafi dan madaidaici, wanda zai sanar da masu mu’amala da wadannan kayayyakin fasaha hanyoyin da za su iya bi wajen warware ‘yan kananan matsalolin da ke addabarsu. Kada ka dauka wannan zai rage maka yawan masu kawo maka gyara, a a, sai ma ya kara. Don ka rubuta littafi kana bayanin ire-iren matsalolin da ke addabar kwamfuta ko wayar salula, da yadda ake hana faruwarsu ko ma magance su, ba shi zai sa a daina kawo maka gyara ba, sam. Kuma kada ka raina dan abinda ka sani. Mai girma ne a wajen wanda bai sani ba.

Wannan hanya ta yawaita rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na da muhimmanci ta bangarori biyu. Na farko shine, za a samu yawaitan abin karatu a wannan fanni. Na biyu kuma hakan zai cusa wa marubuta da dama sha’awar rubutu a fannin, maimakon takaituwa da nasu fannin kadai. Ga wadanda basu fara ba kuma zai samar musu abin yi da kuma dogaro. Haka kuma, za a samu tabbatacciyar tsarin rubutu cikin wannan fanni. Wannan hanya na bukatar matukar bincike kan fannin, tare da yin amfani da kwarewar da marubuci ke da ita wajen siffata hanyoyi ko tsarin da ilimin ya kebanta da su.

Sai hanyar gyara ta biyu, wacce ta kumshi fassarawa ko tarjama littafan da aka rubuta cikin wasu harsunan dabam, kan ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere. Wannan hanya na da muhimmanci ita ma, kuma ita ce galibin daulolin da suka yi fice a fannonin rayuwa dabam-daban suka dauka wajen bunkasa al’ummar su. Don haka, yana da muhimmanci a samu masana su fassara littafai da kuma rahotannin da ke dauke da sakamakon bincike kan nau’ukan ilimi masu yawa. Wannan zai taimaka wajen kara samar da abin karatu cikin fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere. Haka kuma zai kara habbakawa tare da motsa sha’awar marubuta a wasu fannonin. Bayan haka, babban abinda hakan zai kara dasawa shine, kyakkyawar fahimtar yadda tsarin wadannan nau’ukan ilimi ke gudanuwa a kai. Kamar yadda muka sani ne, duk yadda ka kai da fahimtar wani nau’in ilimi da aka karantar da kai cikin wani harshe, ba zai kai yawan fahimtar da za ka samu ba idan da harshenka aka karantar da kai. Don haka samuwar littafai da aka fassara daga wani harshen zuwa Hausa, zai kara gyatta fahimtar masu karatu a wannan harshe, su fahimci abin daidai. Domin a bayyane yake cewa galibin masu karatu cikin wadannan fannoni a halin yanzu cikin harshen Turanci, ba duk za su iya kwatanta maka ko karantar da kai ilimin da suka koya cikin harshen Hausa ba, har ka fahimce shi yadda ya kamata. Duk kuwa da cewa su sun fahimci ilimin cikin harshen da aka karantar da su. Idan aka bunkasa harkar tarjama da fassara, babu shakka tsarin ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da na kere-kere zai samu bunkasa shi ma.

Hanya ta gaba ita ce, a shigar da wadannan nau’ukan ilimi cikin abinda ake karantar da masu koyon harshen Hausa daga Firamare zuwa Jami’a. Tirkashi! Ba zan mance ba, lokacin da nake sakandare, an karantar da mu ilimin magungunan gargajiya, cikin harshen Hausa. Wannan ya taimaka mani matuka wajen fahimtar abubuwa da dama. Har nake tunanin cewa, da a ce za a dore da wannan tsari, ko da tun muna Firamare aka fara karantar da mu, da na dauki fannin ilimin sarrafa magunguna, watau Pharmacy a Jami’a. Domin na samu kyakkyawar fahimta kan hakan. Yin haka tun daga Firamare na da tasiri wajen cusa wa yara fahimtar tsarin da kayayyakin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere ke gudanuwa a kai. Kuma na tabbata tun nan za a samu masu sha’awar wadannan fannoni; ko dai wajen karantarwa ko kuma karatu. Shekarun baya da suka gabata, hatta harshen Hausa galibi da Turanci ake karantar dashi a jami’o’in kasar nan. Wanda ya fara yin kuru wajen sauya wannan tsari shine Farfesa Muhammad Hambali Jinju. Ga abinda yake cewa, lokacin da Jaridar AMINIYA ta yi masa tambaya kan hidimar da yayi wa harshen Hausa: “...kokarin da nayi, shi ne kokarin da duk jama’a suka sani kuma suka shaida, kuma sun sani kuma suna fadi, musamman ma malaman Hausa, wadanda na karantar da su a Jami’o’i. Na san dai nayi iyakan kokari na kan Hausa, yadda ta haka har ta samu ci gaba. Idan zan ba ka misali, lokacin da naje Kwalejin Abdullahi Bayero, Kano, na iske duk kwasa-kwasan Hausa, da Turanci ake koya su. Ni na yi kokarin aka maida koyarwa da Hausa. A tsarin jami’a a lokacin, da Turanci ake koyarwa, amma ni da na je na rika koyarwa da Hausa. Duk da na san laifi ne kuma kasada ce, sai kawai na canza zuwa tsari na. Ni kai na ban san abinda ya ingiza ni na dauki wannan mataki ba. Ko kishin Hausar ne, ko kuwa kuruciya ce, ni dai ban iya bambancewa ba.”

Hanya ta gaba mai kamar wuya, ita ce, a samu wata cibiyar bincike ko makaranta ta musamman, wacce za ta dauki nauyin karantar da ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere musamman, cikin harshen Hausa. Ba kowa zai yarda da wannan shawara ba, amma kuma in har za a dabbaka ta, za a samu ci gaba. A kasashen Larabawa (irin su Saudiyya da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa) suna da makarantu irin wannan. (Duk da yake na san tsarinmu da nasu ya sha bamban, wajen shugabanci da kuma tsarin dokar kasa). Akwai malamai kwararru kan ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, kuma masana kan harshen larabci. Idan ka shiga makarantar, akwai kwasa-kwasan Turanci kam, amma galibin abinda za ka koya duk da harshen Larabci za a koyar da kai. Wannan tasa a yanzu ake samun masana harkar likitanci da fasahar sadarwa kwararru. Wannan har wa yau yayi tasiri wajen bunkasa tsarin rubuce-rubuce cikin wadannan fannoni da harshen Larabci. Sai ka ga littafi kan ilimin kwamfuta da tsarin hada alaka a tsakanin kwamfutoci, watau Networking, an rubuta shi tsaf, da harshen larabci. Ga hotuna da taswirori da komai da komai. Ko ka ga littafi kan yadda ake warware matsalolin lissafi, duk cikin harshen Larabci. Me zai hana mu samu wata hukuma ko gwamnatin jiha a Arewa, ko kuma wani mai kishin al’ummar Hausawa, ya bude mana irin wannan makaranta mai suna makamanciyar wannan: Hausa Institute of Science and Technology (Cibiyar Binciken Kimiyya da Fasahar Kere-kere Cikin Harshen Hausa)? Wannan ba ya nufin mu daina amfani da harshen Turanci, maimakon haka ma, zai kara wa ‘ya’yanmu kwazo ne a makarantun da suke zuwa. Wadanda basu kware a Turanci ba, zasu yi kokarin kwarewa, don sun san cewa duk abinda zasu rubuta ko karanta don karantarwa ko rubuta wani littafi a wannan fanni nan gaba ko a yayin da suke karatun, daga littafan turanci za su tsamo su.

Har wa yau, zai dace a samu mujallu da jaridu na musamman kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa, masu fitowa a duk mako ko wata. Hakan zai kara cusa wa al’umma sha’awar abin, don za a samu marubuta masu yin bayani filla-filla kan fa’idojin da ke tattare da bunkasa wannan fanni, tare da yin sharhi kan muhimman ci gaban da ake samu a fannonin a duniya. Tabbas muna sane da matsalar da ke addabar Arewa kan batun assasawa da kuma rike kamfanin jarida ko mujallu musamman a shekarun baya, amma yanzu an farfado, kuma ga dukkan alamu za a dore a haka in Allah Ya yarda. Don haka samun ire-iren wadannan kafafen ilimantarwa zai taimaka matuka wajen bunkasa wannan fanni.

Abu na karshe da zamu kawo shine, a samu wani tsari na gamayyar masana harshen Hausa, da zai rika lura da kuma tantance kalmomi na musamman kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, ta amfani da harshen Hausa. Domin rashin wannan tsari na cikin abinda ya kara rage wa wannan fannin armashi. Wasu na son su yi rubutu amma samun kalmomin da suka dace da abinda suke son rubutawa ko fassara shine babban matsalansu. Misali, akwai karancin kalmomin Hausa na musamman cikin fannin ilimin kwamfuta, domin rubuce-rubuce basu yadu sosai a kan haka ba. Har wa yau, littafai irin su Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci Gaba, wanda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya rubuta, da ma sauran makamantansu, na bukatar bita a kai a kai. Saboda a kullum abubuwa na caccanzawa ne. Duk wanda ya dauki littafin Farfesa ya san tabbas yayi kokari, nesa ba kusa ba, wanda kuma da a ce a yanzu ne ya rubuta littafin, da kalmomin da zai yi amfani dasu, da kuma fannonin da zai taskance sun fi wadanda ya zuba cikin littafin yawa. Don yanzu an samu bunkasar dukkan fannonin da yayi nazari kansu. Don haka a samu malaman jami’a, kwararru kan harshen Hausa, su rika kirkirar kalmomi na musamman ga dukkan fannonin da ke bunkasa a yanzu na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere.

Kammalawa

Kafin in karkare, yana da kyau in sanar da masu karatu cewa, daidai lokacin da nake wannan rubutu (bayan na fitar da kashi na daya da na biyu, an buga), sai na samu sakon wasu cikin masu karatu da ke jawo hankalina zuwa ga wani littafi da Malam Isa Musa ya rubuta, mai suna: Mu Koyi Gyaran Rediyo (1 – 2). Wannan bawan Allah, a cewar masu wannan fadakarwa, ma’aikacin NEPA ne da ke zaune a Kano, dan garin Gumel da ke Jihar Jigawa. Sun nusar da ni ne kan batun da na rubuta cewa duk da dadewar da rediyo yayi a kasar Hausa, har yanzu babu wani littafi da aka rubuta kan yadda yake aiki balle yadda ake gyaransa idan ya lalace. Na fadi haka ne ta la’akari da rashin yaduwar ire-iren wadannan littafai. Ban taba cin karo dashi ba, kuma ban taba samun labari kan littafin ba. Wannan ba karamin kokari bane, zan kuma so in samu littafin don yin nazari kansa. Haka kuma na sake samun labarin wani bawan Allah da yayi rubutu kan fannin Fiziya (Physics) da Hausa, duk da yake ba a riga an buga littafin ko ba. Wannan abin farin ciki ne shi ma, kuma idan muka ci gaba da samun ire-iren su, babu shakka abubuwa za su ci gaba da gyaruwa. Zan kuma ci gaba da sanarwa duk lokacin da na samu labarin wani kokari makamancin wannan, abin yabawa. Wannan ita ce kasida ta karshe kan wannan fanni in Allah Ya yarda. Idan Allah Ya kaimu wani mako za mu shiga wani fanni kuma dabam. Muna mika sakon gaisuwar mu ga dukkan masu karatu, musamman masu bugo waya ko kira don tambaya ko neman karin bayani. Allah bar zumunci, amin.

BUNKASA HARSHE DA AL’UMMAR HAUSAWA: DAGA ADABI ZUWA KIMIYYA DA FASAHAR SADARWA TA ZAMANI (3)

Matsaloli

Akwai matsaloli da dama da suka haddasa karancin littafai ko rubutu cikin fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere a kasar Hausa. Daga cikinsu akwai rashin tallafi daga hukumomi, musamman gwamnatin jihohin Arewa. Da sun dauki wannan al’amarin da muhimmancin da ya kamace shi, da sauran kungiyoyi ko daidaikun mutane marubuta sun bi tsarin da suka assasa. Amma sai ya zama da dama cikin gwamnatin jihohi basu ma damu da abin ba. Ba ma ta wannan kadai ba, hukumar ilimi ma ba wani damuwa ake da ita ba balle wani fanni na musamman. Kamar yadda Farfesa Abdallah Uba Adamu yake nunawa ne kwanakin baya a hanyarsa ta dawowa daga kasar Jamus, bayan wani taro da suka halarta kan bunkasa harsuna da al’adu, (inda Ado Ahmad Gidan Dabino ya gabatar da wata makala kan harshen Hausa), cewa, da mun san yadda ake girmama harshen Hausa a sauran kasashen duniya, da mun daina masa irin wannan rikon sakainar kashin da muke masa. Galibin Hausawa, ba ma gwamnatoci kadai ba, basu dauki harshen Hausa a bakin komai ba. Matsala ta biyu kuma ita ce ta rashin sha’awar marubuta kan wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere. A gaskiya galibin masu rubutu cikin harshen Hausa basu cika damuwa da wani fanni da ya wuce na kirkirarrun labarai ba. Watakil saboda mutane sun fi sha’awar karanta labarai, wannan tasa kasuwar wadannan littafai tafi ci. Don haka suna ganin idan sun yi rubutu, wa zai saya? Wannan kuskure ne. Domin su masu karatu fa cusa musu sha’awar ake yi. Ya danganci tsarin rubutunka da kuma irin usulubin da kayi amfani da ita. Matsala ta gaba ita ce ta karancin sha’awar masu karatu, kamar yadda bayani ya gabata a matsalar baya.

Sai kuma matsalar tsoron rashin kwarewa a ilimin zamani, wanda da dama cikin wadanda Allah Ya hore musu kudurar ilimin kere-kere suke fama da ita. Ma’ana zaka samu mutum ya kware wajen iya kere-kere, ko wajen hada wasu sinadaran kimiyya masu amfanin al’umma, amma don tunanin cewa ba makarantar boko yaje ya koyo ba, idan kace masa ya taskance wannan ilimin nasa a rubuce don wasu su amfana, sai yace maka ai shi ba kwararre bane, don bai da shedar karatu kan kwarewar. Wannan shi ma kuskure ne. Domin zuwa makaranta don samun takardar gamawa fa sheda ce kawai, ba wai ilimin ba kenan. Akwai da yawa cikin mutane masu ilimin da ke amfanar da jama’a, kuma ba makaranta suka je suka koyo ba. Akwai misalai da dama, ba sai na kawo su daya bayan daya ba. A takaice idan muka dauki Bill Gates, tsohon shugaban kamfanin Microsoft da ke kasar Amurka, kamfani mafi girma da dukiya a fannin manhajar kwamfuta a duniya, asalinsa bai taba zuwa makaranta don koyon ilimin kwamfuta da manhajojinta ba, har abada! Lokacin da ya gama sakandare, mahaifinsa ya tura shi jami’a don karantar fannin tsimi da tanadi, watau Economics kenan, yana aji daya ya bar makarantar, don samun damar rubutawa da tsara manhajar kwamfuta ta farko; shekarunsa a lokacin basu wuce goma sha hudu ba. Tun sa’adda ya bar makarantar, har yanzu bai koma ba. Don daga can ya kafa kamfanin Microsoft, shekarunsa ashirin da biyar. Amma ya kirkiro ilimin gina manhajar kwamfuta mai suna BASIC, wanda Allah kadai ya san miliyoyin mutanen da ke cin abinci sanadiyyar kwarewarsu da wannan fannin ilimi. Kun ga ba makaranta yaje ya koya ba. Allah cikin ikonsa ya yassare masa kwarewar. Kuma akwai da dama cikin mutanenmu a nan cikin gida da waje, masu irin wannan mauhiba ta Bill Gates, amma zai yi wahala ka samu kashi hamsin cikin su da suka taskance iliminsu kan kwarewarsu. Wannan ma illa ce mai zaman kanta.

Wata matsala har wa yau ita ce ta tsoron rashin kudurar rubutu da karatu. Abinda wannan ke nufi shine, za ka samu mutum ya kware a wani fanni na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, amma saboda bai ma iya rubutun boko da karatu ba, haka wannan kwarewa zai tafi da zarar ya rasu, saboda ba zai taskance shi ba. Don me? Wai bai da kudurar rubutu da karatu! A wasu kasashe irinsu Amurka fa akwai wadanda basu iya rubutu da karatu ba, kada ka dauka nan ne kadai muke da irin wannan. Kuma mu daina daukan wannan tsarin rubutu da karatun boko a matsarin daya-dayan tsarin taskance ilimi, sam. Idan muka yi la’akari da wakokin su Marigayi Aliyu dan Sidi, da Malam Aliyu Akilu, da sauransu, zaka samu duk da tsarin rubutun Ajami suka rubuta su. Daga baya aka zo aka mayar dasu zuwa tsarin rubutun latin, aka buga su a matsayin littafai, kamar yadda muke saya mu karanta a yanzu. Kai ma kana iya rubuta abinda ka sani na ilimi ko kwarewarka ga wata sina’a ta kimiyya da fasaha cikin Ajami, ba a rasa wanda zai juya shi zuwa hausan boko. Wannan shi yafi komai sauki ma. Har wa yau, watakil kace ai kai baka iya rubutun Ajami ba, ko kuma makaho ne kai ko kurma, duk akwai yadda za a yi. Kana iya karanto wa mai ji da gani da kudurar rubutu da karatu, ya taskance abinda ka sani. Mu fa sani, galibin sahabban manzon Allah (SAW) masu ruwaito hadisai, basu iya rubutu da karatu ba. Irin su Abu Hurairah, da Abdullahi dan Umar, duk ba su rubutu, amma ga ilimin da suka taskance a kwakwalwarsu ya same mu. Haka ma galibin tabi’ai suke. Littafin Al-Musnad na Imamu Ahmad dan Hambali, wanda a yanzu mujalladi talatin ne (sifili sittin), da ka yake halarto hadisan, ana rubutawa. Littafin Adwaa’ul Bayaan, wanda tafsirin Kur’ani ne na babban Malami Aminud Deen Shanqeeti, dan kasar Mauritaaniya, da ka yayi tafsirin shi ma. Mujalladi goma ne (sifili ashirin), aka taskance a kaset na rediyo, daga baya aka rubuce su tsaf! Me yasa? Don bai iya rubutu da karatu ba. Idan ka rubuto masa wasika, sai dai a karanta masa. Haka suke! Sai dai su karanto abinda suka sani daga kwakwalwarsu, a taskance a rubuce. Don haka matsala ce babba, kace sai ka iya rubutu da karatun boko sannan za ka yada abinda ka sani na ilimi ko kwarewar fasaha da kere-kere. Wannan na cikin abinda ya dada dakushe karancin rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere a kasar Hausa.

Matsala ta gaba ita ce matsalar talauci. Akwai da yawa masu so da kuma sha’awar rubuce-rubuce, ba a fannin kimiyya da fasahar sadarwa kadai ba, har da sauran fannoni, amma ba su da kudi da zasu buga ko yada littafan. Wannan ma matsala ce, wacce da ace gwamnatocin Arewa na da wani tsarin tallafi, da an shawo kanta. Akwai kuma matsalar rashin sha’awar rubutu daga kwararru. Da ace duk wanda yaje ya koyo wani ilimi na kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere dole ne ya rubuta littafi na musamman cikin harshen Hausa, wacce gwamnati za ta dauki nauyin bugawa, wallahi da al’amura sun canza. Wannan shine galibin tsarin da wasu cikin kasashen Larabawa suke amfani da ita. Idan kaje wata kasa ka koyo wani ilimi, kowane iri ne, da harshen turanci ko faransanci, dole ka rubuta littafi ko wata doguwar makala wacce ke bayyana nau’in ilimin da ka koyo, a kowane fanni ne cikin ilimin. Na samu labarin cewa wannan shine tsarin da gwamnatin Iraki karkashin marigayi Saddam Hussein ke amfani da ita a baya, ban san yanzu ba. Wannan na da muhimmanci, domin zai sanya sha’awa cikin zukatan kananan dalibai da ke sakandare, don sanin mahangar da zasu dauka da zarar sun shiga jami’a. Kowa ya san tarin kwararrun da muke dasu a kasar nan, kan kowane fanni ne na kimiyya; daga likitanci zuwa fannin zane-zanen gidaje da kere-kere. Mu kaddara ace kowanne daga cikinsu ya rubuta wani littafi cikin Hausa, kan fagen kwarewarsa, yaya? Da yanzu muna da tafka-tafkan dakunan karatu a jihohi dabam-daban. Allah kadai ya san tarin littafan da za a samu, da irin kwararrun da zamu samu, tare da samuwar ingancin ilimi a Arewa. Domin idan rubuce-rubuce musamman irin na tsarin lissafi suka yawaita a Arewa cikin harshen Hausa, zasu sawwake da yawa cikin matsalolin da ke fuskantar ilimin ‘ya’yanmu na boko, wajen dasa kwadayin fannin lissafi da kuma sawwake shi. A bayyane yake cewa tsarin ilimin kasar nan na tattare da matsala musamman na abinda ya shafi yadda ake bayar da ilimin. Dalibai na koyon ilimin ne tare da koyon harshen da ilimin yazo dashi, duka a lokaci guda. Dole su fahimci harshen sosai, idan suna son fahimtar ilimin da yazo dashi. Ta la’akari da sauran matsalolin da suka shafi yadda gwamnati ke tafiyar da harkar ilimin, za a ga cewa samuwar kwarewa a fannonin biyu na samun matsala shi ma.

Matsalar karshe da zamu kawo, ita ce ta rashin bunkasar tsarin rubutu kan kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere. Wannan na cikin matsalolin da Farfesa Muhammad Hambali Jinju yayi ta kokarin shawo kanta lokacin da yake koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya, da Jami’ar Bayero da ke Kano, da kuma Jami’ar Danfodio da ke Sakkwato. Tsarin rubutu kan kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere na bukatar samuwar sabbin kalmomi wadanda za a yi amfani dasu wajen aiyana wasu abubuwan da ake son siffatawa. Har wa yau, yana bukatar dawo da wasu tsoffin kalmomin Hausa da aka daina amfani dasu a baya, don rayar da su. A bangaren karshe kuma, yana bukatar wasu kalmomi da za a aro daga harshen da aka samo ilimin ta hanyarsa. Domin aiki ne da ya kumshi fassara ko tarjama wasu littafai da ke dauke da wannan ilimi, daga wani harshen zuwa harshen Hausa. Kasancewar harshen Hausa bai da wadatan kalmomi, kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya tabbatar kwanakin baya, musamman kan abinda ya shafi ilimin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, dole a aro wasu kalmomin. In kuwa haka ne, to wa zai tsara wadannan tsare-tsare? Ko shakka babu, kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju yayi a baya, hakkin hakan na kan Malaman Jami’ah ne su binciko hanyoyin yin hakan, ta hanyar kwarewarsu kan ka’idar kirkiran sabbin kalmomi da kuma sarrafa wadanda ake dasu, tare da fadada ma’anar masu rai. Hakan kuwa, kamar yadda kowa zai sheda, ba ya samuwa ta yadda ya kamata. Don haka duk mai sha’awar rubutu kan wannan fanni musamman ma a yanzu, dole zai ta cin karo da matsalolin da idan ba yayi hakuri ya kuma jure ba, sai ya ma fasa aikin. Misali, shekaru uku da suka gabata lokacin da na yanke shawarar rubuta littafi kan yadda ake amfani da fasahar Intanet cikin harshen Hausa, na fuskanci wannan matsala. Bayan karancin kasidu kan fasahar kimiyya da fasahar sadarwa (Information Technology), babu wani tsari ko wasu littafai da zasu sawwake maka hanyar sarrafa kalmomin don siffata abinda kake son siffatawa. Sai makala guda da na samu wajen Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero, wacce ke dauke da Tubalin Fahimta kan wasu kalmomi da suka shafi fasahar kwamfuta da Intanet. A takaice dai, matsalolin suna da yawa, amma za mu takaitu da wadannan, don samun bayanin hanyoyin shawo kansu.

BUNKASA HARSHE DA AL’UMMAR HAUSAWA: DAGA ADABI ZUWA KIMIYYA DA FASAHAR SADARWA TA ZAMANI (2)

Ilimin Kimiyya da Fasaha Cikin Harshen Hausa

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, fannin rubutaccen adabin kirkirarrun labarai ne ke da kaso mafi tsoka cikin fannonin ilimi da muke dasu a rubuce cikin harshen Hausa a yanzu. Wannan tsari idan muka duba zamu ga ba tun shekarar 1980 ya faro ba, a a, tun lokacin mulkin mallaka ya faro. Su shugabannin mulkin mallaka sun karfafa tsarin rubuce-rubuce ne da tsarin rubutun latin, watau haruffan boko da muke amfani dasu a yanzu, don tabbatar da cewa sun kawar da tsarin rubutun ajami, wanda shi suka samu muna amfani dashi don tafiyar da tsarin mulki da koyon ilimi da addini da kasuwanci. Wannan tasa za a ga galibin rubuce-rubucen duk labarai ne kirkirarru, wadanda aka shirya gasa don karfafa rubutunsu, ko kuma aka sanya wasu masana a lokacin (irinsu Malam Abubakar Imam da sauransu) su fassara daga wasu harsuna kamar turanci ko larabci ko kuma harshen Masar. Don haka ba abin mamaki bane ganin yadda littafai suka yi karanci kan sauran fannonin ilimi, musamman na kimiyya da fasaha. Tabbas akwai ‘yan kananan littafai da aka rubuta kan kimiyyar halittu, irinsu Halittun Gida da na Daji, wadanda hukumar mulkin mallaka ta dauki nauyin bugawa, ake karantar da su a makarantu, amma basu taka kara sun karya ba. Haka bayan an samu ‘yancin siyasa, ba a samu yaduwar rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasaha ba. Wani abin bakin ciki ma shine, wadanda aka rubuta a baya, sai aka tsayar da buga su. Wannan tasa ire-iren wadannan littafai suka yi karanci a kasuwa da makarantu da dakunan karatu.

Wajen shekarun 1980 zuwa 1990 an samu dan motsi wanda yafi labewa, lokacin da masana kuma masu kishin bunkasa harshen Hausa irin su Farfesa Muhammad Hambali Jinju suka fara tayar da kaimi wajen ganin cewa an samu bunkasa harshen Hausa ta hanyar yawaita rubuce-rubuce a wasu fannonin ilimi, musamman ma fannin kimiyya da fasahar kere-kere. Alal hakika Farfesa Hambali Jinju bai yi kasa a gwiwa ba wajen wannan kokari nasa. Domin bayan kasidu da yayi ta gabatarwa a tarurrukan kara wa juna sani don tallata wannan manufa mai matukar muhimmanci, ya rubuta wasu littafai biyu masu matukar fa’ida. Littafin farko da ya rubuta mai suna Littafin Maganin Gargajiya, yayi fa’ida sosai. Domin da dama cikin mutane sun amfana da shi ba a Nijeriya kadai ba, har ma da Jumhuriyar Nijar. Samuwar wannan littafi na nuna cewa ashe ba sai fannin ilimin da mutane ke dauka na zamani ne kadai za a iya rubutu a kai ba, a a, duk wani abinda ka san ilimi ne, zai amfani al’umma, to taskance shi yana da muhimmanci.

Littafi na biyu kuma ya rubuta shi ne kan fannonin ilimi da dama, irin su fannin lissafi (Mathematics), da kimiyyar kididdigar lissafi (Statistics), da kimiyyar halittu (Biology), da kimiyyar sararin samaniya (Space Science), da kimiyyar kwamfuta da kere-kere (Computer Science Technology), da kimiyyar man fetur (Petroleum Engineering), da kimiyyar sinadarai (Chemistry) da dai sauran fannonin ilimi da dama. Ya sanya wa wannan littafi suna: Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci Gaba. Sunan wannan littafi ya samu ne daga irin manufa da kuma kishin da wannan marubuci ke da ita wajen ganin dacewa da kuma yiwuwar amfani da harshen Hausa a matsayin harshen kasa, tsakanin Nijeriya da Jumhuriyar Nijar. Yace dukkan wani ilimi da ka sani, ana iya taskance shi cikin harshen Hausa, kuma hakan, a cewar Farfesa Muhammad Hambali, shine abinda zai kawo mana ci gaba, musamman ta la’akari da saukin fahimta da kuma kishi da mutane zasu ji na ganin kare wannan harshe ta hanyar ingantawa da kuma bunkasa shi. Har wa yau, a shekarar 1988, madaba’ar Triumph da ke gidan Sa’adu Zungur a Kano, ta samu masana kiwon lafiya sun rubuta wasu littafai kan lura da lafiya. Littafan kashi-kashi ne; babban taken su dai shine: Aikin Likita – Ilimin Cuce-Cuce Na Jikin Mutum. Kamfanin ya samu kwararru ne kan harkar lafiya suka rubuta wadannan littafai, wadanda suka shafi nau’i dabam-daban kan kimiyyar magunguna da lura da lafiyar dan Adam. Cikin wadannan littafai akwai wanda Likita Muhammad Kabir ya rubuta mai suna: Yadda Magani Ke Aiki a Jikin Mutum. Littafi ne mai kyau da fa’ida, wanda ke dauke da bayanai kan yadda ake shan magani, irin maganin da ya kamata a sha, da kuma lokaci ko tsarin da ya dace a sha shi. A cikin wannan dan karamin littafi har wa yau, yayi bayanin cututtuka dabam-daban, da kuma magunguna masu hadari ga jikin dan Adam, irinsu guba da sauransu. Wani babban abin farin ciki shine irin usulubin da mawallafin yayi amfani da ita, wacce ta kumshi hotuna da taswirori da kuma gajarta bayanai ta yadda mai karatu zai amfana da ilimi mai yawa cikin kankanin lokaci da shafuka.

Cikin ‘yan shekarun da suka gabata har wa yau, akwai rubuce-rubuce da wasu suka yi kan wannan fannin na kimiyya da fasaha. Misali, akwai littafi da wani bawan Allah ya rubuta kan kwamfuta da yadda ake amfani da ita. Akwai kuma kananan littafai kan yadda ake amfani da wayar salula. Bayan littafan da kamfanin Triumph ya dauki nauyin bugawa kan likitanci, akwai wasu kuma wadanda aka buga, kanana, masu bayani kan tsarin likitanci da magunguna a tsarin musulunci. Ire-iren wadannan littafai sun kunshi bayanai ne kan tasirin zuma da yadda ake amfani da ita wajen kawar da cututtuka dabam-daban. Da kuma wadanda aka rubuta kan yadda ake amfani da zaitun da habbatus-sauda, da tafarnuwa da sauransu.

Akwai sauran fannonin da ba ka samun wani labari kan rubuce-rubucen da aka yi, (idan ma an yi kenan), balle samun littafan su kansu. Misali, fannin lissafi cikin harshen Hausa. Ban ci karo da wani littafi mai bayanin yadda ake warware matsalolin lissafi da kididdiga ba, watau Mathematics & Statistics, wanda aka rubuta cikin harshen Hausa. Wanda kowa ya san muhimmancin lissafi a fannin kimiyya da fasaha. Ba ka samun littafai kan fasahar kwamfuta da kere-kere, da yadda ake amfani da kayayyakin sadarwa masu alaka da su. Misali, zai yi wahala ka samu littafi kan yadda ake gyaran talabijin, duk da tsawon shekarun da muka yi muna amfani da wannan fasaha. Ga shi kuma muna da kwararru masu gyaran talabijin. Babu littafai kan yadda ake gyaran rediyo, duk da cewa muna amfani da rediyo sama da shekaru talatin a kasar nan. Haka aikin walda (welding), babu rubutu kan yadda ake sina’ar walda. Wacce sina’a ce mai matukar muhimmanci ga al’umma a ko ina take, musamman ma yanzu. Balle kace kana neman littafai kan yadda ake gyaran mota da babur da keke. Ko kuma yadda tsarin jirgin sama yake, ko yadda jirgin kasa ke aiki. Duk da shaharar wayar salula da samuwar masu gyaran wannan fasaha a kasar Hausa, har yanzu babu wani littafi tsayayye wanda ya zurfafa bayanai kan yadda tsarinsa yake, balle yadda ake gyaransa. Fasahar tauraron dan Adam ta dade da shigowa kasar nan, amma har yanzu baka samun littafi guda kan wannan fasaha. Kuma ga shi muna da masu wannan aiki, kwararru a kai. In kuwa kana son neman jidali, to ka nemi littafi kan fasahar makami ko makamashin nukiliyya a harshen Hausa, ka ga ko za ka samu. Kai a takaice dai, duk wani fannin rayuwa da ka sani, muna da kwararru a cikinsa, amma me yasa har yanzu babu littafai da zasu share maka hawaye in ka tashi nema? Yanzu idan wani ya shigo kasar nan, mai sha’awar bincike kan ci gaban al’umma da al’adunta, sai mu ji kunya. Domin hatta sina’o’inmu na gargajiya da muka tashi muka samu ana yi, littafai basu yadu ba kan yadda ake yin su ko tafiyar da su. Sai dai yaje inda ake yi, ya taskance bayanai da kansa. Da zarar masu ilimin sun mutu, shikenan sai su tafi da iliminsu. Somin hatta ‘ya’yansu, basu cika son koyon wadannan sina’o’i, wai don suna makarantun boko. To wa yace maka wai don kana makarantar boko baza ka zauna don koyon wasu sina’o’in ba? Mai yasa wasu sina’o’in suka mace?

Idan muka koma bangaren wadanda aka rubuta kuma, in ka kebe littafan da kamfanin Triumph ta dauki nauyin bugawa, da wadanda Hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya da dauki nauyin bugawa cikin littafan Farfesa Muhammad Hambali Jinju, ban ci karo da wadanda wasu kamfanoni ko hukumomin Arewa ko wata Jiha suka dauki nauyin rubutawa tare da bugawa ba. Zai iya yiwuwa akwai, amma ni ban ci karo dasu ba. Wannan ke nuna cewa, galibin kokarin duk daidaikun mutane ne ke yi don ganin sun sanar da al’umma abinda Allah Ya sanar da su. Wannan ke nuna cewa, littafai ko kokarin bunkasa rubuce-rubuce a fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere cikin harshen Hausa, an barsu ne a hannun daidaikun mutane. Wanda kawai ya ga dacewar yin hakan, don burgewa, ko kudi, ko kokarin ciyar da al’umma gaba, yayi. Duk da yake sauran fannonin da rubuce-rubuce suka yadu a ciki ma haka abin yake, amma wannan bai dace ba. Wannan ba zai kai mu ko ina ba. In har muna son bunkasawa tare da ciyar da al’ummar Hausawa gaba ta fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere, dole a samu wani tsari da zai kai mu ga gaci. Kafin kawo bayanai kan hanyoyin kai wa ga gaci, zai dace mu tabo kadan cikin matsalolin da suka haddasa rashin bunkasar littafai cikin wannan fanni.