Monday, March 30, 2009

Wasu Cikin Labarai

“Sinadaran Batir Za Su Dada Samun Tagomashi” – A Cewar Sakamakon Wani Bincike

clip_image002Ga dukkan alamu, nan da shekaru uku masu zuwa duk wani mai amfani da batir nau’in Lithium-ion Phospate, watau nau’in batiran da muke amfani dasu a wayoyin salularmu da kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptop), da na’urar taskance wutar lantarki (UPS) da sauran makamantansu, zai samu sauki wajen takaitan lokacin caji da kuma karkon rayuwa wajen amfani da shi. Abinda wannan ke nufi shine, nan gaba kana iya caja batirin wayar salularka cikin kasa da minti daya! Ba ma nan aka tsaya ba, batirinka na iya shekaru uku ko sama da haka ba tare da karkonsa ya ragu ba. Wannan shine abinda sakamakon wani bincike da wasu masana kimiyyar lantarki suka gudanar a Cibiyar Fasaha da ke Massachusettes, watau Massachusettes Institute of Technology (MIT) ya tabbatar. Sakamakon binciken, wanda mujallar Nature ta hakaito ranar 12 ga Maris yace masu wannan bincike sun yi tsawon shekaru biyar suna fafatawa kafin gano manyan dalilan da ke jawo saibi wajen cajin batir yayin da aka jona shi da wutar lantarki, duk kuwa da cewa sinadaran lantarkin nau’in Neutrons da ke ciki suna aikinsu yadda ya kamata. Wanda kafin wannan lokaci galibin masanan lantarki na alakanta rashin cajin ire-iren wadannan batira cikin sauri ne da cewa sinadaran da ke ciki ne basu kai-komo cikin gaugawa don tara makamashin lantarkin da batirin ke bukata. Amma a cewar Injiniya Gerbrad Ceder da Byoungwoo Kan, shugabannin tawagar injiniyoyin da suka kaddamar da wannan bincike, wannan ba shine dalilin da ke sa wayar salula ta dauki kusan sa’a guda tana caji ba kafin batirin ya cika, a misali.

Batir nau’in Lithium-ion Phospate dai shine nau’in batiran da wayoyin salula da sauran kayayyakin fasahar zamani masu amfani da batir ke amfani dashi. Har wa yau akwai motocin zamani masu amfani da wannan batiri su ma. Wannan nau’in batir dai ya samu wannan shahara ne sanadiyyar iya taskance makamashin lantarki da yake yi idan an hada shi da wutar lantarki, ya kuma ci gaba da amfani da wanda ya taskance, har sai yayi kasa, sannan a sake caja shi. Wannan ya saba wa batira irin na agogon bango ko na tocila, wadanda da zarar sun yi rauni shikenan, sai dai ka zubar dasu ka sayo wasu. Amma nau’in Lithium-ion Phospate, kana iya shekaru dasu; sai dai kawai ka rika caji idan sun yi kasa, don kara musu kuzari. Matsalar da ke tattare da ire-iren wadannan batira dai a cewan masana fasahar lantarki, shine idan ka jona su da wuta sai sun yi kusan awa guda ko sama da haka, kafin su yi cajin da zai dauke ka kwanaki biyu ko uku kana amfani dasu. Kafin wannan rahoto da aka fitar, galibin masana harkar lantarki na danganta matsalar ne ga yanayin tafiyar sindaran Neutron da ke cikin batirin, wadanda aikinsu ne su rika caja batirin ta hanyar yin tsere a tsakaninsu daga hagu zuwa dama, duk sa’adda ka jona wayar ko batirin kana caji, suna shiga wasu yan ramuka (watau Tunnels) da aka tanada musu. Wannan kai-komo da suke yi shi ke tara makamashin lantarkin da wannan batir ke bukata. Da zarar ya cika, ka jona wa wayar salularka a misali, sai su fara kai-komo daga dama zuwa hagu, duk lokacin da ka kunna wayar. Wannan safa-da-marwa da suke yi, shi zai rika rage yawan makamashin lantarkin da ya taru yayin da suke caja wayar, har sai ya kare. Sannan su canja yanayin tafiya idan ka jona wayar da wutar lantarki don yin caji a karo na gaba. Tsohuwar sakamakon da masana suka fitar a baya ita ce: wadannan sinadarai na Neutron basu tafiya cikin gaugawa don tara makamashin lantarkin da wayar ke bukata ne, shi yasa wayar ke daukar kusan awa guda ko sama da haka kafin cajin ya cika. To amma sakamakon da Injiniya Ceder da abokan bincikensa suka fitar makon jiya ya karyata wannan tsohuwar zato da masana harkar lantarki ke da ita shekaru aru-aru.

Injiniya Ceder yace sun yi nazarin wannan safa-da-marwa da sinadaran Neutron ke yi yayin caji basu samu wata matsala da abinda ya shafi yanayin tafiyarsu ba, sam ko kadan. Suka ce sun lura da wannan tafiya ta hanyar na’urar kwamfuta, inda suka jona batir nau’in Lithium-ion Phospate, suna kallon yadda wadannan sinadaran na Neutron ke tafiya a guje, suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Wannan, a cewarsu, ba shine matsalar da ke haddasa rashin cajin batir din da wuri ba. Suka ce matsalar da ke haddasa wannan saibi wajen caji ita ce: ba dukkan wadannan sinadaran na Neutron ne ke shigewa cikin wadannan ramuka da aka tanada musu ba a lokaci guda. Galibinsu, musamman wadanda ke sama-sama, suna sulmuya ne a wofi, basu samun damar shiga ramin balle caji yayi sama cikin lokaci. Abinda zai warware wannan matsala kuwa, a cewar wadannan injiniyoyi, shine a sake tsara wasu ramukan (Tunnels) daga sama (watau cikin kogin sinadaran da ke cikin batirin kenan), don baiwa wadannan sinadaran da ke sulmuya a sama damar samun shiga su ma, don kauce wa sulmuyar wofi da suka yi ta fama da shi a baya. Wannan shine kadai abinda zai sa batir ya dauki karancin lokaci wajen caji, kuma bayan haka ma, zai samo rayuwa mai karko da inganci.

Wannan ikirari ba da ka suka yi shi ba. Rahoton da Injiniya Kan da tawagarsu ya fitar a mujallar Nature, yace sun aiwatar da bincike kan batira guda biyu; batir na farko sabo ne, wanda suka kera ta hanyar amfani da sabon tsarin da suka tabbatar a bincikensu, dayan kuma irin wanda kowa ke amfani ne dashi, ma’ana mai dauke da tsohuwar fasaha kenan. Dukkan batiran mizaninsu daya ne, sinadaran da ke cikinsu iri daya ne, kuma dukkansu nau’in Lithium-ion Phospate ne. Da suka jona su da caji, batirin farko mai dauke da sabuwar fasaha ya samu cikakkiyar caji tsakanin dakiku goma zuwa ashirin (10 – 20 Seconds), yayin da dayan batirin mai dauke da tsohuwar fasaha ya dauki tsawon mintuna shida (6 minutes) kafin ya cika. Sun kuma sake tabbatar da cewa lallai wannan batir mai dauke da sabuwar fasaha zai yi karko fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu. A karshe suka tabbatar da cewa: “samun damar caji da kuma amfani da batira cikin sauki da gaugawa zai dada samar da damar kera wasu sabbin kayayyakin fasaha ne, wanda hakan ke iya zama sanadiyyar tafiyar da rayuwa cikin sauki da inganci”. Tuni dai hukumar NASA da kuma Hukumar Makamashi na kasar Amurka suka karbi sakamakon wannan bincike da hannu bibbiyu. Kuma har an samu wasu kamfanonin fasaha guda biyu ma da suka karbi lasisin amfani da wannan sabuwar fasaha ta inganta batir nau’in Lithium-ion. Nan da shekaru uku masu zuwa ake sa ran fitar wadannan batira masu dauke da wannan sabuwar fasaha.

“Duniya Na Dada Dusashewa Sanadiyyar Gurbatar Yanayi” – Bincike

Tun wajajen shekclip_image004arun 1970s zuwa yau, yanayin da duniya ke gudanuwa a ciki sai dada tabarbarewa yake sanadiyyar gurbatar yanayi da ke samun karfin gwiwa daga gurbatattun abubuwa a yanayin iskar da ake shaka ko ake fitarwa, ko hayaki ko kuma kura da ke tudadowa sanadiyyar juye-juyen dan Adam wajen neman abin tasarrufi. Wannan tabbaci ya fito ne daga sakamakon wani bincike da wasu kwararru kan hanyar yanayi da muhalli da ke Jami’ar Tekzas (University of Texas) da Jami’ar Mariland (Maryland University) da ke kasar Amurka. Rahoton, wanda Farfesa Robert Dickinson da ke Jami’ar Texas da wasu kwararru biyu daga Jami’ar Meriland suka fitar a makon da ya gabata, ya tabbatar da cewa an samu raguwar kaifin gani tsakanin mutum biyu da ke hangar juna daga ‘yar madaidaiciyar tazara, sanadiyyar karuwar kura da hayaki mai haddasa dusashewar ido. An kuma gano cewa an samu wannan raguwar kaifin gani ne daga alkaluman bayanai da aka samo daga shekarar 1973 zuwa shekarar 2007 daga cibiyoyin tantance yanayi (watau Metreological Center) guda dubu uku da dari biyu da hamsin da ke warwatse a kasashen duniya.

Masu wannan bincike suka ce manya cikin dalilan da ke haddasa hakan kuwa su ne hayakin da ke fitowa daga motoci masu amfani da man fetur da gas, da kuma hayakin kone-kone na daji da kurmi, da kuma gagarumar gobara ko wutar daji ke yawan tashi a dazukan Amurka da Ostiraliya ko wasu wurare. Bayan haka, daga cikin abubuwan da ke dada sanyan yanayin duniya ke dada dusashewa akwai kurar da ke fita daga hayakin wuta da ke ci a yayin dukkan wata kone-kone. Masu wannan bincike suka taruwar wadannan na gurbata yanayin haske ko annurin da duniya ke dauke dashi, ta yadda hakan ke iya shafar lafiyar ganin dan Adam da rage masa kaifi, tare da haddasa masa cututtuka masu alaka da huhu da dai sauransu. Kwararrun suka wannan yanayi ya fi muni a kasashen da ke gabashi da kudancin Asiya, da nahiyar Amurka da Ostiraliya da kuma nahiyar Amurka. Amma nahiyar Turai da Arewacin Amurka basu samu karuwar wannan yanayi mai muni ba, saboda dokokin hana kone-kone da rage dumamar yanayi da suka assasa kuma suke lura da su.

Wannan rahoto har wa yau ya kara tabbatar da cewa kasashe irinsu Sin da Indiya su suka fi kowa dalilan da ke fitar da wannan mummunar yanayi na kura da hayaki da sinadarai masu kashe kaifin ganin dan Adam, bayan gurbata yanayi da suke yi. Manyan cikin wadannan dalilai su ne yawaitan manyan masana’antun sarrafa kayayyakin abinci da abin hawa da sauran abubuwan more rayuwa, wadanda ke fitar hayaki da kura sanadiyyar kone-konen makamashin da suke amfani dashi a kullum. Bayan nan, su suka fi sauran kasashe yawan ababen hawa masu fitar da hayaki mai gurbata yanayi. Illar hakan, muddin ba duniya bata hada kai wajen rage dalilan da ke janyo dumama da gurbatar yanayi ba, to za a ci gaba da kasancewa cikin hadari mai girma, a cewar wadannan kwararru. Domin yawaitan kan haddasa matsananciyar sanyi mai daskararwa, ko tsananin zafi mai cutarwa ga sararin samaniyan wannan duniya. Sannan, yawan bazuwar wannan hayaki na aikawa wani haske mai kaifi zuwa sararin samaniya wanda ke rage yawan makamashin da ke dauke cikin hasken rana da ke shigowa wannan duniya tamu don amfanar da mu, ko kuma ya hadiye makamashin, ta hanyar hana shi tasiri.

Tuesday, March 24, 2009

Dumamar Yanayi: Ma’ana, Asali, Musabbabai da Illoli (1)

Gabatarwa

Kamar kowane irin halitta da Allah Madaukakin Sarkclip_image002i ya halitta, wannan tsari da yanayin da wannan duniya tamu ke gadanuwa na canzawa ne iya canjin zamanin da muke ciki; iya gwargwadon jujjuyawar dan Adam wajen nemo hanyar sarrafa wannan muhalli da Allah Ya zaunar dashi a ciki; iya gwargwadon ilimi da wayewarsa; iya girma ko fadin tasirin da zai yi wajen sarrafa wannan muhalli. Har wa yau, wannan tasiri na dan Adam na caccanzawa ne shi ma zamani-zamani. Don haka idan muka dubi bangaren lafiya, za mu ga cewa mutanen da suka yi rayuwa shekaru dari biyu ko sama da haka da suka gabata, basu san wata cuta mai suna kanjamau ba, ko ciwon siga, ko ciwon asma da dai sauransu. Haka kuma ire-iren cututtukar da aka yi fama da su cikin wadancan zamunna ko karnoni da suka gabata, a halin yanzu bamu dasu. Idan muka dubi bangaren sadarwa har wa yau, zamu sake ganin irin wannan bambanci; shekaru dari biyu da suka gabata babu wani fasaha da dan Adam ya kirkira a matsayin abin hawa daga gari zuwa gari, sai dai dabbobi irin dawaki da rakuma da jakuna da sauran makamantansu. Haka hanyoyin da yayi amfani dasu wajen sadar da sakonni a wancan lokaci, a yanzu duk ba a amfani dasu. Idan muka koma kan yanayin isar sakon kuma, shekaru dari ko tamanin da suka gabata, ba ma can nesa ba, ba kowa zai yarda ba idan aka ce masa nan gaba cikin ‘yan dakiku kana iya aika sako daga bangon duniya ta gabas zuwa bangonta da ke yamma, cikin kasa da minti daya! Amma yanzu ba yarda da yiwuwar hakan bane abin mamaki, a a, rashin yarda shine abin mamaki.

Duk dai wannan, a takaice, na nuna mana ne cewa iya nisan zamani, iya girma da nau’in tasirin da dan Adam ke yi a doron wannan kasa. In kuwa haka ne, to dole akwai amfani da yake samu, wanda a bayyane yake; ga motoci, ga jiragen sama, ga gidaje nau’uka dabam-daban, ga nau’ukan abinci nan kala-kala, ga kuma kayayyakin sadarwa da fasaha masu tasiri fiye da tunanin dan Adam wajen samar masa da amfani ta hanyar wayar da shi, da kara masa ilimi da hore masa hanyoyin sarrafa muhallinsa. Haka kuma a daya bangaren, akwai wasu illoli da suka haddasu sanadiyyar wannan juyin zamani da dan Adam ke samu a rayuwarsa. To wasu illoli ne? Akwai illoli da dama; ga karuwar cututtuka, ga matsalolin tattalin arzikin kasa – irin su yawaitan marasa aikin yi, talauci da ire-irensu - ga rashin zaman lafiya ga al’umma, ga rashin sukuni ga daidaikun mutane, ga kuma uwa uba, dumamar yanayi da muhallin da ake rayuwa ciki. Wannan matsala ta dumamar yanayi da a harshen Turanci ake kira Global Warming, na cikin manyan matsalolin da duniyar yau ke fama da su, musamman a kasashen da suke ikirarin ci gaba a fannonin tafiyar da rayuwa. Shin, me ake nufi da “dumamar yanayi”? Yaushe duniya ta fara samun irin wannan matsala da har Turawa ke ganin babu matsala irin ta a yanzu? Me ke haddasa haka? Wasu illoli wannan matsala ta dumamar yanayi ke haddasawa? A karshe, me duniya (ina nufin kasashen Turai da Amerika) ke yi wajen ragewa ko takaita shi? Cikin wannan silsila da muka faro yau, zamu gabatar da amsoshin wadannan tambayoyi iya gwargwadon hali da sani. Hakan na da muhimmanci don samun karuwar ilimi, musamman ganin cewa wannan kalma ta “Dumamar Yanayi” ko Global Warming a harshen Turanci, na cikin kalmomin da kusan a kullum sai an ambace su a kafafen watsa labaru, har kafafen watsa labaru cikin harshen Hausa da ke sauran kasashen duniya. Na kuma tabbata da dama cikinmu bamu taba damuwa da neman bayani kan ma’ana ko abinda wannan kalma ta kunsa ba. To ga budi Allah Ya kawo cikin sauki. Sai a gyara zama don bibiyar wannan shafi sau da kafa. Sai dai kafin mu shiga fagen bayani kan dumamar yanayi, ga wata ‘yar tunatarwa nan.

Tsarin Turawa Wajen Binciken Kimiyya

Yana da kyau a kullum mai karatu ya fahimci tsarin da turawa ke amfani da shi wajen binciken da suke yi musamman na ilimi kan abinda ya shafi kimiyya da fasaha. Wannan zai sa ka fahimci abubuwa da dama; mai yasa suke danganta kaza ga kaza? Me ya sa suke ganin kaza ne ya haddasa kaza ba Allah ba a misali? A takaice, shin duk abinda suka binciko ne daidai ko kuwa? In haka ne, mai yasa wasu lokuta suke fadan wasu abubuwa sabanin yadda Allah Ya fade su ko yadda yake a zahiri ko a Kur’ani? To ga amsa. A karo na farko dai, ‘yan Adam ne irinmu; suna da tawaya da nakasa irin wacce muke da ita, iya gwrgwadon sani ko jahiltar abinda suke tutiyar saninsa. Sannan, kashi casa’in da takwas cikin dari (98%) na masu binciken kimiyya ba musulmi bane. A wasu lokuta ma ba Kiristoci bane su. Galibinsu basu da addini. A inda aka samu Kiristoci ko Musulmi a wasu fannonin, zaka samu addini baya tasiri a rayuwarsu. To me yasa?

An samu wani zamani a kasashen Turai, daidai lokacin da suke kokarin fitowa daga kaidin jahilci a dukkan bangaren rayuwa (watau Dark Ages), inda aka yi ta samun masana a fannonin rayuwa musamman na kimiyya suna ta kirkirar abubuwan mamaki da dama, irin su Galileo, wanda ya kirkiro na’urar hangen nesa da a Turance ake kira Telescope. Ba shi kadai ba, akwai da dama da suka yi zamani daya. Daidai wannan lokaci kuma shugabannin majami’a ne ke da karfi, watau addinin Kirista kenan. Sai aka shiga kama su, ana karkashe su; don me zasu rika binciko abubuwa irin haka? Wannan, a cewar wadannan shugabanni, ya saba wa karantarwar addininsu, kuma fito-na-fito ne da Ubangiji, inji su. Don haka duk wanda aka samu ya kirkiro wani abu mai ban mamaki, sai kawai a kashe shi. Haka dai abubuwa suka ci gaba da faruwa har zuwa lokacin da ruwa ya kare wa kada, lokacin da mulki ya koma hannun ‘yan boko, wanda kuma sun san abubuwan da suka faru a baya. Suna samun shugabanci, sai suka yi juyin juya hali, inda aka tumbuke shugabannin addini daga mulki zuwa majami’ansu. Kuma sakamakon wannan ta’addanci da Malaman majami’a suka yi a baya, wadannan sabbin shugabanni suka sanya dokar raba shugabanci da addini, ko kuma dukkan wata ka’ida ta rayuwa aka raba ta da addini; in za ka yi addininka, a cewar wannan ka’ida, ka yi a gidanka, ko a wajen ibadanka, amma ba a bainar jama’a ko hukumomin gwamnati ba. Wannan tsari, kamar yadda na tabbata duk mun santa, ita ake kira Secularism, kuma daga cikinta ne aka fitar da wata ka’ida da galibin malamai masu binciken kimiyya a Turai suke amfani da ita.

Wannan ka’ida dai ‘yar zahiriyya ce. Kuma ka’ida ce da a Turance ake kira The Cause and Effects Theory. Wannan ka’ida abinda ta kumsa shine, “duk abinda ka ga ya faru ko yake faruwa, to dole wani abu ne yayi sanadiyyarsa, kuma wannan abin da yayi sanadi, dole ne ya zama ana ganin shi ko jin shi ko iya taba shi”. In kuwa babu daya cikin wannan, to, zamani ko tsawon lokaci ne ke tafiyar da shi, amma ba wai wani Allah ba. Basu yarda akwai wani mai tafiyar da duniya, mai haddasa faruwar abubuwan da ke faruwa a zahiri ba, in dai ba ganin shi ake yi, ko jin shi ko kuma hankaltarsa ba. Ma’ana, su basu yarda wani abu na iya faruwa ba tare da samun wata alama bayyananniya da ke sanadin faruwarsa ba. Inda suka kasa gane dalili kuwa, sai su yi kirdadon wani dalili na wucin-gadi, sannan su ci gaba da bincike. Abinda ya sha karfinsu kuma tun fil azal, sai su jingina shi ga dabi’a kawai, watau Nature, kamar yadda suke fada. Kai kuma Musulmi ka saba da yin imani da abinda baka gani ba, watau gaibu, don shine asalin addini da imani. Dole kaji abin yai maka bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya!

Bayan wannan tunani ko ka’ida da suka kudurce, Allah Ya hore musu kayan bincike. Don haka duk abinda hankalinsu bai kwanta da shi ba, sai su bincika. Wasu lokuta sakamakon bincikensu ya zama daidai da abinda Allah ya fada ko tsara. Wasu lokuta kuma sakamakon ya karyata abinda Allah Ya fada, ko kuma rabi ya dace, rabi ya kauce. Wasu lokuta abinda suka tabbatar a matsayin sakamakon wani bincike, ya canza sanadiyyar tsawon zamani da yawaitan ilimi da canjin tsarin bincike. Wannan ke sa ka samu ka’idojin fahimtar wani nau’in ilimi sama da guda biyar. Hakan na faruwa ne saboda karancin kayan aikin mai bincike, da karancin fahimtar mai bincike, da kuma kasawarsa wajen sanin komai da komai game da abinda yake bincike. Dole kuwa haka ta kasance, domin shi mai bincike ba Allah bane, halittarsa aka yi. To amma tunda su ba damuwa suka yi da hakkin Allah ba, idan ma suna da addinin kenan, sai kawai su toge a kan sakamakon bincikensu. Kuma tunda su ne da kafafen watsa labarai, su ne ke tsara wa duniya tsarin karantar ilimi da bincike, su ne ke tsara ka’idojin bincike da karatu da karantarwa, sai su rubuta abinda yayi musu daidai, su watso wa duniya don kowa ya ci gaba da tafiya a kan turbarsu. Hakan shine daidai a garesu, domin duniya ce manufarsu, kuma ita suka sa a gaba. Duk abinda ya wuce wannan duniyar, to sai dai ka basu labari, amma ba su baka ba.

A musulunci ba yin amfani da wannan ka’ida bane kuskure, a a, illa dai dole ne ka hada da cewa Allah ya kaddara wa kowane abu lokaci da yanayi da kimtsi da kuma tsarin da yake gudanuwa. Ko ka yarda ko kada ka yarda, wannan abin a haka zai ci gaba da kasancewa zuwa lokacin da Allah Ya haddade masa. Wasu kan ce tunda wannan ita ce dabi’a da tsarin turawa wajen bincike, to kenan galibin abinda suke fada a matsayin sakamako duk karya ne, kuma baza mu yi amfani da shi ba. Wannan kuskure ne babba. Abinda ya kamata shine a yi amfani da abinda suka fada wanda zai kaimu ga samun rayuwa mai sauki da warware dukkan matsalolinmu a matsayinmu na al’umma, wanda ya saba masa kuma, ko zai kai mu ga halaka, dole ne a guje masa. Hanya mafi sauki a karshe dai ita ce samun ‘yancin kai a ilimance; mu yi karatun, mu yi binciken da kanmu, a nan kadai zamu iya gane zurfin karyarsu ko rashinsa. Don haka, a cikin wannan dan karamin bincike da zamu gabatar kan dumamar yanayi zamu rika cakuda dalilai ne tsakanin wadanda bincike ya tabbatar dasu a wannan zamani, da kuma wadanda daman can akwai su a zamunnan baya. Abubuwa ne da suke tabbatattu kana iya jinsu, wasu kuma kana iya fahimtarsu idan ka kwatanta lokacin da kake rayuwa ciki yanzu da lokutan baya. Don haka duk abinda ba a fahimta ba a yi tambaya. Allah sa mu dace, amin. (Zamu ci gaba)

Monday, March 16, 2009

Wasikun Makon Jiya

Daga wannan mako in Allah ya yarda zamu rika kawo wasikun da kuke aiko mana iya gwargwadon hali, don kauce wa taruwansu. A nan zamu rika amsa wasu cikin tambayoyin da kuke yi, tare da nuna godiya kan wadanda kuka aiko don nuna gamsuwarku. Sai a ci gaba da kasancewa tare da mu. – Baban Sadik

Assalamu Alaikum, ina yi maka fatan alheri tare da addu’a a gareka a bisa namijin kokarin da kake yi wajen fadakar da mu ta hanyar Intanet. Allah kara maka kwarin gwiwa amin. Don Allah Malam ina so kayi min bayani kan yadda duniya take juyawa, da bayani a kan “gravity”. Sako daga Yusif Chamo, Kano: 08030413951

Malam Yusif Chamo barka da war haka, kuma muna godiya da wannan karfin gwiwa da ka kara mana. Allah saka da alheri kai ma, amin. Bayani kan yadda duniya ke juyawa (earth revolution) na bukatar bincike natsattse, kuma in Allah Ya so zamu yi iya abinda ya sawwaka wajen kawo hakan. Dalili kan hakan shine, akwai sakamakon binciken da turawa suka yi kan haka, wanda galibi shi ake karantar da ‘ya’yanmu a makarantun zamani, wanda kuma daga baya bayanai sun nuna cewa akwai nakasar inganci kan wadannan bincike da aka yi, shekaru da dama da suka gabata. Har wa yau, sakamakon juya hankali da wasu kwararru suka yi daga tsarin binciken turai, zuwa bayanan da Alkur’ani ya kawo kan yadda tsarin da duniya ta samu, da yadda take gudanuwa, an samu bambancin ra’ayi da sakamako tsakanin wadannan masu bincike. Dukkan wannan na bukatar kyakkyawar nazari da tantancewa, wanda bazai samu ba cikin dan kankanin lokaci. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Salamu alaikum Baban Sadiq, tambaya ta a nan ita ce, a kan tashoshin rediyo na wayar salula (mobile phone radio frequency band); na ga duk sun fi amfani da tsarin FM (Frequency Modulation), a kan AM (Amplitude Magnification). Malam akwai masu amfani da AM kuwa? Allah taimaki malam da daliban wannan shafi mai albarka na Kimiyya da Fasaha, amin. Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034332200, 07025815073

Malam Aliyu barka da kokari, kamar yadda aka saba, muna kuma kara godiya ga irin kokarin da kake wajen lura da wannan shafi mai albarka. Watau kamar yadda ka sheda, cewa akwai tsarin tashar rediyo na wayar salula mai suna FM, ba shi kadai bane, akwai wayoyin salula masu rediyo mai tsarin SW (Short Wave), watau “Gajeren Zango”, duk da yake suna da tsada kwarai da gaske. Da irinsu kana iya kama tashoshin BBC da VOA da sauran tashoshin da ke kasashen waje. Dangane da wayoyin salula masu tsarin AM, ban taba cin karo dasu ba, kuma ban samu labari kansu ba, ta yiwu ba a fara kera irin su ba, ko ma baza a kera irinsu ba – domin tsohon yayi ne. Amma wannan baya nufin baza a iya bane, ya danganta da yanayi da kuma zurfin bincike. Abinda ke faruwa shine, duk wata sabuwar fasaha da ka ga an sanya wa wayar salula, yin hakan bai samu ba sai da aka gudanar da bincike kan yadda tsarin zai tabbata, ba tare da ya yi mummunar tasiri kan asalin aikin wayar ba. Misali, zai yi wahala ka samu wayar salula mai tsarin sadarwar tashar rediyo ta FM da kuma SW a lokaci guda. Mai yasa? Watakil an gwada, sai aka lura yin hakan na iya haddasa matsalar sadarwa ga wayar baki daya, dole a cire daya a bar daya. Ba abin mamaki bane nan gaba a samu, amma sai bayan dogon bincike, mai daukan lokaci. Da fatan ka gamsu.

Assalamu Alaikum Baban Sadik, ba abinda zan ce maka sai Allah Ya saka maka da alheri. Domin a dalilin bayanin da kayi mana na yadda ake shiga Intanet ta hanyar wayar salula, a yanzu na kan shiga tashar Sashen Hausa na BBC don sauraran labaransu kafin ma lokacin yada shirye-shiryensu yayi. Haka kuma nakan shiya gidan yanar sadarwa ta Harun Yahya – www.harunyahya.com – da na MTN – www.mtnonline.com – da dai sauransu. Ba abinda zan ce maka sai Allah saka da alheri. Daga Muhammad Abbas, Lafiyan Bare-bari, Nassarawa State: 08036647666

Malam Abbas, mun fi ka farin ciki da jin haka, wannan ke nuna cewa abinda ake gabatar muku a wannan shafi yana yin tasiri matuka; wanan shine abinda ake so, kuma dalilin assasa shafin kenan. Sai a ci gaba da amfana da wannan tsari ta hanyar da ta dace, don samun ilimi da fadakarwa mai amfani. Muna kara godiya da wannan wasika taka.

Salamu alaikum Baban Sadik, ita na’ura mai kwakwalwa (computer) bata da bera ne (mouse)? In akwai, to yaya aikinsa yake ne? Kuma allon rubutu (keyboard) shi ma ya aikinsa yake? Malam, idan aka ce ba daya daga cikinsu, shin kwamfuta za ta yi aiki kuwa? Kuma wanne yafi muhimmanci gareta wajen sarrafa ta? Daga Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034442200

Dara taci gida kenan! Malam Aliyu shafin Kimiyya da Fasaha na mamakin samun wannan tambaya ta farko daga gareka, ai tun shekarar da ta gabata muka gabatar da bayanai shafi guda kan Beran Kwamfuta; tarihi da na’uka da kuma yadda yake aiki. Watakil baka samu wannan kwafe ba! Kana iya samun kasidar a wannan rariyar: http://fasahar-intanet.blogspot.com/09/2008/beran-kwamfuta-computer-mouse.html. Dangane da allon shigar da rubutu kuma, fasaha ne mai dauke da dabarun sadarwa tsakaninsa da allon kwamfuta, watau “Motherboard”. Shine shahararren hanyar shigar da bayanai cikin kwamfuta kai tsaye. Ai ko tantama babu; allon shigar da bayanai yafi beran kwamfuta amfani ga kwamfuta. Domin idan babu beran kwamfuta, kana iya sarrafa kwamfuta kai tsaye; ka bude masarrafar da kake so, kayi rubutu, ka rufe, sannan in ta kama ma kana iya buga bayanan da ka rubuta (printing) cikin sauki, duk ta hanyar allon shigar da bayanai. Sai dai ba kowa zai iya hakan ba, musamman a yanzu da mutane suka shagwabe wajen amfani da beran kwamfuta. Da zarar ka kawo kwamfuta babu beranta, ka sanya su cikin garari. Idan muka yi la’akari da tsohuwar babban manhajar kwamfuta ta kamfanin Microsoft mai suna DOS (Disk Operating System), ai bata bukatar beran kwamfuta. Da allon shigar da bayanai ake kunna ta, a shiga inda ake son shiga, sannan a fita, zuwa kashe kwamfutar. Da fatan ka gamsu.

Salamun alaikum, da fatan kana lafiya. Kokarin da ya kamata Malam yayi mana shine, dukkan littafan da aka rubuta su da Hausa kan fannin Kimiyya (da Fasaha), irinsu likitanci, da kanikanci da sauransu. In har sun shiga hannunka, ka dora mana su a shafin Kimiyya da Fasahar a Intanet, don amfanin dukkan daliban da suke wannan makaranta, a ko ina suke a duniya. Ka huta lafiya. Daga dalibinka Sani Abubakar (Na ‘Yan Katsare), Jas: 08026023796

Malam Sani kwana biyu mun ji ka shiru, da fata kana cikin koshin lafiya, amin. Wannan shawara taka na da muhimmanci, musamman ganin irin bukatun da muke tattare da su kan samuwar wadannan fannoni cikin harshen Hausa. Sai dai aiki ne mai wahala: daga abinda ya shafi samun littafan, zuwa kan kwafansu ko rubuce su a kwamfuta, zuwa tsara gidan yanar sadarwar da zata dauke su, da dai sauran abubuwa. Zan yi iya kokari na kan haka, amma kada a dauki wannan a matsayin alkawari mai kiyastaccen lokaci. Sai yadda ta kasance, iya halin da na samu kai na da wadanda zasu iya taimaka mani. Watakil ma sai na hada da dukkan daliban wannan shafi in Allah Ya yarda. Mun gode da wannan shawara, kuma muna mika gaisuwarmu ga dukkan daliban wannan shafi da ke garin Jas da Gumel da Kano da Kaduna da Fatakwal da Nasarawa da Bauchi da Birnin Kebbi da Sakkwato da Legas sauran wurare. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Damuwar Kasashen Turai Kan Shirin Bunkasa Fasahar Sararin Samaniya

A karon farko, kasar Iran ta harba tauraron dan Adam da ta kera a kasarta cikin falaki, a cclip_image002ewar shugaba Ahmadinajad, ranar Talata, 17 ga watan Fabairu, 2009. Hakan ya zo ne daidai lokacin da kasar ke bikin cika shekara 30 da kafa gwamnatin Islama, kuma ta fara hakan ne cikin kokarinta na ganin ta habaka bincike kan kimiyyar sararin samaniya don samar da ingantacciyar hanyar sadarwa da ilimi da kuma lura da lardunanta da ke fama da girgizar kasa lokaci-lokaci. Kamar yadda Shugaba Ahmadinajad ya sanar, gwamnatin kasar Iran ba don komai ta fara wadannan shirye-shirye ba kama hannun yaro ba sai don wadannan dalilai, da kuma ci gaba da kokarinta wajen samar da ingantacciyar zaman lafiya da lumana a duniya, sabanin yadda sauran kasashen Turai da Amurka ke tunani.

Jim kadan da harba wannan tauraron dan Adam da kasar ta sanya wa suna Omid, ma’ana “kyakkyawar fata” a harshen Farsi, jami’an gwamnati masu lura da shawagin taurarin dan Adam a sararin samaniya na kasar Amurka sun tabbatar da hakan, duk da yake sun ki yin wani karin bayani kan haka. A nasu bangaren su ma, hukumomin kasar Faransa sun sake tabbatar da haka, cewa lallai sun lura da wani sabon tauraron dan Adam da ya isa cikin falaki a wannan safiya. Sai dai kuma a nasu bangaren, sun nuna damuwarsu ga ire-iren “wadannan shirye-shiryen karkashin kasa kan harkar sararin samaniya da ana iya amfani da su wajen harba makamai masu guba”, a cewar Ministan Harkokin Waje na kasar, Mr. Eric Chevallier. Ire-iren wadannan ikirari da gurguwar fahimta dai sun dade suna kai-komo tsakanin kasashen Turai da Amurka tun sa’adda kasar ta fara shirinta na habaka makamashin Yuraniyon don samar da wutar lantarki ga mutanenta.

Shugaba Ahmadinajad dai yace wannan tauraron dan Adam da kasar ta harba ya isa muhallinsa cikin falaki, har ma ya fara shawagi, duk da cewa ba dukkan gabobinsa bane suka fara aiki kai tsaye. Sun kuma gane hakan ne ta hanyar sadarwa da tauraron ya samu yi da jami’an da ke lura da shawaginsa a kasar. Hakan ke nuna cewa lallai ya isa lafiya, tun da har ya fara shawagi. An kuma harba wannan tauraro na Omid cikin falaki ne ta hanyar mizail mai suna Safir-2, wanda yayi tafiyar kilomita kusan dari biyar daga sararin wannan samaniya tamu, kafin ya cilla tauraron don isa muhallinsa. Wannan mizail mai suna Safir-2 dai shine makamin da kasar Iran ta yi gwajinsa bayan an kera shi cikin watan Agustar shekarar da ta gabata, kuma makami ne mai matsakaicin zango wajen tafiya. Rahoton da gidajen rediyo a kasar suka bayar bayan harba wannan sabon tauraro zuwa falaki na nuwa cewa zai rika kewaya wannan duniya ne sau goma shabiyar a dukkan awanni ashirin da hudu na kowace rana. Kuma babban aikinsa shine taskancewa tare da aiko sakonni ko rahotanni zuwa cibiyar sararin samaniya da ke kasar. Yana da tafarkin sadarwa guda biyu, da kuma kunnuwar aika sakonni guda takwas, wadanda za su rika taimaka masa wajen aikawa da sakonnin da ya taskance zuwa wannan duniya tamu. Shugaban ya kara da cewa wannan wani hobbasa ne kasar ta yi wajen habaka harkar fasahar sadarwa a kasar. Bayan wannan yunkuri, in ji Ahmadinajad, abinda ya saura wa kasar Iran yanzu shine ta “ci gaba da ingantawa tare da habaka wadannan mizail da kuma karfinsu wajen daukan wasu taurarin dan Adam da suka fi wannan nauyi nan gaba”. Wannan ke nuna cewa nan gaba ma kasar za ta sake kerawa tare da harba wani tauraron dan Adam din cikin falaki. A karshe, shugaba Ahmadinajad ya ce “muna bukatar kimiyya ne don sadar da zumunci, da karfafa ‘yan uwantaka, tare da tabbatar da adalci.”

Wannan wata shagube ce ake ganin Shugaba Ahmadinajad ke wa sauran kasashen Turai da Amurka, wanda tuni ya sha zarginsu da nuna karfi wajen tirsasa wa sauran kasashen duniya don bin ra’ayinsu, duk da irin zaluncin da suka siffatu da shi, tare da azarbabi kan abinda ya shafi harkokin wasu kasashen dabam. Babbar damuwar wadannan kasashe dai kan wannan sabon shirin habaka fasahar sararin samaniya na kasar Iran shine, duk da cewa sun yarda sauran kasashe na yin haka ne wajen ciyar da kansu gaba wajen sadarwa, suna nuna damuwa ne da irin tsarin shugabancin da ke Iran, wacce a cewarsu, tana iya amfani da wadannan makaman mizail da take kerawa kuma ta ke cilla tauraron dan Adam da su, don kai hari ta sararin samaniya ga kasashen da bata ga-maciji da su. Amma kasar Iran ta karyata ire-iren wadannan jita-jita, inda take nuna cewa ba komai yasa ta fara wadannan shirye-shirye na sararin samaniya ba sai don lura da lardunanta da ke fama da girgizar kasa lokaci-lokaci, da kuma habaka harkar kimiyya da fasahar sadarwa don ci gaban al’ummarta. Tace a bayyane yake cewa kasar Amurka na amfani da ire-iren wadannan taurarin dan Adam da ta cilla cikin falaki ne don lura da kasashe irin su Afganistan da kasar Iraki, amma su a nasu bangaren, zasu yi hakan ne wajen kare kasarsu da mutuncinta a idon duniya.

Wannan dai shine tauraron dan Adam na farko da kasar ta cilla, wanda musamman ta kera shi da kudinta, da kuma kayan aikinta, a kuma kasarta. Sabanin wanda ta cilla cikin shekarar 2005 ta hadin gwiwa da kasar Rasha, wacce ake ganin ita ce ke da alhakin taimaka wa kasar Iran wajen habaka shirin ta na fasahar sararin samaniya da ma wanda take yi kan makamashin nukiliya a halin yanzu. A shekarar 2005 ne gwamnatin Iran ta ware kudi wuri na gugan wuri har dalar Amurka miliyan dari biyar don wannan shiri na habaka fasahar sararin samaniya, kuma a na sa ran kasar za ta sake cilla wasu taurarin guda uku, nan da shekarar 2010. Wannan ke nuna cewa har yanzu kasar Iran bata yi ko gizau ba daga ire-iren tuhume-tuhumen da kasashen Turai da Amurka ke mata a kullum, wanda hakan ke dada tayar musu da hankali. Basu gushe ba wajen shirya tarurruka tsakaninsu da jami’an gwamnatin Iran, wanda a cewar masu lura da siyasar duniya, suna hakan ne don tursasa wa kasar a siyasance, ta amince da tuhume-tuhumen da suke mata, don su tabbatar wa duniya gaskiyarsu. Sai dai ga dukkan alamu, hakan zai yi wahala, wai cire wando ta ka!