Wannan ita ce kasidar da na gabatar a taron TSANGAYAR
ALHERI na shekara shekara, wanda aka yi a makera Motel da ke hanyar Daura a
Katsina birnin Dikko. Duk da cewa a baya
na gabatar da wasu daga cikin abubuwan da ke kasidar, amma da yawa daga cikin
al’amuran da ta kunsa baki ne ga mai karatu. A sha karatu lafiya.
Wata Sabuwar Duniya
Ray Lam dai wani matashi ne a birnin Vancouver
na jihar British Colombia da ke ƙasar Kanada; ya gama jami'a, ya kuma yi ayyuka
sosai wajen ganin ci gaban rayuwarsa. Ganin
haka tasa yayi tunanin shiga siyasa don kawo sauyi a mazaɓarsa. Nan take ya
kama kamfe, jama'a suka ta zagaye shi: "Sai ka yi…sai ka yi…sai ka
yi," kamar dai yadda ake wa 'yan siyasanmu a yau. Ya shahara sosai har abokan hamayyarsa suka
fara neman yadda za su kayar da shi, amma abu ya ci tura. Sai ta hanyar Dandalin Facebook suka ci
nasara. Yana da shafi inda yake kamfe a
dandalin, wanda ke cike da hotunansa na zamanin samartaka. Daga ciki akwai waɗanda ya ɗauka yana dafe da
ƙirjin budurwarsa a gidan rawa ana holewa, da kuma waɗanda ya dauka masu
bayyana al'aurarsa. Nan take suka ɗauko waɗannan hotuna suka ta rabawa; ana
mannawa a wurare. Wannan ya rage masa shahara, da cewa ashe ɗan iska ne, har
yana bayyana tsaraicinsa ga duniya.
Wannan bai kamata ya zama shugaba ba.
Wannan ya tilasta masa fita daga jerin 'yan takara, abokan hamayyarsa
suka samu nasara a kansa. Babban dalili
shi ne katoɓarar da yayi wajen ɗora hotunansa marasa kyau, masu nuna rayuwarsa
ta baya, wanda hakan ya kai shi ya baro.
Jama'a, ina mana barka da shigowa wata sabuwar
duniya a cikin wannan duniya tamu, wadda har yanzu bamu gama sanin haƙiƙaninta
ba. Duniya ce mai cike da annashuwa, da
raha, da sauƙin rayuwa, da sauƙin mu'amala, da sauƙin sadarwa, da sauƙin yin
abota, da hanyoyin samun faɗakarwa, da hanyoyin gabatar da faɗakarwa, da sauran
hanyoyin gabatar da harkokin rayuwa a wani tsari mai kama da haƙiƙa. Kai, ba kama bane, rayuwar haƙiƙa ce, sai dai
a wani irin yanayi mai cike da mamaki, irin wanda ke wautar da fahimtar ɗan
adam. Domin a yayin da wannan sabuwar duniya ta mu ke
bamu waɗancan hanyoyi na farin ciki da annashuwa da bayaninsu ya gabata, har wa
yau dai ita ce ke cike da abubuwan mamaki na baƙin ciki, da damuwa, da shagwaɓa,
da ruɗi mara iyaka, da wasu munanan halaye masu jefa mutum cikin irin halin da
matashi Ray Lam ya samu kansa a ciki, kamar yadda kuka ji a farko.
Wannan duniya dai ba wata bace illa sabuwar duniyar
da ci gaba a fannin kimiyyar sadarwa da fasahar sarrafa bayanai ya tsunduma mu
ciki tsundum, daidai gab da ƙarshen karnin da ya gabata. Wannan ita ce sabuwar duniyar tsarin sadarwa
ta Intanet, wadda a farkon lamari ta faro da 'yan kwamfutocin da basu shige ɗari
ba, amma a halin yanzu akwai sama da biliyan uku masu ɗauke da bayanai da muke
aikawa a tsakaninmu. Samuwar fasahar
Intanet da yadda bunƙasarta ya kasance abu ne mai cike da mamaki ga duk wanda
ya san asalin lamarin, amma bai kai irin mamakin da ke ɗauke da sabuwar duniyar
da ta tsiro a cikinta bayan 'yan shekaru ƙasa da goma da suka shige ba. Wannan duniya dai Jama'a, ita ce duniyar
gamewar mu'amala a mahallin sadarwa. Daga kowace nahiyar duniya a yau jama'a
sun game, sun zama ɗaya; suna samun sanayya a tsakaninsu. Wannan ta kai ga samun natsuwa, da kuma ruɗuwa,
inda aka wayi gari jama'a suka sake; komai na rayuwarsu ma suna iya bayyana
shi; cikin rubutu ne, ko hotuna ne, ko zane ne, ko murya ne, ko kuma hoton
bidiyo ne mai motsi. Ba abin da ya shafe
su. Wannan shi ne irin ruɗin da ya jefa
matashi Ray Lam cikin halin da ya samu kansa.
Ta yaya wannan sabuwar duniya ta tsiro daga mahallin giza-gizanin
sadarwa ta duniya?
Samuwar Dandalin Abota a Intanet
Tsarin samar da bayanai a Intanet ya kasu
kashi biyu. Tsarin farko shi ne tsohon
tsari; watau hanyar samar da bayanai ta gidan yanar sadarwa. Wannan shi ne tsohon yayi, kuma shi ne abin
da a farkon zamanin mu’amala da fasahar Intanet ya shahara. Da tafiya tayi nisa, harkar kasuwanci ta fara
haɓaka a duniyar Intanet, sai ‘yan kasuwa suka shiga binciken sanin hanyoyi ko
irin buƙatun da masu sayen hajojinsu a
Intanet ke da su ko suke bi. Wannan ta
sa aka fara ƙirƙirar gidajen yanar sadarwa ko mudawwanai masu baiwa mai ziyara
a gidan yanar sadarwa damar faɗin albarkacin bakinsa kan hajar ko abin da yake
so ko yake sha’awa. A ɗaya gefen kuma
sai ga manyan gidajen yanar sadarwa – irin su Yahoo!, da MSN, da Google - sun
ƙirƙiro hanyoyin da masu ziyara ke haɗuwa suna tattaunawa kan buƙatunsu na
rayuwa, da ɗanɗanonsu kan rayuwa, da abubuwan da suke buƙata, da dai sauran
abubuwan da suka shafe su. Hakan kuwa ya
samu ne ta hanyar Majalisun Tattaunawa da Zaurukan Hira (wato Cyber
Communities – ko “Ƙauyukan Intanet”), waɗanda kuma suka haɗa da Groups, da
Internet Chat Rooms, da Communities, da kuma Bulletin Board ko
Forums. A waɗannan wurare, masu
karatu da masu ziyara da masu saye da sayarwa ne ke tattaunawa a tsakaninsu kan
buƙatunsu da ɗanɗanonsu. Kuma wannan
tsari, a harshen Kimiyyar Sadarwa ta Zamani, shi ake kira User Content; wato
tsarin samar da bayanai ta hanyar mai ziyara.
Samuwar wannan tsari ne har wa yau, ya haifar da samuwar ire-iren
dandamalin abota da ake dasu a Intanet a yau, irin su Facebook, da NetLog,
da JHoos, da LinkedIn da dai sauran makamantansu. Waɗannan su ake kira Social Networking
Sites.
A mahangar Kimiyyar Sadarwar Zamani, idan aka
ce “Social Network” ana nufin dandalin shaƙatawa ne da yin abota. Wuri ne ko kace “Dandali” ne da ke haɗa
mutane daga wurare daban-daban, masu launi daban-daban, masu harshe
daban-daban, daga wurare daban-daban, masu matsayi daban-daban, masu matakin ilimi
daban-daban, kuma masu manufofi daban-daban.
Haɗuwar waɗannan mutane a “mahalli ɗaya” shi ke samar da wani dandali buɗaɗɗe,
mai kafofi daban-daban, inda kowa ke zaɓan abokin hulɗarsa ta hanyar masarrafa
ko manhajar kwamfuta da aka ƙirƙira a irin wannan dandali. Kafin mu yi nisa,
yana da kyau masu sauraro su san cewa wannan dandali ba wani abu bane illa wani
gidan yanar sadarwa ne na musamman da wasu ko wani kamfani ko mutum ya samar
don wannan manufa. Manufar a farko ita
ce samar da muhallin da mutane za su tattauna da juna ta hanyar yin abota da yaɗa
ra’ayoyinsu kan wasu abubuwa da suke sha’awa.
Wannan manufar asali kenan. Amma a
yau wannan manufa ta canza nesa ba kusa ba.
Akwai manufar kasuwanci, da yada manufa ta siyasa ko addini, da samar da
hanyoyin bincike kan ɗanɗanon mutane dake dandalin.
Bunƙasar Dandalin Abota a Intanet
Samuwa da yaɗuwa da bunƙasar dandalin abota a
Intanet ya kashe wa zauruka da majalisun tattaunawa kasuwa, duk da cewa har
yanzu akwai su. Dalilan bunƙasa da haɓakansu
kuwa ba nesa suke ba. Abu na farko shi
ne ingantuwar hanyoyin gina manhajar sadarwa tsakanin gidan yanar sadarwa zuwa
wani gidan. Sai yaɗuwar na'urorin
sadarwa masu ɗauke da ƙa'idar sadarwar Intanet (Internet Protocols) irin
su wayoyin salula da dukkan nau'ukansu (kamar su iPhone, da iPad,
da iPod, da BlackBerry, da Samsung Galaxy Note da
sauransu). Abu na uku shi ne sauƙin
hanyoyin rajista a waɗannan dandalin abota.
A yayin da ake buƙatar dole sai ka kai shekaru 18 kafin ka iya mallakar
akwatin Imel, a wajen rajistar mallakan shafi a dandalin abota ana buƙatar
shekaru 13 ne kacal. Abu na hudu shi ne bunƙasar
hanyoyin kasuwanci da nau'ukansu a giza-gizan sadarwa ta Intanet. Abu na biyar
shi ne sauƙin mu'amala da waɗannan shafuka suke tattare dashi. Duk rashin karatunka kana iya sarrafa su iya
gwargwado. Sai abu na shida, wato
ingantuwar tsarin sadarwar fasahar Intanet a ƙasashe masu tasowa, musamman
nahiyar Afirka, da Gabas-ta-tsakiya, da Gabashin Asiya da kuma Kudancin Amurka.
Wannan bunƙasa yana da ban al'ajabi matuka. Domin ba matasa kadai ya game ba, har da
manya, da tsofaffi, da kuma kananan yara. Ba 'yan birni kadai abin ya shafa ba, har da
'yan karkara, da makiyaya. Kai, lamarin ma ya hada da nakasassu ta ɓangaren
gani da ji; duk ba a barsu a baya ba. Shahararru daga cikin dandalin abota da aka fi
shawagi a cikinsu dai su ne: Dandalin Facebook, da Dandalin Twitter, da
Dandalin Instagram, da Dandalin Pinterest, da kuma Dandalin Google+. Waɗannan dandamali dai ana ji da su a ƙasashen
duniya, saboda tasirinsu wajen kame zukatan masu mu'amala da su. Abin ya wuce hankali da sanin ya-kamata.
Dandalin Facebook, wanda ya faro daga ɗaliban
jami'a zuwa 'yan sakandare shekaru 8 da suka gabata, a yanzu yana da mambobi
masu rajista a duniya sama da biliyan 1.2!
Mutum miliyan 4 ne suka "so" jawabin nasara da shugaba Obama
ya rubuta a shafinsa na Facebook. Kashi 25 cikin masu amfani da shafin Facebook
basu damu da wata kariya ba. A duk wata
a ƙalla mutum miliyan 800 ne ke shiga Dandalin Facebook. Mutum miliyan 488 ne kuma ke mu'amala da
shafin Facebook ta wayar salula. Sama da kashi 23 kan shiga shafinsu na Facebook
sau biyar a duk yini. A ƙalla akan
shigar da hotuna sama da miliyan 250 a duk rana. Zuwa ƙarshen shekarar 2012, an saurari waƙoƙin
da tazarar lokacinsu ya kai tsawon shekaru 210,000 a Dandalin Facebook. Kashi 80 cikin 100 na masu neman hajojin
kasuwanci sun fi son samunsu ta hanyar Dandalin Facebook. Kashi 43 cikin masu mu'amala da shafukan Facebook
maza ne, a yayin da sauran kashi 57 ɗin duk mata ne.
A ɓangaren Dandalin Twitter ma haka
lamarin yake. A tsawon kwanakin shekara
ta 2012, duk rana masu mu'amala da Dandalin Twitter kan aika sakonni
miliyan 175. Ya zuwa yanzu tun bayan buɗe
shafin Twitter, an samu saƙonni sama da biliyan 163. Jawabin nasarar shugaba Obama ne yafi kowane
saƙo yawan tallatawa, yayin da aka tallata shi (retweeted) sau miliyan
800! Lokacin zaɓen ƙasar Amurka da ya
gabata an aika da saƙonnin da suka danganci zaɓe wajen biliyan 31.7! Cikin masu amfani da fasahar Intanet gaba ɗaya,
kashi 32 na amfani da masarrafar Twitter. A tsawon kwanakin shekarar 2012, a duk rana
an samu masu rajista a ƙalla miliyan ɗaya.
Shafin da jama'a suka fi bi a Dandalin Twitter shi ne na
shahararriyar mawaƙiya Lady Gaga, inda ta wayi gari da masu binta sama da
miliyan 31. Shafin kamfanin da jama'a suka fi bi a dandalin twitter kuma shi ne
na Youtube, inda ya samu masu bi sama da miliyan 19. Kashi 50 cikin ɗari na masu mu'amala da
Dandalin Twitter na yin haka ne ta hanyar wayar salula. Kai jama'a, in taƙaice muku zancen, a
Dandalin Twitter a duk sakwan guda, sai an samu masu rajista mutum 11.
Idan muka koma ɓangaren Dandalin Google+, wanda
bai jima da bayyana ba, za mu ga abin mamaki nan ma. Shafin, wanda gwarazan
masana harkar manhajar kwamfuta sama da 500 ne suka gina shi, ya zuƙi dala na
gugan dala wajen miliyan 585! A duk rana
jama'a kan matsa alamar Google+1 sau biliyan 5! Cikin kashi 100 na kamfanonin da suka fi
yawan dukiya a duniya, kashi 48 na da shafi a Dandalin Google+. A duk rana mutane sama da 625,000 ne ke
amfani da shafin Google+. Cikin
mutum miliyan 400 da suka mallaki shafi a Dandalin Google+, kashi 27 ne
masu aure, sauran duk tuzurai ne; marasa
aure. Cikin wannan adadi har wa yau,
kashi 68 maza ne, sauran kashi 32 mata ne.
Kashi 60 cikin 100 na mamabobin Dandalin Google+ kan shiga
shafinsu a duk yini.
Wannan ƙididdiga mai kama da almara, kaɗan ne
daga cikin abubuwan mamaki da waɗannan shafukan abota suke ɗauke dasu. Goma daga cikin mafiya yawansu su ne: Facebook
(biliyan 1.2), sai Twitter (miliyan 500), sai Qzone (miliyan
480), sai Google+ (miliyan 400), sai kuma SinaWeibo (miliyan
300). Sauran sun haɗa da: LinkedIn
(miliyan 160), da Orkut (miliyan 100), da NetLog (miliyan 95), da
hi5 (miliyan 80), sai kuma dandalin MySpace, wanda tuni ya mace
(miliyan 30).
Idan muka dawo nahiyar Afirka, ƙasashen da
suka fi mu'amala da Dandalin Facebook su ne: Misra (miliyan 12.1), da
Najeriya (miliyan 6.7), da Afirka ta kudu (miliyan 6.4), da Maroko (miliyan 5),
sai kuma Aljeriya (miliyan 4). A ɓangaren
dandalin twitter kuma, ƙasar Afirka ta kudu ce a gaba, da yawan saƙonni sama da
miliyan 5 a shekarar 2011. Sai ƙasar Kenya
da saƙonni sama da miliyan 2. Sai kuma ƙasarmu
ta gado Najeriya, mai saƙonni sama da miliyan 1.6. A nahiyar Afirka, kashi 57 na saƙonnin Twitter
da ake aikawa duk ta hanyar wayar salula ne.
Kashi 60 cikin masu amfani da Dandalin kuma duk matasa ne 'yan shekaru
20 - 29. Ƙididdiga kuma ya tabbatar da
cewa duk masu rajista a Dandalin Twitter, suna da rajista a Dandalin
Facebook, da Youtube, da Google+, da kuma LinkedIn. A duniya gaba ɗaya, kashi 23 cikin masu
mu'amala da shafukan abota a duk rana matasa ne. Kuma
kamar yadda bayanai suka gabata, matasa sun fi shawagi a Dandalin Facebook,
saboda keɓantattun siffofin da ya keɓanta dasu.
Don haka, sauran bayanan da ke tafe kan tsarin mu'amalar matasanmu a
dandalin abota na Intanet, za su taƙaita ne kan wannan dandali.
Sana'ar Matasanmu a Dandalin Facebook
A bayyane yake cewa akwai matasanmu da yawa a
Dandalin Facebook; tsakanin 'yan mata da samari, da tsofaffi da zawarawa,
da gwagware da tuzurai, duk sun yi rajista kuma suna sada zumunci iya
gwargwado. Babban abin da ya sawwaƙe yaɗuwarsu
a wannan dandali kuwa dalilai ne guda biyu.
Abu na farko shi ne samuwar wayar salula a hannun jama'a, wanda ya game
gari da duniya baki ɗaya. Abu na biyu
shi ne sauƙin mu'amala. Shafin facebook
yana da sauƙin mu'amala. Wannan yasa duk
wanda ya shiga sau ɗaya sau biyu, ba ya buƙatar wani darasi kuma. Cikin amfanin da matasanmu ke samu a Dandalin
Facebook akwai sadarwa, da yin abota, da samar da sanayya mai amfani da
amfanarwa, da fahimtar rayuwa ta hanyar kallon yadda wasu ke tafiyar da
rayuwarsu a duniyar da suke. Akwai kuma samartaka tsakanin 'yan mata da
samari, da koyon addini, da siyasa, da raha, da faɗakarwa, da kuma
sambatu.
A ɗaya ɓangaren kuma, akwai majalisu da
matasanmu suka kafa masu amfani sosai.
Akwai zaurukan tattaunawa na musamman masu amfani su ma. Akwai kuma shafukan gwaraza da suka buɗe don
koyi dasu ko karantarwarsu. Akwai
zaurukan zumunta na musamman. Wasu daga
cikinsu sun haɗa da: Zauren Sahabban Manzon Allah (7,608), da Dandalin Marubuta
(7,292), da Tsangayar Alheri (4,570), da Dandalin Ilmantarwa da Nishandantarwa
(1,614), da Dandalin Tsaraba daga Mimbarorin Jumu'a (1,392), sai Dandalin
Tambayoyin Musulunci (273). Sauran sun
haɗa da: Dandalin Zauren Sunna (2,845), da Dandalin Buhariyya Zalla (10,293),
da Dandalin Siyasa (5,283), da Dandalin Iyantama (13,377), sai kuma Dandalin Dariya
(8,801). A ɓanganren shafukan gwaraza
kuma akwai shafin Dakta Sheikh Mansur Sakkwato (5,707), da shafin Marigayi
Sheikh Ja'afar (23,670), sai Zaure na musamman mai take: Zauren Malam Ja'afar
(10,454). Dukkan wannan adadi, tsakure ne cikin
daruruwan shafuka da zaurukan da matasanmu suka buɗe kuma suke aiwatar da
sadarwa a tsakaninsu a wannan Dandali.
A ɗaya ɓangaren kuma, wannan dandali ya baiwa
matasanmu wata sabuwar hanyar faɗakarwa da karantarwa da tunatarwa da kuma
gayyata. Wanann tsari ya samar da wata
hanya ta gayyatar biki, ko suna, ko taro, ko duk wani sha'ani nay au da kullum. A ɓangaren siyasa ma haka abin yake; kowa na
bayyana ra'ayinsa yadda yake so, ba tare da tsangama ba. Waɗannan kaɗan ne cikin amfanonin da matasa
ke samu a wannan dandali.
Manyan Ƙalubale
A duk inda aka ce samari da 'yan mata sun haɗu,
a yanayin da ba a ganin juna, a yanayi mai jefa hankali da zuciya wata nahiyar
nishaɗi mai girma, to, dole a samu 'yar karkata. Domin tatsuniyar Gizo, kamar yadda muka sani,
ba ta wuce Ƙoƙi. Daga cikin manyan ƙalubalen
da ke fuskantar matasanmu a wannan dandali shi ne na rashin alƙibla a galibin
lokuta, musamman a shafukansu. Wannan ke
sa a kashe lokaci ana lilo a shafin Facebook amma in ban da sambatu ba
abin da ake yi. A ɗaya ɓangaren kuma
muna yawan ruɗuwa da hotunan 'yan mata.
Waɗanda suka fi yawan abokai a shafukansu su ne mata, a duk faɗin Dandalin
Facebook. Dalilin hakan kuwa ba
sai na gaya muku ba. Su kansu 'yan matan
sun fahimci haka. Wasu daga cikinsu kan
loda hotunan da ba nasu ba, musamman idan ba kyawawa bane su. Idan ka ga irin yabon da samari ke yi kan
hotunan 'yan mata, kare bazai ci kalaman ba.
Ƙalubale na gaba shi ne rashin kiyaye
sirri. Kowa da irin tsarinsa a rayuwa,
amma wannan
ba ya nufin komai na rayuwarka sai ka bayyana wa jama'a a shafinka. Kada mu mance lamarin marigayiya Cynthia,
wacce wasu samari suka ruɗa a shekarar da ta gabata, a ƙarshe suka mata fyaɗe,
suka kuma kashe ta bayan sun gayyace ta birni Ikko, tun daga jahar Nasarawa. Da yawa mukan rubuta sirrin rayuwarmu, mu
loda hotunan sirri a shafinmu, da duk abin da ya shafe mu, ba tare da tunanin
cewa wani na iya dauka ya sarrafa su don wata mummunar manufa ba. Bayan haka, mu faɗaka; akwai jami'an leken
asiri na gwamnati da na ɓarayi, masu neman inda rauni ko sakaci yake, don
tattaro bayanai kafin su aiwatar da aikinsu, mummuna ne ko mai kyau. Galibin lokuta har wa yau mukan sanar da
duniya jujjuyawarmu a shafinmu. Wanann
akwai kuskure a ciki, iya gwargwadon matsayinmu a rayuwa. Da yawa cikin ta'addancin da ake aikatawa a
zamanin yau, tsakanin ƙasashen turai da namu, masu yin hakan na samun bayanan
ne ta hanyar Dandalin Facebook.
Daga cikin ƙalubale da ke fuskantar matasanmu
a Dandalin Facebook akwai matsalar yaudara da ƙarya wajen bayyana asali
da tarihi a shafi. Wannan matsala ce mai
girma. Da yawa cikinmu kan rubuta cewa mun yi makaranta a ƙasa kaza, ko mu
mazauna ƙasa kaza ne, alhali wataƙila ko ƙwaryar jiharmu bamu taɓa bari zuwa
wata jiha ba. Wasu kuma mazaje ne, amma
sai su buɗe shafi na musamman da sunan mata, da hotunan mata, har da lambar
waya na bogi. Duk wannan bai kamaci
mutum natsattse mai dattako ba. Su ma
'yan mata suna da nasu. Yaudara cikin
zance da yaudara cikin hotuna. Wasu kan
loda hotuna masu motsa tsimin namiji, don su ji me za a ce. Duk wannan bai kamata ba. Manyan dalilan da ke haddasa su su ne:
sakakkiyar 'yanci, da rashin tarbiyya, da yawan ruɗuwa da ƙyale-ƙyale, da kuma
rigima wajen latse-latse. Da yawa cikin
mutane a wasu ƙasashe sun rasa rayuwarsu, wasu sun rasa dukiyarsu, wasu sun
rasa mutumci da darajarsu, wasu kujeru da mulkinsu, duk ta sanadiyyar
latse-latse marasa kan-gado a shafin Facebook. Waɗannan kaɗan ne daga cikin ƙalubale da ke
fuskantar matasanmu kan abin da ya shafi mu'amala da juna a Dandalin Facebook.
Hanyoyin Gyara
Ga dukkan alamu wannan tsari na rayuwa a
Dandalin Abota dake Intanet wani abu ne da ya zo, kuma akwai tabbacin ya samu gindin
zama musamman a zukatan matasa. In kuwa
haka ne, to dole a kullum a nemi hanyoyin gyara cikin tafiyar, tunda tafiya ce
doguwa. Bayan doguwar nazari da bincike
kan irin nau'ukan wauta, da sakaci, da ganganci, da gidadanci, da tumasanci, da
ƙauyanci da ke faruwa a Dandalin Facebook, tashar talabijin hukumar
Kanada mai suna CBC, cikin wani shirinta na musamman mai take: Facebook
Follies, ta nemi shawarar Mista Graham Cluly, ɗaya daga cikin manyan ma'aIkatan
kamfanin SOPHOS, kuma shahararre a hanyoyin kariyar bayanai da tsarin
sadarwa a kwamfuta da Intanet, dangane da hanyoyin da jama'a za su bi wajen
samun natsuwa a Dandalin Facebook, sai ya fara da cewa: "Facebook
ba kyauta bane, domin sun fi ka riba ma, duk da cewa kana ganin kyauta kake
komai a ciki, ba ka biyan kuɗi. To, amma
ya kamata mutane su san cewa, duk abin da ka latsa a shafin Facebook, ko
ka rubuta a shafinka ko a shafin wani, ko ka "so" (like), ko duk wani
hoto da ka loda ko bidiyo, duk kuɗi ne a gare su. A taƙaice ma dai, kai ne hajar da masu shafin
Facebook ke tallatawa."
Graham Cluly ya ci gaba da cewa: "Ya
kamata kuma mu san cewa, duk abin da ka rubuta shi a shafin Facebook, ko
wani hoto da ka loda a shafin, to, ka rasa shi kenan har abada. Domin ba ka da wani iko a kansa. Wani na iya ɗaukawa
yayi duk abin da yake so a kai." Abin da wannan batu ke nufi shi ne, in dai
kana da wani abu da ka san sirri ne na rayuwarka; hoto ne, bayanai ne, ƙasida
ce, bidiyo ne, sauti ne, to kada ka loda a shafin Intanet. Domin kamar ka kai kasuwa ne ka ajiye, duk
wanda ya masa, zai iya tayawa. Shi yasa
a gaba Cluly ya ci gada da cewa: "Muddin ka san ba za ka iya zuwa tsakiyar
kasuwar garinku ka ɗaga murya kana gaya wa jama'a sirrin rayuwarka ba, to ko kaɗan
kada ka rubuta ko loda su a shafin Facebook. Duk abin da ka san ba ka son kowa ya sani,
kada ka rubuta shi a shafin Facebook." Wannan saƙon a fili yake, ba ya buƙatar
sharhi.
Dangane da abin da ya shafi yin amfani da
shafin Facebook wajen aikata miyagun ayyuka da laifuka kuwa, Graham Cluly yace:
"Dandalin Facebook ne shafin miyagun laifuka da ayyukan yanar gizo
da yafi saurin haɓaka a duniya yanzu.
Akwai satar bayanan sirri, da yaɗa ƙwayoyin cutar kwamfuta, da aikata
miyagun ayyuka da laifuka da ake yi a Dandalin Facebook fiye da kowane
irin shafi a duniya. Idan kana son zuwa
babbar matattarar 'yan ta'addar yanar sadarwar duniya a yanzu, to ka je Dandalin
Facebook." Wani mai sharhi kan
harkokin sadarwar Intanet ya sanar da Umar Shehu 'Yan Leman, wakilin BBC Hausa
dake Legas, cewa: "Mu'amala a shafin Facebook lalube a cikin duhu.
Baka san abu ba bai sanka ba. Ba ka
ganshi ba bai ganka ba." Wannan shi
ne haƙiƙanin gaskiya wanda babu tantama
a cikinsa.
Kammalawa
A ƙarshe, rayuwar matasanmu a Dandalin Facebook
abu ne da yazo, kuma za a ɗauki tsawon lokaci yana tare damu. Abin da ya rage kawai shi ne neman hanyoyin gyara
ɗabi'u, da tarbiyyan kai, da manufa ƙaƙƙarfa, da kiyaye sirri, da kaffa-kaffa
da miyagun abokai, da kamewa daga sha'awa mara kangado, da kuma tsantsene. Waɗannan su ne manyan guzurori da suka kamata
duk wani mai shawagi a duniyar Intanet na zamanin yau ya riƙe su, don samun isa
masauƙi lafiya lau. Allah Ya mana
jagora, amin.