Kandagarki
Bari mu fara da yin kandagarki, kada mai karatu yace “me ya hada harkan Intanet da babban kundin mazhaban Malikiyya kuma?”. To ba nan muka dosa ba a wannan mako. Makalarmu na wannan mako zata ilimantar da mai karatu ne yadda zai zama daya daga cikin masu zuba bayanai a saman giza-gizan sadarwa ta Intanet, wani ya karanta, maimakon karanta bayanan wasu da yake yi a kullum, wajen sanin halin da duniya ke ciki ko karuwa da wani ilimi da bashi dashi. Wannan hanya kuwa ita ce ta hanyar Mudawwana, kamar yadda Larabawan zamani masana fasahar Intanet ke kiranta yanzu, ko kace Web Log, ko Blog, a turance.
Ma’ana:
Kalmar Web Log ko Blog a farkon al’amari, na nufin kundin sirri na Intanet (Internet Diary/Journal). Gidan Yanan Sadarwa ne wanda mai shi ke rubuta batutuwan da suka shafe a bisa karankansa, ko wani nashi, ko kasarsa, ko al’ummarsa, ko addininsa. A takaice dai, idan ka shiga Blog, babu abinda zaka yi ta cin karo dasu sai batutuwan da suka shafi mai shi. Don haka muka yi ta’arifinsa da “Kundin Sirri”, ko “Diary” kamar yadda masana harkan Intanet ke masa lakabi yanzu. Wasu na budewa ne don bayyana abinda da suke so a rayuwarsu; ko mota, gida, abinci, tufafi da dai sauransu. Wasu kuma ‘yan jaridu ne, masu dawwana irin halin da suka shiga sanadiyyar yanayin aikinsu. Ko kuma masu sharhin halin da duniya ko kasarsu ke ciki. Wasu kuma sukan bude ne don bayyana ma duniya wasu sabbin ci gaban da ake samu a fagen ilimi. Galibin masu wannan zaka samu Malaman Jami’o’I ne da ke kasashen duniya. Ta wannan hanya suke samun ra’ayoyin mutane da ma dalibansu, kan tasiri ko ci gaban da hazakansuke haifarwa. Sai dai a yanzu galibin abubuwan da ake zubawa cikin Blog ya sha banban da sanadiyyar da bayanan da suka gabata. A yanzu zaka samu kamfanoni sun gina Blog don dawwanawa da kuma tallata hajojinsu. Na tabbata hakan na faruwa ne sabod glaibin mutane a yanzu sun gwammace su bude Mudawwana da su gina gidan yanan sadarwa mai zaman kansa. Tunda komai na da asali, ta yaya Mudawwana ta faro ne?
Tarihin Mudawwana
Samun hakikanin asali da lokacin da aka fara gina Mudawwana a giza-gizan sadarwa ta Intanet, abu ne mai wahala. Abinda masana suka tabbatar shine, ta la’akari siga da kuma yanayinsa, Mudawwana ta samo asali daga Majalisun tattaunawa (Mailing Lists), musamman kulallu, wanda Madugu ke da hakkin hana mai shigowa shiga, sai da izni (Moderated Lists). A cikin 1994 ne shahararren dan jaridan nan, Mr. Justin Hall ya fara dawwana bayanansa, da yin sharhi kan harkokin yau da kullum. Yayi shekaru a kalla goma sha hudu yana wannan aiki, kafin Mudawwana ya samu shahara a duniyar gizo. Bayan shi, sai Mr. Jerry Pournelle, wanda shi ma dan Jarida ne, ya bude nasa. Har zuwa shekarar 2000, lokacin da mutane suka gano wannan sassaukar hanya ta yada tunani da ra’ayoyi. Daga nan aka fara samun gidajen yanan sadarwa masu bad a daman bude Mudawwana kyauta, watau Free Blog Hosting Sites. Ganin haka ke da sai mutane, musamman ma dalibai a makarantu, suka fara budewa, suna dawwana ra’ayoyinsu. Wannan ta kai a shekarar 2005, gidan yanan sadarwan mudawwana ta Xanga.com, ta ayyana cewa tana da a kalla kundayen Sirri guda Miliyan ashirin, daga guda dari da ta fara dasu a shekarar 1996. Ana shiga wannan shekara ta 2007, sai Gidan Yanan Matambayi Ba Ya Bata na Mudawwana, watau Technorati.com ta bayyana cewa a halin yanzu ana da a kalla Mudawwana Miliyan Saba’in da Biyar a giza-gizan sadarwa ta duniya. Wannan ke nuna muhimman da mutane suka ba wannan hanya na dawwana bayanai a Intanet. To me yasa haka?
Amfanin Mudawwana
Lallai akwai amfani mai yawa tattare da manhajan mudawwana ta Intanet. Wannan tasa mutane da dama suka kama gina nasu, maimakon su tsaya karanta bayanan wasu kadai. Daga cikin amfanonin da ke ciki, akwai saukin mu’amala, musamman ma da yake an samu manja wacce zata taimaka maka wajen yin rajista da kuma gina irin kundin da kake so, mai launin da kake so a irin yanayin da kake so. Akwai fadin albarkacin baki ba tare da tsangwama ba. Galibin yan jaridu zaka samu sun bude mudawwana don yin sharhi kan al’amuran yau da gobe. Har wa yau, galibin mudawwana kyauta ake bude su; zaka yi rajista kyauta, ka zabi adireshin da kake so kyauta, sannan ka rinka aikawa da bayanai ko sakonnin da kake so kyauta! Sannan a yayin da kake zuba naka bayanai, akwai kafar da masu karatu zasu iya yin sharhi kan abinda ka rubuta. Nan ma wata dama ta wasa kwakwalwa ko karuwa da abinda wani zai fada wanda baka sani ba. Sannan zaka iya zuba tsagwaron bayanai (texts), ko hotuna (pictures/images) ko kuma hota mai motsi da ma mara motsi. A takaice dai, maimakon ka zama mai karatu kadai, sai ka zama mai karatu da karantarwa. A yanzu ya kamata mai karatu ya san yadda zai iya bude nasa mudawwanar, ko kuwa?
Ginawa da Tsarawa
Gina mudawwana ko Blog, ba wani abu bane mai wahala. Cikin yan mintuna sai ka gina naka, har ka fara watsa bayanai don wasu su karanta. Da farko dai, akwai gidajen yanan sadarwan da ke taimaka ma mai son budewa yin hakan cikin sauki. Shahararru daga cikinsu sune: Xanga (www.xanga.com), New Blog (http://newblog.com), LiveJournal (www.livejournal.com), Bluekaffe (www.bluekaffe.com), Blogger – na kamfanin Google kenan – (www.blogger.com/start), sai kuma Blog.com (http://blog.com). Dukkan wadannan gidajen yanan sadarwa, zaka iya shiga ka bude mudawwana a ciki. A halin yanzu zamu kawo misali Blogger.com, na kamfanin Google kenan. Da farko dai dole ya zama kana da adireshin Gmail. Idan ba ka dashi, sai kaje http://mail.google.com, ka matsa inda aka rubuta “Sign Up for Gmail”, don yin rajista. Da zaran ka gama, sai ka shiga wannan zauren http://www.blogger.com/start. Ka shigar da suna (username) da kuma kalmar iznin shiga (password) na Gmail da ka bude. Manhajar zata maka jagora har ka gama ginawa da kuma tsara mudawwanarka. Idan kana son shigar da hotuna da sauti, duk akwai bayanai kan haka. A nan ne zaka zabi sunan mudawwanan, da adireshin da kuma sunan da kake so ya rinka bayyana a zauren, a duk lokacin da mai ziyara ya shigo ya gani.
Mu Kewaya Yawo
Kafin mu karkare, yana da kyau mu leka yawo don ganin wasu mudawwanai da aka tsara su musamman cikin harshen Hausa. Da farko dai idan mai karatu bai mance ba, wannan shafi na da mudawwananta da na bude watanni biyu da suka gabata. Ina da kyakkyawan zaton wannan shine mudawwana na farko da aka taba budewa cikin harshe Hausa. Ga adireshinsa nan: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Sai kuma mudawwanar Malam Ibrahim Sheme, mai mujallar Fim. Za a samu wannan mudawwana a http://ibrahim-sheme.blogspot.com. Malam Ibrahim na dawwana ra’ayoyinsa ne cikin harsuna biyu; turancin ingilishi da kuma harshen Hausa. Don haka da zaran ka shiga zaka yi ta cin karo da bayanai kan adabin Hausa da Hausawa da kuma matsalolin Nijeriya. Sunan mudawwanarsa it ace: BAHAUSHE MAI BAN HAUSHI. Sai kuma Mudawwanar wani sha’iri, mai hazaka cikin matasan Kano, watau Malam Muhammad Fatuhu, wanda za a iya samunsa a http://shairai.blogspot.com. A wannan mudawwana, Malamin ya dauki nauyin jero wakokin Hausa ne, wadanda yake rubutawa lokaci-lokaci. Idan kana son karantawa, sai ka shiga don karantawa. Sai kuma mudawwanan Madugu Uban tafiya, watau Farfesa Abdallah Uba Adamu dake Jami’ar Bayero da ke Kano. Za a samu kundinsa a http://arewanci.blogspot.com. Shi kuma ya kebance mudawwanarsa ne da al’adun Hausawa. Akwai kasidu masu matukar amfanarwa. Sai a garzaya don fa’idantuwa da su.
Kammalawa
Daga karshe, yana da kyau mai karatu yayi kokarin bude mudawwana a kalla guda daya, don yada manufofi da hikimar da Allah Ya hore masa. Zaka iya rubutu da kowane irin yare, kamar yadda muka ga samfuri daga mudawwanan da suka gabata. Idan ka cije a hanyarka na gina wannan mudawwana, sai ka tuntubeni ko da a waya ne, zan taimaka gwargwadon fahimta. Allah sa a dace, amin.
Abdallah Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Securities and Exchange Commission
Abuja.
080 34592444 salihuabdu@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com