Friday, November 7, 2008

Wasikun Masu Karatu

Ga wasikun masu karatu nan, tare da amsoshi. Kamar yadda na sha sanarwa, idan akwai bukatar Karin bayanai masu tsawo, a rika rubutowa ne ta Imel, sai in samu damar bayar da gamsassun bayanai kan haka. Muna mika sakon gaisuwarmu ga dukkan masu karatu a ko ina suke, musamman masu bugo waya, wanda adadinsu ba ya kiyastuwa. Kada su ji ba a ambaci janibinsu ba. Mun gode matuka.

Assalam alaikum,
Bayan gaisuwa mai yawa da fatan alhairi, na ga cewa wannan muhimmin shafi namu ya sami cika shekaru biyu, tun daga lokacin da ya fara fitowa. Ina fata Allah ya kara wa marubcin wannan shafi lafiya, don ya ci gaba da ilmantar da mu kamar yadda ya saba. Ita kuma jaridar AMINIYA Allah ya kara bunkasa ta, amin summa amin. -Muhammad Rabiu Isa Ayagi
Kano; 08029157450
rabiuisaayagi@yahoo.com

Malam Rabi’u muna godiya matuka da sakonka, Allah saka da alheri, Ya kuma bar zumunci, amin. - Baban Sadiq

Assalamu alaikum, ina yi maka barka da aiki. Suna na Auwalu Muhammad. Ni ma’abocin karanta jaridar AMINIYA ne duk sati; ba ma kamar shafinka. Dan Allah kaci gaba da yi mana bayani kan wadannan miyagun makamai na Nukiliya. Na gode, sai ka sake ji na. - Auwal Muhammad, 08024898216

Malam Auwal, mun gode sosai, kuma Allah saka da alheri. Zamu ci gaba da bayanai kan makamin nukiliya, musamman ta fannin makamashi. Mun gode.

- Baban Sadiq

Assalam Baban Sadiq, don Allah nawa mutum zai tanada ya bude gidan yanar sadarwa (website)? Sannan mene ne bambancin (da ke tsakanin) Yahoo da MSN?

- Ahmad Muhammad Amoeva, 08066038946

Malam Ahmad, ya danganci kamfani ko wanda zai gina maka gidan yanar sadarwar. Babu wani tabbataccen farashi kan haka. Yahoo! Gidan yanar sadarwar kamfanin Yahoo! Inc. ne, mai manhajar wasikar sadarwa ta Imel – yahoo.com. Shi kuma MSN (Microsoft Network), gidan yanar sadarwar kanfanin Microsoft ne, mai dauke da manhajar wasikar sadarwa ta hotmail. Da fatan ka gamsu. – Baban Sadiq

Salam Baban Sadiq, ina godiya da gaisuwanka; jarabawa ne ya boye ni. Shi yasa kaji ni shiru. Amma na kusa kammalawa. Sai a sanya mu cikin addu’ar samun nasara. – Muntaka, Zaria. 08036397682

Malam Muntaka Allah baka sa’a cikin jarabawanka, ya kuma sa mu dace baki daya, amin. – Baban Sadiq

(Tuna Baya): Salamu alaikum Baban Sadiq, a yi min bayani kan tsohuwar kyamara irin ta da mai hoto baki da fari (black & white); dauka yanzu hoto yanzu. Da kuma irin ta zamani wacce minti daya hoto (one minute picture). Malam, sakamakon kimiyya da fasahar da aka samu yanzu a duniya na kere-kere da kwaskwarimar abubuwa; ga shi waccan ta shude shekaru aru-aru tun hoton iyaye da kakanni da muke gani. Malam, a rika zakulo mana irin wadannan su ma, mu kara karuwa dasu. Allah Ya taimakeka, amin. - Aliyu Mukhtar Sa’id, Kano. 08034332200

Malam Aliyu muna godiya da wadannan shawarwari, kuma kamar yadda na sanar da kai ta text kwanakin baya, ina nan tafe da ire-iren wadannan, ba ma ga na’urar daukan hoto kadai ba, har da sauran kayayyakin fasaha irin na da. Mun gode. – Baban Sadiq

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, Malam yaya kwana biyu? Ina fata kana lafiya. Ina tunanin ko ka mance da tambayata ta kwanakin baya, amma sai ga shi na ga amsar a jarida. Gaskiya nayi murna. Har yanzu kar ka gaji damu; tambaya ta ita ce, kamar yadda ake zama a kalli tashoshin satelait, ana ganin duniya dabam-daban, haka shi ma kwamfuta ko laptop yake? In haka ne, ana biya ko ba a biya? Ina fatan Malam za ka bani amsa. Nine dalibinka, Alhaji Mala. 08033598315

Alhaji barka da hutawa, ina kara godiya da gaisuwarka kamar kullum. Kwamfuta ba kamar tashoshin satelait yake ba; sai idan ka jona shi da Intanet, zaka iya kamo tashoshin da ke gidajen yanar masu tashar, har ka kalli shirye-shiryen da suke yadawa. A nan baza ka biya komai ba, sai dai kawai kaji da kudin jona ka da Intanet da aka yi. Sannan, kwamfuta ana amfani da shi ne wajen rubutu da karatu da kuma adana abubuwa da dama. Ba kallo kadai ake yi da shi ba. Da fatan ka gamsu. - Baban Sadiq

Malam, bayani kan tauraron dan Adam; ainihin tarihinsa tun tali-tali ya zuwa yanzu. Kuma yana da ire-ire ne? Wanne ne karami, kuma wanne ne babba a taurarin? Da kuma sunayensu? Kuma wane irin gudunmuwa yake bayarwa a bangaren kimiyya da fasaha ga ‘yan Adam? Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu, Kano. 08034332200

Malam Aliyu barka da kokari. Na tabbata yanzu kam baka bukatar doguwar amsa, ga kasidu nan mun kwararo. Sai mun samu wasu tambayoyin naka kuma. Na gode. – Baban Sadiq

Malam barka da yamma, yaya kokari? Allah yayi jagora, amin. Malam, mu masu karatun shafinka na Kimiyya da Fasaha a jaridar AMINIYA mai albarka, zamu so mu san alakar da ke tsakanin makamin nukiliya da wutar lantarki. Daga AbdurRahman Sa’ad, Kano. 08038272727

Malam AbdurRahman, kasida ko kasidu kan haka na nan tafe in Allah Ya yarda. Na dan dakata ne don mazayawa zuwa wani fannin kimiyyar. A dakace mu! - - Baban Sadiq

Da fatan ka sha ruwa lafiya. Muna taya ku murnar cika shekara biyu da fara yada shirye-shiryenku a jaridar Amintattu. Daga Sani Abubakar (Na ‘Yankatsare, Jos). 08026023796

Malam Sani muna mika dimbin gaisuwarmu ga dukkan ‘yan makarantarka, Allah bar zumunci amin. - Baban Sadiq

Salam, Malam Abdullahi ina maka fatan alheri. Daga sabon dalibinka, Ashsharir. 08038443566

Malam mun gode da gaisuwa, muna kuma mika tamu fatan alherin zuwa gareka. Allah bar zumunci, amin. – Baban Sadiq

Malam ya ibada? Allah karbi ibadarmu, amin. Ni ma ina taya jaridar jaridu (AMINIYA) murnar cika shekaru biyu, musamman ma wannan shafi mai albarka na kimiyya da fasaha wanda yai daidai da wannan zamani. Malam, kungiyar makarantar jaridar AMINIYA ta jahar Kano nake tambaya? Domin kada ai nisa da darussa ban shiga ba. Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano. 08034332200

Malam Aliyu har wa yau muna kara yabawa da kokarinka. Allah saka da alherinsa, amin. Dangane da abinda ya shafi hadin kan masu karatun AMINIYA a birnin Kano (da gewayenta), kana iya tuntubar Malam Rabi’u Isa Ayagi, akwai lambar wayarsa a wasikar farko da ke sama. – Baban Sadiq

Malam Abdullahi ina fatan kana lafiya. Ni kam wata tambaya zan maka: idan nayi digiri a fannin Kimiyyar Fasahar Sadarwa (Information Technology), zan iya samun aiki dashi a fannin soji a Nijeriya? - 07030875753

Kamar yadda na sanar da kai, kana iya samun aiki a dukkan ma’aikatar da ke mu’amala da kwamfuta a ko ina take a duniya, ba ma Nijeriya kadai ba. Ilimi kan Kimiyyar Fasahar Sadarwa shine ke ci a halin yanzu, kuma duk wani fanni da kake kai, idan ka hada shi da wannan ilimi, sai kayi fice, nesa ba kusa ba. Allah yai mana jagora, amin. – Baban Sadiq

Assalamu alaikum, sakon gaisuwa gareka mai tarin yawa, da fatan kayi sallah lafiya, amin summa amin. Kuma ina addu’ar Allah Ya karbi ibadarmu, amin summa amin. Daga: Rufa’i Ibrahim Danyaro, 08023222864, ibrahimrufai2006@yahoo.com

Malam Rufa’i barka ka dai, kai ma da fatan kayi salla lafiya. Muna kara mika godiyarmu gareka. - Baban Sadiq

Barka da yau Baban Sadiq, da fatan kayi salla lafiya, Allah yasa haka amin. Ni daya ne daga cikin dalibanka daga Niamey a Jamhuriyar Nijer,  na gamu da makarantarka ce a irin yawon da nake a Intanet. Na yi matukar farin ciki da samun wannan makarantar. Za ka rika ganin sakonni na akai-akai, dan neman karin bayani a kan wadansu mas'aloli. Daga: Hamza M. Djibo, Niamey, Nijer. alhamza_mjn@yahoo.fr

Malam Hamza muna godiya da wannan kokari da kayi, kuma Allah saka da alheri da wannan sako naka. Nai matukar farin ciki da ganin daga Jumhuriyar Nijar kake, kuma a ci gaba da ziyartar Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa da ke Intanet, za a rika cin karo da dukkan kasidun da ake bugawa a Jaridar AMINIYA da ke nan Abuja, Nijeriya. Mun gode matuka.    - Baban Sadiq

Tarihi da Nau'ukan Tauraron Dan Adam (3)

Harbawa da Tafiyar da Tauraron Dan Adam

Kera tauraron dan Adam, ba ma harba shi kadai baclip_image002, wata jigila ce ta dimbin kudade da lokaci mai tsawo. Kasancewar wannan fasaha zai je wani muhalli ne bako, mai dauke da kalubale na hakika, hakan ya tilasta wa masu kera shi yin amfani da kayayyaki masu inganci da jure wahala. Bayan kerawa, babbar kalubale da ke tafe ita ce ta cillawa ko harba shi zuwa cikin falaki don gudanar da aiyukansa. Wannan aiki na harbawa, shi ma aiki ne mai bukatar dimbim dukiya da kayan aiki da cikakkiyar nazari. Wannan tasa ba kowace kasa ke gangacin fara kera tauraron dan Adam ba, balle tayi tunanin harba shi, sai kasar da taci ta batse wajen ilimin kimiyyar sararin samaniya, ta kuma tara dimbin dukiya. Dangane da abinda ya shafi harbawa da kuma tafiyar da wannan fasaha zuwa cikin falaki, akwai matakai kamar haka:

Matakan Harba Tauraron Dan Adam

Harba tauraron dan Adam daga wannan duniya tamu zuwa sararinta (atmosphere) har zuwa cikin falakinta, abu ne da ke bukatar makamashin da zai tafiyar da injin roket mai wannan aiki a farkon lamari, ko kuma dukkan wani mashin da zai harba kumbon. Bayan nan kuma, tauraron na bukatar iya kimar nisan da ya dace dashi daga wannan duniya tamu, don gudanar da aikinsa. Mafi karancin nisan da kowane tauraron dan Adam ke bukata daga kasa zuwa muhallin da zai iya gudanar da wani abu, shine kilomita dari biyu daga ganin mai gani zuwa cikin sama. Sannan kuma da kimar gudun tafiya na kilomita dubu ashirin da tara a duk sa’a guda (29,000 km/h), don kai wa cikin falaki. Dole ne kowane tauraron dan Adam ya samu wadannan abubuwa biyu; tarin makamashi (na lantarki ko hasken rana), da kuma karfin da zai tura shi zuwa cikin falaki daga doron kasa, don samun isa ga muhallinsa. Wannan tazara da yake bukata daga doron kasa zuwa cikin sama, shi ake kira altitude a turancin kimiyyar sararin samaniya. Bayan haka, akwai matakai a kalla biyu, da kowane tauraron dan Adam yake wuce su kafin kaiwa ga muhallinsa cikin falaki. Wadannan matakai dole ne ya wuce su muddin za a cilla shi ne ta amfani da roket.

Matakin farko shine tashinsa daga doron kasar wannan duniya zuwa saman sararin samaniyar wannan duniya tamu, watau atmostphere. Wannan matakin shine matakin da ke lazimtar samuwar makamashin lantarki da zai sarrafa roket din da ke tunkuda tauraron zuwa can. A kan sanya tauraron dan Adam din ne cikin wani kumbon harbawa (launch vehicle), sannan a sanya kumbon cikin kwanson roket mai cillawa. Daga nan sai a kunna wannan roket, ya dau zafi, sai ya mike kai tsaye zuwa cikin sama, a guje. Da zarar ya wuce tarin hazo da iskar da ke saman wannan duniya, sai ya yanke daga jikin kumbon harbawan, ya fado duniya. Sai kuma mataki na biyu, wanda kumbon da ke dauke da tauraron dan Adam din zai cika. Da zarar roket din ya yanke ya fado kasa, sai kumbon ya cilla cikin falaki, dauke da tauraron dan Adam din. Shi ma wannan kumbo na dauke ne da makamashin lantarkin da zai taimaka masa aiwatar da wannan aiki. Idan aikin tauraron a iya falakin wannan duniya ne, sai kumbon ya cilla shi cikin muhallinsa kai tsaye. Idan kuma tauraron na bukatar zuwa wata duniyar ce don gudanar da aikinsa, misali zuwa cikin falakin duniyar Mirrik (Mars), to daman kowane tauraron dan Adam na dauke ne da injin roket mai taimaka masa gudanar da aiyuka dabam-daban; don haka sai injin roket din ya harba shi zuwa duniyar, wanda mafi karancin tazarar da yake bukata ita ce kilomita dubu talatin da biyar (35,000 km) daga doron wannan kasa. Idan ya isa falakin, sai wannan inji dai har wa yau, ya daidaita masa tsayuwa, don fuskantar jihar da yake bukata a cikin falakin. Yin hakan shi zai sa ya rika shawagi a sifar da’ira, don kewaya duniyar da yake aikinsa cikinta. Wannan shine tsarin harba tauraron dan Adam cikin falaki na farko, mai dauke da wadannan matakai biyu zuwa uku. Har wa yau, hanyar gargajiya kenan, watau wacce aka saba amfani da ita tun tale-tale.

Amma a shekarar 1990, sai kasar Amurka ta kirikiro wani tsari da ya shafi harba taurarin dan Adam zuwa falaki ta yin amfani da jiragen sama masu nisan taku daga doron kasa. Duk da cewa ana amfani ne da jiragen sama, wannan tsari ya kunshi yin amfani kumbon harbawa masu amfani da injin roket. Wadannan kumbon harbawa, watau launch vehicle, su ke cilla taurarin dan Adam din zuwa cikin falaki da zarar jiragen sun wuce dukkan gargada da galof din da ke cikin sararin samaniya. Sai dai kuma ba kowane iri tauraron dan Adam ake iya harbawa ta amfani da wannan tsari ba, sai kanana masu karamin ruwa. Domin jiragen ba wasu manya bane. Don haka duk tauraron da ke da girma basu iya cilla shi zuwa cikin falaki. Amfani wannan tsari shine don rage yawan kudaden da ake kashewa wajen amfani da tsarin roket daga doron kasa don harba tauraron dan Adam zuwa sama. Domin, kamar yadda bayani ya gabata, hakan na bukatar kashe kudade masu dimbin yawa, wanda a tsarin amfani da jiragen sama ba a kashewa. Bayan nan, tsarin amfani da jiragen sama na rage iya matakan da tauraron dan Adam ke bukata, da kuma tarin makamashin da ake Konawa wajen kutsawa da shi cikin gargada da galof din da ke sararin wannan samaniya namu.

Tsari na uku kuma shine ta amfani da Babban Kumbon Tashar Binciken Sararin Samaniya, watau US Space Shuttle, wanda ke can sararin samaniya, don cillawa ko harba tauraron dan Adam, musamman ma manya daga cikinsu. Wannan tasha ta binciken sararin samaniya, kumbo ne mai dauke da kwararru kan kimiyyar sararin samaniya. Wadannan kwararru na iya harba tauraron dan Adam cikin falakinsa daga wannan tasha, kuma su lura da shawaginsa. Yin amfani da wannan tsari na da amfani biyu manya; na farko shine, rage yawan kudaden da ake kashewa wajen amfani da tsarin farko da na biyu da bayaninsu ya gabata, sai kuma dammar lura da tauraron da aka harba – lafiya ya isa ko ba lafiya ba? – wanda yin hakan daga doron kasa ba karamin aiki bane. Yin sa a can, a takaice, shi yafi sauki. Sannan kuma, duk wani tauraron dan Adam day a samu matsala a halin shawaginsa, su wadannan kwararru da ke wannan tasha na iya dauko shi su dawo dashi doron wannan duniya tamu don a gyara shi, idan sun kasa gyara shi a can kenan. Nan ba da dadewa ba, akwai tsarin da ake son fitowa da shi mai suna Single Stage to Orbit, ko ince Tsalle-daya Zuwa Falaki a Hausance. Wannan tsari zai dada rage yawan matakai da kudaden da ake kashewa wajen harba tauraron dan Adam zuwa cikin falaki daga wannan duniya tamu. Tsarin zai tanadi yin amfani ne da wani kumbon harba tauraron dan Adam na musamman, mai sifa da dabi’a irin ta Babban Kumbon Tashar Bincike da ke sararin samaniya, don harbawa da gyatta kowane irin tauraron dan Adam ne, zuwa cikin falaki. Domin da zarar an sanya tauraron dan Adam din cikinsa, wannan kumbon zai yi jigilarsa, ya tsunduma shi cikin falaki da taku guda, ba sai an ta amfani da matakan da suka gabata ba a baya. Wannan tsari zai rage yawan kudade da makamashin da ake kashewa wajen harba tauraron dan Adam, nesa ba kusa ba.

Tsarin Tafiyar da Tauraron dan Adam

Bayan tauraron dan Adam ya samu kansa a cikin falaki, ba abinda zai ta yi sai shawagi don gudanar da aikinsa, sai in matsala ya samu. Tsarin tafiyar da tauraron dan Adam a cikin falaki yana bukatar abubuwa kamar haka:

Wutar Lantarki

Kowane tauraron dan Adam akan kera shi ne tare da makamashin da zai rika gudanar da rayuwarsa da shi. Don haka a yayin da kumbun harbawa ya harba zuwa cikin falaki, da makamashinsa ya tafi. Hanyar samun makamashin kowane tauraron dan Adam ya kasu kashi biyu ne; akwai makamashi na farko wanda yake a siffar batir ne. Wannan batir shi ke samar da wutar lantarkin da ke tafiyar da injin roken din da yake dauke da shi. Galibin amfanin wannan batir cikin dare ne, ko lokacin da babu hasken rana, musamman da yamma. Amma da zarar rana ta hasko, akwai wasu fika-fikai da aka kera masa; hagu da dama, masu dauke da faya-fayan taskance makamashin hasken rana (sola radiation panels), suna sarrafa injin. Wannan shine hanyar samar da makamashi na biyu. Da wadannan hanyoyi kowane tauraron dan Adam ke rayuwar da yake yi a sararin samaniya. Kowane tauraron dan Adam akan kera masa batirinsa ne iya gwargwadon girma da kuma dadewansa yana shawagi a cikin falaki. Haka ma faya-fayan da ke taskance masa makamashin hasken rana, dole su zama manya masu fadi. Misali, tauraron dan Adam mai suna The Hubble Space Telescope, mai dauke da na’urar hangen nesa da bayaninsa ya gabata a makon jiya, yana dauke ne da fankacecen faifan taskance hasken rana wanda fadinsa ya kai murabba’in mita 290 (290 sq m), kuma yana taskance hasken rana da kimarsa ya kai watt dubu biyar da dari biyar (5,500 watts). Wadannan fika-fikai na budewa ne da zarar kumbon harba tauraron ya cilla shi cikin falaki, sai su bude, don fara gudanar da aiyukansu. Wutar lantarki, wanda ke samuwa ta hanyar makamashin da ke batir ko na hasken rana, shine abu na farko kuma mafi muhimmanci da kowane tauraron dan Adam ke bukata. Sai abu na gaba.

Yanayin Shawagi

A yayin da tauraron dan Adam ya samu kansa cikin falaki, dole yana da jiha ta musamman, ko yanayi na musamman da yake kasancewa cikinsa. Wannan yanayi shi ake kira Satellite Orientation. Da zarar ya fara shawagi, yakan bude fuka-fukansa ne suna fuskantar rana (don taskance masa makamashin da yake bukata), sannan ya juya na’urorin daukan bayanansa (Antennas and sensors) zuwa jihar wannan duniya tamu, ko kuma dukkan abinda aka harba shi don yin nazarinsa. Idan tauraron sadarwa ne (communication satellite), sai ya fuskantar da na’urar daukan bayanansa zuwa wannan duniya; idan na lura da yanayi ne, zai fuskantar da kemararsa ne shi ma zuwa wannan duniya tamu; amma idan tauraron binciken sararin samaniya ne, zai fuskantar da na’urar hangen nesansa ne zuwa halitta ko duniyar da aka aike shi yin nazarinta. Har way au, kowane tauraron dan Adam na dauke ne da inji na musamman, wanda ke taimaka masa tabbatuwa a jiha ko yanayin da zai taimaka masa yin aikinsa.

Yanayin Muhallin Shawaginsa

Kamar yadda bayanai suka gaba a fakon wannan silsila, taurarin dan Adam na fuskantar kalu-bale iri-iri a yayin da suke shawagi a cikin falakinsu. Wannan dole ne ya faru, domin da farko dai, an kera su ne wasu maddodi (karafa ko gilasai) wadanda ba za su iya jure wa muhallin da aka jefa su ciki ba. Sannan, idan ma suna iya jurewa, na dan wani lokaci ne, dole wata rana na zuwa da zasu kode, har su rasa ingancin da zai basu damar jure wa muhallin da suke cikinsa. Idan aka cilla tauraron dan Adam cikin falaki, kalu-bale na farko da zai fara karo dashi shine na tsananin zafin rana, wacce ke haskowa, tare da darkake shi babu kakkautawa. A cikin falaki, tauraron dan Adam ba shi da inuwar da zai iya fakewa don shan inuwa. Bayan nan, shi kanshi tauraron dan Adam yana dauke ne da wasu injina na roket, masu haddasa masa tsananin zafi. Abin da ke taimaka masa kawai shine, an yi masa wani inji da ke sanya shi mazayawa lokaci-lokaci, don baza zafin da tururin da ke damfare dashi, ta hanyar jujjuyawa. Wanda in da a wuri guda yake tabbace a kullum, zafin na iya haddasa masa illa mai tsanani. Sannan idan yamma tayi, wata ya hasko, akwai tsananin sanyi da zai sake darkake shi, tare da rage masa inganci. Bayan haka, a can sararin samaniya, ba irin nan duniya ba, akwai iska mai tsananin karfi da ke bugawa babu kakkautawa. Idan da rana ne, wannan iska kan rikide tare da zafin rana; haka idan da dare ne, sai ta rikide tare da sanyin dare. A daya bangaren kuma, akwai taurarin da kwanakinsu yak are, suka farfashe, balgacen su kan warwatsu cikin falaki; wasu su fado cikin duniyarmu, kamar yadda bayanai suka gabata a baya, wasu kuma su ta shawagi a cikin falaki. A yayin shawaginsa, tauraron dan Adam kan ci karo dasu, har su kwakkwafe shi, ko su babbale masa fuka-fukansa, ko kuma su haddasa masa wata illa babba da ka iya hana shi ci gaba da aiyukansa.

Yanayin Shigowa Duniya

Dangane da yanayin rayuwa da yin zamani a cikin falaki, tauraron dan Adam ya kasu kashi uku; akwai wadanda ke yin shawaginsu har su gaba ba tare da samun wata matsala ba. Idan suka gama rayuwa da shekaru ko muddar da aka yanke musu, sai su nemi hanyar shigowa duniya da kansu. Da zarar sun kutso sararin samaniya (earth’s atmosphere), sai su kone gaba daya. Idan kuma rayuwarsu bata kare ba, amma akwai na’urorin da ake son cirewa daga garesu don sarrafawa, sai ayi amfani da kwarewa ta kimiyya, a harbe injin da ke sarrafa tauraron, nan take sai ya rage gudunsa, ya fara saukowa cikin duniya da kansa, har a riske shi. sai kashi na uku, wadanda injinsu ko wasu sassansu masu muhimmanci ke lalacewa, su daina aiki, kawai sai tauraron ya “haukace”, yayi ta shawagi ba-kai-ba-gindi, cikin falaki. Wadannan su ake kira space junk, watau sun zama sharan cikin falaki kenan. Haka za su yi ta kai-komo har su kone.

Sannan, iya girma da rashin nauyin tauraro, iya saukin da zai samu wajen shigowa duniya; iya gajarta da nauyinsa, iya wahalar da zai sha wajen shigowa, saboda tasiri da karfin iska da ke janyo jiki zuwa kasa. Iya nisan tauraro da duniya, iya yawan shekaru ko lokacin da zai iya daukawa yana shawagi. Taurarin da ke shawagi a falakin da bai wuce nisan kilomita dari biyu ba, basu wuce mako guda zuwa watanni uku suna shawagi a ciki. Wadanda ke iya nisan kilomita dari uku kuma, suna iya yin shekaru biyu ko fiye da haka. Idan tauraro ya kai nisan kilomita dubu daya kuma, yana iya shawagi a cikin falaki na tsawon shekara dubu ko fiye da haka. To ko ma dai a ina yake, da zarar kwanakinsa sun kare, dole ya nufo gida. In ya iso lafiya alhamdulillahi. Idan kuma kwanaki sun kare, sai kone a yayin shigowarsa, ko wasu sassansa su daina aiki sanadiyyar dimbin kalu-balen da ke samunsa a can, har ya zama shara, wacce iskar falaki ke dibansa na iya wani zamani, kafin ya kwanta dama.

Wannan shine dan abinda ya samu, kan abinda ya shafi bincike kan tauraron dan Adam ya tsarin tafiyar da aiyukansa. Abubuwa ne masu ban mamaki, kamar yadda mai karatu ya ji kuma ya karanta. Amma abinda ya fi komai mamaki shine, wanda ya halicci mai wannan tunani, watau Allah. Idan wannan bayani ya bamu mamaki, to mu san cewa ikon Allah shi yafi komai zama abin al’ajabi. Don shine wanda ya halicci dan Adam din da yayi tunanin kirkiran dukkan wadannan abubuwa da bayanansu ya gabata, da kuma halittun da ake gudanar da binciken kansu. Idan muka dubi hatta wadannan taurarin dan Adam din, sai mu ga ai kwaikwayon halittar Ubangiji aka yi, don samun ci gaba. Allah Yai mana afuwa, Ya kuma sa mu dace, amin.