Saturday, December 4, 2010

Tsarin Amfani da Wayar “Blackberry”

Tsarin Amfani da Waya Nau’in Blackberry

Daga cikin wayoyin salula na zamani masu tashe a yau, akwai wayoyi nau’in Blackberry da ake amfani da su. Wayoyin salula nau’in Blackberry suna kan yaduwa a duniya a halin yanzu. Kuma duk da cewa wayoyi ne na alfarma, kuma masu tsada da ba kowa bane ke iya mallakarsu, shafin Kimiyya da Kere-kere ya ga dacewar gabatar da ‘yan takaitattun bayanai ga masu karatu don fahimtar yadda tsari da kintsinsu yake. Har wa yau, na tabbata da yawa cikinmu mun samu labarin cewa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe wasu daga cikin hanyoyin amfani da wannan waya mai matukar tasiri sanadiyyar wasu dalilai. To me ya kawo haka? Kuma wani irin tsari ne wannan nau’in wayar salula ke da shi da har zai sa wata kasa ta dauki mataki makamancin wannan? Duk wadannan na cikin abubuwan da za mu karanta cikin wannan mako da makon da ke tafe in Allah Ya yarda. Da farko dai, ga bayani nan kan ma’ana da samuwar wannan waya ta Blackberry.

Ma’ana da Asali

Kalmar Blackberry, a turancin Kimiyyar Sadarwa ta Zamani a yau, na ishara ne zuwa ga wani jerin wayoyin salula na musamman nau’in Smartphone, masu dauke da masarrafar Imel da kamfanin Research in Motion (RIM) na kasar Kanada yake kerawa. Wannan waya ta Blackberry na dauke ne da masarrafai na musamman da ake amfani da su ta hanyoyi na musamman, kuma a wani irin yanayi da ya sha bamban da sauran hanyoyin sadarwa. Wasu cikin wadannan masarrafai dai sun hada da masarrafar Imel mai zaman kanta, watau Mobile E-mail, da manhajar kalanda, da masarrafar taskance bayanai, da masarrafar allon rubutu na kamfanin Microsoft – irinsu Microsoft Word, da Excel – da taskar adireshi, da manhajar mu’amala da tsarin sadarwa ta wayar iska, watau Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), da masarrafar sauraro da shan kida, da rariyoyin saduwa da Dandalin Facebook, da MySpace, da na Twitter. Har wa yau akwai masarrafar gano bigire, watau Geographical Positioning System (GPS), da manyan ka’idojin da ke tafiyar da manhajar Imel: Post Office Protocol (POP) da Internet Message Application Protocol (IMAP), sai kuma manhajar hirar ga-ni-ga-ka, watau Instant Chat Messenger, mai taimakawa wajen gudanar da hira tsakanin mai wayar da duk wanda ke giza-gizan sadarwa ta duniya, irinsu Yahoo Messenger, da Windows Live Messenger, da ICQ, da Google Live Talk da dai sauransu.

Wannan waya ta musamman mai suna Blackberry, kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada ne ya fara kera su cikin shekarar 1999. Zubin farko da kamfanin ya fara kerawa dai su ne nau’in Blackberry Pearl, kuma shafukansu launin fari da baki ne, babu wasu kaloli daban, watau Monochrome kenan. Cikin shekarar 2002 ne ya fara kera na zamani masu dauke da manhajoji masu kayatarwa. Kuma a haka kamfanin yake tafiya har zuwa yau; inda yake ta kera wasu nau’ukan daban masu dauke da abubuwa da dama. A kididdigar da masana kuma masu lura da tsari da tasirin tsarin sadarwa ta wayar salula a duniya suka bayar, bayan wayoyin salula masu dauke da manhajar Symbian OS da kamfanin Nokia ke kerawa, babu wata wayar salula da ta fi samun kasuwa a duniya irin Blackberry.

Manufa

Sabanin sauran wayoyin salula wadanda tun asali an kera su ne don aiwatar da sadarwar murya musamman (Voice Communication), su wayoyin salula nau’in Blackberry an samar ko kera su ne musamman don sawwake ayyukan ofis, da kamfanoni, da kuma mu’amala da fasahar Intanet dare da rana safe da yamma. Wannan kuwa a fili yake, musamman idan mai karatu yayi la’akari da irin manhajoji da kuma masarrafan da wayar ke dauke da su.

Idan kana dauke da waya nau’in Blackberry, wacce ke hade babu kwange tare da ita, to sadarwa a gare ka ba wata matsala bace. A kowane lokaci tana jone ne ta giza-gizan sadarwa ta duniya, watau Intanet. Kana iya karba da aika sakonnin Imel a duk sa’adda ka ga dama. Kana iya hira da duk wanda kake so a duniya muddin a jone yake da Intanet. Kai a takaice ma dai, kana iya tafiyar da ayyukan kamfaninka ko hukumar da kake wa aiki a duk inda kake. Da wannan nau’in wayar salula, ana gudanar da harkar kasuwanci, da shugabanci, da siyasa, da addini, da duk abin da ya shafi zamantakewa. Kana zaune a gidanka ne, ko a cikin jirgi kake, ko a cikin mota, ko kwance kake, ko a kasuwa kake, ko a maraya kake, ko kuma a karkara; duk ba ka da matsala. Bayan haka, wannan waya ce da idan ka caja batirinta, kana iya kwanaki masu tsawo baka bukaci na’urar caji ba. Domin dukkan manhajojin da ke cikinta ba su cin makamashi fiye da kima, balle har kuzarin batirinka ya gaza nan take. A halin yanzu wannan waya na sahun kayayyakin sadarwa na tafi-da-gidanka masu canza tsarin rayuwa a duniya, watau Convergent Devices.

Babbar Manhaja

Kamar yadda masu karatu suka sha karantawa a wannan shafi, kowace wayar salula na dauke ne da bangarori guda biyu; da bangaren gangar jiki, da kuma ruhi. Bangaren ruhi ne muke wa lakabi da “manhaja”. Domin manhajar ce ke tafiyar da wayar; daga kunnawa har zuwa kashewa – idan babu manhaja a tare da ita, to gwamma a jefar a bola, watakila yara su tsinta su rika wasa da ita. To, wayoyin salula nau’in Blackberry na dauke ne da babbar manhaja (watau Operating System) mai suna Blackberry OS 6.0. Wannan shi ne zubin manhajar na zamani. Wannan babbar manhaja tana da kuzari matuka, kuma idan kana da Blackberry tsohuwar yayi wacce ke dauke da babbar manhajar baya, kana iya kara mata kuzari (watau Software Update) ta hanyar zuwa shafin kamfanin ta Intanet daga wayar, ko kuma ka yi amfani da manhajar shigar da masarrafai ta kwamfuta, watau Blackberry Desktop Manager wajen yin hakan.

Bayan babbar manhaja, kowace wayar salula nau’in Blackberry na gudanuwa ne a saman masarrafar tafiyar da ruhin waya nau’in ARM. Nau’in Blackberry na farko sun yi amfani ne da Intel-80386. Daga baya kuma sa’adda kamfanin ya tashi kera Blackberry zubin 8000 Series, sai yayi amfani da nau’in ARM XScale 624MHz, in ka kebe zubin Blackberry 8707 wacce aka dora ta a saman nau’in Qualcomm 3250. Wannan mizani ne na tsarin sadarwa mai taimaka wa injin kwamfuta ko wayar salula sauri da gaugawar karba da aiwatar da umarnin da aka ba ta, kuma shi ake kira Processor a turancin kimiyyar sadarwar kwamfuta.

Tsarin Amfani da Wayar Blackberry

Ana iya amfani da wayar Blackberry ta hanyoyi uku. Hanyar farko ita ce, ka sayi wayar a kasuwa, ka sanya katin SIM dinka a ciki, sai kawai ka ci gaba da amfani da ita kamar sauran wayoyi. A wannan tsari, za ka iya yin kira, kuma a kira ka; ka yi tes, kuma a aiko maka. A takaice dai, za ka rika amfani da tsarin sadarwar kamfanin da ka sanya katinsu. Amma ba za ka iya amfana da galibin masarrafai da manhajojin da wayar ke dauke da su ba. Hanya ta biyu kuma kana iya saya, ko kaje daya daga cikin kamfanonin waya da muke da su a Nijeriya ka saya (kowanne cikin kamfanonin waya da muke da su a kasar nan suna sayar da wannan waya), sannan ka bukaci su farkar maka da ita, watau Activation kenan. Kowace waya nau’in Blackberry na zuwa ne da kalmomin iznin shiga (Pin Cord) guda takwas, kuma da su ake amfani wajen gabatar da abubuwa da dama a wayar. Kamfanin zai bukaci wadannan kalmomi a gidan yanar sadarwarsa, ko kuma a lokacin da kaje, don su shigar da wayarka cikin babbar manhajar sadarwarsu, kafin ka fara amfana da tsarin Intanet da na Imel da wayar ke dauke da su. Wannan tsari na biyu shi ake kira Blackberry Internet Service (BIS). Kamfanonin wayar kasar nan na da wannan tsari, kuma idan ka shiga, a kullum za ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, da manhajar Imel, da kuma hanyar hirar ga-ni-ga-ka. Duk lokacin da ka samu sako a akwatin Imel dinka, nan take wayar za ta sanar da kai cewa sakon Imel ya shigo; kamar dai yadda wayarka ke sanar da kai idan ka samu sakon tes. Sai dai kuma, dangane da tsarin biya da ke tsakaninka da kamfanin, duk wata za ka rika biyan kudin hanya, ko dai kafin wata ya kama, ko kuma bayan ya kare. In kuwa ba haka ba, to ba ka da sabis.

Sai tsari na uku, wanda kamfanoni ne ke amfani da shi, kuma ya kunshi jona wayar da wata manhaja ta musamman mai suna Blackberry Enterprise Server (watau BES). Wannan manhaja za a sanya ta ne cikin kwamfuta ta musamman a ofishin kamfanin, sannan a hada ta da tauraron dan Adam, wanda zai rika aiwatar da sadarwa ta wayar iska tsakaninsa da dukkan ma’aikacin kamfanin da ke dauke da wayar, da Cibiyar Bayanai (Network Operations Center – NOC) da ke kamfanin Research in Motion a can kasar Kanada, da kuma kamfanin sadarwar da wayoyin ke amfani da katin SIM dinsa. Wannan tsari yana da tsada sosai, amma ba abin da ya fi shi kayatarwa wajen sadarwa. Shi ma, kamar tsarin da ya gabace shi, dukkan kamfanonin sadarwar wayar salula da ke kasar nan na iya aiwatar da shi. Bari mu dan kara bayani kan yadda wannan tsari na BES ke gudanuwa.

Mu kaddara Malam Jatau na da kamfani mai dauke da ma’aikata 30, kuma yana son a dukkan lokuta kowane ma’aikaci na bakin aikinsa; a gida yake, ko ofis, a gari yake, ko a halin tafiya. Sai ya je kamfanin MTN misali (kamfanin Zain da Etisalat da Glo ku yi hakuri, misali nake bayarwa) ya bukaci wannan tsari. Kamfanin MTN zai baiwa kowane ma’aikaci wayar Blackberry ne guda daya, mai dauke da katin SIM din kamfanin, wanda kuma aka jona shi da babbar cibiyar sadarwar kamfanin. Sannan sai ya je inda ofishin kamfanin Malam Jatau yake, don sanya wannan manhaja ta Blackberry Enterprise Server a Uwar Garken (Network Server) da ke ofishin. Sannan ya jona dukkan na’urorin da za su hada alaka a tsakanin babbar cibiyar sadarwarsa ta waya, da wayyoin salular da ya baiwa wadancan ma’aikata, da kuma babbar cibiyar taskance bayanai ta kamfanin Research in Motion da ke can kasar Kanada. Da zarar yayi haka, an gama komai. Da wannan tsari, kowanne cikin ma’aikatan nan zai iya aiko sakon Imel cikin gaugawa zuwa ofis, don sanar da ofis halin da yake ciki kan aikin da aka tura shi. Haka za a iya aika masa da sakon Imel ta gaugawa. Haka za a iya hira da shi a tsarin hirar ga-ni-ga-ka, watau Intstant Messenger. Idan kamfanin ya bayar da lambar wayarsa ne ga masu hulda da kamfanin, to duk sa’adda suka aiko sakon tes, ko na Imel, kai tsaye zai wuce zuwa wayarsa, inda wayar za ta sanar da shi cewa sako ya iso. Idan yana bukatar karantawa, ba ya bukatar sai ya bude wayar; akwai alamar da aka tanada masa a jikin wayar wacce zai matsa, sai kawai sakon ya budo.

Dukkan sakonnin bayanai – irinsu tes, da Imel, da rubutattun sakonnin hirar ga-ni-ga-ka – suna bin hanyoyi uku ne ko hudu, kafin su isa inda aka aike su, a wannan tsari na BES. Idan aka aika wa wani ma’aikaci sakon Imel misali, sakon za ta zarce ne kai tsaye zuwa cikin wannan babbar manhaja ta BES da ke kamfanin, wacce a dakace take tana jiran sakonni masu shigowa. Da zarar ta kalli sakon da ya shigo, sai ta cilla wa wancan babbar cibiyar bayanai na kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada. Wancan cibiya da ke kasar Kanada kuma sai ta cilla wa cibiyar sadarwar kamfanin MTN, wacce mai’aikacin ke dauke da katin SIM din kamfaninta. Da zarar sakon ya iso kamfanin MTN, sai ita kuma ta aika wa ma’aikacin cikin wayarsa. Duk wannan zai faru ne cikin kankanin lokaci, sanadiyyar tasirin kayayyaki da hanyoyin sadarwa ta wayar iska. Sakon na shigowa wayar za ta sanar da shi nan take. Wannan shi ne yadda ake gudanar da sadarwa a tsakanin manhajar BES da kuma wayar Blackberry.

Zubin Wayoyin Blackberry

Akwai wayoyin Blackberry da dama da aka kera su a yanayi da kintsi daban-daban. Kashin farko su ne wadanda aka kera cikin shekarar 1999, wadanda kuma galibinsu duk ba su da wasu launukan da suka wuce fari da baki (watau monochrome, ko kuma black and white). Daga shekarar 2006 zuwa 2008 sai kamfanin ya samar da zubin da yayi wa lakabi da Blackberry Pearls. Kafin shekarar 2008 ta kare, sai kamfanin ya samar da wasu zubin masu suna Blackberry Curve, kuma irinsu yayi ta kerawa har sai da shekarar 2009 ta kare. A karshen shekarar kuma sai ya kirkiri zubin Blackberry Storm, wadanda yayi ta kerawa har cikin shekarar 2010. Daga farkon shekarar 2010 kuma zuwa tsakiyar shekarar, kamfanin Research in Motion ya sake kera wasu nau’uka da sake sanya musu sunan Blackberry pearls, da Blackberry Curve. Dukkan wadannan zube-zube na nau’in Blackberry suna dauke ne da adadin 7000, da 8000, da kuma 9000 series, kamar yadda ake kiransu a jumlace. Wayar Blackberry ta baya-bayan nan da kamfanin ya kera ita ce nau’in Blackberry 9300.

Wayoyin Salula Masu Kama da Blackberry

Akwai wasu cikin wayoyin salula na zamani da aka kera su dauke da masarrafar Imel ta musamman da wayar Blackberry ke dauke da ita, watau Blackberry Email Client. Wannan ke sa su sifatu da wata dabi’a ko yanayi irin na Blackberry, to amma fa, kama da wane ba ta wane, ko kadan. Zan so mai karatu ya samu sunayensu, domin idan mun kasa mallakar wayar Blackberry, to mu san cewa akwai wasu nau’uka da za mu iya mallaka don huce fushin rashinta. Tabbas Blackberry waya ce abin alfahari da morewa, to amma Allah bai yi yatsun hannayenmu iri daya, balle zanen da ke tafukan hannunmu su dace.

Wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel irin na Blackberry dai su ne: AT&T Tilt, da HTC Advantage X7500, da HTC TyTN, da Motorola MPx220, da Nokia 6810, da 6820, da 9300, da 9300i, da kuma 9500. Cikin jerin wayoyin har wa yau akwai dukkan ayarin wayoyin Nokia zubin E-series (ban da E71 da E66), sai kuma Qtek 9100, da Qtek 9000, da Samsung E719, da Siemens SK65, da SonyEricsson P910, da P99, da M600i, da kuma P1. Wadannan, a halin yanzu, su ne nau’ukan wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel na wayar Blackberry, watau Blackberry Email Client. Ba mu san abin da gobe zai haifar ba.

Tasirin Amfani da Blackberry a Duniya

Ko shakka babu amfani da wayar salula nau’in Blackberry yana tasiri sosai wajen aiwatar da sadarwa a yanayi kayatacce kuma mai gamsarwa. Musamman ganin cewa kamfanoni da hukumomi da daidaikun mutane sun rajja’a wajen amfani da wannan waya. Dalilan hakan dai ba nesa suke ba. Da farko, bayan yawaitan hanyoyi da manhajoji ko masarrafan sadarwa da wayar ke dauke da su, akwai kuma ingancin tsaro wajen sadarwa, wanda shi ne abin da galibin kamfanoni ke bukata. A tsarin aikawa da sakonni ta Blackberry, da zarar ka rubuta sako ka aika, nan take za a narkar da sakon don kariya, har sai ya isa inda aka aike shi. Wannan ta sa wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya suka fara damuwa da wannan tsari na boyewa tare da narkar da bayanai ta yadda babu na’ura mai iya hangowa balle ta karance su yadda za a fahimci sakon da ke cikinsu. Daga sakon tes, zuwa Imel, har rubutattun sakonnin hira da na murya, duk narkar da su ake yi har sai sun isa inda aka aike su.

Wani abin da ya kara wa wannan tsari wuyan sha’awi ga hukumomi masu son tace bayanai na murya ko rubutattu da ake aikawa a tsakanin kayayyakin sadarwa kuma shi ne, dukkan sakonnin da ake aikawa sai sun dire a Uwar Garken kamfanin da ya kera wayar a can kasar Kanada, sannan su isa muhallin da ake jiran isansu. Shi yasa a ranar 1 ga Augusta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe kafar amfani da tsarin Intanet da Imel da rubutattun hira ta hanyar wayar Blackberry, saboda dalilai na tsaro. A kasar hukuma ta saba tace ire-iren wadannan bayanai daga wayoyin salular da ake amfani da su, don tsaron lafiyar jama’a da ma baki da ke shigi-da-fici a kasar a kullum. To amma saboda tsananin tsaro da wannan waya ta Blackberry ta sifatu da shi, sun kasa samun isa ga ire-iren wadannan bayanai da mutane ke aikawa ta wannan waya. Don haka suka toshe dukkan kafar Intanet da duk wani mai Blackberry zai iya bi ya aika da sako. A halin yanzu idan kana Dubai, sai dai ka kira, ko ka yi tes, amma batun Imel da Intanet kam sai dai ka hakura. Hukuma tace muddin kamfanin bai yi wani hobbasa ba wajen ganin ya warware wannan matsala kafin 11 ga watan Oktoba, to za ta toshe hanyar amfani da wayar ma gaba daya. A halin yanzu akwai wayar salula nau’in Blackberry guda 500,000 da ake amfani da su a kasar.

A kasar Saudiyya ma hukuma ta koka da wannan tsari na mu’amala da wayar Blackberry. Don haka ita ma, daidai lokacin da ake wancan dambarwa a Hadaddiyar Daular Larabawa, ta yi barazanar cewa za ta toshe kafar sadarwar Intanet ga duk mai wannan waya, muddin kamfanin Research in Motion bai yi wani abu ba wajen ganin hukuma ta samu kai wa ga ire-iren bayanan da take so ko ake aikawa. Ai nan take sai kamfanin ya fara shirye-shiryen ganin ya amsa wannan kira. Domin akwai wayoyin Blackberry wajen 700,000 da ake amfani da su a kasar. Ya zuwa yanzu, kamfanin ya fara tattaunawa da hukumar Saudiyya, inda yayi tayin sanya wata Uwar Garke (Network Server) da dukkan sakonnin da masu wayar ke aikawa za su rika bi, gwamnati na tace su, kafin su zarce zuwa ga wadanda aka aika musu su, a kasar suke ko a wajen kasar. Domin kasar Saudiyya da ma galibin kasashen Larabawa duk suna tace tsarin sadarwa da ake gudanarwa ta hanyoyin kayayyakin sadarwa irinsu kwamfuta da wayoyin salula da sauransu. Bayan kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar Indonesiya, da kasar Bahrain, da kasar Indiya, da kasar Aljeriya da kuma kasar Lebanon, duk sun fara tayar da kura kan wannan tsari na rashin iya tace bayanan da wannan waya ta Blackberry ke aikawa, kuma akwai hasashen cewa su ma suna iya cew sai an musu irin abin da ake son yi wa kasar Saudiyya, in kuwa bah aka ba, to duk wani mai wayar Blackberry ya jefar da ita a bola.

Dandalin “Facebook” a Manhagar Masana (4)

Yin Rajista a Dandalin Facebook

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, clip_image002kafin ka fara mu’amala da mutane ko abokananka a Dandalin Facebook, dole kana bukatar yin rajista. Yin rajista babu wahala, kuma kyauta ne. Sai ka je shafin dandalin da ke http://www.facebook.com. Kana shiga shafin, za ka inda aka rubuta “Sign Up – It’s Free, and Always Will Be.” A kasan wannan bayani za ka samu dan karamin fam da za ka cike. Wannan sabon tsari ne da suka bullo da shi don saukaka wa masu son yin rajista. Amma a baya alamar “Sign Up” za ka matsa, sai a kaika inda wannan fam yake. To, da zarar ka gangaron inda wannan fam yake, za ka samu yana dauke ne da wuraren shigar da bayanai guda bakwai, da kuma alamar da za ka matsa don yin rajistar, a can kasa.

Da farko sai ka shigar da sunanka na farko a inda aka rubuta “First Name”, sannan ka shigar da sunan mahaifinka a inda aka ce “Last Name”. Ba dole bane sai ka shigar da “hakikanin sunayen”; idan ka ga dama kana iya amfani da lakabi kadai – misali kace “Baban” a wurin farko, da “Sadiq” a wuri na biyu, duk zai dauka. Daga nan kuma sai ka shigar da adireshin Imel dinka a wurin da aka ce “email” – fasaha2007@yahoo.com, misali. Sai ka kara gangarawa kasa inda aka ce “Re-enter Email”, ka kara shigar da adireshin Imel dinka. Bayan ka shigar a karo na biyu, sai ka sake gangarawa inda aka ce “Password”, ka shigar da kalmomin iznin shiga da kake son tsare shafinka da su. A nan, kirkira za ka yi, wasu kalmomi da suka hada da lambobi ko alamu, daga hudu zuwa goma sha biyu, misali. Bayan ka shigar, sai ka gangara zuwa inda aka rubuta “Sex”, ka zabi jinsinka: “Male”, idan na namiji ne, ko “Female”, idan mace ce. Sai kuma kafa ta karshe, inda za ka shigar da tarihin haihuwarka, watau “Date of Birth”.

A can kasa karshe, sai ka matsa alamar da ta ce: “Sign Up”. Matsa wannan alama ke da wuya, za a budo maka wasu haruffa a sifar alamu, da ake son ka shigar da su cikin wata ‘yar akwati. Wannan shi ake kira “Security Checker”; kuma kariya ne ga shafinka baki daya. Da zarar ka shigar, sai a zarce da kai shafin da ka bude kai tsaye, inda za a baka zabin zaban abokanai, ko shigar da sunayen wasu mutane da ke da alaka da yanayin sunanka ko jinsinka. A daya bangaren kuma, kana iya zarcewa jakar Imel dinka nan take, inda za ka samu sakon Imel da aka aiko maka, ana maka maraba da shigowa Dandalin Facebook. A cikin sakon har wa yau, akwai wata alama da za a umarce ka da matsawa, don karasa rajista. Da zarar ka matsa alamar, nan take za ta zarce da kai shafinka ba tare da bata lokaci ba. Wannan, a takaice, shi ne yadda ake yin rajista a shafi ko Dandalin Facebook. Mai karatu ba ya bukatar wani bayanin da ya wuce wannan. Sauran abubuwan da kanka za ka koyi yadda ake yinsu.

Yaduwar Dandalin Facebook a Duniya

Kamar yadda dukkan masu karatu suka sani, Dandalin Facebook ya shahara a duniya, kamar rana da wata. Dalilan da suka haddasa wannan shahara kuwa ba a nesa suke ba. Na farko dai asalin wannan dandali su ne matasa. Daga matasan da ke jami’a, zuwa ‘yan sakandare, har zuwa kan kananan yara masu sama da shekaru goma sha uku. Wadannan matasa su ne kusan kashi sittin cikin masu rajista a wannan dandali. Galibin ‘yan jami’a duk sun yi rajista; daga samari zuwa ‘yan mata. Kuma su ne masu raya wannan Dandali wajen harkar abota da yada bayanai.

Abu na biyu da ya kara wa wannan dandali shahara shi ne samuwar kafafen yada labarai ta hanyar dandalin. Galibin gidajen yanar sadarwa masu yada labarai ko samar da bayanai, duk suna da shafi a dandalin Facebook. Daga gidajen rediyo irinsu BBC da VOA da Deustchwelle, har zuwa gidajen talabijin irinsu CNN, da sauransu, duk sun mallaki shafuka a wannan dandali. Hakan ya karkato akalar masu karatunsu zuwa shafin ko dandalin Facebook, inda su ma suka mallaki shafuka don samun saukin mu’amala da labaran da suke nema a wadancan shafuka. Haka kuma, kafafen jaridu da mujallu ma sun mallaki shafuka a wannan dandali. Duk samuwar hakan na cikin manyan dalilan da suka kara wa wannan dandali shahara nesa ba kusa ba.

Abu na gaba kuma shi ne samuwar kafofin kasuwanci zuwa wannan muhalli na Facebook. Da farko dai wannan dandali an kirkire shi ne don abota da tattaunawa a tsakanin mutane daga wurare daban-daban. Amma da tafiya ta yi nisa, sai gidajen yanar sadarwa na kamfanonin kasuwanci da ke kasashen Turai da Amurka da Asiya suka fara bude shafuka a dandalin. Bayan su, akwai kamfanonin saye da sayarwa na Intanet da ke saka tallace-tallacen hajojinsu a dandalin. Sannan a karshe, akwai ‘yan kananan shagunan saye da sayarwa a kowane shafi ka bude, watau Market Place. Samuwan wadannan kafofin saye da sayarwa a shafin Facebook na cikin abin da ya dada kara wa shafin shahara.

Dalili na gaba kuma shi ne yaduwan hanyoyin yada ra’ayoyin siyasa musamman. Wannan ya ba da damar yaduwar shafukan yada ra’ayoyin jam’iyyun siyasa daga kasashe daban-daban. A halin yanzu, babu wani shahararren dan siyasa a duniya da bai mallaki shafi a dandanlin Facebook ba. Ko dai ya zama shi ya bude da kansa, ko wasu suka bude da umarninsa, ko kuma, a karo na karshe, ya zama an bude ne don yada ra’ayoyi da manufofinsa na siyasa a dandalin. Daga kan shugabannin Amurka, da na Ingila, zuwa kan sarakunan gargajiya na kasashe daban-daban, duk za ka samu sun mallaki shafuka a Facebook. Ba nan kadai ba, akwai kungiyoyin sa-kai masu kokarin tabbatar da wasu manufofi ko na siyasa, ko na gargajiya, ko kuma na tsarin zamantakewa; su ma suna da shafuka a wannan dandali. Kari a kan haka, akwai kungoyoyin addini – musamman na kirista - a jam’ance ko a daidaikun mutane, duk sun bude shafuka. Wannan tsari shi ma, yana cikin abin da ya kara wa Dandalin Facebook shahara a duniya.

Abu na gaba shi ne samuwar masarrafai masu sawwake mu’amala a dandalin baki daya. Masarrafai, ko kace “applications” a turance, su ne kananan sinadaran da ke baka damar aiwatar da abubuwa da dama; daga shigar hotuna, zuwa karban rokon abotar wasu, har zuwa nemo sunaye ko adireshin wasu, duk da wadannan masarrafai za ka yi. Su ne kayan aiki a dandalin. Su ne kanwa uwar gami. Sannan, kana iya makala alamar shafinka a wani gidan yanar sadarwa ko Mudawwanarka. Bayan haka, kana iya amfani da wadannan masarrafai wajen makala adireshin gidan yanar sadarwa ko Mudawwanarka a shafinka na Facebook. Dukkan wadannan na cikin abin da ya kara wa dandalin shahara a tsakanin jama’ar Intanet.

Sai kuma sauki da tsarin dandalin ya sifatu da shi. A bayyane yake cewa, neman sauki dabi’a ce ta dan Adam. Duk inda sauki yake, to shi ma yana wajen. Wannan dandali na Facebook ya shahara ta bangaren saukin mu’amala a yayin da mai ziyara ke mu’amala da shafi ko abokan huldarsa a dandalin. Akwai sauki wajen yin rajista. Akwai sauki wajen shiga. Akwai sauki wajen sanya hotuna. Akwai sauki wajen neman abokai. Akwai sauki wajen yada bayanai. Akwai sauki wajen neman bayanai. Akwai sauki wajen karanta bayanai da sakonni. Akwai sauki wajen rubutawa da aikawa da sakonni. Akwai sauki wajen mu’amala da masarrafan da ke shafin. Sannan, a karo na karshe, akwai sauki tattare da mu’amala da abokan hulda a shafin baki daya. Wannan dabi’a da sifa ta sauki, na cikin ababen da suka kara wa shafin Facebook shahara a duniya baki daya.

Bayan sifar sauki da dandalin ya dabi’antu da ita, abu na gaba shi ne yawan sauye-sauyen da masu dandalin ke yi a shafin, da kuma damar da suka baiwa kwararru kan manhajar kwamfuta don ginawa tare da ajiye kananan masarrafai masu sawwake mu’amala a shafin. Kamar yadda bayanai suka gabata a makonnin baya, akwai kwararru kan harkar kwamfuta, watau Developers, sama da dubu arba’in da hudu masu rajista kuma suke taimakawa wajen gina kananan masarrafai don amfanin masu rajista a dandalin. Ire-iren wadannan sauye-sauye na cikin abubuwan da suka kara wa wannan dandali shahara a tsakanin masu amfani da Intanet.

Dalili na karshe, shi ne shahara a bakin mutane. Akwai da dama da suka saba da Kalmar “Facebook” a bakinsu, amma ba su ma taba shiga shafin ba. Wannan ke nuna cewa lallai shaharar ta kasaita, tunda har wadanda ma basu taba shiga shafin ba sun san sunan shafin a bakinsu.

Dandalin “Facebook” a Mahangar Masana

Tsarin Mu’amala a Dandalin Facebook

Tsarin mu’amala a dandalin Facebook ba wahala. Abu na clip_image001farko da ake bukata wajen duk mai sha’awar yin hakan shi ne yin rajista a zauren gidan yanar sadarwar kamfanin, wanda ke www.facebook.com. Yin rajista dai kyauta ne, kamar yadda na tabbata mai karatu ya san hakan. A lokacin yin rajistan za a bukaci sunanka ne, da suna ko lakabin da kake so ka rika shiga shafinka da shi (Username ko User ID), da kalmomin iznin shiga (Password), sai kuma adireshin Imel dinka. Kana gama shigar da wadannan bayanai, za a sanar da kai cewa an tura maka sako a akwatin Imel dinka, sai kaje can ka budo. Idan ka budo za ka ga sakon da ke ciki, mai dauke da rariyar likau din da za ta kai ka can shafin da ka bude. Da zarar ka matsa rariyar da aka aiko maka, za ta zarce da kai ne shafinka kai tsaye.

Daga nan sai ka ci gaba da shigar da bayanai; kamar cikakken sunanka (idan kana son yin hakan), da adireshin gida da na ofis, da adireshin shafin Intanet idan kana da shi, da aikin da kake yi, da ra’ayoyinka na siyasa ko addini misali, da irin dandanon da kake da shi a rayuwa (kamar abubuwan da kake so – abin ci ko sha ko aiki ko duk abin da ke baka sha’awa), da dai sauran abubuwa da sai ka shiga za ka gani. Bayan haka sai ka shigar da hotonka ko na duk abin da kake so, da suna ko lakabin da kake son a rika shaida shafinka da shi, da dai sauran abubuwa. Kasancewar wannan dandali ne na abota da haduwa da juna, akwai masarrafar da za ta baka damar gayyatar abokanka da kake da adireshin Imel dinsu a akwatin sadarwarka ta Imel. Idan kuma ba ka da su, duk bai baci ba; akwai inda za ka yi tambaya, a nemo maka mutanen da suke nahiyar da ka fito, ko irin aikin da kake yi, ko irin makarantar da ka gama, ko irin jinsinka, ko kuma irin dabi’u da dandanonka. Duk wadannan hanyoyi ne da za ka iya samun abokanai don yin mua’amala a tsakaninka da su.

Idan ka gama gyatta shafinka, kana iya gayyatar mutane kamar yadda bayanai suka gabata, sannan akwai bango da aka tanada maka (watau Wall) don shigar da bayanai saboda masu ziyara su karanta. Wannan bango yana tsakiyan shafin ne daga sama zuwa kasa. Akwai kuma inda za ka rika rubuta ra’ayoyinka, da abin da ko halin da kake ciki. Wannan wuri shi ake kira Status, kuma da shi ne dukkan abokanka za su rika sanin halin da kake ciki, ko yanayin da kake ciki, ko inda ka tafi; muddin ka rubuta su, to za su gani. Sannan dukkan bayanan da suke dauke cikin wannan wuri masu bayyana hali ko yanayinka, za su rika bayyana a cikin bangonka, kuma duk wanda ka taskance a matsayin abokinka, zai rika ganin wadannan bayanai a bangonsa – kamar yadda kai ma za ka iya ganin nasa a bangonka.

Bayan haka, akwai masarrafar yada labarai (watau Live Feeds), wacce ke kwaso maka wainar da ake toyawa tsakaninka da abokanka, ko tsakanin abokanka da abokansu, da wadanda ke kulla alaka, da kuma tsokacin da wasu ke yi a shafinka (watau Comments). Kana da damar shigar da bidiyo a shafinka, wadanda ka dauka a wayarka ta salula ko kyamarar bidiyo dinka. Sannan kana da damar shigarwa ko bude albom na hotuna iya son ranka. Wadannan hotuna ana iya ganinsu a shafinka; musamman ma abokanka. Sannan kai ma kana iya ganin hotunansu da suka zuba, har ma kayi tsokaci ko Karin bayani na yabo ko suka kan hotunan. A bangaren raha kuma akwai masarrafar naushi ko tsikari (Poke) wacce kana iya yinta ga kowane cikin abokanka. Da zarar ka matsa alamar a shafinsa, sai alamar masarrafar ta alamanta a sunansa cewa “wane ya tsikari wane”, a misali. Kana kuma iya taskance bayanan sirri a masarrafar allon rubutunka da ke shafinka, watau Notes.

Kana kuma iya yin hirar ga-ni-ga-ka (watau Intstant Chat) kamar yadda ake yi a manhajar Yahoo Messenger misali. Akwai kuma dan karamin shagon saye da sayarwa (watau Market Place) da ke cikin kowane shafi. A wannan shago, kana iya tallata kayayyakin da kake da su na sayarwa. Amma wannan masarrafa ta fi amfani ne ga wadanda ke sauran kasashe inda tsarin kasuwanci irin wannan ke ci. Dukkan wadanann masarrafai, da ma wasu, za ka same su a shafin da ka bude. A karshe kuma dole ne kayi hakuri da tarin hotunan tallace-tallace da ke kowane shafi. Da su ne masu gidan yanar sadarwar ke samun kudaden shiga. A takaice dai duk wadannan hanyoyin mu’amala da bayanansu suka gabata sun samu ne sanadiyyar babbar masarrafa ko manhajar da ke gidan yanar sadarwar, wacce ke ba da damar kirkirar kananan masarrafan da ke sawwake tsarin mu’amala a shafukan duka. To yaya tsarin wannan masarrafa ko manhaja yake?

Babbar Manhajar Facebook

Daga lokacin da ka shiga gidan yanar sadarwar dandalin Facebook, ka shigar da bayanai, ka gayyaci abokai, ka amince wa masu nemanka da abota, ka yi tsokaci kan bayanan wasu, ka sanya hotuna ko ka kalli na wasu, ka kai ziyara ko kuma kayi hira da wani kai tsaye, har zuwa lokacin da za ka fice daga gidan yanar sadarwar ko dandalin, kana yin hakan ne a saman wata manhaja ko babbar masarrafa (watau Software Platform) da dandalin ke gudanuwa a samanta. Wannan masarrafa ita ce ruhin dandalin gaba daya. Wannan babbar manhaja ko masarrafa, ita ce masu gidan yanar suke kira “Facebook Markup Language”. Manhaja ce da aka gina ta da dabarun gina manhajar kwamfuta. Kuma da wadannan dabaru ne har wa yau duk mai sha’awar gina wa dandalin manhajar da za a rika amfani da ita don sadarwa ke dogaro.

Dukkan masarrafan da masu amfani da shafin Facebook ke amfani da su suna damfare ne da wannan babbar manhaja; daga gareta aka kago su, kuma a kanta suke rayuwa, tare da habaka. Daga masarrafar bayar da kyaututtuka (watau Gift App), har zuwa masarrafar da masu shafin ke amfani da ita wajen sanya bidiyo da na wasan kwamfuta (watau Chess), duk daga wannan babbar manhaja suka samo asali.

Wannan masarrafa ko babbar manhaja ta Facebook Markup Language ta fara bayar da damar kirkirar kananan masarrafai ne tun cikin shekarar 2007, kuma ya zuwa shekarar 2008 an kirkiri kananan masarrafai sama da dubu talatin da uku (33,000). Ba wai masu gidan yanar sadarwar kadai ke wannan aiki na samar da hanyoyin yada abota da zumunci a wannan dandali ba, a a, duk mai sha’awa, wanda kuma ke da kwarewa ta ilimin gina manhajar kwamfuta (watau Developer ko Web Programmer) yana da damar da zai iya taimakawa. Ya zuwa shekarar 2009 an samu masu wannan hidima sama da kwararru dubu dari hudu (400,000).

Wannan babbar manhaja bata tsaya wajen bayar da damar mu’amala da dandalin Facebook ta kwamfutar kan tebur (Desktop) da kuma ta tafi-da-gidanka (watau Laptop) kadai ba, hatta ga wayoyin salula masu tsarin mu’amala da fasahar Intanet ma na iya mu’amala da shafin kai tsaye, tare da ribatan habakakkun masarrafan da ke saman wannan manhaja, iya gwargwadon damar da masu kera wayar suka bata wajen yin hakan. Masarrafar da aka gina mai bayar da damar mu’amala da dandalin Facebook a wayar salula nau’in Samartphones dai ita ce: “Facebook iPhone App”, wacce aka kirkira a watan Agusta ta shekarar 2007. Kintsatssiyar nau’in wannan masarrafa a yanzu dai ita ce Facebook iPhone App 3.0, wacce kamfanin ya fitar a shekarar 2009. Duk mai wayar salula irin ta zamani nau’in Smartphone na iya shiga wannan shafi ya kuma yi mu’amala da mutane kamar a kwamfuta yake. Haka kamfanin Nokia Corporation ma ya samar da wannan masarrafa a cikin wayoyin salularsa masu dauke da babbar manhajar S60 (misali N97) ta hanyar masarrafar ovi Store da ke dauke a wayar. Idan muka ziyarci kamfanin Google shi ma haka za mu gani. Ya samar da wannan masarrafa cikin babbar manhajar wayarsa ta salula da ya kera mai suna Android 2.0. A karshe har wa yau, akwai wannan masarrafa cikin wayoyin salula nau’in Blackberry. Idan ka samu wadannan nau’ukan wayoyin salula duk kana iya mu’amala da dandalin Facebook kai tsaye, tare da masarrafan da suka dace da tsarin wayarka.

Wannan babbar manhaja ta Facebook Markup Language na dauke ne cikin manyan kwamfutoci ko kace Uwargarke mai bayar da damar mu’amala da bayanan da ke cikinta. Masarrafar da wannan Uwargarke ke amfani da ita wajen bayar da damar mu’amala da shafin (watau Front-end Servers) dai ita ce PHP LAMP, watau Hypertext Preprocessor LAMP. Wannan manhaja ce ta musamman da ake gina ta da tsarin gina manhajar kwamfuta a gidajen yanar sadarwa mai suna PHP. Aikinta dai shi ne ta sadar da kai da Uwargarken, ta hanyar nuna maka shafukan da ka bukata, a irin yanayin da suka kamata. Masarrafar da ke can kurya mai lura da babbar manhajar kuma an gina ta ne da dabarun gina manhajar kwamfuta nau’uka daban-daban, wadanda suka hada da: C++, da Java, da Phython, da kuma Erlang. Na san ba lalai bane mai karatu ya fahimci wadannan abubuwa, saboda fahimtarsu na bukatar zurfin karatu cikin fannin kimiyyar sadarwa ta kwamfuta da yada bayanai.

Dandalin “Facebook” (1)

Mabudin Kunnuwa

Babu wani dandalin Intanet da ya samu shaclip_image002hara da ambato irin wanda Dandalin Facebook yake samu a halin yanzu. Nan ne matattarar samari da ‘yan mata; matattarar masana da masu neman sani; matattarar masu neman bayanai da masu samar da su; matattarar masu saye da masu sayarwa; matattatar masu bincike da wadanda ake bincike kansu; matattarar malamai da dalibansu; matattarar shuwagabanni da wadanda ake shugabanta; matattarar masarrafai da masu samarwa da kuma masu amfani da su; matattarar masu leken asiri da wadanda ake leken asirinsu. Kai a takaice dai, idan kace Dandalin Facebook ya tattaro “kowa da kowa” daga “ko ina da ko ina”, a mahangar zamani, to baka yi karya ba.

Duk da cewa akwai wasu dandalin a Intanet, inda ake taruwa kamar clip_image004irin taruwar da ake yi a Dandalin Facebook, ko ake bincike kamar yadda ake yi a nan, sai dai akwai bambancin tsari da yanayi da kuma tasiri a tsakaninsu. Wasu cikin dandamalin da ake da su dai sun hada da Dandalin MySpace, da Dandalin NetLog, da Dandalin Jhoos, da Dandalin hi5, da Dandalin LinkID, da dai sauransu. Wadannan sababbin dandamali ne suka kashe wa majalisu da wuraren shakatawa da ake da su a Intanet a baya, irinsu: Yahoo! Messenger, da Windows Live Messenger, da ICQ, da AOL Messenger, da majalisu irinsu Yahoo! Groups, da Google Groups, da sauran makamantansu. Duk da cewa wadannan majalisu da wuraren tattaunawa suna nan har yanzu, amma hankalin galibin mutane, musamman samari da ‘yan mata, ya fi komawa kan wadannan dandamali da na zayyana a sama. Shin meye ake yi a cikinsu? Yaya aka yi suka samo asali? Wa ya samar da Dandalin Facebook kuma yaushe? Yaya tsarin Dandalin Facebook yake? Me ya bashi shahara? Me ye amfanin da ke tattare da wannan dandali na Facebook? Shin akwai matsaloli da ke tattare da amfani da wannan dandalin? In eh, wasu matsaloli ne ake da su kuma ina dalilan samuwarsu? Wadannan ne, da ma wasu tambayoyi masu nasaba da su, muke son gabatar da bincike kansu a mahangar ilimi da bincike, ba wai a mahangar labarin baka kadai ko shaharar baki ba. Sai dai kafin nan, zai dace mai karatu ya fahimci wani sabon tsarin samar da bayanai a Intanet, wanda kuma hakan ne ya dada taimakawa wajen samar da ire-iren wadannan wuraren shakatawa a Intanet.

Tsarin Samar da Bayanai a Intanet

Tsarin samar da bayanai a Intanet ya kasu kashi biyu, tun sa’adda aka kirkiri wannan fasaha mai matukar tasiri a rayuwar mutane. Tsarin farko shi ne tsohon tsari; watau hanyar samar da bayanai ta gidan yanar sadarwa. Wannan shi ne tsohon yayi, kuma shi ne abin da a farkon zamanin mu’amala da fasahar Intanet ya shahara. Duk wanda ke neman bayanai kan wasu abubuwa ko wani fanni na ilmi, to a gidan yanar sadarwa (watau Website) zai samu. A wancan lokacin kuma galibin masu gidajen yanar sadarwa duk basu wuce malaman makaranta ba, ko masu sha’awar yada ilmi ta hanyar bincike a Intanet, ko kuma hukumomin gwamnati masu kokarin sanar da al’umma halin da hukuma ke ciki. Nau’ukan bayanan da ake samu ta wannan hanya ko tsari kuwa sun hada da tsagwaron bayanai – kamar kasidu da makaloli ko baituka da dai sauransu – da hotuna da kuma hotuna masu motsi, watau bidiyo kenan. A wannan zamani ko tsari, mai gidan yanar sadarwa – mutum ne ko hukuma ko kamfani – shi ke zuba irin bayanin da ya ga dama, a yanayin da yayi masa, a kuma irin tsarin da ya dace da manufarsa.

Da tafiya tayi nisa, harkar kasuwanci ta fara habaka a duniyar Intanet, sai ‘yan kasuwa suka shiga binciken sanin hanyoyi ko irin bukatun da masu sayen hajojinsu a Intanet ke da su ko suke bi. Wannan ta sa aka fara kirkirar gidajen yanar sadarwa ko mudawwanai masu baiwa mai karatu ko mai ziyara ko mai sayen wata a haja a gidan yanar sadarwa damar fadin albarkacin bakinsa kan hajar ko abin da yake so ko yake sha’awa. A daya gefen kuma sai ga manyan gidajen yanar sadarwa – irin su Yahoo!, da MSN, da Google - sun kirkiro hanyoyin da masu ziyara ke haduwa suna tattaunawa kan bukatunsu na rayuwa, da dandanonsu kan rayuwa, da abubuwan da suke bukata, da dai sauran abubuwan da suka shafe su. Hakan kuwa ya samu ne ta hanyar Majalisun Tattaunawa da Zaurukan Hira (watau Cyber Communities – ko “Kauyukan Intanet”), wadanda kuma suka hada da Groups, da Internet Chat Rooms, da Communities, da kuma Bulletin Board ko Forums. A wadannan wurare, masu karatu da masu ziyara da masu saye da sayarwa ne ke tattaunawa a tsakaninsu kan bukatunsu da dandanonsu. Kuma wannan tsari, a harshen Kimiyyar Sadarwa ta Zamani, shi ake kira User Content; watau tsarin samar da bayanai ta hanyar mai ziyara.

Wannan tsari ne ya zaburar da masu sauran gidajen yanar sadarwa a Intanet, inda suka fara sanya kafofin jin ra’ayoyin masu ziyarar gidajen yanar sadarwarsu, ko masu karatun makaloli da kasidun da suka taskance a Mudawwanansu. Haka gidajen yanar sadarwar jaridu da mujallu, duk suna da wannan tsari. A karshe dai, dukkan bayanan da masu karatu ko masu ziyara ke rubutawa ko sanyawa, ana taskance su ne a kwamfutocin masu gidan yanar sadarwar. Kuma wadannan bayanai na masu karatu ko ziyara na cikin nau’ukan bayanan da manhajojin Matambayi Ba Ya Bata (Search Engines) ke nannado su, don baiwa masu neman bayanai kan fannoni daban-daban a Intanet a yau. Samuwar wannan tsari ne har wa yau, ya haifar da samuwar ire-iren dandamalin abota da ake da su a Intanet a yau, irin su Facebook, da NetLog, da JHoos, da LinkID da dai sauran makamantansu.

Dandalin Abota a Intanet (Social Network)

A mahangar Kimiyyar Sadarwar Zamani, idan aka ce “Social Network” ana nufin dandalin shakatawa da yin abota. Wuri ne ko kace “Dandali” ne da ke hada mutane daga wurare daban-daban, masu launi daban-daban, masu harshe daban-daban, daga wurare daban-daban, masu matsayi daban-daban, masu matakin ilmi daban-daban, kuma masu manufofi daban-daban. Haduwar wadannan mutane a “waje daya” shi ke samar da wani dandali budadde, mai kafofi daban-daban, inda kowa ke zaban abokin huldarsa ta hanyar masarrafa ko manhajar kwamfuta da aka kirkira a irin wannan dandali. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mai karatu ya san cewa wannan dandali ba wani abu bane illa wani gidan yanar sadarwa ne na musamman da wasu ko wani kamfani ko mutum ya samar da shi don wannan manufa. Manufar a farko ita ce samar da muhallin da mutane za su tattauna da juna ta hanyar yin abota da yada ra’ayoyinsu kan wasu abubuwa da suke sha’awa. Wannan manufar asali kenan. Amma a yau wannan manufa ta canza nesa ba kusa ba. Akwai manufar kasuwanci, da yada manufa, da samar da hanyoyin bincike kan dandanon masu ziyara ko masu tattaunawa a majalisar, da dai sauran manufofin da mai karatu zai ji su nan gaba.

Bayan haka, wadannan dandamali suna nan nau’uka ne daban-daban; akwai wadanda ake harkar abota ta hanyar samar da bayanai zalla, akwai wadanda kuma hotuna ne zalla ake taskancewa kuma su kadai ake yadawa wajen abotar. Akwai kuma wadanda musannan aka samar dasu don manufar tara kwararru kan fannonin ilmi ko kasuwanci daban-daban. A takaice dai, akan gane nau’in dandali ne ta hanyar suna ko nau’ukan masarrafai ko manhajojin da ake amfani da su don sadar da zumuncin aikawa da sakonni ko neman abokanai masu ra’ayi ko sana’a ko kwarewa irin wanda kake da ita. Amma abin da yafi shahara a wadannan dandamali shi ne harkar kasuwanci. A yayin da kake ganin kana iya bude shafi, ka sanya bayanai, ka nemo abokai, ka kuma aiwatar da sadarwa ta hanyar da kake so ba tare da ka bayar da ko ahu ba, a daya bangaren kuma an ci riba a kanka fiye da yadda kake zato. Babban abin da ya baiwa Dandalin Facebook shahara a kan sauran dandalin abota a Intanet shi ne samuwar hanyoyin mu’amala da juna da yada bayanai da kuma hanyoyin samarwa tare da kirkirar nau’ukan bayanai fiye da daya; daga tsagwaron bayanai zuwa hotuna daskararru da masu motsi (watau bidiyo), da dai sauran abubuwa masu kayatarwa. To ta yaya wannan Dandali na Facebook ya samo asali?

Yadda Aka Samar da Dandalin Facebook

Dandalin Facebook ya samo asali ne cikin watan Fabrairun shekarar 2004, kuma wanda ya kirkiri gidan yanar sadarwar dai wani matashi ne mai suna Mark Zuckerberg, wanda kuma a lokacin yake karatun fannin Kwamfuta a Jami’ar Harvard da ke kasar Amurka. Ya kirkiri wannan gidan yanar sadarwa na Facebook ne a kwamfutarsa nau’in Mac, a cikin dakin kwanan dalibai (Dormitory), da misalin karfe goma na dare. Daga nan ya sanar da wasu cikin abokan karatunsa su uku, wadanda su ma fannin kwamfuta suke karantawa a lokacin, ya kuma shigar da su cikin wannan aiki don su taimaka wajen ingantawa tare da yada wannan aiki da ya faro. Wadannan abokai nasa dai su ne: Eduardo Saveri, da Dustin Moskovitz, sai kuma Chris Hughes.

Tunanin da ya haifar da samar da wannan dandali na Facebook dai ya samo asali ne daga tsarin da wata makaranta ke bi wajen buga sunayen dalibai da ke makarantar, tare da fannonin da suke karantawa, don raba wa dalibai saboda samar da sanayya a tsakaninsu. Wannan makaranta dai ita ce Philips Exerta Academy, wacce Mark ya halarta kafin zuwansa Jami’ar Harvard. Daga wannan dan karamin littafi da makarantar ke raba wa dalibai ne – wanda sauran daliban makarantar suka sanya wa suna “Facebook” a tsakaninsu - Mark ya dauko wannan suna. A farko dai Mark ya samar da wannan gidan yanar sadarwa ko dandali ne don yada hotunan abokansa da kuma na wasu dabbobi, inda ya sanya wata manhaja da masu ziyara ke amfani da ita wajen jefa kuri’a kan hoton dabba ko hoton wani abokinsa da ya fi kyau da kayatarwa. Daga baya sai aka samar da yadda duk mai ziyara zai iya mallakar shafinsa na musamman, don zuba nasa hotuna ko bayanai, da kuma hanyoyin gayyatar duk wanda kake son ya zama abokinka. Da tafiya ta kara gaba sai kwararru kan gina manhajar kwamfuta (watau Computer Programmers ko Developers) suka fara samar da hanyoyin gina kananan manhajoji ko masarrafai masu sawwake mu’amala da juna a wannan shafi.

Shafin Facebook na asali dai ya takaita ne ga abokanan Mark kadai, daga baya sai suka fadada wannan dandali zuwa sauran daliban da ke Jami’arsu, daga suka sake fadadawa zuwa daliban da ke Jami’ar Standford. Da lifafa ta ci gaba kuma, sai suka sake fadada damar shiga zuwa ga dukkan daliban Jami’a kadai. Daga nan suka ce ‘yan Sakandare ma na iya shiga. Da abin ya dada kasaita sai suka fadada dandalin ta yadda duk mai shekaru goma sha uku zuwa sama zai iya yin rajista, ya kuma mallaki shafinsa na kansa. A halin yanzu, wannan dandali na Facebook na dauke ne da mambobi masu rajista wadanda suka mallaki shafin kansu sama da miliyan dari hudu (400 Million). Wannan ya sanya Dandalin Facebook a sahun farko wajen yawan masu rajista da masu ziyara a dukkan duniya.

Dandalin “Facebook” a Mahangar Masana (2)

Mabudin Kunnuwa

Babu wani dandalin Intanet da ya samu shahara da ambato irin clip_image002wanda Dandalin Facebook yake samu a halin yanzu. Nan ne matattarar samari da ‘yan mata; matattarar masana da masu neman sani; matattarar masu neman bayanai da masu samar da su; matattarar masu saye da masu sayarwa; matattatar masu bincike da wadanda ake bincike kansu; matattarar malamai da dalibansu; matattarar shuwagabanni da wadanda ake shugabanta; matattarar masarrafai da masu samarwa da kuma masu amfani da su; matattarar masu leken asiri da wadanda ake leken asirinsu. Kai a takaice dai, idan kace Dandalin Facebook ya tattaro “kowa da kowa” daga “ko ina da ko ina”, a mahangar zamani, to baka yi karya ba.

Duk da cewa akwai wasu dandalin a Intanet, inda ake taruwa kamar irin taruwar da ake yi a Dandalin Facebook, ko ake bincike kamar yadda ake yi a nan, sai dai akwai bamban tsari da yanayi da kuma tasiri a tsakaninsu. Wasu cikin dandalin da ake da su dai sun hada da Dandalin MySpace, da Dandalin NetLog, da Dandalin Jhoos, da Dandalin hi5, da Dandalin Linkid, da dai sauransu. Wadannan sababbin dandula ne suka kashe wa majalisu da wuraren shakatawa da ake da su a Intanet a baya, irinsu: Yahoo! Messenger, da Windows Live Messenger, da ICQ, da AOL Messenger, da majalisu irinsu Yahoo! Groups, da Google Groups, da sauran makamantansu. Duk da cewa wadannan majalisu da wuraren tattaunawa suna nan har yanzu, amma hankalin galibin mutane, musamman samari da ‘yan mata, ya fi komawa kan wadannan dandula ko dandaloli da na zayyana a sama. Shin meye ake yi a cikinsu? Ya aka yi suka samo asali? Wa ya samar da Dandalin Facebook? Yaushe? Yaya tsarin Dandalin Facebook yake? Me ya bashi shahara? Me ye amfanin da ke tattare da wannan dandali na Facebook? Shin akwai matsaloli da ke tattare da amfani da wannan dandalin? In eh, wasu matsaloli ne ake da su kuma ina dalilan samuwarsu? Wadannan ne, da ma wasu tambayoyi masu nasaba da su, muke son gabatar da bincike kansu a mahangar ilimi da bincike, ba wai a mahangar labarin baka kadai ko shaharar baki ba. Sai dai kafin nan, zai dace mai karatu ya fahimci wani sabon tsarin samar da bayanai a Intanet, wanda kuma hakan ne ya dada taimakawa wajen samar da ire-iren wadannan wuraren shakatawa a Intanet.

Fasahar “Fiber Optic” (1)

Tsari da Bangarorin Wayar Fiber Optics

Wayoyi nau’in Fiber Optics na tattare ne da bangarori guda uku. Bangaren farko shi ne wanda ya kunshi dukkan tsintsiyar wayoyin gilasan da ke daukan bayanai daga ma’aika zuwa makarba. Wadannan silin wayoyin gilasai su ake kira Core a turancin kimiyyar sadarwar zamani. Kuma su ne a can kurya, a cure wuri daya; kamar daurin tsintsiya. Sai kuma bangare na biyu, wanda ke dauke da curin gilashi mai rankabo haske daga jikin bangaren farko, ya sake mayar da shi. Wannan bangare shi ake kira Cladding, kuma a saman bangaren farko ake dora shi. Da zarar wancan bangaren farko mai suna Core ya debo haske daga tushin wayar, sai wannan bangare na biyu watau Cladding, ya taimaka wajen rankabowa tare da mayar da hasken zuwa jikin wadannan silin wayoyin gilasai, don tabbatar da hasken, da kuma taimakawa wajen isar da sakon da ke dauke cikin hasken nan take babu bata lokaci. Bangare na uku kuma shi ne fatan roban da ke suturce wadannan bangarorin biyu da bayaninsu ya gabata. A takaice dai, shi ne roban da ke waje, mai dauke da dukkan bangarorin guda biyu. Aikin wannan roba ko riga shi ne ya suturce wadannan silin gilasai masu sadar da hasken da ke dauke da bayanan da ake so aikawa, da kare su daga jikewa, ko rubewa da lalacewa. A turancin kimiyyar sadarwar zamani, wannan roba shi ake kira Buffer Coating, a tsarin sadarwar zamani. Wadannan, a takaice, su ne bangarorin wannan fasahar sadarwa mai suna Optical Fiber.

Wannan hanya ta Optical Fiber na amfani ne da ballin haske (watau Light Pulse) wajen aikawa da sakonni daga ma’aika zuwa makarba. Kuma fasahar tana da karfin aikawa da sakonnin bayanai a kalla miliyan goma, a dukkan ballin haske guda daya. Tsarin Fiber Optics na iya aikawa da bayanai masu dimbin yawa cikin kankanin lokaci, da inganci, kuma babu kwangen bayanai (watau Data Loss). Wannan ta sa wayoyin sadarwa nau’in Optical Fiber suka fi sauran wayoyi musamman na karfe ko dalma (watau Metal Wires) ingancin sadarwa da kuma sauri. Suna iya tsare bayanai, su isa lafiya, kuma basu cin karo da matsalar sinadaran hasken maganadisun lantarki (watau Electromagnetic Interference) a yayin da suke aikawa da bayanai.

Asali da Samuwar Wayoyi Nau’in Fiber Optics

Duk da cewa wannan fasaha ta Optical Fiber bata shahara ba sosai sai a yanzu, amma ta samo asali ne sama da shekaru dari da tamanin. A takaice dai tsohuwar fasaha ce. A iya binciken shafin Kimiyya da Kere-kere, wanda ya fara samar da bayanai kan haske da launi da yadda suke samuwa da yadda ake rankabo haske, shi ne babban malamin Musulunci mai suna Ibnul Haitham. Shi ne ya rubuta wani littafi mai suna Kitaabul Manaazir cikin harshen larabci, ko Kitaabul Manzaraah a harshen Farisanci, ko kuma The Book of Optics a turance. Wannan littafi an fassara shi zuwa harsunan duniya da dama, kuma har yanzu malaman kimiyyar fiziya da ke yammaci da gabashin duniya na amfanuwa da wannan littafi. A halin yanzu marubucin wannan littafi ya kai shekaru dubu daya da rasuwa. Sai cikin shekarar 1840 wasu masana ‘yan kasar Faransa suka gudanar da wani bincike kan tsarin tafiyarwa ko aikawa da haske ta amfani da alar da ke rankabo shi a halin tafiyarsa, watau Light Reflector. Wadanann masana dai su ne Daniel Colladon da kuma Jacques Babinet, kuma sun gudanar da binciken ne a birnin Paris. Wannan tsari na rankabo haske na cikin ginshikin wannan fasaha na Optical Fiber.

Daga nan kuma sai wani masani mai suna Tyndall John a wani littafinsa da ya rubuta mai suna Light Properties a shekarar 1870. Wannan littafi na bayani ne kan tsarin haske da yadda ake sarrafa shi, musamman yadda ruwa da gilashi da kuma daimon ke rankabo haske a kimiyyance. Ana shiga karni na ashirin kuma sai wasu masana suka gudanar da wani bincike mai fadi kan wannan fanni. Wadannan masana dai su ne Clarence Hansell da kuma John Logie Baird, a shekarar 1920. Ci gaban da aka samu sakamakon wannan bincike nasu shi ne samar da tsarin tallabo haske don ganin lungu-lungu. Wannan tsari a turancin kimiyyar zamani shi ake kira Close Internal Illumination. Bayan wannan tsari, binciken ya samar da tsarin aikawa da hotuna ta amfani da sinadaran haske, watau Image Transmission. Shekaru goma bayan wannan bincike na su Hansell da Baird, sai wani masani mai suna Heinrich Lamm ya samar da tsarin amfani da sinadaran haske wajen aikin likitanci – musamman kan abin da ya shafi aikin tiyata, da gano cututtuka da dai sauransu. Wannan bincike Lamm ya yi shi ne cikin shekarar 1930, watau shekaru goma kenan bayan binciken su Hansell da Baird.

Bayan shekaru ashirin ne aka samar da tsarin amfani da haske ta hanyar fasahar Optical Fiber. Wanda yayi wannan bincike ya kuma samar da fasahar dai shi ne wani jarumi a fannin kimiyyar fiziya mai suna Narinder Singh Kapany, cikin shekarar 1952. Bayan shekaru goma kuma sai wanann fasaha ta yadu cikin kasashen Turai ta Yamma (Western Europe), inda aka ta amfani da ita wajen kera wayoyin sadarwa nau’in Fiber Optics don sadarwa daga zango zuwa zango. Wannan zamani ne ya yi tasiri wajen habakar wannan fasaha ta Optical Fiber, musamman samuwar wani bincike da wani Malami dan kasar Japan yayi mai suna Jun-ichi Nashizawa da ke Jami’ar Tohoku. Malam Nashizawa ya kididdige bincikensa ne cikin wani littafi da ya rubuta, wanda ba a samu dabba’a shi ba sai cikin shekaru takwas da suka gabata a kasar Indiya. Wannan kera wayoyin sadarwa nau’in Optical Fiber ana ta amfani da su, duk da cewa ana samun ‘yan matsaloli da tangardar sadarwa sanadiyyar tsarin kirar da aka musu. Wannan tasa wasu masanan kimiyya da ke aiki a kamfanin kera wayoyi na kasar Burtaniya (watau Standard Telephones and Cables – STC), masu suna Charles K. Kao da kuma George A. Hockhan suka gudanar da wani bincike da ya samar da hanyar cire dukkan matsaloli da tangardar da ake fuskanta wajen mu’amala da wannan fasaha. Hakan ne kuma ya samar da nau’ukan wayar Fiber Optics da ake amfani da su a yanzu.

TAKAITACCEN TARIHIN “BABAN SADIK”

Wasu cikin masu karatu sun bugo waya suna neman in rubuta takaitaccen tarihi na don su karanta. Na basu uzuri kan cewa babu wani abin ji a cikin tarihi na, amma sun dage sai sun ji. Don haka na dan tsakuro muku wani abu cikin tarihin rayuwata.

Suna na Abdullahi Salihu Abubakar, an kuma haife ni ne a Unguwar Hausawa ta Garki Village da ke Karamar Hukumar Municipal, a babban birnin tarayya ta Abuja, cikin shekarar 1976. Shekaru na 34 kenan. Mahaifi na shi ne Malam Abubakar Salihu, shi kuma Salihu kakana ne. Asalin kakanni na (da ma sauran mazauna Unguwar Hausawa a Garki Village) daga Kano suke. Zama ne ya kawo su wannan wuri, wacce a wancan lokaci ta zama kamar zango, kusan shekaru dari biyu da suka gabata. Kuma ma saboda tsawon zamani da halin zamantakewa, a halin yanzu duk mun rikide mun zama Hausawan Abuja. Na yi makarantar Firamare, da Sakandare da kuma Jami’a duk a Abuja. A halin yanzu ina da digiri kan fannin Tattalin Azkirin Kasa (Economics), wanda na samu daga Jami’ar Abuja. Ina kuma kan neman ilmin Kur’ani da sauran fannonin Ilmin musulunci har yanzu.

Ni mutum ne mai sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance. Ina kuma son binciken ilmi kan fannonin ilmi irinsu Tattalin Arzikin Kasa (Economics), da Fasahar Sadarwar Zamani (Information Technology), da Fasahar Intanet, da Tsarin Harsuna (Linguistics), da Fassara (Translation), da Aikin Jarida (Journalism) da Kimiyya (Science) da dai sauran fannoni masu nasaba da wadannan. Allah Ya hore min juriyar karatu da rubutu iya gwargwado. A halin yanzu na rubuta littafi kan fasahar Intanet, mai suna “Fasahar Intanet a Sawwake”, wanda ake gab da bugawa. Akwai kuma wadanda nake kan rubutawa a halin yanzu, kamar “Tsarin Mu’amala da Fasahar Intanet”, da kuma “Wayar Salula da Tsarin Amfani da Ita”. Sai kuma kasidun da nake rubutawa a wannan shafi a duk mako.

A halin yanzu ina zaune ne a Sabon Garin Garki (watau New Garki Town) da ke nan Abuja. Ina da mata daya, da ‘ya’ya uku: Abubakar Sadiq, da Nabeelah, sai kanwarsu Hanan. Wannan shi ne dan abin da ya samu.

Monday, May 17, 2010

Tsarin Sadarwa ta Wayar Salula (Mobile System Communication) (1-3)

Matashiya

Cikin silsilar da muka faro sama da makonni biyar da suka gabata kan wayar salula da tsarinta, a yau za mu ci gaba. Idan ba a mance ba, a baya mun kawo bayanai ne kan ma’anar wayar salula, da tarihin samuwarta, da tarihin tsarin sadarwar wayar salula tun farkon samuwa har zuwa yanzu, da shahararrun kamfanonin wayar salula a duniya, da bunkasar wayar salula a duniya, sai kuma bayani na karshe da muka yi kan bangarorin wayar salula, da alakar da ke tsakanin gangar-jiki da ruhinta. A nan muka kwana, kuma a halin yanzu ga shi mun dawo don ci gaba.

A yau kuma za mu kawo bayanai ne kan Tsarin Sadarwa ta Wayar Salula, watau Mobile Communication System a harshen Turancin Kimiyyar Sadarwa. Wannan tsari kuwa ya kunshi Nau’ukan Tsarin Sadarwa ta Wayar Iska, watau Wireless Communication System, da Tsarin Sadarwa ta GSM, da Yanayin Sadarwa, watau Network Service, da Kamfanin Sadarwa, watau Telecom Operator kenan, da Matakan Sadarwa, da Nau’urorin Sadarwa, sai kuma Tsarin Hada Wayar Salula - wanda ke kunshe da wayar hannu, da Katin SIM, da kuma lambar waya. In ana tare da mu, za a samu dukkan wadannan bayanai cikin gamsarwa. A halin yanzu ga bayani nan kan Nau’ukan Tsarin Sadarwa ta Wayar Iska, watau Wireless Communication System.

Nau’ukan Tsarin Sadarwa ta Wayar Iska

Da farko dai, tsarin sadarwa (na bayanai ko sauti ko hotuna) ta wayar-iska, daga tashar aikawa zuwa tashar karba, shi ake nufi da Wireless Communications, a turance. Wannan tsari na iya kasancewa ta amfani da kowane irin kayan fasahar sadarwa; daga wayar salula zuwa kwamfuta, ko talabijin irin na zamani, ko dukkan wasu kayayyakin sadarwa masu dauke da sinadaran sadarwa irin na zamani. A wannan tsari na Wireless Communication, babu alaka ta zahiri tsakanin tashar da ke aikawa da sakon, da tashar da ke sadarwa a tsakani, da kuma tashar da ke karba a karshe. A yayin da tsoffin wayoyin tangarahon gidajenmu ke bukatar dogayen wayoyin sadarwa nau’in Twisted Pair RJ11, daga babban tashar sadarwa zuwa gidajenmu don jona wannan waya da tangarohonmu kafin yin magana da wanda muke son magana da shi, a tsarin Wireless Communication duk ba a bukatar haka. Dukkan tsare-tsaren ana yin su ne ta hanyar tashoshin da ke sadarwa, ba a bukatar wani dan aike bayananne a tsakani.

Wannan hanya ta Wireless Communication na da nau’uka da dama wadanda ko dai an yi amfani da su a baya wajen aikawa da sakonni ta wayar iska, ko kuma ana ma amfani da su a yanzu haka. Wadannan hanyoyi dai su ne: Advanced Mobile Phone System (AMPS), da Global System for Mobile Communication (GSM), da Cellular Digital Packet Data (CDPD), da Personal Digital Cellular (PDC), da Total Access Communication System (TACS), da Nordic Mobile Telephone (NMT), da International Mobile Telephone Standard 2000 (IMTS-2000), sai kuma Universal Mobile Telecommunications Systems (UMTS). Wadannan shahararru daga cikinsu kenan. Amma wanda ya dame mu a duk cikinsu shi ne Global System for Mobile Communications (GSM), wanda kuma shi ne muke amfani da shi a tsarin sadarwa ta wayar salula a Nijeriya yanzu.

Tsarin Sadarwa ta GSM

Tsarin TDMA, wanda aka fi sani da “Global System of Mobile Communications”, ko GSM a gajarce, shi ne tsari mai inganci na sadarwa da duniya ke ji da shi a halin yanzu. Wannan tsari na GSM ya fara aiki ne a kasar Finland cikin shekarar 1991, inda ya samar da damar aikawa da kuma karbar sakonnin tes. Kuma har zuwa karshen shekarar 1999, shi ne sauran kasashen duniya suka yi amfani da shi - in ka kebe kasar Amurka. Da aka shiga shekarar 2000, sai Hukumar Habaka Harkar Sadarwar Tarho ta Duniya, watau International Telecommunication Union (ITU), ta fitar da wasu sababbin hanyoyin sadarwa na wayar salula da ta sanya wa suna “International Mobile Telecommunications-2000”, ko kuma “IMT-2000” a gajarce. Wannan sabuwar hanyar sadarwa ta wayar salula da ITU ta bullo da shi a shekarar 2000, ayarin ka’idojin sadarwa ne da ke sawwake yanayin kira da sadar da shi, da aikawa da sakonnin tes (SMS), da tsarin kira ta hanyar bidiyo (Video Call), da kuma tsarin GPRS da dai sauransu. Bayan haka, karkashin wannan tsari, na’urorin sadarwa na iya aikawa da sakonni nau’uka dabam-daban a lokaci daya. Misali, wayar salularka na iya karbar sakon tes a lokacin da kake amsa kira ko magana da wani a wayar, ba tare da sai ta jira ka gama Magana kafin ta aika ko karba ba. Dukkan wadannan sabbin tsare-tsare sun samu ne karkashin ingantacciyar tsarin GSM mai suna “GSM EDGE”, wanda wannan hukuma ta ITU ta samar tun daga shekarar 2000 zuwa yanzu.

A karkashin tsarin sadarwa ta GSM wayoyin salula suna mu’amala da junanansu ne tamkar yadda mutane ke mu’amala a tsakaninsu. Ma’ana, wata wayar salular tana iya fahimtar inda ‘yar uwarta take, har ta kira ta, su kuma yi Magana, ta hanyar mika bayanai a tsakaninsu. Sannan bayan haka, an samu saurin yaduwar kayayyakin fasahar sadarwa sosai, inda kamfanoni suka yi ta kera nau’uka daban-daban masu dauke da sinadaran sadarwa a cikinsu. Tsarin GSM bai da wahalar sha’ani ko kadan, domin ba ya amfani da ramzozin garuruwa wajen bayar da lamba, watau Codes. Misali, a tsohuwar tsarin sadarwar wayar tarho da muka saba amfani da ita a baya, duk wanda ya kira ka daga garin Kano kana iya ganewa ta hanyar lambobin farko, watau “064”. Amma a tsarin GSM kuwa sai dai ka iya sheda kamfanin da mai kiranka ke amfani da lambarsu, amma ba daga ina yake kiranka ba. Wannan tasa Hukumar Kasar Amurka ta ki amfani da wannan tsari saboda dalilan tsaro. Duk da yake suna da wayoyin salula da kuma tsarin kira ta wayar iska, amma ko daga ina ka kira ana iya ganewa, tare da sanin bigiren da kake, da ma lokacin da kake kira. A takaice dai, tsarin GSM ya taimaka matuka wajen yawaitawa tare da sawwake tsarin sadarwa a duniya baki daya.

Hanyar Sadarwa ta Wayar Salula

A tsarin sadarwa ta wayar iska, abu na farko da ya kamata mai karatu ya sani shi ne hanyar sadarwa, ko kuma hanyar da muryarsa ke bi wajen isa ga wanda yake son Magana ko sadarwa da shi. Domin duk wata ala ta sadarwa tana da hanyar da take bi wajen sadar da sakon da aka dora mata hakkin sadarwa; mota tana da nata hanyar; keke da babur su ma suna da nasu hanyoyin; jirgin sama da na kasa suna da nasu hanyoyin. To haka sadarwa a tsarin sadar da bayanai, na sauti ne ko rubutu ko waninsa. A takaice dai sadarwa a tsakanin wayoyin salula na samuwa ne ta yanayin aikawa da sauti ko bayanai ta hanyar siginar rediyo, watau Radio Waves, wanda a tsarin kimiyyar sadarwa ta zamani ake kira Sine Waves. Wannan hanya na samuwa ne ta hanyoyin sadarwa masu dimbin yawa da ke sararin samaniya da Allah Ya hore wa dan Adam. Kuma hanyar na kunshe ne da abubuwa uku masu tabbatar da sadarwan ga duk wanda aka aika masa. Abu na farko shi ne kadarin lokacin da sakon ke daukawa wajen isa, wanda ke ta’allaka da lokaci, watau Period. Sai kuma kadada, watau iya nisan da sako ke iya dauka na tsawon wani lokaci a halin tafiyarsa, watau Wavelength. Abu na karshe kuma shi ne maimaituwan sadarwa a wani lokaci na iya nisan da sakon ya dauka a farko, watau Frequency.

Wannan tsari na sadarwa ta siginar rediyo (Radio Waves) na da dabakar kadadar saurin sadarwa, watau Range, wajen takwas. Wadannan dabakoki sune: Very Low Frequency (VLF), da Low Frequency (LF), da Medium Frequency (MF), da High Frequency (HF), da Very High Frequency (VHF), da Ultra High Frequency (UHF), da Super High Frequency (SHF), sai kuma Extremely High Frequency (EHF), na kololuwa kenan. Tsarin sadarwa ta siginar rediyo, wacce ke isar da sadarwa irin ta wayar salula da rediyo da talabijin, na amfani ne da dabakar Very High Frequency, watau VHS. Wannan hanyar sadarwan kenan, wacce ke daukan sauti da sakon mutane daga wayoyin salularsu zuwa wadanda suke son Magana da su. Sai abu na gaba.

Yanayin Sadarwa (Network Service)

Bayan samuwar hanyar da ke daukan sakonni daga tashar sadarwa zuwa wata tasha, sai kuma yanayin da ke bayar da wannan dama, watau Network. Wannan yanayi na samuwa ne ta hanyar kayayyakin fasahan da ke sawwake wannan sadarwa, wadanda suka kunshi na kamfanin sadarwa da kuma wanda mai son sadarwan ke da shi. Wadannan na’urori ko kayayyakin fasaha su za su sheda wayar salular da ke neman sadarwa, su tabbatar cewa mai kyau ce, wacce aka kera da dukkan ka’idojin da aka amince da su a duniya da sauran bayanai. Kafin kowane irin nau’in sadarwa ya yiwu tsakanin mai son sadarwa da wanda ake son sadar masa, ana bukatan abubuwa kamar takwas da za su yi mu’amala da juna a lokaci guda, wajen isar da wannan sako. Abu na farko da ya zama dole shi ne, samuwar wayar salular da za a bugo wayar daga gareta, watau Mobile Station. Mobile Station, a tsarin sadarwa ta wayar iska, ita ce wayarka ta salula, wacce aka kera a bisa yardaddun ka’idojin sadarwa ta wayar salula ta duniya, mai dauke da lambobi guda goma sha hudu, a rukunin lambobi uku, kuma ake kira International Mobile Equipment Identity (IMEI). Duk wayar salular da bata cika wadannan ka’idoji ba, to ba a iya isar da sako daga gareta, duk tsadarta kuwa. Wadannan lambobi sha biyu da ke rukunin lambobin uku, za ka iya ganinsu a jikin wayarka da zarar ka cire marafan wayar, ka cire batir (musamman idan ta kamfanin Nokia ce), za ka ga wasu lambobi a jikin wayar, kamar haka: 357964/00/651435, a misali. Wannan na waya ta kenan. Rukunin farko, watau 357964, su ake kira Type Approval Code (TAC). Rukuni na biyu kuma, watau 00, ana kiransu Final Assembly Code (FAC). Sai kuma rukuni na karshe, watau 651435, wanda ake kira Serial Number (SNR). Ka ji amfanin wadannan lambobi, ba wai rubuta su kawai aka yi don kawa ba. Duk wayar da ba ta da su a manne a jikinta, to kayi hankali. Ita wayar salula, kamar yadda muka sani, saya za ka yi a kasuwa ko wajen kamfanin da ke sadarwa idan suna da su.

Bayan samuwar wayar salula watau Mobileclip_image002 Station, sai rukunin lambar sadarwa ta duniya, watau International Mobile Subscriber Identity (IMSI). Su ma lambobi ne da ke rukuni uku kuma sun kunshi lambobi ne da ba su kasa goma shabiyar ba (ko dai goma shabiyar ne ko kasa da haka, misali), idan ba ka da su, to ba maganar sadarwa. Ga misali nan: +234 (080) 34592444. Rukunin farko, watau +234, su ake kira Mobile Country Code (MCC), watau lambar sadarwa ta kasa. Kowace kasa na da nata. Na Nijeriya shi ne +234, kamar yadda na tabbata duk mun sani. Sai rukuni na biyu, watau (080), ko kace Mobile Network Code (MNC), kuma sun takaita ne da kamfanonin sadarwa, irinsu MTN, da ZAIN, da GLOMOBILE da sauransu. Wannan lamba na iya canzawa, kamar yadda mun san akwai masu (070) da (090) da dai sauransu. Sai rukunin karshe: 34592444, wanda ake kira Mobile Station Identification Number (MSIN). Wannan ita ce lambar da ake iya sheda kowace wayar salula (ko mai amfani da ita) da zarar ya nemi sadarwa tsakaninsa da wani. Wannan tasa kaga ba a ma tambayarka sunanka wai don ka je sayan layin wayar salula. Duk da yake wasu kasashe kan yi rajistar sunaye da adireshin masu lambobin waya yayin da suka zo saya, don halin tsaro. Su da wadannan lambobi suke iya sheda kowa, da su ake amfani wajen sanin yawan kudinka, ko rashinsa. To wadannan rukuni idan kana da su, kana iya buga waya ko ina ne a duniya.

Sai abu na gaba, watau Subscriber Identity Module, wanda muke kira SIM Card (ko Katin SIM, a Hausance). Wannan kati ne ke dauke da rukunin lambobin sadarwa ta duniya da bayaninsu ya gabata. Kuma ana sanya shi ne cikin wayar salula, don neman wanda ake so ta hanyar tashar kamfanin da ke bayar da sadarwan. Wannan kati na SIM na dauke ne da kalmar iznin shiga (Password ko PIN Code), wanda mai shi ke amfani da su wajen tsare lambobi da sauran bayanansa da ke ciki. Hakan na faruwa ne ta hanyar wayar salula, ma’ana idan ya shigar da katin cikin wayar salularsa. Wannan kati har wa yau, shi ne babban “dan aike” na farko da ke tsakanin wayar salula da tashar kamfanin da ke isar da sadarwa. Abin da wannan ke nufi shi ne, idan kana da wayar salula, duk tsadanta, muddin babu katin SIM a ciki, to ka hakura da tunanin karba ko isar da sako ta cikinta. Sai abu na gaba, watau Cell Tower, ko kace na’urar sadarwa da ke wani kadada ko fadin birni a wani gari ko kauye. Na’ura ce da kamfanin sadarwa ke aijyewa a wani bangare ko zango na gari ko birni. Misali, kamfanin sadarwa na iya raba birnin Kano zuwa gunduma-gunduma ko shiyya-shiyya. Kowace gunduma ta kunshi lambobin mutanen da ke wannan wuri. Cell Tower ce ke dauke da yanayin sadarwa, watau Network da ke wannan wuri ko kadadan sadarwa. Sai kuma Base Transceiver Station (BTS), watau na’urar da ke aikawa da sako tsakanin wayar salularka da ke wannan kadadan sadarwa zuwa tashar Cell Tower da ke wannan wuri. Wannan na’ura na aikawa da wannan sako ne ta hanyar siginar rediyo, watau Radio Waves. Misali, idan kana Unguwa Uku da ke birnin Kano, sai ka bukaci yin Magana da wani ta hanyar wayarka, da zarar ka buga lambarsa, na’urar BTS ce za ta dauki bukatarka zuwa tashar Cell Tower da ke zangon Unguwa Uku.

Abu na gaba shi ne samuwar Base Station Controller (BSC), watau tashar da ke sadar da sakon masu bugo waya daga wani zango (Cell Tower) zuwa wani. Ita ce babbar zangon da ke hada dukkan zanguna da ke birni ko gari daya. Misali, idan kana Unguwa Uku sai ka buga ma abokinka da ke Mariri, Base Station Controller ce ke da hakkin sadar da bukatar ka daga unguwar da kake zuwa inda ka bukaci a sadar da kai. Sai kuma babban zango ta karshe, watau Mobile Switching Center (MSC). Wannan tasha ita ke dauke da dukkan lambobi da bayanan masu lambobin sadarwa na kamfanin gaba daya. Kwaya daya ce tinkwal, kuma ita ce ke tabbatar da cewa duk wani mai bugo waya, daga ko ina ne, ta hanyar lambobin kamfanin ne ko na wani kamfanin ne daban, daga gida Nijeriya ne ko daga waje, muddin wanda ake son Magana da shi na lambar kamfanin ne, to wannan tasha ce za ta isar da sadarwan idan zai yiwu ko kuma mayar da bukatan mai bukatan saboda wasu dalilan da za mu karanta nan gaba. Wannan babban zango, watau Mobile Switching Center, ta kunshi manyan bangarori ne guda hudu, kuma a halin yanzu ga bayanin kowanne daga cikinsu nan.

Home Location Register (HLR)

Bangaren Home Location Register (HLR), shi ne mai lura da dukkan bayanan da suka shafi layi ko lamban da kake amfani da shi a wayar salularka; yaushe ka fara amfani da shi? Nawa ka zuba a ciki tunda ka saya? Wani layi ka kira na karshe? Kai a ina ma kake a halin da ake Magana? Idan mai karatu bai san wannan ba, ya dubi fuskar wayar salular sa, zai ga tana nuna masa sunan bigiren da yake; a Area 1 ne ko Wuse ko Kano ko Kaduna; Unguwa Uku ne ko Sallare ko BUK? Duk inda kake, Home Location Register ne ke dauke da bayanin inda kake. Kuma wannan zai rika nunawa (idan ka tsara wayarka ta rika nunawa kenan). Har wa yau, aikin wannan bangare ne ya rika hada ka da wanda kake son Magana da shi yayin da ka buga lambarsa; ya kuma rika isar da masu nemanka ta lambar da kake amfani da ita a wannan lokaci. Haka idan ka zo karshen maganan da kake yi da abokin maganarka, Home Location Register ce za ta tsayar da sadarwar (idan ka kashe wayarka ko abokin maganarka ya kashe tasa). Wannan kadan cikin aikin wannan bangare kenan da ke Mobile Switching Center (MSC), watau babban zangon sadarwa da kowace kamfanin sadarwa ta wayar salula ke amfani da shi.

Visitor Location Register (VLR)

Sai kuma bangaren Visitor Location Register (VLR), wanda aikinsa ne ya taskance lambobin wani zangon da ba nasu bane, a matsayin “masu ziyara” kenan. Misali, idan a Kaduna kake, Unguwar Sarki, sai ka je ziyara a Bauchi, kuma wayar salularka na da layin MTN, kana zuwa, Visitor Location Register za ta sheda ka, cewa bako ne kai, duk da cewa kamfanin daya ce. Hujja a nan kuwa shine, don dukkan bayanan da lambarka ta kunsa suna zangon sadarwa (watau Cell Tower) ne da ke Unguwar Sarki na Kaduna. Kana shigowa sai Visitor Location Register ta taskance bayananka na wucin-gadi, har ka gama abin da ya kawo ka, ka tafi. Iya zamanka a Bauchi, za ka samu sadarwa da wadanda suke wasu wurare kuma kai ma za a iya samunka. Haka idan kana tsarin Roaming ne, (watau tsarin da ke bayar da daman wuce kadadan yanayin sadarwan kamfanin da ke sadar da kai, don ci gaba da samun hanyar sadarwa ba tare da matsala ba) da zarar ka bar wannan bigire, sai a share bayanan lambarka da ke wannan taska.

Authentication Center (AuC)

Bangaren Authentication Center rumbun bayanai ne na nau’ukan kalmomin shiga da masu lambobin sadarwa ke tsare layukansu da su. Misali, idan ka sanya wa layin sadarwarka PIN Code, to kalmomin da ka shigar na zarcewa ne kai tsaye zuwa Authentication Center. Wannan wani nau’i ne na tsaro ga masu layukan, inda babu wanda zai iya ganin asiran da suka taskance a layukan sadarwarsu sai su ko kuma wanda suka ga daman bashi kalmomin da suka shigar. Har wa yau, idan kana da PIN Code babu wanda zai iya katse maka sadarwarka ta kowace hanya ce, a halin da kake Magana da wani. Kowace irin na’ura yayi amfani da ita kuwa. Wannan tasa hukumar Amurka ta ki amincewa da wannan tsarin sadarwa na GSM, domin idan mutum ya bugo maka waya, ba za ka iya sanin daga ina yake bugo maka ba, sai in gaya maka yayi. Hakan na da wahalar ganewa domin dukkan layukan, lambobin kamfani daya suke amfani da su, kuma sun takaita ga kamfanonin sadarwan ne, ba wata jiha ko wasu birane ba. Sabanin tsarin sadarwar tarho na Landline, inda za ka iya sanin daga inda ake bugo maka. Amurka ta ki wannan tsari ne saboda dalilai irin na tsaro. Idan ana son gano inda kake, daga inda kake waya kawai ana iya tace maganan da kake yi da abokin maganarka; ana iya sanin daga bigiren da kake bugowa ko kake karban sakon, da dai sauran bayanai. Amma da tsarin GSM ba su iya wannan sam ko kadan. Ire-iren wadannan hanyoyi sun hada da PIN Code, da PUK Code, da kuma Security Code. Dukkansu a taskance suke cikin wannan rumbu ta Authentication Center.

Equipment Identity Register (EIR)

Wannan bangare ne ke dauke da dukkan sunayen wayoyin salular da ke dauke da layi ko lambar kamfanin sadarwan. Ma’ana, idan ka sayi layin MTN, ka sanya cikin wayar salularka nau’in Nokia 5320 XpressMusic misali, wannan bangare ne zai taskance nau’in wayar da kake amfani da ita, ya tabbata mai kyau ce wacce aka kera ta amfani da ka’idojin sadarwa ta duniya, mai kuma dauke da lambobin sadarwa ta duniya da bayaninsu ya gabata a sama, watau International Mobile Equipment Identity. Idan ba mai kyau bace, ko kuma bata cika wannan ka’ida ba, wannan bangare na Equipment Identity Register zai lika mata alamar “Invalid”, ma’ana wacce bata cika ka’ida ba, kuma ba za a iya amfani da ita ba. Haka idan aka sace maka wayar salularka mai dauke da layin sadarwanka a ciki, kana iya sanar da kamfanin sadarwanka, za su lika mata wannan alama ta “Invalid”. A wasu lokuta ma suna iya bata wayar idan kana so, ya zama barawon yayi aikin banza kenan. Amma ba duk kamfanin sadarwa ke yin haka ba, saboda tsoron keta da wani na iya ma wayar wani. Don babu aminci a tsakaninmu kuma mutane basu bin doka, shi yasa. Wadannan a takaice su ne manya kuma muhimman bangarorin da ke dauke cikin wannan babban zangon kamfanin sadarwa, watau Mobile Switching Center (MSC). A yanzu ga dan takaitaccen tsarin da kowane sako na kira ko text ke bi kafin isa ga wanda aka aika masa.

Tsarin Bugawa da Karban Kira ko Tes

Kana rike da wayar salularka mai dauke da lambar MTN misali, a zangon (Cell Tower da ke) Jimeta, sai ka buga wa abokinka da ke wani wuri don son yin Magana da shi. Kada mu fadi sunan bigiren da yake a yanzu. Kana bugawa, Base Transceiver Station (BTS), watau na’urar da ke aikawa da sako tsakanin wayar salularka da ke wannan kadadan sadarwa zuwa tashar Cell Tower da ke wannan wuri ta dauki wannan sako ko bukata taka, ta mika wa na’urar Switching Center, watau babban zango mai dauke da manyan bangarorin da bayanansu suka gabata a sama. Ita kuma Switching Center sai ta lalubo bangaren Home Location Register don sanin ko wanda kake son Magana da shi yana zangon da kake ne ko kuma a wani zango daban yake. Ko kuma shigowa yayi a matsayin “bako”. Idan bako ne shi, ma’ana ba a wannan zangon lambarsa take, sai Home Location Register ta binciko kundin adana lambobin baki da suka shigo wannan zango, watau Visitor Location Register, don nemo wannan lamba da kake nema na abokinka. Amma idan a zango daya kuke da shi, to ba sai ma ta je Visitor Location Register ba; daga Home Location Register kawai za ta sheda mai lambar. To da zarar an samu lambar, sai Mobile Switching Center ta cilla wa bangaren Equipment Identity Register, wacce aikinta ne taskance dukkan wayoyin salular da ke dauke da lambobin sadarwan wannan kamfani, don tabbatar da cewa wayar abokinka ta cika ka’idar sadarwa na lambobin da muka kawo bayanansu a sama, da kuma cewa ko an kera wayar a tsarin ka’idojin sadarwa ta duniya ko a a. Idan ta samu wayar na dauke da alamun “Invalid”, sai ta mayar da wannan bukata taka, cewa baza ta iya sadar da kai ta wannan waya ba. Amma idan garau wayar take, ta kuma cika ka’ida, to sai babban zango, watau na’urar Mobile Switching Center ta mika sakonka kai tsaye, sai yaji wayarsa ta fara bugawa; kai ma za ka ji haka, a naka bangaren. Sai sadarwa ya wakana a tsakaninku. Duk wannan kai-komo na iya samuwa ne cikin kasa da dakiku goma (10 seconds), muddin babu wata matsala a yanayin sadarwa, watau Network.

To amma watakil mai karatu zai ce mai yasa wasu lokuta ga-ka-ga-mutum, idan ka buga layinsa sai ace maka ba ya nan; alhali wayarsa a kunne take, kuma ta cika dukkan ka’idojin da ake bukata? Hakan na faruwa ne daga tsarin sadarwan kamfanin, musamman idan yanayin sadarwan na yin sama da kasa. Kada mu mance, nace mana tsarin sadarwa ta hanyar salula na samuwa ne ta hanyar siginar rediyo, wanda kuma ta hanyoyin wayar-iska yake bi. In kuwa haka ne, ashe akwai watakilancin samuwan tsaiko wasu lokuta. Ka kwatanta hakan da irin ingancin sautin rediyo da kake ji a wasu lokuta daban-daban. Me yasa wasu ke kama tashar rediyon Kaduna garau, amma wasu sai sun fita kofar gida kafin su samu. Hakan ya ta’allaka ne ga dalilai biyu; na farko shine ingancin yanayi ko gyaruwansa, dangane da iskar da ke bugawa a sararin samaniya. Bicike ya nuna akwai alaka na kut-da-kut tsakanin sakonnin da ke bin hanyoyin iska a sararin samaniya, da kuma irin yanayin da ke wannan bigire. Idan akwai hadari kuma ana cida da walkiya, yanayin sadarwa musamman ta rediyo kan samu matsala. Haka ma sadarwa ta Intanet, ta kan samu matsala. Hatta masu kallon tashoshin tauraron dan Adam ta NileSat, sukan samu matsala da zarar an fara ruwa. Wannan kenan. Abu na biyu kuma shi ne inganci ko nau’in na’urar da ke aikawa ko karban wannan sako. A yayin da tashoshin NileSat ke yayyankewa idan aka fara ruwa ko hadari ya hadu, masu kallon tashoshin DSTV ba su samun wannan matsala ko kadan. Me yasa? Don tsarin NileSat na cafke siginarsa ne ta amfani da tauraron dan Adam nau’in KU-Band. Su kuma kamfanin DSTV na amfani da tauraron dan Adam mai cafko bayanai nau’in C-Band, wanda yanayin iska da ke sararin samaniya ba ya cikakken tasiri a kansa. Wannan tasa za ka ga masu wayar salula nau’in Nokia sun fi kowa samun yanayin sadarwa mai kyau, fiye da masu amfani da wayar Motorola. Idan ka je inda babu yanayi mai kyau, baza ka samu matsala ba muddin wayar Nokia kake da ita. Amma Motorola ta dinga maka tsowa kenan, don sanar da kai cewa “yanayi ya dauke”, “yanayi ya dawo”. A gafarce ni, ba talla nake wa kamfanin Nokia ba, kawai misali nake bayarwa. Wadannan sune manyan dalilai biyu da ke haddasa samun matsalar sadarwa. Amma bayan wadannan, babu wani matsala kuma sai wanda ya ta’allaka da wanda kake son samu; ko dai ya zama yana Magana da wani a yayin da ka buga masa, sai a ce maka “Network Busy”. Ko kuma ya zama wayarsa na kashe a lokacin da ka kira.

Monday, April 19, 2010

Samuwar Haske da Tsarinsa a Kimiyyance (1 & 2)

Wannan ita ce kasidar da aka fara bugawa a Jaridar AMINIYA ta ranar 16 – 22 na watan Afrilu.  Kasancewar jigonta ya ta’allaka ne da tsarin Kimiyyar Sinadarai, ta sa na sanya ta a Mudawwanar “Kimiyyar Kere-Kere” da ke http://kimiyyah.blogspot.com.  Sai a zarce can don samun kasidar gaba dayanta. 

A sha karatu lafiya.

Baban Sadik

Friday, April 9, 2010

Sakonnin Masu Karatu ta Tes

Ban Hakuri

Sabanin yadda nayi alkawri cikin shekarar da ta gabata cewa a duk mako zan rika buga sakonnin tes ko na Imel da masu karatu ke aikowa, tare da amsa su, hakan bai faru ba saboda shagala irin tawa. Da fatan za a min hakuri kan abinda ya wuce, kuma zan ci ga da ganin cewa na lazimci wannan dabi’a, don tafi sauki. A yau zan amsa dukkan sakonnin tes da kuka aiko a baya, sannan kuma a makonni masu zuwa in ci gaba da bin tsarin da nayi alkawari. Kamar kullum, muna mika godiyarmu ga dukkan masu aiko da sakonnin godiya da gamsuwa, da masu bugo waya don yin hakan su ma; musamman ganin cewa baza mu iya ambaton sunayensu ba, saboda yawa da kuma maimatuwan hakan a lokuta dabam-daban. Mun gode matuka.

Mu’amala da Intanet a Wayar Salula

Salamun Alaikum Baban Sadik, don Allah ko zan iya saukar da Opera Mini a cikin waya ta nau’in “Sagem My X-7”, don shiga Intanet a saukake? - Dalibinka, Abdu Maigyada, Jas: 07031297258.

Malam Abdu Maigyada sannu da kokari, kuma mun gode da wannan sako naka. Saukar da manhajar “Opera Mini” a wayar salula ba wani abu bane mai wahala. Sai kaje inda ake shigar da adireshin gidan yanar sadarwa a wayar, ka sanya wannan rariyar likau din: http://mini.opera.com. Idan shafin ya budo, sai ka zabi zubin (version) manhajar (“Version 4.2”), ka matsa. Nan take wayarka zata saukar da manhajar a cikinta, sannan ta tambayeka ko kana son a loda maka wannan manhaja ta yadda zaka iya amfani da ita. Idan ka amsa, sai ta loda maka. Daga nan sai kaje inda aka ajiye maka ita, don ci gaba da amfani da ita. A karshe, ka tabbata kana da rajista da kamfanin wayarka, in kuwa ba haka ba, to baza ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar ba. Da fatar ka gamsu.

Assalaamu Alaikum, don Allah ka taimaka min wajen samar da hanyar karanta jarida ta hanyar Intanet a waya ta. Wayar ita ce “TECNO 570”. - 07084085752

Bayanai kan yadda ake iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula sun sha maimaituwa a wannan shafi. Amma a gurguje, kayi rajista da kamfanin wayarka don samun damar iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, sannan ka tabbata akwai ka’idojin WAP da ke taimaka ma wayar salula yin hakan. Wadannan, a takaice, su ne muhimman hanyoyin. Idan ana tare damu cikin silsilar da muka faro kan Wayar Salula da dukkan tsare-tsarenta, za a samu cikakken bayani in Allah Ya so. Da fatan za a amfana da dan abinda ya samu yanzu. Mun gode.

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan kana cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin. Don Allah ina son ka sanar dani game da yadda zanyi saitin fasahar Intanet a waya ta. Domin duk sadda na tashi don na ziyarci shafin yanar sadarwa, sai a ce dani: “GPRS Not Subscribed”. Da na tuntubi kamfanin layin wayar, sai su ce: “Cannot Send Setting to this Type of Phone, Please Visit www.mtnonline.com. Idan na tuntube su, sai suce bazan samu damar tuntuba ko kuma “Subscribe” din “GPRS” ba. To ko akwai wata hanyar da zan bi ba tare da ita “General Packet Radio Service” ba? Da fatan za ka amsa min. - Mustafa Rabi’u, Kano: 08131904162

Malam Mustafa sannu da kokari. Lallai ka sha zagaye-zagaye. Kuma ga shi baka gaya mana nau’in wayar da kake amfani da ita ba. Domin ba kowace irin waya bace ke karba, tare da iya sarrafa sakonnin da kamfanin waya ke aiko mata. Abinda wannan ke nufi shine, sai an je an sanya maka dukkan ka’idoji da kuma kalmomin da ake bukata, da hannu, watau “manual configuration”. A ka’ida, kamata yayi ace da zarar kamfanin waya ya aiko sakon tes, wayar ta kalli sakon da ya aiko. Idan na mai wayar ce, sai ta adana masa, tare da sanar dashi cewa ya samu sako. Idan kuma sako ne irin wanda waya ke iya sarrafa shi nan take, za ta ajiye masa ne. Da zarar ya budo ya karanta, zai ga abinda ake bukatar yayi da sakon. Idan bai fahimci sakon ba, kuma yayi kokarin rufewa, wayar za ta sanar dashi abinda ya kamata yayi da sakon, ta hanyar tambayarsa. Wannan na yiwuwa ne a galibin wayoyin salula na zamani, kuma na asali. Akwai wasu wayoyin da ba a tarbiyyantar dasu yin hakan ba tun wajen kera su. Ire-iren su sune irin wayoyin da ke zuwa daga kasashen Asiya. Shawarata a nan ita ce, kaje wajen duk wani mai gyarar wayar salula da ka sani, kwararre (zan maimaita: kwararre), don ya maka saitin wayar da hannu. Allah sa a dace, amin.

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina amfani da waya nau’in SonyEricsson Z520i, don Allah ina son a taimaka min da yadda zan rika aikawa da sakonni da bude su idan an aiko mani. - Ibn Fiqh, Saabiqus-Thabaty, Trikania, Nassarawa, Kaduna: 08131392572

Malam Saabiq barka da war haka, da fatan ana lafiya. Baka sanar damu ko a halin yanzu kana iya mu’amala da fasahar Intanet a wayarka ba. In kana iyawa, sai kaje inda ake shigar da adireshi a wayar, ka sanya: http://mobile.yahoo.com/mail/p Ga masu amfani da wayar salula nau’in “iPhone”, su shigar da: http://mobile.yahoo.com/mail/iPhone Wannan shine adireshin shiga manhajar Imel na kamfanin Yahoo! a wayar salula. Shafi zai budo inda zaka shigar da suna (username) da kalmomin shiga (password), sannan ka matsa inda aka rubuta “login” ko “enter”, don shiga. Idan ka shiga, za ka ga sakonninka, sai ka matsa duk wanda kake son karantawa. Idan kuma sako kake son aikawa, sai ka dubi sama a shafin, za ka ga alamar “compose”, sai ka matsa. Shafin allon rubutu zai budo maka, sai ka shigar da adireshin wanda kake son aika masa, ka gangaro kasa don shiga allon rubutun, in ka gama rubutawa kuma, sai ka gangaro kasa har wa yau, ka matsa alamar “Send”, don aikawa. Idan baka mu’amala da Intanet a wayar, sai ka nemi kamfanin wayarka ya aiko maka da tsarin da zai taimaka maka wajen yin hakan. Gamsassun bayanai kan wannan tsari na nan tafe a silsilar da muka faro kan wayar salula. Da fatar ka gamsu.

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Bayan haka, wai shin don Allah me yasa idan kana lilo a Intanet ta wayar salula, baka samun shafin da ka ziyarta gaba dayansa, ba kamar yadda kake samu ba idan a kwamfuta ce, sai dai kawai a dan tsakuro maka wasu bayanai? - Ahmad M. Umar, Na’ibawa, Kano: 07068196146

Malam Ahmad barka da war haka. Ai “kama da wane, bata wane”. Ma’ana, babu yadda za a yi a samu daidai tsakanin shafin kwamfuta da na wayar salula wajen bayyana shafukan gidajen yanar sadarwa a wayar salula. Saboda girman shafukan da ke gidajen yanar sadarwar, baza su yi daidai da girman shafin da ke wayar salula ba. Abu na farko kenan. Abu na biyu kuma shine, a halin yanzu galibin gidajen yanar sadarwa suna kera shafuka na musamman da wayoyin salula ke iya shigansu ba tare da wata matsala ba. Zaka samu muhimman abinda kake bukata a shafin baki daya. Gidajen yanar sadarwa na manyan kamfanonin kwamfuta irinsu “Yahoo!”, da “Google” da “MSN” duk suna da irin wannan tsari. Don haka idan kana amfani da rariyar lilon da ke wayar ne (watau “Phone Brower”), wacce wayar ta zo dashi, to kana iya samun shafuka wadanda suka dace da yanayin wayarka. Da zarar ka shiga shafin, sai a loda maka wadannan shafukan na musamman da suka dace da wayar. Amma idan kana amfani ne da “Opera Mini”, misali, kana iya zuwa wajen “Settings”, ka tsara masarrafar ta yadda shafukan da ka shiga zasu rika budowa daidai da yanayin wayarka. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu Alaikum, don Allah me yasa wayoyin salula na kasar Sin (China) basu iya shiga Intanet? - Sa’idu Danjuma, Kawo, Kaduna: 08096420965

Malam Danjuma, ban taba amfani da wayoyin salula na kasar Sin ba, amma nakan ji jama’a na korafi kansu sosai. Tabbas na gansu, na kuma shiga cikinsu don ganin yanayi da tsarinsu a fasahance. Suna da nakasu sosai ta bangaren sadarwa da mu’amala da wata waya ‘yar uwanta. Don haka, matsalar rashin iya mu’amala da fasahar Intanet a wayoyin Sin na komawa ne zuwa ga dayan dalilai biyu: na farko, ko dai ya zama saboda yanayin kiransu ne – ma’ana basu da ingancin da zasu iya taimakawa wajen yin hakan ta dadi. Na biyu kuma yana iya zama saboda rashin samun sinadaran da zasu taimaka mata don yin haka daga mai wajen mai ita ne. Misali, dole ne a samu tsarin da ke taimaka wa waya daga kamfanin waya, watau “Configuration Settings” kenan, kuma ya zama wayar tana da ka’idar mu’amala da Intanet, watau “Wireless Application Protocol”, ko “WAP” a gajarce. Da fatan ka gamsu.

Salamu Alaikum, ina son na kwafi bayanai daga Mudawwanar “Fasahar-Intanet” zuwa waya ta, amma da zarar na fara, sai ta nuno min: “out of memory”. Ya lamarin yake ne? - Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07027275459

Idan haka ta kasance, hakan ke nuna cewa ma’adanar wayar salularka bata iya daukan yawan bayanan da kake son zuwa mata daga shafin da ka kwafo su. Don haka ka tabbata kana da wuri ko ma’adana mai yawa da zai iya karban mizanin bayanan da kake son kwafowa zuwa wayar. “out of Memory” na nufin mizanin ma’adanar wayarka yayi kadan ga bayanan da ka kwafo. Da fatan ka gamsu.

Kwayar Cutar Wayar Salula

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kai da abokan aiki kuna cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin. Shin da gaske ne wai kamar yadda na’ura mai kwakwalwa ke harbuwa da cuta (virus infection), haka ma wayar salula (irinsu Nokia E-Series da makamantansu) ke harbuwa da cutar? Kuma ko mutum zai iya sa wa wayarsa kariya, watau Anti-virus? - Uncle B. Bash, Jimeta, Yola: 07069045367

Dubun gaisuwa da fatan alheri ga Uncle Bash, da fatan ana cikin koshin lafiya. Tabbas haka ne; wayoyin salula na kamuwa da kwayoyin cuta kamar yadda kwamfutoci ma ke kamuwa. Domin kusan duk tsarinsu iri daya ne. Kai ba ma su kadai ba, hatta na’urorin janyo siginar tauraron dan Adam na zamani da muke amfani dasu wajen kallon tauraron dan Adam (watau “Satellite Receivers” ko “Decorders”), duk suna iya kamuwa da kwayoyin cutar. Babban dalili kuwa shine, saboda tsari da kimtsin ruhin da suke amfani dashi duk iri daya ne. Ana iya sanya wa wayar salula manhajar kariya da goge kwayoyin cuta, watau “Anti-virus”. Akwai manhajoji na musamman da aka gina don wannan aiki. Wasu kyauta ake samunsu. Wasu kuma sai da kudi. Yana da kyau mai karatu ya san cewa samun wadannan manhajoji kyauta a wajen masu sanya abubuwa a wayar salula da muke dasu a biranenmu, ba zai iya kare wayar daga kamuwa ba, sai ana kara wa manhajar tagomashi ta hanyar Intanet, don tabbatar da cewa ta haddace sunayen dukkan kwayoyin cutar da ke rayuwa a zamanin da take. Wannan shi ake kira “Virus Update”, kuma kana iya yin hakan ne ta hanyar manhajar, idan akwai ka’idar Intanet a wayar. Idan kaje inda ake yin “Update” din, ka matsa, za a shige da kai ne kai tsaye zuwa shafin kamfanin da ya kirkiri manhajar, don bai wa manhajar damar haddace sabbin sunayen kwayoyin cutar da bata sansu ba. In kuwa ba haka ba, to babu wani amfani da za a samu na kariya, wai don an sanya ma waya wannan manhaja. Da fatan ka gamsu.

Salam, don Allah ka taimaka min da inda zan yi da kwayar cutar kwamfuta a waya ta, watau Virus. Don suna tayar min da hankali. Ka huta lafiya! - 08023672341

Shawarar da zan bayar ita ce, aje a samu masu gyarar wayar salula don su duba wayar. Don a nan bazan iya sanin wasu dabi’u take nunawa ba balle in san shin kwayar cutar kwamfuta ce ta kama ta ko a a. Amma idan aka je wajen masu gyara, suna iya fahimtar hakan. Allah sa a dace.

Shawara kan Kwarewa a Ilmin Kwamfuta

Assalam Baban Sadik, Allah Ya kaddare ni da karanta kasidarka mai taken: “Hanyar Sadarwa ta Rediyo a Intanet”, wadda ka rubuta a jaridar AMINIYA tun watan Agustar bara (2008), kuma nayi murna musamman ma da na ga wanda ya rubuta ta musulmi ne. Bayan haka, nayi Difloma kan Ilmin Kwamfuta amma har yanzu ban samu kwarewa mai zurfi ba a fannin Intanet, amma wasu hanyoyi suka kamata na bi? Wassalam - 08063446395

Malam barka da war haka, kuma mun gode da wannan sako na neman shawara. Ya danganci abinda kake nema ko son kwarewa a kai. Idan so kake ka dauki fannin Intanet a matsayin fannin kwarewa da cin abinci, sai ka sake neman makarantun da ake koyar da ilmin kwamfuta, don yin nazari na musamman a kai. Idan kuma a matsayin fannin sha’awa ne kawai da motsa kwakwalwa, sai ka lazimci ziyartar gidajen yanar sadarwa don sabawa da fasahar. Kwarewa kan fasahar Intanet ba karatu bane tsantsa, a a, aikata abinda aka koyo ne lokacin karatu. Wannan, a takaice shine abinda zan iya cewa. Ina kuma rokon Allah ya baka juriya da kwazo da dagewa kan abin. Da fatar ka gamsu.

Girgidin Jirgi a Saman Tsauni

Malam Abdullahi nakan ji wasu suna cewa: idan jirgin sama yazo saitin tsaunuka, ana fahimtar jirgin yana girgiza. Me ye gaskiyar lamarin ne? - Khalil Nasir Kuriya, Kiru: 07069191677

Malam Khalil barka da kokari. Watau wannan Magana haka take: lallai jirgi kan girgiza idan yazo saman tsauni a halin tafiyarsa. Ba ma tsauni kadai ba, ko cikin hazo ya shiga akan samu irin wannan girgiza…kaji kamar a saman duwatsu kuke tafiya. Duk wanda ya taba hawa jirgin sama, zai tabbatar maka da hakan. Bayan wadannan wurare har wa yau, idan jirgi yazo saman teku ma, yana iya samun wannan cikas. Babban dalilin da ke haddasa wannan cikas da jirgi ke samu kuwa shine idan iskar da ke sama ta kara kiba da tumbatsa zuwa sama ko kasa ko kuma gefen dama da hagu, sanadiyyar wani abinda ya tare ta a halin tafiyarta. Misali, idan iskar da ke can sama na tafiya daga gabas ne zuwa yamma, a guje, da zarar taci karo da wani tsauni, nan take sai iskar ta takura wuri guda, tayi toroko zuwa sama, ko kasa, ko kuma gefen dama da hagu. To idan aka yi sa’a (ko rashin sa’a) jirgi yazo saman wannan tsauni a daidai lokacin da iskar taci karo dashi, sai ya fara girgiza, saboda sauyin yanayin iska da ya samu. Idan a baya yana tafiya ne lafiya lau, yanzu iskar da tsaunin ya kado zuwa sama, zai kara tunkuda jirgin sama ko kasa, ko kuma zuwa wani gefe daban. Haka abin yake idan jirgi ya shiga cikin hazo. Domin shigansa cikin hazon na sauya masa yanayin iskar da ya baro a kasa ko can sama ne. Wannan tsari na sauya wa jirgi yanayin tafiyarsa sanadiyyar sauyin yanayin iska da ke sama, shi ne Malaman Fiziya (Physics) ke kira “Turbulence”. Da fatan ka gamsu.

Tasirin Wayar “Fiber-Optics” Wajen Sadarwa

Salam, tare da fatan alheri, ina fatan dukkan makaranta wannan fili muna lafiya, amin. Baban Sadik, wai ita wannan waya da kamfanin MTN take sanyawa a kasa, mene ne amfaninta ga sadarwa? Kuma mutane suna cewa tana hade da sadarwa irin ta Intanet wajen sauri; meye gaskiyar al’amarin? - Ibrahim Yahaya Mai Ruwa Dan-hutu: 07080948888

Malam Ibrahim Dan-hutu lallai wannan tambaya ce mai muhimmanci ga harkar sadarwa kowane iri ne kuwa. Ina fatan Allah ya bamu lokaci na musamman don mu gabatar da doguwar kasida kan yadda wannan tsari ke aiki. Da farko dai abinda kaji ana fada na alakar da ke tsakanin wannan waya da ake binnewa a karkashin kasa da kuma sadarwa ta wayar tarho musamman, gaskiya ne ko shakka babu. Na biyu kuma, wannan waya da ake shimfidawa, ba waya bace kamar sauran wayoyi. Waya ce ta “kunun gilasai”, wadda aka tsattsaga gwargwadon kaurin silin gashin kai. Yadda abin yake shine, gilasai ake narkawa, ko damawa, kamar kunu, sannan a sandarar dashi, tare da yayyanka shi filla-filla, ko sille-sille, ko sili-sili, gwargwadon kaurin gashin kai, sannan a hada su wuri guda, a suturce su da gasassun robobi (plastics), sannan a maye samansu da dafaffiyar roba (rubber). Wannan nau’in waya ita ake kira “Fiber-Optics”, ko kuma “Optical Fiber Cables”. Kuma su ne wayoyin da suka fi saurin isar da sakonnin murya ko bayanai ko bidiyo, saboda suna tafiya ne a matsayin haske, cikin gaggawa ba bata lokaci. Idan kana son fahimtar yadda tsarin saurin isar da sako da wannan waya ke yi, ka dubi yadda haske ke saurin isa idan aka haska tocila daga bakin wani bututu, zuwa karshensa. Nan take zai isa. Idan ma bututun ba a saiti yake ba, sai ka dubi inda yake da kwana, ka sanya gilashi a wajen. Da zarar ka kara haskawa, dungun da ke dauke da gilashi zai cilla hasken zuwa gaba, har ya isa inda ake son yaje. To idan ka dubi wannan waya da aka kera da gilasai, sai ka ga cewa da zarar ballin haske ya sauka kan sillin waya guda daya, to duk zata haskaka sauran, tare da isar da hasken da ke dauke da bayanan cikin gaugawa. Wannan kuma ya shafi hasken da ke dauke da murya ne (Tarho da Rediyo), ko bayanai (Intanet), ko kuma hotuna masu motsi da daskararru (TV da Bidiyo), misali. Don haka kake ganin kamfanin MTN (da ma GLO) suna binne wannan waya, don inganta tsarin sadarwarsu tsakanin tashoshin sadarwarsu da suka game dukkan jihohin kasar nan. Kai ba nan kasar kadai ba, galibin manyan tekunan duniya na dauke ne da wadannan wayoyi a cikinsu, ko karkashinsu, wadanda kamfanonin sadarwa na kasashe dabam-daban ke binnewa don isar da sadarwa cikin gaugawa da sauki a duniya baki daya. Da fatan ka gamsu.

Sabuwar Mudawwana

Assalaamu Alaikum, Malam a duba min mudawwana ta da ke: http://munbarin-musulunci.blogspot.com, a Intanet. - Aliyu M. Sadisu: 08064022965

Malam Aliyu sannu da aiki. Lallai na shiga Mudawwanar “Munbarin Musulunci” da ka bude a Intanet, na kuma gamsu da irin sakonnin da kake isarwa na ciyar da al’umma gaba a Musulunce. Wannan aiki ne mai gwabin lada, kuma Allah Ya albarkaci wanann yunkuri taka, amin. Dangane da tsarin Mudawwanar kuma, ina ganin ba wata matsala. Domin kana shigar da kasidun yadda ya kamata. Illa dai abinda zan iya cewa shine, ka cire alamar ruwa biyu (watau :) da ka sanya a tsakanin “BARKA DA ZUWA” da kuma “MUNBARIN MUSULUNCI”. Kawai ka mayar dashi jumla guda, kamar haka: “Barka da Zuwa Munbarin Musulunci”. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Manhajar Canja Murya a Wayar Salula

Salamu Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: tsarin canje-canjen sautin murya na wayar salula, watau Magic Voices; Malam karin bayani nake nema dangane da yadda tsarinsa yake? - Aliyu Muktar Sa’id (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu sannu da aiki, kwana biyu bamu gaisa ba. Da fatan kana cikin koshin lafiya, amin. Tsarin “Magic Voices” a fannin sadarwar tarho ko wayar salula, shine tsarin da ke bai wa mai waya damar canja sautin muryarsa da aka sanshi da ita, zuwa wata murya dabam. Misali, kana iya canja muryarka ta koma ta mace, idan namiji ne kai, ko kuma ta zama siririya, idan babbar murya kake da ita. Hakan na faruwa ne cikin sauki a wayar salula sanadiyyar wata manhaja da aka kera wayar da ita. Sannan kana iya neman ire-iren wadannan manhajojin canjin murya ka sanya wa wayarka. Duk wanda ya kira ka, kafin ka amsa, kana iya canja muryarka. Maimakon ya ji asalin muryarka, sai yaji wata murya dabam. Sai dai kuma, idan ba tsananin bukata bace ta kama, bai dace a kullum mutum ya rika yaudarar mutane da wata murya ba: ko don ba ya son Magana dasu, ko don kauce musu. Yana da kyau a kullum mutum ya zama yana wakiltar kansa. Ire-iren wayoyin salular da ke zuwa da irin wannan tsari galibinsu daga kasar Sin (China) ake zuwa dasu. Da fatar ka gamsu.

Godiya da Yabo

“Yabon gwani ya zama dole”. A cikin duka shafukan AMINIYA, shafi na 16 (watau Shafin “Kimiyya da Fasaha”) shine gwani na, saboda ina karuwa dashi ainun, kasancewar ni mutum ne mai son mu’amala da na’urar kwamfuta da sauransu. Baban Sadik Allah ya kara maka basira a kan aikinka, amin. - Bashir (GZG964), Minna, Neja: 08034629830

Malam Bashir mun gode da wannan addu’a taka, kuma Allah ya mana jagora baki daya, kuma inda an ga kura-kurai cikin abinda muke ciyar da kwakwalen mutane, to don Allah a rika tunatar damu. Allah saka maka da alheri, amin.

Jakar “Recycle Bin” a Kwamfuta

Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: meye amfanin “Recycle Bin” a jikin kwamfuta? - Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu amfanin jakar “Recycle Bin” da ke shafi ko fuskar kwamfuta, shine taskance dukkan bayanan da ka goge ko share daga kwamfutarka. Kamar kwandon zuba shara ce, ko bola. Duk sa’adda ka goge wasu bayanai (delete) daga kwamfutar, an tsara kwamfutar ne ta yadda za ta rika zuba su a cikin wannan Kwando ko burgamin adana bayanai. Hikimar yin hakan shine, idan ka canza ra’ayi daga baya kaji kana bukatar abinda ka share ko goge, to kana iya bude wannan jaka, ka matsa jakar bayanin da kake bukata, za a mayar maka da jakar bayanin zuwa inda aka dauko ta da farko. Har way au, kana iya share karikitan da ke cikin wannan jaka gaba daya. Sai dai kuma idan ka share shikenan. Baza ka taba samun abinda ka zuba ciki ba. A takaice dai, aikin “Recycle Bin” shine ajiye maka share da ka sharo daga cikin kwamfuta. Idan kana bukata, kana iya komawa ka nemo su. Amma idan ka share su duka daga cikin jakar, shikenan. Da fatan ka gamsu.

Tsarin “GPRS” a Wayar Salula

Assalaamu alaikum, Baban Sadik ina fatan kana lafiya. Bayan haka, tambaya ta a kan GPRS ne: wani lokaci alamar “G” na bayyana a waya, wani lokaci kuma alamar “E” ne ke bayyana. Ko hakan me yake nufi, dangane da bambancin da wadannan haruffan? - Muhammad Abbass, Lafiya, Nassarawa: 08036647666

Malam Muhammad Abbass barka da war haka. Babu wani bambanci dangane da abinda wadannan alamu guda biyu ke nunawa a shafin wayarka a yayin da kake lilo ko mu’amala da fasahar Intanet. Bayyanar hakan shi ke nuna cewa kana mu’amala da fasahar Intanet ne ta hanyar tsarin “GPRS” da kamfanin wayarka ke da ita. Don haka, idan ka ga alamar “G” ko “E”, to duk suna nufin tsarin “GPRS” ne, wanda ke amfani da tsarin nau’in sadarwa ta “2G”. A wayoyin salula na zamani masu amfani da tsari ko nau’in sadarwa ta “3G” ko “3.5G”, alamar “3.5G” suke nunawa. Don haka idan kaga “E” ko “G”, to duk tsarin “GPRS” ne. Duk da yake wasu masana sun tafi a kan cewa alamar “E” na ishara ne zuwa ga ingantacciyar tsarin “GPRS” mai suna “EGPRS” (watau “Enhanced General Packet Radio Service”), mai amfani da tsarin sadarwa nau’in “2.5G”. Da fatan ka gamsu.

Majalisun Yahoo Groups

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, wane irin alfanu Internet Groups, irinsu Yahoo Groups ke dauke da shi? Malam mai zai hana ka bude wa wannan filin nashi? - Ahmad Muhammad Amoeva, Kano: 08066038946

Malam Ahmad abinda ake nufi da “Yahoo Groups” shine “Majalisun Tattaunawa ta Intanet”. Matattara ce inda mutane ke haduwa don tattauna wasu al’amura na rayuwa da addini. Wasu sun ta’allaka ne kan abinci, ko abin sha, ko tufafi, ko motocin hawa, ko zamantakewa, ko addini da dai sauransu. Tattaunawar ana yin ta ne ta hanyar sakonnin Imel. Da zarar ka shiga cikin majalisar ta hanyar rajista, duk sa’adda wani mamba ya aiko da sako, akwai wata manhaja ko masarrafar kwamfuta mai suna “Listserver” da ke cilla sakon ga dukkan mambobi. Sai ya zama abinda Malam “A” ya gani, shine abinda Malam “B” zai gani a jakar Imel dinsa. Shahararrun Majalisun Tattaunawa na harshen Hausa su ne: Majalisar Fina_finan Hausa, da Majalisar Marubuta, da Majalisar Nurul-Islam (wacce nake lura da ita), da kuma Majalisar Hausa-da-Hausawa. Wannan shawara ce mai kyau, kuma zan duba yiwuwar hakan in gani. Abinda wannan tsari ke bukata shine hadin kai da kuma lazimtar majalisar, don amfanuwa da abinda ake tattaunawa a ciki. Idan ma har na bude, to zai zama wajen tattaunawa ce da neman agaji kai tsaye ga dukkan masu matsaloli, kamar dai yadda ake yi ta hanyar tes. Tun farko ban yi hakan bane don tunatin cewa wayar salula a halin yanzu ta rinjayi rayuwar mutane. An fi karkata wajen aiko da sakonni ta hanyar wayoyin salula da hanyar Intanet. Wannan tasa na dan ja da baya. Amma dai, kamar yadda nace a sama, zan duba yiwuwar hakan nan gaba. Mun gode.

Asalin Launuka

Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta ita ce: meye asalin launuka (colours) ne? – Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu wannan tambaya ce mai muhimmanci, kuma kasancewar bayanai kan haka sun ta’allaka ne ga tsantsar Kimiyyar lissafi da halitta a lokaci guda, nake ba da hakuri cewa sai hali ya samu zamu yi zama na musamman, don gabatar da bincike na musamman kan haka. Amsa kan haka na bukatar gamsasshen bayani, wanda fili irin na amsa tambayoyi bazai iya bamu dama ba. Don haka nake neman afuwa sai zuwa wani lokaci. Na gode.

Tsarin ‘Yan Dandatsa (Hackers)

“Hackers” da “Botnets”: akwai wani bambanci ne a tsakaninsu, ko duk abu daya ne? Ka huta lafiya. - Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677

Ko kadan ba daya suke ba. A ilmin sadarwa ta kwamfuta, idan aka ce “Hackers”, ana nufin ‘yan Dandatsa kenan, masu amfani da kwarewarsu ta ilmin kwamfuta da dukkan hanyoyin sadarwa, wajen cutar da kwamfutocin mutane ko hukumomi ko kungiyoyi, a ko ina suke a duniya. Duk da yake wasu kan yi amfani da kalmar har wa yau wajen nufin kwararru kan ilmin kwamfuta da hanyoyin sadarwa a sake ba kaidi, su kuma yi amfani da kalmar “Crackers” ga nau’in kwararru na farko. Amma abinda yafi shahara a bakin mutane a duniya yanzu idan aka ambaci “Hackers”, shine kwararru masu ta’addanci ga kwamfuta. A daya bangaren kuma, kalmar “Botnets” kalma ce mai tagwayen asali. Daga kalmomin “Robot”, da kuma “Networks” aka tsago ta. A ilmin kwamfuta da tsarin sadarwa na zamani, idan aka ce “Botnets” ana nufin gungun kwamfutoci wadanda suka samo asali daga kasashe dabam-daban, da wasu ‘Yan Dandatsa suka mallake su ta hanyar miyagun masarrafan kwamfuta, kuma suke basu umarni don su darkake wasu kwamfutoci na musamman da ke wasu kasashe ko birane a duniya. Suna yin hakan ne ta hanyar amfani da kalmomi ko lambobin kwamfutocin da suke son darkakewa, watau “Internet Protocols” ko “IP Address” a turance. Don haka, Kalmar “Hackers” tana nufin masu yin dandatsanci. Ita kuma kalmar “Botnets” na nufin tsarin aikin ta’addancin da suke yi. Da fatar ka gamsu.

Aika Sakonnin Imel

Baban Sadik, tambaya ta ita ce: shin yaya zan yi in aika da sakon Imel ga mutane da yawa a lokaci guda? - Bashir, Minna, Naija: bashir.kasim@yahoo.com

Malam Bashir, aikawa da sakon Imel ga mutane masu yawa babu wahala. Idan ka budo allon rubutu, watau “Compose”, sai ka shigar da adireshin wadanda kake son aika musu a filin da aka rubuta “To”. Idan ka rubuta adireshin farko, sai ka sanya alamar wakafi (watau “comma” - , -), sannan ka sanya na biyu, ka sa wakafi, ka sanya na uku, ka sa wakafi…har sai ka sanya dukkan adireshin wadanda kake son aika musu. Wannan haka tsarin yake: a kwamfuta kake, ko a wayar salula. Da fatar ka gamsu.

Wayoyin Salula Masu Katin SIM Biyu

Salam Malam, sai naga layin MTN a wayar salula mai Katin SIM guda biyu, yana komawa “MNT”. A wata wayar kuma, layukan suna komawa lambobi maimakon sunan kamfanin wayar. - Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07027275459

Malam Khalil, ta yiwu akwai matsala tare da wayar. Don kusan dukkan wayoyin salula na zamani suna da manhajar da ke iya nuna sunan kamfanin wayar da aka sanyan musu katin SIM dinsa. Idan kaga wayar na nuna maka “MNT”, maimakon “MTN”, a iya cewa matsalar daga wayar ce, ba daga kamfanin wayan ba. In kuwa daga kamfani wayan ne, to bai kamata ya zama a wayarka ce kadai matsalar ba, musamman a bangaren da kake. Kamata yayi a ce dukkan masu amfani da katin MTN su ma nasu ta rika nuna “MNT”. A daya bangaren kuma, rashin nuna sunan kamfanin waya a fuskar waya kuma, ya danganci kirar wayar. In har wayar ‘yar asali ce (irin nau’in “Samsung” mai katin SIM guda biyu, ‘yar asali), ba irin kirar Sin ba, ya kamata ta nuna. Amma idan kirar Sin ce, ba matsala idan bata nunawa. Hakan na iya zama nakasa ce daga kamfanin da ya kera wayar; ma’ana bai tarbiyyantar da ita yin hakan ba. Da fatan ka gamsu.

Me Ke Cin Batir a Wayar Salula?

Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta dangane da wayar salula ce: shin da kira, da amsa kira, wanne ne yafi cin batirin waya ne? - Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Ya danganci tsarin mu’amala da wayar. Idan wayar salula tana ajiye a kunne, ba a amfani da ita, bata cin batir sosai. Kamar mota ce ka tayar da ita, ka barta tana diri (slow). Idan kana shiga wurare don shigar da lamba ko gogewa ko wani abu daban, cin batirinta yafi na lokacin da take ajiye babu komai. Idan kuma kana sauraron wakoki, ko kallon talabijin, ko sauraron rediyo, ko yin wasa (da “games”) da sauran makamantansu, cin batirinsa yafi na yanayin baya. A karshe, idan wayar tana mu’amala da wata wayar, ta hanyar aika sako ta Bluetooth ko Infra-red ko Kwamfuta, ko kuma tana halin kara sanadiyyar kira (ringing), ko yanayin amsa kira ko yin kira da Magana da abokin kira, ko neman balas, ko neman yanayin sadarwa (Network Search), wayar tafi cin batir sosai. A takaice dai, idan waya tana mu’amala da wata wayar (ta hanyar kira ko amsa kira ko karba ko aika bayanai), ko kuma tashar sadarwar kamfanin waya (Telecom Base Station), tafi cin batir sosai. Illa dai yanayin cin ya danganci tsawon lokacin da aka dauka ne ana kira ko amsa kiran, ko aikawa da sakonnin ko karbansu. Da fatan