Saturday, December 4, 2010

Dandalin “Facebook” (1)

Mabudin Kunnuwa

Babu wani dandalin Intanet da ya samu shaclip_image002hara da ambato irin wanda Dandalin Facebook yake samu a halin yanzu. Nan ne matattarar samari da ‘yan mata; matattarar masana da masu neman sani; matattarar masu neman bayanai da masu samar da su; matattarar masu saye da masu sayarwa; matattatar masu bincike da wadanda ake bincike kansu; matattarar malamai da dalibansu; matattarar shuwagabanni da wadanda ake shugabanta; matattarar masarrafai da masu samarwa da kuma masu amfani da su; matattarar masu leken asiri da wadanda ake leken asirinsu. Kai a takaice dai, idan kace Dandalin Facebook ya tattaro “kowa da kowa” daga “ko ina da ko ina”, a mahangar zamani, to baka yi karya ba.

Duk da cewa akwai wasu dandalin a Intanet, inda ake taruwa kamar clip_image004irin taruwar da ake yi a Dandalin Facebook, ko ake bincike kamar yadda ake yi a nan, sai dai akwai bambancin tsari da yanayi da kuma tasiri a tsakaninsu. Wasu cikin dandamalin da ake da su dai sun hada da Dandalin MySpace, da Dandalin NetLog, da Dandalin Jhoos, da Dandalin hi5, da Dandalin LinkID, da dai sauransu. Wadannan sababbin dandamali ne suka kashe wa majalisu da wuraren shakatawa da ake da su a Intanet a baya, irinsu: Yahoo! Messenger, da Windows Live Messenger, da ICQ, da AOL Messenger, da majalisu irinsu Yahoo! Groups, da Google Groups, da sauran makamantansu. Duk da cewa wadannan majalisu da wuraren tattaunawa suna nan har yanzu, amma hankalin galibin mutane, musamman samari da ‘yan mata, ya fi komawa kan wadannan dandamali da na zayyana a sama. Shin meye ake yi a cikinsu? Yaya aka yi suka samo asali? Wa ya samar da Dandalin Facebook kuma yaushe? Yaya tsarin Dandalin Facebook yake? Me ya bashi shahara? Me ye amfanin da ke tattare da wannan dandali na Facebook? Shin akwai matsaloli da ke tattare da amfani da wannan dandalin? In eh, wasu matsaloli ne ake da su kuma ina dalilan samuwarsu? Wadannan ne, da ma wasu tambayoyi masu nasaba da su, muke son gabatar da bincike kansu a mahangar ilimi da bincike, ba wai a mahangar labarin baka kadai ko shaharar baki ba. Sai dai kafin nan, zai dace mai karatu ya fahimci wani sabon tsarin samar da bayanai a Intanet, wanda kuma hakan ne ya dada taimakawa wajen samar da ire-iren wadannan wuraren shakatawa a Intanet.

Tsarin Samar da Bayanai a Intanet

Tsarin samar da bayanai a Intanet ya kasu kashi biyu, tun sa’adda aka kirkiri wannan fasaha mai matukar tasiri a rayuwar mutane. Tsarin farko shi ne tsohon tsari; watau hanyar samar da bayanai ta gidan yanar sadarwa. Wannan shi ne tsohon yayi, kuma shi ne abin da a farkon zamanin mu’amala da fasahar Intanet ya shahara. Duk wanda ke neman bayanai kan wasu abubuwa ko wani fanni na ilmi, to a gidan yanar sadarwa (watau Website) zai samu. A wancan lokacin kuma galibin masu gidajen yanar sadarwa duk basu wuce malaman makaranta ba, ko masu sha’awar yada ilmi ta hanyar bincike a Intanet, ko kuma hukumomin gwamnati masu kokarin sanar da al’umma halin da hukuma ke ciki. Nau’ukan bayanan da ake samu ta wannan hanya ko tsari kuwa sun hada da tsagwaron bayanai – kamar kasidu da makaloli ko baituka da dai sauransu – da hotuna da kuma hotuna masu motsi, watau bidiyo kenan. A wannan zamani ko tsari, mai gidan yanar sadarwa – mutum ne ko hukuma ko kamfani – shi ke zuba irin bayanin da ya ga dama, a yanayin da yayi masa, a kuma irin tsarin da ya dace da manufarsa.

Da tafiya tayi nisa, harkar kasuwanci ta fara habaka a duniyar Intanet, sai ‘yan kasuwa suka shiga binciken sanin hanyoyi ko irin bukatun da masu sayen hajojinsu a Intanet ke da su ko suke bi. Wannan ta sa aka fara kirkirar gidajen yanar sadarwa ko mudawwanai masu baiwa mai karatu ko mai ziyara ko mai sayen wata a haja a gidan yanar sadarwa damar fadin albarkacin bakinsa kan hajar ko abin da yake so ko yake sha’awa. A daya gefen kuma sai ga manyan gidajen yanar sadarwa – irin su Yahoo!, da MSN, da Google - sun kirkiro hanyoyin da masu ziyara ke haduwa suna tattaunawa kan bukatunsu na rayuwa, da dandanonsu kan rayuwa, da abubuwan da suke bukata, da dai sauran abubuwan da suka shafe su. Hakan kuwa ya samu ne ta hanyar Majalisun Tattaunawa da Zaurukan Hira (watau Cyber Communities – ko “Kauyukan Intanet”), wadanda kuma suka hada da Groups, da Internet Chat Rooms, da Communities, da kuma Bulletin Board ko Forums. A wadannan wurare, masu karatu da masu ziyara da masu saye da sayarwa ne ke tattaunawa a tsakaninsu kan bukatunsu da dandanonsu. Kuma wannan tsari, a harshen Kimiyyar Sadarwa ta Zamani, shi ake kira User Content; watau tsarin samar da bayanai ta hanyar mai ziyara.

Wannan tsari ne ya zaburar da masu sauran gidajen yanar sadarwa a Intanet, inda suka fara sanya kafofin jin ra’ayoyin masu ziyarar gidajen yanar sadarwarsu, ko masu karatun makaloli da kasidun da suka taskance a Mudawwanansu. Haka gidajen yanar sadarwar jaridu da mujallu, duk suna da wannan tsari. A karshe dai, dukkan bayanan da masu karatu ko masu ziyara ke rubutawa ko sanyawa, ana taskance su ne a kwamfutocin masu gidan yanar sadarwar. Kuma wadannan bayanai na masu karatu ko ziyara na cikin nau’ukan bayanan da manhajojin Matambayi Ba Ya Bata (Search Engines) ke nannado su, don baiwa masu neman bayanai kan fannoni daban-daban a Intanet a yau. Samuwar wannan tsari ne har wa yau, ya haifar da samuwar ire-iren dandamalin abota da ake da su a Intanet a yau, irin su Facebook, da NetLog, da JHoos, da LinkID da dai sauran makamantansu.

Dandalin Abota a Intanet (Social Network)

A mahangar Kimiyyar Sadarwar Zamani, idan aka ce “Social Network” ana nufin dandalin shakatawa da yin abota. Wuri ne ko kace “Dandali” ne da ke hada mutane daga wurare daban-daban, masu launi daban-daban, masu harshe daban-daban, daga wurare daban-daban, masu matsayi daban-daban, masu matakin ilmi daban-daban, kuma masu manufofi daban-daban. Haduwar wadannan mutane a “waje daya” shi ke samar da wani dandali budadde, mai kafofi daban-daban, inda kowa ke zaban abokin huldarsa ta hanyar masarrafa ko manhajar kwamfuta da aka kirkira a irin wannan dandali. Kafin mu yi nisa, yana da kyau mai karatu ya san cewa wannan dandali ba wani abu bane illa wani gidan yanar sadarwa ne na musamman da wasu ko wani kamfani ko mutum ya samar da shi don wannan manufa. Manufar a farko ita ce samar da muhallin da mutane za su tattauna da juna ta hanyar yin abota da yada ra’ayoyinsu kan wasu abubuwa da suke sha’awa. Wannan manufar asali kenan. Amma a yau wannan manufa ta canza nesa ba kusa ba. Akwai manufar kasuwanci, da yada manufa, da samar da hanyoyin bincike kan dandanon masu ziyara ko masu tattaunawa a majalisar, da dai sauran manufofin da mai karatu zai ji su nan gaba.

Bayan haka, wadannan dandamali suna nan nau’uka ne daban-daban; akwai wadanda ake harkar abota ta hanyar samar da bayanai zalla, akwai wadanda kuma hotuna ne zalla ake taskancewa kuma su kadai ake yadawa wajen abotar. Akwai kuma wadanda musannan aka samar dasu don manufar tara kwararru kan fannonin ilmi ko kasuwanci daban-daban. A takaice dai, akan gane nau’in dandali ne ta hanyar suna ko nau’ukan masarrafai ko manhajojin da ake amfani da su don sadar da zumuncin aikawa da sakonni ko neman abokanai masu ra’ayi ko sana’a ko kwarewa irin wanda kake da ita. Amma abin da yafi shahara a wadannan dandamali shi ne harkar kasuwanci. A yayin da kake ganin kana iya bude shafi, ka sanya bayanai, ka nemo abokai, ka kuma aiwatar da sadarwa ta hanyar da kake so ba tare da ka bayar da ko ahu ba, a daya bangaren kuma an ci riba a kanka fiye da yadda kake zato. Babban abin da ya baiwa Dandalin Facebook shahara a kan sauran dandalin abota a Intanet shi ne samuwar hanyoyin mu’amala da juna da yada bayanai da kuma hanyoyin samarwa tare da kirkirar nau’ukan bayanai fiye da daya; daga tsagwaron bayanai zuwa hotuna daskararru da masu motsi (watau bidiyo), da dai sauran abubuwa masu kayatarwa. To ta yaya wannan Dandali na Facebook ya samo asali?

Yadda Aka Samar da Dandalin Facebook

Dandalin Facebook ya samo asali ne cikin watan Fabrairun shekarar 2004, kuma wanda ya kirkiri gidan yanar sadarwar dai wani matashi ne mai suna Mark Zuckerberg, wanda kuma a lokacin yake karatun fannin Kwamfuta a Jami’ar Harvard da ke kasar Amurka. Ya kirkiri wannan gidan yanar sadarwa na Facebook ne a kwamfutarsa nau’in Mac, a cikin dakin kwanan dalibai (Dormitory), da misalin karfe goma na dare. Daga nan ya sanar da wasu cikin abokan karatunsa su uku, wadanda su ma fannin kwamfuta suke karantawa a lokacin, ya kuma shigar da su cikin wannan aiki don su taimaka wajen ingantawa tare da yada wannan aiki da ya faro. Wadannan abokai nasa dai su ne: Eduardo Saveri, da Dustin Moskovitz, sai kuma Chris Hughes.

Tunanin da ya haifar da samar da wannan dandali na Facebook dai ya samo asali ne daga tsarin da wata makaranta ke bi wajen buga sunayen dalibai da ke makarantar, tare da fannonin da suke karantawa, don raba wa dalibai saboda samar da sanayya a tsakaninsu. Wannan makaranta dai ita ce Philips Exerta Academy, wacce Mark ya halarta kafin zuwansa Jami’ar Harvard. Daga wannan dan karamin littafi da makarantar ke raba wa dalibai ne – wanda sauran daliban makarantar suka sanya wa suna “Facebook” a tsakaninsu - Mark ya dauko wannan suna. A farko dai Mark ya samar da wannan gidan yanar sadarwa ko dandali ne don yada hotunan abokansa da kuma na wasu dabbobi, inda ya sanya wata manhaja da masu ziyara ke amfani da ita wajen jefa kuri’a kan hoton dabba ko hoton wani abokinsa da ya fi kyau da kayatarwa. Daga baya sai aka samar da yadda duk mai ziyara zai iya mallakar shafinsa na musamman, don zuba nasa hotuna ko bayanai, da kuma hanyoyin gayyatar duk wanda kake son ya zama abokinka. Da tafiya ta kara gaba sai kwararru kan gina manhajar kwamfuta (watau Computer Programmers ko Developers) suka fara samar da hanyoyin gina kananan manhajoji ko masarrafai masu sawwake mu’amala da juna a wannan shafi.

Shafin Facebook na asali dai ya takaita ne ga abokanan Mark kadai, daga baya sai suka fadada wannan dandali zuwa sauran daliban da ke Jami’arsu, daga suka sake fadadawa zuwa daliban da ke Jami’ar Standford. Da lifafa ta ci gaba kuma, sai suka sake fadada damar shiga zuwa ga dukkan daliban Jami’a kadai. Daga nan suka ce ‘yan Sakandare ma na iya shiga. Da abin ya dada kasaita sai suka fadada dandalin ta yadda duk mai shekaru goma sha uku zuwa sama zai iya yin rajista, ya kuma mallaki shafinsa na kansa. A halin yanzu, wannan dandali na Facebook na dauke ne da mambobi masu rajista wadanda suka mallaki shafin kansu sama da miliyan dari hudu (400 Million). Wannan ya sanya Dandalin Facebook a sahun farko wajen yawan masu rajista da masu ziyara a dukkan duniya.

2 comments:

  1. Salam.

    A yau na ci karo da wannan blog din naka, kuma na karu da shi sosai. Allah ya kara taimako bisa wannan aiki da ka ke yi na ilmantarwa.

    Tsohon abokinka.

    ReplyDelete
  2. Wa alaikumus salam, Malam na gode da wannan sako naka. Har yanzu ni abokinka ne, tunda lafiya muke, ba gaba muke ba. Illa dai yanayin aiki ne kawai. Allah ya saka da alheria.

    ReplyDelete