Saturday, December 4, 2010

Tsarin Amfani da Wayar “Blackberry”

Tsarin Amfani da Waya Nau’in Blackberry

Daga cikin wayoyin salula na zamani masu tashe a yau, akwai wayoyi nau’in Blackberry da ake amfani da su. Wayoyin salula nau’in Blackberry suna kan yaduwa a duniya a halin yanzu. Kuma duk da cewa wayoyi ne na alfarma, kuma masu tsada da ba kowa bane ke iya mallakarsu, shafin Kimiyya da Kere-kere ya ga dacewar gabatar da ‘yan takaitattun bayanai ga masu karatu don fahimtar yadda tsari da kintsinsu yake. Har wa yau, na tabbata da yawa cikinmu mun samu labarin cewa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe wasu daga cikin hanyoyin amfani da wannan waya mai matukar tasiri sanadiyyar wasu dalilai. To me ya kawo haka? Kuma wani irin tsari ne wannan nau’in wayar salula ke da shi da har zai sa wata kasa ta dauki mataki makamancin wannan? Duk wadannan na cikin abubuwan da za mu karanta cikin wannan mako da makon da ke tafe in Allah Ya yarda. Da farko dai, ga bayani nan kan ma’ana da samuwar wannan waya ta Blackberry.

Ma’ana da Asali

Kalmar Blackberry, a turancin Kimiyyar Sadarwa ta Zamani a yau, na ishara ne zuwa ga wani jerin wayoyin salula na musamman nau’in Smartphone, masu dauke da masarrafar Imel da kamfanin Research in Motion (RIM) na kasar Kanada yake kerawa. Wannan waya ta Blackberry na dauke ne da masarrafai na musamman da ake amfani da su ta hanyoyi na musamman, kuma a wani irin yanayi da ya sha bamban da sauran hanyoyin sadarwa. Wasu cikin wadannan masarrafai dai sun hada da masarrafar Imel mai zaman kanta, watau Mobile E-mail, da manhajar kalanda, da masarrafar taskance bayanai, da masarrafar allon rubutu na kamfanin Microsoft – irinsu Microsoft Word, da Excel – da taskar adireshi, da manhajar mu’amala da tsarin sadarwa ta wayar iska, watau Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), da masarrafar sauraro da shan kida, da rariyoyin saduwa da Dandalin Facebook, da MySpace, da na Twitter. Har wa yau akwai masarrafar gano bigire, watau Geographical Positioning System (GPS), da manyan ka’idojin da ke tafiyar da manhajar Imel: Post Office Protocol (POP) da Internet Message Application Protocol (IMAP), sai kuma manhajar hirar ga-ni-ga-ka, watau Instant Chat Messenger, mai taimakawa wajen gudanar da hira tsakanin mai wayar da duk wanda ke giza-gizan sadarwa ta duniya, irinsu Yahoo Messenger, da Windows Live Messenger, da ICQ, da Google Live Talk da dai sauransu.

Wannan waya ta musamman mai suna Blackberry, kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada ne ya fara kera su cikin shekarar 1999. Zubin farko da kamfanin ya fara kerawa dai su ne nau’in Blackberry Pearl, kuma shafukansu launin fari da baki ne, babu wasu kaloli daban, watau Monochrome kenan. Cikin shekarar 2002 ne ya fara kera na zamani masu dauke da manhajoji masu kayatarwa. Kuma a haka kamfanin yake tafiya har zuwa yau; inda yake ta kera wasu nau’ukan daban masu dauke da abubuwa da dama. A kididdigar da masana kuma masu lura da tsari da tasirin tsarin sadarwa ta wayar salula a duniya suka bayar, bayan wayoyin salula masu dauke da manhajar Symbian OS da kamfanin Nokia ke kerawa, babu wata wayar salula da ta fi samun kasuwa a duniya irin Blackberry.

Manufa

Sabanin sauran wayoyin salula wadanda tun asali an kera su ne don aiwatar da sadarwar murya musamman (Voice Communication), su wayoyin salula nau’in Blackberry an samar ko kera su ne musamman don sawwake ayyukan ofis, da kamfanoni, da kuma mu’amala da fasahar Intanet dare da rana safe da yamma. Wannan kuwa a fili yake, musamman idan mai karatu yayi la’akari da irin manhajoji da kuma masarrafan da wayar ke dauke da su.

Idan kana dauke da waya nau’in Blackberry, wacce ke hade babu kwange tare da ita, to sadarwa a gare ka ba wata matsala bace. A kowane lokaci tana jone ne ta giza-gizan sadarwa ta duniya, watau Intanet. Kana iya karba da aika sakonnin Imel a duk sa’adda ka ga dama. Kana iya hira da duk wanda kake so a duniya muddin a jone yake da Intanet. Kai a takaice ma dai, kana iya tafiyar da ayyukan kamfaninka ko hukumar da kake wa aiki a duk inda kake. Da wannan nau’in wayar salula, ana gudanar da harkar kasuwanci, da shugabanci, da siyasa, da addini, da duk abin da ya shafi zamantakewa. Kana zaune a gidanka ne, ko a cikin jirgi kake, ko a cikin mota, ko kwance kake, ko a kasuwa kake, ko a maraya kake, ko kuma a karkara; duk ba ka da matsala. Bayan haka, wannan waya ce da idan ka caja batirinta, kana iya kwanaki masu tsawo baka bukaci na’urar caji ba. Domin dukkan manhajojin da ke cikinta ba su cin makamashi fiye da kima, balle har kuzarin batirinka ya gaza nan take. A halin yanzu wannan waya na sahun kayayyakin sadarwa na tafi-da-gidanka masu canza tsarin rayuwa a duniya, watau Convergent Devices.

Babbar Manhaja

Kamar yadda masu karatu suka sha karantawa a wannan shafi, kowace wayar salula na dauke ne da bangarori guda biyu; da bangaren gangar jiki, da kuma ruhi. Bangaren ruhi ne muke wa lakabi da “manhaja”. Domin manhajar ce ke tafiyar da wayar; daga kunnawa har zuwa kashewa – idan babu manhaja a tare da ita, to gwamma a jefar a bola, watakila yara su tsinta su rika wasa da ita. To, wayoyin salula nau’in Blackberry na dauke ne da babbar manhaja (watau Operating System) mai suna Blackberry OS 6.0. Wannan shi ne zubin manhajar na zamani. Wannan babbar manhaja tana da kuzari matuka, kuma idan kana da Blackberry tsohuwar yayi wacce ke dauke da babbar manhajar baya, kana iya kara mata kuzari (watau Software Update) ta hanyar zuwa shafin kamfanin ta Intanet daga wayar, ko kuma ka yi amfani da manhajar shigar da masarrafai ta kwamfuta, watau Blackberry Desktop Manager wajen yin hakan.

Bayan babbar manhaja, kowace wayar salula nau’in Blackberry na gudanuwa ne a saman masarrafar tafiyar da ruhin waya nau’in ARM. Nau’in Blackberry na farko sun yi amfani ne da Intel-80386. Daga baya kuma sa’adda kamfanin ya tashi kera Blackberry zubin 8000 Series, sai yayi amfani da nau’in ARM XScale 624MHz, in ka kebe zubin Blackberry 8707 wacce aka dora ta a saman nau’in Qualcomm 3250. Wannan mizani ne na tsarin sadarwa mai taimaka wa injin kwamfuta ko wayar salula sauri da gaugawar karba da aiwatar da umarnin da aka ba ta, kuma shi ake kira Processor a turancin kimiyyar sadarwar kwamfuta.

Tsarin Amfani da Wayar Blackberry

Ana iya amfani da wayar Blackberry ta hanyoyi uku. Hanyar farko ita ce, ka sayi wayar a kasuwa, ka sanya katin SIM dinka a ciki, sai kawai ka ci gaba da amfani da ita kamar sauran wayoyi. A wannan tsari, za ka iya yin kira, kuma a kira ka; ka yi tes, kuma a aiko maka. A takaice dai, za ka rika amfani da tsarin sadarwar kamfanin da ka sanya katinsu. Amma ba za ka iya amfana da galibin masarrafai da manhajojin da wayar ke dauke da su ba. Hanya ta biyu kuma kana iya saya, ko kaje daya daga cikin kamfanonin waya da muke da su a Nijeriya ka saya (kowanne cikin kamfanonin waya da muke da su a kasar nan suna sayar da wannan waya), sannan ka bukaci su farkar maka da ita, watau Activation kenan. Kowace waya nau’in Blackberry na zuwa ne da kalmomin iznin shiga (Pin Cord) guda takwas, kuma da su ake amfani wajen gabatar da abubuwa da dama a wayar. Kamfanin zai bukaci wadannan kalmomi a gidan yanar sadarwarsa, ko kuma a lokacin da kaje, don su shigar da wayarka cikin babbar manhajar sadarwarsu, kafin ka fara amfana da tsarin Intanet da na Imel da wayar ke dauke da su. Wannan tsari na biyu shi ake kira Blackberry Internet Service (BIS). Kamfanonin wayar kasar nan na da wannan tsari, kuma idan ka shiga, a kullum za ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, da manhajar Imel, da kuma hanyar hirar ga-ni-ga-ka. Duk lokacin da ka samu sako a akwatin Imel dinka, nan take wayar za ta sanar da kai cewa sakon Imel ya shigo; kamar dai yadda wayarka ke sanar da kai idan ka samu sakon tes. Sai dai kuma, dangane da tsarin biya da ke tsakaninka da kamfanin, duk wata za ka rika biyan kudin hanya, ko dai kafin wata ya kama, ko kuma bayan ya kare. In kuwa ba haka ba, to ba ka da sabis.

Sai tsari na uku, wanda kamfanoni ne ke amfani da shi, kuma ya kunshi jona wayar da wata manhaja ta musamman mai suna Blackberry Enterprise Server (watau BES). Wannan manhaja za a sanya ta ne cikin kwamfuta ta musamman a ofishin kamfanin, sannan a hada ta da tauraron dan Adam, wanda zai rika aiwatar da sadarwa ta wayar iska tsakaninsa da dukkan ma’aikacin kamfanin da ke dauke da wayar, da Cibiyar Bayanai (Network Operations Center – NOC) da ke kamfanin Research in Motion a can kasar Kanada, da kuma kamfanin sadarwar da wayoyin ke amfani da katin SIM dinsa. Wannan tsari yana da tsada sosai, amma ba abin da ya fi shi kayatarwa wajen sadarwa. Shi ma, kamar tsarin da ya gabace shi, dukkan kamfanonin sadarwar wayar salula da ke kasar nan na iya aiwatar da shi. Bari mu dan kara bayani kan yadda wannan tsari na BES ke gudanuwa.

Mu kaddara Malam Jatau na da kamfani mai dauke da ma’aikata 30, kuma yana son a dukkan lokuta kowane ma’aikaci na bakin aikinsa; a gida yake, ko ofis, a gari yake, ko a halin tafiya. Sai ya je kamfanin MTN misali (kamfanin Zain da Etisalat da Glo ku yi hakuri, misali nake bayarwa) ya bukaci wannan tsari. Kamfanin MTN zai baiwa kowane ma’aikaci wayar Blackberry ne guda daya, mai dauke da katin SIM din kamfanin, wanda kuma aka jona shi da babbar cibiyar sadarwar kamfanin. Sannan sai ya je inda ofishin kamfanin Malam Jatau yake, don sanya wannan manhaja ta Blackberry Enterprise Server a Uwar Garken (Network Server) da ke ofishin. Sannan ya jona dukkan na’urorin da za su hada alaka a tsakanin babbar cibiyar sadarwarsa ta waya, da wayyoin salular da ya baiwa wadancan ma’aikata, da kuma babbar cibiyar taskance bayanai ta kamfanin Research in Motion da ke can kasar Kanada. Da zarar yayi haka, an gama komai. Da wannan tsari, kowanne cikin ma’aikatan nan zai iya aiko sakon Imel cikin gaugawa zuwa ofis, don sanar da ofis halin da yake ciki kan aikin da aka tura shi. Haka za a iya aika masa da sakon Imel ta gaugawa. Haka za a iya hira da shi a tsarin hirar ga-ni-ga-ka, watau Intstant Messenger. Idan kamfanin ya bayar da lambar wayarsa ne ga masu hulda da kamfanin, to duk sa’adda suka aiko sakon tes, ko na Imel, kai tsaye zai wuce zuwa wayarsa, inda wayar za ta sanar da shi cewa sako ya iso. Idan yana bukatar karantawa, ba ya bukatar sai ya bude wayar; akwai alamar da aka tanada masa a jikin wayar wacce zai matsa, sai kawai sakon ya budo.

Dukkan sakonnin bayanai – irinsu tes, da Imel, da rubutattun sakonnin hirar ga-ni-ga-ka – suna bin hanyoyi uku ne ko hudu, kafin su isa inda aka aike su, a wannan tsari na BES. Idan aka aika wa wani ma’aikaci sakon Imel misali, sakon za ta zarce ne kai tsaye zuwa cikin wannan babbar manhaja ta BES da ke kamfanin, wacce a dakace take tana jiran sakonni masu shigowa. Da zarar ta kalli sakon da ya shigo, sai ta cilla wa wancan babbar cibiyar bayanai na kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada. Wancan cibiya da ke kasar Kanada kuma sai ta cilla wa cibiyar sadarwar kamfanin MTN, wacce mai’aikacin ke dauke da katin SIM din kamfaninta. Da zarar sakon ya iso kamfanin MTN, sai ita kuma ta aika wa ma’aikacin cikin wayarsa. Duk wannan zai faru ne cikin kankanin lokaci, sanadiyyar tasirin kayayyaki da hanyoyin sadarwa ta wayar iska. Sakon na shigowa wayar za ta sanar da shi nan take. Wannan shi ne yadda ake gudanar da sadarwa a tsakanin manhajar BES da kuma wayar Blackberry.

Zubin Wayoyin Blackberry

Akwai wayoyin Blackberry da dama da aka kera su a yanayi da kintsi daban-daban. Kashin farko su ne wadanda aka kera cikin shekarar 1999, wadanda kuma galibinsu duk ba su da wasu launukan da suka wuce fari da baki (watau monochrome, ko kuma black and white). Daga shekarar 2006 zuwa 2008 sai kamfanin ya samar da zubin da yayi wa lakabi da Blackberry Pearls. Kafin shekarar 2008 ta kare, sai kamfanin ya samar da wasu zubin masu suna Blackberry Curve, kuma irinsu yayi ta kerawa har sai da shekarar 2009 ta kare. A karshen shekarar kuma sai ya kirkiri zubin Blackberry Storm, wadanda yayi ta kerawa har cikin shekarar 2010. Daga farkon shekarar 2010 kuma zuwa tsakiyar shekarar, kamfanin Research in Motion ya sake kera wasu nau’uka da sake sanya musu sunan Blackberry pearls, da Blackberry Curve. Dukkan wadannan zube-zube na nau’in Blackberry suna dauke ne da adadin 7000, da 8000, da kuma 9000 series, kamar yadda ake kiransu a jumlace. Wayar Blackberry ta baya-bayan nan da kamfanin ya kera ita ce nau’in Blackberry 9300.

Wayoyin Salula Masu Kama da Blackberry

Akwai wasu cikin wayoyin salula na zamani da aka kera su dauke da masarrafar Imel ta musamman da wayar Blackberry ke dauke da ita, watau Blackberry Email Client. Wannan ke sa su sifatu da wata dabi’a ko yanayi irin na Blackberry, to amma fa, kama da wane ba ta wane, ko kadan. Zan so mai karatu ya samu sunayensu, domin idan mun kasa mallakar wayar Blackberry, to mu san cewa akwai wasu nau’uka da za mu iya mallaka don huce fushin rashinta. Tabbas Blackberry waya ce abin alfahari da morewa, to amma Allah bai yi yatsun hannayenmu iri daya, balle zanen da ke tafukan hannunmu su dace.

Wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel irin na Blackberry dai su ne: AT&T Tilt, da HTC Advantage X7500, da HTC TyTN, da Motorola MPx220, da Nokia 6810, da 6820, da 9300, da 9300i, da kuma 9500. Cikin jerin wayoyin har wa yau akwai dukkan ayarin wayoyin Nokia zubin E-series (ban da E71 da E66), sai kuma Qtek 9100, da Qtek 9000, da Samsung E719, da Siemens SK65, da SonyEricsson P910, da P99, da M600i, da kuma P1. Wadannan, a halin yanzu, su ne nau’ukan wayoyin salula masu dauke da masarrafar Imel na wayar Blackberry, watau Blackberry Email Client. Ba mu san abin da gobe zai haifar ba.

Tasirin Amfani da Blackberry a Duniya

Ko shakka babu amfani da wayar salula nau’in Blackberry yana tasiri sosai wajen aiwatar da sadarwa a yanayi kayatacce kuma mai gamsarwa. Musamman ganin cewa kamfanoni da hukumomi da daidaikun mutane sun rajja’a wajen amfani da wannan waya. Dalilan hakan dai ba nesa suke ba. Da farko, bayan yawaitan hanyoyi da manhajoji ko masarrafan sadarwa da wayar ke dauke da su, akwai kuma ingancin tsaro wajen sadarwa, wanda shi ne abin da galibin kamfanoni ke bukata. A tsarin aikawa da sakonni ta Blackberry, da zarar ka rubuta sako ka aika, nan take za a narkar da sakon don kariya, har sai ya isa inda aka aike shi. Wannan ta sa wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya suka fara damuwa da wannan tsari na boyewa tare da narkar da bayanai ta yadda babu na’ura mai iya hangowa balle ta karance su yadda za a fahimci sakon da ke cikinsu. Daga sakon tes, zuwa Imel, har rubutattun sakonnin hira da na murya, duk narkar da su ake yi har sai sun isa inda aka aike su.

Wani abin da ya kara wa wannan tsari wuyan sha’awi ga hukumomi masu son tace bayanai na murya ko rubutattu da ake aikawa a tsakanin kayayyakin sadarwa kuma shi ne, dukkan sakonnin da ake aikawa sai sun dire a Uwar Garken kamfanin da ya kera wayar a can kasar Kanada, sannan su isa muhallin da ake jiran isansu. Shi yasa a ranar 1 ga Augusta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe kafar amfani da tsarin Intanet da Imel da rubutattun hira ta hanyar wayar Blackberry, saboda dalilai na tsaro. A kasar hukuma ta saba tace ire-iren wadannan bayanai daga wayoyin salular da ake amfani da su, don tsaron lafiyar jama’a da ma baki da ke shigi-da-fici a kasar a kullum. To amma saboda tsananin tsaro da wannan waya ta Blackberry ta sifatu da shi, sun kasa samun isa ga ire-iren wadannan bayanai da mutane ke aikawa ta wannan waya. Don haka suka toshe dukkan kafar Intanet da duk wani mai Blackberry zai iya bi ya aika da sako. A halin yanzu idan kana Dubai, sai dai ka kira, ko ka yi tes, amma batun Imel da Intanet kam sai dai ka hakura. Hukuma tace muddin kamfanin bai yi wani hobbasa ba wajen ganin ya warware wannan matsala kafin 11 ga watan Oktoba, to za ta toshe hanyar amfani da wayar ma gaba daya. A halin yanzu akwai wayar salula nau’in Blackberry guda 500,000 da ake amfani da su a kasar.

A kasar Saudiyya ma hukuma ta koka da wannan tsari na mu’amala da wayar Blackberry. Don haka ita ma, daidai lokacin da ake wancan dambarwa a Hadaddiyar Daular Larabawa, ta yi barazanar cewa za ta toshe kafar sadarwar Intanet ga duk mai wannan waya, muddin kamfanin Research in Motion bai yi wani abu ba wajen ganin hukuma ta samu kai wa ga ire-iren bayanan da take so ko ake aikawa. Ai nan take sai kamfanin ya fara shirye-shiryen ganin ya amsa wannan kira. Domin akwai wayoyin Blackberry wajen 700,000 da ake amfani da su a kasar. Ya zuwa yanzu, kamfanin ya fara tattaunawa da hukumar Saudiyya, inda yayi tayin sanya wata Uwar Garke (Network Server) da dukkan sakonnin da masu wayar ke aikawa za su rika bi, gwamnati na tace su, kafin su zarce zuwa ga wadanda aka aika musu su, a kasar suke ko a wajen kasar. Domin kasar Saudiyya da ma galibin kasashen Larabawa duk suna tace tsarin sadarwa da ake gudanarwa ta hanyoyin kayayyakin sadarwa irinsu kwamfuta da wayoyin salula da sauransu. Bayan kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar Indonesiya, da kasar Bahrain, da kasar Indiya, da kasar Aljeriya da kuma kasar Lebanon, duk sun fara tayar da kura kan wannan tsari na rashin iya tace bayanan da wannan waya ta Blackberry ke aikawa, kuma akwai hasashen cewa su ma suna iya cew sai an musu irin abin da ake son yi wa kasar Saudiyya, in kuwa bah aka ba, to duk wani mai wayar Blackberry ya jefar da ita a bola.

No comments:

Post a Comment