Idan mai karatu na tare da mu a wannan jerin kasidu da muka taso tun shekarar da ta gabata kan Dandalin Facebook, ya san mun dakata ne a kasidar da ke dauke da bayani kan dalilan yaduwar wannan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani a duniya. Kuma kada a mance, mun yi alkawarin kawo dukkan bayanan da suka shafi wannan shafi ne gaba daya, cikin yardar Allah; iya gwargwadon sani da fahimta. Wannan ita ce kasida ta shida. A yau kuma ga mu dauke da bayanai kan Matsalolin da ke tattare da wannan dandali. Yana da kyau a rayuwarmu mu rika kiyaye wani abu guda daya; cewa duk lokacin da wani abu ya shahara a duniya wajen amfani, muddin abu ne na mu'amala ba wai ibada ba, to duk yadda alherinsa ya yawaita, sai an samu matsaloli sanadiyyar amfana da ake yi da shi. Ko dai ya zama matsalar daga jikin abin ne, ko kuma daga wajen masu mu'amala da abin. In kuwa haka ne, to kada mai karatu da ke tinkaho da Dandalin Facebook a wajen abokai ko 'yan matansa - yana ganin ai shi wani dan birni ne wayayye, mai amfani da wata hanyar sadarwa mai tasiri da a tunaninsa kowa da kowa suka yarda da shahararta - bayan ya ga wannan kasida kuma yaji hankalinsa ya tashi. Wannan ka'ida ce ta rayuwa. Don haka sai mu kiyaye.
Kamar yadda muka yi bayani a baya, wannan dandali ya shahara, ya kasaita, ya kuma tumbatsa a duniyar Intanet. Wanda ya mallaki wannan dandali, watau Mark Zuckerberg, a halin yanzu yana daga cikin matasa masu kudi a duniya. Wannan ke nuna cewa hatta a bangaren kasuwanci dandalin ya bunkasa. To amma kuma akwai matsaloli masu dimbin yawa da ke tattare da wannan shafi na dandalin Facebook. Wadannan matsaloli sun kasu kashi biyu. Na farko sun samo asali ne daga shafin shi kanshi; yadda aka tsara shi, da yadda ake tafiyar da shi. Na biyu kuma sun samo asali ne daga yadda masu mu'amala da shafin ke amfani da shi. Babban abin da ya zaburar da ni wajen kawo wadannan bayanai dai shi ne don mutanenmu Hausawa da suka fara yaduwa da barbazuwa a shafin, ta hanyar mallakar shafukansu na kashin kansu, wadanda kuma galibinsun matasa ne; maza da mata. Wajibi ne mu fahimci cewa akwai bambancin al'ada da addini a tsakaninmu da mafi yawancin masu amfani da wannan shafi a wasu kasashe, musamman kasashen yammacin duniya. Wannan zai taimaka mana wajen daina kwaikwayon da yawa cikin abubuwan da suke yi marasa kyau a shafin, wadanda kuma muna gani, muna karantawa. Ire-iren wadannan matsaloli ne ma tasa wasu daga cikin malaman addinin musulunci musamman suke ganin kamar haramun ne musulmi ya rika mu'amala da shafin ko a shafin. Kuma ba komai ya kawo wannan fatawa mai zafi ba sai don ganin abin da ke faruwa a shafin dandalin Facebook. Ni dai a iya 'yar gajeriyar fahimta ta, ya danganci yadda ka yi amfani da shafin. Idan ya zama ka kiyaye dokokin Ubangiji a matsayinka na musulmi a yayin da kake mu'amala da jama'a a wannan dandanli, to, hakika ka tsira. Amma idan ka dauki tafarkin 'yan duniya, masu ganin ai yanzu duniyar ta waye, dole ne a tafi da zamani, to kai ka jiwo, sautun mahaukaciya. Kada mu tsawaita, a halin yanzu ga wasu daga cikin wadannan matsaloli. Da fatan za mu kiyaye. Allah ya mana jagora, amin.
Cin Mutuncin Addini
Wannan ita ce matsala ta farko daga cikin matsalolin da suka fi shahara a dandalin Facebook. Kuma daga cikin addinan da wannan matsala ta shafa akwai addinin musulunci. Kuma wannan matsala ta cin mutuncin addini ta samo asali ne daga wajen masu amfani da wannan shafi. Shekaru biyu da suka gabata wata kungiya da ba a san ko su waye ba sun bude wani shafi da ke kira zuwa ga zanen hoton Manzon Allah (SAW), a daidai lokacin da suke gab da bikin farin cikin zagayowar ranar da wani mai zane dan kasar Denmak ya aiwatar da wannan mummunar aiki, kamar yadda suka sanar. Wannan lamari ya tayar da kura a dandalin gaba daya, inda har musulmai suka bude shafi don nuna damuwarsu kan wannan lamari. Nan take sauran musulmi da ke dandalin suka fara bore. Aka kirkiri wata rajista ta musamman don baiwa kowane musulmi sanya hannu kan kira ga shugabannin Dandalin Facebook su rufe wancan shafi da ke kira zuwa aibanta Manzon Allah ta hanyar zana hotonsa. Cikin awanni ashirin da hudu aka samu musulmi sama da dubu hamsin da takwas da suka rattafa hannunsu kan wannan rajista. Bayan nan kuma, musulmin kasar Pakistan sun yi zanga-zanga a gaban ginin majalisar dokokin kasar don kira ga majalisar ta fitar da dokar da za ta haramta mu'amala da shafin Facebook a kasar gaba daya. Ganin haka ke da wuya sai hukumar dandalin Facebook ta rufe wancan shafi.
Faruwar wannan lamari ya baiwa da yawa cikin musulmi haushi, inda suka yi ta fita daga dandalin, suka ta rufe shafukansu, kuma suna ta kira ga duk wani musulmi ya fice daga wannan dandali. Duk da cewa hukumar Facebook ta kulle wancan shafi da ke batanci ga Annabi Muhammad (SAW), da yawa cikin musulmi basu sake da ita ba, domin a yarjejeniyar asali da hukumar shafin ta tanada, sun nuna cewa kowa yana da hakkin bayyana ra'ayinsa na siyasa ne ko na addini, muddin ba zai ci mutuncin addinin wani ko al'adarsa ba. In kuwa haka ne, to bai kamata ma tun asali hukumar ta bar masu wancan shafi na batanci har su kai gaci ba, tunda ra'ayin da suke kokarin bayyanawa ya ci karo da wannan yarjejeniya. To me yasa ba a hana su ba har sai da musulmi suka nuna damuwarsu, har aka yi kokarin kawar da shafin daga kasar Pakistan, sannan suka rufe? Wannan, a cewar da yawa cikin musulmin kasar, alama ce da ke nuna cewa lallai hukumar Dandalin Facebook basu dauki addinin musulunci a bakin komai ba. Wannan matsala ta farko kenan.
Gulma da Hirar Banza
Ba dandalin Facebook kadai ba, duk inda majalisar Intanet take, ana samun yawaitar gulmace-gulmace da karairayi marasa tushe. To amma wanda ake samu a dandalin Facebook ya fi kowanne yawaita da maimaituwa. Ba don komai sai don hanyoyin mu'amala da shafin sun yawaita matuka. Bayan kwamfuta da ake iya amfani da ita wajen shiga dandalin, kana iya amfani da wayar salularka, wacce kake damfare da ita a duk inda kaje, muddin akwai Intanet a ciki. Wannan ke bayar da damar ganin a kowane lokaci ka fadi wani abu, ko halin da kake ciki, ko inda kaje, ko wani abin da ka gani, ko abin da wani ya fada. Duk wanda ke ziyartar shafukan Hausawanmu matasa a Facebook zai fahimci abin da nake nufi. Bayan zumunci, wanda ake yinsa sosai kuma abin alfahari ne a garemu, akwai batanci da ke samuwa, da zage-zage ga wasu daga cikin shugabanninmu wadanda suka shude ko suke kan mulki. Dukkan wannan, a riyawar masu shafukan da kuma wadanda suka assasa shafin, fadin albarkacin baki ne. To amma da za a auna wa mutum nauyin kalmomin da yake fada miyagu a kan wasu, da irin hukuncin da ke jiransa a kabari ko a kiyama, da ba haka ba. Wajibi ne kowane musulmi ya san cewa, kamar yadda za a tambayeshi kalmomin da ya fada da harshensa, da wadanda ya daka ko ya yafuta da hannunsa ba tare da hakki ba, to haka za a titsiye shi ya yi bayanin abin da ya rubuta da hannunsa a filin kiyama. Wannan matsala ta gulmace-gulmace da hirar banza marasa alfanu su suka fi yawa a shafukan dandalin Facebook. Tabbas akwai raha da ake yi a tsakanin abokai, ko magoya bayan wasu kungiyoyi na kwallo ko na siyasa. Wannan raha da ake yi dole ne yana da ma'auni. Ma'auninsa kuwa shi ne tabbaci ko rashin tabbacin kalmomin da ake fada a yayin da ake rahan. Ma'ana, gaskiya ko rashin gaskiyar kalmar da aka fada. Don haka sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Haifar da Tsana da Hassada
Daga cikin matsalolin dandalin Facebook manya akwai haifar da tsana da hassada. Watakila mai karatu zai yi mamaki, musamman ganin cewa rubuce-rubuce ne kawai ake yi a shafukan. Da farko dai babu abin da ke haifar da yawan tsana a tsakanin masu mu'amala da shafin sai gulmace-gulmace. Ire-iren wadannan matsaloli kan haddasa yankewar alaka a tsakanin wadanda abin ya shafa, ko da kuwa a zahirin rayuwa suka hadu. Yawan zage-zage, da gulma, da rade-radi marasa tushe, da kuma fadi-ba-tambayeka ba, duk su ne ke haddasa tsana a tsakanin dandalin. Babban abin da ke haddasa samuwar hassada kuma shi ne yadda wasu ke sifata rayuwarsu da abin da suke riya cewa sun mallake shi wanda karya ne, ko darajan ilminsu, ko martabarsu a rayuwa, ko wasu mukamai da aka basu a shafi ko dandalin. Mai karatu zai mamakin jin cewa akwai mukamai na sarautar gargajiya da ake dasu a shafukan Facebook; bangaren dandalin Hausawa nake nufi. Wadannan mukamai na sarauta don raha ne aka kirkiresu. Amma shaharar masu mukaman ko ganin yadda suka samu karbuwa a wajen mambobin da ke dandalin, na iya haifar da hassada a zukatan wasu. Wannan a tabbace yake, domin hatta a Majalisun Tattaunawa na Yahoo! da Hausawa suka mallaka, ana samu wannan matsala. To, a shafukan Facebook ma akwai ta. Ba komai ya dada taimakawa ba sai ganin cewa gilli da hassada wasu dabi'u ne da Allah ya rakkaba dan adam a kansu wajen halitta. Maganinsa na samuwa ne ta hanyar karantar ilmin addini da kuma aiki da shi. Sai matsala ta gaba.
Gajiya da Damuwa
A duniyar Intanet, babu abin da ya fi haddasa gajiya da damuwa (Stress and Fatige) kamar shafukan abota irinsu Facebook. Hakan na samuwa ne sanadiyyar dadewan zama ana abu daya, da kallon gilashin kwamfuta ko wayar salula masu dauke da sinadaran hasken da ke cutarwa a hankali a yayin da ake karatu ko rubutu, da kuma tsawaita tunani ko damuwa ko bakin ciki kan abin da ya faru ko yake faruwa a shafi ko dandalin da mutum ya mallaka. Bayan haka, idan mutum ya kamu da mummunar shakuwa kan Intanet, watau Cyber Addiction, wata matsala mai zaman kanta na iya samuwa. Matsalar kuwa na iya nuna kanta ne ta hanyar zazzabi a duk lokacin da ba a samu damar shiga dandali ko shafin ba, da kuma tsawaita bakin ciki mara misali da ma'ana kan abin da mai shafin yake kullawa. Kai a takaice ma dai, ana iya kaiwa wani mataki wanda shi kanshi mai shafin ba zai taba samun natsuwa da jama'ar da yake rayuwa da su a gida ko unguwarsu ba, sai ya shiga dandalin Facebook da ke wata duniya tsakanin mafarki da hakika. Sai matsala ta gaba.
Kashe-Kashe da Ta'addanci
Nau'ukan kashe-kashe da ta'addanci mara misaltuwa – wadanda kafafen labarai suka hakaito da wadanda ba a hakaito ba – ruwan dare ne a duniyar Intanet, kuma hakan ya fi shahara ne a kasashen yammacin duniya. To, watakila mai karatu yace ai mu ba ruwanmu da wannan bakin rayuwa. A a, daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, maza ka nemi gulbi ko tafki ko kududdufi ka tsoma naka a ciki. A dandalin Facebook an samu ire-iren wadannan matsaloli, inda masu sace kananan yara ke amfani da adireshin gidajen iyayensu, ko barayi ko kuma wadanda aka tura su don kashe wani, galibi sukan yi amfani ne da shafukan Facebook don sanin fici-da-shigin wanda suke son kamawa ko kashewa ko masa ta'addanci. Domin dandalin Facebook taska ce inda galibin turawa sukan rubuta duk abin da ya shafi rayuwarsu baki daya. Sannan ko tuntube suka yi a kan titi, sai sun rubuta. To, haka ma mutanenmu da ke dandalin. Sai ka ga mutum ya rubuta cewa, yanzu bacci nake ji, ko yunwa nake ji, ko ba ni da lafiya, ko jiya na je wajen wance ta wulakanta ni, ko na fi sha'awan abin ci ko abin sha nau'i kaza. Dukkan wadannan bayanai ne na sirri da suka shafi rayuwarka, kuma wani abokin gaba na iya amfani da su wajen cutar da kai, kamar dai yadda muke jin labari a wasu kasashen. Tabbas babu abin da zai faru da kowane dan adam sai abin da Allah ya kaddara masa, to amma Allah da kansa ya sanar da mu cewa mu kiyaye. Don haka sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Dodorido
Kalmar dodorido ta shahara a dandalin Hausawa a Intanet. Kuma abin da kalmar ke nufi shi ne yin amfani da fuska ko sunan wani daban don boye kai. Ma'ana wani ya bude shafi da sunan wani shahararren mutum, yana nuna cewa shi ne wannan mutumin, alhali ba haka bane. Yana iya nemo hoton mutumin ya lika, ya samo ra'ayoyinsa na siyasa ko na addini, ya kattaba a shafin, yana muzurai wai shi ne wane. Duk wannan na samuwa ta hanyar dandalin Facebook. In kuwa haka ne, to ya kamata ka san da wa kake mu'amala. Karairayi da yaudara sifofi ne guda biyu da suka shahara a duniyar Intanet. Dole ne ka zama mai iya tantancewa; da wani irin mutum kake alaka? In kuwa ba haka ba, za ka sha mamaki. Wani abin bakin shi ne, masu irin wadannan dabi'u na boye kai sun fi shahara a shafukan abota irin su Facebook da Twitter. Don haka sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Batsa da Ashararanci
Yadda batsa da ashararanci suka yadu a duniyar zahiri da muke rayuwa a ciki, to haka suka yadu a duniyar Intanet. Akwai shafuka na musamman masu sayar da zina ko hotunan batsa. Amma a dandalin Facebook galibi hanyoyin "hada waya" ne ake da su. Ma'ana, ta hanyar wannan dandali da yawa cikin masu wannan dabi'a kan hadu, su yi abota, su shirya wurin haduwa, sannan a yi abin da ake son yi. Kowa da jama'arsa! Galibin abotan da ake shiryawa ko kullawa a ire-iren wadannan shafuka – ko dai tsakanin maza da mata, ko tsakanan mata da mata, ko kuma tsakanin maza da maza. Al'amuran sai dai addu'a. A wajen masu wannan dabi'a, dandalin Facebook wajen neman abokan hulda ne da harka. Domin a wajen bayanan da suka shafi mutum kana iya sanin manufarsa idan ya rubuta. Maza yake son abota da su ko mata kadai. Mace take son yin abota da ita ko maza kadai, duk za ka samu. Bayan haka, wasu ma kan wuce gona da irin shukawa, su bayyana hakikanin abin da suke nufi ko so. Wasu kalmar baka ce kadai, ba sa nufin abin da suka rubuta, amma wasu kuma da gaske suke yi. Sai an latsa ake iya bambancewa. Allah kiyashe mu mummunar latsi. Sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Yawan Shagaltuwa da Shagaltarwa
Da yawa cikin makarantun da ke kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, sukan sanya wa shafin dandalin Facebook takunkumi, ta yadda idan a makarantar kake, ba za ka iya shiga shafin ba. Ba don komai ba sai don yadda dalibai suka jarabtu da shafin, wajen abota da hirarraki marasa alfanu. Wanda kuma hakan yana mummunar tasiri kan karatunsu. Domin ba su samun daman zama su yi nazarin darussan da aka karantar da su. Haka hukumomi da ma'aikatun da ke wadannan kasashe, har da ma kasashe masu tasowa, sukan sanya wa wannan shafi takunkumi a ma'aikatar, ta hanyar masarrafar garkuwar wuta, watau Firewall. Domin an lura cewa galibin ma'aikata kan shagaltu da wannan shafi, har kadarin aikin da suke yi ya ragu. Wannan na cikin abin da ke dada harzuka masu wadannan ma'aikatu, har dai a karshe suka ga ba sarki sai Allah, suka katange ma'aikatansu daga wannan bala'i.
Wadannan dabi'u na shagaltuwa da shagaltarwa a bayyane suke a wannan dandali. Domin idan ka fara mu'amala ko abota da mutane, gaba daya zuciyarka za ta koma kan dandalin ne kacokam. Za ka ji in ba shafin kaje ba, kamar baka samu cikakkiyar rayuwa ba. Idan har ka fara jin haka, to ka san cewa lallai wadannan miyagun dabi'u guda biyu sun shige cikin kwaroron jinin jiki da zuciyarka, kamar yadda guban cizon sauro ke kwararowa cikin jiki. A matsayinka na wanda makaranta ko ma'aikatar da kake aiki basu katangeka daga wannan matsala ba, ka san cewa kana da aiki mai girma. Domin babu abin da ya fi wahala irin tarbiyyantar da kai. Don Allah a rika kiyayewa, a san cewa lokaci yana da tsada, kuma da zarar ya wuce fa, ba zai kara dawowa ba.
Matsalolin Gudanarwa
Matsalolin da za mu dakata a kansu su ne matsalolin gudanarwa da wannan dandali ke fama da su. Da farko dai, akwai rade-radin da ya game duniyar Intanet mai nuna cewa lallai hukumar gudanarwar dandalin Facebook na sayar da bayanan da suka shafi jama'a, wanda suke taskancewa cikin kwamfutocinsu, ga kamfanonin kasuwanci da binciken dabi'un mutane a Intanet. Wannan, in har gaskiya ne – wanda kuma akwai alamar hakan – ba karamar cin amana bace. Domin a cikin kundin yarjejeniyar da kowane mamba ke yarda da su kafin a bashi shafi, sun nuna cewa ba za su bayyana bayanansa na sirri ga wani daban ba. Yanzu kuma a samu labarin cewa kamfanin na sayar da wadannan bayanai da suka shafi sirrin rayuwar jama'a ga wasu, ba karamar cin amana bace.
Bayan haka, idan kana mu'amala da shafin Facebook, a duk lokacin da ka shiga matsala, to ba ka da wanda zai warware maka matsalar da ka tsunduma ciki. Da zarar ka je shafin neman taimako, watau Help Page, babu abin da za ka ci karo da shi sai tsofaffin bayanan da ko kadan ba za su dace da matsalarka ba. Wannan matsala kuwa ta samo asali ne saboda masu gudanar da wannan shafi basu ajiye wani mutum na hakika, wanda zai rika zama yana amsa matsalolin masu shafuka a dandalin ba. Manhajar kwamfuta ce suka tanada, wacce da zarar ka tura musu bukatar a warware maka wata matsala, sakonka na isa inda take, sai kawai ta cillo maka rariyar likau din da za ta kaika wajen wancan shafi da muka yi bayaninsa a sama. Wannan ke nuna mana cewa lallai araha ba ta ado.
Sannan a wasu lokuta ba abin mamaki bane ka nemi shiga dandalin ma gaba daya, sai a ce maka: "Yi hakuri, a halin yanzu muna fuskantar wasu 'yan matsaloli ne…nan da minti daya ka sake kokarin shiga." Minti daya na karewa idan ka nemi shiga za ka sake samun wannan sako. Wannan ba karamar matsala bace. Domin idan ya zama rayuwarka da farin cikinka gaba daya suna cikin shafin Facebook ne, to watarana idan aka yi rashin sa'a kwanakinka suka kare, sai buzunka. Wajibi ne a kan masu gudanar da wannan dandali su tanadi kwamfutoci masu dimbin yawa da girman mizani, da masarrafai ko manhajoji masu nagarta da tasiri wajen tsare bayanai da iya mika su cikin lokaci. In kuwa ba haka ba, abin da ya samu shafuka irin su MySpace, zai same su. Abin da yaci Doma, ko kadan ba zai bar Awe ba. Muddin mutane ba su samun daman shiga shafukansu a lokacin da suke so, kamar yadda aka musu alkawari, to, da zarar an samu wani shafi da yafi shi nagarta, kowa zai kaurace masa ne.
Sai matsala ta karshe, watau "goge" shafi daga kwamfutocin kamfanin Facebook. Idan ka gaji da mu'amala da shafinka na Facebook, ba ka da wata hanyar goge shafin gaba daya, sai dai ka "kulle". Idan ka je bangaren "Settings" da ke shafinka na Facebook, a can kasa, za ga an rubuta "Deactivate Your Account". Kalmar "Deactivate" na nufin ka kulle shafin ne daga amfani da shi, amma dukkan bayananka, da hotunanka, da sauran abubuwanda suka shafeka, suna nan daram-dakam a kwamfutocinsu. Ma'anar wannan kalma ta sha bamban da kalmar "Delete", wanda duk masanin harkar sadarwa ya san gogewa ake nufi. Wannan kuma ke nuna cewa nan gaba suna iya amfani da su. Watakila mai karatu ba zai fahimci matsalar da ke tattare da hakan ba, tunda mu a nan bamu cika damuwa da sirrin bayanan da suka shafe mu ba. Amma ga wadanda suke wasu kasashe, ba karamar matsala bace da kuma barazana ga rayuwa ko mutuncinsu. Duk da yake wasu sun gano wata sabuwar hanyar da ake bi a goge shafin baki daya, amma da sauran rina a kaba. Musamman ganin cewa masu gudanar da wannan shafi sun ki fitowa fili karara don nuna wa masu mu'amala da shafukansu yadda za su iya goge dukkan abin da suka rubuta ko adana a ciki. To me yasa suka ki bayyanawa? Oho! Allah kadai ya san addu'ar kurma. Abin da yake wajibi ga mai mu'amala kawai shi ne, ya san irin bayanan da zai rika zubawa a ciki, da irin kalmomin da zai rika amfani da su, don komai na iya faruwa a kowane lokaci. Allah mana jagora, amin.
No comments:
Post a Comment