Mabudin Kunnuwa
Babban abin da yake bambance dan adam a bangare daya, da sauran dabbobi a daya bangaren, shi ne samuwar ilmi, da kuma tunani ko hankali wajen sarrafa ilmin ta yadda zai canza tsarin rayuwarsa da zamantakewarsa a duniya. Duk wani abin da dan adam zai iya bude ido a yanzu ya ganshi, ko ya taba shi, ko ya tuna shi, ka ya hankalto shi, ko kuma ya sinsinoshi, to yana da alaka da ilimi. Alaka ta kai tsaye ko alaka karkatacciya. Ma'ana, ko dai ya zama ilmi ne yayi sanadiyyar samuwar abin – kamar mota, da keke, da babur, da burodi, da gida, da kudi, da dai sauransu – ko kuma shi kanshi ilmi ne da yake da alaka wajen samar da abubuwan da dan adam ke mu'amala da su a yanzu ko a baya.
Babban dalili kuwa shi ne, lokacin da Allah ya saukar da Annabi Adamu da matarsa Hauwa'u daga sama zuwa doron wannan duniya ta mu, su biyu kadai suka sauko. Babu nassi da ya tabbatar da cewa sun zo ne da kwanukan dafa abinci daga Aljanna, ko da gadon kwanciyarsu, ko katifa, ko wani abin tafiyar da ruwa. A a; daga su sai su. Ma'ana, tsuransu suka zo. Da ilmin da Allah ya hore masa ne ya fara tunanin yadda zai tafiyar da rayuwarsa, wajen neman abinci, da sarrafa abincin, da samar da nau'in abincin daban-daban. Da ilmin da Allah ya hore masa ne yayi tunanin me zai samu da zai tufatar masa da jikinsa daga tsananin zafin rana, ko zafin bazaar, ko sanyin hunturu. Daga ilminsa ne ya fara tunanin yadda zai samar da muhallin zamansa. Da dai sauran abubuwa makamantan wannan. In kuwa haka ne, ashe ma iya cewa, duk wani abin da dan adam ya samar da shi daga baya, to, ta hanyar ilmi ne.
Da wannan ne muka ga dacewar fara wannan silsila mai tsawo iya gwargwado, don kawo tarihin masana wadanda kuma suka yi tasiri wajen kirkirar abubuwan amfani ga al'umma ta hanyar kwazo da ilmi da hangen nesansu, a fannin Kimiyya – kamar kimiyyar likitanci, da lissafi, da injiniyanci, da gine-gine – da fasahar sadarwar bayanai – kamar bangaren kwamfuta, da dukkan sauran kayayyakin sadarwa – da kuma kere-kere – musamman a bangaren safara; irinsu motoci, da kekuna, da babura, da sauransu. Amma kafin nan, yana da kyau mu yi mukaddima kan abin da ya shafi hikima, da basira, da hanyoyin da suka taimaka wa wadannan masana wajen ilminsu, da fannonin da wadannan masana suka taimaka a ciki, da asalin wadannan masana ta bangaren addini da zamantakewa da al'adu, da dacewa ko rashin dacewan tunani ko asalin ilminsu ko binciken da suka yi, da kuma kalubalen da muke fuskanta a wannan duniya ta mu, duk da batsewar da tayi da kayayyakin more rayuwa. Me yasa muke fama da talauci, da kuncin rayuwa, a lokaci ko zamanin da ake ganin ilmi ya fi yaduwa, da kuma kayayyakin kere-kere da sadarwa fiye da baya? Sai a biyo mu sannu a hankali.
Hikima da Basira
Duk inda aka samu ilmi, to, ya kamata a samu hikima da basira. Wadannan sifofi ne guda biyu da ke taimaka wa duk wani mai ilmi wajen sarrafa abin da ya koya ko karanta na ilmi, a aikace. Wadannan kuma baiwa ne da duk wani mai ilmi ke samunsu. Don haka idan Allah ya baka ilmi, to lallai za a samu hikima da basira a tare da kai. Kaifi da girman wadannan sifofi biyu sun danganci tsarin alakarka ne da Ubangijinka. Idan ilmi ya hadu da tsoron Allah, yakan haifar da hikima da basira mai girman gaske. Kuma ba abin mamaki bane a samu wanda ba musulmi ba amma mai ilmi, da hikima da basira. Domin baiwa ne da Allah ke yinshi ga duk wanda ya ga dama. Don haka, idan ka kalli dukkan abubuwan da masana suka samar ta hanyar ilmi, za ka samu akwai hikima a tare da su, sannan basira yayi aiki wajen samar da su.
Musabbabai
Daga cikin dalilan da suka taimaka wa wadannan masana wajen kirkire-kirkire da bincikensu akwai baiwa, wacce Allah ke jefa musu cikin kwakwalensu, a yayin bincike ko karantar ilmin da suka karanta, ko sana'anta abin da suka kirkira. Bayan baiwa, akwai kuma dagewa. Abin da nake nufi da dagewa shi ne, tsananin naci. Tsananin naci na daga cikin dabi'un da ke taimaka wa mutum kwarewa cikin ilmi, yana kara basira, da kuma samar da hikima kan kere-kere. Amma idan mutum rago ne, mara naci, ba zai taba zama gwarzo ba a fagen ilmi. Dabi'a ta uku ita ce dabi'ar sha'awa. Sha'awar wani fanni na daga cikin abin da ke taimakawa wajen sa mutum ya zama mai kwazo don bincike cikin fannin. Don haka wasu malamai ke ganin cewa, kada ka bata lokacinka cikin fagen ilmin da ka san ba ka da sha'awa a cikinsa. Misali, babban malamin nahawun larabci mai sun Sibawaihi, a farkon rayuwarsa ya fara karatu ne cikin fannin ilmin hadisi, amma sai ya ji abin ya masa tsauri sosai. Sai ya koma fagen ilmin nahawu, nan take sai ga shi ya zama gagarau a fannin, har yanzu ana kafa hujja da ra'ayoyinsa wajen ilmin nahawu a duniya.
Daga cikin dalilan da suka taimaka wa wadannan masana har wa yau, akwai samun kansu cikin halin kalubale; ma'ana wani yanayi ya jefa su cikin halin bukatuwa zuwa ga wani nau'i na ilmi ko neman wani abu. Malaman ilimin dabi'a sun nuna cewa, kwakwalwar dan adam kan tsattsafo da fahimta da basira a lokutan da yake fuskantar kalubale a rayuwarsa. Ma'ana, da zarar ka samu kanka cikin halin kunci da ya tilasta maka yin wani abu, nan take za ka ji tunani nau'uka daban-daban sun fara bijirowa cikin kwakwalwarka; yi kaza, kaza za ka taba, fita ta wajen kaza…da dai sauransu. Sai dalili na karshe da za mu dakata a kanshi, watau fassara ko tarjama; wanda ya kunshi juya nau'ukan ilmin kimiyya da kere daga wani harshe zuwa wani. Wannan hanya na daga cikin abin da ya taimaka wajen samar da gwarazan malaman musulunci da suka yi fice wajen ilmin kimiyya a karnonin baya. Galibin ilmin likitanci, da ilmin sararin samaniya, da bangaren kwamfuta a yau, da kuma fannin kimiyyar lissafi a jiya da yau, duk sun samo asali ne mai inganci daga abin da malaman musulunci suka kattaba a karnonin baya, kamar yadda za mu karanta nan gaba in Allah ya so. Turawa sun yi haka ne bayan yake-yaken da suka yi wajen tarwatsa daular musulunci a kasar Andalus, da kwashe abin da suka gani na nau'ukan ilmin zaman duniya, da kona wadanda suka shafi ilmi addini zalla, don fassara su a sawwake, da mallake shi, da kuma sassauya duk abin da bai musu ba, ta yadda suke so. Don haka, har yau, tarjama ko fassara makami ne babba, wanda za a iya amfani da shi don kwafo wani nau'in ilmi mai muhimmanci da ya shafi rayuwar jama'a, don sawwake hanyar samunsa ga wasu al'ummar da ke da bukatuwa zuwa gare shi.
No comments:
Post a Comment