Ka'ida ta karshe ita ce: Wayoyin salula (da sauran kayayyakin sadarwa na zamani) na'urori ne masu taimakawa wajen tafiyar da rayuwa cikin sauki. Wannan ka'ida, duk saukinta wajen fade, ta fi wahala wajen dabbakawa. Amma idan mutum ya dabbaka, to zai tafiyar da rayuwarsa cikin sauki. Daga kira, zuwa taskance bayanai, zuwa kintsawa tare da tsara su, har zuwa aiwatar da lissafi, da lura da lokaci, da tsara abubuwan da mutum ke son yi; na alkawura, da tunatarwa, da ziyarce-ziyarce da dai sauransu. Idan mutum yayi amfani da wayarsa wajen yin komai ta yadda suka kamata, zai yi rayuwa cikin sauki ta taimakon wayar salularsa, duk araharta kuwa. Dukkan wadannan ka'idoji da bayaninsu ya gabata, za a iya amfana da su ne idan mai karatu ya mayar da hankalinsa kan bukatunsa a cikin waya. Sau tari wasu kan kira ni suna neman in basu shawarar irin wayar da ta kamata su saya, nakan tambayesu irin bukatarsu ne a jikin wayar. Me da me kake son yi da wayar ko a jikin wayar? Domin na lura a yanzu galibin mutane suna sayan wayar salula ne irin wacce suka ga ana yayi, ko irin wanda abokai ko kawaye ko samari ko 'yan matansu ke amfani da su. In kuwa haka mutum yake, to zai rika hasarar kudinsa ne a banza. Idan kana son amfanuwa da wayar da za ka saya, to, ka zauna ka kididdige irin bukatun da kake dasu a jikin wayar salula, kafin ka san wace irin waya ce ke da irin abubuwan da kake bukata. Da haka sai ka amfana da wayar da za ka saya. Amma idan ka zama dan "a bi Yarima a sha kida," to, kai ka sano.
Ayyukan Waya
Ayyukan kowace wayar salula na iya samuwa ne ta hanyoyi uku. Hanyar farko ita ce ta hanyar sadarwa, mai amfani da ka'idojin fasahar sadarwa ta wayar iska, watau Mobile Communication Protocols. Hanya ta biyu kuma ita ce hanyar amfani da manhajojin da wayar ta zo dasu, ko dai wajen taskance bayanai, ko wajen samar da su, ko tsara su, ko kuma mika su. Wannan hanya ba ta bukatar amfani da tsarin sadarwa ta wayar iska kafin a iya amfani da wayar wajen aiwatar da su. Sai kashi na uku, wanda ya kunshi hanyar amfani da waya a tsakaninta da kamfanin sadarwar waya. Wannan hanya tana bukatar samuwar tsarin sadarwar wayar iska, amma ba ka bukatar kashe ko sisinka wajen aiwatar da ita. A halin yanzu ga wasu daga cikin ayyukan wayar salula.
Aiki na farko da wayar salula ta shahara da shi, wanda kuma tun asali da shi aka santa, shi ne aikin kira da sadar da kira. Duk wata wayar salula an kera ta ne don aiwatar da kira da kuma karbarsa, a farkon lamari. Za ka iya kiran duk wanda kake da lambarsa, ko shi ya kira ka. Idan kai ne ka kira shi, za a cire ladan kira daga layinka ne, amma idan shi ne ya kira ka, daga layinsa za a cire ladan kira. Wannan tsari shi ake kira Caller Charged. A wasu kasashe kuma, irin su kasar Amurka da wasu kasashen Turai, wanda aka kira ne zai biya ladan karbar kira. Wannan tsari kuma shi ake kira Receiver Charged. Tsarin yin kira da amsa kira, ya danganci yadda aka kera wayar ne. Amma ta yadda duk ka amsa kira ko ka kira, wajibi ne ka san cewa wannan tsari ne da ya ta'allaka dari bisa dari da tsarin sadarwar wayar iska. Aikin waya na gaba shi ne aikawa da karbar gajerun sakonnin tes, watau Short Message Service, ko SMS. Wannan tsari na waya yana samuwa ne ta hanyar tsarin sadarwar wayar iska, ma'ana, idan babu katin SIM a wayar, ba za ka iya amfani da tsarin SMS ba. Wannan tsari an fara amfani da shi ne a wayar salula bayan samuwar tsarin kira a wayar. Kuma yana daga cikin tsarin da ya kara wa wayar salula shahara da tumbatsa a duniya.
Sai aikin waya na gaba, watau kirkira da taskance bayanai. Kowace wayar salula na iya ba ka damar kirkiran bayanai, kamar adireshin abokananka, ko lambobinsu, ko sunayen wasu abubuwa da kake son saye nan gaba, ko kuma tarihin wasu al'amura da suka faru ko suke faruwa, ko kuma tarihi da kwanan watan ranar da aka haifeka ko 'ya'yanka, da dai sauransu. Bayan dukkan wannan, idan aka turo maka wasu bayanai duk kana iya taskance su, musamman bayanan da suka shafi hotuna daskararru, da hotuna masu motsi, watau bidiyo, ko kuma sakonnin tes da ka karba daga wajen wasu. Tsarin kirkirar bayanai a wayar salula ba ya bukatar tsarin sadarwar wayar iska, ma'ana, ko babu katin SIM a wayarka kana iya kirkirar bayanai. Amma abin da ya shafi karbar bayanai rubutattu misali, dole sai kana sanya katin SIM a wayar. Aiki na gaba shi ne tsarin karba da aika sakonnin Imel. Galibin wayoyin salula na zamanin yau suna iya baka damar tsara wayar ta yadda za ka iya aikawa da karbar sakonnin Imel, ko idan an aiko maka ka iya karbarsu. Duk arahar waya, musamman wayoyin Nokia ko Samsung ko SonyEricsson, kana iya yin haka da su. Bayan haka, wasu daga cikinsu na da masarrafai na musamman masu sadar da dukkan akwatin Imel dinka zuwa cikin waya, watau Mobile Email kenan a Turance. Wayoyin salula na musamman irin su Smartphone ko Black Berry, ko wayoyin salula na kamfanin Nokia nau'in Eseries, da Nseries, duk za ka samu suna da ire-iren wadannan masarrafan Imel na musamman. Wannan tsari na Imel ya na amfani ne da tsarin sadarwa ta wayar iska, watau Wireless Communication Protocols. Don haka wajibi ne ya zama akwai katin SIM a wayarka, muddin kana son mu'amala da fasahar Intanet a wayar. Sai aiki na gaba, watau mu'amala da fasahar Intanet. Shi ma aiki ne na musamman mai amfani da tsarin sadarwar wayar iska, da kuma tsarin GPRS din kamfanin waya. Wannan tsari, kamar tsarin SMS da ya gabace shi, yana cikin ayyukan da suka kara wa wayar salula shahara a duniya. A sauran kasashen duniya, galibin mutane na mu'amala da fasahar Intanet ta hanyar wayoyin salularsu; tsari ne da ke bukatar katin SIM, domin duk tsawon lokacin da ka dauka kana lilo a giza-gizan sadarwa ta Intanet, za a rika cire kudin ne daga layinka.
No comments:
Post a Comment