Matashiya
Kamar yadda na sanar a makon da ya gabata, a yau ga mu dauke da
amsoshin sakonninku da kuka aiko ta tes, da wadanda kuka aiko ta jakar Imel
dinmu. Kamar yadda na saba, wasu daga
cikin sakonnin na amsa su ta hanyar tes ko ta Imel inda aka aiko su. Ire-iren wadannan sakonni ban kawo su tunda
na amsa su tuni. Bayan haka, akwai
wadanda ke bugo waya har yanzu – duk da cewa na roki a daina bugo waya. A haka dai nakan saurare su, har in ba da
amsa iya gwargwadon hali. Wasu kuma in
ce su yi hakuri sai na rubuto musu. Akwai wadanda kuma ke cewa kada in buga
sakonsu a shafin jarida, su ma nakan yi iya kokari wajen ganin ban buga ba, ta
hanyar ba su jawabin tambayarsu. Bayan
haka, har yanzu akwai masu damu na da filashin.
Ire-iren wadannan mutane ina rokonsu da su ji tsoron Allah su
daina. Ba na ganinsu, amma Allah na
ganinsu kuma ya sansu, ya kuma san abin da suke yi, zai kuma yi musu sakamakon
da ya dace da ayyukansu, ba ruwana.
Har wa yau, akwai wanda ya rubuto yana neman fassarar wasu kalmomi
a gaggauce, saboda an bashi aikin gida ne (watau Assignment) a
makaranta, kuma lokacin da ya aiko ya nuna yana son amsar a ranar don idan gari
ya waye zai gabatar a makaranta. A
gaskiya ban samu damar bashi amsa ba, saboda sakonsa ya same ni cikin yanayin
zirga-zirga ne. Ire-iren wadannan bukatu
yana da kyau a rika gabatar da su cikin lokaci, don nima in samu damar bincike
– idan sakon na bukatar bincike – kafin in san amsar da zan bayar. Don haka ina neman afuwa daga wurin wanda ya
turo wancan bukata da ban samu damar amsawa ba. A gafarce ni, sai wani jikon
idan Allah ya sake hada mu.
A karshe kuma akwai wadanda suka rubuto tsokaci mai tsawo, ban san
inda zan sa ba – shin tambaya ce, ko nasiha suke mini, ko gargadi, wallaahu
a'alamu - kan batun yadda ruwa ke
samuwa. Da cewa su sunyi imani da abin
da Allah ya fada a Kur'ani cewa ruwa daga sama yake, ba tare da wani dogon
bayani ba. Da dai sauran bayanai makamantan wannan. To, ni dai iya abin da na sani kenan na
rubuta. Kuma ba da ka nayi rubutun ba,
sai da na gudanar da bincike a kimiyyance, sannan na gudanar da bincike a
addinance, ta hanyar nassoshin Kur'ani da na duba, da sharhin malaman tafsiri,
da hadisai, da dai sauran hanyoyi. Na
kuma sanar da masu karatu dukkan ayoyin da na ciro, da hujjojin da suke kokarin
tabbatarwa. To amma akwai alamar wasu
basu gamsu ba, ko basu fahimci inda na dosa ba, ko kuma ra'ayinsu ya sha bamban
da nawa kan wancan lamari, ko kuma basu samu karanta dukkan kasidun ba. Abin da na so su yi shi ne, su nuna mini inda
na yi kuskure, da hujjojinsu, da kuma abin da yake shi ne daidai, don nan gaba
in gyara. To amma hakan bai samu
ba. Wannan nake sauraro. In kuwa bai samu ba, to duk wani sakon da aka
aiko mai alaka da haka, wanda kuma ba tambaya bace ta neman sani, zan ajiye ta. Allah mana jagora.
A yanzu dai ga amsoshin tambayoyinku nan. Duk abin da ba a fahimta ba, don Allah, a
nemi karin bayani. In Allah ya so zan fadada bayani iya gwargwadon iko. Allah shi ne masani, mai cikakken sani da
fahimta, wacce babu nakasa a tare da ita.
Allah sa mu dace:
…………………………………………………………
Assalamu Alaikum, Baban Sadik, shawara ta gareka ita ce, ina ganin
cewar kalmar 'tes' da 'Imel' ba kalmomin Hausa bane. Ya kamata kayi amfani da
ainihin fasarar da za'a fahimci manufar sakonnin. Huta lafiya. Musa Ningi,
No.22 Prison Road, Ningi, Jihar Bauchi.
Malam Musa muna godiya da wannan tsokaci da kayi, Allah saka da
alheri. Watau abin da ya sa nake amfani
da kalmar "tes" da "Imel" shi ne, don su ne kalmomin da
mutane suka fi fahimta, sabanin yadda kake zato. Duk bahaushen da kace masa "tes" ko
"Imel" a wannan zamani, zai fi saurin fahimta nesa ba kusa ba, da
kace masa "gejeren sakon waya" ko "wasikar hanyar sadarwa ta
Intanet." Dalili na biyu kuma shi
ne, wadannan kalmomi sun fi sauki ta wajen gajarta, bayan saukin fahimta. Sannan kuma duk da cewa kalmomin Turanci ne,
ba wani laifi, domin aron kalma a ilmance ba laifi bane. A takaice ma dai, duk harshen da ba ya aron
kalmomi daga wasu harsuna, to ba zai taba ci gaba ba. Hatta kai kanka sai da
kayi amfani da wannan tsari sannan na fahimci sakonka. Domin ka yi amfani da "kalma" da kuma
"fasara", wadanda kuma duk ba Hausa bane a asalinsu. Kalmomin larabci ne. A tsarin aron kalma kuwa ba a bambancewa
tsakanin wani harshe da wani. Aron kalma
dai aron kalma ne; daga harshen Larabci ne ko Turanci. Don haka, dangane da yadda malamai suka
tabbatar, ba laifi bane don na yi amfani da wadannan kalmomi. Na kuma tabbata
masu karatu na fahimta. Da ba su fahimta
da tuni an dame ni da neman karin bayani.
Tunda na bude wannan shafi shekaru biyar da suka wuce, kai ne mutum na
farko da ka yi inkarin wannan tsari, duk da cewa kaima ka fahimci abin da nake
nufi. Da fatan dai ka gamsu da wannan
jawabi nawa.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, Allah ya kara maka basira amin. Ina son ka yi mini cikakken bayani ne a kan
na'uran nan ta "iPad 2"; yaya tsarin sadarwarta take? Daga Hambali Azare: 08036966225.
Malam Hambali, iPad 2 dai wata na'urar sadarwa ce da kamfanin Apple
Inc ya fara kerawa shekaru kusan uku da suka wuce. Akwai "iPad Wi-Fi", da "iPad
3G", da kuma "iPad 2 Wi-Fi."
Wannan na'urar sadarwa dai ana amfani da ita ne wajen taskance bayanai
rubutattu – musamman littattafai - da
bidiyo, da kuma bayanan sauti. Haka
kuma, akwai masarrafai da dama da ke sawwake mu'amala da wadannan bayanai. Akwai tsarin sadarwa mai inganci, wanda ke
sawwake mu'amala da Fasahar Intanet, watau "Wireless Frequency." Fasahar iPad na cikin sababbin kirkirarun
kayayyakin fasahar sadarwa masu inganci da tsada da tasiri a duniyar yau. Sai dai ba wayar salula bace, don ba ta da
inda aka sanya katin SIM. An yi ta ne
don mu'amala da bayanai da bidiyo da bayanan sauti da kuma littattafan da suke
a tsarin na'urar sadarwar zamani. Idan
ka saya, ba za ka iya mu'amala da fasahar Intanet ba sai ka sa mata makalutun
sadarwa. Kana iya zuwa kamfanin waya na
MTN, ko GLO, ko Etisalat, don su jona ka da tsarin sadarwarsu. Idan suka jona ka, za ka rika biyan kudin
layi a duk wata ko yadda tsarinsu ya kama.
Wannan na'urar sadarwa dai tana da kafar da ake shigar da katin SIM,
sannan tana amfani da tsarin sadarwar zamani na GSM. Mafi karancinta a mizani, watau iPad 2
(16GB), ta kai naira dubu dari da ashirin a nairan Najeriya. Da fatan ka gamsu.
Me yasa wayoyi kirar CDMA suke daukar zafi kuma cajin batirinsu
yake saurin karewa a wurin da babu tsarin sadarwar na katin SIM din da ke
kansu? Abubakar Wada Kadi.
Alal hakika ban da masaniya kan cewa wannan matsala ta takaita ne
kadai ga wayoyin salula masu amfani da tsarin sadarwa ta CDMA. Abin da na sani shi ne wayoyin salula kan yi
zafi, kuma daga cikin dalilan da ke haddasa musu wannan zafi akwai matsalar
batir; ko dai saboda jabun batir, ko kuma batirin da ke cikinsu ya samu
matsatsi daga mummunar yanayin zafin rana ko muhallin da wayar ke ajiye. Cikin shekarar 2003 da 2004 an samu
rahotannin wayoyin da suka yi ta fashewa da wuta sanadiyyar zafi da suka yi a
kasar Amurka da sauran kasashen Turai.
An kuma danganta dukkan wadannan matsaloli ne ga jabun batira ko kuma
zafin yanayi da muhalli. Daga karshe ma
dai an gano cewa ko da ingantattun batira ne suna iya fashewa idan akwai
yanayin da suke ciki ya dumama. Daga
cikin dalilan har wa yau daukan tsawon lokaci ana amfani da waya ko wata masarrafa
da ke cikinta. Wannan shi ma yakan janyo
zafi ga wayar salula. Amma zafin da waya
ke yi sanadiyyar rashin yanayin sadarwa a inda waya take, babu wani alaka a
tsakaninsu. Ta yiwu dai batirin da ke
wayar ya lalace, ko kuma jabu ne, ba ingantacce ba. A takaice dai, jabun batira
sun fi haddasa zafi ga wayar salula fiye da kowace irin matsala. Don haka ne ma kamfanonin waya a yanzu suka
dauki matakin sanya wasu hanyoyin kariya a cikin batiran masu nuna tantance
ingantaccen batir da jabunsa. Kuma hakan bai takaitu ga wayoyin salula masu
amfani da tsarin sadarwa nau'in CDMA ba. Wannan shi ne dan abin da na sani. Da fatan an gamsu.
Baban Sadiq da fatan an tashi lafiya, tambayata ita ce, na bude shafin
Facebook, ya yi, amma da na sake budewa jiya sai aka ce mini "Pls
be patient while testing the connection for the first time." Idan ya dan jima, can sai ya ce: "Connection
failed. Check Your internet setting."
Ina neman karin bayani. A. Sadiq
Abin da wannan sako ke nufi shi ne, akwai matsala da tsarin
sadarwar Intanet da ke wayar. Don haka
sai a duba a gani. Idan akwai
"Internet Settings" sama da guda daya ne a wayar, sai a zabi guda
daya a mayar da shi "Default."
Idan kuma babu ne gaba daya, sai a aika wa kamfanin waya sako don su
turo. Allah sa a dace.
Assalamu
alaikum, da fatan kana lafiya? Dan Allah meye amfanin WLAN Service? Kuma
yaya zan yi amfani da shi? Na ga kasidarka game da IPv4 da IPv6,
zan iya canzawa daga IPv4 zuwa IPv6? Dan Allah meye bambamcin tura sako ta imel da
tes? Kuma me yasa idan na tura sako ta imel ba ya tafiya? Waya ta {C3 Nokia} ce
ko akwai wani abin da ya kamata na yi ne wanda ban yi ba? Wasalam nine Ibrahim
Muhammad, Toro, Bauchi; 08065750790
Amfanin "Wireless LAN Service" shi ne aiwatar da sadarwar
Intanet ta hanyar yanayin sadarwar wayar iska.
Galibin wayoyin salular zamani suna amfani da wannan tsari ne. Amma ba za ka iya amfani da shi ba sai a
wurin da ake da tsari irin wannan. Idan ka kunna shi, wayar za ta sanar da kai
cewa "Akwai yanayin sadarwar wayar iska a nan." Bayan haka, za ka iya amfani da wannan tsari
don shiga Intanet iya gwargwadon yadda tsarin yake. Akwai tsarin WLAN da ke kulle, watau
"Secured WLAN" kenan. Irin
wannan tsari ba ka iya mu'amala da shi sai an tsara maka, ta hanyar shigar da
kalmomin sirrin da aka tsare tsarin da su.
Akwai kuma budadden tsarin sadarwar wayar iska, watau "Unsecured
WLAN." Shi wannan da zarar ka jona
wayarka da shi kawai shikenan, sai ka ta kwasan garabasa kyauta. Tsarin IPv4 dai shi ne wanda ake amfani da
shi har yanzu. Ba a riga aka yi hijira
zuwa IPv6 ba. Idan lokacin yayi, ba sai
ka yi hijira da kanka ba, wayar da kake amfani da ita za ta iya yin haka nan
take. Domin galibin wayoyin salula da
kayayyakin sadarwa na zamani a yanzu suna zuwa ne da dukkan tsare-tsaren guda
biyu. Amsar tambayarka ta gaba kuma ita
ce, akwai bambanci tsakanin Imel da sakonnin Tes. Imel dai hanyar aikawa da sakonni ne ta
Intanet, wacce ke da tsari da kintsi da hanyarta na musamman, da kuma ka'idojin
sadarwa masu taimakawa don yin hakan; a wayar salula ne ko a kwamfuta. Amma tsarin Tes kuwa hanyar aikawa da sakonni
ne ta amfani da yanayin sadarwar kamfanin wayar tarho, ta wayar iska. Tsarin Imel a wayar salula da kwamfuta duk yana
bukatar sai an tsara shi, watau "Configuring" kenan, a turancin
kimiyyar sadarwa. Na kuma tabbata rashin tsarin ne ya sa idan ka yi kokarin
aikawa da sakonnin Imel sai ya kasa tafiya.
Ka duba kundin da wayar ta zo dashi, za ka ga yadda ake saitawa. Amma tsarin Tes a wayar salula ba ya bukatar
wani saiti; da zarar ka sayi waya, ka sa mata katin SIM, nan take kana iya
rubuta sakonnin tes ka aika. Domin
dukkan tsare-tsarenta na cikin katin SIM, wanda ke aiwatar da sadarwa ta kai
tsaye da yanayin sadarwar kamfanin waya.
Da fatan an gamsu.
Salam, Baban Sadik barka dai.
Na ga wata waya nau'in BlackBerry 8.0 kirar china, ko ya take da
wacce kake bamu labarinta? Daga S.S Dala
Akwai bambanci a tsakaninsu sosai kuwa. Wayoyin salula nau'in Blackberry da ke zuwa
daga kasar China sun kasu kashi biyu ne.
Akwai ingantattun wayoyin Blackberry da ake gwanjonsu, wadanda wasu suka
gama amfani da su. Ire-iren wadannan
ingantatu ne, babu matsala tare da su, kuma kana iya saya, ka je kamfanin waya
a saita maka su ka kama mu'amala da tsarin da suke gudanuwa a kai wajen
sadarwa. Kuma duk irinsu ne muka yi
bayani akansu, kuma kamfanin Research in Motion ne ke kera su. Amma wadanda ke zuwa daga kasar Sin masu
lambobi (kamar wadanda kake magana akai), jabun Blackberry ne, kuma ba su da
wadannan sifofi da muka yi bayaninsu a baya.
Akwai wadanda ke zuwa ma da katin SIM biyu. Duk jabu ne. Da fatan an gamsu.
Wato inason ka bani shawara ne, a hakika ina son fara "Online
business," kuma a yanzu na tanadi hanyoyi masu inganci, masu
yawa, kai har littafi na rubuta don koya wa mutane, amma matsalata kawai itace
ta tsarin aiwatar da biyan kudade. Wato Mastercard da sauransu. Ta yaya
zan mallaki wadancan katuna? Daga Sadiq
Tukur, gwarzan gwaraza. Gwarzo
Malam Sadiq lallai ka cancanci jinjina. Idan kana bukatar katin ai samunsa ba
wahala. Ka je bankin GTBank, ko
Fidelity, ko Zenith, sai ka musu bayani, za su bude maka taskar ajiya mai dauke
da katin. Amma kafin nan, ka tabbata ka
yi rajistan kamfaninka, da hajojin da kake son sayarwa. In kuwa ba haka ba, to zai yi wahala su bude
maka taskar. Allah sa a dace.
Salam Baban Sadik dan allah wai da gaske ne Katin ATM yana daukan
magana, kamar yadda blackberry take daukar sirri zuwa wani waje. Daga M. J. Jos
A gaskiya ban taba karantawa ba, ban kuma taba ji ba. Abin da na sani dai shi ne dan abin da na
gabatar a kasidun baya. Da fatan ka
gamsu.
Barka da war haka Baban Sadiq, ga 'yan tambayoyi na; 1) Me ake nufi
da ICT a harshen Hausa? 2) wace irin gudunmuwa ICT ke ba wa
harshen hausa? 3) A fada mini gidajen
yanar sadarwa guda 10 da ke bayani da harshen Hausa kamar gumel.com da sauransu:
shamoo04@yahoo.com
Cikin yardar Allah na aika maka makalar da Farfesa Abdallah Uba Adamu
ya rubuta kan wannan haka a shekarar 2004, mai take: Hausa and Information
Communication Technologies (ICTs). A
ciki za ka samu amsar dukkan wadannan tambayoyi naka. Makalar tana da tsawo,
don shafuka 24 ne. Sai ka saukar za ka iya bugawa ko karantawa a shafin
kwamfuta; duk wanda ka so yi. Allah sa
mu dace, amin.
Salamu alaikum Baban Sadiq, ni ne Haruna Katsina da na kira ka
dazun da safe. Da ma abin da nake son
tambaya shi ne: akan Gmail ne;
yaya yake? Kuma ya ake amfani da shi?
Nayi rejista dinsa amma na dauka duk tare suke da Imail; amfaninsu daya kuma,
amma sai naga sabanin haka. Shi ne nake son ayi man bayani akan shi Gmail
din tare da kuma shi Imail din baki daya.
Wannan shi ne username din Gmail din da nayi rejista:
Ibrahimharuna1@gmail.com. Sannan inda dama ka ba ni adireshin da zan iya samun
Imai din, domin waya ta ba ta da Imail. Na gode
Malam Haruna akwai alamar ba ka taba amfani da masarrafar Imel
ba. Ai kalmar Imel gamammen suna ne da
ke ishara ga dukkan hanyar wasikar sadarwa ta Intanet, da wacce ake amfani da
ita a tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci a gajere da dogon zango. Da Yahoo Mail, da Hotmail, da Gmail (ko
Google Mail), duk nau'ukan Imel ne. babu
wani bambanci tsakanin Imel da Gmail sai na suna. Idan kana da jakar wasikar Gmail, to ka
mallaki Imel a rayuwarka. Abin da kalmar
"Email" ke nufi shi ne, "Electronic Mail." Don haka kada ka damu, ka riga ka samu Imel,
tunda kana da Gmail. Gmail wani nau'in
Imel ne da kamfanin Google da ya bude ba jimawa ba. Haka Yahoo Mail, nau'in Imel ne na kamfanin
Yahoo! Haka ma Hotmail, nau'in Imel ne
na kamfanin Microsoft. Dangane da
wayarka kuma, ban san wace iri bace, amma ina kyautata zaton cewa lallai tana
da Imel. Idan kana son gane haka, ka je
"Menu", sai ka shiga "Message", daga nan ka matsa wajen
"Create Message", za a budo maka nau'ukan sakonnin da za ka iya
rubutawa ka aika. A misali, za ka ga:
"Text Message, Multimedia Message, Audio Message, Email", a
jere. Sai dai shi tsarin Imel da ke
cikin wayoyin salula ya sha bamban da wanda ke jikin Intanet kuma ake shiga ta
kwamfuta. Wanda ke cikin wayar salula na
bukatar a saita shi, kuma hakan na bukatar kwarewa, a gaskiya. Don haka idan kana bukatar mu'amala da Imel
ta wayar salula cikin sauki, ka shiga gidan yanar sadarwar Google ko Gmail ta
wayarka kawai (da ke http://mail.google.com), sai ka shigar da bayananka.
Salamu alaikum Baban sadik, Tambayata itace ko mutum zai iya tafiya
akan doron Wata (Moon) domin wani bincike a kansa? Daga Aliyu Mukhtar
Sa'idu (I.T) Kano, aliitpro2020@.com 08034332200
Malam Aliyu ai tuni har an yi kuwa.
Abu ne mai yiwuwa, kamar yadda tarihi ya nuna lokacin tafiyar su Neil
Armstrong a shekarar 1969. Sun taka
saman Wata, inda suka gudanar da binciken da suke son yi. A karshe suka debo samfurin kasar wurin, don
shigowa da shi duniya da ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin wurin. Sai dai kuma ya kamata mu sani, muhallin da
ke saman Wata ya sha bamban da irin muhallinmu. Domin a yayin da muke da iska mai kadawa da
muke shakarta a nan, a can babu irin wannan iska. Don haka masu zuwa duniyar Wata ke sanya wasu
tufafi masu dauke da na'urar shakar iska, wacce ke taimaka musu wajen numfasawa
yadda ta kamata. Sannan a can babu
tsarin Janyo nauyi kasa, watau "Force of Gravity" kamar yadda muke da
shi a sararin wannan duniya tamu. Wannan
tasa za ka gansu kamar suna tafiya ne a saman iska, ba su daidaituwa wuri daya
a lokaci daya, saboda karancin tasirin wannan tsari a can. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Abu Sadik, don Allah ina son karin bayani akan intanet
da Network. Muh'd L Igabi al-igabaawy1986@yahoo.com
Kalmar Intanet dai na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci ko
sauran kayayyakin sadarwar zamani, da ke taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa
ba tare da wata matsala ba, a ko ina suke a duniya. A daya bangaren kuma, kalmar
"Network" na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci ne a a wani
wuri na musamman. Misali, ana iya hada
kwamfutoci kamar goma a gida daya, su rika aiwatar da sadarwa a tsakaninsu.
Haka ana iya hada alaka a tsakanin kwamfutocin da ke wani gida da wani gida da
ke unguwa guda, ko gari guda, ko jiha guda.
Duk wadannan tsare-tsare ana kiransu "Networking". Idan a gida daya ne, sai a kira su
"Locak Area Network" (LAN).
Idan a tsakanin gari da gari ne, ko unguwa da unguwa, sai a kira shi
"Wide Area Network" (WAN).
Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, Intanet ta fi fadi sama da
"Network." A takaice ka iya
cewa, Intanet hadaka ce ta nau'ukan "Network" a duniya. A yayin da tsarin Network ke da iya haddi da
tsaro da kuma mai lura da tsarin (watau Network Administrator), a tsarin
Intanet babu wannan. Ita Intanet muhalli
ne ko wata duniya ce mara iyaka. Ta ko
ina kana iya shiga. Ta ko ina kana iya
fita. A kowane lokaci kana iya shiga. A kowane lokaci kana iya fita. Amma a tsarin Network dole sai an baka iznin
shiga, da lokaci, da kuma inda za ka tsaya; baka isa ka wuce ba. Dukkan wadannan kaidoji ba su a tsarin
Intanet. Da fatan ka gamsu.
Salam ya aiki? Ina da kwamfuta amma ban san yadda zan yi rejistan
intanet ba, ko a waya ma ban iya ba. Don Allah yaya zan yi?
Wannan abu ne mai sauki. Ka je ofishin kowanne daga cikin
kamfanonin wayar salula da muke da su, ka sanar da su cewa kana son
"Internet Modem", watau makalutun sadarwa ta Intanet. Za su sayar maka, sannan su jona maka
kwamfutar nan take. Sai dai zaka rika
loda kati a duk sadda kudinka yak are, don ci gaba da samun sadarwa a
kwamfutar. Ko a duk sadda iya adadin kwanakin da suka yanke wa kudin. Ma'ana, idan ka loda kudi, akwai iya adadin
bayanan da za a baka; kamar 200MB, ko 500MB misali. Idan wata guda ya kare baka gama cinye
wadannan adadin bayanai ba, za a kulle sai ka sa kudi sannan a kara maka wasu a
kan wadanda suka rage. Dangane da wayar
salula kuma, ka aika sakon tes ga kamfanin wayar da kake amfani da layinsu, ko
kaje ofishinsu kawai zai fi sauki, ka sanar da su cewa kana son a saita maka
wayar don ka rika mu'amala da fasahar Intanet, za su saita maka, kyauta. Da fatan an gamsu.
Assalamu alaikum, Baban Sadiq ina yi maka fatan alheri. Dan Allah mene
ne banbancin MMS da kuma SMS a wajen tura sakwanni? Daga Yusuf
Muhammad Gagarawa, Jihar Jigawa, Najeriya. 08061123657, 08154627050
Malam Yusuf muna godiya da addu'a. Haruffan MMS na nufin
"Multimedia Message" ne, watau tsarin aika sakonni na murya ko hotuna
ko bidiyo. A daya bangaren kuma,
haruffan SMS na nufin "Short Message Service" ne, watau tsarin aika
gajerun sakonni rubutattu ta wayar salula. Bambancin da ke tsakaninsu dai na yanayi
ne, da kuma hanyar da suke bi wajen aikawa.
MMS dai ta kunshi sauti ne da hotuna masu motsi da daskararru, a yayin
da SMS ta kunshi rubutattun sakonni kadai.
Tsarin MMS na bin tafarkin yanayin sadarwar wayar salula mai amfani da
fasahar Intanet ne, a yayin da tsarin SMS ke amfani da tsarin yanayin sadarwar
wayar salula kadai. Don haka ko babu
tsarin Intanet a wayar salula za ka iya aika sakon SMS, amma tsarin MMS dole
sai da tsarin Intanet a tare da ita. Da
fatan an gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, a fasahar kere-kere kamar akwai dan
tsafi wajen kera wani abu, ko dai zunzurutun ilmi ne? Don wani malami ya ce mana duk inda fasaha
tayi yawa, akwai sihiri. Ka huta lafiya, daga Kabiru Ahmad Gombe 08182374782 uribak.ahmad@yahoo.com
Malam Kabiru ai tun wajen Malaminku ka bar amsar tambayarka. Domin ban san wani bangaren fasahar kere-kere
bane ke kunshe da sihiri ko tsafi. Sihiri
dai shi ne juya hakikanin wani abu zuwa wani abu daban, ta hanyar da ta sha
karfin tunanin dan adam a al'adance, tare da taimakon shedan ko kangararrun
aljanu. Da yace idan fasaha ta yi
yawa akwai sihiri a ciki, abin da zan iya cewa kawai shi ne; sihiri nau'i biyu ne,
kamar yadda wasu malamai ke bayani.
Akwai hakikanin sihiri da tsafi, wanda kowa ya sani, wanda kuma ke
tasiri wajen warware imanin duk wani musulmi. Akwai kuma sihiri ta dabi'a,
watau dan adam ya yi wani abin da zai kama hankali da tunanin mutane, saboda
kwarewa ko tasirin abin, ba tare da taimakon wani aljani ko shedani ba. Irin wannan sihiri shi ne wanda Manzon Allah
(SAW) ke magana a kansa a cikin wani hadisi da yake cewa, "Lallai a cikin zance
hakika akwai sihiri…" duk malamai sun tafi a kan cewa ba hakikanin sihirin
da ke warware imani ba yake nufi. Domin
sahabbai sun sha kulla baitukan wake a gabanshi, wasu lokuta ma waken shi ake
yabo a ciki, kuma bai hana ba. Kamar su
Hassaan bn Thaabit, da Abdullahi bn Rawaaha, duk mawakansa ne masu yabonsa. Abin da yake nufi shi ne, lallai wake na
cikin abin da ke tasiri a zukatan mutane, irin tasirin da kusan sihiri ke yi
wajen kama zuciya da dabi'a. Wannan kuwa
wani abu ne sananne ga duk wanda ya san rayuwar Larabawa musamman kafin zuwan
Musulunci. To, idan wannan malami na
nufin irin wannan nau'in tasiri ne ko sihiri, sai mu ce eh, akwai. Domin duk wanda ya ga inda ake abubuwa da
dama na kere-kere, musamman inda ake kera jiragen sama, da yadda kwamfutoci ke
sarrafa injina ko na'urorin da ke gudanar da wadannan ayyuka, zai ga kamar
akwai sihiri a ciki, amma ina; tsantsar ilmi ne da kwarewa. Wasu kan ce wai Turawan kanfani kan yi tsafi
a yayin da suke kokarin gina gadoji a cikin teku, da wasu gidaje da ke wasu
wuraren da ake tunanin akwai kwankwamai a ciki, wai shi yasa ma idan suna haka,
sai leburori ma'aikata su ta fadawa cikin teku, ko su yi ta hadari, don aljanu
na shan jininsu ne sanadiyyar tsafin. Duk wadannan wasu abubuwa ne ko zantuka
da babu hakika a cikinsu. Ban ce karya
bane kai tsaye, ban kuma ce turawa ba su yin sihiri ko tsafi ba, a a, suna
yi. Amma abin da ya bayyana mana da shi
muke hukunci. Wannan shi ne abin da zan iya cewa. Idan malam yana kusa, sai ya taimaka maka da
karin bayani. Allah shi ne masanin
hakikanin abubuwa. Da fatan an gamsu.
Salam, tambaya ta kan ATM ne. Kamar ina da kudi a Current
yaya zan juya su su koma cikin Savings ga na'urar ATM?
Eh to, abin da na sani shi ne, bankuna na iya jona miki taskar
ajiyarka guda biyu (Savings da Current) su rika amfani da katin ATM guda
daya. Ma'ana kina iya shiga kowanne daga
cikinsu don cire kudi. Dangane da juye
adadin kudaden da kike da su daga Current zuwa Savings kuwa, wannan sai dai ki
bi tsarin "Transfer" don yin hakan.
Wannan ne zai baki damar shiga da kudaden da kike da su a Current su
koma Savings. Idan kika sanya katin, za
ki ga inda aka rubuta "Transfer", idan kika matsa akwai inda za ki
shigar da adadin kudin da kike son fitarwa, da nau'in taskar da kike son mayar
da kudin, da sauran bayanai. Babu wahala
tsarin inshallah. Da fatan kin gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, barka da warhaka. Ina fatan kana
lafiya, Allah yasa haka, amin. Tambaya ta ita ce: Me yasa idan mutum yana kallon
bidiyo a intanet sai ya rika tafiya lakakai-lakakai, sannan ya dan tsaya, sai
kuma ya ci gaba? Ba kamar yadda muka saba kallo a bidiyo CD/DVD ba? Wassalam!
Daga Uncle Bash, J/Yola 07037133338, unclebbash@yahoo.com
A gaida Uncle Bash namu.
Wannan tsari na kallon hoto mai motsi ta Intanet shi ake kira
"Streaming." Idan kai tsaye
(Live) kake kallo a lokacin da abin ke gudanuwa, ana kiransa "Live
Streaming." Dalilin da yasa kake
ganin abin ba ya tafiya da sauri kamar ya kamata, shi ne babu inganci cikin
tsarin Intanet din da kake amfani da shi.
Da a ce muna amfani da tsarin "Broadband" ne, da garau za ka
gani, babu wani saibi balle tangarda.
Wannan shi ne kokarin da ake ta yi wajen ganin an inganta tsarin
sadarwar Intanet a Najeriya. A wasu
kasashe ba ka iya bambance tashar talabijin ta gama-gari, da tashar talabijin
ta Intanet (Internet TV), saboda ingancin sadarwar Intanet a kasashen. Da fatan
ka gamsu.
Salam, barka Baban Sadiq. Ga tambaya ta: wacce irin gudunmawa kake
ganin fasahar ICT za ta iya bayarwa ga nazarin Hausa? Ga adireshin Imail
dina nan. ismailaliyu@gmail.com Daga Waziri
Malam Ismaila sai ka duba akwatin Imel dinka, tuni na tura maka
kasidar Farfesa Abdallah Uba Adamu. Sai
ka saukar ka buga. Allah sa mu dace.
Assalamu alaikum, shin akwai yadda za a yi mutum ya samu
makalolinka na aminiya wadanda ka gabatar a baya ta hanyar Imail? Bissalam
Eh kana iya samu, sosai kuwa. Sai dai kuma ganin cewa suna da yawa,
ba za ka ji dadin karbarsu a lokaci daya ba.
Domin sun kai wajen 28MB, ma'ana mizaninsu ya kai wajen miliyan ashirin
da takwas. Sai dai a turo maka su kadan-kadan.
Ko kuma ka je shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don daukansu daya bayan daya, a duk
sadda kake so. idan kuma ka fi
sha'awansu samunsu ta Imel din, sai ka turo adireshinka a turo maka.
Assalamu alaikum, ka yi bayani dalla-dalla kan makalarka ta na'urar
ATM, amma ban ga ka ambaci na'urar daukar hoto ba, ko babu ita? Allah ya kara maka basira da lafiya. Alh. Ado
Damaturu
Alhaji Ado mun gode da wannan tsokaci naka. Hakika akwai na'urar
daukar hoto (Camera) a jikin wannan mashin.
Mancewa na yi ban ambace ta ba.
mun gode. Allah sa mu dace.
Baban Sadiq, ina gaisheka da kokari. In na fahimceka, shi kamfanin Interswitch
ke da ma'aikatan da ke rarraba kudaden ga bankunan da abin ya shafa kenan
kullum in gari ya waye? Kuma ladansu shi ne Naira 100 nan? Bashir Ibrahim, Port
Harcourt
Malam Ibrahim wannan wani abu ne da ba zan iya ce maka eh ko a a
ba. Sai dai ta la'akari da yadda ake gudanar da wannan abu a kullum; dare da
rana safe da yamma, zai yi wahala ace ma'aikaci ake turawa a duk safiya ya biya
bankuna. Abin da ke faruwa shi ne, akwai
cibiya ta musamman wacce ke tantance adadin kudaden da kowane bangare ke samu,
da kuma hanyar da ake bi wajen biya.
Wannan shi ake kira Electronic Clearing System. Da fatan ka gamsu.
Salam, zanso baban sadik yayima 'yan uwa yadda ake yin "money
tranfer ta hanyar na'urar ATM zuwa wani bankin. Daga Baban Mus'ab, Kaduna
An gaida Baban Mus'ab. Aiwayatar da wannan tsari na "Money
Transfer" bai da wata wahala ko kadan.
Idan ka je inda na'urar take, ka sa katinka, sai ka shigar da kalmomin
sirrinka (watau "Password"), za a budo maka inda za ka zabi
"Funds Transfer." Sai ka matsa,
ka zarce inda za ka shigar da lambar asusun wanda kake son aika masa, da bankin
da yake ajiya, da kuma adadin kudaden da kake son aika masa. Wadannan su ne abubuwan da ake bukata. Tsarin
bai da wahala ko kadan. Abin da za ka
kiyaye kawai shi ne, wajen shigar da lambar asusun wanda kake son aika masa, ka
tabbata ka shigar daidai, don kada a jefa kudaden zuwa asusun wani. Idan haka ta faru kuwa, kafin a mayar maka da
kudadenka zai dan dauki lokaci. Don sai
sun yi amfani da kundin adana bayanan da na'urar ke taskancewa, don tababtar da
da'awarka. Sai a kiyaye.
Salam, Baban Sadiq muna matukar farin ciki da rubutunka. Munji
dadin bayanin yadda ake mu'amala da katin ATM, wanda daman mafi yawanmu mata
bamu fahimce shi sosai ba. Allah ya yawaita mana irinka a cikin al'umma musulma,
amin. Daga Maman Abdulsamad Gombe.
Allah saka da alheri da wannan jinjina mara iyaka. Bai kamata albarka da rahamar da ke cikin
wannan addu'a su shafe ni ni kadai ba.
Ina rokon Allah ya sadar da su ga dukkan masu karatu, da masu lura da
wannan shafi a ofishin AMINIYA, da
editan jaridar baki daya, kai, da ma kamfanin Media Trust baki daya. Allah tara mu cikin alheri, ya sa mu cikin
sahun masu ciyar da al'umma gaba baki daya, amin. Mun gode.
Salam, barka da kokari Baban Sadik. Dan gyara ne akan makalar da ka
yi a Aminiya ta 23 ga watan Satumba, inda kace "Marigayi Mudi Sipikin." Yana nan da ransa. A huta lafiya. Bashir Gwale, Kano
To, malam Bashir na gode. Kafin wannan sako naka ma akwai wadanda
suka bugo waya suka mini gyara kan haka.
Gaskiya ba gani nayi a rubuce ba, illa dai na dade ban ji duriyarsa ba
tsawon shekaru, sai na dauka ya rasu.
Don ina da mantuwa sosai; akwai wadanda Allah ya musu rasuwa, amma
saboda tsawon zamani sai in dauka suna raye.
Wannan nakasa ce daga gare ni.
Allah sa mu cika da imani. Na
gode.
Shin, me ke haifar da rikicewar sauti idan aka yi amfani da wayar
salula a kusa da rediyo ko talabijin? Daga Ashiru Dan'azumi Gwarzo.
Malam Ashiru ai kuwa mun sha yin bayani a wannan shafi a baya. Watakila ba ka riski bugun da ke dauke da
bayanin da nayi ba. Abin da ke haddasa
haka shi ne, da sauti, da haske, da iska, duk kowanne daga cikinsu yana da
hanyarsa daban ne a sararin wannan duniya ta mu. Duk sadda wani ya shiga hanyar wani, nan take
ake samun tangarda. Kamar ruwa ne da
muke sha da kuma iskar da muke shaka; kowanne hanyarsa daban. Idan wani ya shiga tafarkin wani, dole a samu
matsala. In abin ma yazo da karen kwana,
shikenan. Tsarin yanayin sadarwar rediyo
ta sha bamban da na wayar salula. Idan
aka samu cin karo a tsakaninsu dole a samu matsala. Haka tsarin sadarwa idan ya ci karo da hanyar
wutar lantarki, a kan samu matsala. Shi
yasa idan ka kusanci dirkan wutar lantarki da rediyonka, za ka ji tashoshin sun
rikice. Da fatan ka gamsu.
Salam Baban Sadik, ya aiki? Kullum idan na shiga shafin Blog
di na na google, sai na ga sako cewa "zan iya samun kudi ta hanyar Adsense."
Shin ya abin yake ne? Bashir Ahmad
Malam Bashir kenan! Ai
wannan wata sabuwar hanya ce da kanfanin Google ya kirkira don samun abin
masarufi ga masu gidajen yanar sadarwa ko shafukan Mudawwanai (Blogs). Idan ka je kayi rajista, za ka basu adireshin
gidanka, da lambar taskar ajiyarka, da adireshin gidan wayarka, da kuma
adireshin gidan yanar sadarwarka. Bayan
wasu 'yan kwanaki za su turo maka wasu shafuka da za ka shigar a shafinka, masu
dauke da tallace-tallace kan abin da ke da nasaba da bayanan da ke
shafinka. Duk wanda ya ziyarci shafinka,
idan ya matsa wadannan bayanai na tallace-tallace masu dauke da bayanai da ke
shafinka, akwai masarrafar da ke kididdige yawan matsawar da masu ziyara ke yi. A karshen wata sai a duba yawan shafukan da
aka matsa na tallace-tallace, sannan a kirga maka kudinka. Kowane matsawa akwai adadin kudinsa. Wannan shi ake kira "Pay Per
Click." Idan a karshen wata kudinka
ya kama dala dari biyar ne, sai su aiko maka da "Money Order." Takardar kudi ce mai dauke da adadin
kudinka. Kana iya zuwa banki ka sanya
cikin taskarka, idan kana da taska mai daukan daloli (Dormiciliary Account). Amma dole mu sani cewa, Google na da masarrafar
da ke lura da wadanda ke matsawa. Haramun ne a gareka a matsayinka na mai shafin,
ka matsa kowanne daga cikin wadannan bayanai na tallace-tallace. Idan ka matsa,
sun sani. Domin wasunmu sai su dauka ko
Google wawaye ne, sai su ta matsawa. Wannan zamba cikin aminci ne, kuma suna
iya ganewa, kuma ba za su kirga da irin wadannan matse-matse na cuta ba. Haka idan ka umarci wasu su rika matsawa don
dabara, duk suna lura. Domin suna da bayani kan inda kake zama, don haka idan
yawan masu matsawan suna wuri guda ne da kai, duk baka tsira ba. Abin da ake so shi ne, ka bar abin yadda
yake, duk wanda ya matsa, za a kididdige maka.
Ko a musulunci bai kamata ka matsa ba, bai kuma kamata ka umarci wani ya
matsa maka ba. Ka hakura da abin da ka samu na halal, shi yafi mai yawa na
haram. Da fatan ka gamsu.
Allah ya kara lafiya da ilimi da nisan kwana. Allah ya raya iyali.
Allah ya sa mu dace, amin. Abba Ibrahim
Gwan-Gwan, Mai bibiyar rubutunka a kodayaushe.
Malam Abba mun gode da addu'ar fatan alheri, kuma Allah biya mana
bukatunmu gaba daya, baki daya, amin.
Duk matsalolin da muke fama da su a al'ummance, Allah mana maganinsu,
amin.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, dan Allah a taimaka mini; duk sadda
na shiga masarrafar Google Maths don aiwatar da wani lissafi, amsar ba
ta fitowa, sai dai a kawo mini wasu misalai daban. Daga Sadiq Usman, Bauchi
Malam Sadiq yana da kyau ka san cewa masarrafar "Google Maths"
masarrafa ce mai dauke da tsarin mu'amala.
Duk sadda ka zo amfani da ita don neman amsar wata ka'ida ta lissafi
(maths formular solution), dole ne ka shigar da ka'idojin da suka kamata. In kuwa ba haka ba, ba za ka samu amsar da
kake so ba. Sai dai ta yi ta rubuto maka
misalai, don ka samu misali kan abin da ya kamata ko yadda ya kamata ka shirya
tambayarka. A tunanina wannan shi ne
abin da yasa suke ta aiko maka da wasu
misalan. Ka tabbata ka shigar da ka'idar
lissafi (maths formular) sananniya, kafin neman a baka amsa. Sai a kiyaye nan
gaba.
Salam, Baban Sadiq ina karuwa da kuma samun annashiwa game da
rubuce-rubucen kimiyyarka a cikin jaridar Aminiya. Sai dai na so in san tazarar
Tauraron binciken daga duniya a zamanin shawaginsa a kololuwar sama da kuma
irin nasarar da ya cimma a lokacin rayuwarsa.
Ibrahim Zubairu, Kufena College Zaria
Malam Ibrahim bayanai makamantan wannan sai dai a je gidan yanar
sadarwar NASA, watau Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta kasar Amurka. Gidan yanar sadarwarta na www.nasa.gov in Allah ya yarda za a samu dukkan
wadannan bayanai. Kada a mance, sunan
wannan Tauraron dan adam dai shi ne: Upper Atmosphere Research Satellite
(UARS). Da fatan an gamsu.
Assalamu alaikum. Yanzu na gama karanta makalarka. Allah Ya saka da
hairan, kuma Ya taimaka. Nadabo Idris Dabi, Ringim.
To amin, Malam Nadabo. Muna
godiya har kullum. Allah saka da
alherinsa, amin.
Assalamu Alaikum, Baban Sadik Allah ya saka ma da alheri akan
wannan karantarwa da kake yi a jaridar Aminiya, a filin Kimiyya. Da fatan Allah
ya kara maka fahimta da ilmi mai amfani, domin anfanarwa, Allah kuma ya yi
jagora, amin. Daga Muhammad, Kyari,
Aumtco.
To ni ma ina godiya sosai Malam Muhammad. Allah mana jagora baki daya, ya kuma sa mu
zama haske ga al'umma ba duhu ba, amin.
Salam Baban Sadik, barka ya aiki. Don Allah ina so ka turomin mukalolin
da ka rubuta a AMINIYA kan Facebook, Twitter, Youtube, Wikileaks da Wikepedia,
ta auwalabdulqadirsani@yahoo.com. Wassalam
There are various online auction sites that you just can check out every so often if you wanted to find the best prices on your ugg boot.
ReplyDeletePeople of every class and level can simply get these because their cost is of every range.
And utilization with the preserving stratum in the knock-off is oftentimes a easy preventative pelage - not the
genuine authenticated guy who can conflict users; the assembly is her toes when her vernacular users of
sea boots check within the U.
Stop by my blog :: グッチ
There is really a lot surprise this particular simply just released sorts
ReplyDeleteare listed below: uggs estimates boots mayfair shoes or boots girls java Highkoo Microsof corporation 5450 fight-style exceptional.
When it comes to the most styling infant, dress your kids in uggs.
Nevertheless, with super delicate ease and convenience,
increased desire, and wintertime season approaching, you can still discover some great
provides.
Here is my blog; gucci
kuşadası
ReplyDeletesakarya
sinop
bolu
burdur
UGS