Matashiya
Cikin shekarar da ta gabata ne muka fara jero kasidu na musamman kan Wayar Salula da tsarin amfani da ita, musamman wayoyin salula na wannan zamani da lokaci da muke ciki. Kasida ta karshe da muka dakata a kanta ita ce wacce mai karatu ya karanta kan wayoyin salula na musamman da ake kira Black Berry. A wannan mako kuma in Allah ya so, za mu kutsa cikin bayani kan abin da ya shafi Ayyukan Wayar Salula. Duk da cewa wannan wani bangare ne da mai karatu watakila zai ce ya san wani abu a kai, sai dai hakan ba shi zai hana kawo bayani kan shi ba. Dalili kuwa shi ne, mun yi alkawarin cewa za mu kawo dukkan bayanan da suka shafi wayar salula ne, ba don komai ba sai don samun isassun bayanai kan wannan fanni.
A fannin kimiyyar fasahar sadarwar zamani, idan aka ce Mobile Phone Services, abin da ake nufi shi ne, ayyukan da wayar salula za ta iya taimaka wa mai mu'amala da ita wajen yi. Wasu lokuta za ka samu waya ta zo da abubuwan amfani masu dimbin yawa, amma mai wayar bai ma san da su ba. A wasu lokuta kuma sai ka samu abin da wayar ta zo da su na amfani ba su da yawa, amma saboda hazaka da kwarewar wanda ke amfani da wayar, za ka ga yana ta anfama da ita ta wasu hanyoyi masu ban mamaki. Wannan, a takaice, shi ne zai nuna mana cewa, ayyukan wayar salula basu tsaya a kan irin abin da kamfanin wayar ya tsara mata kadai ba, a a, har da kwarewar da mai amfani da wayar ke da ita, wanda hakan ne ke dada fitar da wasu hikimomin da ke taimakawa wajen sake kirkirar wasu wayoyin masu irin dabi'ar da aka yi amfani da su a baya.
Ayyukan wayar salula suna da yawa, wasu a bayyane suke, wasu kuma a boye suke. Wasu kuma, kamar yadda bayani ya gabata a sama, sai mai karatu ya caja kwakwalwarsa sannan zai hankalto abin da wayarsa za ta iya yi. Su wayoyin salula kamar kwamfuta suke; iya gwargwadon kwarewarka wajen fahimtar tsarin amfani da su, iya gwargwadon amfanin da za ka iya yi da su. A nan nake ganin dacewar sanar da masu karatu wasu ka'idoji masu saukin fahimta, wadanda kuma za su iya taimaka musu yadda za su yi mu'amala da kayayyakin fasahar sadarwa. Ina ganin zai dace in fara kawo su, kafin mu shiga bayani kan irin ayyukan da wayoyin salula za su iya taimaka wa mutum aiwatarwa.
Wasu Ka'idojin Fasahar Sadarwar
Ga wasu ka'idoji guda uku masu saukin fahimta, kuma muddin mai karatu ya lazimce su zai samu sauki wajen mu'amala da wayar salula, ko kwamfuta ko duk wani kayan sadarwa na zamani, in Allah ya so. Ka'ida ta farko ita ce: wayar salula na'ura ce ta sadarwa, kuma tana iya aikin sadarwa tsakaninta da duk wani kayan sadarwa na zamani a yau. Abin da wannan ka'ida ke nufi shi ne, idan kana da wayar salula, to, kana iya aiwatar da sadarwa a tsakaninka da duk wani kayan sadarwa na zamani, irinsu kwamfuta, da wata wayar salula irinta, da talabijin, da fasahar Intanet, da kuma na'urar sadarwa ta kamfanin wayar salula. Kana iya amfani da wayarka wajen zuba bayanai a kwamfuta, da mayar da wayar zuwa makalutun sadarwar Intanet, watau Internet Modem, don aiwatar da sadarwa a tsakaninka da Intanet, ko kiran abokinka ta hanyar kwamfutar da ka jona da wayarka. Sannan kana iya amfani wayarka don kallon tashoshin talabijin, musamman ga wayoyin da aka kera su musamman don aiwatar da irin wannan nau'in sadarwa. Kana iya aiwatar da sadarwa tsakanin wayarka da fasahar Intanet, kai tsaye, muddin wayar tana da ka'idojin mu'amala da tsarin sadarwa ta wayar iska, watau Wireless Application Protocol, ko WAP a gajarce. Bayan haka, kana iya aiwatar da sadarwa a tsakanin wayarka da na'urar kamfanin sadarwar tarho, wadanda kake amfani da katin SIM dinsu. Wannan abu ne mai sauki, kuma na tabbata duk muna yi lokaci-lokaci, idan mun fara fuskantar wasu matsaloli da layinmu.
Ka'ida ta biyu ita ce: Wayoyin salula (da sauran kayayyakin sadarwa na zamani) na'urori ne masu kawo tsari cikin rayuwar mai amfani da su. Wannan ka'ida za ta fi fitowa fili ne idan mai karatu yayi la'akari da irin manhajonjin da wayoyin salula na zamani ke zuwa da su, musamman a yau. Wadannan manhajoji kuwa su ne wadanda ke taimaka masa wajen taskance bayanansa, da tsara su dabaka-dabaka, da alkinta su, da kuma nemo su cikin sauki, a duk sa'adda ya tashi bukatarsu. Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, muddin kana da wayar salula, to, lallai za ka iya amfani da ita hanyoyin da za su taimaka maka tsara rayuwarka a wayar, musamman wajen adana bayanai, rubutattu, ko na murya/sauti, ko kuma na bidiyo. Idan kana son sanin karfin wayarka wajen tsara rayuwarka, ka zauna ka tsara yadda kake ka aiwatar da hakan, sannan ka dauko wayar ka fara zartar da tsarin da kake so.
No comments:
Post a Comment