Fadakarwa
Na lura a duk lokacin da muka gabatar da wata kasida kan fannin likitanci ko kimiyyar magunguna, sau tari sai masu karatu su yi ta bugo waya ko aiko sakonnin tes suna neman bayanai kan wasu nau'ukan kawayoyi ko cututtuka da yadda za a magance su. Ba komai ya jawo haka ba sai don irin bayanin da suka gani a shafin, wanda a cewarsu sun gamsu da su. Wanann a baya kenan. A yanzu da kashin farko na wannan kasida kan hasken leza ya bayya a makon baya, wasu ma sun yi ta kira suna neman bayanai kan yadda za su fusktanci wasu matsaloli masu alaka da bayanan da suka karanta, inda nan take nake katse su saboda rashin alaka a tsakanin abin da suke nema da kwarewar mai rubutun.
Na sha maimaita mana a baya, zan kuma kara maimaitawa cewa, wannan shafi na FADAKARWA ne kawai. Duk da cewa muna taimakawa wajen magance matsalolin da suka shafi wayoyin salula da yadda ake mu'amala da fasahar Intanet a aikace, amma a bangaren likitanci babu abin da zan iya yi sai fadakarwa. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa ban cika son kawo bayanai kan fannin likitanci ba, don ba fanni na bane ko kadan. Duk wanda ke son shawara kan abin da ya shafi kiwon lafiya gaba daya, akwai shafin Dakta Auwal Bala, kana iya daukan lambar wayarsa ka rubuta masa tes don neman Karin bayani. Amma Baban Sadiq ba likita bane, ba kuma kwararre bane a fanni likitanci, don Allah mu kiyaye. SHAFIN KIMIYYA DA KERE-KERE SHAFIN FADAKARWA NE KADAI, BA SHAFIN BA DA SHAWARA KAN HARKAR KIWON LAFIYA BANE. Haka akwai masu bugo waya suna neman Karin bayani kan hotunan wayoyin salula ko kwamfuta da ake sanyawa a shafin; idan na sayarwa ne, suna so. Wannan ma ba na sayarwa bane. Kuma ba na sayar da kwamfuta ko wayar salula, sai dai in ba da shawara kan irin wacce za a iya saya, iya gwargwado. Duk hoton da aka gani a shafin, an sa ne don fadakarwa, da kuma munasabar bayanin da ke shafin da hoton da aka sa. Domin wasu har cewa suka yi idan na sayarwa ne za su aiko da kudi. Ba haka lamarin yake ba. Don Allah mu kiyaye. Na gode.
No comments:
Post a Comment