Wednesday, November 2, 2011

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu ta Tes

A yau kuma, kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, ga mu dauke da sakonninku da kuka aiko to tes. Galibin sakonnin da nake samu ta Imel nan take nake amsa su, musamman idan ba suna dauke ne da wasu bukatu da ke bukatar doguwar bincike ba. Bayan haka, idan sako ya sha maimaituwa ba na amsa shi. Don haka sai dai a yi hakuri. Idan muka ce za mu rika maimata tambayoyi, musamman ma wadanda suka sha maimaituwa a wannan shafi, a gaskiya ba za mu ci gaba ba. Da fatan za a yi hakuri da wannan ka'ida. A yanzu dai ga abin da ya sawwaka.

…………………………………………………….

Baban Sadik, da fatan kana lafiya amin. Tambayata ita ce, ko akwai wani tsari da za a iya yi kamar yadda ake sa kudi a waya, dangane da harkar zabe, wajen amfani da "finger print scanning machine" yadda idan ka yi sau daya ba za ka sake yi ta dauka ba? Daga Alh. Zubairu Garabasa, Kazaure.

Alhaji Zubairu ai wannan ba wani abu bane, ya danganci irin tsarin da Gwamnati ke so ko ke da karfin yi. Dangane da abin da ya shafi ingancin rajistar masu zabe akwai tsare-tsare da na'urori daban-daban. A wasu kasashe suna amfani ne da katin dan kasa, watau "National ID Card", don duk wanda ka ganshi da katin, to dole ya cika shekaru 18 kafin aka bashi. Da zarar lokacin zabe ya zo, sai dai kaje wajen hukumar zabe ta tantance ka kawai. Don haka da Gwamnatin tarayya za ta dage ta inganta wannan tsari, cikin lumana kowa ya samu, ba wai a kama bikin kaddamarwa, har ana kayyade iya ranakun da za a yi rajistar ba, a a, a bar abin a bude kawai. Duk sadda ka cika shekara 18 kaje ofishin hukumar lura da harkokin cikin gida ta maka rajistan katin dan kasa, shikenan. Da mun huta da galibin matsalolin da muke fuskantarsu a duk lokacin da zabe ya taso. Allah shige mana gaba, amin.

Salamu Alaikum, wai shin da gaske ne akwai TV mai amfani da fasahar Bluetooth? Kuma ana iya samu a saya? - Ameerah

Malama Ameera sosai kuwa. Ai duk abin da aka ce akwai shi an kera, ya kamata a same shi a kasuwa har a saya. Ba wai Talabijin mai amfani da fasahar Bluetooth kadai ba, hatta talabijin mai amfani da fasahar Intanet akwai, wanda kamfanin Apple ya kera shekaru kusan hudu da suka gabata. A halin yanzu akwai talabijin mai amfani da fasahar Bluetooth da kamfanonin Apple, da Samsung, da LG suka kera kuma ake sayarwa a kasuwa, musamman turai. Na kamfanin LG ne ya fito a baya-bayan nan. Sauran kuma sun jima da fitowa. Da fatan Malam Ameera ta gamsu.

Salamun alaikum Baban Sadik. Tambayata ita ce, me ye bambancin da ke tsakanin MS-DOS da MS-WINDOWS? - Aliyu Mukhtar Sa'idu (I-T) Kano: aliitpro2020@yahoo.com 08034332200/08186624300.

Malam Aliyu akwai bambanci mai girman gaske a tsakanin manyan manhajojin guda biyu. Da farko dai, ita MS-DOS, ko kuma "Microsoft Disk Operating System" a warware, ita ce babbar manhajar kwamfuta da kamfanin Microsoft ya fara ginawa da sayar da ita ga kamfanin kera kwamfuta ta IBM, shekaru sama da ashirin da suka gabata. Wannan manhaja ce da ke amfani da hanyar mu'amala da kwamfuta da ake kira "Command Prompt", don baiwa kwamfutar umarni kan abin da za ta yi. Idan kana bukatar gudanar da wasu ayyuka kamar rubuce-rubuce ko kuma amfani da wasu manhajoji, dole ne sai ka tsofa mata manhajar ta amfani da ma'adanar "Floppy Disk", sannan za ta iya dauka. Wannan ya faru ne saboda kwamfutoci a lokacin nan ba su da mizanin sarrafa bayanai ko gudanar da ayyuka masu inganci, da karfi, kuma ga rashin mizanin ma'adana isasshe.

Amma daga baya wajen shekarar 1990, sai Bill Gates ya gina babbar manhajarsa mai suna "Windows 3.0", wacce ke amfani da tsarin gudanarwa mafi sauki; za ka baiwa kwamfuta umarni ta hanyar matsa wata alama, ita kuma ta amsa maka, ko dai ta hanyar aiwatar da aikin kai tsaye, ko kuma idan tana neman karin bayani sai ta cillo maka tambaya ita ma a rubuce, kamar dai yadda kwamfutoci suke a yanzu. Wannan tsari shi ake kira "Graphical User Interface" ko "GUI" a gajarce. Daga nan ake kiran wannan babbar manhaja da suna "Microsoft Windows" ko kuma "MS-Windows" a gajarce. Bambancin da ke tsakanin manhajojin biyu kuwa a bayyane yake. Na farko dai MS-DOS tana amfani ne da tsarin "Command Prompt" wajen baiwa kwamfuta umarni, a yayin da manhajar MS-Windows ke amfani da tsarin "Graphical User Interface", kamar yadda bayanai suka gabata. Sannan tsarin MS-Windows ta fi ingnaci da saukin mu'amala fiye da tsarin MS-DOS. Bayan haka, a tsarin MS-DOS dole ne ka tanadi dukkan masarrafan da kake bukata a cikin ma'adanar "Floppy Disk", domin kwamfutoci a lokacin ba su da hanyar shigar da bayanai na CD/DVD, ko USB, sai dai FDD kawai. Don haka idan masarrafai talatin kake son amfani da su, dole ne ka tanadi ma'adanan Floppy Disk guda talatin masu dauke da su. Amma a tsarin MS-Windows duk ba ka bukatar yin haka. Idan kana bukatar amfani da wata manhaja, to za ka same ta cikin kwamfutar gaba daya, idan ma babu a ciki, kana iya saya, sai ka loda mata, ba sai ka tanada a cikin ma'adanar Floppy Disk ba. A takaice dai wadannan su ne kadan daga cikin bambance-bambancen da ke tsakanin MS-DOS da MS-Windows. Da fatan ka gamsu.

Salamu Alaikum Baban Sadik, Tambayata itace: tsarin hada alaka a tsakanin kwamfutoci (NETWORKING) ya kasu gida nawa ne malam?. Daga Aliyu Mukhtar Sa'idu (I.T) Kano Email: aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 / 08186624300.

Tsarin hada alaka a tsakanin kwamfutoci dai ya kasu kashi uku ne muhimmai. Akwai hadin gajeren zango, watau "Local Area Network," ko LAN a gajarce. Wannan tsari ne da ya shafi hada alaka a tsakanin kwamfutoci ta hanyar jojjona su da wayoyin kebul nau'in RJ45. Kuma hakan na yiwuwa ne a tsakanin kwamfutocin da ke cikin wani gida, ko ofishi da ke wuri daya, ko wata ma'aikata da ke waje daya. Idan ma'aikatar na da reshe daban-daban a wasu garuruwa ko jihohi, sai a yi amfani da tsari na biyu, watau "Wide Area Network," watau WAN kenan a gajarce. Shi wannan tsari yana amfani ne da tsarin sadarwar wayar iska, watau "Wireless Communication System." Tsari na uku kuma shi ne "Virtual Private Network," ko VPN a gajarce. Shi wannan tsari shi ma dai kamar wanda ya gabace shi ne, sai dai shi ya fi dogaro kan tsarin sadarwa ta wayar iska fiye da WAN, sannan ana amfani da shi wajen sadarwar wayar tarho irin na zamani a tsakanin rassan kamfani guda da ke wasu bangarorin jiha ko kasa daya. Da fatan ka gamsu.

Salamu alaikum Baban Sadik, Tambayata itace, ko adadi nawa ne da kamfanoni Manhajar Imel a Duniya? Daga: Aliyu Mukhtar Sa'idu (IT) Kano Email: aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 / 08186624300.

Kamfanonin manhajar Imel suna da yawa a duniya. Da farko dai manhajar Imel nau'i biyu ne; akwai wanda ke ta'allake da fasahar Intanet. Wadannan su ake kira "Internet Mail Program", kuma ire-irensu sun hada da na kamfanin Yahoo, da Hotmail, da Gmail da dai sauransu. Sannan akwai manhajar Imel wacce ake loda wa kwamfuta don amfani da su a tsarin sadarwa na gajeren zango ko dogon zango, kamar yadda bayanai suka gabata a sama. Ire-iren wadannan manhajar Imel ba su bukatar samuwar Intanet a kwamfuta kafin aika ko a karbi sako ta hanyarsu. Su ma akwai su da yawa; akwai Outlook na kamfanin Microsoft, akwai Thunderbird na kamfanin Mozilla da dai sauransu. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina son in saita Imail na wayar salula Nokia x2-01. In na tura musu sai a ce "Invalid Password", yaya zan yi? – Daga Legas

Akwai alamun dayan abu biyu. Ko dai ba ka da tsare-tsaren kamfanin waya mai sawwake hanyar sadarwa, watau "Configuration Settings," ko kuma ka mance kalmomin iznin shiganka na Imel. Idan har kana iya mu'amala da Intanet a wayar, to, ba matsala, watakila ka mance kalmomin iznin shiganka ne, watau "Password." Amma idan ba ka iya mu'amala da Intanet gaba daya a wayar, dole ne ka bukaci kamfanin wayarka ya aiko maka da wadannan tsare-tsare. Da fatan an gamsu.

Salam, ina jin dadin rubutunka. Don Allah ina son ka yi min bayanin yanda zan yi amfani da faifan dish wajen shiga yanar gizo. Allah ya kara basira. Daga N. I. Usman

Malam Usman hanyar amfani da dish wajen zuko tsarin sadarwa ta Intanet zuwa jikin kwamfuta ba abu bane mai sauki, domin yana bukatar kwarewa a fannin mu'amala da tsarin sadarwar tashoshin tauraron dan Adam, da kuma sanayya kan tsarin sadarwa ta kwamfuta. Bayan haka, akwai wasu kalmomin sirri da ake shigarwa, wadanda kuma ke caccanzawa a lokuta daban-daban. A takaice dai ba abu bane mai yiwuwa ta dadi, domin yana bukatar dabaru nau'uka daban-daban. Idan akwai kwararru masu gyaran tashoshin tauraron dan adam kana iya tuntubansu. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, wai don Allah wace shekara ce aka kirkiro kwamfuta? Kuma wa ya kirkirota? Kuma dan wace kasa ne? Sannan wane kamfani ne a yanzu ya fi kera kwamfuta? Wacce tafi kowacce tsada? Kuma da gaskene akwai kwamfuta marar malatsi ko daya watau touch screen? Na gode. Daga Ibrahim Aliyu Marcury

Malam Ibrahim a gaisheka. Dangane da wanda ya kirkiri kwamfuta, babu mutum guda daya da za a ce shi ne ya kirkiro kwamfuta. Domin kuwa na'ura ce mai dauke da bangarori da yawa. A takaice dai masana sun nuna cewa kwamfuta ta samo asali ne daga na'urar kidaya, watau "Counting Machine", irinsu "Abacus" da dai sauransu, kuma wanda ya yi fice dai cikin wannan fanni shi ne Charles Babbage. Bayan shi, akwai kwararru masana fannin lissafi yan kasar Sin da suka kirkiri irin wannan fasaha. Kuma daga wannan fasaha ce aka samu fikira da tunanin kirkirar kwamfuta. Babu wanda za a ce shi ne ya kirkireta shi kadai, sannan babu wata shekara da za a ce lokacin ne kwamfuta ta samu kai tsaye. Saboda kamar yadda na fada a farko, tana dauke ne da bangarori daban-daban. Akwai bangaren gangar-jiki da bangaren manhajarta. Kowannensu yana da nashi tsari da tarihi. Akwai kwamfutoci nau'uka daban-daban a yanzu kam, har da marasa malatsi kamar yadda kaji. Babu wani kamfani har wa yau da za a ce shi ne yafi kera kwamfutoci, da'iman. Ya danganci lokaci ne kawai. Akwai kamfanonin da ke gina manhajar kwamfuta zalla, irinsu kamfanin Microsoft, kuma shi ne kamfanin da ke kan gaba dangane da abin da ya shafi manhajar kwamfuta. Akwai masu kera gangar-jikin kwamfuta zalla, tare da masarrafar da ke tafiyar da su, irinsu HP, da Dell, da Gateway, da IBM da dai sauransu. Kwamfutar da tafi kowacce kudi ita ce wacce tafi su yawan mizani, da ingancin masarrafar gudanarwa (Processor), da ingancin kira, da kuma shaharan kamfanin da ya kera kwamfutar. Samun wadannan sifofi a jikin kwamfuta guda daya ba abu bane mai yiwuwa a yau. Idan aka samu wacce tafi ingancin masarrafar gudanarwa, za ka samu akwai wacce ta fi ta girman mizani. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, muna karuwa da wannan shafi Allah ya saka da alheri amin. Ina neman shawararka wajen bude shafi a Dandalin Facebook; wanne layin sadarwane ya fi, tsakanin layin MTN da Glo da Airtel? Godiya nake sai na ji ka. Daga salisu Nagaidan mai biredi, Jama'are Jihar Bauchi 08063461480

Malam Salisu muna godiya kamar kullum da addu'o'inku. Allah bar zumunci, amin. A gaskiya ba zan iya ce maka ga layin da yafi inganci ba, don ban taba amfani da su duka a dukkan jihohin Najeriya ba. Abu na biyu kuma shi ne, ya kamata ka san cewa ingancin sadarwar wayar tarho da ta Intanet, duk suna ta'allaka ne da inda kake zaune. Ba wai abu bane wanda yake bai daya. Misali, tsarin sadarwar wayar salula a galibin lokuta sun fi karfi da inganci a manyan birane fiye da kauyuka. Ko kusa ba za ka hada ba. Sannan a manyan biranen ma sun fi karfi a cikin gari, idan ka kwatanta da karfinsu a wajen birni, kafin a shiga kauyuka. Don haka sai ka yi la'akari da bayanan da nayi a sama, duk wanda ya dace da yanayinka sai ka dauka. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, shin wai dole ne duk wanda zai bude shafin Facebook sai yana da rajistar Imel? Bashari I. Gumel

Malam Bashari wannan zance haka yake. Sai kana da adireshin Imel, idan kuwa ba haka ba, ba za a baka damar budewa ba. Sai a yi kokari a bude, don a samu damar shiga da damawa da sauran jama'a.

Baban sadik ya aiki? Ina da sakonnin tes a wayata, kuma ina son in canza wayar, ko akwai yadda zan iya kwafar su zuwa wata wayar? Kuma me ya sa 8 Gigabyte ba ya yi a wasu wayoyin? A. W. Ayagi

Dubun gaisuwa ga Abul Waraqaat. Ya danganci irin wayar da kuma wadda ake son canzawa. Idan dukkansu wayoyin Nokia ne, ai ba matsala Malam Rabi'u. Idan ka kunna sabuwar, sai ka je cikin "Menu" inda aka rubuta "Switch", sai ka matsa, za a budo maka hanyoyin da ake gudanar da wannan aiki cikin sauki. Ba shi da wahala. Abin da ya rage shi ne, dole ka kunna fasahar Bluetooth din tsohuwar wayar, wacce kake son kwaso kayayyakinka daga cikinta. A haka sabuwar za ta kwaso maka dukkan bayananka, daga sakonnin tes, zuwa na murya da bidiyo da hotuna. Bayan haka, mizanin ma'adanar bayanai na 8Gigabyte ba lallai bane ya yi a jikin kowace wayar salula. Kowace waya akwai iya girman mizanin da za ta iya dauka, wanda shi yayi daidai da karfin masarrafar gudanarwarta. Da fatan Abul Waraqaat ya gamsu.

Gaisuwa ga Baban Sadik. Dan allah me ye ke kawo kwayoyin cutar kwamfuta (Virus) a waya? Daga zahra'u Kawo, Kano state.

Malama Zahra'u akwai dalilai masu yawa da ke haddasa samuwar kwayoyin cutar kwamfuta a jikin wayar salula. Wasu daga cikinsu su ne, idan aka kwafa bayanai ta hanyar Bluetooth, muddin wayar da ke bayar da sakon tana dauke da wadannan kwayoyin cuta, to mai karba ma za ta kamu nan take. Haka idan ta fasahar Infra-red ne. Haka idan aka yi amfani da wayar debo bayanai a kwamfuta zuwa wayar salula, watau USB Cable. Idan kwamfutar da za ta bayar da bayanan ita ma tana dauke da kwayoyin cutar, dole wannan waya ta kamu nan take. Haka idan kika yi amfani da ma'adanar bayanai ta wayar salula, watau "Memory Card" mai dauke da kwayoyin cutar a wayarki, nan take wayar za ta kamu. Wadannan, a takaice, su ne shahararrun hanyoyin da wayar salule ke iya kamuwa da wadannan kwayoyin cutar kwamfuta, watau Virus. Da fatan Malama ta gamsu.

Assalamu alaikum Malam, shin da gaske ne kowanne dan adam kalar zanen yatsunsa daban suke da na sauran yan adam? Daga Sabiu Uba, New Nigeria, Jimeta/Yola

Malam Sabi'u wannan zance haka yake. Kowane dan adam da ka gani yatsun tafukan hannunsa sun sha bamban da na wani daban, ko a ina yake kuwa. Kai ba ma wannan ba kadai, a duniya ba za ka taba samun mutane biyu masu kama ta kowane bangare ba, ko da kuwa 'yan biyu ne. Idan ka kalle su kyakkyawar kallo sai ka gane akwai bambancin kira da tsarin jiki a tsakaninsu. Wannan aya ce mafi girma da Allah ya samar a jikin dan adam, don yayi nazari kansu, ya san Ubangijinsa shi ne wanda ya cancanci bauta tabbas, ba wani ba. Sanin hakan kuwa daga jikinsa shi yafi sauki. Wannan ne har wa yau ta sa masana suka kirkiri hanyoyin tantance zanen yatsun hannu ta hanyar amfani da na'urorin zamani. Domin a duniya, kamar yadda ka ji, babu mutane biyu masu zanen hannu iri daya. Ba a taba ba ko a baya, ba a yi ba halin yanzu, sannan nan gaba ma Allah ba zai taba halittar mutane biyu masu zanen hannu iri daya ba. Wannan na daga cikin cikakkun hikimomin Ubangiji a tsakanin halittarsa. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, don Allah Malam Abdullah ina neman karin bayani dangane da ilimin sararin samaniya, shin mene ne shi da turanci? Sannan mene ne "Girka" ko "Girkanci"? Daga Kabiru Yusuf Illela LG, Sokoto State.

Malam Kabiru, abin da kalmar "Ilmin Sararin Samaniya" ke nufi a harshen Turanci shi ne "Astronomy", kuma shi ne fannin ilmin da ke lura da halittar duniya baki daya; da rana, da wata, da taurari, da dukkan halittun da Allah Ya sanya a tsakaninsu. Kalmar "Girka" kuma, tana nufin kasar "Greece" ce ta yau. "Girkanci" kuma na nufin harshen "Greek"; daya ne daga cikin harsunan duniya da suka fi dadewa. Da fatan an gamsu.

Assalamu alaikum don Allah Baban Sadik ina son a min bayanin yanda ake yin hasashen rana da na ruwa? Allah ya kara basira. Daga Umar Honest man Numan, Jihar Adamawa.

Malam Umar bayani kan yadda ake hasashen yanayi gaba daya, ba abu ne da za a iya yinshi a wannan muhalli da yanayi. Hakan na bukatar bincike da tantancewa. Don haka idan Allah ya so za mu yi bincike na musamman kan hakan, don samar da abin dogaro na ilmi a kimiyyance, kuma cikin sauki. A gafarce ni.

Baban Sadik barka da warhaka. Wata rana cikin shekarar 1995, muna kasar Chadi misalin shabiyu da rabi na dare, a cikin dokar daji, muna shan irin shayinsu sai wani abu ya bi ta samanmu yana huci, a guje. Yana gudu fiye da gudun jirgi. Tsawonsa bai fi zira'i biyu ba, haskensa farin haske ne. Idan ya wuce inda kuke ganinka zai dauke gaba daya saboda tsananin haske. Ga kuma ban tsoro. Ko mene ne kuma wannan? Daga Babangida: 08033966164

Ire-iren wadannan al'amura suna nan da yawa, wadanda a gaskiya babu wanda zai iya maka bayani cikakke kan ko mene ne, musamman idan ba a wurin yake ba. Akwai abubuwan mamaki masu faruwa a dukkan lokuta, kawai ya danganci wanda ka gani ne. Wani Malami dan kasar Masar mai suna Sheikh Ibrahim Ibrahim Al-Kurdee, ya rubuta wani littafi mai suna "Allamanil Kur'an, Min Aina Ataitu, Wa Ila Aina Aseeru", inda a ciki ya taskance ire-iren wadannan abubuwan al'ajabi da suka faru da shi lokacin da yake yaro dan karami, ko waninsa, ko kuma wadanda ya karanta a jaridu, da wadanda masana kimiyya suka labarta da dai sauransu. A takaice dai, ire-iren wadannan abubuwa ba kowa bane zai iya maka bayanin me suka kunsa, hatta cikin malaman kimiyya kwararru, sai da bincike, da bin kwakkwafi. Allah sa mu dace, amin.

Dan Allah Baban Sadiq yaya zan yi wa wayata don mu'amala da fasahar Intanet. Domin duk sadda na shiga zan yi sai ta rubuto min cewa: GPRS not subscribed, ko kuma ta rubuto min: Connection failed. Dan Allah yaya zan yi na magance wannan matsalar? Allah ya magance mana amin. Daga Shamsuddeenn Hamisu Maishinku Kano

Malam Shamsuddeen ai tuni wayar ta sanar da kai matsalar da take fuskanta. Abin da ya rage shi ne, ka yi kokari ka bukaci tsare-tsaren waya masu taimakawa a yi mu'amala da Intanet, watau "Configuration Settings", daga kamfanin wayarka. Idan MTN ne kake amfani da shi, sai ka rubuta SETTINGS ka tura zuwa wannan lambar 3888. Nan take za a turo maka wadannan tsare-tsare. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik da fatan kana lafiya. Watau ni makarancin shafinka ne na Kimiyya da Kere-kere. A yau ina duba shafinka na bayanin kwakwalwar dan adam shi ne na ga inda kace "silbi" ne ko kuma "saibi" domin kalmar "saibi" bakuwa ce a Hausa.

To, Malam na gode da wannan gyara naka. Sai dai kuma da ka sanar da ni cewa kalmar "saibi" (ba "silbi" ba rubuta ba) bakuwa ce, baka sanar da ni wacce ce ta dace in yi amfani da ita ba. Sannan, ina ganin duk da cewa kalmar bakuwa ce, hakan ba ya hana a yi amfani da ita, muddin an sanya ta a muhallin da mai karatu ko mai sauraro zai fahimci sakon da ke cikinta. Domin galibin kalmomin Hausa ai duk baki ne, wasu daga larabci, wasu kuma daga turanci. Duk da haka na gode da wannan tsokaci naka. Allah saka da alheri.

Assalamu alaikum. Baban Sadiq ina fatan kana lafiya, yaya aiki? Ko za ka yi mana karin bayani kan shafin intanet na manyan harsunan Afrika; an bude ne a halin yanzu, ko nan gaba ne za'a bude? In dai an bude, yaya adreshin wanan shafin take? Ka huta lafiya. Daga Abdullahi Zaria.

Malam Abdullah, a halin yanzu akwai shafukan Intanet da ke dauke cikin manyan harsunan Afirka ai, irinsu Suwahili da Hausa da sauransu. In har kana bukata, bayanai kawai za ka nema masu alaka da harshen da kake so, za ka samu. Ban san adireshin wani shafin Intanet na harshen Suwahili ba, amma akwai na harshen Hausa tinjin a Intanet. Da fatan ka gamsu.

Salam Baban Sadik, Ina tambaya ne kan duk lokacin da zan kalli wani launin hoto mai motsi wato bidiyo, sai a nuna min cewa sai na yi downloading din adobe flashplayer kuma ko da nayi hakan ba na samun damar ganin bidiyo din. Yaya zan yi? Allah ya kara lafiya. Maikudi marafa sagagi. aleemarafa@yahoo.com

Abin da ke faruwa shi ne, duk wani abin da za ka iya mu'amala da shi a Intanet ta hanyar wayar salularka, akwai wani manhaja ko masarrafa da aka tanada masa. Idan wannan masarrafar bata samu ba, babu yadda za a yi ka iya mu'amala da shi. Shi "Adobe flash player" 'yar karamar masarrafa ce da ke taimakawa wajen kallon hotuna masu motsi, watau bidiyo, idan ba ka da wannan masarrafa, ba za ka iya ba. Idan kuma kana da masarrafar, dole sai da ma'adanar bayanai mai dan girma a wayar, watau "Storage", kamar "Memory Card", ko ya zama wayar tana da ma'adana mai dan yawa. Domin a duk sadda ka budo wani bidiyo za ka kalla, wayar za ta saukar maka dashi ne cikin ma'adanarta kafin ka fara kallo, in kuma babu isasshen ma'adana, ka ga akwai matsala kenan. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, barkan ka da war haka. Da fatan kana lafiya, Allah Yasa haka, amin. Na kanyi lilo (Browsing) ta opera a wayata 'kirar Nokia. Amma da zarar na fara, wani lokaci sai ya fidda min wasu kalamai kamar haka: "Application Erro: Out of Memory Error. Java/Lang/OutOfMemoryError" Daga karshe sai wayar ta sake kunna kanta. Shin hakan me yake nufi ne? Kuma ko akwai wata hanyar da za'abi a magance aukuwar hakan? Wassalam. Daga Uncle Bash Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com, 07037133338.

A gaida Uncle Bash namu. Watau matsalar da wayar ke fuskanta dai shi ne rashin isasshen ma'adanar sarrafa bayanai, watau "Memory" kenan. Sai ka duba, akwai tabbacin wayar an cike ta da bayanai na sauti ko bidiyo, ta yadda ta makare, babu sauran wurin numfashi a gare ta. Idan haka ta kasance, dole ta kashe kanta don ta sake farfadowa ko za ta samu wurin numfasawa. Watau galibin na'urorin sadarwa suna da ma'adanai guda biyu ne. Akwai babbar ma'adana, wacce ke dauke da babbar manhajarta, watau Hard Disk kenan, ko kuma ROM (Read Only Memory). Amfanin wannan ma'adanar shi ne taskance dukkan manhajoji da masarrafan da na'urar ke amfani da su, a mace. Sai ma'adana ta biyu, wacce ake kira RAM (Random Access Memory), wadda ke aikin adana masarrafai ko manhajojin da aka kunna kuma ake mu'amala da su. Misali, idan ka kunna wayar salularka, da zarar ka budo menu a misali, sai bayanan su taso daga ROM zuwa RAM. Ma'adanar RAM kamar farfajiya ce ko falo, inda duk masarrafan da aka kira su suke zama, a gama abin da ake yi da su, sannan su koma inda suka fito su kwanta. To idan kwamfuta ce, ba ta da matsala sosai, domin kowanne cikin ma'adanan nan guda biyu yana da nashi bangare. Amma a wayar salula, ma'adana guda daya ce ake gutsira ta. Idan ka shake wayar salularka da hotuna da bidiyo da wakokinsu Mai Asharalle a misali, sai ta kasa samun wurin da za ta ajiye wasu manhajojin idan ka kira su kana son yin amfani da su. Don haka, ka rage yawan bayanan da ka taskance a wayar, ko kuma ka kara mata ma'adana ta hanyar sanya mata "Memory Card." Da fatan Malam Bash ya gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, dan Allah meye alakar Bluetooth da USB Cable? Godiya muke. Daga Salisu Nagaidan Jama'are: 08063461480

Malam Salisu ai babu wata alaka a tsakaninsu sai alakar kasancewa hanyoyin shigar da bayanai ne su ko hanyar mikawa, zuwa wayar salula ko kwamfuta. Ita fasahar Bluetooth tana aiki ne da tsarin sadarwa ta wayar iska, watau "Wireless Communication System," a yayin da Wayar USB kuma ke amfani aikawa da sakon bayanai ta hanyar damfaruwa a jikin wayar salula ko kwamfutar da ke aikawa ko karba. Da fatan an gamsu.

No comments:

Post a Comment