Fannoni
Ilmi wani abu ne mai fadi, ta duk yadda ka so kayyade shi da wani bangare nasa, sai ka ga hakan ba ya yiwuwa ta dadi. Abin nufi a nan shi ne, duk da cewa ilmi nau'i-nau'i ne, amma galibi za ka ga akwai alaka tsakanin nau'ukan, musamman kan ilmin da ya shafi sana'a da kere-kere. Idan muka koma kan ilmin addini ma haka za mu gani; akwai bagaren tauhidi, da bangaren fikihu, da bangaren hadisi da dai sauransu. Amma a karshe idan ka dunkule su duka, sai ka ga suna komawa ne ga ilmin tauhidi ko ibada ga Allah, domin shi ne abin da yake asali kan alaka tsakanin wanda ya sanar da ilimin, watau Allah, da kuma wadanda ake son su yi bautar, watau dan adam da aljan kenan. To haka sauran nau'ukan ilmi su ma suke.
Binciken da masana suka yi ko suke kan yi a yanzu, daga karnonin baya zuwa cikin karnin da muke ciki, sun taimaka wajen kacalcala ilmi zuwa bangare bangare, iya gwargwadon wayewa da zamanin da ake ciki. Wannan tasa idan muka dubi tasirin binciken da masana magabata suka yi a baya, zuwa na yau, za mu ga sun karkasu ne zuwa fannoni kamar; fannin likitanci ko kiwon lafiya, da fannin sararin samaniya, da fannin lissafi, da fannin sarrafa bayanai, da fannin zane-zane (na gidaje, ko na'urori, ko garuruwa), da fannin safara – kamar mota, da keke, da babur, da injina, da jiragen sama, da jiragen kasa – da fannin sadarwa – kamar na tarho, da fas, da talabijin, da rediyo,da tauraron dan adam, da yanayin sadarwa. Wadannan a takaice, su ne shahararu cikin fannonin ilmin da za mu kawo masanan da suka yi bincike mai zurfi a cikinsu, ko suka yi sanadiyyar gano su, ko kuma suka habaka su.
Asali da Akidu
Sau tari, abin da ya fi komai tasiri wajen ilmi da karantar da shi, shi ne akida ko asalin wanda ya yi bincike ko ya karantar da ilmin. Wannan a fili yake. Duk malamin da ya karantar da kai wani nau'in ilmi, to, akwai tabbacin akidarsa na iya tasiri wajen nau'in abin da ya karantar da kai. Na kawo wannan bayani ne don in nuna mana cewa, dukkan fannonin ilmi da muke karantawa ko karantarwa a yanzu, akwai tasirin akidun masanan da suka yi bincike a cikinsu tun asalin zamunnan baya.Hakan ya faru ne saboda bambancin akidun addini da rayuwar masanan da bayanin tairihin rayuwarsu zai zo nan gaba, kamar yadda taken kasidar take nunawa.
Kamar yadda wasunmu suka sani ne, akwai musulmai daga cikinsu, wadanda su ne asali wajen assasa turban galibin nau'ukan ilmin kimiyya da fasahar kere-kere, da bangaren ilmin likitanci, da fannin ilmin sararin samaniya, a zamanin farko. Wadanda suka biyo bayansu galibi ba musulmai bane, musamman wadanda suka yi binciken ilmi kan harkar kimiyya da kere-kere bayan rushewar daular musulunci da ke Andalus a lokutan baya. Wasunsu kiristoci ne, wasu yahudawa, wasu kuma maguzawa ne, irinsu Charles Darwin, wanda ake tinkaho da bincikensa kan fannin Ilmin Halittu, da asalin halittu (watau Evolution) da dai sauransu – duk da cewa ya gina wannan nau'in ilmi ne a bisa akidarsa ta maguzanci da rashin yarda da mahalicci. Don yana nuna cewa dukkan halittu suna samuwa ne daga dabi'a da tsawon zamani, babu wanda ke samar da su, kuma da zarar sun gama zamaninsu suka mutu, wasu za su maye musu, shikenan haka rayuwa za ta ci gaba da gudanuwa. Wannan akida ce ta wasu nau'ukan maguzawa da Malam Musulunci ke kira "Dahariyyah", kamar yadda wasu ayoyin Kur'ani suka yi ishara. Wanda kuma hatta a kasar Amurka ma akwai masana da yawa da suke sukar wannan sakamakon binciken ilmi. A takaice dai, masana nau'ukan ilmi sun karkasu ne zuwa gida hudu; da musulmai, da kiristoci, da yahudawa, da kuma maguzawa. Haka na da muhimmanci ne wajen fahimtar nau'ukan ilmin da muke karantawa a halin yanzu da wadanda muka karanta a baya.
Tsarin Asali da Samuwa
Kamar yadda bayanai suka gabata a baya kuma kamar yadda muka sani, asalin kowane ilmi dai daga Allah ne, amma yana sanar da shi, ta hanyar ilhama ga wasu daga cikin bayinsa, wadanda ya hore musu kwazo da fahimta da juriyar bincike; musulmi ne ko wadanda ba musulmi ba. Daga cikin masana akwai wadanda ake danganta wa asali wajen samuwar nau'ukan ilmi. Ire-iren wadannan su ne wadanda asalin binciken fannin ilmi ke komawa zuwa gare su. Bayan haka, akwai wadanda su kuma habbaka fannin suka yi, ta hanyar fadada bincike cikin wani bangare ko kan asalin binciken farko. Sannan akwai wadanda suka kirkiri wasu fannoni ko bangarori cikin wani fanni na ilmi. Misali, a fannin ilmin sararin samaniya (watau Astronomy) akwai wadanda suka yi bincike kan taurari, wasu kan Wata, wasu kan Rana, wasu kuma kan tsari da rayuwar taurari. Sannan akwai wadanda suka yi bincike kan na'urorin da ke taimakawa wajen hango taurari, da wata, da rana, da ma dukkan buraguzan da ke shawagi a cikin falaki. Wannan ke sa a samu bangarori daban-daban cikin wani fannin ilmi guda daya. Kamar a fannin ilmin lissafi misali, akwai wadanda suka yi bincike kan tsarin lissafi. Akwai wadadna suka yi kan ka'idojin lissafi (watau Scientific or Mathematical Formulas). Akwai wadanda suka yi bincike kan alakar fannin lissafi da ilmin kere-kere. Akwai wadanda suka yi kan agajin fannin lissafi ga ilmin kwamfuta. Akwai wadanda suka yi kan fannin lissafi da bangaren likitanci, da dai sauransu. Wannan na daga cikin dalilan da suka haddasa yaduwar ilmi sosai, har ya game duniya, musamman dai kasashen da ke da hakkin habbaka shi a wannan zamani.
Tasirin Ilmin Kimiyya a Rayuwar Yau
Tasirin ilmin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere a rayuwarmu ta yau yana da gamewa ainun. Tasirin ya kasu ne kashi biyu; akwai tasiri mai kyau – kamar ci gaban rayuwa a bangaren kasuwanci, da daukan ilmi, da karantar da shi, da bangaren kiwon lafiya, da sadarwa, da safara, da yada bayanai da sadar dasu, da bangaren kere-kere. A takaice dai, a iya cewa an samu ci gaba, kuma ana kara samun haka a halin yanzu, musamman a kasashe masu tasowa. A daya bangaren kuma akwai munanan tasiri da yaduwar ilmin ke haddasawa a duniya, musamman dai a kasashen da ke alfaharin ci gaba a wannan fanni.
Wadannan munanan tasiri dai suna da gamewa, kuma daga inda ake yinsu, suna yada tasirinsu ga sauran al'ummomin da ke sauran kasashe musamman masu tasowa. Manufar ilmi shi ne ya shiryar da wanda ke dauke dashi, ya sada shi da Ubangijinsa, ya inganta masa rayuwarsa, ya kuma haskaka masa rayuwarsa baki daya ta kowane bangare. Amma a yau idan muka dubi kasasen Turai da Amurka, da sauran nahiyoyin da ake ganin sun ci gaba, za mu ga kamar sun fi mu tabarbarewa wajen rashin ingancin rayuwa, da rashin sanin alkiblar rayuwa, da rashin alaka a tsakaninsu da mahaliccinsu, da kuma rashin kwanciyar hankali cikin al'ummar ma gaba daya.
Idan muka yi la'akari da alkalumar bayanai da ke fitowa daga kasashe irin su Amurka, da Turai, da Rasha, da nahiyar Asiya – irinsu Jafan da sauransu – za mu ga cewa lallai akwai matsala cikin rayuwarsu; a matsayin daidaikun mutane ne ko jama'a gaba daya. Tabbas idan ka je kasashen za ka ga ko ina tsaf-tsaf, babu kwatami, babu bola ko ina kamar yadda ake gani a kasahenmu a yanzu, sannan ga asibitoci, ga ababen safara ta ko ina, ga tsarin tafiyar da al'umma mai kayatarwa, sannan kuma duk inda za ka je za ka samu wanda zai maka jagora; ko dai wani jami'in tsaro, ko wani ma'aikaci, ko kuma rubutu ko wani zanen taswira da zai maka jagora zuwa inda za ka je. Rayuwa kam za ka ganta tsaf-tsaf. Amma ruhin jama'a, da dabi'unsu, duk akwai matsala galibi, saboda rashin tasirin ilmi a zukatansu.
Wannan tasa za ka ga yawan sakin aure ya fi yawa a kasar Amurka, ga yawan zinace-zinace da gidan karuwai da 'yan luwadi, ga yawan sace-sace, ga tabarbarewar tarbiyyar yara. Ina cikin rubuta wannan kasida muke karanta labarin wani yaro dan shekaru goma da iyayensa suka lallabe shi da ya rika share dakin kwanansa da kansa, za su rika bashi fan 10 a duk wata. Dakinsa ne, amma sai sun biya shi kafin ya share. Yana cikin sharewa rannan sai ya yanke a yatsar hannunsa. Ya gaya wa iyayensa sai basu yi komai a kai ba, sai ya kaisu kotu, cewa; ya yanke yatsa amma basu nuna damuwarsu ba, don haka alkali ya kwatan masa hakkinsa! Wannan ba zai taba faruwa a nahiyarmu ba, sai in aron al'adu da akidunsu muka yi. To a takaice dai, maimakon a ce rayuwar zuci da bayyane ta gyaru sanadiyyar yawaitan ilmi, sai ya zama rayuwar bayyane ce kadai ta zama tsaf-tsaf, amma zuciyar al'umma a cike take da kaskanci da damuwa. Yawan kisan gilla, da kashe kai, da sace yara, da satar motoci, da rashin tausayi, sun yawaita a dukkan kasashen da suka shahara a fannin ci gaban kimiyya da kere-kere. To duk mene ne dalilin samuwar wadannan abubuwa, bayan ilmi ya wanzu?
Babbar matsalar da ke tattare da ilmin zamani ko na boko kamar yadda muke cewa, shi ne rashin tarbiyya ta addini, da rashin alaka tsakanin mai karatun ilmin da mahaliccinsa. Da kuma kokarin karantar dashi don samun duniya kadai. Duk sadda mutum ya bambance tsakanin rayuwa da addini, to, halin da zai samu kansa a ciki kenan. A turai da Amurka da sauran kasashe makamantansu, ba ruwan gwamnati da addini, duk tsare-tsaren gwamnati daban suke, haka kuma addini. Babu wanda zai damu da addini sai mai yinsa ko wanda ya yarda da addinin. Don haka hatta a makarantu ba a karantar da tarbiyya mai kama da wani addini, sai dai a karantar da kai abin da "ya kamata" ka sifatu da shi a matsayinka na dan adam, don ka bambanta da dabba. Wannan kuwa ba karamin matsala bane. Domin za a wayi gari ga ilmin ga komai, amma ba dabi'a, ba tawakkali, ba sanin ya kamata, balle addini.
Haka idan muka yi la'akari da tsarin ilminmu a kasar nan da sauran kasashe masu tasowa, haka yake; bai damu da addini ba. Duk da cewa akwai bangaren karatun addini a sakandare da firamare, amma idan ka duba za ka ga ba wani damuwa aka yi da su ba. Shi yasa duk wanda ya yi karatun boko zalla ba tare da karantar addini ba, rayuwar sai ta zama kamar ta bature. Komai yana kiyasta shi ne da hankali, ba da addini ko dokar Ubangiji ba. Shi yasa a Turai daga cikin ka'idar likitanci a wajensu, idan mara lafiya ya ji cutar da yake fama da ita ta gundure shi, yana iya gaya wa likita ya bashi dama, don ya ba da izini a kashe shi kawai, "ya huta," a riyawarsu. Wannan shi ake kira "Mercy Killing." Rashin addini ne ya kawo haka. In ba haka ba me zai sa a ce wanda aka karantar da shi don ya ceci ran jama'a kuma zai taimaka wajen salwantar da ita? Don haka, babbar matsalar da ke damun wadannan al'ummomi kenan; rashin tarbiyyar addini a rayuwarsu. Ba ruwansu da Allah, balle bin dokokinsa. Shi yasa duk yawan ilminsu, sai zuciyarsu ta zama cikin kunci, da tashin hankali, fiye da na wadda yake jahili ko yake zama a al'ummar da ke rayuwa cikin tsarin addini.
Mafita
Mafita na cikin daukan ilmi tare da imani. Sanin mahalicci da yarda da dokokinsa. Yarda da cewa dukkan ilmi daga Allah yake. Yarda da cewa babu banbanci tsakanin ayyukan mutum a kasuwa, da asibiti, da ofis, da rayuwar yake ta addini. Dukkan wannan kuwa zai samu ne idan aka cakuda dukkan wani nau'in ilmin zamani da tarbiyyar addini.
Cikin watan da ya gabata ne daya daga cikin makarantun sakandare masu zaman kansu a Abuja ta gayyace ni da in gabatar wa dalibanta jawabi na musamman kan alakar tarbiyyar addini da karatun zamani. Mai wannan makaranta ba musulma bace, abin mamaki. Sannan shugaban makarantar wani dan kasar Gana ne, kuma shi ya kawo wannan shawara cewa, ya kamata a rika shigar da addini cikin lamurran karatu. Wannan jawabi da na gabatar da kayatar sosai, cikin yardar Allah. Na kuma kawo wa daliban misalai daga kasashen turai, wadanda rayuwarsu ta tabarbare, duk da tutiyar ilmi da suke yi. Don haka sai mu dage; duk ilmin da kake koyo, ka shigar da tarbiyyar addini a ciki. Da wannan za ka yi ilmi biyu; ga abin da ka karanta, sannan ga alaka mai kyau tsakaninka da mahaliccinka.
Wannan gabatarwa ce muka yi, zuwa mako mai zuwa muna nan tafe da tarihin masana. Da fatan za a kasance tare da mu.
No comments:
Post a Comment