Wata Sabuwar Duniya
Lokacin da shahararriyar marubuciyar nan mai suna Francis Caincross ta yi hasashen cewa, nan da wasu 'yan shekaru, tsarin kimiyyar sadarwa ta zamani a duniya zai bunkasa, ya mamaye duniya, har ya yi tasiri wajen canza tsarin shugabanci a duniya, da yawa cikin masu karatu ko masu lura da al'amuran duniya basu zaci abin na iya faruwa cikin gaggawa kamar yadda al'amura ke faruwa a yanzu ba. Ta yi wannan hasashe ne a cikin littafinta mai suna The Death of Distance, cikin shekarar 1998; shekaru goma sha biyu kenan a yau. Haka ma hasashen da tsohon Shugaban Kamfanin Microsoft watau Bill Gates yayi cikin littafinsa mai suna The Road Ahead, kan gagarumin tasirin fasahar Intanet da gamayyar hanyayoyin sadarwar zamani, watau Network Convergence. Shi kuma nasa hasashen a shekarar 1995 yayi, kuma kusan dukkan abin da yayi hasashe ya tabbata, kusan fiye da yadda ake zato ma. Tabbatuwar abubuwan da wadannan mutane suka yi hasashensu ba ya nuna cewa wai sun san gaibi ne, a a. Kwarewa ce da suka yi kan harkar, sai Allah ya basu ma'auni don yin gejin abin da ke faruwa, sannan suka fitar da wani hukunci na wucin-gadi kan abin da ake tsammanin zai iya kasancewa nan gaba. Kuma ga su suna kasancewa.
Masu karatu, a yau zamu yi tsokaci ne kan yadda hanyar sadarwar zamani, watau Information Communications Technologies, da kuma gamayya ko tsarin zumunci tsakanin kayayyakin sadarwar zamani, watau Network Convergence ke yin tasiri wajen sauya tsarin tattalin arzikin kasa, da kuma siyasar wasu kasashe, musamman abin da ya faru a kasar Masar, da Tunisiya, da wadanda ke faruwa a wasu kasashe, sannan mu yi waiwaye – abin da Bahaushe ke kira adon tafiya – don tuno abin da ya faru a wasu kasashe masu alaka ko kama da wanda ya faru ko yake faruwa a kasashen larabawa a yau.
Wasu Misalai
Kafin wannan lokaci da muke ciki, galibin shugabannin kasashe a duniya gaba daya, ba wai kasashen larabawa kadai ba, sun fahimta, tare da hankaltar tasirin da kayayyakin sadarwar zamani – irin Intanet, da wayar salula, da Imel, da sababbin hanyoyin taskance bayanai da yada su da kuma mu'amala da su – don haka suka fara kokarin sanya musu takunkumi, da yumke su, musamman a cikin kasashensu. Kamar yadda mai karatu ya karanta a kasidun da muka gabatar masu take: Yadda Kasashe Ke Sanya Wa Fasahar Intanet Takunkumi, duk wata kasa mai da'awar rajin kare 'yancin dan Adam a yau, idan ka bi diddiginta za ka samu a baya ta yi wani yunkuri wajen dakushe hanyoyin sadarwa a kasarta don hana bayyanar tasirin wannan hanya, saboda cinma wasu burace-buracen siyasa. Daga kasar Amurka, zuwa Ingila, da Faransa, da Kanada, da Ostiraliya, da Rasha, da Jamus, da Sin, da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya, duk harkar daya ce. A kasashenmu na Afirka ba a cika samun wannan matsala ba sosai, idan ka kebe kasashen da suka ci gaba irin su kasar Masar, da Tunisiya, da Aljeriya, da Maroko, wadanda suna da sanayya fiye da sauran kasashen Afirka kan tasirin wadannan hanyoyin sadarwa. Wadannan kasashe suna iya kokarinsu ne wajen ganin sun dakushe wadannan hanyoyin sadarwa ba don komai ba, sai don karyata hasashen mummunar tasirinsu da aka yi a baya. To amma, bakin alkalami ya riga ya bushe.
Duk mun san abin da gwamnatin kasar Bama (Myanmar ko Burma) ta yi don hana sauran kasashen duniya sanin halin da kasar ke ciki a lokacin da Sojoji suka yi juyin mulki, ba da dadewa ba sai aka yi girgizar kasa a kasar, mai muni. Hukumar kasar ta hana 'yan jaridu musamman na kasashen yamma shiga kasar balle su ruwaito wa duniya halin da ake ciki. In ka kebe wakilan Al-Jazeera, babu wanda aka bari ya shiga kasar. Daga nan kuma suka sa aka toshe kafar sadarwa ta Intanet. Don haka ko ka shiga kasar a matsayin mai yawon bude ido (watau Tourist) da niyyar bayan ka shiga ka rikide, ba za ka samu hanyar sadarwa ta Intanet ba, balle ka aika wa kamfanin da kake wakilta labarai kan halin da ake ciki. To amma duk wannan bai hana a samu bayanai ba na hakika, ta hanyar wayar salula. Bayan haka, hukumar kare 'yancin dan adam, watau Human Rights Watch ta samar da wata kafa ta yada bayanai da take amfani da ita ta hanyar ma'adanar Flash Drive. Inda jami'anta ke taskance bayanai – na bidiyo, ko sauti, ko rubuce-rubuce - ta wannan ma'adana, a sawwara su da yawa, sannan a fita da su daga kasar.
Irin wannan har wa yau ya faru a kasar Kuba (Cuba) da ke gabashin Amurka. Gwamnati ce ke da iko da dukkan hanyoyin sadarwa a kasar. Akwai Intanet tabbas, amma ba kowane gidan yanar sadarwa za ka iya shiga ba. Ita ma da irin wancan hanya ta amfani da ma'adanar flash drive ake shigar da bayanai da kuma fitar da su. A wasu lokuta kuma a sawwara su ta hanyar amfani da wayar salula, sannan a aika da su zuwa ga 'yan uwa da abokan arziki da ke wasu kasashen. Bayan wannan, kasar Iran ma na daga cikin kasashen da ta yi fice wajen wannan kokari na dakushe hanyoyin sadarwa. Lokacin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu da suka gabata haka abin ya faru, ya zama ba a iya mu'amala da fasahar Intanet, sai ta wayar salula ake ta aiwatar da sadarwa a tsakanin mutanen kasar da sauran wadanda ke waje. Wannan ya samo asali ne sanadiyyar toshe kafar sadarwa da hukumar kasar ta yi, saboda zanga-zanga da jam'iyyun hamayya suka ta yi, tare da daliban jami'a da sauran jama'ar gari.
Haka a kasar Tunisiya, wadda ita ce kasa ta farko a wannan karni da hanyoyin kimiyyar sadarwar zamani suka yi tasiri matuka wajen taimaka wa al'ummar kasar neman 'yancinsu karfi da yaji. Bayan makonni da al'ummar kasar suka kwashe suna ta zanga-zanga a fadin kasar baki daya, a karshe dai gwamnatin kasar ta samu matsin lamba daga waje har cikin kasar cewa lokaci ya yi da za ta san na yi. Wannan kuma shi ne abin da ya faru a karshe; shugaban kasar ya gudu, aka nada gwamnatin wucin-gadi don gyatta al'amura.
Yin wannan ke da wuya, sai mutanen kasar Masar su ma suka ga cewa ai duk jirgi daya ne ya kwaso su da mutanen kasar Tunisiya. Matsalar kasar Masar ta samo asali ne tun shekaru talatin da suka gabata, ba matsalar yau bace. Kimiyyar sadarwar zamani dai ta zama sila ce wajen kawo sauyi, amma ba samuwarta bane ya haddasa wannan juyin juya halin ba. Duk da haka, da yawa cikin masana suna ganin cewa wannan hanya ta taimaka gaya wajen samar da sauyin da aka samu. Bayan toshe hanyar sadarwar Intanet da hukuma ta yi, rana guda da fara wancan zanga-zanga, sai sauran jama'a suka fara amfani da wayoyin salularsu suna daukan hotuna da bidiyo da sautin hirarraki don sanar da sauran kasashen duniya halin da suke ciki. Bayan wadannan hanyoyi, tashar talabijin ta Al-Jazeera ma ta taimaka gaya wajen wannan aiki. Wannan tasa a farkon lamari hukumar kasar Masar ta hana wannan tasha sakat. Ta rika yada jita-jita cewa tashar Al-Jazeera ce ke kokarin haddasa fitina a kasar, ba wai mutanen kasar bane ke son sauyi a bisa karan-kansu. Nan take suka toshe ofishin Al-Jazeera da ke birnin Al-Qahira, sannan suka fara kama jami'an tashar, suna tuhumarsu. A karshe dai abin da hukumar kasar ke tsoro shi ne abin da ya faru; an kayar da ita har kasa warwas!
Ganin abin da ya faru a kasar Masar ke da wuya sai jama'ar da ke sauran kasashen Larabawa – irinsu Libiya, da Jodan, da Bahrain, da Iran, da Aljeriya da sauran makamantansu – suka fara zanga-zanga su ma. Sabanin sauran lokuta inda hukumomi ke toshe hanyar sadarwar Intanet kadai, ko wasu gidajen yanar sadarwa irin su Facebook da Twitter, a wannan karo an wayi gari hatta tsari da yanayin sadarwar wayar salula ma toshe shi ake yi. Kasar da wannan al'amari ya fi kamari ita ce kasar Libiya, inda bayanai ta hanyar hotunan bidiyo na wayar salula da hotuna da sautin bayanai suka tabbatar da cewa an kashe mutane sama da dari biyu cikin kasa da mako guda. A kasar Libiya a halin yanzu ba ka-safai ake samun hanyar sadarwa cikin sauki ba. Gidajen yanar sadarwa kuwa ba ka iya amfani da su; musamman wadanda ake ganin ta cikinsu ake yada labarai da bayanai kan abin da ke faruwa a kasar. Kafafen yada labarai na gwamnati kuma ba su nuna hakikanin abin da ke faruwa, sai dai su yi ta nuna tarurrukan da masu goyon bayan shugaban kasar ke yi don nuna goyon bayansu gare shi. Wannan ta sa gidan yanar sadarwa ta Google ta bullo da sabuwar hanyar yada bayai ta hanyar wasu lambobin wayar salula mai suna Talk-to-Tweet. Wannan hanya ce da ke amfani da muryar mai kira, don taskance abin da yake fada a rubuce nan take. Ma'ana, idan ka kira lambobin, sai ka fadi duk abin da kake son fada, ko ka bayar da labarin halin da ake ciki; kana fada, na'urar na rubuce abin da kake fada, kuma nan take za a dora dukkan bayanan a Intanet. Wadannan dai, a takaice, suna cikin kalubalen da ke fuskantar shugabannin kasashen duniya, wadanda ke bin tsarin Dimokuradiyya, da masu bin tsarin shugabanci irin na gado ko mulkiya.
Tasirin Kimiyyar Sadarwa ta Zamani
Yana da kyau mai karatu ya san cewa, tasirin wadannan kayayyakin sadarwar zamani na takaituwa ne cikin dalilai ko al'amura guda uku. Abu na farko shi ne saukin mu'amala. Wannan wata ka'ida ce wadda dukkan kayayyakin sadarwar zamani suke sifatuwa da ita. Lokacin da wayoyin salula suka fara bayyana, da yawa cikin mutane suna ganin kamar ba za su iya mu'amala ko amfani da su ba. Amma yau da gobe ta ki wasa. Don haka, da wadannan kayayyakin sadarwa suka fara yawaita, sai farashinsu ya sauko, mutane da yawa suka ci gaba da saya, kuma nan take sai aka saba mu'amala da su. Shi yasa ma da yawa cikin masu mu'amala da wayar salula ko wadanda suka saba amfani da kwamfuta duk za ka ga sun iya taskance bayanai; ko dai na bidiyo, ko na sauti, ko kuma hotuna da suke daukawa da dai sauransu.
Abu na biyu kuma shi ne game duniya. Wadannan kayayyakin sadarwa sun game duniya a yanzu, kuma akwai gamammiyar tsarin sadarwa har wa yau da ke hade tsakaninsu. Don haka, sabanin yadda al'amura suke a baya, a yanzu mai wayar salula na iya sauraron shiryen-shiryen gidajen rediyo, da na talabijin, da kuma mu'amala da fasahar Intanet, duk ta wayarsa. Wannan gamayya ce ke samar da wani gamammen tsarin zumunci a tsakanin su kansu kayayyakin sadarwar, watau Network Convergence kenan a Turance. Wannan tsari ne kuma ke hada alaka ko zumunci a tsakanin mutane a duk inda suke a duniya, kuma wannan shi ne abu na uku. Don haka ba abin mamaki bane ganin yadda duniya gaba daya hankalinta ya koma kan kasar Masar a lokutan baya, ko kasar Libiya a halin yanzu, misali. Duk da cewa ba wadannan hanyoyin sadarwa bane ke aiwatar da wadannan zanga-zanga, amma su ne masu rura wutar matsin da ake samu a wadannan kasashe; na cikin gida ko matsin da ke zuwa daga waje.
Bayan haka, a yayin da galibin mutane musamman ma shugabannin kasashe ke ganin kimiyyar sadarwar zamani a matsayin wani makami da za su iya amfani da shi wajen sanar da masu jefa kuri'a ko neman kurku da shi don ci gaban manufofinsu na siyasa, a daya bangaren kuma dole ne su san cewa duk abin da suka yi bayan sun dare karagar mulki – mai kyau ko mara kyau – da wadannan hanyoyin sadarwa ana iya sanar wa duniya abin da suka yi, sannan, in ma ta kama, a karshe a tumbuke su; suna ji suna gani. Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta….!
No comments:
Post a Comment