Laraba, Oktoba 5, 2011
Marigayi Steve Jobs |
Ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba ne dai
tsohon shugaban kamfanin Apple Inc.,
watau Steve Jobs, ya kwanta dama, makonni shida da mika ragamar shugabancin
kamfanin. Jobs dai ya rasu ne bayan fama
da yayi da mummunar cutar sankara da ake kira Pancreatic Cancer, na tsawon shekaru bakwai. Kafin rasuwarsa dai ana kirga shi daga cikin
mutanen da suka yi tasiri mafi girma a duniya wajen habbaka harkar sadarwa da
kere-kere, musamman kan wayar salula, da kwamfuta, da na’urorin sadarwa nau’uka
daban-daban, da allon shigar da bayanai na kwamfuta (Keyboard), da lasifika da dai sauransu. An kiyasta cewa Jobs ya mallaki hakkin
mallaka (Patents) kan kirkirarrun kayayyakin fasahar sadarwa har wajen
338. Shi ne ya kafa kamfanin Appl Inc. da kamfanin NeXT Computer (kamfanin da ya kera kwamfutar
da aka fara amfani da ita wajen kirkira da mu’amala da fasahar Intanet), da
kuma kamfanin Pixar & Disney. Jobs ya shahara a fannin sadarwa a duniya,
don haka duniya ta dauka a ranar rasuwarsa – daga shugabannin kasashe zuwa ‘yan
makaranta. Daga cikin shahararrun kirkire-kirkirensa, akwai na'urar sauraren
wakoki mai suna iPod da dukkan nau'ukanta – irinsu iPod Classic, da
iPod Nano, da kuma iPhod Touch – da kwamfutar Mac da
dukkan nau'ukanta – irinsu Macbook Air, da Macbook Pro – da wayar
salula nau'in iPhone da dukkan nau'ukanta – irinsu iPhone, da iPhone
3G, da iPhone 3GS, da iPhone 4G, da kuma iPhone 4S, wadda
ake gab da fitarwa kafin mutuwarsa – sai kuma shahararriyar na'urar
sarrafa bayanan nan mai suna iPad. Kafin
rasuwarsa, Jobs na da shekaru 56 a duniya, kuma ya mallaki tsaban kudi da
kadara – dala na gugan dala – har wajen dalar Amurka biliyan takwas
($8billion), watau kusan Tiriliyon daya da biliyan dari uku da goma shabiyu
kenan (N1.312 tr) a nairan Najeriya. A halin yanzu ga fassarar shahararriyar jawabin
nan da ya taba yi wa daliban Jami’ar
Stanford, daya daga cikin jami’o’i masu kima a duniya, ranar bikin yaye
dalibai a shekarar 2005. A sha karatu lafiya:
.......................................................
“Rayuwarku ‘Yan Kwanaki Ne Takaitattu...”
“Ina matukar farin cikin kasancewa tare da ku a wannan rana da ake bikin
yaye ku daga daya daga cikin Jami’o’i masu nagarta a duniya. Ni kam ban samu damar gama Jami’a ba a
rayuwata. A hakikanin gaskiya ma dai,
wannan shi ne lokacin da yafi kusantar da ni da bikin yaye dalibai a
jami’a. A yau zan baku wasu labarai ne
guda uku daga tarihin rayuwata. Su kenan.
Babu wani dogon bayani. Labarai uku ne kacal.
Labarin farko dai waiwaye ne, abin da masu iya magana kan kira
"Adon tafiya."
Na yanke shawarar gujewa daga Jami’ar Reeds ne watanni shida bayan fara karatu. Amma sai na tsaya a makarantar ina rabe-rabe
tsakanin darussa, har na tsawon watanni goma shatakwas, kafin a karshe dai na
gudu. To me yasa na kasa gama karatuna?
Dalilin dai ya samo asali ne tun kafin a haife ni. Mahaifiyata wata budurwa ce dalibar Jami’a,
wacce bayan ta dauki cikina, a karshe ta yanke shawarar bayar da ni ga wasu
ma’aurata bayan ta haife ni. Ita dai
tana ganin lallai ya kamata a ce ta bayar da ni ne ga wadanda suka yi karatu,
don haka, haihuwata ke da wuya sai ga wani Lauya da matarsa sun zo, don sa
hannu kan takardar yarjejeniyar karba ta a matsayin dansu. To amma da suka duba suka ga namiji ne, sai
suka fasa, domin su mace suke so. Daga
nan sai aka mika ni ga iyaye na (na yanzu), wadanda a lokacin suke jira, tunda
wadancan ba su son namiji. Cikin
tsakiyar dare aka bugo musu waya ana tambayarsu: "Mun samu da namiji, duk
da cewa ba namiji muke tsammani ba; kuna bukatarsa?" Sai nan take suka ce: "Sosai kuwa." Sai bayan an mika ni ne daga baya asalin
mahaifiyata ta gano cewa ashe wanda ya karbe ni bai gama Jami’a ba, matarsa ma
ko sakandare bata gama ba. Wannan yasa
mahaifiyata ta ki sa hannu a kan takardar yarjejeniyar da aka rubuta. Sai da aka yi ta mata magiya, da alkawarin
cewa za a sa ni a makaranta har sai na gama, sannan ta sa hannu kan
yarjejeniyar.
Haka kuwa aka yi. Bayan na
cika shekaru 17 aka sa ni a Jami’a. To
amma sai nayi ragon azanci na zabi Jami’a mai dan karen tsada, irin Jami’ar Stanford, inda aka wayi gari duk
albashin iyayena yana karewa ne wajen biyan kudin makarantar. Bayan tsawon watanni shida sai na ga wannan
tsari bai da wata fa’ida. Ni dai ban da
wani tunani kan yadda zan tafiyar da rayuwata nan gaba, balle tunanin yadda
karatun Jami’a zai iya taimaka mini cinma burina a rayuwa. Amma ga shi duk dan abin da iyaye na ke samu
na albashi na karewa wajen karatun. Don
haka na yanke shawarar fita daga makarantar, ina mai yakinin cewa lallai komai
zai daidaita a karshe. Wannan shawara da
na dauka mai matukar hadari ce a lokacin, amma ta la'akari da abin da ya biyo
baya, a halin yanzu ina iya cewa ita ce shawara mafi muhimmanci da na taba
yankewa a rayuwata. Da na yanke shawarar
barin Jami'ar, sai na daina halartar dukkan darussa, sai wadanda nake da
sha'awa a kai kadai.
Lamarin dai ba yadda aka so ba.
Domin ko dakin kwana ba ni da shi a Jami'ar; a kasa nake kwanciya a
dakin abokai. Sannan sai na je aike nake
samun dan taro da kwabon da zan sayi abin da zan sa a bakin salati. Kuma sai na yi tafiyar tazarar mil 7 a duk
ranar lahadi nake samun abinci mai dadi a Hare Karishna. Na ji dadin hakan. Domin galibin abubuwan da na koya sanadiyyar kwazo
da neman sani, a karshe sun fa'idantar da rayuwata baki daya. Bari in baku wani misali:
A lokacin nan, Jami'ar Reeds ce kadai ke da kwararrun
malamai masu karantar da darasi kan Fasahar Zane (Calligraphy) a duk
fadin kasar nan (Amurka). Duk wani hoto
mai kayatarwa, duk wani taswira da zane da ka gani a manne a jikin kujerun
dalibai ko a jikin gine-ginen Jami'ar, to, da hannu aka zana shi. To, ganin cewa na yi niyyar barin Jami'ar
gaba daya, kuma ba dole bane in halarci dukkan darussa, sai kawai na yanke
shawarar lazimtar darasin koyon ilmin Fasahar Zane (Calligraphy) kadai,
don samun kwarewa a wannan fanni. Na
koyi yadda ake zana haruffan Sans Seriff – daya daga cikin haruffan
rubutu a kwamfuta - da dukkan nau'ukansa, da nau'ukan tazarar da ake so
tsakanin hadakar haruffa a zane, da kuma dukkan hikimar da ake bukata wajen
tsara rubutu ya kayatar. Wannan abu yana
da ban sha'awa ainun; cike da tarihi, da fasaha mai kyatarwa, irin kayatarwar
da kimiyyar zamani ba ta iya bayarwa. Hatta ni kaina abin ya birge ni sosai.
Duk da wannan kwarewa da na samu, ban taba tunanin watarana zan
kwatanta abin da na koya a aikace ba.
Amma shekaru goma da suka gabata, sadda muke tsara sabuwar kwamfutarmu
ta farko nau'in Macintosh, sai wannan ilmin Fasahar Zane (Calligraphy)
da na koya a Jami'ar Reeds ya halarto ni. Kuma nan take muka yi amfani da wannan ilmin Fasahar
Zanen haruffa muka shigar da haruffa masu kayatarwa cikin Mac. Don haka, ita ce kwamfutar farko da ta zo
da haruffa masu kayatarwa. To, da a ce
ban lazimci darussan koyon wannan fasahar ba a Jami'a, da wannan sabuwar
kwamfuta ta Mac bata samu wadannan haruffa masu kayatarwa tare da tsarin
tazara tsakanin haruffa ba, ko kadan.
Kuma musamman ganin cewa manhajar Windows ta kwaikwayi Mac ne
wajen tsarin haruffa, kenan da ba don samuwarsu a cikin Mac ba, da babu
wata kwamfuta a duniya da za ta mallake su.
Da a ce ban yanke shawarar barin Jami'a ba a lokacin, da ba zan taba
tunanin barin sauran darussa ba balle har in lazimci darasin koyon Fasahar Zanen
nan kadai. Kuma da abin da wannan ke
nufi shi ne: kwamfutoci ba za su samu wadannan haruffa masu kayatarwa ba kamar
yadda suke da su a yau. Tabbas, sadda
nake Jami'a nake ta wannan bundun-dundun, ban taba zaton hakan zai iya faruwa
nan gaba ba, ko kadan. Amma a halin
yanzu a bayyane yake, duk sadda na kalli rayuwata shekarun goma baya.
Har wa yau, ya kamata ku san cewa ba za ku taba iya fahimtar ci
gaban rayuwarku ba idan kuna kallon me za ku yi nan gaba. Za ku fahimci hakan ne kawai idan kuka kalli
rayuwar da kuka yi a baya. Don haka,
dole ne ku tabbatar wa zuciyarku cewa nan gaba rayuwa za ta yi kyau. Ya kamata ku zama masu yakini kan wani abu –
kwazonku ne, ko kaddara, ko rayuwa, kai ko ma mene ne. Wannan tsarin tafiyar da rayuwa da na dauka
bai taba kai ni ya baro ba, kuma shi ne abin da yayi tasiri mafi girma a
rayuwata.
Labarina na biyu kan soyayya ne da rashi.
Na ci sa'a – don na koyi abin da na fi sha'awar yi tun da
kuruciyata. Ni da Woz mun kafa kamfanin Apple ne a garejin gidanmu,
lokacin ina dan shekaru 20 a duniya. Mun
yi aiki tukuru ta yadda bayan shekaru 10, kamfanin Apple da ya faro da
mutum biyu kacal a gareji, sai ga shi ya kasaita zuwa kamfanin da kimarsa ta
kai dalar Amurka biliyan biyu ($2billion), da ma'aikata sama da mutum 4000! Daidai wannan lokaci muka fitar da hajarmu ta
farko mai kayatarwa, watau kwamfutar Macintosh, kuma daidai lokacin ne
har wa wa yau na cika shekaru 30 a duniya.
Ana cikin haka sai aka kore ni daga kamfanin! Babban magana! Ta yaya za
a yi a kore ka daga kamfanin da kai ka kafa shi? Watau abin da ya faru shi ne, lokacin da
kamfanin Apple ya fara habaka, sai muka yi hayan wani bawan Allah da
nake da yakinin yana da kwarewar da zai iya taimaka mini wajen tafiyar da
kamfanin. Shekara daya bayan zuwansa
komai ya tafi daidai. Amma daga lokacin
da mahangarmu kan tafiyar da kamfanin ta fara shan bamban da juna, sai sabani
ya shigo. Da haka ta faru, sai manyan
daraktocin kamfanin suka goyi bayan ra'ayoyinsa. Don haka ina cika shekaru 30 na fice daga
kamfanin. Kuma ficewa ce wacce ta yadu
ko ina. Nan take na rasa duk alkiblar
rayuwar kuruciyata baki daya. Wannan abu
ya dagula mini lissafi matuka.
Har aka samu wasu watanni ban san me ya kamata in fuskanta ba. Sai naji na fara zargin kaina kan rashin
karfin halin rike nauyin shugabancin da aka dora mini, wanda kuma sa'o'ina suka
damka a hannu na (sadda nake kamfanin Apple). Nan take na hadu da David Packard da Bob
Noyce, inda na yi kokarin basu hakuri kan wannan abin da nayi (na barin
kamfanin Apple). Na gaza matuka,
inda har a karshe na yi tunanin barin kasar ma baki daya. To amma sai wani
tunani ya fara shigo mini – ai har yanzu ina sha'awar abin da nayi (a baya). Abin da ya faru a kamfanin Apple (na
korar da aka mini) bai canza son da nake wa sana'ata ba. Tabbas an kore ni, amma har yanzu ina
sha'awar sana'ata. Don haka na sake
gwada wani kokarin.
Duk da cewa ban ji dadin abin
da aka mini ba, amma daga baya na gano cewa, korar da aka mini daga kamfanin Apple
alheri ne ga rayuwata. Domin
dawainiyar da ke kaina a wancan lokaci na shugabanci, yanzu ya sauka. Na kuma samu sauki, inda na faro komai daga
farko – cikin rashin tabbacin zan dace ko bazan dace ba. Wannan ne ya bani damar shiga wata sabuwar
marhala a rayuwata da ke cike da kwazo da hikimar kirkire-kirkire; babu nauyin
kowa a kaina.
Bayan shekaru biyar da wannan kora ne na kafa kamfani mai suna NeXT,
da wani kamfanin mai suna Pixar, kuma ana cikin haka na hadu da wata
baiwar Allah mai ban al'ajabi da a karshe muka yi zaman aure da tare. Ta hanyar kamfanin Pixar ne aka fitar
da wani fim da aka yi, ta amfani da Fasahar Zanen Kwamfuta (Computer
Animation) mai take: Toy Story, wanda shi ne na farkon irinsa a
duniya. Kuma wannan kamfani na Pixar ne
ya tsere sa'o'insa wajen shahara da cin nasara a wannan fanni a duniya. Abin mamaki, ana cikin haka kuma sai kamfanin
Apple ya sayi wannan kamfani na NeXT da na kafa. Wannan shi ne abin da ya dawo da ni kamfanin
a karo na biyu, kuma fasahar da muka samar a kamfanin NeXT ta zama
ita ce kashin bayan ci gaban kamfanin Apple kamar yadda kuke gani a yau. Daga nan kuma na auri Laurene, muka ci gaba
da rayuwa mai armashi.
Na tabbata da ba a kore ni daga kamfanin Apple ba a farkon
lamari, da babu ko daya daga cikin wadannan ci gaba da za su riske ni. Dandanon magani bai da dadi ko kadan, amma na
tabbata shi ne abin da mara lafiya ya fi bukata. Wasu lokuta rayuwa kan dake ka da guduma.
Idan haka ya faru, duk kada ka yanke kauna da rayuwa. Na gamsu cewa lallai abin da ya taimaka mini
wajen tafiyar da rayuwa shi ne, ina sha'awar abin da nake yi (na aiki). Don haka, wajibi ne ku lazimci abin da kuka
fi sha'awan yi a rayuwa. Kuma wannan shi
ne abin da ya kamata ta bangaren aikin yi, da alakarku da masoyanku. Domin aiki
shi ne abin da zai ci kaso mafi yawa na rayuwarku, kuma hanyar da za ku bi
kadai don samun gamsuwa a rayuwa ita ce ta yin abin da kuka fi sha'awa. In har baku samu abin da kuka fi sha'awan yi
ba a rayuwarku yanzu, to, ku ci gaba da nema.
Kuma, kamar alaka ce tsakanin masoya, duk sadda shekaru suka yi nisa,
tana kara armashi ne. Don haka ku ci gaba da bincike har sai kun samu abin da
kuka fi sha'awan yi. Kada ku yarda da
wani abin da ba wannan ba.
Labarina na uku a kan mutuwa ne.
Lokacin da nake dan shekaru 17, na taba karanta wani zance mai kamar
haka: "In har a kullum kana riya cewa ba za ka kai karshen yinin da ka samu kanka a ciki ba, to, da sannu watarana
tunaninka zai zama gaskiya." Wannan zance yayi tasiri matuka a ruhi na,
kuma sama da shekaru 33 da suka shige, duk safiya idan na kalli fuskata a
madubi nakan tambayi kaina: "A kaddara wannan shi ne yinina na karshe a
duniya, shin, zan so in ci gaba da yin abin da na kuduri aniyar yi a yau?"
Daga sadda na ci gaba da baiwa kaina amsar wannan tambaya da cewa, "A a,"
iya tsawon kwanakin da na yi ta yi wa kaina tambayar, daga nan na fahimci
lallai ya kamata in canja wani abu a rayuwata.
Tunanin cewa lallai nan ba da dadewa ba zan iya mutuwa, shi ne
muhimmin abin da na taba cin karo da shi, wanda kuma ya taimaka mini wajen tantace
duk wani abin da zan yi a rayuwata. Duk
wani abu mara kima a rayuwa – kamar burace-buracen zuci, da girman kai, da
tsoron abin kunya, ko tsoron rashin cin nasara – da zarar an ambaci mutuwa, nan
take duk sai su gushe. Ba abin da zai saura sai muhimman al'amuran rayuwa. Yawan tuna cewa nan gaba za ka mutu, a iya
tunanina, shi ne kadai abin da zai sa ka kauce daga fadawa tarkon yawan damuwa
da wata hasara ta dukiya da kake tsoro. Ba ka da wata mafaka. In kuwa haka ne, ba ka da wani dalilin da zai
hana ka bin shawara kan abin da zai fisshe ka.
Kimanin shekara daya da ta wuce (2004) aka tabbatar mini cewa na
kamu da cutar sankara mafi muni (Pancreatic Cancer). Da misalin karfe
7:30 na safiya aka dauki hoton ciki na, inda a karshe aka gano ina da wannan
cuta ta sankara. Ban ma taba sanin me
ake nufi da wannan bangaren ciki da ake kira Pancreas ba. Nan take
likitoci suka sanar da ni cewa, wata irin nau'in cutar sankara ce wacce ba ta
da magani, kuma nan gaba ba zan wuce tsawon watanni shida ba a duniya. Daga nan
dai likita ya shawarce ni da in koma gida "in gyatta al'amura na." Wanda hakan, a kaikaice, hannunka mai sanda ne
da likitoci ke yi wa mara lafiya cewa, ka je ka shirya wa zuwan mutuwa kawai. Abin
da wannan ke nufi shi ne ka je ka sanar da iyalinka duk abin da ka san ya
kamata su sani daga nan zuwa shekaru 10, a tsawon 'yan watannin da ke
tafe. Hakan na nufi ne har wa yau, cewa
ka tabbatar da cewa komai ka gama kintsa shi, don sawwake wa iyalinki duk wata
matsala da ka iya tasowa bayan mutuwa. A takaice dai, ka je ka musu wasiyya da bankwana!
Da tunanin wannan cuta dai na yini tsawon wannan rana. Can dai zuwa
yamma, sai aka zo aka tsakuro samfurin wannan cuta daga ciki na. An yi hakan ne
kuwa ta hanyar tsofa na'urar hango cuta a ciki (Endoscope) wacce ke
dauke da wani dan karamin allura, ta bi ta makogwaro da ciki da hanji, har ta
karasa inda mikin ciki yake (Pancreas), ta tsukuro kwayoyin halitta (Cells)
daga cutar da ta tsiro a jiki. A lokacin
an mini allurar bacci, amma mai dakina tana wurin, kuma tace daidai lokacin da
aka fito da wannan samfurin cuta, da aka sa shi karkashin na'urar hangen nesa,
sai duk likitocin suka kama kwalla saboda murna. Domin ya bayyana musu cewa wannan nau'in cutar
sankara ce ta musamman da ake iya warkar da ita ta hanyar tiyata. Tuni har an
mini tiyatan, kuma a halin yanzu na samu sauki.
Wannan shi ne lokacin da na samu kaina mafi kusanci da mutuwa, kuma
ina fatan wannan lamari ya kusantar da ni zuwa wasu shekaru masu yawa nan gaba. Bayan na wuce wannan marhala ta rayuwa, a
yanzu ne zan iya sanar da ku wani zancen da a baya ba zan iya gaya muku shi ba,
saboda rashin fahimtar mutuwa hakikatan. (Ga sako na gare ku):
Babu mai son ya mutu. Hatta
wadanda ke ganin sun yi aikin kwarai ba su cikan son su mutu ba, sai dole. Amma kuma babu makawa, mutuwa ce masaukin da
za ta tattaro mu duka. Babu wanda ya
taba guje wa mutuwa a baya. Kuma haka
lamarin ya kamata ya zama. Domin mutuwa ce abin da har zuwa yau duniya bata
taba samar da irinta ba. Ita ce abin da
ke kawo canji a rayuwa. Ita ce ke share
tsohuwar al'umma don kawo sabuwa. A
halin yanzu da nake muku wannan jawabi, ku ne sabuwar al'umma, amma nan ba da
dadewa ba, watarana za ku zama tsohuwar al'umma, a share ku don kawo wata
sabuwar. Ku mini afuwa idan wannan zance
nawa ya firgita ku, amma wannan ita ce hakikanin gaskiya.
Rayuwarku 'yan kwanaki ne takaitattu, don haka kada ku shagala
wajen kwaikwayon rayuwar wani. Kada ku
zama 'yan abi yarima a sha kidi. Kada ku
yarda surutan wasu su hana ku bin shawarar da za ta fisshe ku a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne, ku zama masu
juriya wajen bin abin da zai zama maslaha a rayuwarku da fahimtarku. Domin su ne kadai suka fi kowa sanin abin da
kuke son ku zama. Duk wani abin da ba
wannan ba, to, ya zo a bayanshi.
Lokacin da nake dan karami akwai wata mujalla mai kayatarwa da ake
kira: Whole Earth Catalog, wadda mujalla ce da kusan kowa yayi amanna da
ita. Wanda ya fara buga wannan mujalla
kuwa wani bawan Allah me mai suna Stewart Brand, wanda ke unguwar Menlo Park
da ke nan kusa da ku. Ya kuma
kayatar da mujallar ne ta hanyar kwarewarsa ta adabin turanci da yake da ita. Wannan lamari ya faru ne tun wajajen shekarun
1960, kafin bayyanar kwamfutoci da tsarin buga mujallu na zamani kenan. Don
haka mujallar gaba dayanta ana buga ta ne ta hanyar amfani da keken rubutu (Typewriter)
na wancan zamani, da almakashi (wajen rage tsawon shafukan), da kuma
na'urar daukan hoto irin ta da (Polaroid Camera). Wannan mujalla dai kamar wata shafin
gidan yanar sadarwar Google ce da aka buga a shafukan takarda, saboda
fa'idojin da take dauke dasu. Duk da
cewa shekaru 35 kenan kafin bayyanar Google, amma mujallar a cike take da
nau'ukan ilmi da fadakarwa, kwatankwacin yadda gidan yanar sadarwar Google take
a yau.
Stewart, tare da abokan aikinsa dai sun buga wannan mujalla na
tsawon lokaci, bayan wasu 'yan lokuta kuma sai aka neme ta aka rasa. Amma kafin nan, sun yi bugu na karshe daidai shekarar
1974 – sannan ina matashi kamarku. A
shafin karshe daga baya, akwai wani hoto mai kayatarwa na wani titi da aka
dauki hotonsa da safe – irin yanayin da wasunku za su so su taka a cikinsa don watayawa.
A karkashin wannan hoto akwai wani karin zance da ke cewa: "Ka zama mai
yunwar ilmi. Ka zama mai budaddiyar zuciya." Wannan shi ne sakon bankwana
da suka sa a shafin karshe na mujallar, kafin su daina buga ta gaba daya. Ka zama mai yunwar ilmi. Ka zama mai
budaddiyar zuciya. Kuma a kullum
nakan yi wa kaina wannan fata. Don haka
na ga dacewar yi muku wannan fata ku ma, a daidai wannan lokaci da kuke kokarin
fara wata sabuwar rayuwa, bayan barin Jami'a, cewa:
Ku zama masu yunwar ilmi a kullum. Ku zama masu budaddiyar zuciya
wajen karbar fahimta.
Na gode matuka."
No comments:
Post a Comment