A yau kuma ga mu dauke da wasu daga cikin tambayoyinku da kuka aiko ta wayar salula da hanyar Imel. Kamar yadda na sha sanarwa dai, duk tambayar da na riga na amsa ta a lokacin da aka aiko ban cika kawo su ba. Sai in na ga akwai wata fa'ida mai gamewa ga sauran masu karatu. Domin wasu kan rubuto tambaya su ce in bamu amsar ta wayar salularsu ko adireshin Imel dinsu, kada in jira sai lokacin amsa tambayoyi a shafin jaridar. Wasu kuma tambayoyinsu na bukatar amsa ne nan take, saboda irin matsalar da ke dauke cikin tambayar, wacce ke bukatar a warwareta nan take. Allah mana jagora, amin. Har wa yau ina mana murnar samun kanmu cikin wannan wata na Ramalana mai tarin albarka. Allah karbi ayyukanmu, ya kuma mu samu tsira daga tabewar duniya da azabar lahira. Don Allah, duk abin da za ka fada, ka fadi alheri. Duk abin da za ka aikata, ka aikata alheri. Duk abin da za ka rubuta, ka rubuta alheri. Da wannan, sai ka samu tsira a rayuwarka ta duniya da lahira baki daya.
……………………………………………………
Salam Malam Abdullahi (baban Sadiq) yaya aiki? Allah ya ba da sa'a. Don Allah kayi min karin bayani a kan "2GO". Na gode: Aminu Sadauki U/dosa kaduna.
Malam Aminu, "2go" dai tsarin sadarwa ne na "ga-ni-ga-ka", watau "real time chatting", wanda ke baiwa masu amfani da shi damar aiwatar da sadarwa kai tsaye, a lokacin da suke yi, ta wayar salula. Wannan tsari bai da bambanci da tsarin hirar kai tsaye da muke da su a Intanet ta hanyar kwamfuta. Bambancinsu kawai shi ne ta hanyoyin da ake aiwatar da su. Yana da kyau ka san cewa wannan tsari yana da amfani, sannan yana da cutarwa. Amfaninsa shi ne za ka samu saduwa da jama'a, a yi zumunci. Rashin amfaninsa kuma shi ne cinye lokaci, ko bata lokaci musamman kan hiran da babu fa'ida tattare da shi. Sai a rika lura da tsawon lokacin da ake kashewa da kuma abin da ake fada a ciki. Allah mana jagora.
Assalamu alaikum, ina fata Baban Sadik ya tashi lafiya. Wato malam akwai ranar da na yi wani rubutu a wannan jarida ta mu aminiya mai farin jini inda har na aika da adireshin Imail di na. To a wannan lokacin wani bawan allah ya kira ni yana tambayana akan yaya zai rika shiga shafukan sada zumunta irinsu facebook da twitter daga wayarsa? To, sai naga akwai bukatar malam yayi bayanin yadda ake saduwa da yan uwa cikin shafukan. Daga Kabeer, Rikkos, jos 07066574843
Malam Kabeer ai bayani kan haka ya sha maimaituwa a wannan shafi. Sai dai wani sabon abu idan ya samu, ko wasu matsaloli da mutum zai fuskanta, a taimaka masa. Amma dangane da abin da ya shafi budewa da mu'amala, sai dai kari. Mun gode da wannan fadakarwa.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, ya aiki? Ina da waya nokia kirar x2-00 ko zan iya aikawa da sakon Imel in kuma karba da ita? Daga Mukhtar Musa Jirgwai
Malam Mukhtar lallai za ka iya, domin wayar Nokia X2-00 na da wadannan ka'idojin sadarwa da za su iya taimaka maka yin hakan. Sai dai ya kamata ka san cewa akwai hanyoyi guda biyu na yin hakan. Akwai tsarin manhajar Imel da wayoyin nokia ke zuwa da ita, wacce ke bukatar sai ka shigar da wasu bayanai da suka shafi adireshinka, da kalmomin shiga da kuma tsarin ka'idar karban sakon imel din da kamfanin imel dinka ke amfani da shi, watau "Email Protocol" kenan (irinsu POP3, da IMAP, da kuma SMTP). Wannan tsari na da wuyan sha'ani idan baka san su ba. Hanya ta biyu ita ce ka bude shafin intanet don shiga akwatin imel dinka. Wannan shi ne gama-gari wanda yafi sauki.
Assalamu alaikum, Baban sadik, muna yi maka fatan alkhairi. Ya Allah muna rokonka ka biya wa bawanka Baban sadik bukatunsa na alkhairi, kamar yadda yake biya muna bukatunmu na kwamfuta da fatam Allah ya kara yawaita muna ire irenku a duniya amin. Tambaya ta a yau itace: ina yin anfani da wayar salula, Nokia E71-1(42) ina son a yi min karin bayani kan yadda zanyi nayi rijistar "Video Call", saboda idan nasa lambar ba ya yi, sai in ga ''Video Call is not supported by network'', Daga sunusi NNPC
Malam Sanusi, lallai Baban Sadik na godiya da wadannan addu'o'i. Allah ya saka da alheri amin. Abin da ya shafi tsarin kira ta hanyar bidiyo a wayar salula, ya shafi tsari ne na kamfanin waya, watau "Network Service." Kowane kamfanin waya kuma yana da tsarinsa dangane da abin da ya shafe shi. Wasu kan tafiyar da tsarin, ma'ana su samar da shi, ta yadda za ka iya kiran wani kuna hira kana kallonsa yana kallonka idan akwai tsarin a wayarsa. Wasu kamfanonin kuma su kashe tsarin. Duk dai wannan ya danganci kamfanin waya. A baya na san kamfanin MTN na da tsarin, domin akwai wadanda ke kira na dashi daga cikin masu karatu da ke jihar Legas. Amma yanzu ban sani ba. Don haka ta yiwu sun kashe tsarin, ko kuma ka je ofishin kamfanin wayarka ka musu bayani, watakil za su gamsar da kai kan haka. Da fatan za a yi hakuri da dan bayanin da ya samu.
Assalamu alaikum Baban Sadik. Bayan gaisuwa ina yi maka fatan alheri da taya ka farin ciki saboda baiwan da Allah ya yi maka, kuma ga shi mutane na amfana da bayanai da kake musu. To Alhamdu lillahi. Ni ma wani lokaci zan aiko da nawa tambayar. Daga Abdullahi Muh'd anguwar Jabba S. G. Zaria
Malam Abdullah mun gode da addu'o'inku, wallahi muna farin ciki da ganin cewa dan abin da muke yi yana tasiri, ba don kowa ba sai don Allah. Allah ya sa mu cikin sahun masu amfanar jama'a cikin dukkan lamuransu, amin. Sai mun ga naka tambayoyin, kuma Allah bamu ikon amsawa, amin.
Assalamu alaikum. Don Allah Baban Sadik ka turo mini da bayanan nan da ka taba yi akan wayoyin BlackBerry ta wannan adireshin Imail din (musulmi5952@yahoo.com). Dalibinka: Abubakar U. Muhammad
Malam Abubakar sai ka duba jakar Imel dinka. Da fatan za a gamsu da dan abin da ya samu. Mun gode sosai.
Gaisuwa ga Baban Sadiq. Ina matukar karuwa da wannan shafi naka. Allah ya taimaka, ya kara basira. Nabude jakar Imail ne ina so in rika karbar sakonni ta wayata Nokia E51. Idan na shiga Retrieve email, na sa "ID" da "Password" na tura, sai ta dowo min da sakon cewa "you are sending…accept it this time or permanently", idan na duba ta lntanet zan ga inbox di na. To ta yaya zan seta in rika karbar sako ta wayata? Sannan abu na biyu shi ne irin bidiyoyin da ake sa wa a shafukan Intanet ta youtube, idan na kunna sai ta ce "kana da matsalar real player, shiga nan ka sabunta ko kuma close an active one first" Dan Allah ina so a yi min bayanin hanyar da zan warware matsalata. Allah yai jagoranci amin.Daga Abba A.S Kano
To, Malam Abba, da farko dai, akwai alamar ko dai baka gama saita tsarin Imel dinka ba, ko kuma akwai matakan da suka kamata ka bi kafin kaiwa zuwa ga jakar Imel din, wanda ba ka isa zuwa garesu. Ban sani ba, shin, kana amfani da tsarin Imail da ke jikin wayar ne ko ta "browser" kake shiga? In tsarin Imel din waya ne, ya kamata a duk sadda aka maka tambayar farko, ka ce "accept permanently", wannan zai sa duk sadda ka tashi shiga, ba za a kara turo maka wadannan tambayoyi ba. Hanya ce ta tantance tsarin shiga wani shafi mai dauke da tsaro irin na bayanai. Matsalar bidiyo kuma wannan matsala da kake samu na nuna cewa lallai masarrafar "Real Player" da ke wayarka ta tsufa, kuma ba za ta iya aiwatar da aikinta ba a shafin Youtube. Domin wayar Nokia E51 tsohuwar waya ce, idan aka yi la'akari da yadda al'amura ke sabuntuwa ko caccanzawa a duniyar sadarwa. Sai ka je shafinsu a http://www.real.co.uk, don ka sauko da sabon zubin, ka loda wa wayarka. Da fatan an gamsu.
Aminci ya tabbata ga Baban sadiq, ina fatan kana cikin koshin lafiya. Ina rokon Allah ya kara basira. Don Allah kayi min karin bayani kan yadda zan yi rijista a imel? Godiya nake Daga Aliyu mai sa a T/wada zaria 08033760456
Malam Aliyu hakika Baban Sadik na godiya da addu'o'in da ake ta yarfo masa. Dangane da abin da ya shafi bude Imel, sai ka je gidan yanar yahoo da ke http://mail.yahoo.com, kada ka haruffan "www", domin a gidan yanar shafin yake. Idan shafin ya budo, a kasa daga hannun dama za ka ga inda aka rubuta "Sign Up" sai ka matsa, za a budo maka fom da za ka cika, sai ka aika musu. Daga nan za ka iya aiwatar da sadarwa ta hanyar Imel. Ka lura, ba kowace wayar salula ke iya bayar da damar yin rajistar Imel ba, idan ba irin su Blackberry bane. Don haka nake bayar da shawarar zuwa "Cyber Café" a yi rajista ta kwamfuta, don haka ya fi sauki. Da fatan an gamsu.
Assalamu Alaikum Baban Sadik, na ga amsar tambayar da ka bayar game da zanen hannu. To tambayata a nan ita ce: tunda zanen hannun kowa daban yake, ba mutun biyu masu zanen hannu iri daya, yaya sakanin hannun dama da na hagu na mutun daya, daidai suke ko su ma daban-daban suke? Muhammad Ibrahim Kaduna
Malam Muhammad ai wannan tambaya ce mai sauki, kana iya gano amsar da kanka. Amma tunda har ka rubuto, amsar ita ce su ma akwai bambanci a tsakaninsu. Ka duba yatsun hannayenka ka gani, za ka tabbatar da hakan. Da fatan an gamsu.
Baban Sadik ina maka fatan alheri, Allah ya saka maka da gidan aljanna bisa gwagwarmayar da kakeyi, muna godiya. Don Allah me ye ma'anar "USB Cable?" Kuma wanda bai san kan kwamfuta ba yana son mu'amala da Intanet ta waya, ya zai yi? Kuma ya za a yi a san waya mai intanet? Kuma za a iya bude imel din da aka rufe yanzu? Harira Said BK KD.
Malama Harira barka da warhaka, da fatan ana lafiya. Ma'anar "USB" dai a takaice shi ne tsarin shigar da bayanai ga kwamfuta ko na'urar sadarwa ta hanya mafi sauki. Cikakken lafazin haruffan USB shi ne: "Universal Serial Bus." Duk kwamfutar da ke dauke da wannan tsari na USB, akwai wayar da ake shigar mata don aiwatar da sadarwa ta wannan tsari. Wannan waya ita ake kira "USB Cable." Ba kwamfuta kadai ba, hatta wayoyin salula suna da wannan tsari mai tasiri. Bayan haka, wannan tsari shi ya fi saurin sanar da kwamfuta ko na'urar sadarwa cewa "ga wasu bayanai nan da ake son shigar miki ko karba daga gareki, don haka ki shirya." Da zarar an tsofa wa kwamfuta wannan waya, nan take yake zarcewa cikin kwakwalwarta ba bata lokaci. Bayan haka, mu'amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ba ya bukatar kwarewa a fannin kwamfuta. Abin da ake bukata mafi karanci shi ne mutum ya iya rubutu da karatu, sai a koya masa yadda zai yi. Hakan ba zai yi a rubuce ba sai a aikace. Sannan ana iya gane wayar salula na dauke da Intanet ne ta hanyar shiga "Menu", a can kasa za a ga alamar "Web", ko "Internet", wannan ke nuna cewa wayar tana dauke da tsarin Intanet. A karshe, ana iya bude ko farfado da akwatin Imel din da aka rufe, wannan shi ake kira "Reactivation of Account", kamar yadda ake farfado da taskar ajiya a banki idan aka dade ba a yi amfani da shi ba. Sai a shiga ta hanyar sanya adireshin Imel din da kalmomin iznin shiga watau "Password", da zarar an matsa enter, shafi zai budo da ke nuna cewa wannan akwatin Imel din an dakatar da shi, idan kana son farfado da shi ka matsa nan, a misali. Da zarar an matsa, nan take za a bude. Da fatan Malama Harira ta gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, barkanka da war haka. Da fatan kana lafiya. Baban sadiq a duba min madawwana da na bude mai wannan adireshi kamar haka: http://b-techcoms.blogspot.com. Shin, na bude ta kamar yadda ya dace? Ko akwai kurakurai? In akwai ta yaya zan gyara? Ina bukatan shawarwari ta yadda zan dada ingantata. Na gode, Allah Ya saka da alkhairi, Ya kuma dada basirah, amin. Wassalam! Daga Uncle Bash, Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com
Uncle Bash na shiga wannan shafi naka, kuma lallai ka yi kokari. Ai na dauka da harshen Hausa ne, ashe da yaren Ingila ne. To Allah taimaka, amin. Abin da na gani wanda ke bukatar gyara shi ne, ka cire bayanan da ka sa a karkashin sunan Mudawwanar, wanda na ga kamar taken kasidar da ka sa a shafin ne. Ba a nan ya kamata ka rubuta taken kasidar ba. Tunda har ka sanya taken a saman kasidar, ka cire wanda ke karkashin sunan Mudawwanarka. Sannan abu na biyu, ka cire adireshin Imel dinka daga jikin Mudawwanar, ka kura cire lambar wayarka. Domin 'yan dandatsa na iya amfani da wannan dama su rika turo maka sakonnin bogi, watau "Spam Mails", haka ma 'yan 419, suna iya daukan lambar wayarka su yi ta damunka. Kana iya cire su, ka je wajen "Settings" ka shigar da su. Duk mai neman Karin bayani kan saduwa da kai na iya zuwa can ya samu. Sannan idan ka zo zuba kasidu a shafinka, ka rika gyatta tsayuwansu, watau "Formatting", ka rika "Justify" din kasidun, wannan zai sa su samu diri mai kyau, ka gansu tsaf-tsaf, kuma rau-rau. Sannan ka lazimci nau'in "font" guda daya. Allah sa a dace, amin.
Assalaamu Alaikum Abban Saddiq, na ga wata ammsar da ka bayar, (Aminiya juma'a 10 ga yuni 2011) cewa sai mutum na da adireshin imel kafin ya samu damar ma'amala da dandalin facebook. To a yanzu an samu gyara; mutum zai iya amfani da lambar waya don bude dandalin facebook kamar kowa ka huta lafiya. Muh'd auwal kurna fagge kano.
Malam Auwal na gode da wannan fadakarwa. Alal hakika haka dama lamarin yake ga masu amfani da wayar salula musamman wajen aika sakonni zuwa shafukansu, ba daga baya bane suka samar da abin. Abin da yasa nake yawan ambaton cewa sai da adireshin Imel shi ne don galibi a kan shiga ne ta shafin facebook mai dauke da tsarin shafin kwamfuta, watau "Normal Mode," kuma a wannan tsarin, ana amfani ne da adireshin Imel, saboda idan ka bude, za su tura maka wasu kalmomi na sirri, wadanda za su bukaci ka sanya su idan ka sake dawowa don bude shafinka. Duk da haka wannan fadakarwa ce mai kyau da muhimmanci musamman ga wadanda basu sani ba. Mun gode.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, barkanka da aiki. Ina fatan kana lafiya, Allah Yasa haka, amin. Tambaya na shine: mutum zai iya saka manhajar kariya daga kwayar cutur 'kwamfuta (Anti-virus software) guda biyu, kamar Avast da AVG Anti-virus a 'kwamfuta daya suna aiki ba tare da wata matsala ba? Ko Kuma yin hakan zai iya kawo wa kwamfutar cikas wajen sarrafata? Wassalam. Daga Uncle Bash, Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com 08185292655
A gaida Uncle Bash na mu. Ai ba zai taba yiwuwa ka sanya wa kwamfuta masarrafar kariya guda biyu ba. Saboda kowanne daga cikin wadannan masarrafai yana da tsarinsa wajen kariya da ya sha bamban da na dan uwansa. Misali, manhajar kariya ta McAffe ta sha bamban da na AVG. Domin wasu bayanan da ba kwayoyin cuta bane, amma za ka ga wasu manhaojin suna nuna maka cewa "ka yi hankali, ga wani abokin gaba nan zuwa," misali. A taikaice dai, sanya wa kwamfuta manhajar kariya guda biyu ba abu bane mai fa'ida. Idan ka sa za su shiga, amma kuma ba za su yi aiki ba. Sannan kwamfutar za ta rika baka sanarwa cewa "akwai cin karo a tsakanin manhajojin kariyarka." Kamar dai mai gida ne ya dauko masu gadin gida guda biyu, daga wasu wurare daban-daban, da tare da kowannensu ya san wannan mai gadin wannan gidan bane. Ka ga duk sadda wannan ya hangi dan uwansa, zai dauka barawo ne, haka shi ma dayan. Don aiki daya ne suke yi, amma kowa da tsarinsa, kowa da irin ma'anar da yake baiwa "kwayar cutar kwamfuta" wacce ta sha bamban da fahimta ko tsarin dan uwansa. Da fatan Uncle Bash ya gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, ya sadik? Da fatan yana lafiya. Dan Allah mai yake sa yawan daukewar sabis? Ko kuma in kayi kira ga shi wayar a bude amma sai taki shiga?
Abin da ke kawo daukewan tsarin sadarwa, ko sabis kamar yadda kace, shi ne rashin ingancin tsarin sadarwar a inda ake, ko dai sanadiyyar matsalar na'urorin sadarwa daga kamfanin, ko sanadiyyar rashin yawaitar cibiyoyin na'urorin sadarwa a jiha ko bigiren da ake. Har wa yau akwai matsalar yanayi, da matsalar rashin ingancin wayar salula wajen jawo tsarin sadarwa. Wayoyin salula da kake gani kowacce na da tsarinta wajen inganci ko rashinsa, na abin da ya shafi jawo tsarin sadarwar, don taimaka wa mai kira aiwatar da kira ko karban kiran. A karshe, idan komai daidai yake, to yana da kyau har way au mu san cewa ana iya samun tsaiko wajen sadarwa saboda tsarin da ake amfani das hi wajen sadarwar wayar tarho, watau "Radio Waves", tsari ne da haka kawai yana iya daukewa, sannan ya dawo. Ya danganci bigire, da tsarin yanayi, da kuma na'urar sadarwa. Da fatan an gamsu.
Salam Baban Sadik, don Allah ya zan bude "Memory Card" di na; duk wayar da na sa sai ta tambayeni "enter password". Daga Haruna Hotoro 08035307128
Malam Haruna, samun wannan sako a duk sadda ka yi kokarin bude wannan kati naka, alama ce da ke nuna cewa an tsare ta da wasu kalmomin sirri. Idan sabuwa ce ka saya, kana da zabi; ko dai ka koma musu da ita su canza maka da wata, ko kuma ka matsa "Options" a jikin wayar idan ka zo inda tambarin katin yake, za ka ga inda aka rubuta "Format Memory Card", sai ka matsa. Da zarar ka matsa, za a sanar da kai cewa duk bayanan da ke ciki za su goge, za ka ci gaba? Sai ka ce eh. Nan take katin za ta koma sabuwa, babu komai a ciki, kuma ba za a kara tambayar ka shigar da "password" ba. Da fatan an gamsu.
Assalamu alaikum, suna na Umar Honestman, Numan, Jihar Adamawa. Baban Sadik don AllaH ina son ayi min bayani game da tauraron dan adam; ya yake? Kuma ya ake yi a turashi sararin samaniya da sauran abubuwan da yake tare da shi?
Malam Umar ai ka makara. Watakila lokacin da muka kawo kasidu na gugan kasidu har wajen uku ko hudu kan Tauraron Dan Adam, ba ka kusa. In da hali kana iya zuwa shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com, don neman kasidar da muka rubuta kan haka shekaru biyu da suka gabata. A ciki za ka samu cikakkun bayanai gamsassu dangane da wannan fasaha. Ayi hakuri da dan abin da ya samu. Na gode.
Babban sadik, yaya ake bude shafin facebook na kungiya? Ana kuma iya juyar da sakonni kan katin sim? Ka huta lafiya. A.w. Ayagi
Baban Waraqaat barka da warhaka. Bude shafin Kungiya a facebook ba shi da wahala. Ida ka shiga shafinka, ka je settings, ko ka duba daga hannun hagu can kasa, za ka ga inda aka rubuta "Create Group", sai ka matsa. Kana iya shigar da dukkan abokananka nan take. Saukar da sakonni zuwa katin SIM kuma ban fahimci tambayar ba sosai. Shin, sakonnin tes na wayar salula, ko sakonnin shafin facebook? In dai na wayar salula ne ai ba wahala wannan, kana iya amfani da masarrafar wayar. Idan Nokia ce kana iya amfani da "Nokia Suite" don saukar da su duka. Amma idan na facebook ne, sai dai ka adana (save) shafin da ke dauke da sakonnin zuwa cikin wayarka, don ka rika budewa a duk sadda kake so. Da fatan Baban Waraqaat ya gamsu.
Salam Baban Sadik, da fatan alkhairi. Dan Allah ina so kai min bayani kan yadda ruwan rijiya yake samuwa. Ka huta lafiya. Da Usman s/mainagge: 08020731981
Malam Usman ruwan rijiya na samuwa ne asali daga ruwan sama da ke saukowa. Idan ruwan sama ya sauka yakan kasu zuwa kashi uku ne a takaice; kashi na farko mutane da dabbobi su yi amfani dashi – mutane suna tara ne su sha ko yi harkokin gida da su, su kuma dabbobi su sha wanda ke taruwa a kududdufai da gulabe – kashi na biyu kuma ya jike kasa don ya shayar da shuke-shuke, su amfani da shi su ma, kashi na uku kuma ya shige can cikin kasa, shi ne wanda idan muka tashi hako rijiya muke samu. Sannan daga irin wannan kaso ne ake samun idaniyar ruwa da ke bubbuga ba tare da an hako ta ba. Akwai kashi na karshe wanda ruwa a saman tekuna da koguna a halin saukansa. Shi wannan kashi yana komawa ne ta hanyar iska, kamar yadda bayanai kan haka sun gabata tuni idan teku bai antayo shi cikin kasa ba kenan. Idan kana son fahimtar wannan tsari cikin sauki ka shiga cikin Suratuz Zumar aya ta 21, za ka ga abin cikin sauki, musamman idan ka karanta ko saurari tafsirin wannan aya daga kwararren malami. Wannan zai ba ka bayani kan asalin yadda lamarin yake, wanda shi ne asali kan dukkan bayanan da malaman kimiyya suka yi. Da fatan an gamsu.
Asslaamu alaikum. Ina son don Allah mallam ya aiko min kasida, akan banbamci da ke tsakanin ayyukan wayar Nokia da Blackberry. Ga addreshin e-mail na: bashariibrahimgumel@gmail.com
Malam Bashir na san za ka ga shiru, wai malam ya ci shirwa. A gaskiya babu wani bambanci na cancan nesa a tsakanin wayoyin biyu. Na san ka karanta kasidar da muka gabatar kan wayoyin salula nau'ukan Blackberry, da kuma kasidar da aka gabatar kan Ayyukan Wayar Salula. Bambancin da ke tsakaninsu kawai shahararru su ne kan tsarin gudanar da kira. Su wayoyin Blackberry idan ka buga lambar mutum don kiransa, sai ta cilla lambarsa zuwa na'urorin kamfanin wayar Blackberry da ke kasar Kanada, watau Research in Motion (RIM), daga nan kuma kamfanin ya cilla lambar zuwa kamfanin wayar da abokinka ke amfani da layinsu, sannan su kuma su nemo maka shi ta hanyar tsarin sadarwarsu, watau Network Service. Sai kuma bambancin masarrafai da ke tsakaninsu, wannan kuwa wani abu ne da hatta a tsakanin wayoyin salula na kamfanin Nokia akwai bambanci. Da fatan an gamsu da dan abin da ya samu.
Salam, dan Allah inaso ayi min cikakken bayani kan yadda ake amfani da "modem," da kuma yadda zan iya bude blog di na a shafin intanet. Dr. R. M. Haidar Kano
Malam Haidar, shi Modem, ko makalutun sadarwa, wata na'ura ce da ke taimakawa wajen sadar da kwamfuta ko wayar salula da shafukan Intanet da ke giza-gizan sadarwa ta duniya. Idan ka makala wa kwamfuta wannan na'ura, ka nemi isa zuwa wani shafin Intanet misali, za ta karbo maka shafin ne ta hanyar wayar R11 da ke makale a jikinta, watau irin wayar da ake aiwatar da sadarwar tarho da ita kenan. Da zarar ta debo bayanan shafukan a matsayin bayanai, sai ta narkar maka dasu a fuskar kwamfuta dinka a matsayin rubutu ko hotuna ko bidyo, kamar yadda suke a asalin shafin. A yanzu galibin kwamfutoci kan zo da wannan na'ura ne a cikinsu, ba wani abu bane da za ka iya gani a waje, musamman idan kana shiga shafin Intanet ta hanyar Gajeren Zangon Sadarwa watau Local Area Network. Amma idan na kamfanin waya ne ka siyo, to wannan kam dole sai ka makala wa kwamfutarka shi, don ka samu shiga. Sannan har wa yau kana iya amfani da wayar salularka idan kana da kwamfuta, wajen shiga Intanet. Sai ka dauko wayar shigar da bayanai da ta zo da shi, watau USB cable, ka makala mata. Kafin nan, dole ka tabbata akwai masarrafar wayar a kwamfutarka. Misali idan wayar Nokia ce, ka tabbata akwai masarrafar "Nokia Suite" a cikin kwamfutar. Ta nan za ka je ka matsa alamar "Connect to the Internet", don samun shiga. Bayani kan yadda ake kera Blog kuma ya sha maimaituwa a wannan shafi. Sai dai a yi hakuri a je shafinmu da ke Intanet don neman kasidar. Da fatan za a yi hakuri da dan abin da ya samu.
Salamu alaikum Baban Sadiq, da fatan an wuni lafiya? Allah yasa haka amin summa amin. Dan Allah ina son katemakamun namanta password na Imail di na. User ID: bbycopshon@yahoo.com, kuma da wannan ID ne nake facebook. Dan girman Allah inda yadda za a yi a taimaka min a gaya min yadda zan yi na samo, ko kuma a binciko min. Wassalam ka huta lafiya.
Malam Ibrahim kamar yadda muka yi Magana a waya, har Allah yasa aka shawo kan lamarin na gyara maka ba wata matsala, zuwa nan gaba duk sadda ka manta kalmomin shiganka na kamfanin masarrafar Imel, ba za ka iya shawo kan lamarin ba sai ka san shekarar haihuwarka da ka shigar a lokacin da kake bude Imel din a farko, da tambayoyi guda biyu da ka yi wa kanka sannan ka amsa su, da amsar tambayoyin, watau "Security Question and Answer." Duk sadda mutum ya mance kalmomin shigansa, sai ya matsa inda aka rubuta: "Forgot Your Password?" ya shiga, za a bijiro masa da wadannan tambayoyi guda uku, sai ya amsa su sannan a bashi daman canza wasu sababbin kalmomin shigansa. Suna yin haka ne don tsaro, da kuma tabbatar da cewa lallai kai ne mai akwatin Imel din, ba wai wani bane yake son ya kwace maka ta hanyar canza su. Da fatan an gamsu.
Salam, Baban Sadik tambaya ta ita ce: wai shin hasken walkiya ko cida suna da tasiri a kan irinsu janareto, da wayar salula, da talabijin, da dai sauransu? Allah ya kara maka basira ameen. Daga Abdulmajid Saleh Gumel(Abu sa'ad)
Baban Sa'adu lallai hasken walkiya da cida suna da wannan tasiri mai girman gaske kuwa a kan wadannan na'urori da ka ambata. Ba komai ya kawo haka ba sai don kasancewar su wadannan na'urori suna amfani da wasu hanyoyin sadarwa ne na musamman da suka shafi aikawa da sakonni ta hanyar iska da haske. Wadannan abubuwa guda biyu kuwa suna da tafarkinsu da suke bi ne a sararin saman duniyan da muke rayuwa a cikinta. Abin da ya shafi wayar salula da talabijin da na'urar tauraron dan adam (watau Decorder), da wayoyin wutar lantarki, duk suna karba ko aikawa da sakonnin makamashin sadarwa ne ta hanyar siginar rediyo, watau "Radio Waves," kuma duk wani abin da ya shigo tafarkin wannan tsarin sadarwa wanda ba jinsinsa bane, to yana yin tasiri mai girma a kanshi wajen jirkita shi ko canza masa amo da kima ko tsarin tafiya, tunda haske ne da ke cikin iska. Shi yasa idan ka kamo gidan rediyon Kaduna a misali sadda ake cida da walkiya, za ka ji tashar tana "cacacau…cacacau…kurrrrr," da dai sauransu. Alamar cewa an samu mishkila a tafarkin tsarin sadarwarta. Su kuma na'urorin tashoshin tauraron dan adam, watau Decorder, sukan kone ne idan aka yi tsawa mai tsanani a halin suna kunne, ko da ba aiki suke yi ba. Shi yasa yake da muhimmanci idan ana ruwa da tsawa, to ka kashe su, ka kashe rediyonka, in dai ba tashar FM kake sauraro ba, ka kuma kashe janaretonka, muddin ba wani abu mai muhimmanci kake yi ba. Duk da cewa idan ba tsawa bane mai tsanani, bai cika tasiri a kan janareto ba. Da fatan an gamsu.
Baban sadiq sannu da kokari, wai da gaske ne ruwan sama yana zuwa da kasa? Musa mohd, b-dogo yankaba kano.
Malam Musa ban taba jin wanann bayani ba, ban kuma taba karanta hakan a ilmance ba. Abin da na san ruwan sama kan zo da shi shi ne kankara, kamar yadda na san ka san wannan. Amma ruwan sama ya zo da kasa, wannan ban karanta ko ji shi a ilmance ba. Da fatan an gamsu.
Bayan gaisuwa, ina fatan kana lafiya. Ina son shiga shafin 'Facebook' da kuma yin ma'amala da shi. Yaya zan yi? Da fatan za ka taimaka mani. Abdulhamid Iliya
Malam Abdulhamid na san ya zuwa yanzu ka karanta amsoshi makamanta wannan da dama a wannan shafi, don haka ba sai na kara jaddadawa ba. Musamman ma ganin cewa baka yi bayanin ta wace hanya kake son aiwatar da wanann mu'amala ba. Ko ma ta wace hanya ce, bayanai dai sun gabata. Don haka ne ma daga yanzu zan daina buga dukkan sakonni makamanta wannan, saboda maimaici ne. Ina shawartan masu karatu cewa a duk sadda suka ga bayani kan wani abin da suke da sha'awa wanda wani ya tambaya aka bashi amsa, to su gamsu da amsar da aka bashi musamman in har abin da suke so na bayani iri daya ne da irin wanda aka amsa. Domin na sha amsa tambaya makamanciyar wannan, amma a duk sadda aka buga amsar tambayar, sai wani ya sake aiko tambaya irinta, a makon da aka buga; wanda hakan ke tabbatar da cewa wancan amsa ce ya gani, kuma yake son a bashi amsar tasa tambayar daban. Mu rika hakuri da abin da muka samu. Abin da yawa, wai mutuwa a kasuwa.
Baban Sadik ya aiki ya jama'a? Na ga tallarku ta GOOGLE+ a jarida, gaskiya na ji dadin haka. Dan Allah in an fara muna so a sanar da mu ta hanyar wannan lamba: 08038272720
Ai ba talla bace, fadakarwa ce irin wacce aka saba yi a shafin, kan duk wani abu sabo da ke samuwa a fannin sadarwa da kimiyya. Don haka wancan kasida da ka/kika karanta fadakarwa ce, cewa ga wata sabuwar masarrafar Dandalin Abota da Zumunta ta samu, amma ana gwaji. Don haka kana/kina iya ziyartar shafin masarrafar lokaci zuwa lokaci, don tabbatar da an fara amfani da ita ko a a. Shafin na: http://plus.google.com da fatan an gamsu.
Allah ya saka maka da alheri, Allah kuma ya bamu irinku da yawa, amin.
Mun gode, mu ma muna godiya da wannan addu'a. Allah saka da alheri, ya kuma albarkace mu baki daya da albarkokin da ke cikin wannan wata mai alfarma, amin.
Salam. Ina fatan kana lafiya. Hakika ina da sha'awar zama mai ilmin sarrafa na'urar kwamfuta, wane matakin farko ne zan soma dauka? (Bin uwaisu).
To, matakin farko dai shi ne kaje makaranta ko duk wata cibiya da ake karantar da ilmin kwamfuta. Dole sai ka fara samun karamar shahadar karatu, watau "Certificate" a fannin kwamfuta, sannan ka zabi bangaren da kake son kwarewa a kai. Don duk inda ake karantar da wannan ilmi, daga kwalejin fasaha har zuwa jami'a, da kuma cibiyoyin karantar da ilmi na masu zaman kansu, duk kana iya samu wannan kwarewa. Allah taimaka, ya kuma yawaita mana irinku a cikin al'umma, amin.
Asalamu alaikum Baban Sadik, na saita wayata a tsarin GPRS kamar yanda na ga kayi bayani a filinka, na kuma samu nasara. Domin ina shiga facebook, amma sauran shafukan ba sa budewa. Shin ya zama dole sai na bude adireshin Imel? Zakiru Elgusawiy, Suleja
Malam Zakiru ba ka'ida bace dole sai ana da adireshin Imel sannan ake iya mu'amala da fasahar Intanet a waya. In akwai tsarin Intanet a wayar, kana iya aiwatarwa ba matsala. Watakila dai baka sanya adireshin shafin da kake son shiga bane daidai. Amma in za ka iya shiga shafin Facebook, wannan alama ce da ke nuna cewa lallai za ka iya shiga wasu shafukan ma. Ka dai dada duba adireshin shafin da ka shigar. Da fatan an gamsu.
Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: kwanakin baya Najeriya ta taba jefa tauraron dan adam ya bace, ga wani za a sake jefawa. Ai fashin-baki game da yadda ake jefa shi, ko kuskure aka samu a na baya ne? Aliyu MukhtarSa'idu (I.T) Kano Email= aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 08099109200
Malam Aliyu ai bayani kan yadda ake jefa tauraron dan adam zuwa sararin samaniya ya gabata da tsawo ma kuwa a wannan shafi, ina ganin dai so kake a yi bayanin irin tsarin da aka bi wajen tafiyar da namu tauraron da ya samu matsala. Idan ba a mance ba, na kawo bayanai masu nuna cewa wancan tauraro mai suna "NigComSat 1" da aka ce ya bace a sararin samaniya, ba bacewa yayi ba. Ya dai samu matsala ne da fikafikansa masu taimaka masa da makamashin hasken rana, watau "Solar Panel" kenan. Wannan ta sa ya daina aiki, har ya zama kamar "sharar sararin samaniya" watau "Space Junk" kamar yadda malaman ilmin sararin samaniya ke cewa. A yanzu haka an dakatar da shi, yana can a sararin samaniya, haka zai gama shawaginsa ya kacalcale ya zama buraguzai har a rasa shi. Cikin makon da ya gabata ne aka jefa wasu guda biyu; da "NigeriaSat 2" da kuma "NigeriaSat R" daga kasar Rasha, don samun cinma manufofin habaka Najeriya a fannin kimiyyar sadarwa da likitanci da yada ilmi mai inganci a zamanance, kamar yadda shugaban kasa ya tabbatar a ranar da aka cilla wadannan taurari guda biyu. Allah fisshe su da mu baki daya, amin. Da fatan Malam Aliyu ya gamsu.
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Baban Sadiq barka da yau. Da fatan su Sadiq suna lafiya. Don Allah tambayata ita ce, na sayi laptop window 7, amma ba ta karbar printer 1020 leaserjet, kuma duk memory card na waya idan na sanya sai ta bata shi. Don Allah ina neman shawara. Wassalam. Daga Nu'uman Usman Katsina State.
Malam Nu'uman da farko dai ina neman afuwa, domin na so in baka amsar tambayarka daidai lokacin da ka aiko, amma ina shagalce sannan, kuma daga baya sai shedan ya mantar da ni, sai sadda na zo fitar da wasikun masu karatu zan amsa sannan na hango taka. Dan Allah a gafarce ni. Abu na farko dai shi ne, su na'urar Printer suna zuwa ne da faifan CD da ke dauke da "Drivers" dinsu, watau masarrafar hada alaka tsakanin kwamfuta da na'urar dabba'a bayanai kenan. Shin, ka sanya wa kwamfutarka wannan "Drivers" din? In har ka sa mata su, ya kamata a ce ta baka daman buga samfuriin shafin gwaji, watau "Test Page" kenan. Amma in har haka kawai ne ka makala mata na'urar don ka dabba'a bayani, ba yadda za a yi ta karba ai, tunda babu abin da ke hada alaka a tsakanin kwamfutar da abin da ka makala mata. Ka sani, babbar manhajar Windows ta XP, ita ce kadai ke zuwa da ire-iren wadannan masarrafai kyauta a cikinta. Amma Windows 7 sabuwar manhaja ce, kuma idan ka dubi na'urar LaserJet 1020, za ka ga tsohuwar Printer ce, ba lallai bane a samu masarrafanta a ciki. To amma kamar yadda na fada a baya, in har ka sa, amma ta ki amincewa da shi, to ya kamataka nemi kwararre kan harkar kwamfuta ya sa maka. Idan shi ma ya buga abin yaki, ga kuma matsalar bata katin MMC, to dole ne ka mayar da ita inda ka siyo, su canja maka da wata. Amma idan a hannun wani ka sayo bayan ya yi amfani da ita, to watakila daman can tana da matsala, musamman matsalar kwayar cutar kwamfuta, watau Virus. Wannan shi ne abin da nake tsammani. Sai ka kai a sanya maka masarrafar kariya, watau "Anti-Virus", sannan a goge su. Allah sa a dace.
Dan Allah Baban Sadik ina bukatar dan takaitaccen bayani a kan layin
nan na jikin taswirar duniya {equator}. Bello Aliyu, belloaliyumani@googlemail.com
Malam Bello wannan layi na Equator da ake iya gani a jikin taswirar duniya, watau Global Map, wani layi ne da ba a iya gani a zahiri (Imagery Line), wanda ya raba kwallon duniya zuwa gida biyu a kwance; aka samu arewaci da kudancin duniya, watau "Northern and Southern Hemisphere." Wannan layi ya raba duniya ne daidai wa daida, daga wadannan bigirori guda biyu. Masana sun zana wannan layi ne a jikin taswirar duniya sanadiyyar lura da aka yi cewa a duk shekara, rana kan cilla haskenta daga mafi kololuwar saman duniyarmu (watau "Zenith") zuwa mafi karancin nisanta a kasa (watau "Nadir"), cikin dukkan watannin Maris da Satunba, daga fitowarta zuwa faduwanta. Wannan layi na Equator dai ya faro ne daga yammacin duniya zuwa gabashinta a kwance, inda ya raba kwallon duniyarmu zuwa gida biyu; daya a sama daya kasa misali. Bangaren arewaci ne a sama, shi kuma bangaren kudanci yana kasa. Idan rana ta cillo ta kan maye kwallon duniyan da wannan layi yake kai ne; daga kasar Burazil, da Tekun Atilantika idan ka shigo nahirar Afirka, zuwa kasar Kenya, da Kongo Zayar, da Tekun Indiya (watau "Indian Ocean"), da Indonesiya, da Ekwado, da French Guina. Tazarar nisan wannan layi na Equator daga inda aka kaddara farko zuwa karshensa dai ya kai nisan tazarar kilomita 40,030.20. Kuma duk da cewa ba a ganin wannan layi a zahiri kamar yadda na sanar a farko, sai dai akwai alamu da wasu kasashe suka sa a daidai inda wannan layi na Equator ya ratsa kasashensu. A kasar Kenya akwai alamar da aka sa a garin Nanyuki, don nuna inda wannan layi ya ratsa. A kasar Indonesiya akwai inda aka sa alamar a garin Pontianak, don nuna inda layin ya ratsa. Idan muka je Tsibirin Sao Tome & Principe ma akwai alamar a garin Ilheu das Rolas. A kasar Burazil akwai alamar mai suna "Marco Zero" da ke garin Macapa, inda layin ya ratsa. Masana sun tabbatar da cewa, akan samu ruwan sama mai yawa a duk shekara daidai inda wannan layi ya ratsa. Wannan shi ne dan abin da ya samu. Da fatan an gamsu.
Salam, Malam dafatan kana lafiya ya aiki da sauran hidimomi? Allah ya kara taimakawa. Na rubuto ne dan in kara jinjina maka a kan irin kokarin da kake yi. Allah ya kara basira, amin. A karshe muna addu'ar Allah ya bar mana kai dan cigaba da irin wanan kokarin. Daga almajirinka Hamza M. Djibo Niyame Jamhuriyar Nijar: alhamza_mjn@yahoo.fr
Alhaji Hamza muna amsawa kuma muna godiya da addu'o'inka kamar yadda ka saba. Allah saka maka da alheri kaima, ya kuma albarkace mu baki daya, amin. mun gode. Mun gode. Mun gode.
Baban Sadik don Allah in Google+ sun ba da dama a bude shafi don Allah ka gaya min ko da ta amiya ne. ahassanabba@yahoo.com
Malam Abba inshallah zan yi kokarin haka idan suka bayar da dama ga kowa da kowa. Amma kafin nan, me zai hana ka je shafinsu da ke: http://plus.google.com don shigar da adireshinka na Gmail idan kana da ita, da zarar sun bude ga kowa da kowa, za su sanar da kai. Da yawa cikin mutane sun bayar da adireshinsu don a tuntube su. Domin ina iya shagala a matsayi na na dan adam. Da fatan za ka yi hakan, don ya fi tabbaci. Allah sa mu dace, amin.
Assalamu alaikum Baban Sadiq, ina mika godiya a gareka a kan amsa tambayoyi da kasidun da kake rubutowa a jaridar aminiya, da fatan Allah ya saka maka da alheri amin. Haka kuma ina rokonka da ka sanya ni a cikin wadanda kake tura wa kasidu masu ilimantarwa ta hanyar Imel. Da fatan za a duba wannan roko nawa. Bissalam. Sani Idris Kawo. Imel: sandris67@yahoo.com
Malam Sani na samu bukatarka, sai dai kuma a halin yanzu babu wata rajista da na ajiye don yin haka. Illa dai duk wanda ke bukatar wata kasida ta musamman wacce na san an dade da bugawa a shafin, wanda kuma watakila neman kasidar a shafin Intanet zai zama masa da wahala, sai in aika masa. Amma babu wadanda nake aika wa kasidu ta Imel a duk mako. Domin idan na dauki wannan tafarki ba zan iya tabbata a kanshi ba, saboda yanayin aiki na. Sai dai in har za ka iya, ka rika shiga shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don samun wadannan kasidun. Hakan zai fi sauki. Duk da cewa na dade ban loda wadanda aka ba tun farkon wannan shekara, zan yi kokarin yin hakan bayan sallah in Allah ya yarda, don baiwa irinka daman samun kasidun cikin sauki. Amma a yanzu kam a gafarce ni. Da fatan an gamsu.
Baban saddik: ban gane ba na ji kace wai ruwan sama maimaituwa yake, bayan fadin Ubangiji "mun saukar da ruwa daga sama mai tsarki." Kuma ko da dandanonsu ne ya sha bamban da na rijiya ko na kogi, haka abin yake ga tsirrai. Domin duk tsirran da ya sha ruwan sama ya fi wanda aka yi masa bayi. Wannan yana nuna maka da cewa sinadaran da ke cikin ruwan sama yayi daban da na teku. Ruwan teku yana dandanon gishiri. Daga Ghali Bauchi
Malam Ghali sannu da aiki, kuma na gode da wannan fadakarwa da tsokaci. Hakika na karu sosai da wannan bayani naka. Duk da cewa har yanzu dai ina kan baka na, domin akwai bangaren hujjojin da ka kawo wadanda basu kai su tunkude abin da na rubuta ba, sai ma kara karfafa su da suka yi. Da farko dai tukun, cewa da Allah yayi ya saukar da ruwa mai tsarki, haka abin yake. Sannan batun dandano, da tasiri a kan shuke-shuke, wannan ba abin mamaki bane don ruwan sama ya zarce sauran nau'uka, domin kamar yadda na sanar, ruwan sama na maimaituwa ne a wani yanayi da tsari, wanda dole ne a samu bambancin dandano tsakaninsa da sauran nau'ukan ruwa da ke duniya. Kuma sanadiyyar wannan tasiri ne ma ake samun kankara da ke sauka daga gira-gizai. Kamar yadda na tabbatar a kasidar, ruwa ba daga jikin sama bane yake zuba, daga jikin gira-gizai ne, haka Malaman tafsirin Kur'ani suka tabbatar. Har wa yau ba abin mamaki bane don ruwan sama ya fi tasiri wajen tsirrai kan sauran nau'ukan ruwa. Wannan albarka ne da Allah ya sa a cikinsa. Albarka kuwa shi ne dukkan wani nau'in alheri da ke samuwa daga wani abu ko wani mutum ko wani gari misali. Kasancewar ruwan sama na da albarka ba ya hana sauran nau'ukan ruwa su zama haka, sai dai kowanne da nashi bangaren da Allah ya killace masa. Misali, ga ruwan zamzam nan, yana da albarka shi ma, amma daga karkashin kasa yake bubbuga.
Amma idan ka ce don Allah yace ruwan sama mai tsarki ne, kuma da haka kake ganin dole ya zama daga wani muhalli ne ba maimaituwa yake ba ta hanyar dalilan kimiyya da suka tabbata ta hanyar bincike, a nan dole ka kawo wa jama'a hujja; daga ina ruwan ke zuwa? Domin ruwan sama na cikin ayoyin Ubangiji da ya kirayi duniya gaba daya ta yi dubi gare shi, dubi irin na tunani da nazari, don gano kudurar Allah. Wannan na cikin aya ta 168 da ke cikin Suratul Bakara. Shi kuma Allah ba ya kalubalantar mutane su yi nazari kan abin da idan sun kalle shi ba za su fahimci sakon da ke cikinsa ba, a dabi'ance. Domin dukkan ayoyin da Allah ya samar a cikin halittunsa duk wani mai hankali na iya fahimtarsu idan ya yi musu kallo na nazari da fahimta, ko da kuwa ba musulmi bane shi. Kuma tunda ruwan sama da tsarin saukansa na cikin ayoyin Allah da ya samar, dole ne ya zama duk wanda ya yi nazari kan samuwansa, da yadda yake haduwa, da yadda yake tasiri idan ya sauka, zai gane abin da ake kiransa a kai. Shi kuma kallo da yin nazari kan abu bai takaitu ga kallo na ido kadai ba, a a, duk wata hanya da za ta iya taimakawa a fahimci tsarin abin ana iya amfani da ita don fahimtar abin da ake son fahimta. Da wannan tsari ne malaman kimiyya suke amfani wajen gano tsarin da ke cikin halittar Allah, musamman sama da kasa da sauran halittu masu rai. Da haka suka gano wannan tsari na saukar ruwa. In kuwa haka ne, duk da cewa ba lalai bane su yi daidai dari bisa dari, amma sai an samu tabbaci da kamshin gaskiya cikin binciken. Domin ba abu bane da aka zauna aka kirkira da ka, ko da tunani, da zace-zace.
Amma sauran halittun Allah da suka shafi gaibu, irin su Kursiyyu, da Al'arshi, da ruwan da ke saman sammai bakwai, wanda Al'arshinsa ke kai – kamar yadda ya fada cikin Kur'ani – duk abubuwa ne da hankali ko ilmi ko zurfin binciken mai bincike ba zai taba iya gano su ba, sai dai ayi imani da su saboda imani da aka yi da Allah. Wannan ta sa ba za ka taba cin karo da wata ayar Kur'ani da ke kira ga masu hankali ko ilmi da su yi bincike kan yadda Kursiyyun Allah ko Al'arshinsa yake ba. Saboda ba abu bane da za a iya gano shi ta hanyar bincike, sai ta hanyar wahayi da imani da gaibu kawai. Don haka ina nan a kan baka na cewa ruwan sama daga gira-gizai yake samuwa, kuma ruwa ne mai maimaituwa a wani tsari da kintsi na musamman, kamar yadda na sanar a wancan kasida tawa. Sannan Allah yana da ikon sanya duk abin da ya ga daman sa wa a cikin ruwan na albarka da sauransu. Kuma ba abin mamaki bane don dandanonsa ya canza, domin ruwan rijiya ma ai asalinsa daga sama ne, amma dandanonsa sun canza saboda muhallin da suke, na bambancin kasa da sauransu. Haka ruwan teku, su kuma haka Allah ya halicce su, da dandanon gishiri, kuma akwai shamaki wanda ido ba ya iya gani a tsakaninsa da ruwan gardi mai zuba daga sama. A karshe muna binka bashin hujja kan cewa ruwan sama daga wani wuri daban yake zuwa ba daga jikin gira-gizai ba. Amma a nawa bincike, wanda ya dogara kan ayoyin Kur'ani da sakamakon binciken malaman kimiyya na gamsu da abin da na karanta. Sai na ji daga gare ka, Malam Ghali.
Salam, na rubuto don in sanar da kai cewa na ga blogs dinka kuma na amfana ni da iyalina kwarai Allah ya saka da alhairi kuma ya kara hasken kwakwalwa amin. Sani Mafara; 2348062104878
Malam Sani ni ne da godiya. Domin ba karamin abin farin ciki bane mutum ya fahimci cewa dan kokarin da yake yi, mai cike da karancin ilimi, yana tasiri ba. Don haka na fi ka farin cikin jin haka. Allah sa mu dace, ya kuma albarkaci duk wata hazaka da ya bamu, amin. Na gode.
Don Allah Baban Sadik ina so a turo min kasidar da kuka gabatar kan wayoyin salula kirar nokia ko blackberry. Kuma ina da waya kirar nokia 3110c amma duk wani kayan application kamar dictionary, da opera da sauransu. Idan aka turo sai ta bata su, (corrupted & invalid appl.) ko menene dalili? Na gode. Daga Ibrahim Hamisu, Kurna Filin Durumi. Ibrahimhamisu68@yahoo.com
Malam Ibrahim da farko dai akwai kasidar da muka gabatar kan wayar Blackberry ce, ba Nokia ba, kuma na tura maka kamar yadda ka bukata. Dangane da abin da ya shafi wayarka kuma, ina ganin dai kamar ta kamu da cutar kwayar kwamfuta ne, watau Virus. Zai dace ka kaita wajen masu gyara su duba maka. Domin idan lafiyarta lau bai kamata ta bata duk abinda aka tura mata ba. An samu canjin dabi'a kenan. Akwai illa tattare da ita. Allah sa a dace, amin.
No comments:
Post a Comment