Wednesday, November 2, 2011

Sakonnin Masu Karatu da Gaisuwar Sallah

A yau kuma ga mu dauke da sakonnin da kuka aiko daga ranar bikin sallar azumi da ya gabata, zuwa ranar litinin din wannan mako. Duk sakonnin gaisuwar salla ba su bukatar wani jawabi, don haka na jero su a farko. Kamar sauran lokuta, akwai wadanda suka bugo waya, da yawa ba kadan ba. Muna musu godiya kan haka. Wadanda suka aiko sakonnin Imel kuma za su gafarce ni, sai mako mai zuwa zan buga sakonninsu in Allah Ya so. A halin yanzu ga dan abin da ya samu. A sha karatu lafiya.

Sakonnin Gaisuwar Salla

Salam Baban Sadiq, yardar Allah, amincin Allah, taimakon Allah, rahamar Allah, alherin Allah, annurin Allah, wadatar Ubangiji Allah, arziki, budi, rufin asiri, su kasance a tare da kai da sauran al’ummar musulmi; duniya da lahira. Barka da salla. Allah ya maimaita mana, ya karbi ibadarmu amin. Daga Sagir A. Nasir Rijiyar Lemo, Kano.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik), Ina maka barka da sallah, da fatan kayi sallah lafiya, to Allah Ya nuna muna na badin badada lafiya, cikin kwanciyar hankali. Sako daga 'Ali Garba Okene, Jahar Kogi

Salam ina yi wa Mallam Abdullah da manyan dalibanka da duk makaranta wannan fili, BARKA DA SALLAH. Ubangiji Ya karbi ibadarmu, Ya sa muna daga cikin wadanda aka ‘yanta, kuma Ya kara daukaka wannan fili, ameen. Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Assalamu alaikum, Ina yi maka fatan alkhairi da fatan an yi sallah lafiya, Allah (SWT) ya karbi ibadunmu, ya kuma maimaita mana amin. Ahmad Ali Aliyu.

Assalamu alaikum, zuwa ga Baban Sadik, da fatan an yi salla lafiya. Daga masoyinka: Salisu Aduya K/Hausa

Assalamu alaikum, ina mika sakon an sha ruwa lafiya, tare da fatan an yi Sallah lafiya, ALLAH ya maimaita mana amin.

Ina wa Baban Sadik gaisuwa, ina sauraron hira da ake yi da kai na Fasahar Internet a bbchausa. Muhammad, Daga gidan Sarkin Fadan Lafia, Jihar Nasarawa.

Bambanci Tsakanin “DVD” da “CD” da “LCD”

Assalamu alaikum Baban Sadik, dan Allah ina son ka wayar min da kai dangane da bambacin da ke tsakaninDVD da CD da LCD. Daga Babawo Mai Takin Mamani, Toro.

Malam Babawo lallai akwai bambanci tsakanin “DVD” da “CD”, a daya bangaren kenan. Sannan kuma da bambancin jinsi a tsakanin su da fasahar “LCD”. Idan aka ce “CD”, ana nufin faifan garmaho na zamani; watau kamar kaset din garmaho irin ta da kenan in ka santa. Ma’anar “CD” shi ne “Compact Disc”, kuma ana amfani da shi ne wajen taskance bayanai na rubutu, da sauti, da kuma hotona daskararru ko masu motsi, watau bidiyo kenan. A takaice dai, wannan fasaha ce ta maye gurbin faya-fayan garmaho da a zamanin da ake amfani da su wajen sauraron sauti kadai. Kuma tana iya daukan mizanin bayanai wajen miliyan dari bakwai (700MG) ne kadai. Shi kuma “DVD”, wanda yake nufin “Digital Compact Disc”, ingantaccen nau’in “CD” ne, wanda ke cin bayanai daga biliyan hudu zuwa biliyan goma sha shida (4GB – 16GB). Idan muka koma kan fasahar “LCD” kuma, wanda ke nufin “Liquid Crystal Display” a zamanance, it ace sabuwar fasahar nuna bayanai a fuskar talabijin, ta amfani da sinadaran gilashi masu dauke a sifar ruwa. A takaice dai, shi tsarin “LCD” nau’i ne na gilashin Talabijin, wanda ya sha bamban da nau’ukan gilasan da ke fuskar talabijin da na LCD ba. Yana da inganci wajen nuna hotuna rau-rau, kuma ba ya fitar da sinadarai masu cutar da idanu a yayin da ake kallonsa, kamar yadda sauran gilasan Talabijin ke fitarwa kuma suke cutarwa. Wannan nau’i na gilashi bai tsaya kan Talabijin kadai ba, har da kwamfuta akwai masu dauke da irinsa, musamman kwamfutocin kan tebur na zamani. Wannan shi ne LCD, kuma sabanin sauran da suka gabata, ba ma’adar bayanai bane, tsarin gilashi ne. Da fatan ka gamsu.

Fasahar Intanet da Imel

Baban sadiq, don Allah yaya zan yi in canza “password” din jakar Imail dina? Rabiu Isa Ayagi

Malam Rabi’u a min afuwa, kuma da fatan an yi salla lafiya. Canza kalmomin shiga (watau Password) na jakar wasikun Imel ba shi da wahala ko kadan. Idan ka budo zauren Imel dinka, watau “Email Home”, ko kuma da zarar ka shiga zauren Imel dinka, ka daga kanka sama zuwa bangaren hagu ko tsakiya, za ka ga inda aka rubuta “My Account”, sai ka shiga wurin. Da zarar ka shiga za ka inda aka rubuta “Change Password”, sai ka matsa kawai. Za su bukaci ka sake shiga da sunan da ka shiga da shi da farko, da kuma kalmomin da ka ke amfani da su, wadanda kake son canzawa. Da zarar ka sake shiga, sai a kaika inda za ka bayar da tsohon “Password”, sannan da sabon da kake bukata. Allah sa a dace, amin.

Assalam alaiKum, Abba na kayi mini bayani kan tsarin karatu a jami’o’in tsallaken kasar nan ta yanar gizo. Yan'uwa kuma barka da SALLAH. Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Malam Sadiq barka da war haka, kuma da fatan kana lafiya. Tsarin karatu ta yanar gizo ko “Online Distance Learning” ana gudanar da shi ne ta hanyar Imel; za ka je shafin makarantar, ka yi rajista ko ka cika fam, ka kuma loda dukkan takardun karatunka na baya, sannan ka aika musu. Idan lokaci ya yi za su aiko maka sako muddin ka yi nasara, sannan da kimar kudin da za ka biya, da kuma yanayi ko tsarin da ake bi wajen daukan darasi, da kuma rubuta jarabawa. Idan ka gama karatun kuma, nan take za su aiko maka da takardar shedar gama karatu. Wannan tsari ne da hatta a nan Afirka akwai kasashen da jami’o’insu ke yi. Misali, Jami’ar Afirka ta Kudu, watau University of South Africa, tana gudanar da wannan tsari na karatu. A karshe, muddin za ka yi karatu ta wannan tsari, to fa dole ne ka tanadi kwamfuta, ko ka tabbata kana da inda za ka rika zuwa kana samun damar mu’amala da fasahar Intanet, domin kusan komai ta Intanet ake gudanar da shi. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum. Baban Sadik yaya aiki? Ina yi maka fatan alheri. Ina da Imail yanzu, yaya zan yi rijista ta “Google Mail”. Allah ya saka maka da alheri. Musa Y Muhammad.

Malam Musa yin rajistar wasikar Imel ta kamfanin Google bas hi da wahala ko kadan. Idan akwai kwamfuta da ke jone da fasahar Intanet, ka je http://mail.google.com, da zarar shafin ya budo, a kasan shafin daga hannun dama za ka ga inda aka rubuta “Sign Up for Gmail”, sai ka matsa. Nan take za a budo maka fam da ake son ka cika. Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu. Magana ta kare. Idan kuma a wayar salula kake nufi, to ya danganci wayar da kake amfani da ita. Idan Blackberry ce, ko wata babbar waya da ke da tsari irin nata (misali Nokia E63, E52, E73), to duk kana iya kwatantawa kamar yadda na sanar da kai. Amma idan ba wata babbar waya bace, to dole ne sai kaje kan kwamfuta mai zaman kanta. Da fatan ka gamsu.

Salaam Baban Sadiq, ya aka ji da mu? Na iya shiga BBC Hausa, amma na kasa samun facebook.

Ka shiga ta wannan adireshin: http://mobile.facebook.com, ko kuma ta wannan adireshi: http://www.facebook.com/mobile. Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, taimako nake so game da sakon Imail da kuma facebook ta wayar salula. Ko sai ta kwamfuta? Ka huta lafiya. Ni ne Alh Dan Azumi 2ic, Fatakwal.

Alhaji Dan azumi ai ba sai lalai ta kwamfuta ba kadai, ko ta wayar salula ma kana iya mu’amala da fasahar Intanet. Abin da ya kamata ka yi shi ne, ka nemi waya wacce ke iya mu’amala da fasahar Intanet, sannan ka samu wanda ya kware wajen hakan don ya nuna maka. Domin hakan zai fi muhimmanci. Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina son a yi mini cikakken bayani game da Google. Daga Bashiru Umar Achida Iddo: 08036295411

Malam Basharu, Kalmar “Google” suna ne na kamfanin masarrafa da harkokin sadarwa a Intanet, kuma ofishin kamfani na kasar Amurka ne. A fayyace, gidan yanar sadarwa ne da ke http://www.google.com da ke dauke da manhajar wasikar Imel, da manhajar Manemar Bayanai, watau “Search Engine”, da sauran manhajoji ko masarrafan kwamfuta masu kayatarwa da ilmantarwa. In kana neman Karin bayani, sai ka je shafin da ke bayani kan kamfanin baki daya, a http://www.google.com/about. Da fatan ka gamsu.

Salam Abban sadik, ina da waya (Tecno system WAP2.0, GPRS class 12 H/W, N5, China) zan iya komai da ita kamar BlackBerry ta Kanada, ma'ana mu'amala da intanet kamar a kwamfuta? Zan so samun amsa ta wayata. Daga masoyinka Aliyu A. Lawan HMB (I D H) Kano.

Malam Aliyu, wayoyin kasar Sin, watau China Phones, suna da matsala guda daya wajen ta’ammali da fasahar Intanet. Ba kowacce bane ke iya sarrafa sakon “Settings” da kamfanin waya zai turo mata ba. Bayan haka, galibinsu kan zo ne da tsare-tsare (watau Settings) na musamman daga wasu kamfanonin waya da ke can kasar. Wannan ke nuna cewa dole sai sanya wadannan tsare-tsare da hannu, watau “Manual Configuration” kenan. Hakan kuma, a daya bangaren, ya danganci kwarewa da sanayyar mai sanya tsare-tsaren ne. In kuwa haka ne, to zan bayar da shawarar cewa a je wajen masu gyaran waya ko masana harkar tsare-tsaren waya. Za su iya taimakawa gaya wajen nemo masalaha dangane da haka. Da fatan an gamsu.

Bambanci Tsakanin “Datacard” da “SIM Card”

Assalamu Alaikum Baban Sadiq. Da fatan kana cikin koshin lafiya tare da abokan aiki, Allah Yasa haka, amin. Baban Sadiq mene ne “Data Card”, kuma ko akwai bambamci da ke tsakaninsa da “SIM Card” ne - ganin cewa dukkansu biyu ana kira ko amsa kira, sannan kuma ana iya lilo a yanar giza-gizai (Browsing) a wayar salula da su. Wassalam Daga Uncle Bash, Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com

A gaida Uncle Bash namu. Lallai akwai bambanci nesa ba kusa ba tsakanin wadannan nau’ukan kati guda biyu, watau “Data card” da kuma “SIM Card”. Da farko dai, shi “Data Card” nau’i biyu ne; akwai wanda ake amfani da shi, kamar yadda kace, wajen yin lilo da tsallake-tsallake a shafin Intanet. Wannan shi ne kamfanonin waya ke bayarwa don samun damar mu’amala da Intanet a kwamfutocin tafi-da-gidanka. Na biyun kuma shi ne wanda ake iya taskance bayanai kadai a ciki, sannan a shigar wa kwamfutar tafi-da-gidanka, watau Laptop. Wannan na biyun a matsayin katin ma’adanar bayanai na wayar salula yake, watau “Memory Card”. Sai dai shi ya kebanta ne da kwamfutar tafi-da-gidanka kadai. Domin suna da ‘yar kafar da aka kebance musu, inda ake tsofa wannan kati, don lodawa ko saukar da bayanan da ke cikinsa baki daya. A daya bangaren kuma, shi “SIM Card”, ko “Subscriber Identification Module”, kati ne da ke dauke da ma’adana (watau Memory ko Storage) nau’uka biyu biyu zuwa uku. Akwai inda ake taskance lambar katin, sai inda ake taskance lambobin mai katin, da kuma inda ake taskance kalmomin sirri (PUK ko Pin Cord ko Security Cord) da mai katin yake sanyawa don bude wayar da su. Kowane katin SIM na yade ne da sinadarin tagulla da ke taimakawa wajen tabbatar da mu’amala tsakanin siginar sadarwar kamfanin waya, da kuma wayar salular da ke dauke da katin. Da fatan ka gamsu.

Shawara da Addu’a ta Musamman

Assalamu alaikum Baban Sadiq, bayan gaisuwa da jinjina, nake so in yi amfani da wannan damar domin rokonka a kan ka fadada wannan baiwar da Allah yayi mana da kai, ka rika buga bayanai muhimmai, su zama littattai domin na baya. Daga Comrade Abdul Dantata, Waratallawa, Kano.

Dubun gaisuwa da fatan alheri ga Comrade. Wannan shawara ce mai kyau, kuma in Allah Ya so zan duba yiwuwar hakan ko da ba yanzu ba. Domin muddin zan yi hakan, dole sai na hada da kwararru ko masana a fannin, wadanda za su yi bita na kwarai kan abin da za a yada. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Baban Sadiƙ barka da aiki, da fatan Allah ya baka fasaha da zalaƙa wajen ilmantar da jama’a game da kimiya da kere-kere, kan da abubuwan da suka shafi zamani, amin. Allah bamu alheri. Daga Nasiru Sani GS

Malam Nasiru na gode da tarin addu’a, Allah karba, ya kuma albarkace mu baki daya, amin.

Yadda Aka Kera Jirgin Ruwan “RMS Titanic”

Baban sadik barka da aiki da fatan duk iyali lafiya, Allah ya kara ilimi. Na karanta shafin Kimiyya da Kere-kere na wannan makon, don ina da tambayoyi, ina fatan Allah ya baka ikon amsawa. Ga su kamar haka: na farko shin Architect Thomas Andrews dan wata kasa ne? Kuma yanzu wannan jirgin shi ne babba a duniya ko da wani?

Architect Thomas Andres dan kasar Ingila ne ko Ireland. Shi dai jirgin Titanic shi ne mafi girma a shekarar da aka kera shi. Amma a halin yanzu akwai jiragen ruwa manya da aka kera wadanda suka fi shi girma nesa ba kusa ba; sun kai wajen talatin. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara fasaha amin. Ka yi bayanin an shirya fim din "Titanic" a 1997, to shin abin da aka nuna a fim din shi ya faru a wancan Jirgin na asali (ko tarihi ne)?. Daga Aminu Shehu, Kano: 08036236878.

Malam Aminu wannan fim din daga baya ne aka shirya shi, bayan shekaru kusan tamanin da biyar da faruwar wancan lamarin. Na kawo bayanin fim din ne don misali da kuma hada alaka a tsakaninsu. Amma asalin jirgin yana karkashin tekun Atilantika a halin yanzu, kamar yadda bayanai suka gabata a shafin. Da fatan ka gamsu.

Salam Baban Sadiq, barka da aiki. Tambayata a nan ita ce, kamar manyan jiragen ruwa ana kera su ne a cikin ruwa, ko kuma sai an gama a sa su a ciki? Na gode, Allah karo basira. Daga Dahiru One One, Kubwa Abuja

Malam Dahiru sai bayan an kera su ake sanya su a cikin ruwa. Galibi kamfanonin kera jiragen ruwa musamman manya suna gina masana’antarsu ne a bakin teku, ko kusa da inda tekun yake. Wannan ke sawwake jigilar daukowa da sanyawa cikin ruwa. Da fatan ka gamsu.

Fannin Mu’amala da Kwamfuta

Meye bambancin “Computer Literacy” da “Computer Science”? Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Malam Khaleel, bambancinsu a fili yake. Shi “Computer Literacy” shi ne tsarin iya mu’amala da kwamfuta a aikace, shin, zuwa ka yi ka koyo, ko kuma da rana tsaka ka kama kwankwasata; muddin ka iya mu’amala da kwamfuta a aikace, to a iya cewa “You are computer literate”, a misali. A daya bangaren kuma, “Computer Science” fanni ne mai fadi da ke lura da dukkan wani ilimi da ya shafi rayuwar kwamfuta baki daya; daga tarihin samuwarta, zuwa ci gaban kere-kere da aka samu a bangaren kwamfuta, zuwa yadda ake taskance bayanai da hanyoyin yin hakan, har aka kai yadda ake tsara manhajoji ko masarrafan da kwamfutar ke amfani da su, duk wadannan suna karkashin wannan fanni ne. Kai a takaice ma dai, hatta shi kanshi fannin “Computer Literary” yana karkashin wannan fanni ne. Don haka fannin “Computer Science” ya fi fadin ma’ana fiye da “Computer Literacy”, duk da cewa asalinsu daya ne. Da fatan ka gamsu, kuma a mika gaisuwata ga Anti.

Rajistan Katin SIM

Assalamu alaikum, da fatan ka yi sallah lafiya. Na karanta amsarka dangane da rajistan katin SIM. To idan mutum ya ba da sunan karya da kuma adireshin karya ya zasu iya gane inda yake idan ya aikata mummunan halin shi? Haka kuma wasu ma suna bayar da layin su ne aje a musu. Kuma za'a iya sace wayan wani aje a aikata abin da ake so da shi. Wanda yin haka zai shigar da wanda bai san hawa ba bai san sauka ba cikin damuwa ya kuma tserar da mai laifin. Kadan kenan daga cikin matsalolin yin rajistan SIM. Ko hakan ma za'a iya hanawa? Suleiman Modibbo Jimeta. Yola, Adamawa.

Malam Suleiman wannan tsokaci naka yana da muhimmanci, kuma ma ban dauke shi a matsayin tambaya ba, domin amsar a fili take. Tuni na tara bayanai don gabatar da kasidu kashi biyu kan wannan tsari da gwamnati ta kawo na yin rajistan Katin SIM, tare da matsalolin da ke tattare da yin hakan a Nijeriyance. Don haka a dakace ni nan da ‘yan makonni. Allah sa mu dace, amin.

Assalam alaikum Baba Sadik, rajistan layi na MTN, sai mutum ya je kamfanin MTN ko zai, iya kiran sashen kwamstoma ya yi rajista? Daga Bashiru Umar Achida Iddo

Malam Basharu kowane kamfanin waya na da nashi tsarin na yin rajista, wanda kuma ya sha bamban da na sauran. Kamar yadda na fada ne a sama, akwai bayanai da ke tafe masu gamsarwa kan wannan tsari. Ban gama gudanar da binciken da nake kan yi bane shi yasa. A dan yi hakuri zuwa wani lokaci kadan nan gaba. Na gode.

Na’urar Gano Bigire

Sallama da fatan alkhairi. Mallam wai meye takamaiman aikin Compass ne? Sannan kuma yar wayar nan ta yan sanda da kuma ta sojoji, tana da bukatar sai an zuba mata kudi ne (phone card)? Ka huta lafiya. Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Malam Khaleel, abin da ake nufi da “Compass” dai wata na’ura ce mai kwakwalwar gano bigire, daga inda mutum yake rike da ita. Sau tari sojoji da matafiya, da kuma masallata kan yi amfani da ita. A wasu lokuta idan kaje wasu Otal a kasashen gabas ko kasashen larabawa, za ka ga an ajiye maka ita a dakinka. Idan kana son gano bigiren da kake nema; gabas, ko yamma, ko arewa, ko kudu, sai ka rike na’urar, za ka ga ta nuna maka bigiren da kake fuskanta. Idan gabas kake fuskanta, za ta nuna maka gabas ta hanyar wani karamin sanda mai kan kibiya. Wannan, a takaice, ita ce na’urar Compass.

Dangane da wayoyin oba oba da sojoji ko ‘yan sanda ke amfani da su kuwa, ba a sanya musu kudi ta hanyar kati kamar yadda muke yi da wayoyinmu a yanzu. Sai dai zuwa kamfani ake yi a biya kudin layi ko cajin Magana da ake yi da su. Ire-iren wadannan wayoyi su ake kira Walkie-Talkie a turance, kuma a asali guda biyu kawai ake bayarwa, sai a rika aiwatar da sadarwa a tsakani, watau Two-way Radio kenan. Amma daga baya sai aka samar da tsarin hada ire-iren wadannan wayoyi su rika sadarwa a tsakaninsu ko da kuwa sun kai dubu ne. Bayan haka, wadanan wayoyi sun sha bamban da irin na zamani, domin suna da takaitacciyar tazarar sadarwa, watau Network Coverage. Galibi ba su wuce tsakanin birni daya. Da fatan ka gamsu.

1 comment:

  1. gaisuwa mai yawa tare da fatan alkhairi a gareku Allah ya kara yawan basira
    ina bukatar koyan abubuwa da dama daga wajenku dangane da e-mail idan da hali
    daga comrade abdulkadir ali ibrahim kano nigeria

    ReplyDelete