Wednesday, November 2, 2011

Amsoshin Wasikun Masu Karatu

Karshen Zango

Bayan tsawon lokaci muna ta kwasan darussa iya gwargwado, a yau za mu karkare wannan marhala a daidai lokacin da ake bikin karamar sallar wannan shekara. Hakan na da muhimmanci don sake tsara wata alkibla kuma a marhalar da ke tafe. Kafin mu yi nisa, shafin Kimiyya da Kere-kere na taya dimbin dalibansa murnar bikin salla. Allah Ya sa ayyukan da muka gabatar cikin watan Ramadana karbabbu ne, ya kuma isar da mu wannan wata mai albarka cikin shekarar da ke tafe lafiya, amin.

Kada a mance, a caja wayoyin salula sosai, a zuba kudi a ciki, a sadar da zumunci (kada a mance a aiko sakonnin zumunci zuwa shafin Kimiyya da Kere-kere), sannan kuma, kowa ya lura da wayarsa. Domin masu satar wayoyin salula sun fi zage damtse lokacin bukukuwa, don sun san mutane a shagalce suke a lokacin. A kira ‘yan uwa da abokan arziki, a aiko sakonnin text masu dauke da dadadan kalmomin zumunci da kaunar juna.

Da zarar mun dawo hutun salla, za mu ci gaba da gabatar da jawabai kan fannonin kimiyya iya gwargwadon hali. Muna mika sakon gaisuwa da godiya ga dimbin masu karatun da ke bugo waya a lokuta daban-daban don tambaya ko neman Karin bayani ko nuna gamsuwa. Dangane da masu aiko sakonnin text kuma, muna mika godiya garesu, musamman masu aiko sakonnin godiya da gamsuwa. A halin yanzu ga sauran sakonnin text da suka saura a jakar wayar salula ta zan amsa. Wadannan sakonni da zan amsa dai sakonnin ne da ba su dauke da maimaici. Duk wadanda suka rubuto sakonnin neman Karin bayani kan abin da muka sha tattauna shi a shafin, sai dai su yi hakuri. Domin kamar yadda na sanar ne a shekarar da ta gabata, cewa idan muka ce za mu yi ta amsa ire-iren wadannan tambayoyi – musamman kan tsarin amfani da Intanet a wayar salula ko yadda ake shiga Facebook – to za mu wayi gari muna ta gewaye ne a waje daya. Duk wanda bai ji sakonsa ba, to ya yi hakuri. A halin yanzu ga wadannan sakonnin neman Karin bayani nan.

Amsoshin Tambayoyinku

Assalaamu Alaikum, yaya kokari? Ina son Karin bayani a kan EMS, MMS, da kuma SMS. – Khaleel Nasir Kuriwa Kiru: 07069191677

Malam Khaleel barka da war haka kuma da fatan an yi salla lafiya. Abin da jerin haruffan “EMS” ke nufi shi ne “Enhanced Message Service”, watau kayatacciyar hanyar aikawa da sakonnin text a wayar salula. A wannan tsari, kana iya aikawa da sakonni ta amfani da haruffa masu launi, da kuma amon kira (watau Ringing Tone). Wannan tsari na amfani a tsarin sadarwar wayar salula ne irin ta da. Jerin haruffan “MMS” kuma na nufin “Multimedia Messaging Service”, kuma hanya ce ta musamman da ake aika sakonni a wayar salula da suka shafi haruffa, da sauti, da bidiyo, da hotuna da dai sauransu. Wannan tsari na amfani ne da tsarin sadarwa ta Intanet na kamfanin waya wajen aikawa da wadannan nau’ukan sakonni. A daya bangaren kuma, jerin haruffan “SMS” na ishara ne ga “Short Message Service”, kuma na tabbata duk mun san wannan tsari; wanda yana amfani ne da tsarin sadarwar kamfanin waya (Network Service) wajen aikawa da sakonni. Da fatan ka gamsu.

Assalamu Alaikum, ina son a min bayani a kan “Settings” din “GPRS” wanda ba a daukan kudi a wayar mai amfani da shi, sabanin wanda ake daukan kudi a wayarsu. Da fatan an gane tambaya ta. - Nine Malam Malam Mai Zanen Hula Gololo: 08032822433

Malam Mai Zanen Hula barka da warhaka. Tun ina sakanadare nake ta jin sunanka a gidajen rediyon kasar nan. Ashe da taimako da nufin Allah za a hadu ta nan. To Allah sa a dace. Bayani kan tsarin amfani da Intanet a wayar salula wanda ba a iya daukar kudi a wayar mai amfani, a kashin gaskiya, ba halattaccen tsari ba ne sam ko kadan. ‘Yan Dandatsa ne ke hankado kofar kwamfutocin kamfanonin waya, ta hanyar amfani da masarrafar “OperaMini” na musamman, don jonuwa da kwamfutocin kai tsaye. Wannan ke bayar da damar shiga ko mu’amala da tsarin Intanet kyauta ta hanyar kwamfutocin, ba tare da manhajar kamfanin ta kalli wayar salularka ba a lokacin da kake lilo a saman giza-gizan sadarwa ta duniya ta hanyar kwamfutocinsu, balle har ta cire kudi. Ba kai kadai ba, da dama cikin masu karatu sun sha bugowa suna neman Karin bayani kan wannan tsari. Akwai ma wanda ya bugo mini cewa ya dade yana amfani da tsarin, amma daga baya abin ya yanke; har yake tambayar wai ko da gaske ne cewa wayarka na iya kamuwa da kwayar cutar kwamfuta, watau Virus a lokacin da kake mu’amala da wannan tsari?

Tabbas wannan tsari ba ya dawwama, nan take kamfanin zai gano wannan badakala har ya toshe hanyar da ake bi ana shiga. Wannan tasa da zarar an fara amfani da shi na tsawon mako ko makonni biyu, sai ka neme shi ka rasa. Har wa yau, akwai hadari wajen amfani da wannan tsari, domin wayar salula na iya kamuwa da kwayoyin cutar kwamfuta, watau Virus. Domin wayar tana mu’amala da giza-gizan sadarwa ne kai tsaye, ta hanyar da babu tsaro, watau “Unsecured Connection”. Don haka sai a hakura da wanda za a iya cire kudi, domin ya fi natsuwa. Da fatan an gamsu.

Assalamu Alaikum Baban Sadik, shin, wace kasa ce ta kirkiri kwayar cutar kwamfuta, watau “Computer Virus”? – Hambali Azare: 08036966225

A gaskiya babu wata kasa da za a ce ita ce ta kirkiro wannan matsala. Domin wani abu ne da ke ta’allake da kwarewa, wanda kuma kowa na iya samunsa a ko ina yake a duniya. A takaice ma dai, ba za a iya cewa ga wanda asali ya fara kirkiran wannan matsala ta kwayar cutar kwamfuta ba. Dalili kuwa shi ne: wannan matsala ta kwayar cutar kwamfuta ta fara samo asali ne ta sanadiyyar kurakuran da masu gina masarrafar kwamfuta ke yi cikin aikinsu, wanda sanadiyyar haka sai a samu matsala wajen aikin manhaja ko masarrafar. Daga baya da magina suka gano tasirin ire-iren wadannan kurakurai, sai wasu suka ribaci wannan dama wajen kirkirar nau’uka daban-daban. Wannan ke tabbatar da cewa babu wata kasa ko wani mutum musamman da za a ce shi ne ko ita ce ta fara kirkirar wannan matsala. Da fatan ka gamsu.

Dan Allah Baban Sadik ina son ka yi min bayani a kan hanyar kasuwanci ta na’ura mai kwakwalwa, watau “Forex Trading”. - Usman Aliyu Gobirawa Sokoto

Malam Usman barka da warhaka, da fatan ana lafiya. A gaskiya bayani kan yadda ake tafiyar da “Forex Trading” na bukatar dogon bayani don samun gamsuwa. Don haka idan Allah Ya kai mu bayan Salla za mu gabatar da bayanai kan amfani da hadarorin da ke tattare da wannan tsarin kasuwanci da dai sauransu. Allah sa mu dace, amin.

Salamu Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: me ye bambancin motoci masu sitiyari a hannun hagu (left driver) da masu sitiyari a hannun dama (right driver)? - Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano) 08034332200

Malam aliyu ai bambancinsu a bayyane yake. Idan kuma kana nufin dalilin samuwar hakan ne, to labarin ba a nesa yake ba. A farkon lamari an fara kera motoci ne masu sitiyari a hannun dama, watau “Right Driver” kenan. Dalilin yin hakan kuwa shi ne don sawwake wa direbobi tsarin tuki, ba tare da sun yi ta kartar dangan gidaje ko fadawa cikin kwatami ba a yayin da suke kokarin shiga kwana, ko kuma suka samu kansu cikin wani lungu. Domin idan direba yana kusa da dangan da ke hannunsa na dama, to zai samu saukin ganin yadda tukinsa ke gudanuwa ba tare da matsala ba. Amma daga baya sai wasu kamfanonin kera motoci suka lura cewa, idan direba yana bangaren dama yana tuki, zai iya samun matsala a duk sadda ya zo yin kiliya (overtaking) ga wata motar da ke gefensa. Watau maimakon ya zama yana kallon tsakiyar hanya don hango motar da ke tafe a yayin da yake yin kiliya, hakan ba ya yiwuwa saboda kasancewarsa a bangaren dama. Don haka sai aka fara kera motoci masu sitiyari a hannin hagu, don sawwake wa direba a yayin da yake tuki a babban titi. Da fatan ka gamsu.

Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: me ye alfanun da ke tattare da umarnin da Hukumar Sadarwa ta Kasa, watau NCC ta baiwa kamfanonin sadarwa masu zaman kansu cewa su fara yin rajistan katin SIM din mutane; yaya tsarin abin yake, kuma ko wasu kasashe na da irin wannan tsarin? - Aliyu Muktar Sa’idu (IT) Kano: 08034332200

Malam Aliyu wannan umarni da Hukumar NCC ta baiwa kamfanonin waya masu zaman kansu dai shi ne su fara yin rajistan katin SIM din kwastomominsu nan take, sannan kuma nan gaba duk wani katin SIM da za su sayar, to dole ne ya zama sun masa rajista kafin sayarwa ga jama’a. Amfanin yin hakan dai shi ne don rage yawan zamba cikin aminci da sace-sace da kuma manyan miyagun assha da wasu bata-gari ke yi ta hanyar wayar salula. Domin a yanzu ba abu bane mai wuya mutum ya sayi katin SIM sabo, ya aikata aika-aikan da yake son yi da shi, bayan ya gama ya jefar ko kona shi. Hakan ne ya sawwake wa da dama cikin masu yin wannan assha samun saukin aiwatar da tsiyatakunsu. Domin babu yadda za a iya gano ko waye mai lambar kati kaza da kaza. To amma da wannan sabon tsari, duk wanda ya sayi katin SIM sabo, ko kuma yaje yayi rajistar katin da yake amfani da shi, to sunansa zai kasance cikin manhajar kamfanin wayar da yake amfani da katinsa. Kuma nan take ana iya gano ko waye; da sunansa, da adireshinsa, da kuma tambarin hannunsa. Akwai wannan tsari a kasashe da yawa, ba wai kasar nan ne kadai ta fara amfani da shi ba. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu Alaikum Abban Sadik, wane bambanci ke tsakanin tsarin sadarwar rediyo na AM da kuma FM? - Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano: 07069191677

Malam Khaleel wadannan tsare-tsare ne guda biyu masu matukar tasiri wajen sadar da siginar rediyo da shirye-shiryensu tsakanin tashar sadarwa zuwa akwatunan rediyon jama’a. Tsarin “Amplitude Modulation” ko “AM” a gajarce dai, shi ne tsarin da ke sadar da shirye-shirye a tashoshin da ke kadadar sadarwar da tazararsa ke tsakanin KiloHerzt 535 zuwa 1605. Hakan kuma na yiwuwa ne ta hanyar cilla sauti ko murya a sigar maganadisun lantarki. Duk wani akwatin rediyo da ke tsakanin wannan kadadar sadarwa (watau 535kHZ zuwa 1605kHz) duk zai iya kama wadannan shirye-shirye. A daya bangaren kuma, tsarin “Frequency Modulation” ko “FM” a gajarce, yana aiwatar da sadarwa ne a kadadan sadarwar da ke tsakanin 88mHz zuwa 108mHz. Kuma sakonnin murya ko sautin na isa ga akwatunan rediyon ne ta hanyar maganadisun lantarki, kamar yadda yake a tsarin AM.

Daga bayanan da suka gabata, za mu fahimci bambanci wajen uku da ke tsakanin wadannan tsarin sadarwa guda biyu. Na farko shi ne bambancin kadadan sadarwa; tsarin AM na tazarar 535kHz ne zuwa 1605kHz, a yayin da tsarin FM ke kadadar da ke tazarar 88mHz zuwa 108mHz. Na biyu, tsarin AM na amfani ne da ma’aunin tazarar aika sauti na “KiloHerzt”, a yayin da tsarin FM ke amfani da ma’aunin aika sauti na “MegaHerzt”. Bambanci na uku kuma shi ne, dangane da tazara da saurin maimaituwa, tsarin AM ya fi cin dogon zango, wanda kuma hakan tasa iska ke cakuduwa da sautin da ake aikawa. Shi kuma tsarin FM yana aiwatar da sadarwa ne a gajeren zango, wanda kuma hakan ya haddasa masa saurin maimaituwa wajen aikawa da sautin, kuma aka wayi gari tsarinsa ya fi na AM ingancin sauti da tagomshi. Da fatan an gamsu.

Assalaamu Alaikum, barka da warhaka Baban Sadik. Wai shin, mene ne tasiri da illan gurbatattan mai (crude oil) din da ke malala a tekun Mexico (Gulf of Mexico) da ke Amurka ne? Kuma ko wannan man da ake yadewa a saman tekun zai yi amfani in an sarrafa shi, ko kuma ya lalace kenan har abada? - Uncle Bash, Jimeta, Yola: 07037133338.

Malam Bash barka da warhaka kai ma, kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci, kuma tun sadda ka aiko nake ta kokarin tanadin gabatar da gamsasshen jawabi a sigar kasida ko makala mai dan tsawo. Domin hakan ne zai taimaka wa mai karatu fahimtar yadda lamarin yake. Don haka yanzu ma ba amsa zan baka ba, sai dai mu dan dada hakuri, akwai kasidu na tanada da zan yi nazari don fitar da makala mai kyau, mai dan tsawo kuma mai fa’idantarwa sama da jawabin da watakila zan bayar a dan kankanin shafin nan, in hakan na yi. A min hakuri zuwa bayan hutun Salla. Na gode.

Sallama, da fatan alheri ga Baban Sadik. Shin, ko zan iya sanin shiyyar da wanda ya aiko min da sakon Imel yake? - Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano: 07069191677

Sanin shiyyar da aka aiko maka da sakon Imel abu ne mai wahala, musamman idan ba kwararre bane kai a fannin hada alaka a tsakanin kwamfuta da yadda tsarin sadarwa ke aukuwa a tsakaninsu. Sannan kuma ya danganci irin manhajar Imel din da abokin huldarka ko wanda ya aiko maka da sakon yake amfani da ita wajen yin hakan. Da farko dai, muddin kana son sanin daga ina aka aiko maka sakon Imel, to dole ne ka san tsurar adireshin kwamfutar da aka yi amfani da ita, watau “IP Address” kenan - gundarin adireshin kwamfutar nake nufi. Kowace kwamfuta na dauke ne da adireshi wanda yake a jerin lambobi (misali: 235.75.4.9.0). Da wadannan lambobi ne take amfani wajen aika sako ga wata kwamfuta ‘yar uwarta; a giza-gizan sadarwa ne ko a zangon sadarwa tsakanin gida ko ofis ko wata jiha ta musamman. Idan daga Intanet aka aiko maka da sakon, to dole ne ka san wadannan lambobi, sai ka sansu sannan za ka iya sanin a inda kwamfutar take. Domin dukkan kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwa a Intanet suna da adireshin da ke nuna daga kasar da suke, kamar yadda ka san kowace kasa tana da tsarin adireshinta na musamman. Idan ba wadannan lambobi ka gani ba, kuma har ka iya tacewa tare da fahimtar kasar da ake danganta adireshin da ita ba, to ba ka iya sanin haka. Kuma ko da ma ka san kasar, ba lallai bane ya zama wanda ya aiko da sakon a kasar yake. Misali, akwai kamfanoni masu adana shafukan yanar gizo ko bayar da damar mu’amala da fasahar Intanet ta amfani da tauraron dan Adam, ire-iren wadannan kamfanoni a kasashen Turai suke, amma za ka samu galibin kamfanoninmu a nan na amfani da adireshin Nijeria ne (na gidajen yanar sadarwarsu) amma kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwar na wasu kasashe ne daban. A irin wannan yanayin kuwa, sai dai kayi ta kirdado, amma ba wai ka san hakikanin inda aka aiko maka ba. Da fatan an gamsu.

Salam, Malam ina son in samu Karin bayani kan yanayin samuwar ruwan sama a duniya, ta yadda za ka ga wani sashi yana samun ruwa ne watanni hudu a shekara, wani kuma fiye ko kasa da wata hudun. – Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano.

Wannan tambaya ce mai bukatar dogon bincke, ba wai Karin bayani ba. Ana yin Karin bayani ne kan abin da aka taba tattaunawa a kai, amma ba a gamsu sosai ba. Sai dai lokaci na tafe in Allah Ya so, za mu yi dogon bayani mai gamsarwa kan hakan. Ire-iren wadannan tambayoyi suna da amsa na kusa ne, da kuma wadanda ke nesa. Amsoshin nesa su ne wadanda ke da goyon bayan hujjojin binciken kimiyya. Na kusa kuma wadanda a al’ada kawai aka sansu, kuma ake iya bayaninsu. Duk da cewa wasu daga cikinsu na dacewa da binciken kimiyya, dogaro a kansu kadai ba zai taba wadatarwa ba, musamman a shafi makamancin wannan. A fannin kimiyya kuwa babu abin da yafi amsoshin nesa amfani. Allah sa mu dace.

Jinjina gareka Baban Sadik, zan so don Allah ka aika min da bayanin da kayi a kan yadda ake bude “Blog” a yanar gizo. – Alhaji A. Palladan, Zaria: ahmedpalladan@yahoo.com

Ina godiya Alhaji, kuma Allah saka da alheri, da fatan an yi sallah lafiya. Sai a dunguma zuwa jakar Imel, tuni na tura. In da akwai Karin bayani da Alhaji ke nema bayan kasidar, kasancewar na jima da rubuta ta, a shirye nake in taimaka. Na gode.

To, Malam Abdullahi wannan bau’in wayar “Blackberry” da ka bamu bayaninta a makonnin da suka gabata, shin ta shigo Nijeriya kuwa? In kuma ta shigo, to, nawa ne farashinta? - Salisu Nagaidan Jama’are: 08063461480

Malam Salisu lallai wannan waya ta shigo kasar nan tuni, har ta fara zama jiki ma. Dangane da farashinta kuwa, sai in ce a je shaguna ko kantinan sayar da wayoyin salula da ke manyan biranen kasar nan, ko kuma aje ofishin kamfanin MTN, ko Zain, ko Etisalat, ko kuma Glo, duk suna sayar da ita. Amma mu a shafin Kimiyya da Kere-kere ba mu sayar da wayoyin salula ko kwamfuta, sai yin bayani kan yadda ake kera su ko ake amfanuwa da su. Wannan bayani na da muhimmanci in kara yinsa a nan, domin da yawa cikin masu karatu kan bugo waya duk sadda suka ga hoton wata kwamfuta ko wayar salula ko wata na’urar sadarwa a shafin nan, suna neman farashinta ko inda za su je su saya. Muna sanya hotunan ne don a gani, kuma hakan na taimaka wa mai karatu wajen fahimtar nau’in abin da ake masa bayani ne. Sai a rika lura. Mun gode.

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, don Allah ina son ka taimake ni da amsar wannan tambaya: wai shin me ke haifar da canje-canje a harsuna ne? Da fatan an sha ruwa lafiya. - Daga Aliyu M. Chiso, dalibi a Jami’ar Danfodio, Sokoto: 08097323092

Malam Aliyu wannan tambaya taka akwai sarkakiya a tare da ita, dangane da abin da muke karantarwa ko yin bayani kansu a wannan shafi. Shin kana nufin canje-canjen harshe a lafazin zance ne, ko kuma a tsarin halitta? Wannan tambaya ce da ke da alaka ta kut-da-kut da fannin harsuna da zamantakewa. Idan kuma ni ne ban fahimci abin da kake nufi ba a tambayar, to don Allah a kara min bayani filla-filla. Na gode.

Assalaamu Alaikum, don Allah ina son bayani a kan na’urar “Fax”. - H. M. Kongolam: 08026817542

“Fax” na’ura ce mai taimakawa wajen sadar da bayanan da ta kwafo daga shafukan takardun da aka ciyar da ita – daga tashar aikawa zuwa tashar karba. Na’urar “Fax” na cikin dadaddun kayayyakin sadarwa na zamani da aka fara amfani da su shekaru kusan hamsin da suka gabata. Na’urorin “Fax” na asali suna amfani ne da tsarin aikawa da karbar sakonni ta siginar lantarki nau’in “Analogue”, kuma sukan dauki tsawon mintuna uku zuwa shida kafin su aika da sakon shafin fallen takarda daya. Wadannan su ake kira “Analogue Fax Machines”. Sai na zamani, masu amfani da tsarin tankwasa kaurin bayanai ta hanyar lantarki na zamani, watau “Digital Compression Methods”. Su kuma sukan dauki tsakanin dakika goma ne zuwa ashirin wajen aikawa da shafin fallen takarda guda daya. Idan aka tashi aikawa da sakon fax, za a dauki shafin takarda ne, sai a dora shafin da ke dauke da bayanan da ake son aikawa a saman wannan na’ura, a matsa ko shigar da lambar na’urar da ke son karbar sakon, sannan a matsa tambarin da zai bata umarnin aikawa da sakon. Daga nan sai wannan na’ura kuma ta dauki hoton shafin da ke dauke da bayanan a sifar hasken lantarki, sannan ta aika wa ‘yar uwarta da ke daya bangaren. Da zarar ta gama aikawa, sai ta fitar da sako cewa “sakon da aka ce in aika wa wane da wane, na aika musu shafi kaza, a lokaci kaza, a kuma rana kaza.” Kowace na’urar Fax na da lambar tarho (ko lambar fax – watau “Fax Number”), wanda da shi ne ake amfani wajen aika mata da sako. A halin yanzu ma ana iya aikawa da sakon fax ta hanyar kwamfuta, ba sai ta hanyar na’urar Fax kadai ba. Domin kwamfuta na dauke da dukkan masarrafan da ke taimakawa wajen yin hakan. Da fatan ka gamsu.

Barka da shan ruwa Abdullahi, wani taimako nake so a yi mini, wato ma'anar na'ura mai kwakwalwa da kuma muhimmancinta ga al'umma. Na gode. - Shamsu Isiyaku: shamoo04@yahoo.com

Malam Shamsu, “Na’ura mai kwakwalwa” dai ita ce kwamfuta da muke amfani da ita. Na’ura ce da ke iya karbar bayanai, ta adana, ta mika idan an tashi bukata, tare da sarrafa su a yanayi daban-daban. Wannan a takaice shi ne ma’anan na’ura mai kwakwalwa. Daga cikin amfaninta ga al’umma akwai sawwake ayyuka, da sawwake lissafi, da sawwake rayuwa, da adana bayanai masu dimbin yawa cikin dan Kankanin muhalli da farashi, da kuma taimakawa wajen samar da aikin yi a rayuwa. Da fatan ka gamsu.

Cikin yardar Allah, Allah ya hada ni da kai ta hanyar jaridar Daily Trust, sai na ga AMINIYA. Samunka sai ya jefa ni a wani sabon yanayi, na ga ai na tsinci dami a kale; kila ni ma na zama "Lu'u Lu'u a cikin juji" inji wani fasihee. A nan nake mika kokon barata ta neman shawarar yadda zan fadada fahimtata a Intanet ta hanyar aiki da wayar salula da taimakamin da guraben da suka kamata na rika kai ziyara. Daga karshe ina da tambaya, sau dayawa idan nazo sauke wata manhaja ko wajen lodawa, sai na ga gargadi cewa 'This is not from trused supplier', 'No security between your phone and this page', 'It may harm your phone, install anyway?' da dai sauransu. To, bijire wa irin wadannan gargadin na iya sa wa na rasa wayar ne ko kuma yaya abin yake? Allah ya karbi ibadunmu cikin wannan wata mai alfarma, ya kuma kara maka basira, fasaha, balaga, da jajircewa wajen ilmantar da al'uma. - Nura Dauda: muktaroskakm@yahoo.com

Malam Nura sannu da kokari, Allah kuma ya taimaka. Hakika na gamsu da hazakarka wajen neman hanyoyin ci gaba. Da farko dai abin da ake bukata wajen neman kowane nau’in ilmi ne ko tafarkin kwarewa, shi ne ka samu sha’awar abin a zuciyarka, sannan ka nemi hanyar da ta dace wajen samu. Sauran al’amura kuma sai ka bar wa Allah. Daga cikin hanyoyin neman kwarewa, ka san abin da kake nema. Sannan ka lazimci gidajen yanar sadarwar neman bayanai, watau “Search Engine Sites” – irinsu Google, da Bing da kuma Yahoo! Wannan zai taimaka maka gaya wajen kaiwa ga gaci. A karshe, sakonnin gargadi da kake samu a shafin wayarka duk sadda ka zo loda wata manhaja ko masarrafa, alama ce da ke nuna cewa manhajar da kake son lodawa bata da lambar lasisin magini ko kamfanin da ya gina ta. Wannan kuma wani abu ne da ba abin da za ka iya yi wajen hana shi faruwa. Hadarinsa waje daya ne kawai, idan manhajar na dauke da kwayar cutar kwamfuta, watau “Virus”. Don haka ake maka gargadi, amma ba wai cewa idan ka loda manhajar ba za ta yi amfani ba. An tsara wayar ne ta rika lekawa karkashin dukkan manhajar da ake kokarin loda mata, idan babu lambar lasisin magini (watau Certificate Verification kenan), to ta sanar da mai kokarin yin hakan cewa akwai hadari. Allah sa mu dace, amin.

Assalamu alaikum baban sadiq, ya aiki? Allah ya taimaka amin. Don Allah na yi rijista da facebook ne, amma har yanzu bai yi dai-dai ba; sai ya rika ce min wai nasa hotona, kuma sai ya rika budo min wani shafi wanda aka rubuta unibasiti da kwaleji a gaba, kuma sai a sa “skip”. To dan Allah ya zan yi ya bude sosai? Sako daga Ali Auwalu Jibril: aliauwalujibril@yahoo.com

Malam Ali, akwai alamar baka karasa aikin bude wannan shafi naka ba a Dandalin. Abin da za ka yanzu dai shi ne, ka shiga shafin kamar yadda ka saba yi, idan aka budo maka wannan shafin da kake Magana akai, sai ka matsa alamar da tace “Skip”, za a zarce da kai zuwa shafinka, kuma za ka ga wurin da za ka matsa don sanya hotonka. Wannan shafi da kake Magana a kai, ana shiryar da kai ne yadda za ka karasa yin rajistar. Sunan jami’a da kake gani, tambayarka ake yi ko kana son a nemo maka abokanan da kayi jami’a ko kwaleji tare da su? Idan ka matsa alamar “Skip”, za a zarce da kai shafinka. In ya so a baya sai ka nemi abokanai da kanka. Da fatan ka gamsu.

No comments:

Post a Comment