Wednesday, November 2, 2011

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

A yau kuma ga mu dauke da wasikunku da kuka rubuto don neman karin bayani ko kuma gamsuwa da kasidun da ke bayyana a wannan shafi a duk mako. Kafin nan, ina baiwa Malam Kamal Bala hakuri kan saba masa alkawari da nayi. A gafarce ni. Na shagala ne saboda lalurorin rayuwa. Bayan haka, shafin Kimiyya da kere-kere na mika godiyarsa ga dukkan masu karatu. Allah ya bar zumunci, amin.

………………………………………………………………..

Malam na taba karanta wani littafi da ke cewa, miliyoyin shekaru da suka wuce, gobara ce ta ci dazuzzuka da namun daji, ta gangarar da tokar ga tekuna, wanda hakan ya samar da Miniral oil. Ya gaskiyar binciken yake ne? Ka huta lafiya. Naka Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Malam Khaleel, ban taba karanta wani bayani makancin wannan ba, duk iya karatu na. Abin da na tabbatar da shi cikin kasidar da ta gabata kwanakin dai shi ne abin da dukkan masana da masu bincike suka tabbatar, kuma a iya tunani na, ina ganin shi ne abin da ya fi dacewa da hankali. Da fatan ka gamsu.

Salamu alaikum, tambaya ta itace, Malam ya ake neman kudi daga asusun banki ta wayar hannu?. Daga: Aliyu Mukhtar Sa'idu (I.T) Kano 08034332200 /08186624300 Email: aliitpro2020@yahoo.com

Hanyar neman kudi ko bukatar cire kudi daga asusun banki ga mai shi, ya danganci tsarin bankin da mai ajiya ke yin ajiya a cikinsa. Kowane banki na da nashi tsarin. Amma a kimiyyar tsarin sadarwar zamani, wannan wata sabuwar hanya ce da mai ajiya zai iya amfani da ita wajen sanar da bankinsa cewa yana bukatar wasu kudade daga abin da ya ajiye a asusunsa. Zai kuma sanar da su wanda za a biya shi kudin, a wani reshe na bankin da ke wani gari ko birni ko unguwa daban. Wannan tsari, a iya sani na, banki daya ne kadai ke amfani da shi a Nijeriya. Bayan bukatar kudi ma, akwai tsarin da zai rika sanar da kai ko nawa aka cire ko ka cire daga cikin asusunka. Wannan tsarin kusan dukkan bankuna suna da shi. A takaice dai dukkan wadannan tsare-tsare ne da kowane banki yana da irin na shi. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, Baban sadiq don Allah yaya ake bude gidan yanar sadarwar ne, watau "Website"? Kuma bayan an bude akwai wasu kudi da ake biya a kowane wata, ko shekara ne.? Rabiu Isa Ayagi

Malam Rabi'u barka da warhaka, kwana biyu. Bude gidan yanar sadarwa yana bukatar abubuwa masu dama. Da farko dai idan kaine ke son a bude maka, za ka tanadi dukkan bayanan da kake so a zuba a shafin. Wannan shi ake kira "Content". Daga nan sai ka nemi wadanda suke aikin gina gidan yanar sadarwa, ko "Web Designers" a turance, ka biya su, su gina maka. Idan kuma ka iya, sai ka gina da kanka. Bayan haka sai ka nemi masu adana gidajen yanar sadarwa a uwar garke, watau Internet Service Providers ko Hosting Companies, a turance. Su ne za su karbi wannan ginannen gidan yanar sadarwa da aka gina maka, mai dauke da dukkan bayanan da ka bayar aka zuba a ciki, su sanya a cikin kwamfutocinsu, su nemo maka suna ko adireshin gidan yanar, wanda da shi ne duniya za ta rika amfani don sheda gidan yanar. Za ka biya su kudin wannan aiki na nemo maka suna ko adireshi, da yin rajistan adireshin, sannan kuma ka biya su kudin adana maka shafin yanar. Idan kuka gama yarjejeniya, ka biya, a cikin kwamfutocinsu ne wannan gidan yanar sadarwa naka zai rika zama, daga nan za a rika ziyartarsa. Idan shafi ne da ke bukatar a rika sabunta bayanan da ke cikinsa, dole ne ka dauki mai lura da shafin, watau Webmaster kenan, kana biyanshi shi ma. Duk lokacin da wasu sababbin bayanai suka samu, shi za ka ba shi ya rika sanyawa a cikin shafin. Dukkann hidima, kamar yadda ka sani, suna bukatar kudade. Ya danganci yarjejeniyar da ke tsakaninka da kamfanin ko mai lura da shafin. Wasu kan karbi na wata wata, wasu kuma shekara shekara. Da fatan ka gamsu.

Baban Sadik Allah ya taimakeka ya raya mana Sadik. A takaice me yasa idan ka bude Imel za ka ga suna a sama kuma da wasu lambobi akan sunanka. Wai me yasa? Daga R. M. Haidar, Kano

Abin da ke faruwa shi ne, a lokacin da kake budewa ko yin rajistar akwatin wasikar Imel dinka ka bayar da sunanka da na mahaifinka ko lakabinka. Don haka a duk sa'adda ka shigo shafin akwatinka, sai a yi maka "barka da shigowa", tare da ambaton sunanka. Dangane da lambobi da kace a saman suna kuma, ban taba lura da wannan ba. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, suna na Abubakar Ayuba, dalibi a A.B.U. Don Allah ko za ka taimaka mini da kasidar "Tsaga a jikin wata: Mu'ujiza ko yawan shekaru?", tun daga na 1 har na karshe ta abuayuba2000@yahoo.com, kasancewar zai tallafa wa fagen da nake so in yi Digiri na na biyu. Na gode!

Malam Abubakar na tura maka dukkan kasidun ta adireshin da ka bayar, kuma muna maka addu'ar Allah ya taimaka maka, ya agaza maka, ya kuma sa ka dace da dukkan sauran 'yan uwa dalibai baki daya, amin.

Salam Baban Sadik, da fatan kana lafiya, yaya aiki? Dan Allah ina son a yi mana bayani akan "Memory Card" na wayar salula. Shin, yana da tsarin sadarwa ne shi ma kamar Katin SIM ko kuwa? Kuma mene ne a makare a cikinsa? Wasu lokuta sai in ga an ce wannan "126MB" ko "256MB" ko "512MB" ko kuma "1GB," amma kuma duk girmansu daya a ido. Mun gode. Mustafa A. Kazaure.

Malam Mustafa barka da warhaka, wannan tambaya taka tana da ma'ana sosai. Da farko dai, lafazin "Memory Card" shi ne katin ma'adanar bayanai irin na wayar salula, wanda take zuwa da shi ko kuma ake iya saya a sanya mata. Amfaninsa shi ne, baiwa mai wayar damar adana wasu bayanai da suka shafe shi, na sauti, ko na haruffa, ko hotuna, ko kuma bidiyo. Bayan haka, a duk lokacin da mai amfani da wayar salula ya shiga Intanet don saukar da wasu bayanai, idan ma'adanar wayar ta cike, watau Phone Memory, nan take za ta karkatar da akalarta ne zuwa cikin wannan kati don adana bayanan. Idan kuwa katin ya cike, to ba za ta iya adana bayanan ba. Bayan haka, katin SIM ya sha bamban da katin ma'adanar bayanai da ake kira Memory Card. Katin SIM ne ke dauke da tsarin sadarwa na kamfanin wayar da ke bayar da shi. Amma katin ma'adanar bayanai na zuwa ne wayam, babu komai a cikinsa. Dangane da abin da ya shafi mizani, katin ma'adanar bayanai na Memory Card nau'i-nau'i ne. Mai daukan bayanai iya nauyin haruffa miliyan dari da ashirin da shida, watau 126MG, da mai daukan nauyin miliyan dari biyu da hamsin da shiga, watau 256MG, da mai daukan nauyin miliyan dari biyar da goma shabiyu, watau 512MG, sai kuma wanda ke daukan nauyin biliyan daya, watau 1GB. Bayan wadannan, akwai masu daukan nauyin biliyan biyu, da uku, da hudu, da biyar, har zuwa talatin da shida ma. Da fatan ka gamsu.

Salamu alaikum, Baban Sadik, tambaya ta ita ce game da nau'urar daukar yatsun hannu, watau "Finger Print Scanning Machine", yadda ba ta ganin hannaye da wuri bayan an dora, wanda hukumar zabe ta kasa ta bayar don sabinta rijistar masu zabe na 2011, matsalar a ina take ne?. Aliyu Mukhtar Sa'idu (I.T) Kano email: aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 08186624300

Dangane da abin da ya shafi matsalar rashin gano zanen yatsun hannun mutane da wannan na'ura ta yi fama da shi, akwai dalilai da dama. Na farko shi ne, idan ya zama mai yatsun ya kankare su sosai, ta yadda zanen sun goge, ba a iya gano layukan da ke saman yatsunsa – ko dai saboda yawan aiki, ko saboda kanta, ko kuma saboda 'yan dabarun da wasu ke yi wajen boye zanen hannayensu don gudun a kama su idan suka aikata wani ta'addanci da hannunsu. A yanayi irin wannan ba abin mamaki bane idan wannan na'ura ta kasa gano zane tafukan hannun mutum. Domin an dabi'antar da ita ne ta rika nuna wadannan zane da zarar mai yatsun ya dora su a kanta. Muddin ya zama babu zane a saman yatsun, babu yadda za a yi a ga wani abu. Wannan ka'ida ce sananniya, cewa: idan babu kira, to babu abin da zai ci gawayi. Wasu lokuta kuma matsalar na iya samuwa ne daga na'urar; ko wanda ke lura da ita bai iya sarrafa ta ba, ko kuma babu makamashi isasshe (ma'ana batirinta ya yi rauni) da dai sauran matsaloli. Da fatan Malam Aliyu ya gamsu.

Salam bayan gaisuwa, ko zan iya mallakar shafin intanet ta hanyar salula? Ni ne Ilyasu Muhammad Kiru, nagode.

Malam Ilyasu wannan ba abu bane mai yiwuwa, sai dai idan an gina maka gidan yanar sadarwar, sai ka yi amfani da wayar salularka wajen shiga. Amma ba a iya amfani da wayar salula wajen mallakar gidan yanar sadarwa. Idan kana da babbar waya, wacce ke da dabi'u irin na kwamfuta a misali, kana iya bude shafukan Mudawwanai, watau Blog Pages, ko shafin Facebook. Amma bude gidan yanar sadarwa mai zaman kansa, wannan sai ta amfani da kwamfuta. Da fatan na fahimci tambayar da kyau.

Assalamu alaikum warahmatullahi taala wabarakatuh, bayan sallama ta Islama, ina mai matukar jinjina da addu'ar Allah ya kara lafiya da basira ga Baban Sadiq tare da fatan alheri ga filin kimiyya. Don Allah ina son in mallaki littafin nan [WHY ASTRONOMY] na Adnan Abdulhamid a ina zan samu. Wassalamu alaikum, ni ne naku Bala Mohammad Zango T/Wada Kaduna.

To, Malam Bala Muhammad samun wannan littafi dai ba wani abu bane mai wahala, sai in bugun da aka yi ya kare. Idan kaje shagunan sayar da littattafan musulunci, za ka samu in Allah ya yarda. Ni kaina a masallacin Jumu'a na sayi nawa. Kafin daga baya na nemi izinin fassarawa tare da buga littafin daga wajen marubucinsa. Allah sa a dace.

Assalamu alaikum, da fatan kuna lafiya. Don Allah ina son a mini bayanin yadda zan yi in bude turaka a shafin "Facebook" ta cikin waya, don Allah a taimaka a mini bayani. Daga Rumanah Abdullahi Gombe.

Dangane da abin da ya shafi yin rajistar shafi a dandalin abota na Facebook, mai son yin hakan na bukatar wayar salula mai iya mu'amala da shafin Intanet, karama ce ko babba. Amma in da hali a samu babba ko 'yar madaidaiciya. Daga nan sai a shiga shafin da ke http://m.facebook.com ko kuma http://www.facebook.com/mobile. Idan aka shiga, sai a matsa inda aka rubuta "Sign Up". Akwai fam da za a budo maka, sai ka cike, sannan a zarce da kai zuwa shafin da ka bude. Idan aka zo yin rajista, za a bukaci adireshin Imel, da kuma kalmomin iznin shiga, watau Password. Da zarar an sanar da kai cewa ka shafinka ya samu, sai ka yi maza ka zarce zuwa akwatin Imel dinka, akwai sakon Imel da aka aika maka, wanda ke sanar da kai cewa shafin ya samu, sannan ga wasu haruffa nan da ake kira Passcord. Idan ka zo shiga shafin nan gaba, za a bukaci wadannan kalmomi da aka aiko maka cikin jakan Imel dinka. Don haka ka kiyaye, kada ka jefar da su. Bayan haka, da yawa cikin masu karatu sun sha bugo mini waya suna cewa sun samu matsala da shafinsu; sun bude amma kuma sun dawo don shiga shafin an ce musu ba za su iya shiga ba sai sun shigar wasu kalmomi, ko kuma a ce musu "Username or Password not correct." Duk ba komai ke kawo haka ba sai wannan matsalar. Sai a rika kiyayewa. Da fatan an gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadiq, yaya aiki da fatan Allah ya kara taimakawa da hazaka, amin. Bayan haka, a gaskiya ina jin dadin yadda kake kokari wajen wayar mana da kai, kasancewar kowane mako ina tare da wannan filin, na fahimci abubuwa da dama. Sai dai har yanzu na kasa fahimtar yadda zan tura bayani ta hanyar Imel ko karba. Na gode. Abubakar Sani Kaigar Malamai, Karamar Hukumar Danmusa, Jahar katsina.

Malam Abubakar bayani kan yadda ake aikawa ko karban sakonni ta Imel a wayar salula ya sha maimaituwa a wannan shafi. Na farko dai ka ta tabbata wayar tana iya mu'amala da fasahar Intanet. Na biyu kuma ya zama kana da adireshin Imel da ka yi rajista da shi, wanda kuma kake amfani da shi. Na fadi haka ne don ka san cewa lallai ba a iya yin rajistar Imel ta hanyar wayar salula, sai in babbar waya ce mai cikakkiyar dabi'a irin ta kwamfuta – kamar su Blackberry a misali. Daga nan sai ka shiga wannan adireshin, wanda zai kaika inda za ka shigar da adireshin Imel dinka da kalmomin iznin shiga. Wannan adireshi kuwa shi ne: http://mobile.yahoo.com/mail. Da zarar ka shiga za ka ga wasikunka na Imel. A sama za ka ga inda aka rubuta "Compose", ko daga can kasa. Idan ka matsa za a kaika inda za ka rubuta sako, har ka iya aika wa wasu ko wani. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum. Baban sadiq, na ga kasidarka game da "Ayyukan Wayar Salula." Na amfana kwarai da gaske da karatun wadannan bayanai. Allah ya saka maka da alherinsa. Ameen. Da fatan nan gaba za ka yi mana bayani gameda "blogging" Haruna Abubakar Sokoto.

Malam Haruna na gode da wadannan addu'o'i, kuma Allah ya saka maka da alheri. A gaskiya mun dade yin bayanai kan abinda ya shafi bude Mudawwana ko Turaka, watau Blogging. Kasidu guda biyu muka gabatar tun cikin shekarar 2008 in ban mance ba. Don haka idan kana bukata, za ka samu wadannan kasidu a Mudawwanar da muka tanada don zuba kasidun wannan shafi gaba da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Da fatan ka gamsu. Allah sa mu dace, amin.

Baban Sadiq ina da tambaya. Tambayar ita ce, ina son na zama mamba a dandalin "Facebook" da yadda zan samu abokan hira. Daga kaninku Kabeer BK Dandago Kano.08032512767/064918663

Babban Magana, ashe Baban Sadiq ya samu kannai a shafin Kimiyya da Kere-kere, bayan abokai marasa iyaka. To na gode Kabiru. Da farko dai za ka shiga shafin Facebook, ka yi rajista, kamar yadda bayanai suka gabata. Sannan ka shiga shafinka, ka nemi abokai, ko ka gayyaci wadanda ka sani. Da zarar ka samu abokai, sai ka koma shafinka, ka gangara can kasa daga hannun dama, ka matsa alamar da aka rubuta: Chat. Idan ya budo, za ka ga iya adadin abokanka da ke cikin shafukansu, sai ka matsa sunan wanda kake son hira dashi, ka kama hira. Allah sa a dace.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alkairi Allah ya kara hazaka amin. Dan Allah Baban Sadik kowace waya ce take da tsarin GPS? Kuma ya ake shiga? Waya ta Nokia 5130c-2 xpressMusic ce tana da shi? Na gode ni ne Hassan Adamu.

Malam Hassan Adamu ka yi hakuri da jinkirin da nayi wajen amsa maka wannan tambaya. A gaskiya galibin wayoyin salula kan zo da kafar masarrafar GPS, watau Global Positioning System, wanda masarrafa ce ko manhaja mai zaman kanta da ke taimaka wa mai waya gano bigiren da yake. Wannan masarrafa ko manhaja na amfani ne da tauraron dan adam, watau Satellite da ke sararin samaniya. To amma in da matsalar take shi ne, ba kowace waya bace ke iya sadar da mai wayar da wannan tauraron dan adam da ke taimakawa wajen gano bigiren. Kananan wayoyi irin wadda ka zayyana a tambayarka ba su iya wannan aiki, kawai ana sanyawa ne don kwadaitar da mai wayar. Ba ma irin wannan kadai ba, akwai da yawa wadanda suka fi ta girma da karfin iko, duk ba su iya aiwatar da wannan aiki. Wayar Nokia nau'in 5130 XpressMusic ba ta da wannan masarrafa ta GPS. Manyan wayoyin salula kadai ke da shi, irinsu Nokia E52, da Nokia E71, da kuma Nokia E72. Kai a takaice dai, galibin manyan wayoyi ne suke dauke da wannan masarrafa. Da fatan an gamsu.

Assalaamu alaikum, zuwa ga Malam Abdullahi da fatan kana lafiya amin. Suna na Adam a nan Kaduna ina so ka min gajeren bayani game da facebook, ina so na yi rajista, na kasa. Shi ne nake bukatar bayani daga gare ka. Da fatan Allah ya taimake ka amin, na gode.

Malam Adam na amsa tambayoyi makamantan wannan, kuma na tabbata zuwa yanzu ka karanta su. Da fatan an gamsu.

Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce, wani irin sanadari ne a tattare da man gas, watau "Diesel Gas". Me yasa idan ya zuba a kan titi ya kan kayar da motoci idan suka taka birki, sabanin sauran nau'ukan man? Daga: Aliyu Mukhtar Sa'idu (I.T) Kano 08034332200.

Malam Aliyu, man dizil na dauke ne da wasu sinadarai da ke hana kasa shanye shi a duk inda ya zuba. Wadannan sinadarai dai su ne sinadaran da bayanai suka gabata a kansu a cikin kasidar da muka gabatar kan Danyen Mai da Yadda ake Sarrafa Shi. A duk inda wannan mai na dizil ya zuba, wadannan sinadarai kan rike shi, ya like da kasa, ko kwalta, musamman, ya kama naso. Da zarar an haye samansa, sai ya goce da mutum. Ba komai ke kawo haka ba sai dabi'ar santsi da ke dauke cikin wadannan sinadarai. Amma man fetur ba shi da wannan dabi'a. Shi da zarar ya zuba a wuce, saboda rashin nauyinsa, sai kasa da iska su shanye ko narkar da shi. Da fatan ka gamsu.

No comments:

Post a Comment