Aikin wayar salula na gaba shi ne mu'amala da fasahar Bluetooth da Infra-red. Wadannan nau'ukan hanyoyin sadarwa biyu su ma sun kara wa wayar salula shahara ta bangaren aikawa da karban sakonnin hotuna da sauti da kuma rubutattun sakonni. Daga cikin abin da ya kara musu shahara akwai saukin sha'ani, sannan kana iya aikawa da karban sakonnin ta hanyoyin biyu ko da babu katin SIM ko tsarin sadarwa (Network Service) a wayar. Ba mu bukatar fadada bayani kan wadannan hanyoyi, saboda mun gabatar da kasidu wajen uku a kansu a shekaru biyu da suka wuce. Daga cikin aikin wayar salula akwai bayar da damar mu'amala da fasahar gano bigire ta GPS, ko Global Positioning System a turance. Wannan masarrafa ce ta musamman, wacce ke baka damar gano inda kake tsaye, da unguwa da kuma gari ko kasar da kake. Duk inda kake, idan ka budo masarrafar GPS wayarka za ta nuna maka sunan unguwar da kake tsaye. Ba a wayar salula kadai ba, a halin yanzu ana sa na'urar da ke dauke da wannan masarrafa a cikin motocin zamani. Duk inda ka nufa, sai ta rika nuna maka hanya.
Daga cikin manyan ayyukan wayar salula har wa yau, akwai tsarin mu'amala da tashoshin rediyo da talabijin. Wadannan hanyoyi, duk da cewa mun saba da su ta asalin hanyoyinsu na al'ada, samunsu a wayar salula abu ne mai kayatarwa. Kana iya mu'amala da tashoshin talabijin da rediyo ta hanyoyi biyu a wayarka. Ko dai ta hanyar fasahar Intanet – akwai tashoshin talabijin a Intanet da yawa, haka ma tashoshin rediyo, watau Internet Radio Service – ko kuma ta hanyar tashoshin rediyo da talabijin wadanda ke samuwa a inda kake da zama, ko kasar da kake. Tsarin farko yana bukatar tsarin sadarwa ta wayar iska, tunda sai ka shiga Intanet kafin ka kamo tashoshin. Amma tsari na biyu ba ya bukatar tsarin sadarwar wayar iska, domin tsari ne na musamman da aka gina su a jikin wayar, masu zaman kansu. Abin da za ka kiyaye kawai shi ne, ka tabbata kana zaune ne a bigiren da ke da tsarin sadarwar tashar rediyo ko talabijin din da kake son kamawa.
Wayoyin salular zamani na iya ba ka damar mu'amala da na'urar daukan hoto, watau kyamara, da na'ura ko masarrafar daukan sauti, watau rikoda, da kuma na'ura ko masarrafar daukan bidiyo, watau Video Recorder a turance. Wadannan hanyoyi ne masu sauki da wayoyin salula ke zuwa da su don ba ka damar daukan hoto, ko bidiyo, ko kuma sauti. Yaduwar wayar salula masu wadannan hanyoyi sun taimaka wa galibin ma'aikatan yada labarai wajen taskance hirarrakin da suke yi da mutane a halin aikinsu. Ba su kadai ba, hatta ma'aikatan talabijin da masu yada labarai ta hanyar Intanet, sukan yi amfani da masarrafar waya ta bidiyo don daukan hotuna da dora su inda suka dace. Dukkan wadannan hanyoyi guda uku ba sa bukatar tsarin sadarwa ta wayar iska don yin amfani da su. Ko akwai katin SIM a cikin waya, ko babu katin SIM a ciki, duk kana iya amfani da su. Inda za ka bukaci katin SIM ko tsarin sadarwar wayar iska shi ne idan ka tashi aikawa da su ta hanyar Intanet ko tes, ko kuma GPRS.
Sai aikin waya mai muhimmanci na karshe, wadanda take iya baka damar aiwatar da su a sawwake. Wadannan suna samuwa ne ta hanyar masarrafar waya, wadanda musamman aka kirkire su don aiwatar da su. Sun kuma hada da abin wasanni, watau Games, da masarrafar lissafi, da masarrafar duba lokaci, watau agogo kenan, da masarrafar rubutu ko mu'amala da bayanai, watau Word Processor. Bayan wadannan masarrafai, akwai manhajar tunatarwa, watau Reminder, da masarrafar kalanda, wacce ke sawwake maka tsarin tafiyar da rayuwarka ta hanyoyi da dama. A cikin wasu nau'ukan wayoyin Smartphones, akan bai wa kwararru daman ginawa da tsara sababbin manhajojin waya, watau Mobile Phone Programming Tools. Akwai makamar gina manhajojin wayar salula masu babbar manhajar S60 da yawa da ake amfani da su a halin yanzu. Wasu daga cikinsu sun hada da Python Programming for S60, da C++ Programming for S60, sai kuma makamar gina masarrafai na Java, duk ana amfani da su wajen wannan aiki. Wannan bangare ne da ya shafi kwararru kan harkar gina manhajar kwamfuta da wayar salula na zamani, kuma hanya ce mai sauki da ake amfani da ita wajen samar da sababbin manhajoji ko masarrafai na musamman, cikin harshen da kake so, sannan cikin tsari da yanayin da kake so. Amma sai dai kuma, wannan aiki ne na kwararru, kamar yadda bayani ya gabata a sama.
Kammalawa
Wadannan, a takaice, su ne shahararrun ayyukan wayar salula. Sauran kuma sun danganci zamani ne, da kuma kwarewar mai amfani da wayar wajen sarrafata ta yadda yake so ko bukata. A makonnin da ke tafe, za mu yi bayani kan alakar wayar salula ne da sauran kayayyakin sadarwa. A ci gaba da kasance tare da mu.
blah blah
ReplyDelete