Cikin makon da ya gabata ne shuguban hukumar da ke lura da samar da tauraron dan adam na kasa mai suna NigComSat Ltd watau Farfesa Timasaniyu Ahmed-Rufai, ya sheda wa manema labaru cewa a karshen shekarar 2011 dai za a kaddamar da sabon tauraron dan adam da aka sake kerawa, bayan rushewar na farko a shekarar 2009. Wannan tabbaci da Farfesan ya bayar ya biyo bayan gwajin da aka yi wa sabon tauraron ne mai suna NigComSat-1R, wanda kuma shi ne zai maye gurbin tauraron farko (NigComSat-1) da ya samu matsala a sararin samaniya bayan dan kankanin lokaci da harba shi.
Farfesa Timasaniyu Ahmed-Rufai ya ce, da zarar an kaddamar da wannan sabon tauraro na NigComSat-1R, hukumarsa ce za ta dauki nauyin lura da shi, ta hanyar manyan Injiniyoyi ‘yan Najeriya masu kwarewa ta musamman kan wannan tauraro da ma fannin baki daya. Ya kara da cewa, kamfanin Great Wall Industry, watau kamfanin da aka dora masa alhakin sake kera wannan sabon tauraron dan adam, ya gudanar da gwaji na musamman, inda jami’an hukumar NigComSat, da Ministan Kudi, da kuma Ministan Kimiyya da Kere-kere suka halarta a kasar Sin. Wannan gwaji dai an yi shi ne a wani kirkirarren yanayi mai dauke da dukkan yanayin da tauraron dan adam ke iya riskarsa, tare da jure shi a tafarkinsa na shawagi a sararin samaniya.
Samun nasarar wannan gwaji a irin wannan kirkirarren yanayi, inji Farfesan, shi ke nuna cewa lallai wannan sabon tauraro na NigComSat-1R zai iya jure yanayin da ke can sararin samaniya, ba tare da samun wata matsala ba, sabanin abin da ya faru da na baya. Kuma wannan shi ne gwajin da daga shi sai kaddamarwa. A nasa bangaren kuma, Ministan Kudi na kasa ya lallabi wannan kamfani na Great Wall Industry da yayi kokarin ganin an kaddamar da wannan tauraron dan adam tsakanin watan Yuli zuwa Satumba, in da hali, sabanin yadda yake niyyar kaddamarwa tsakanin watannin Satumba zuwa Disambar shekarar. A karshe dai, Farfesa Timasaniyu ya sheda cewa kamfanin Great Wall Industry zai kera wasu taurarin dan adam guda biyu: NigComSat-2 da NigComSat-3, wadanda za su rika ci gaba da aiki da zarar wannan ya samu matsala. Ya kuma sheda wa ‘yan Najeriya cewa su sha kuruminsu, da zarar wannan tauraro ya fara aiki, tsarin sadarwar tarho da Intanet da hanyoyin yada bayanai da samar da su za su inganta a kasa baki daya.
Wannan tabbaci da Farfesa Timasaniyu ya bayar dai ya kamata a yi masa kaidi, musamman tabbacinsa na cewa da zarar NigComSat-1R ya soma aiki za a samu ingantacciyar hanyar sadarwa a kasa baki daya. Ba ma bangaren samar da bayanai kadai ba, ya taba bayar da tabbacin cewa hatta wadannan mashinan daukan sunaye da taskance bayanai (MRI Machines) da Hukumar Zabe ta Kasa take hakilon shigowa da su don su taimaka wajen ingancin zabe a kasa baki daya, muna iya kera su, tare da lura da bayanan da suke taskancewa, ba tare da wata matsala ba.
Hakika a bayyane yake cewa, tsarin samar da bayanai da yada su a Najeriya, idan aka kwatanta arziki da yawan jama’ar da ke wannan kasa, da kuma yawan kwararru da muke da su a fannonin da suka shafi wannan lamari, a gaskiya za mu ga cewa har yanzu a baya muke. Ko kadan ba ma tantama kan cewa a Najeriya akwai kwararru da suka kware, wadanda kuma suna iya zuwa kowace kasa ce a duniya su taka rawa kan fannoni da dama, amma irin yanayin siyasa da yadda ‘yan siyasa ke tafiyar da tsarin ci gaban tattalin arzikin kasar nan shi ne abin da ke ba da tsoro, duk sa’adda wani tabbaci na ci gaba a kowane fanni ne ya shiga kunnen dan Najeriya. Kamar yadda wannan shafi ya tabbatar a kasidar Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-kere, galibin matsalolin da ke hana ruwa gudu a kasar nan ba na rashin karatu bane, a a, na rashin tsari ne, da kasa barin al’amura su tafi yadda aka tsara su.
A nan kasar babu ci gaba a fannin tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, watau Continuity in Economic Policies. Da zarar wani shugaba ya zo, sai ya dubi abin da wanda ya gabace shi yayi, nan take sai ya rusa tsohon tsarin da ya tarar, sannan ya kafa kwamitin shirme, ko na bincike kan “badakalar” da aka yi a baya. Wannan na daga cikin manyan dalilan da suka kasa ciyar da kasar nan gaba. Shugabanci a Najeriya kusan daya yake da kasuwanci; duk wanda ya shiga, ribar abin da ya kashe yake nema, bai wai ciyar da al’umma gaba ba. Misali, idan muka dubi tsarin samar da wutar lantarki a kasa baki daya, za mu ga cewa duk shugaban kasar da ya zo sai ya kawo nasa tsarin, kuma duk tsarin da ka duba, sai ka ga kamar shi ne yafi dacewa, amma da zarar tafiya ta yi nisa, sai ka ji shiru, wai Malam ya ci shirwa. Zuwan gwamnati mai ci yanzu an kawo tsare-tsare sun fi uku, daga wanda tsohon shugaban kasa Obansanjo ya kafa, zuwa wanda Allah jikan rai ‘Yar adua ya assasa, kawo ga lokacin da shugaba mai ci a yanzu ya tsara; inda a farko ya mayar hukumar samar da wutar lantarki zuwa ofishinsa, “don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai”. A farkon wannan mako nake sake karanta wani sabon tsari kuma da shugaba mai ci yanzu yake kokarin kawowa, shi ne irin tsarin samar da wutar lantarki irin na kasar Burazil. Ire-iren wadannan kwam-gaba-kwam-baya na cikin manyan matsalolin kasar nan.
Dukkan wadannan misalai na kawo su ne don in nuna mana yadda muke wa kanmu ko kasarmu kisan mummuke, da sunan neman hanyoyin ci gaba. In kuwa haka ne, samar da ingantacciyar hanyar yada bayanai da samar da su ta hanyar tauraron dan adam da muke hasashen assasawa ta hanyar NigComSat-1R da ke tafe, yana fuskantar hadari mai girma, sai mun sake lale. Domin tsari ne da ke bukatar wutar lantarki mara dauke daukewa, da kyakkyawar tsarin aiki da gudanarwa, da kuma samar da kudaden shiga babu kakkautawa. A karshe kuma, yana bukatar a ci gaba da tafiyar da shi babu yankewa. Idan har Allah ya sa muka samo masa wutar lantarki mara yankewa (ta hanyar babban tsarin samar da wutar lantarki ta kasa ko ta hanyar janareto), muka samar da tsarin gudanarwa mai kyau (ta hanyar hana cin hanci da rashawa, da cuwa-cuwa), muka samar masa da kudaden shiga babu yankewa (ta hanyar yin kasafin kudin kasa na musamman, ko ta hanyar tallafi daga kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya ko kasashen waje), wani tabbaci muke da shi cewa wannan tsari zai ci gaba da tabbatuwa a matsayin tsarin kasa na tilas, wanda dole ne kowane shugaba ya tafiyar da shi?
Wadannan al’amura guda hudu suna da matukar muhimmanci wannan hukuma ta yi la’akari da su. Domin akwai tsare-tsare masu matukar muhimmanci da aka taba assasawa, wadanda dan Najeriya yafi bukatarsu a rayuwarsa, amma a karshe wasu shugabannin sun rusa su, sun kawo nasu, wanda ya dace da manufa da soye-soyen zuciyarsu. Wannan kasa na fuskantar kalubale mai girma a wannan fanni na samar da bayanai da sarrafa su, musamman idan muka yi la’akari da yawanmu, da kuma yadda hakan zai taimaka wajen tafiyar da mulki cikin sauki. To amma, muna bukatar sadaukar da kai fiye da komai, da yi wa kanmu karatun ta-natsu. Da haka sai mu cinma maunfarmu, tare da zama abin koyi a duniya baki daya. Allah ya daukaka Najeriya!
Ana Kama Tashoshin Sashen Hausa Na DW Radio Da BBC Ta Tauraron NileSat
Ga masu sha’awar sauraron tashoshin BBC Hausa da Muryar Jamus na rediyo, watau Deustwelle Hausa ko DW Hausa, yanzu nesa ta zo kusa. Cikin shekarar da ta gabata ne wadannan tashoshi suka hau tauraron adan adam mai suna NileSat, inda duk mai kallon tashoshin tauraron dan adam ta wannan tauraro na NileSat zai iya kamo su, ya kuma saurari shirye-shiryensu cikin lokutan da suke yadawa, garau radau, ba tare da wata matsala ba.
Idan kana da tauraron adan adam na NileSat wanda kake kallo kyauta ba tare da ka biya ko ahu ba, kana iya samun tashar shashen Hausa na BBC a TP 11.843, a bigiren Horizontal, wacce ke dauke a Symbol Rate (SR): 27.500. Da zarar ka shigar da wadannan kalmomin nema, za ka samo tashar ba tare da bata lokaci ba. Bayan haka, muddin kana iya kama sashen BBC World na harshen turanci a bangaren talabijin, to, kana da wannan tasha ta Hausa. Idan kana son ganewa, sai ka je bangaren tashoshin rediyo – ka matsa maballar da aka rubuta TV/Radio a jikin rimot dinka, za a zarce da kai tashoshin rediyo nan take. Sai ka budo tashoshin, ka nemi wannan tasha. Sunan tashar dai shi ne BBC Hausa Radio. Ga wadanda ke amfani da karamar dish ta NileSat mai girman 1.8, samun wannan tasha zai musu wahala idan a birnin Abuja suke, sai sun sanya babbar dish mai girman 2.4. Amma idan a Arewacin Najeriya suke, za su samu. Saboda an fi samun yanayi mai kyau a can.
Ga masu neman tashar DW Hausa Radio kuma, sai su neme te a TP 11.900, a bigiren Vertical, a Symbol Rate (SR): 27.500, kuma sunan tashar shi ne DW2. Da zarar an shigar da bayanan nema za a samu. Kuma idan ma kana iya kama tashar DW ta Turanci ko DW Arabic, to, ina kyautata zaton za a samu wannan tasha, ba sai an bincika ba. Bayan haka, duk wanda ya dubi tashoshinsa na rediyo bai samu ba, to, yana iya kiran masu sanya tauraron dan adam su binciko masa, in har ba zai iya bincikowa da kansa ba.
A tashoshin tauraron dan adam na Multichoice kuwa, watau DSTV, wannan tasha ta BBC Hausa na nan tun fil azal. Idan kana amfani da DSTV amma baka taba sanin wannan ba, ka je bangaren tashoshin rediyo daga rimot dinka (ka matsa “Shift”, ka rike, da zarar koren haske ya bayyana, sai ka saki ka matsa maballin “TV” nan take). Sai ka nemi tasha mai suna BBC 2, ko BBC 3, za ka saurari shirye-shiryensu. Idan ma tashar sashen turanci kake so, ita ce BBC 1. Allah sa a dace.
No comments:
Post a Comment