Assalaamu Alaikum, barka da warhaka Baban Sadik. Wai shin, mene ne tasiri da illan gurbatattan mai (crude oil) din da ke malala a tekun Mexico (Gulf of Mexico) da ke Amurka ne? Kuma ko wannan man da ake yadewa a saman tekun zai yi amfani in an sarrafa shi, ko kuma ya lalace kenan har abada? - Uncle Bash, Jimeta, Yola: 07037133338.
Malam Bash barka da warhaka kai ma, kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci, kuma tun sadda ka aiko nake ta kokarin tanadin gabatar da gamsasshen jawabi a sigar kasida ko makala mai dan tsawo. Domin hakan ne zai taimaka wa mai karatu fahimtar yadda lamarin yake. Don haka yanzu ma ba amsa zan baka ba, sai dai mu dan dada hakuri, akwai kasidu na tanada da zan yi nazari don fitar da makala mai kyau, mai dan tsawo kuma mai fa’idantarwa sama da jawabin da watakila zan bayar a dan kankanin shafin nan, in hakan na yi. A min hakuri zuwa bayan hutun Salla. Na gode.
Sallama, da fatan alheri ga Baban Sadik. Shin, ko zan iya sanin shiyyar da wanda ya aiko min da sakon Imel yake? - Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano: 07069191677
Sanin shiyyar da aka aiko maka da sakon Imel abu ne mai wahala, musamman idan ba kwararre bane kai a fannin hada alaka a tsakanin kwamfuta da yadda tsarin sadarwa ke aukuwa a tsakaninsu. Sannan kuma ya danganci irin manhajar Imel din da abokin huldarka ko wanda ya aiko maka da sakon yake amfani da ita wajen yin hakan. Da farko dai, muddin kana son sanin daga ina aka aiko maka sakon Imel, to dole ne ka san tsurar adireshin kwamfutar da aka yi amfani da ita, watau “IP Address” kenan - gundarin adireshin kwamfutar nake nufi. Kowace kwamfuta na dauke ne da adireshi wanda yake a jerin lambobi (misali: 235.75.4.9.0). Da wadannan lambobi ne take amfani wajen aika sako ga wata kwamfuta ‘yar uwarta; a giza-gizan sadarwa ne ko a zangon sadarwa tsakanin gida ko ofis ko wata jiha ta musamman. Idan daga Intanet aka aiko maka da sakon, to dole ne ka san wadannan lambobi, sai ka sansu sannan za ka iya sanin a inda kwamfutar take. Domin dukkan kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwa a Intanet suna da adireshin da ke nuna daga kasar da suke, kamar yadda ka san kowace kasa tana da tsarin adireshinta na musamman. Idan ba wadannan lambobi ka gani ba, kuma har ka iya tacewa tare da fahimtar kasar da ake danganta adireshin da ita ba, to ba ka iya sanin haka. Kuma ko da ma ka san kasar, ba lallai bane ya zama wanda ya aiko da sakon a kasar yake. Misali, akwai kamfanoni masu adana shafukan yanar gizo ko bayar da damar mu’amala da fasahar Intanet ta amfani da tauraron dan Adam, ire-iren wadannan kamfanoni a kasashen Turai suke, amma za ka samu galibin kamfanoninmu a nan na amfani da adireshin Nijeria ne (na gidajen yanar sadarwarsu) amma kwamfutocin da ke dauke da gidajen yanar sadarwar na wasu kasashe ne daban. A irin wannan yanayin kuwa, sai dai kayi ta kirdado, amma ba wai ka san hakikanin inda aka aiko maka ba. Da fatan an gamsu.
Salam, Malam ina son in samu Karin bayani kan yanayin samuwar ruwan sama a duniya, ta yadda za ka ga wani sashi yana samun ruwa ne watanni hudu a shekara, wani kuma fiye ko kasa da wata hudun. – Khaleel Nasir Kuriwa Kiru, Kano.
Wannan tambaya ce mai bukatar dogon bincke, ba wai Karin bayani ba. Ana yin Karin bayani ne kan abin da aka taba tattaunawa a kai, amma ba a gamsu sosai ba. Sai dai lokaci na tafe in Allah Ya so, za mu yi dogon bayani mai gamsarwa kan hakan. Ire-iren wadannan tambayoyi suna da amsa na kusa ne, da kuma wadanda ke nesa. Amsoshin nesa su ne wadanda ke da goyon bayan hujjojin binciken kimiyya. Na kusa kuma wadanda a al’ada kawai aka sansu, kuma ake iya bayaninsu. Duk da cewa wasu daga cikinsu na dacewa da binciken kimiyya, dogaro a kansu kadai ba zai taba wadatarwa ba, musamman a shafi makamancin wannan. A fannin kimiyya kuwa babu abin da yafi amsoshin nesa amfani. Allah sa mu dace.
Jinjina gareka Baban Sadik, zan so don Allah ka aika min da bayanin da kayi a kan yadda ake bude “Blog” a yanar gizo. – Alhaji A. Palladan, Zaria: ahmedpalladan@yahoo.com
Ina godiya Alhaji, kuma Allah saka da alheri, da fatan an yi sallah lafiya. Sai a dunguma zuwa jakar Imel, tuni na tura. In da akwai Karin bayani da Alhaji ke nema bayan kasidar, kasancewar na jima da rubuta ta, a shirye nake in taimaka. Na gode.
To, Malam Abdullahi wannan bau’in wayar “Blackberry” da ka bamu bayaninta a makonnin da suka gabata, shin ta shigo Nijeriya kuwa? In kuma ta shigo, to, nawa ne farashinta? - Salisu Nagaidan Jama’are: 08063461480
Malam Salisu lallai wannan waya ta shigo kasar nan tuni, har ta fara zama jiki ma. Dangane da farashinta kuwa, sai in ce a je shaguna ko kantinan sayar da wayoyin salula da ke manyan biranen kasar nan, ko kuma aje ofishin kamfanin MTN, ko Zain, ko Etisalat, ko kuma Glo, duk suna sayar da ita. Amma mu a shafin Kimiyya da Kere-kere ba mu sayar da wayoyin salula ko kwamfuta, sai yin bayani kan yadda ake kera su ko ake amfanuwa da su. Wannan bayani na da muhimmanci in kara yinsa a nan, domin da yawa cikin masu karatu kan bugo waya duk sadda suka ga hoton wata kwamfuta ko wayar salula ko wata na’urar sadarwa a shafin nan, suna neman farashinta ko inda za su je su saya. Muna sanya hotunan ne don a gani, kuma hakan na taimaka wa mai karatu wajen fahimtar nau’in abin da ake masa bayani ne. Sai a rika lura. Mun gode.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, don Allah ina son ka taimake ni da amsar wannan tambaya: wai shin me ke haifar da canje-canje a harsuna ne? Da fatan an sha ruwa lafiya. - Daga Aliyu M. Chiso, dalibi a Jami’ar Danfodio, Sokoto: 08097323092
Malam Aliyu wannan tambaya taka akwai sarkakiya a tare da ita, dangane da abin da muke karantarwa ko yin bayani kansu a wannan shafi. Shin kana nufin canje-canjen harshe a lafazin zance ne, ko kuma a tsarin halitta? Wannan tambaya ce da ke da alaka ta kut-da-kut da fannin harsuna da zamantakewa. Idan kuma ni ne ban fahimci abin da kake nufi ba a tambayar, to don Allah a kara min bayani filla-filla. Na gode.
Assalaamu Alaikum, don Allah ina son bayani a kan na’urar “Fax”. - H. M. Kongolam: 08026817542
“Fax” na’ura ce mai taimakawa wajen sadar da bayanan da ta kwafo daga shafukan takardun da aka ciyar da ita – daga tashar aikawa zuwa tashar karba. Na’urar “Fax” na cikin dadaddun kayayyakin sadarwa na zamani da aka fara amfani da su shekaru kusan hamsin da suka gabata. Na’urorin “Fax” na asali suna amfani ne da tsarin aikawa da karbar sakonni ta siginar lantarki nau’in “Analogue”, kuma sukan dauki tsawon mintuna uku zuwa shida kafin su aika da sakon shafin fallen takarda daya. Wadannan su ake kira “Analogue Fax Machines”. Sai na zamani, masu amfani da tsarin tankwasa kaurin bayanai ta hanyar lantarki na zamani, watau “Digital Compression Methods”. Su kuma sukan dauki tsakanin dakika goma ne zuwa ashirin wajen aikawa da shafin fallen takarda guda daya. Idan aka tashi aikawa da sakon fax, za a dauki shafin takarda ne, sai a dora shafin da ke dauke da bayanan da ake son aikawa a saman wannan na’ura, a matsa ko shigar da lambar na’urar da ke son karbar sakon, sannan a matsa tambarin da zai bata umarnin aikawa da sakon. Daga nan sai wannan na’ura kuma ta dauki hoton shafin da ke dauke da bayanan a sifar hasken lantarki, sannan ta aika wa ‘yar uwarta da ke daya bangaren. Da zarar ta gama aikawa, sai ta fitar da sako cewa “sakon da aka ce in aika wa wane da wane, na aika musu shafi kaza, a lokaci kaza, a kuma rana kaza.” Kowace na’urar Fax na da lambar tarho (ko lambar fax – watau “Fax Number”), wanda da shi ne ake amfani wajen aika mata da sako. A halin yanzu ma ana iya aikawa da sakon fax ta hanyar kwamfuta, ba sai ta hanyar na’urar Fax kadai ba. Domin kwamfuta na dauke da dukkan masarrafan da ke taimakawa wajen yin hakan. Da fatan ka gamsu.
Barka da shan ruwa Abdullahi, wani taimako nake so a yi mini, wato ma'anar na'ura mai kwakwalwa da kuma muhimmancinta ga al'umma. Na gode. - Shamsu Isiyaku: shamoo04@yahoo.com
Malam Shamsu, “Na’ura mai kwakwalwa” dai ita ce kwamfuta da muke amfani da ita. Na’ura ce da ke iya karbar bayanai, ta adana, ta mika idan an tashi bukata, tare da sarrafa su a yanayi daban-daban. Wannan a takaice shi ne ma’anan na’ura mai kwakwalwa. Daga cikin amfaninta ga al’umma akwai sawwake ayyuka, da sawwake lissafi, da sawwake rayuwa, da adana bayanai masu dimbin yawa cikin dan Kankanin muhalli da farashi, da kuma taimakawa wajen samar da aikin yi a rayuwa. Da fatan ka gamsu.
Cikin yardar Allah, Allah ya hada ni da kai ta hanyar jaridar Daily Trust, sai na ga AMINIYA. Samunka sai ya jefa ni a wani sabon yanayi, na ga ai na tsinci dami a kale; kila ni ma na zama "Lu'u Lu'u a cikin juji" inji wani fasihee. A nan nake mika kokon barata ta neman shawarar yadda zan fadada fahimtata a Intanet ta hanyar aiki da wayar salula da taimakamin da guraben da suka kamata na rika kai ziyara. Daga karshe ina da tambaya, sau dayawa idan nazo sauke wata manhaja ko wajen lodawa, sai na ga gargadi cewa 'This is not from trused supplier', 'No security between your phone and this page', 'It may harm your phone, install anyway?' da dai sauransu. To, bijire wa irin wadannan gargadin na iya sa wa na rasa wayar ne ko kuma yaya abin yake? Allah ya karbi ibadunmu cikin wannan wata mai alfarma, ya kuma kara maka basira, fasaha, balaga, da jajircewa wajen ilmantar da al'uma. - Nura Dauda: muktaroskakm@yahoo.com
Malam Nura sannu da kokari, Allah kuma ya taimaka. Hakika na gamsu da hazakarka wajen neman hanyoyin ci gaba. Da farko dai abin da ake bukata wajen neman kowane nau’in ilmi ne ko tafarkin kwarewa, shi ne ka samu sha’awar abin a zuciyarka, sannan ka nemi hanyar da ta dace wajen samu. Sauran al’amura kuma sai ka bar wa Allah. Daga cikin hanyoyin neman kwarewa, ka san abin da kake nema. Sannan ka lazimci gidajen yanar sadarwar neman bayanai, watau “Search Engine Sites” – irinsu Google, da Bing da kuma Yahoo! Wannan zai taimaka maka gaya wajen kaiwa ga gaci. A karshe, sakonnin gargadi da kake samu a shafin wayarka duk sadda ka zo loda wata manhaja ko masarrafa, alama ce da ke nuna cewa manhajar da kake son lodawa bata da lambar lasisin magini ko kamfanin da ya gina ta. Wannan kuma wani abu ne da ba abin da za ka iya yi wajen hana shi faruwa. Hadarinsa waje daya ne kawai, idan manhajar na dauke da kwayar cutar kwamfuta, watau “Virus”. Don haka ake maka gargadi, amma ba wai cewa idan ka loda manhajar ba za ta yi amfani ba. An tsara wayar ne ta rika lekawa karkashin dukkan manhajar da ake kokarin loda mata, idan babu lambar lasisin magini (watau Certificate Verification kenan), to ta sanar da mai kokarin yin hakan cewa akwai hadari. Allah sa mu dace, amin.
Assalamu alaikum baban sadiq, ya aiki? Allah ya taimaka amin. Don Allah na yi rijista da facebook ne, amma har yanzu bai yi dai-dai ba; sai ya rika ce min wai nasa hotona, kuma sai ya rika budo min wani shafi wanda aka rubuta unibasiti da kwaleji a gaba, kuma sai a sa “skip”. To dan Allah ya zan yi ya bude sosai? Sako daga Ali Auwalu Jibril: aliauwalujibril@yahoo.com
Malam Ali, akwai alamar baka karasa aikin bude wannan shafi naka ba a Dandalin. Abin da za ka yanzu dai shi ne, ka shiga shafin kamar yadda ka saba yi, idan aka budo maka wannan shafin da kake Magana akai, sai ka matsa alamar da tace “Skip”, za a zarce da kai zuwa shafinka, kuma za ka ga wurin da za ka matsa don sanya hotonka. Wannan shafi da kake Magana a kai, ana shiryar da kai ne yadda za ka karasa yin rajistar. Sunan jami’a da kake gani, tambayarka ake yi ko kana son a nemo maka abokanan da kayi jami’a ko kwaleji tare da su? Idan ka matsa alamar “Skip”, za a zarce da kai shafinka. In ya so a baya sai ka nemi abokanai da kanka. Da fatan ka gamsu.
Wace hanya ce zan iya yin (Search Engine) na kaina
ReplyDelete