Wednesday, November 2, 2011

Yadda Shafin “Wikileaks” Ya Canza Tsarin Samar da Labarai a Intanet

Mabudin Kunnuwa

Fasahar Intanet na daya daga cikin hanyoyin yada labarai da neman bayanai tclip_image002a yanayi da tsari masu ban al’ajabi a duniya. Kasa da shekaru arba’in da kirkirar wannan fasaha, tasirinta wajen gamewa a duniya ya sha karfin hanyoyin sadarwar da aka kirkira shekaru kusan hamsin kafin bayyanarta. Hakan ba wani abin mamaki bane, musamman idan mai karatu ya yi la’akari da yadda wannan fasahar sadarwa ke habbaka kamar wutar daji a dukkan rana da lokaci. Duk wanda yake nazarin halin ci gaban hanyoyin watsa labarai a duniya ya san haka. Daga cikin hanyoyi masu tasiri wajen gamewa da wannan fasaha ta Intanet take takama da su, akwai hanyar samarwa ko yada labarai, wadda ta shafi kamfanonin jaridu da mujallu da talabijin da kuma na rediyo da ke aikinsu ta hanyar giza-gizan sadarwa ta Intanet. Daga cikin kamfanonin yada labarari ta wannan hanya ne aka samu wani sabon shafin yada labarai da ya bayyana shekaru hudu da suka wuce mai suna WikiLeaks (www.wikileaks.org), wanda aikinsa a farko shi ne samar da labarai ko boyayyun bayanai na sirri da suka shafi gwamnatoci ko kamfanoni masu zaman kansu a duniya; irin labaran da ba a samunsu ta kafofin watsa labarai na yau da kullum.

Wannan sabuwar hanyar samar da bayanai ko labarai da shafin WikiLeaks ya kirkiro na cikin abin da ya dauki hankalin duniya cikin wannan shekara musamman, wanda kuma har yanzu tasirinsa na kan gamewa – daga kan bayanan sirrin da suka shafi yakin Afghanistan, da na Iraki, da kuma uwa uba, bayanan sirrin da shafin ya hankado kan kundin sadarwar diflomasiyya tsakanin kasar Amurka da sauran kasashen da take alaka da su. Wannan badakala ca ta jefa siyasar duniya cikin rudani musamman cikin watan da ya gabata, domin dukkan bayanan sirrin da shafin ya hankado sun shafi kusan kowane nahiyar duniya baki daya, ciki har da kasarmu Najeriya. Wannan dambarwa ne ya fito da shafin WikiLeaks a idon duniya, tare da sabon tsarin samar da bayanai da yake amfani da su.

Za mu yi nazari kan abubuwa biyu dangane da wannan shafin na WikiLeaks cikin wannan mako da makon da ke bi masa. Abu na farko shi ne tsarin samar da bayanai da wannan shafi ke amfani da shi. Shin, muhallin Intanet zai ci gaba da daukan wannan sabon tsari da salo irin na WikiLeaks, har ma wasu daban su sake fitowa masu manufa da tsari irin nasu don ci gaba da habaka wannan sabuwar hanya, ko kuwa daga kansu shikenan, sanadiyyar irin kiraye-kiraye da ‘yan siyasar kasar Amurka ke yi cewa a kama shugaban wannan shafi, ko ma a kashe shi – don ya tona wa kasar Amurka asiri da ma sauran kasashen da wannan badakala ta shafa? Abu na biyu kuma shi ne, za mu yi nazari kan tasirin wannan tsari wajen samar da bayanai na musamman a Intanet; shin, mai neman bayanai musamman na sirri a Intanet, zai iya dogaro da ire-iren wadannan kafafe na shafin WikiLeaks, ko a a? Amma kafin nan, ga ‘yar gajeriyar mukaddima kan asali da masu tafiyar da wannan shafi na WikiLeaks.

WikiLeaks: Daga Ina Kake?

An samar da shafin WikiLeaks ne a shekarar 2006, don samar da labarai ko bayanai na musamman, clip_image004galibi na sirri, wadanda kuma suka shafi siyasa, da diflomasiyya, da kasuwanci, don ilmantar da jama’a kan wani abin da gwamnatoci ke boye musu dangane da yadda ake tafiyar da al’amuran mulkin kasarsu. Daraktan wannan shafi shi ne Julian Assange, wani matashi ne dan shekara 39, dan kasar Ostiraliya, mai ra’ayin ‘yanta Fasahar Intanet daga dukkan wata kaidi da gwamnatoci ke sanyawa na doka, masu hana yada bayanai don a amfana da su; kowane irin bayani ne kuwa. Bayan shi, akwai sauran ma’aikata da suka hada da Phillip Adams, da Wang Dan, da C. J. Hinke, da Ben Laurie, da Tashi Namgyal Khamsitsang, da Xiao Qiang, da Chico Whitaker, sai kuma Wang Youcai, wadanda masana kan fannin lissafi, da kwamfuta, kuma sun fito ne daga kasashen Sin, da Taiwan, da Afirka ta Kudu, da Turai. Babbar manufar wannan shafi dai ita ce taimakawa wajen tona asirin gurbatattun gwamnatoci masu ci da gumin jama’arsu, ta hanyar hankado bayanan sirri da suka shafi yadda suke tafiyar da al’amuran mulki a kan talakawansu.

Da farko dai shafin WikiLeaks na dauke ne da masarrafa wacce za ka shiga, ka yi rajistar sunanka, idan kana da bayanai na sirri, sai ka aika musu. Bayan haka, dukkan abin da jama’a suka aiko na bayanai, kana iya karantawa, har ma ka budo, tare da canza wasu bayanai wadanda kake ganin ba haka suke ba. Dukkan wani shafi a Intanet mai dauke da wannan masarrafa tare da wannan tsarin sarrafa bayanai, shi ake kira “Wiki Site”, kuma wacce tafi kowanne shahara cikin ire-iren wadannan shafuka dai ita ce shafin Wikipedia (www.wikipedia.org), wacce taska ce ta ilmi mai zaman kanta, wanda masu karatu ko ziyara ke ginawa da kansu. To, da haka wannan shafi na WikiLeaks ya faro. To amma daga baya sai ya canza salo, ya zama sai dai ka karanta bayanan sirrin da aka zuba a shafin kadai, amma ba za ka iya canza wani bayani ba. A karshe kuma sai abin ya zama cewa masu shafin ne ke zuwa su yi farautar bayanan sirri da kwarewarsu (dukkansu masana harkar kwamfuta ne na kololuwa), don baiwa mutane daman karantawa a shafin.

Masu wannan shafi dai na dogaro ne kan tallafin da jama’a ke taimaka musu da shi ta shafin, don gudanar da ayyukan da suke bukata baki daya. Duk cikinsu babu wadanda ake biya ko kwabo, domin aiki ne na kashin kai, kuma kusan kowanne daga cikinsu na da aikin yi. Bayan wadannan shugabanni da sunayensu suka gabata a sama, akwai kuma masu agaza musu wajen sama da mutum 80 a warwatse a sauran kasashen duniya, kuma dukkansu kwararru ne kan tsarin sadarwa ta kwamfuta. Kuma duk ta hanyar Imel suke aiwatar da galibin ayyuka a tsakaninsu. Shugaban wannan shafi dai ya bar kasarsa ta asali, saboda tuhuma da hukuma ke masa. Daga nan ya zarce kasar Suwidin, wacce kasa ke mai tsauraran dokokin da ke hana bincike kan asalin da kafafen yada labarai ke dogaro da su wajen samo labaransu. Lokacin da shafin WikiLeaks ya fara tasiri a duniya, sai hukumar kasar ta fara tuhumarsa da laifin tirsasa wa wasu mata guda biyu da tace ya yi don saduwa da su. Wannan tasa ya baro kasar zuwa kasar Ingila a boye. A halin yanzu dai hukumar kasar Burtaniya ta kama shugaban wannan shafi na WikiLeaks, watau Julian Assange, inda tace ta samu wasikar sammaci ne daga kasar Suwidin cewa a kama shi, kuma tuni ta gurfanar da shi a gaban kuliya kan tuhumar da kasar Suwidin tace tana masa na lamarin wadannan mata biyu, inda a karon farko kotu ta hana shi beli. Amma bayan sauraron kara karo na biyu a ranar 14 ga wannan wata, sai ta bayar da belinsa.

A daya bangaren kuma, da yawa cikin masu lura da al’amuran yau da kullum, da kuma magoya bayan wannan shafi na WikiLeaks, sun ce sam karya ne hukumar kasar Suwidin take yi, kawai dai tana rabewa ne da guzuma don ta harbi karsana. Abin nufi a nan shi ne, tana kokarin kama shi ne don mika shi ga kasar Amurka da ke nemansa ruwa a jallo kan batun bayanan sirri da shafinsa ya yada cikin makon karshe na watan Nuwamba na wannan shekara. Don haka suke cewa bai ma kamata tun farko a kama shi ba, domin manufar ba wai na tirsasa wa wadansu mata bane kamar yadda ake riyawa, a a, don wasu manufofi ne na siyasa da kasar Amurka ke son cin musu. Idan ba a mance ba, tun sa’adda wannan shafi na WikiLeaks ya fara yada bayanan sirri mai take Kundin Yakin Afghanistan (The Afghan War Diary) cikin watan Yuli, da kuma bayanan sirri na baya-bayan nan kan kasar Iraki, mai take Kundin Yakin Iraki (The Iraq War Logs), tare da wani bidiyo da ke nuna yadda sojin kasar Amurka suke kashe mutane a kasar Iraki, kasar Amurka ke neman wannan matashi don huce fushinta. Wannan ta sa ya daina kai ziyara kasar Amurka, don kauce wa fushin hukuma. Lokacin da suke shirye-shiryen gudanar da taronsu na shekara-shekara mai take Hackers On Planate Earth (HOPE) Conference, kungiyar ‘yan dandatsa ta duniya ta bayar da sanarwar cewa Assange na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi na musamman a wajen taron. Jin haka ke da wuya sai hukumar Amurka ta fara sa ido. Wannan tasa ya ki halartar taron, sai wani mataimakinsa ne ya gabatar da jawabin a madadinsa. Shi kanshi bai tsira ba, domin bayan dawowarsa daga wata bulaguro da yaje a kasar Holand, jami’an tsaron kasar Amurka sun tsare a shi filin jirgin sama, inda suka kama masa tambayoyi, shi kuma ya ki amsawa, yace sai a gaban lauya zai amsa tambayoyin da suka masa. Wannan tasa suka kyale shi, amma sun kwace masa dukkan wayoyin salularsa guda uku, tare da gudanar da bincike na kwakwa kan kwamfutarsa. Wannan ke tabbatar da cewa, ba ma Assange kadai ba, duk wanda aka san yana da alaka da wannan shafi na WikiLeaks, to, kasar Amurka musamman tana dakonsa ne. A halin yanzu dai an bayar da belin Julian Assange.

Hankado Bayanan Sirri

Kamar yadda mai karatu ya karanta a baya, wannan shafi na WikiLeaks ya shahara ne wajen hankado bayanan sirri da suka shafi wasu gwamnatoci ko kamfanoni da ke badakala da kudin jama’a, a kowace kasa ce kuwa. Dangane da haka ya hankado bayanai masu dama da za su iya mummunan tasiri a siyasar duniya, wanda kuma hakan ne ya kara masa shahara a duniyar hakika da ta Intanet. Bayanan sirrin da wannan shafi ya fara hankadowa, wanda kuma yayi tasiri a siyasar duniya shi ne kan batun kashe-kashe da jami’an tsaro suka yi ta yi a kasar Kenya tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi na biyu. Wadannan bayanan sirri da shafin ya hankado ya dumama iskar siyasar duniya, inda har a karshe Kungiyar Amnesty International ta bashi kyauta ta musamman a fagen fafutikar neman ‘yancin dan adam a shekarar da ta gabata. Bayan haka, shafin ne ya fara buga nassin Jakar Sadarwar Imel din Gwabnar jihar Alaska ta kasar Amurka, watau Palin. Kuma kowa ya amince cewa lallai da gaske jakar Imel dinta ne wasu ‘yan Dandatsar kasar Amurka suka hankado daidai lokacin da ake kokarin gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, inda take takarar mataimakiyar shugaban kasa. Labarin wannan lamari na fara yaduwa, sai wannan shafi na WikiLeaks ya buga nassin sakonnin da wadannan mutane suka hankado, cikin shafinsa; kowa ya gani.

Bayan wadannan, shafin WikiLeaks ya sake hankado bayanan sirrin kasar Amurka da suka shafi Yakin Afghanistan, kamar yadda bayanai suka gabata a baya, ya hankado wani faifan bidiyo da ke nuna yadda sojin Amurka suka karkashe mutane a kasar Iraki, tare da dimbin bayanan sirri har wa yau kan Yakin Irakin ma gaba daya. Shahararren bayanin sirri na karshe da wannan shafi na WikiLeaks ya sake hankadowa sun shafi sakonnin diflomasiyya ne tsakanin kasar Amurka da sauran kasashen da take huldar diflomasiyya da su, watau Diplomatic Cables ko kuma Cablegate, kamar yadda shafin ya ayyana su. Wannan lamari na karshe ne ya fi tasiri da kuma tayar wa gwamnatin kasar Amurka hankali fiye da kowanne, saboda hakan tonon asiri ne kan tsarin huldodin da suka shafe ta da sauran kawayenta. Bayanan na da yawa, domin har gobe kara hankado shafin yake yi. Nassin sakonnin da ke dauke cikin wannan kundi na diflomasiyyar kasar Amurka ya kai kusan miliyan daya – ciki har da wasu kalaman siyasa da suka shafi kasa da hukumar Najeriya mai ci a yanzu, da kuma kamfanin hakon mai na Shell. Wannan lamari ya bai yi wa kasar Amurka dadi ba, duk da cewa wasu na ganin kamar akwai hadin baki tsakaninta da wannan shafi, don cin ma wata manufa ta siyasa. Hakika babu kamshin gaskiya cikin wannan zargi ko kadan. Wannan zance ne na siyasa wanda ba za mu tattauna shi ba a nan. A halin yanzu ga bayani kan yadda suke hankado wadannan bayanai, tare da yada su.

Tsarin Bincike Wajen Hankado Bayanai

Da farko dai tukum, zai dace mai karatu ya san cewa wadanda suka mallaki wannan shafi na WikiLeaks dukkansu kwararru ne kan harkar kwamfuta, ba wai ‘yan jarida bane kadai, kamar yadda galibin masu shafuka irin wannan suke. A takaice ma dai, akwai tabbataccen bayani kan cewa ‘Yan Dandatsa ne, watau Hackers, masu amfani da kwarewarsu wajen hankado bayanai a ko ina suke. Wannan ba zai hana samuwar wasu kwararru ‘yan uwansu ko wadanda suke basu hadin kai ta karkashin kasa ba. Hakan ma shi ya fi sauki, musamman ta la’akari da dabi’un wadannan mutane wajen zumuncin musanyar bayanai kyauta, ta hanyar da su kadai ke iya fahimtar tsarinsu. Wannan ne ma yasa lokacin da aka kama Assange, aka gurfanar da shi a gaban kuliya a kasar Ingila, har wasu kamfanonin karbar tallafi ta Intanet suka rufe taskarsa da yake amfani da su wajen karban tallafi, nan take sai magoya bayansa – ‘Yan Dandatsa – suka fara kai ma shafukan Intanet din wadannan kamfanoni farmaki, inda suka rufe su, suka hana mutane mu’amala da su. Kai, hatta shafin Intanet din wasu hukumomin kasar Suwidin ma, duk an kai musu hari. Abokin biri, in ji Hausawa, suka ce kare.

Kamfanin da ke dauke da kwamfutocin da wannan shafi ke dauke a ciki yana kasar Suwidin ne, sunansa PRQ, kuma kamfani ne da yayi rajista a layin tsarin kasuwancin da ba ya bukatar sanin asali da tsarin wadanda yake mu’amala da su, balle har ya adana wasu bayanai da suka shafi abokan huldarsa. Yana da kwamfutoci bila adadin a warwatse a duniya – musamman Turai. Bayan haka, kasar Suwidin ce kadai ke da dokokin da basu yarda a kama binciken yadda wani kamfanin yada labarai ya samo bayanansa ba balle har a tuhume shi kan abin da ya yada. Wannan ya baiwa su Julian Assange damar kafa wannan shafi cikin sauki a kasar, tare da girke shi cikin wasu kwamfutoci da babu mai iya kaiwa garesu duk kwarewarsa wajen dandatsanci. Bayan haka, sun samar da ma’adana na musamman masu dauke da dukkan shafukan da ke asalin shafin da mutane ke mu’amala da shi. Sun yi hakan ne don “ajiya” – gida biyu maganin gobara. Idan aka rufe shafin ta hanyar dandatsanci, nan take sai su bude wani shafin daban. Wannan tsari shi ake kira Server Back-up ko kuma Server Prototyping, a fannin Kimiyyar Sadarwa ta zamani.

Gidan yanar sadarwar wannan shafi na WikiLeaks na dauke ne da zaratan masarrafan kwamfuta da ake takama da su a fannin tsaro da sato bayanai a ko ina ne. Ire-iren wadannan masarrafai ko manhajar kwamfuta dai sun hada da: MediaWiki, da Freenet, da Tor, da kuma PGQ. Da wadannan masarrafai ko manhajoji ne suke gudanar da harkokinsu. Masarrafai ne masu matukar tasiri wajen yada bayanai, da nemo su, da kariya ga bayanai, da kuma tsarin shiga da mu’amala da su. Duk sa’adda aka kai musu hari a shafin da suke gudanar da al’amura, sai su koma wani shafin nan take. Daga ko ina suke suna iya zuba bayanai a shafin, kuma suna iya sarrafawa tare da tsara yadda suke so su kasance a shafin. A haka suka zama gagarabadau; ta yadda duk suka so suke nemo bayanai.

Idan wani ya turo musu bayanai, akwai kwamiti da suka kafa wanda ke yin nazari kan wanda ya turo bayanan, da kasar da ya fito, da alakarsa da bayanan da ya turo, da kuma sana’a ko abin da yake yi. Bayan haka, suna da kwararru a harkar gina manhajar kwamfuta, watau Programmers, masu lura da tsarin bayanan, ko yanayin da aka turo, ko kuma irin masarrafar da aka yi amfani da ita wajen turo su. Akwai kwararru a fannin harsunan duniya, masu yin nazari kan harshe ko yaren da aka turo bayanan cikinsu. Sannan ka’ida ta karshe ita ce, ya zama bayanan ba wasu sanannun bayanai bane wadanda kowa ya saba da su. Domin suna neman bayanan sirri ne, masu tasiri a fannin siyasa ko diflomasiyya, saboda kimtsattsiyar manufarsu na kafa wannan shafi. Idan bayanin da aka turo musu ya cika wadannan ka’idoji, kuma ya tsallake siradin masu nazari, sai su buga shi a shafinsu, ko waye ya shafa, babu ruwansu.

Tasirin Shafin WikiLeaks a Fannin Sadarwar Zamani

Tasirin wannan shafi na WikiLeaks a bayyane yake, musamman ma a siyasar duniya. To amma tunda damuwarmu a wannan shafi shi ne fahimtar tasirinsa a harkar Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta zamani, ba za mu tabo wancan janibi na siyasa ba. A wannan fanni na kimiyyar sadarwar zamani shi ma, tasirin wannan shafi da ayyukansa a Intanet a fili suke. Janibin farko da za mu duba, kamar yadda muka yi alkawari, shi ne bangaren da ya shafi tsarin yada labarai da nemo su, musamman labarai ko bayanan da ba ko ina ake iya samunsu ba, sai da wata kwarewa ta musamman. Wannan fanni, wanda a turancin yada labaran ake kira Investigative Journalism, hanya ce da ta shafi gudanar da bincike na musamman, na kwakwaf, ta hanyar karkashin kasa – ta hanyar da ta dace da wacce bata dace ba. Wannan a tsari da Kalmar aikin jarida kenan. Amma a tsarin yada labarai ta Intanet, wannan kalma ta fi fadi da gamewa. Domin ta hada da yin amfani da hanyar dandatsanci, watau Hacking ko Cracking, don “sato” bayanan sirri, kamar yadda masu wannan shafi ke yi ko bi. Duk da cewa an dade ana hankado bayanai ta wannan hanya da tsari a Intanet, amma a ba irin wannan sifa ba. Domin bayyanar shafin WikiLeaks ne ya fara haska hanya a wannan fage, inda ya samu karbuwa a idon da yawa cikin mutanen da ke mu’amala da wannan fasaha ta Intanet. Kai hatta daga shugabannin wasu kasashe ma ya samu karbuwa. Domin lokacin da wannan shafi ya fara hankado bayanan sirri kan diflomasiyyar kasar Amurka, shugaban kasar Benuzuwela, Hugo Chavez, ya jinjina musu sosai. Bayan haka, hatta wasu kafafen yada labarai masu kima a duniya, irinsu tashar tauraron dan adam ta Aljazeera, watau Aljazeera English sun yi na’am da wannan tsari. Hakan a fili yake, inda har wanann shafi kan baiwa tashar daman shiga ko isa zuwa ga bayanan da ya fara hankadowa a karon farko, irin damar da ba a baiwa tashoshi irinsu CNN ko BBC ba a misali.

Bayan haka, a yanzu haka akwai wani sabon shafi da wasu suka bude mai suna OpenLeaks, wanda shi ma kusan tsarinsa daya ne da shafin WikiLeaks. Abin da ya bambanta su kawai shi ne, shafin OpenLeaks yana baiwa masu ziyara daman turo tushen jakar bayanai ne a shafin, ta yadda idan masu karatu suka bukaci budowa ko sauko da bayanan, wannan shafi nasu zai je cikin kwamfutar da ke dauke da wadannan bayanai, a ko ina take a duniya, don budo su. Amma shafin WikiLeaks, duk da cewa shi ma da haka ya fara, amma a karshe sai ya rufe kofa; sai masu shafin kadai suke zuba bayanai don amfanin masu ziyara, shi kadai yake kidi da rawansa. Bayyanar wannan sabon shafi mai gudanar da aiki makamancin na WikiLeaks, shi ke nuna mana cewa lallai ga dukkan alamu, nan gaba za a ci gaba da samun ire-iren wadannan hanyoyin yada labarai da bayanai na sirri a duniyar Intanet.

Bangare na biyu kuma shi ne, tasirin wannan tsarin samar da bayanai zai canza yadda mutane ke neman bayanai a Intanet. A yayin da a bayan mutane na mu’amala ne kadai da bayanan da mai gidan yanar sadarwa ya ga daman zubawa da aikawa kadai, a yanzu masu ziyara na iya karanta abin da ya shafi bayanan sirri dangane da kasashensu. Wannan, duk da cewa ba abu bane zai iya haifar da mai ido a galibin kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, da kasashen Asiya irin su kasar Sin da sauransu, zai dada wayar da idanun masu mu’amala da Intanet, tare da samar da wani sabon salon hanyar samun bayanai kai tsaye daga shafuka na musamman. Bayan haka, akwai tabbacin cewa mutane za su aminta da ire-iren bayanan da suke samu, cewa lallai gaskiya ne, musamman idan sun shafi wasu al’amura da bayaninsu ya zama boyayye ga jama’a a duniya ko kasashen da abin ya shafa. Duk wanda ya bibiyi dambarwar da aka ta yi tsakanin jami’an gwamnatin Amurka da masu wannan shafi na WikiLeaks bayan sun bayar da sanarwar cewa za su fitar da bayanan da suka fitar daga baya, zai fahimci cewa lallai bayanai ne gaskiya, abubuwan sun faru, kuma an boye su ne ga jama’a don wasu manufofi na siyasa – masu kyau ko munana. Wannan, a karshe, shi ke nuna mana cewa rayuwa a duniyar Intanet, kusan ta game da irin rayuwar da muke yi a zahiri. Duk da cewa aikin dandatsanci laifi ne a dokokin mu’amala da Intanet, amma kuma, a dokokin kasashen Yamma – musamman kasar Amurka – sato bayanai ta hanyar dandatsanci, wadanda suka shafi yadda ake gudanar da mulki, da siyasa, da kuma al’amuran jama’a, da kuma yada su ga jama’ar da abin ya shafa, ba laifi bane ko kadan. In kuwa haka ne, tsarin samar da bayanai a Intanet zai canza nesa ba kusa ba, saboda masu neman bayanai na sirri za su karu, hakan kuma shi

No comments:

Post a Comment