Kaddamar da Masarrafar Google+
Ga dukkan alamu dai dan adam ba zai taba gushewa ba cikin gasa a wannan duniya tamu, saboda dabi'ar kishi da Allah ya kintsa masa a dabi'arsa. A yayin da a duniyar Intanet ake ganin kamar dandalin abota ta Facebook ta gama samar wa jama'a duk abin da suke bukata wajen hada alaka a tsakaninsu da abokansu; maza ne ko mata, sai kwatsam ga wata sabuwar masarrafar daga daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa, watau Google. Da ace wannan masarrafa daga wani kamfanin sadarwa ne da bai kai Google shahara da kwarewa da girma ba, da babu wanda zai damu da shi balle har ya san me ya zo da shi. Amma nan take masana suka fara sharhi. Wasu suka ai don hamayya da kamfanin Facebook ne ta sa Google ya kirkiri wannan manhaja, saboda ya kashe wa Dandalin Facebook kasuwa. Wasu kuma suka ai duk dai gautar ja ce; babu wani bambanci a tsakanin masarrafan guda biyu. Wasu kuma suka ce wannan kaddamarwa da kamfanin yayi shi ne daidai, domin daman sun gaji da matsalolin da ke addabarsu a Dandanlin Facebook, wanda kuma hukumar kamfanin ta kasa magancewa. Da dai sauran korafe-korafe ko tsokaci da masana suke kan yi, tun daga ranar da aka kaddamar da wannan sabuwar masarrafa.
A makon karshe na watan Yunin da ya gabata ne dai kamfanin sadarwar masarrafar neman bayanai a Intanet watau Google, ya kaddamar da wata sabuwar masarrafa mai suna Google+ (watau Google Plus). Wannan sabuwar manhajar sadarwa a tsakanin jama'a dai kusan tsari daya take da shi da na dandalin sadarwar Facebook ko MySpace a zahiri. Amma cikin bayanan da Injiniyoyin kamfanin Google suka yi a wajen kaddamar da wannan sabuwar masarrafar sun nuna akwai bambanci tsakanin abin da suka gina da wadanda ake amfani da su a wasu gidajen yanar sadarwar a halin yanzu.
Wannan masarrafa ta Google+ dai masarrafa ce da ke gidan yanar sadarwa, wacce ke sawwake tsakanin sadarwa a tsakanin mutane, daga yada bayanai rubutattu, zuwa kan hotuna, sai bidiyo (hotuna masu motsi), da kuma hira da abokin mu'amala ta hanyar bidiyo ba tare da wata matsala ba. Har wa yau, masarrafar na dauke da manhajar da ke sawwake loda hotuna da zarar ka sanya su cikin kwamfuta ko ka dauke su daga wayar salularka, nan take. Bayan wasu lokuta kuma ta bayyana su a shafinka, don masu bukata su gani. Wadannan, kadan ne daga cikin sifofin wannan masarrafa ta Google+.
A halin yanzu dai kamfanin Google bai bude wannan shafi ga kowa da kowa ba. An dai baiwa wasu zababbun mutane ne damar shiga don yin gwaji, kafin a bude shafin ga dukkan jama'a masu sha'awan shiga. Mutum na farko da ya fara samun damar shiga da bude shafi a wannan masarrafa dai shi ne Mark Zukerberg, watau shugaban kamfanin Facebook kenan. Kuma ya zuwa wannan lokaci da nake wannann rubutu, an kiyasta cewa yana da abokai sama da dubu 30 da ke binsa a shafin (watau Followers kenan). Wannan adadi ya shallake adadin mutane da ke bin shugaban kamfanin Google gaba daya, watau Larry Page; inda ya samu mabiya dubu 24.
Sai dai bayan wadanda aka diba don gwaji, a halin yanzu an haramta shiga ko yin rajista, duk da yake kana iya zuwa gidan yanar sadarwar ka shigar da adireshin Imel dinka don kasancewa cikin jerin wadanda za a tuntuba da wuri da zarar wannan sabuwar dandali ta Google+ ta zama budaddiya ga kowa da kowa. Adireshin shafin dandalin shi ne: http://plus.google.com kada ka sanya "www", don a cikin babbar gidan yanar sadarwar Google shafin yake. Don haka ba ka bukatar sanya wadannan haruffa.
Tsari da Sifofin Dandalin Google+
Tsarin Dandalin Google+ ya sha bamban da na Facebook da sauran dandamalin yin abota a Intanet, duk da cewa manufarsu guda daya ce, watau sawwake sadarwa a tsakanin jama'an da ke wurare ko kasashe ko nahiyoyi daban-daban, cikin sauki ba tare da shan wahala ba. Wannan na daga cikin sifofin da fasahar Intanet ne kadai ke iya yinshi cikin kankanin lokaci da yanayi. Inda dandalin Google+ ya sha bamban da sauran shi ne wajen tsari da yanayin mu'amala a shafin. Ga bayanai kan yadda tsarin wannan sabuwar Dandali da Google+ yake a takaice:
Rajista
Kafin ka bude shafi a Dandalin Google+ dai dole ne ka yi rajista, watau ya zama kana da suna (username) da kalmomin iznin shiga (password) a shafin Google. Sabanin yadda ake rajista a shafin Facebook, inda za ka shigar da adireshin Imel dinka ne da sauran bayanai, a Dandalin Google+ sai kana da adireshin Imel na gidan yanar sadarwar Google, watau Gmail kenan. Da zarar ka yi rajista za a baka daman isa zuwa shafinka. Daga nan sai ka ci karo da sauran bangarorin da ke cikin shafin.
Google+ Circles
Da zarar ka shiga shafin, abu na farko da za ka fara cin karo da shi dai shi ne tsarin Google+ Circles, watau rajistan da za ka shigar da dukkan wadanda kake mu'amala da su. Wannan shi ne kwatankwacin jakar rajistan sunayen abokai dake shafin Facebook, watau Friends List. Sai dai bambancin da ke tsakaninsu shi ne, a shafin Facebook "kowa" aboki ne. Hatta mahaifa, da kannai, da yayyai, da abokai, da kakanni, duk a matsayin "abokai" suke. Amma a tsarin Google+ babu wannan. Masarrafar Circles za ta baka damar bambancewa tsakanin nau'ukan mutanen da ka shigar da su cikin shafinka, ta hanyar rarraba su da baiwa kowa matsayinsa. Bangaren iyaye daban, bangaren abokai daban, bangaren kannai daban, haka ma bangaren 'ya'yanka, idan ka shigar da su, duk zai zama kowa da bangarensa ne. Wannan shi zai baka daman mu'amalantar kowa a matsayinsa. Irin hiran da kake yi da mahaifinka ya sha bamban da wanda za ka yi da abokai, ko kannai ko matarka. Wannan tsari shi ne abu na farko mai kayatarwa a cikin wannan masarrafa. Injiniyoyin da suka tsara wannan masarrafa suka ce bai kamata a baiwa kowa matsayi daya ba, wannan, a cewarsu, ya saba wa yadda muka saba mu'amala da juna a rayuwar zahiri. Wannan shagube ne ga shafin Facebook, wanda ya dauki kowa a matsayin aboki.
Google+ Hangout
Wannan ita ce masarrafar hira ta bidiyo, kai tsaye. A wannan bangare kana iya shigar da mutane goma, wadanda ke zaune kan kwamfutarsu a sadda kake shafin, ka bukaci yin hira da su, suna ganinka kaima kana ganinsu, iya tsawon lokacin da kuke so. Wannan tsari shi ma ya saba wa sauran hanyoyin gudanar da hirar kai tsaye (real time chatting) da sauran dandamalin Intanet ke amfani da shi, inda za ka shigar da sunan mutum ne kawai, ya sani ko bai sani ba, sannan idan ka ga alamar da ke nuna maka yana nan, ba lalai bane ya zama hankalinsa na tare da kai. Amma a tsarin Google+ kuwa, duk wanda ka gayyace shi har ya shigo farfajiyarka ta Hangout, to hakika ya tabbatar maka cewa a shirye yake ku shakata ko ku zanta. Wannan masarrafa ita ma ta dada kayatar da wannan Dandali na Google+.
Google+ Sparks
Wannan ita ce masarrafar da za ka rika amfani da ita wajen zabo irin ababen da kake sha'awar karantawa daga yanar gizo, ka shigar da su cikin jakar Sparks, ya zama duk sadda ka tashi bukatar karantawa ko kallonsu, sai ka shige ciki ka nemo su, ba sai ka tsallaka shafukan Intanet ba. Wannan tsari ne mai kayatarwa, kuma ya sha bamban da tsarin shafin Facebook wajen tulin bayanan da ake nuno maka a shafinka, wanda kuma duk tallace tallace ce, marasa alaka da dabi'a ko rayuwarka. Amma a tsarin Google+ masarrafar Sparks kadai ta isheka wajen gyatta irin bayanan da kake so, cikin sauki da tsari.
Google+ Stream
Shi kuma manhajan Stream wuri ne da za ka rika cin karo da kalaman dukkan mutanen da ka shigar da su a shafinka, kai tsaye, a lokacin da suke aikowa. Wannan shi ne kwatankwacin masarrafar Live Feeds da ke shafin Facebook, wanda kuma ke cike maka gaba, duk sadda ka budo shafin za ka ci karo ne da shi, ba yadda ka iya. Amma a shafin Google+ yana killace ne wuri daya, duk sadda ka ga daman ganin me suke cewa, sai kawai ka matsa alamar masarrafar Stream, kai tsaye za a cilla ka can.
Google+ Upload
Wannan masarrafar amfaninta galibi a wayar salula ne, domin kamfanin Google zai shigar da wannan Dandali na Google+ cikin dukkan wayoyin salularsa na Android nan ba da dadewa ba. Don haka idan kana da wayar salula mai dauke da manhajar Android, to za ka samu wannan masarrafa a ciki, kuma amfanin Upload shi ne, a duk sadda ka dauki hotuna daga jikin wayar salularka, nan take zai taskance hotunan, ya boye su zuwa wani dan kankanin lokaci, kafin ya bayyana su a shafinka da ke Google+ din kai tsaye. Don haka, duk wadanda ka taskance sunayensu a shafinka za su iya ganin hotunan ba tare da matsala.
Wadannan, a takaice, su ne muhimman sifofin da wannan sabon Dandali na Google+ ke dauke da su. Sai mu saurari lokacin da kamfanin zai baiwa kowa daman mallakar shafi a wannan dandali.
No comments:
Post a Comment