Wannan shi ne kashin karshe na Amsoshin Tambayoyi a wannan marhala. Ina mika gaisuwa da godiyata ga dukkan masu karatu, musamman masu aiko da addu'o'i kan gamsuwarsu, da masu aiko tsokaci ko gyara kan kurakuran da ake tafkawa. Allah saka da alheri, amin.
...................................................
Salam, a
bisa bayanin da kayi kan ATM da kuma yadda yake aiki da shi, ina so ka yi mini bayanin yadda zan
sayi wani abu ta intanet kuma na biya kudin ta hanyar amfani da katin ATM di na. Ina amfani da katin masta ne (Mastercard). Ina maka fatan alheri. Na gode, Bashiru Musa, Zaria.
Malam
Bashiru ban san bankin da kake amfani da katinsa ba, ina kyautata zaton GTBank
ne. In haka ne, lallai za ka iya
cinikayya da katin ta hanyar Intanet.
Sai dai ya danganci shafin da za ka yi cinikayyan a cikinsa. Domin wasu kamfanonin sayar da kayayyaki a
Intanet ba su yarda da 'yan Najeriya wajen cinikayya a Intanet. Wannan ke sa
idan kaje shafin don aiwatar da kasuwanci, akwai inda za ka zabi kasarka, idan
ka duba za ka ga babu Najeriya a ciki.
Wannan kuwa ba sai na gaya maka dalilin ba. Amma dai a takaice za ka iya. Na farko, ka tabbata akwai isassun kudi a
cikin taskar ajiyarka ta banki. Na biyu
kuma, za ka je shafin da kake son sayan hajar ne, ka zabi hajar da kake bukata
(za ka ga an rubuta "Add to cart" a kasar hajar, ko a gefen hajar, ko
ka ga an rubuta "buy" ko wata kalma makamanciyarta). Idan ka matsa za a budo maka bayanai kan
hajar. Abu na uku, za a bukaci ka yi
rajista a shafin, inda za ka shigar da bayanan da suka dangance ka, da
adireshin gidanka, da jahar da kake, da lambar katinka na ATM, da adireshin da
kake son a kawo maka hajar (gida ko ofishinka misali), da nau'in katin da kake
amfani da shi (Mastercard, ko Visacard), da tsawon lokacin da kake son hajar ta
riske ka, da kuma kamfanin aika wasiku (Courier Service Provider – irin su
Fedex, ko DHL dsr) da kake son ayi amfani da shi wajen aiko maka. Daga nan za a zarce da kai shafin da zai
kididdige maka dukkan kudaden da za ka biya; da kudin haja, da kudin aikowa.
Daga nan sai ka tura. Za a turo maka
sako ta adireshin Imel dinka ana sanar da kai cewa an tura sakonka, kuma rana
kaza zai iso. Idan masarrafar kwamfuta
ce, ko littafin da ke yanayin masarrafar kwamfuta (eBook), wadannan ba ka
bukatar kamfanin aikawa, nan take za a
tura maka rariyar da za ka bi don saukar da ita kai tsaye. Amma kafin nan, sai kamfanin kati sun
daidaita da bankin da kake ajiya da su, a cire musu nasu kason, sannan banki ya
turo maka sako don sanar da kai kan haka.
Wadannan, a takaice, su ne 'yan bayanan da suka sawwaka. Da fatan ka gamsu.
Assalamu
Alaikum Baban Sadiq, da fatan kana lafiya. Tambayata itace. Ina neman karin
bayani game da yadda ake amfani da Blog, kuma ya ake yin register da shi
kuma ya ake zuba labaru a cikin shafin mutum. Na gode. Daga Ismail Bello (IT
Student Katsina University), Katsina.
Malam
Ismail barka da warhaka. Idan kana
bukatar bude shafin Mudawwana na Blogspot, sai ka je zauren gidan yanar da ke www.blogspot.com/start ka matsa inda aka rubuta "Sign Up"
don mallakar akwatin Imel na Gmail, sannan ka matsa inda aka rubuta
"Create a Blog." Bayanan da za
a bukata ba su da yawa, kuma ba su da wahalar bayarwa. Sunan shafin ne, da adireshin shafin, yadda
kake so ya kasance, da kuma tsare-tsaren da kake son shafin ya sifatu da
su. Idan ka gama, za a kai ka inda za ka
iya kirkirar bayanai don lodawa a shafin.
A saman shafin daga hannun dama akwai inda aka rubuta "Create a New
Post," da zarar ka matsa zai zarce da kai shafin da za ka rubuta bayanan
da kake son shigarwa, kana gamawa akwai inda aka rubuta "Publish"
daga saman shafin da kake a hannun dama shi ma, sai ka matsa don lodawa a
shafinka. Lamarin ba wahala. Idan ka shiga, akwai abubuwa da yawa da za ka
iya yinsu da kanka, ba sai ka tambaye ni ba.
Abin sauki ne dashi, kamar cire wando ta ka! Da fatan malam Ismail ya gamsu.
Salamu
alaikum, Baban Sadiq muna godiya da karuwa da muke yi da kai a shafukanka da ke
Intanet, da kuma gidajen radiyo. Allah
kara taimako da ilmi mai amfani amin. Na ga ka yi bayani kan na'urar ATM, amma na fahimci ka fi ba da karfi
wajen aikinta na fitar da kudi, alhali ka ce akwai wasu ayyukan da take yi
kamar na biyan kudin wuta, ko na katin waya da dai sauransu. Ina fata in hali ya yiwu za a yi mana bayani a
kansu nan gaba. Na gode. Lawal B Yusuf 08020636825
Malam Lawal wannan bayani naka haka yake. Abin da yasa na takaita bayani kan wadannan
abubuwa kadai shi ne don su ne suka fi shahara, kuma su ne asalin dalilan da
suka sa aka kera wannan na'ura. Duk
sauran abubuwa daga baya ne suka samu.
Dalili na biyu kuma shi ne, duk da cewa biyan kudin wuta da sayan katin
waya (watau "Quick Teller" kenan) ba wasu abubuwa bane masu wahala
wajen aiwatarwa, sai dai ga mutumin da bai saba yinsu ba, akwai rikitarwa, kuma
karamin kuskure na iya sa mutum ya kidime.
Idan ya kidime a muhalli irin wannan, ba kowane mai zuwa wurin bane zai
iya agaza masa. Domin cikin kashi dari
na masu amfani da wannan na'ura, za ka samu kashi goma ne ko kasa da haka suke
aiwatar da ayyuka irin wadannan. A takaice dai abu ne da ke bukatar kwarewa da
kuru. Wannan yasa na takaita bayani kan
abin da yake mafi sauki, wanda kuma ake samun agaji a kansa cikin sauki. Da
fatan an gamsu.
Salam
Baban Sadik, gidan yanar Yahoo! ne yanzu ba na iya shiga. Ban san dalili ba. Sai a ce mini: "Page not found". Shin, su
ne da matsala? Nagode daga Sharif
Liman Giwa: 08090547770
Liman Giwa: 08090547770
Malam Sharif duk sadda ka samu sako irin wannan
wajen mu'amala da wani shafi a Intanet, dayan biyu ne: ko dai baka shigar da
adireshin gidan yanar sadarwar daidai ba, ko kuma akwai matsalar sadarwar Intanet
tsakanin wayar salularka ko kwamfutarka, da kamfanin da ke ba ka sabis na
Intanet. Abu na farko sai ka duba
adireshin ka gani. Idan daidai ka
shigar, sai kuma ka duba tsarin sadarwa ta Intanet da ke wayar, watakila
yanayin sadarwa ya yanke, watau "Network" kenan, ko kuma a lokacin da
kake kokarin shiga shafin, wani kira ya shigo, ko wani tes ya shigo. Idan kana mu'amala da shafin Intanet a waya
sai aka kira ka, to nan take yanayin sadarwar intanet din zai yanke, sai ka
gama zancenka sannan ya dawo. Da fatan
ka gamsu.
Salamu
alaikum Baban Sadik, Tambayata ita ce; dangane da na'urar hangen nesa,
watau Telescope; ya yake ne? Kuma iri nawa ne? Har yanzu ma ana
aiki da shi sosai kuwa?. Daga Aliyu Mukhtar Saidu (I.T) Kano, aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 / 08099109200.
Malam
Aliyu barka da warhaka. Lallai har yanzu
akwai wannan na'ura ta hangen nesa da ake kira "Telescope" a harshen
Turanci. Wannan na'ura ana amfani da ita
ne wajen hango abubuwan da ke cikin sama, wadanda suka sha karfin idon dan
adam, don ganin hakikaninsu, da girmansu, da kuma yadda suke. Wannan na'ura ta hangen nesa dai an fara
kirkirarta ne a kasar Nedalands da ke nahiyar Turai, cikin karni na 17. Shekara guda bayan kirkirar wannan na'ura ne
shahararren masanin kimiyyar nan mai suna Galileo ya fara amfani da ita wajen
gano wasu daga cikin duniyoyin da ke makwabtaka da wannan duniyar tamu. A haka ya gano wasu taurari da ke shawagi a
gewaye da wadannan sababbin duniyoyi na Jofita da Benus da ya gano. Wannan bincike da Galileo yayi ne ya haska wa
duniya fa'idar da ke tattare da na'urar hangen nesa a wancan zamani. Wannan ne ma yasa har wasu ke ganin cewa ko
shi ne ya fara kirkirar na'urar. Ba shi
bane. Wannan na'ura ta hangen nesa dai
tana amfani ne da haske da ke darsanuwa a jikin gilashin da ke cikin na'urar,
don jawo shi kusa, da bayyana hakikaninsa.
Akwai nau'in da ke janyo hoton abu daga nesa ta amfani da haske, sai ta
cillo shi cikin na'urar, inda gilashin da ke ciki daga tsakiya yake cafke
hasken, sannan ya cilla shi zuwa kasa, daidai inda idon mai nazari ke
kallo. Wannan nau'i shi ake kira
"Reflective Telescope." Sai
kuma nau'i na biyu da ke amfani da gilashi mai rage kaifin haske (watau Lens),
don jawo hasken da ke dauke da hoton abin da ta hasko, sai wannan gilashi na
farko ya cilla hasken zuwa wani dan karamin gilashin rage kaifin haske da ke
gab da idon mai nazari, don ba shi damar ganin hoton abin da ke kunshe cikin
hasken ba tare da wata matsala ba. Wannan nau'i shi ake kira "Rafractive
Telescope." Dangane da girma kuma,
sun kasu kashi kashi. Akwai kanana wadanda ake iya rikewa da hannu a hango abin
da ake son hangowa. Akwai wadanda ake
girkewa a kan sanda, a cilla su zuwa inda ake son hangowa. Akwai kuma manya
wadanda ke saman farantin tauraron dan adam.
Mafi girma cikin nau'ukan na'urar hangen nesa shi ne wanda masana ke
amfani da shi wajen hango sirrin da ke sararin samaniyar halittar duniya baki
daya, ba wannan duniyar da muke ciki ba kadai.
Wanann nau'i shi ake kira "The Hubble Space Telescope." Dangane da tambayarka ta karshe, lallai har
yanzu ana amfani da wannan na'ura ta hangen nesa, sai ma abin da yayi
gaba. Da fatan malam Aliyu ya gamsu.
Assalamu
alaikum. Baban Sadik, Barka da aiki. Da fatar kana lafiya. Baban Sadak don Allah a taimaka min da bayani a kan wace
hanya ce bankuna da kamfanoni ke bi wajen tura wa Jama'a sako ta layukansu (Sim),
sannan ko kamfanin Yahoo yana da irin wannan hanyar? Sannan shi ma dandalin
sada zumunta na Facebook yana da irin wannan hanyar? Sannan wai idan ma
akwai wannan, to me yasa jama'a ba sa amfani da wannan hanyar? Na gode. Daga:-
Hassan Muh'd Binanci. A Jihar Sakkwato/ h.muhammad30@yahoo.com
Wannan
tsarin aikawa da sakonni dai shi ake kira "Bulk Messaging." Idan na sakonnin waya ne, akan kira shi
"Bulk SMS", idan kuma na Imel ne "Bulk Messaging" ma ya
isa. Tsari ne da ake amfani da shi wajen
aikawa da sakonni masu dimbin yawa, iri daya, zuwa ga jama'a masu yawa, cikin
lokaci daya. Wannan tsari dai yana da
masarrafa ce ta musamman, duk da cewa za a iya gudanar da ita ta hanyar wayar
salula ma, ma'ana kana iya aika wa dukkan wadanda kake da lambarsu sako iri
daya kai tsaye, a lokaci guda. To amma
idan kamar mutane miliyan daya ne fa? Ya
za ka yi? Kamfanonin wayar salula suna
da wannan tsari a cikin na'urorinsu.
Idan ka je za su gaya maka nawa za ka biya, sai ka basu nassin sakon da
kake son a aika, kamar na gayyatar biki misali ko wani taro, duk sai ka bayar. Nan take za su tura wa kowa da kowa. Haka ma idan ta Imel ne, akwai masarrafar da
ake amfani da ita don aikawa. Kamfanin
Yahoo! Ba su rasa wannan tsari, don kamfanin sadarwa ne, kuma suna da kwararru
kan haka. A tsarin Facebook ma ba za a
rasa ba, sai dai kuma wannan ya kebanci masu kamfanin ne ko ma'aikatansu. Suna iya aika wa kowa da kowa sako nan take,
amma masu amfani da shafuka damarsu wajen yin hakan takaitacciya ce. Za su iya
aika wa dukkan abokanansu sako iri daya a lokaci daya, amma ba dukkan mai
amfani da dandalin Facebook ba. Da fatan
ka gamsu.
Salamu alaikum Baban Sadik, don Allah ina da tambaya. Na aje memory card kimanin kwanaki 40, kuma
akwai abubuwa da yawa saboda babba ne. Wallahi
saboda shi na sayi waya mai tsada, amma na yi ta fama ya ki ya nuna komai. To yanzu yaya zan yi? Ina son abubuwan da ke
ciki. Salisu Bare, Dikko, Suleja Naija 08065275983
Babbar
magana, wai dan sanda ya gawar soja!
Malam Salisu ban san me ya samu wannan kati naka ba mai matukar
muhimmanci ba. Zan so in san irin
matsalar da wayar ke nunawa a sadda ka tsofa mata katin. Shin, tana cewa a shigar da
"Password" ne? In haka ne, to
watakila sadda kake amfani da katin a baya ka sanya masa makullan tsaro ne, sai
ka lalubo so don shigarwa. Idan kuma ta
ki karba ne gaba daya, to watakila akwai matsala a baya, tun sadda kake shigar
mata da bayanan. Domin idan kana shigar
mata da bayanai, sai ka cire tun bayanan basu gama shiga ba, to ko ka bukaci
amfani da ita ba za ka samu komai ba, domin dukkan bayanan da ke ciki za su
gurbace. Ko kuma ruwa ya taba, ko tsananin sanyi, ko kuma kura sun cike ta, ko
kuma kwayar cutar wayar salula, watau "Virus" ta shige ta. Duk wadannan na iya zama musabbabai. A takaice dai, in da hali ka kai wa masu
gyaran wayar salula don su duba maka.
Idan matsala ce da za su iya gyarawa ba tare da an yi hasarar bayanan da
ke ciki ba, za su taimaka. Idan kuma
bayanan da ke ciki sun gurbace (watau "Corrupted"), to a nan fa sai
dai a yi hakuri. Haka rayuwa ta gada. Allah sa a dace, amin.
Thanks for another great article. The place else may
ReplyDeletejust anybody get that kind of information in such a
perfect means of writing? I have a presentation next week, and I'm at the look for such information.
Also see my webpage > buy vietnam dong
Malaysia & Singapore & brunei greatest on the internet blogshop for wholesale &
ReplyDeletequantity korean accessories, accessories, earstuds, pendant, rings, trinket, bangle & hair
add-ons. Offer 35 % wholesale price cut. Ship Worldwide
My blog blocked drain plumber
It is appropriate time to make some plans for the longer term
ReplyDeleteand it is time to be happy. I have learn this put up
and if I may I desire to recommend you few fascinating issues or
advice. Maybe you can write next articles regarding this
article. I want to read more things about it!
Feel free to visit my blog :: Smith Mountain Lake Vacation Rentals
Hi, Neat post. There's a problem with your web site in internet explorer, might test this? IE still is the marketplace chief and a huge component of folks will pass over your excellent writing because of this problem.
ReplyDeleteFeel free to surf to my web site - lose weight with HCG
This website really has all of the information
ReplyDeleteand facts I needed about this subject and didn't know who to ask.
Feel free to visit my site :: sex chat video
At this moment I am going to do my breakfast, once having my breakfast coming
ReplyDeleteagain to read other news.
my blog ... www.babesflick.com
Its like you read my mind! You seem to know so much about this, like you wrote the
ReplyDeletebook in it or something. I think that you could do with some pics to drive the message
home a little bit, but other than that, this is magnificent blog.
A fantastic read. I will definitely be back.
my site http://Xxx-fuck.net/
Keep on writing, great job!
ReplyDeletemy blog www.wildpartygirls.org
Spot on with this write-up, I actually believe
ReplyDeletethat this amazing site neds far more attention. I'll probably be
returning to reasd more, thanks for the advice!
Here is my blog :: dick
Thanks for sharing!
ReplyDeleteInax