Siffofin Internet Explorer 6.0
Hausawa suka ce alkawari kaya ne. Idan mai karatu bai mance ba, makonni biyu da suka gabata ne muka fara koro bayanai
Da zaran ka budo wannan masarrafa ta Internet Explorer wacce ka saba amfani da ita, za ka samu a kalla bangarori shida ne, wadanda ke taimaka ma dukkan mai amfani da ita. Wadannan bangarori dai su ne: Title Bar, Menu Bar, Tool Bar, Address Bar, Display Page, da kuma Process Bar. Wadannan bangarori dukkansu kowanne aikinsa daban ne da na dan uwansa; kamar yadda maginin Rariyar ya gina ko tsara su. Kuma duk da yake a wuri daya suke, wani a saman wani, kowannensu manhaja ne mai zaman kansa a can cikin tumbin kwamfutar da kake amfani da ita. Duk lokacin da ka kira daya daga cikinsu, sai kwamfuta ta zakulo maka shi cikin kiftawa da bisimilla, don ya gabatar maka da aikin da kake bukata, sannan ya koma mazauninsa. A halin yanzu ga bayanin kowanne daga cikinsu, a fayyace:
Title Bar
Wannan shine shudin layi ko gurun da ke saman shafin masarrafan gaba daya. An kuma kira shi da wannan suna ne saboda shine ke bayyana maka sunan masarrafa, da kuma sunan shafin gidan yanan sadarwan da kake ciki. Da zaran ka budo shafin gidan yanan sadarwa da Internet Explorer, kana daga kanka sama daga hannun hagu, zaka ga an rubuta “Yahoo! – Microsoft Internet Explorer”, idan gidan yanan sadarwan Yahoo! ka shiga, misali. Idan kuma ka dubi can kuryan dama, zaka samu wasu alamu guda uku, wadanda ke taimaka kara fadin shafin da kake ciki, ko rage zuwa kasa, don budo wani shafi, ko kuma ma ka rufe shafin gaba daya. Na farko ne zai taimaka ma sauko da shafin kasa (minimize), na biye da shi kuma ya taimaka maka kara fadin shafin (maximize), shi kuma na karshen aikinsa shine rufe shafin gaba daya (close). Har way au, idan kana bukatan kara fadin shafin, zaka iya yi ba tare ka je “minimize” ba, a a, sai kawai ka saman Title Bar din sau biyu a lokaci daya (double-click). Shafin zai karu gaba daya, iya fadinsa na asali. Wannan aikin Title Bar kenan.
Menu Bar
Shi kuma Menu Bar shine layin da ke kasan Title Bar, yana daga cikin bangarori masu muhimmanci ga duk mai amfani da masarrafan lilo da tsallake-tsallake. Menu Bar na dauke ne da hanyoyi guda bakwai da zasu taimaka maka aiwatar da wasu ayyuka masu muhimmanci yayin da kake yawace-yawacenka a gidajen yanan sadarwa ta Intanet. Wadannan bangarori ko hanyoyi sune: File (mai dauke da hanyoyin budo wani sabon shafi, ko binciko bayanan da ka ajiye cikin kwamfutarka don loda su a shafin yana, ko adana wasu bayanan da ka samo daga Intanet, zuwa kwamfutarka, ko kuma ya taimaka maka buga - print – bayanan da ka samo masu muhimmanci), Edit (mai taimaka wajen yanko wani bayani da ka gani zuwa kwamfutarka, ko kwafo shafin gaba daya), View (wanda zai kai inda zaka iya kara yawan makaman aikin da ke Tool Bar, ko kuma taimaka maka wajen ganin fasahan da aka gina shafin da kake ciki da shi, watau View Source), Favourites (wanda zai taimaka maka wajen adana adireshin shafin yanan da kake ciki, idan ya kayatar da kai, ko kuma yadda zaka tsara wasu adiresan da ka adana a baya), Tools (zai taimaka maka wajen tsara saitin kwakwalwan rariyarka.
Tool Bar
Wannan shine bangaren da ke dauke da almun da zasu aiwatar maka da wasu ayyuka na gaggawa, ba tare da sai ka je Menu Bar ba. Alamun na dauke ne da sunan nau’in aikin da kowannensu ke yi. Tool Bar na kasan Menu Bar ne. daga hagu zuwa dama, zaka fara cin karo da alamar kibiyar da tayi hagu, an kuma rubuta Back daura da ita. Zai taimaka maka ne wajen dawowa baya daga inda kake, a shafin yanar gizo. Sai kibiyar da yayi gaba, don taimaka komawa shafin da ka fito, idan ka yi baya da farko. Sai alamar Stop, wacce za ta dakatar da masarrafa, idan da farko ka bata umarnin nemo maka wani shafi. Sai Refresh, wacce idan ka ga alamar “Page Cannot Be Displayed”, ita zaka matsa, don ta farfado maka da shafin da kake nema. Sai Home, wacce zaka isar da kai asalin adireshin da aka dabi’antar da masarrafan ka a kai (a Internet Options ake wannan). Da dai sauran alamun da ke wajen, wanda zaka samu kowanne da sunansa ko aikin da zai maka.
Address Bar
Wannan a fili yake; shine farin layin da ke kasa da Tool Bar, kuma aikinsa shine ya zakulo maka gidan yanan sadarwan da kake bukata, ta hanyar shigar masa da adireshin gidan yanar. Idan baka shigar da adireshin daidai ba, bazai gyara maka ba, don bai san manufarka ba. Afuwan da zai iya maka kawai shine ya taimaka maka wajen shigar da haruffan http:// idan ya zama www.yahoo.com kawai ka shigar, a misali. A gaba dashi zaka samu wasu rariyoyin likau da aka tanada maka, wadanda zaka iya matsa su a zarce da kai gidan yanan kai tsaye.
Display Page
Shafin masarrafan kenan, inda zai rinka budo maka dukkan shafin yanar da kake so, idan ka shigar da adireshin daidai kenan. Idan baka shigar da adireshin daidai ba, za t ace maka: Page Cannot Be Displayed. Za kuma ta iya nuna maka wannan alama idan ya zama siginar Intanet ta dauke daga kan kwamfutar da kake kai, saboda tsananin ruwan sama da ake tafkawa, ko kuma tsananin hazo ko yawan masu lilo a inda kake, ko kuma wayar da ke sadar da kai da uwar garke (server) ta cire.
Process Bar
Shi kuma Process Bar shine layin da ke kasan shafin gaba daya. Shima ba zaman banza yake a wajen ba, a a, yana da nasa ayyukan da yake yi, ko ka kula shi ko baka kula shi ba. Ayyukansa muhimmai guda hudu su ne; ya sanar da kai cewa ya gama budo maka shafin da kake nema, ta hanyar “done” da zaka gani a rubuce, ko ya sanar da kai cewa yana kan lalubo maka shafin da kake nema, ta hanyar “connecting to . . . .” da zaka gani a rubuce; ko sanar da kai cewa sauran kadan shafin da kake nema ya gama budowa, ta hanyar “4 items remaining”, da zaka gani a rubuce, a misali. Wazifansa na karshe kuma shine ya sanar da kai cewa akwai siginar Intanet a kwamfutarka ko babu, ta hanyar tambarin taswiran duniya da zaka gani, kamar yadda yake a Menu Bar. Idan ka ga ba ya juyawa, to da matsala. Wadannan su ne siffofin Microsoft Internet Explorer 6.0. Sai dai a wasu lokuta, zaka samu wasu layuka a kasan Address Bar, masu dauke da wasu karikitai wajen taimaka maka gabatar da wasu ayyuka daban, kamar yadda mai karatu zai gani a hoton masarrafan da muka gabatar a sama. Ire-iren wadannan makale-makale ana kiransu Add-ons, ko kuma Plug-ins, a turancin kwamfuta.
Add-Ons/Plug-Ins
Wadannan karikitai su ma manhajoji ne ko masarrafa, masu taimaka ma Rariyar Lilo gabatar da wasu ayyuka, kamar su budo jakunkunan bayanan da aka tsara da wasu manhajojin da kwamfutarka bata zo da su ba, irin su PDF (Portable Document Format) dsr. Har wa yau, su
Kammalawa
Daga karshe, yana da kyau mai karatu ya budo Microsoft Internet Explorer yin nazari kan dukkan ababen da aka sanar da shi, duk da yake galibin manhajojin da zaka iya dirowa (downloading) da su, na bukatar a ce kwamfutar taka ce. Shi ilimi wani abu ne da saninsa ke da muhimmanci, ko da kuwa watakil mutum ba zai aikata shi ba, musamman
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off
Garki II –
080 34592444 fasaha2007@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com