Ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu ne na halarci babban taron sabuwar shekara
na kungiyar Tsangayar Alheri da ke Dandalin Facebook. An gayyace na gabatar da
kasida ta musamman kan Bunkasar Fasahar Sadarwar Zamani a Najeriya: Kalubale da Ci Gaba. A sha karatu lafiya.
.......................................................
BUNKASAR FASAHAR SADARWAR ZAMANI A
NAJERIYA: KALUBALE DA HANYOYIN CI GABA
Gabatarwa
Shekaru 22 da suka gabata a Najeriya, kalmomi irinsu Nokia, da
Samsung, da Internet, da Email, da SMS, duk ba
abubuwa bane sanannu a kwakwalen mutane, balle harsunansu. Ba wai ga gama-garin jama'a ba kadai, hatta a
harshen masana a jami'o'i da sauran cibiyoyin ilmi wadannan kalmomi basu shahara
ba. Faruwan hakan ba ya nufin wadannan
kalmomi ko sunaye baki ne a duniya baki daya, a'a, sai don rashin isarsu gare
mu ne, sanadiyyar halin da kasar ke ciki na rashin bunkasar fannin kimiyya da
fasahar sadarwar tarho da abin da ya shafi na'urorin sadarwa da sarrafa
bayanai, irinsu kwamfuta, da wayoyin salula, da fasahar Intanet. Duk da cewa akwai hukumar lura da harkar
sadarwa ta Gwamnatin Tarayya, wacce ita ce kadai ke da alhakin bayar da
lambobin wayoyin tarho tare da yin rajistarsu ga masu bukata, wannan bai sa an
samu bunkasar wannan fanni mai matukar muhimmanci da tasiri ga al'ummar kasar
ba, sai bayan bude kafar zuba jari da aka yi a 'yan shekarun baya.
Kafin wannan lokaci, layukan tarho da hukumar gwamnati ke bayarwa
basu wuce 500,000 ba, a kasa mai dauke da al'umma sama da miliyan dari! Bayan haka, duk da karancinsu, babu yanayin
sadarwa mai inganci a kasar. Ba komai ya
kawo haka sai don na'urorin sadarwar na amfani ne da tsohon tsarin sadarwa,
watau Analogue, sannan ga gagarumin matsalar rashin wutar lantarki da
kasar ke fama da shi. A bangaren
na'urorin sadarwa irinsu kwamfuta kuwa, sai ofishin kamfanonin kasashen waje
masu zaman kansu da ke kasar, da wasu 'yan daidaikun shagunan buga bayanai ake
samunsu. Hatta a makarantun kasar nan
kwamfuta ba ta shahara ba sosai, balle tsarin amfani da su a hukumomin
gwamnatin jiha ko na tarayya. Galibi ana
amfani ne da keken rubutu, watau Typewriter irin na kamfanin IBM, (IBM
Digital Typewriter), sai kadan daga cikin kwamfutoci kanana na kamfanin IBM
masu amfani da tsohuwar manhajar kwamfuta ta kamfanin Microsoft mai
suna MS-DOS, ko Disk Operating System a warware. Dangane
da abin da ya shafi fasahar Intanet da Imel kuwa, babu wanda ya sansu, in ka
kebe 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, irinsu Amurka da Ingila da
sauran kasashen Turai.
To amma a yanzu lamari ya canza; Najeriya ta shiga sahun kasashe
masu ta'ammali da bayanai nau'uka daban-daban, ta hanyoyi daban-daban, a yanayi
daban-daban. Daga birane da maraya zuwa
kauyuka da rugage, duk jama'a na iya aikawa ko karban sakonnin murya, ko tes,
ko ta'ammali da fasahar Intanet ta hanyoyi daban-daban. Wannan kasida za ta
duba wannan ci gaba ne da aka samu, da dalilansu, da nau'ukan fa'idojin da 'yan
Najeriya suke samu ta wannan hanya, da kuma kalubale ko matsalolin da suke
fuskanta. A karshe kuma ta duba hanyoyin
da hukuma ko jama'a a matsayinsu na al'umma za su bi wajen shawo kan wadannan
matsaloli, don samun ci gaba mai alfanu.
Bunkasar Fasahar Sadarwa a Duniya
Fasahar sadarwar zamani ko Information Communication
Technologies (ICTs) a harshen turanci, tsari ne na aiwatar da sadarwa mai
inganci da fa'ida, ta amfani da kayayyakin sadarwar zamani – irinsu kwamfuta,
da wayoyin salula, da tauraron dan adam, da na'urorin sadarwar zamani – ta
hanyoyin sadarwar zamani – kamar su
fasahar Intanet, da Imel, da sakonnin tes, da shirye-shiryen talabijin masu
inganci da dai sauransu. Wannan alaka da
ke tsakanin kayayyakin sadarwa da hanyoyin sadarwar na kulluwa ne da taimakon wasu
ka'idojin kimiyyar sadarwar zamani, irinsu IP Address, da WAP, da
POP3, da IMAP, da SMTP da dai sauran ka'idoji
makamantansu. Wannan tsari ne ya hade duniya zuwa wata dunkulalliyar unguwa
saboda gamewarsa, da tasirinsa, da kuma saurin yaduwarsa.
Daga cikin mutum biliyan 7 da ke rayuwa a wannan duniya a yau, alkaluman
bayanai sun nuna sama da biliyan 2 na amfani da fasahar Intanet. Daga cikin wannan adadi, kashi 45 duk matasa
ne 'yan kasa da shekaru 25[1]. Har wa yau an samu karuwan masu ta'ammali da
fasahar Intanet a kasashe masu tasowa daga kashi 44 a shekarar 2006 zuwa kashi
62 a shekarar 2011. A wadannan kasashe,
bayanai sun nuna cewa matasa sun fi tsofaffi kashe lokacinsu wajen mu'amala da
fasahar Intanet. Daga cikin adadin nan har wa yau, kashi 30 duk 'yan kasa da
shekaru 25 ne. Daga shekarar 2000 zuwa
2011 an samu karuwar masu amfani da fasahar Intanet a nahiyar Afirka da kashi
2,527. Domin a shekarar 2000 mutum
miliyan 4.5 ne kacal ke ta'ammali da fasahar, amma shekaru goma bayan wancan
adadi, a yau ana da mutum miliyan 118.6 masu shawagi a giza-gizan sadarwa daga
nahiyar Afirka[2]. Akwai hasshen cewa idan gwamnatoci a nahiyar
Afirka suka shigar da tsarin sadarwar zamani a makarantun firamare da sakandare
da jami'o'i, za a samu karin matsa masu shawagi a giza-gizan sadarwar duniya
sama da biliyan daya[3].
Idan muka karkato zuwa Najeriya kuwa, za mu ga an samu ci gaba a
wannan bangare sosai. Domin shekaru goma
da suka gabata adadin masu ta'ammali da fasahar Intanet a kasar duk bai shige
mutum 200,000 ba. Amma a yau, daga cikin
mutum miliyan 118.6 da ke kutsawa giza-gizan sadarwa ta Intanet a nahiyar
Afirka, miliyan 44 duk daga Najeriya suka fito.
Wannan shi ne adadi mafi yawa da kaso mafi girma a nahiyar. Najeriya ce ta daya a yawan masu amfani da
Intanet a nahiyar Afirka. Dangane da abin da ya shafi masu shawagi a Dandalin
abota na Facebook kuwa, daga cikin mutum miliyan 710.7 da suka yi
rajista a duniya, mutum miliyan 30.6 daga nahiyar Afirka suke, a yayin da
Najeriya ta zo na uku a yawan masu rajista da miliyan 3.4, bayan kasashen
Misra, da Afirka ta kudu da suka shallake ta[4].
Daga cikin abin da ya dada taimakawa wajen karuwar adadin masu
ta'ammali da fasahar Intanet a Najeriya da sauran kasashen Afirka akwai samuwar
wayoyin salula da yaduwarsu. Domin a
yanzu akwai layukan wayoyin salula masu rai a duniya wajen biliyan 6. Wannan adadi ya samu ne sanadiyyar karuwar
masu amfani da wannan tsari a kasashe masu tasowa da kashi 79. Daga cikin abin da ya dada taimakawa wajen
wannan kari a wadannan kasashe, akwai saukin farashin wayoyin salula sanadiyyar
yawaita, da samun nau'uka daban-daban[5]. Domin a shekarar 2007 kadai an samu karuwan
masu amfani da wayoyin salula wajen miliyan 65.
A shekarar 2008 wannan adadi ya haura zuwa miliyan 250[6]. A halin yanzu akwai masu rajistan layin wayar
salula sama da miliyan 90 a Najeriya[7].
Ba wai kira kadai jama'a ke aiwatarwa da wayar salula ba, akwai
ta'ammali da fasahar Intanet, da rubutawa tare da aika sakonnin tes. A yini guda kacal, mutanen birnin Bejin na
kasar Sin sun taba aikawa da sakonnin tes sama da biliyan daya. A jajibirin bikin shigan sabon shekarar 2008
kuwa, alkaluman bayanai sun tabbatar cewa sakonnin tes wajen biliyan 43 ne suka
sauya hannu a tsakanin al'ummar duniya.
Daga cikin wannan adadi, sakonnin tes biliyan daya daga kasar Indiya ne,
a yayin da aka samu mutum miliyan 50 na kasar Filifin masu wayar salula suka aika
sakonnin tes wajen biliyan 1.39[8]. A
bincken da ta gudanar a wani shiri na musamman, talabijin kasar Kanada mai suna
CBC, ta tabbatar da cewa a kowane yini a kalla jama'a kan aika sakonnin
tes wajen biliyan biyu[9]. A
karshe dai, adadin sakonnin tes da ake aikawa a duniya ya kusan haura biliyan
dubu bakawai, tun daga ranar da wani matashi dan shekaru 22 mai suna Neil
Papworth ya fara aikawa da sakon tes daga kwamfutarsa zuwa wayar salular
abokinsa mai suna Richard Jarvis, a ranar 3 ga watan Disamba, shekarar
1992[10]. Su
kansu masu kera wayoyin salula ba a barsu a baya ba. Domin daga cikin wayoyin salula sama da
biliyan 1.3 da aka turo kasuwa a shekar 2010, kamfanin Nokia kadai yana
da miliyan 453, biye da kamfanin Samsung mai miliyan 280, sai kamfanin LG
mai miliyan 116. Daga cikin wancan
adadi har wa yau akwai miliyan 51 da kamfanin ZTE ya turo, da miliyan 48
daga kamfanin Research in Motion (RIM) da ke kera wayoyi nau'in Blackberry,
sai kuma ragowan miliyan 437 da wasu kamfanoni suka turo kasuwa[11].
Yaduwar fasahar sakonnin tes da ke jikin wayoyin salula ko kadan
bai kashe wa fasahar Imel tagomashi da habaka ba. Domin adadin masu mu'amala da
fasahar Imel musamman a kasahen da suka ci gaba ya haura sosai. Bayan samuwar
wannan tsari a kwamfuta, akwai shi a jikin wayoyin salula. Don haka fasahar
Imel na ci ne daga akushi biyu.
Bayanan da suka gabata duk suna mana ishara ne ga irin halin da
duniya ke ciki na dunkulewa ta bangaren gamayya da sadarwa. Domin a yau kusan
duk abin da ba a tunanin za a iya aiwatar da sadarwa da shi, sai ka ga ana
yi. Bayan sadarwa da ke yiwuwa tsakanin
shahararrun kayayyakin fasahar sadarwa irinsu kwamfuta da wayar salula, a yanzu
ana aiwatar da sadarwa tsakanin kwamfuta da talabijin, tsakanin kwamfuta da na'urar
dumama abinci, tsakanin wayar salula da na'urar sauraren wakoki, tsakanin wayar
salula da talabijin, har wa yau, na san masu sauraro za su yi mamakin jin cewa
hatta agogon da ake daurawa a hannu duk ana aiwatar da sadarwa ta hanyarsa. Daga cikin fasahohin sadarwar da suka yi ruwa
suka tsaki wajen aiwatar da hakan kuwa akwai fasahar Bluetooth, da
fasahar tauraron dan adam masu aiwatar da sadarwa, musamman fasahar GPS na
kasar Amurka, da fasahar GLONASS na kasar Rasha, da fasahar Galileo mai
dauke da tauraron dan adam 24 da kasashen Turai suka cilla sararin samaniya,
sai wadanda kasar Sin ta harba 'yan kwanakin baya, don killace kanta da wannan
tsari na sadarwa mai inganci. Bayan wadannan, akwai taurarin dan adam masu
cilla shirye-shiryen kafafen talabijin (Satellite Channels) sama da 300
a sararin samaniya suna shawagi. Sannan ga
babban tauraron dan adam na giza-gizan sadarwar duniya ta Intanet mai suna SAT3.
Bunkasar Fasahar Sadarwa a Najeriya
Kafin isowar fasahar Intanet kasar nan, fasahar Imel ta gabace ta.
Wannan ya faru ne saboda duk da cewa dukkansu su fasahohi ne na sadarwa da a
galibin lokuta suke zama wuri daya, amma kowanne ka'idar gudanuwarsa sun sha
bamban da na dan uwansa. A shekarar 1990
ne jami'ar Mc Master da ke kasar Kanada ta jona jami'ar Ilorin na jihar
Kwara da hanyar sadarwa ta Imel. Daga
jami'ar Ilorin kana iya aikawa da sakonnin Imel zuwa kasashen duniya. To amma
mutum nawa ma ya san abin da wannan fasaha take nufi balle alfanun da ke
tattare da ita? Don haka ba wanda ya san
ana yi, wai kunu a makwabta. Zuwa shekarar 1993 sai gwamnatin tarayya, ta
hanyar hukumar sadarwa ta jona kasar da babbar tafarkin sadarwar fasahar Imel,
watau Post Office Protocol 3 (POP3), wadda babbar hanya ce mai dauke da
ka'idar sadarwar aikawa da karban sakonnin Imel, daga Najeriya zuwa kasar Amurka. Sai dai wannan ka'ida an jona ta ne da
Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke Legas, watau Yabatech. Har zuwa wannan lokaci dai fasahar
Intanet bata leko kasar nan ba, sai shekarar 1997, sanadiyyar wani kamfanin mai
da ya bude reshensa a Kaduna da Fatakwal.
Wannan kamfani ya mallaki kwamfutoci, kuma suna dauke da fasahar
Intanet, ta amfani da makalutun sadarwa, watau Internet Modem. Daga nan ne kadai ake iya mu'amala da
fasahar Intanet a dukkan fadin kasar nan[12].
Zuwa shekarar 1998 sai aka fara samun kamfanonin sadarwar Intanet
masu zaman kansu. Kamfanin farko shi ne Hyperia,
wanda ya bude ofishi a Kaduna, kuma yake jona kwamfutoci da fasahar Intanet
ta hanyar makalutun sadarwar tarho, watau Dial-up kenan. Daga nan sai hukumar gwamnatin tarayya watau NITEL
ta bude kafar bayar da lasisin bude ire-iren wadannan kamfanoni da kuma
mashakatar tsallake-tsallake, watau Cyber Café, a shekarar 1999. A shekarar ne ta bayar da lasisi wajen 40 ga
masu bukata, amma galibinsu a biranen Legas ne da Kaduna. A wannan shekarar ne dai fasahar Intanet ta
samu isowa Kano birnin dabo, kuma akwai tabbacin cewa ta sanadiyyar wannan
kanfani ne mai suna Hyperia[13].
Daga nan aka samu masu bude wuraren mu'amala da fasahar Intanet a manyan
biranen kasar nan, irinsu Legas, da Kaduna, da Kano, da Jas, da Abuja, da
Fatakwal da sauransu.
A daidai wannan lokaci fannin sadarwar tarho bai bunkasa ba. Domin layukan
tarho duk na gida ne (Land Lines), kuma babu yanayin sadarwa mai
inganci. Duk da cewa akwai kamfanin
sadarwar wayar tarho na Intercellular da ke aiwatar da sadarwa ta wayar
iska, amma fannin bai bunkasa ba sai cikin shekarar 2000, sadda gwamnatin
tarayya ta bude kafar zuba jari a fannin.
Daga nan ne aka samu kamfanonin sadarwar tarho da muke dasu a
yanzu. A halin yanzu, kamar yadda
bayanai suka nuna a baya, akwai layukan tarho masu rai sama da miliyan 90 a
kasar nan. Wannan adadi ya dada
taimakawa wajen yaduwar sauran fasahohin sadarwa musamman fasahar Intanet, da
fasahar Imel, da fasahar Infra-red, da fasahar Bluetooth da dai
sauran makamantansu. Ba wannan kadai ba,
an samu bunkasar tsari da ingancin sadarwa a bangaren fasahar tauraron dan
adam. Wannan yayi sanadiyyar habaka wannan fanni mai muhimmanci da tasiri, inda
a yanzu kusan galibin jama'an da ke birane da kauyuka sun mallaki wayar tarho.
Sanayya kan kwamfuta ya karu, haka ma'adanan bayanai irinsu Flash Drive, da
Memory Card, da Hard Disk, da nau'ukan faya-fayan CD da DVD
duk sun zama 'yan gari a idon jama'a.
Dalilan Yaduwar Fasahar Sadarwar Zamani
Kayayyakin fasahar sadarwar zamani suna da saurin yaduwa cikin
jama'a. Daga cikin dalilan da ke haddasa haka akwai saukin mu'amala; ko baka
iya karatu ba kana iya sarrafa wayar salula misali, ta hanyar aiwatar da kira,
da amsa kira da dai sauransu. Ba wayar salula kadai ba, duk galibin kayayyaki
da hanyoyin fasahar sadarwa haka suke.
Kuma tunda galibin dabi'ar dan adam ta fi karkata zuwa ga sauki, sai
hakan ya basu saurin yaduwa a kasashen duniya. Abu na biyu shi ne saukin
farashi. A farkon bayyanar wayar salula
Najeriya suna da dan karen tsada. Amma ta dalilin yawaitansu a kasuwa daga
kamfanoni daban-daban, an samu saukin farashi, wanda hakan ya bayu zuwa ga
shahararsu a tsakanin jama'a. Sannan
samun na'uka daban-daban ma ya kara musu yaduwa. Domin kowane irin matsayi kake, ko wane irin
dandano kake dashi, akwai irin waya da ta dace da kai. Sai tsarin zumunci a tsakanin kayayyakin sadarwa,
watau Network Convergence. A
yanzu kana iya aiwatar da sadarwa tsakanin kwamfuta da wayar salula, ta hanyar
sakonnin tes, ko Imel, ko aikawa da hotuna masu motsi, ko daskararru. Dukkan wannan shi ma ya taimaka wajen yaduwar
fasahar sadarwa a duniya baki daya. A
daya bangaren kuma akwai bunkasar binciken ilmi kan hanyoyin sadarwa a
duniya. Dukkan abin da wayar salula za
ta iya aiwatarwa, ko kwamfuta, ko wani tsari da wani hanyar sadarwa ke amfani
dashi wajen aiwatar da sadarwa, duk hakan ya samu ne sanadiyyar binciken ilmi
da malamai ke yi a jami'o'i da kamfanonin sadarwa a warwatse a duniya. Sannan akwai samuwar hanyoyin sadarwa masu
inganci, ta amfani da fasahar tauraron dan adam, wanda wannan ya dada taimakawa
wajen samun yanayin sadarwar tarho mai inganci a duniya. Hatta a Najeriya an samu ci gaba a wannan
fanni, idan muka kwatanta da yadda yanayin yake a farkon bayyanar wannan tsari.
Idan muka koma bangaren fasahar Intanet za mu ga cewa ta fi dukkan
sauran hanyoyin sadarwa shahara da tasiri a tsakanin jama'a. Hakan ya faru ne sanadiyyar wasu dunkulallun
dalilai guda uku[14];
dalilin farko ya riga ya gabata, watau saukin mu'amala. Sai dalili na biyu,
watau game duniya. Duk inda kake kana
iya mu'amala da fasahar Intanet muddin ka mallaki na'urar da za ta baka daman
hakan. Kana iya shiga ta kowace kafa, ka
fita ta kafar da kake so, sannan a lokacin da kake so; babu kaidi. Dalili na karshe shi ne, dangane da abin da
ta kunsa, fasahar Intanet wata jakar magori ce; duk abin da kake nema yana
ciki. Daga warakar jahilci zuwa warakar
lafiyar jiki, duk akwai. Daga sana'a zuwa neman aiki, duk akwai. Daga zumunci
zuwa nazarin ilmi, duk akwai. Haka idan
ka koma bangaren nau'in hanyoyin sadarwa – daga talabijin, zuwa tsarin wayar
tarho, da rediyo, da tasoshin tauraron dan adam – duk akwai su a cikin
Intanet. Intanet jakar magori ce, duk
abin da kake nema akwai a cikin Intanet. Dukkan wadannan sifofi da dabi'u na
cikin abin da suka haddasa yaduwa da bunkasar harkar sadarwar zamani a duniya
baki daya.
Abu na karshe da ya dada taimakawa wajen yaduwar wadannan hanyoyi
da kayayyakin sadarwa a duniya akwai ingancin ka'idojin kimiyyar sadarwa da
wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke taimakawa wajen samarwa. A bangaren Intanet akwai kungiyar Internet
Corporation for Assigned Names and Numbers (ICANN) wacce ke da alhakin
samar da adireshin gidajen yanar sadarwa a Intanet. Sai kungiyar Internet Engineering Task Force
(IETF) wacce ke da alhakin samar da ka'idojin da fasahar Intanet ke
gudanuwa a kansu a cikin kwamfuta, irinsu IP Address da sauransu. Sannan akwai kungiyar World Wide Web
Consortium (www3) wacce ke da alhakin samar da ka'idojin habbaka shafuka da
gidajen yanar sadarwa da tsarin isa gare su cikin sauki, a kwamfuta ne ko a
wayar salula. A bangaren sadarwar wayar
tarho kuma akwai kungiyar International Telecommunication Union (ITU). Ita kuma aikinta shi ne habbaka tsari da
yanayin sadarwar tarho a duniya baki daya.
Bayan wadannan akwai wasu kungiyoyin kuma a bangaren kerawa da tsara
na'urorin sadarwa da lantarki. Dukkan
wadannan sun taimaka gaya wajen samar da inganci, da shahara, da kuma gamewa ga
kayayyaki da hanyoyin fasahar sadarwar zamani.
Fa'idojin Fasahar Sadarwa Ga Al'ummar Najeriya
Kamar sauran al'ummomin da ke wasu kasashe, al'ummar Najeriya na
amfana da kyawawan tasirin fasahar sadarwar zamani, wanda kuma wannan ya dada
taimakawa wajen inganta zamantakewa a tsakaninsu. Abu na farko shi ne fa'idar sadarwa, abin da
a baya ya ta'azzara, sanadiyyar rashin yaduwar hanyar sadarwa da rashin ingancin
yanayinsa. Sadarwa a yanzu abu ne mai
sauki; ba wai a tsakanin al'ummar kasar kadai ba, hatta zuwa wasu kasashe duk
dan Najeriya na iya aiwatar da sadarwa. Domin
a halin yanzu tsarin fasahar sadarwar tarho ya game duniya. Kashi 90 cikin 100
na kasashen duniya duk suna aiwatar da sadarwa a tsakaninsu. Wannan tsari ya taimaka har wa yau wajen
neman bayanai da nazarin ilmi. Ta hanyar
Intanet samun bayanai ya sawwaka. Kana
iya gabatar da binciken ilmi, ka tantance bayanan da kake so, ka rubuta abin da
kake son rubutawa ba tare da ka je dakin karatu ba a jami'arku; duk ta
albarkacin Intanet. Har wa yau ta
wadannan hanyoyin sadarwa harkokin da'awan addini musamman na Musulunci sun
habaka. Daga wayar salula zuwa kwamfuta, duk kana iya samun bayanan shiriya kan
addini, kana iya aika fatawa, zuwa ga wani malami da ke wata uwa duniya, ya
aiko maka da amsa nan take ba tare da bata lokaci ba.
A daya bangaren kuma akwai tsarin karatu da karantarwa, akwai
tsarin neman magani ko waraka na bangaren lafiya, duk ta hanyar Intanet. Akwai
hanyoyin neman aiki, da hanyoyin sana'o'i daban-daban duk ta Intanet. Daga gidanka kana iya yada manufofinka ta
hanyar Intanet ko wayar salula, kamar yadda 'yan siyasa ke yi a lokutan
zabe. Kana iya mu'amala da hukumomin
gwamnati; musamman makarantu. Domin a
yanzu galibin makarantun gaba da sakandare da ke Najeriya duk sun mallaki
shafin Intanet, inda za ka je ka nemi bayani kan makarantar, da yadda ake
daukan dalibai, sannan kana iya yin rajista a matsayinka na sabo ko tsohon
dalibi, duk ta wannan kafa. Bayan dukkan
wadannan, kana iya yankan tikitin jirgi a Najeriya ta hanyar Intanet.
A bangaren wayar salula an samu ayyukan yi musamman ga masu gyara
wayar salula, da masu sayar da su, da masu sayar da katin waya, an kuma samu
ayyukan yi ta bangaren kamfanonin sadarwa da ke da rajista a kasar. Har wa yau, fasahar Intanet ta samar da aikin
yi ga masu mashakatar lilo da tsallake-tsallake, watau Cyber Café. Sannan hukumar tarayya ta samu kudaden
shiga ta hanyar haraji da take karba daga wadannan kamfanonin sadarwa, da kuma
kudaden lasisi masu dimbin yawa da a baya ta karba. Wannan, kadan ne daga cikin fa'idojin da
fasahar sadarwar zamani ke samarwa ga al'umma.
Kalubale da Matsaloli Ga Al'umma
A daya bangaren kuma, yaduwar hanyoyin sadarwar zamani na da nasa
aibun ko kalubale, musamman ga matasa; ganin cewa su suka fi yawan mu'amala da
shi a kullum. Abu na farko dai shi ne
yawaitan bayanai a lokaci guda, a kuma muhalli guda. Wannan tsari, wanda tsohon Shubaban kamfanin Microsoft
watau Bill Gates, ya kira Information Overload, abu ne mai
cutarwa sosai. Domin idan ba kana da mizanin
tantancewa ba, sai ka rasa wanne za ka dauka.
Abu na biyu shi ne: wadannan hanyoyi da kayayyakin sadarwa suna yin
mummunar tasiri a kan kwakwalwa da tunanin dan adam, kamar yadda suke da tasiri
a kan dangantakarsa da 'yan uwansa ko abokanansa, da tasiri kan lafiyarsa, da
tasiri kan lokacinsa, da kuma tasiri kan manufofinsa – musamman idan ya kamu da
ciwon shakuwa dasu. Wannan kan kai shi
ga shiga wani hali da rayuwa cikin kawalwalniya, da gaugawar zuci ko
ci-da-zuci, da kuma dawwamammiyar kadaici.
Daga cikin kayayyaki da hanyoyin sadarwar da aka fi samun wadannan
matsaloli dai akwai kwamfuta, wacce ke dauke da fasahar Intanet, da wayar
salula, da kuma wasu masarrafan sadarwa da ke dandalin abota irinsu Facebook,
da MySpace, da NetLog, da Twitter, da sauran majalisun
tattaunawa na Intanet irinsu Yahoogroups, da Googlegroups da
sauran makamantansu.
A ire-iren wadannan majalisu da dandamali, akwai matsaloli masu
dama da suka hada da: cin mutuncin addini (musamman Musulunci), da leken asiri
saboda rashin sirri da ke tattare da su, da yawan gulma da hirar banza, da
haifar da tsana da hassada, da samar da gajiya da damuwa, da haifar da
kashe-kashe da ta'addanci ga mutunci, da batsa da ashararanci, da yawan shagala
da shagaltarwa, da kuma uwa uba munanan akidu da al'adu. Wadannan dunkulallun matsaloli ne da galibin
matasa musamman basu cika damuwa da su ba a yayin da suke ta'ammali da wadannan
masarrafai. Matasa kan kashe lokacinsu a dandalin Facebook musamman,
suna hirar banza mara alfanu; ka ji mutum na cewa "yanzu na tashi daga
bacci," ko "bacci nake ji," ko "abu kaza nake ci," ko
"wance ta bata min rai…" da dai sauran shirme marasa amfani. Maimakon fasahar Intanet ta taimaka mana
wajen amfani da kwakwalenmu mu fa'idantu da alherin da ke ciki, sai mu buge da
shashanci.
A daya bangaren kuma, wayar salula na da nata matsalolin. Da farko dai wayar salula taskar ajiya
ce. Wayar salula kundin tarihi ce. Wayar salula na'urar sauraran sauti ne. Wayar salula kafar mu'amala da fasahar
Intanet ce. Sannan kana iya amfana da
ita wajen aikawa da sakonnin tes masu fa'ida.
To amma mutum nawa ke haka daga cikin matasa? Da yawa daga cikinmu kan kwana muna hira da
'yan matanmu ne ko samarinmu. Mun dauka
kamfanin MTN ko Etisalat da ke bayar da wannan dama, wawaye
ne. Da yawa daga cikinmu wayoyin
salularmu na dauke ne da hotunan 'yan mata da samari. Da hotunan bidiyo na batsa ko na raha da
shashanci. Da sakonnin tes na soyayya
zalla ko na raha da shashanci. Da kuma masarrafai masu shagaltarwa irinsu Facebook,
da 2go; masu dauke kaso mafi tsoka na lokutanmu a rayuwa. Da wayar salula muke satar amsa a
makarantu. Galibi idan kaji dalibi ko
daliba na cewa "ance an ga wata," ko "muna jiran ganin wata
ne," to, za ka samu tana jiran a turo mata satar amsa ne a wayarta. Amma
ko kadan ta kasa amfana da wayar salularta wajen taskance darasin malami. Ta
kasa amfani da masarrafar 2go da ke cikin waya wajen tattaunawa da
sauran dalibai 'yan uwanta kan darussan da aka karantar da su.
Abu na gaba shi ne rashin tantance ingancin bayanai da ke Intanet
ko wadanda ake turo mana a waya. Da
zarar lokutan azumin Ramalana sun shigo, za ka ji sakonni na ta shiga wayarka
daga wajen 'yan uwa da abokan arziki.
Sau tari wasu daga cikin hadisan da ake turo su ba ingantattu bane ko
kadan. Musamman wadanda ake turowa kan
falalar watan Rajab, da falalar wanda ya sanar da wani shigan watan
Ramalana. Har wa yau, akwai matsala
wajen yadda muke ciro bayanai masu alaka da shari'a daga Intanet. Domin kuwa ba kowa bane yake da mizanin tantance
ingantacce daga mai rauni. Wannan ba
karamin kalubale bane a gare mu matasa.
A daya bangaren kuma, duk da habbaka da bunkasar wannan fanni a
Najeriya, har yanzu muna fama da matsalar rashin ingancin tsarin sadarwar
Intanet da rashin yanayin sadarwar wayar salula. Wannan ke sa mu kasa amfana da katin da muke
sa wa wayoyinmu, musamman ga wadanda suke karkara. Shi yasa kuma har wa yau, za
ka ga mutum daya da wayoyin salula guda uku rikis a hannunsa, ko ka ganshi da
wayar salula mai amfani da layuka uku, duk saboda tsoron rashin tabbacin da ke
tattare da yanayin sadarwar kamfanonin waya ne.
Idan akwai ingancin sadarwa, duk ba ka bukatar daukan wayoyi ko layuka
sama da guda daya.
Bayan dukkan wadannan, akwai matsalar tsaro. Domin sata ya koma kan wayoyin salula da
kwamfutoci yanzu. Galibin lokuta da
zarar barayi sun tsare mutane ba abin da suke kwacewa a farko sai
wayoyinsu. Haka idan mota aka gani da
jakar kwamfuta ko wayar salula, nan take ana iya fasa gilashin motar a
dauke. Wannan kalubale ne ga hukuma.
Hanyoyin Gyara da Ci Gaba
Wajibi ne ga matasanmu su koyi ladabin mu'amala da wadannan
kayayyaki da fasahar sadarwar zamani.
Abu na farko da ya kamata su sani shi ne, wadanda suka kirkiri wadannan
kayayyakin fasaha, duk da 'yancin da muke ganin yana tare dasu kayayyakin, dabi'arsu
da akidarsu da addininsu sun sha bamban da namu. Don haka wajibi ne mu koyi tarbiyya wajen
ta'ammali da lokaci, da ta'ammali da manufa. Domin idan ka kasa tantance manufarka a yayin
mu'amala da wadannan abubuwa, shi zai sa komai ka gani ka shagaltu da shi. Idan haka ta faru kuwa, za ka zama kamar yaro
a kantin alawa. Abu na gaba shi ne
tarbiyyar dabi'a da zuciya. Ma'ana, mu
zama masu kiyayewa cikin abubuwan da muke yi a wadannan wurare. Idan al'amura sun cushe maka, dole ne ka zama
mai neman shawara, musamman kan nau'ukan bayanan da aka aiko maka ta waya ko ta
Imel ko ka karanta a shafukan Intanet masu alaka da shari'a. Idan ba ka da mizanin tantancewa, ka nemi
shawara wajen kwararru.
Har wa yau, ka zama mai manufa a dukkan abin da kake yi. Wannan zai
sa ka ribaci lokacinka, da lafiyarka, da kwarewarka, da kuma ilminka. A daya bangaren kuma, wajibi ne ga iyaye su
rika lura da 'ya'yansu, su koya musu tarbiyya, ta yadda ko da ba su kusa da su,
za su kiyaye, su lazimci abin da yake daidai.
A karshe, yana da kyau Gwamnatin tarayya da na jihohi su kara kaimi
wajen tabbatar da samuwar ingantacciyar hanyar sadarwa ta amfani da fasahar
tauraron adam. Sannan su karfafi hukumomin
da ke da alhakin bunkasa wannan fanni, tare da samar da wutar lantarki mai
inganci a kasa baki daya, don dada sauke farashin sadarwa. Sannan ta samar da tsaro ga jama'a da
dukiyoyinsu, ta hanyar karfafa tsarin rajistan layukan waya, a karshe kuma ta
samar da Babbar Rumbun Babayanai na kasa, watau National Database, don
samar da kyakkyawan shugabanci a kasa baki daya.
Kammalawa
Daga bayanan da suka gabata, a tabbace yake cewa yanzu ne muka fara
cin gajiyar wannan fanni na fasahar sadarwar zamani. Da zarar hukuma ta taimaka wajen samar da
muhalli mai kyau, al'amura da zau dada inganta, a samu karin ci gaba.
[1] The
World in 2011: ICT Facts and Figures – www.itu.int
[2] World
Internet Users and Population Statistics, March 2011 – www.internetworldstats.com
[3] The
World in 2011: ICT Facts and Figures – www.itu.int
[4] Facebook
Users in the World, 2011 Q2 - www.internetworldstats.com
[5] The
World in 2011: ICT Facts and Figures – www.itu.int
[6] African
Telecommunication/ICT Indicators 2008: At a Crossroads – www.itu.int
[7] Nigeria
Mobile Market: Overview, Statistics, & Forecasts – www.budde.com.au
[8] ICT
Statistics Newslog: SMS - www.itu.int
[9] Are
We Digital Dummies? – www.cbc.co.ca/doczone
[10] Text
Messaging – http://en.wikipedia.org/wiki/text_messaging
[11] Global
Mobile Statistics 2011 – http://mobithinking.com/mobile-marketing-tools/latest-mobile-stats#
[12] Malam
Magaji Galadima, Kaduna, Najeriya.
[13] Fasahar
Intanet a Sawwake: Abdullahi Salihu Abubakar, 2009, Abuja, Najeriya.
[14] The
Death of Distance: Frances Cairncross, Harvard University Press, 2000.
Shafi na 95-98