Friday, September 28, 2007

Tsarin Sadarwa A Tsakanin Kwamfutoci (2)

Makon Jiya

A cikin kasidar da ta gabata makon jiya ne mai karatu ya samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, abinda a Turance ake kira Computer Networking. Bayan ‘yar gajeriyar gabatarwa, mun kawo bayani kan ma’ana da kuma nau’ukan tsarin sadarwan da ke tsakanin kwamfutoci, inda daga karshe muka nuna ma mai karatu cewa samun cikakkiyar fahimta kan irin tsarin da kwamfutoci ke sadar da bayanai a tsakaninsu ba abu bane mai sauki, musamman ma ganin cewa kashi sittin ko sama da haka na alakar da ke tsakanin ruhin kowace irin na’ura ta sadarwa da gangar-jikinta, ba alaka bace da za a iya gani a zahiri, sam. Don haka sai dai kawai a kwatanta ma mai karatu don ya samu kiyastaccen tsarin a kwakwalwansa. Amma duk da haka, wannan alaka na nan, kuma tabbatacciya ce. Wannan ma tasa muka kawo ka’idar “Black Box”, don yanke hanzari. Har wa yau, mun dan fara bayanai kan komatsen da ke taimakawa wajen wannan alaka a tsakanin kwamfutoci, inda muka ambaci kayayyaki da na’urori irinsu Fiber-Optic Cables, Coaxial Cables, Twisted Pair (dukkan nau’ukan ta), Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), Routers, Switches, Satellite Dish/Mast, da dai sauran karikitai. Wadannan su ne galibin abubuwan da mai karatu zai iya gani da idonsa, a yayin da aka hada kwamfutoci suke sadarwa ko Magana da junansu, wanda kuma hakan wani dan yanki ne kawai cikin tsarin alakar. To a yau zamu ci gaba da bayani kan ka’idojin da ke taimaka ma kwamfuta hada alaka da ‘yar uwanta, bayan samuwan wadannan komatse da bayanansu suka gabata makon jiya.

Ka’idojin Sadarwa (Network Protocols)

Bayan komatsen sadarwa na zahiri da muke iya gani, sai kuma ginannun ka’idojin da kowace kwamfuta ta mallaka a halittarta da aka halitta ta a kai tun ran gini. Muna yawan ambaton kalmar ka’ida a galibin lokuta kan abinda ya shafi kwamfuta, dole ce ta kawo haka, domin ka’ida, kamar yadda muka nuna a kasidar Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet, ba a rayuwa sai da ita; rayuwar nan mai kyau ce ko mummuna. Don haka ka’ida na iya zama kyakkyawa ko mummuna, amma dai dole ne a same ta a dukkan mu’amalar rayuwa. To haka abin yake a tsarin mu’amala ko sadarwan da kwamfuta ke yi da ‘yar uwanta. Ka’idar Sadarwa ko Protocol, a ilimin kwamfuta, na nufin “tsarin da kowace kwamfuta ke amfani dashi wajen mikawa da karban kowane irin sako ne tsakaninta da wata kwamfuta ko na’urar sadarwa.” Yadda ka san mutane na da irin nasu hanyar da suke bi wajen sadarwa; ya zama suna jin yare daya; sun fahimci manufar juna; ba matsala wajen karban sakon. Duk da yake wasu lokuta akan samu wani baya jin yaren wani, amma akan iya sadarwa ta amfani da luggan bebaye ko kurame. Amma a kwamfuta haka baya yiwuwa. Dole ne kowace kwamfuta ta fahimci yaren da mai aiko mata sako ke yi, idan ba haka ba, babu sadarwa. Wannan tasa aka gina kwamfutoci akan yardaddun ka’idojin sadarwa a duniya. Wannan na nufin duk inda ka samu kwamfuta, to zaka samu tana jin yaren ‘yar uwanta, muddin lafiyarta kalau ne ba zazzabi mai tsanani take ba. Hukumar da ke lura da gina wadannan ka’idoji kuwa ita ce International Standard Organisation (ISO) da ke kasar Amurka. Hukuma ce da ta tattaro masana kan harkan kwamfuta da manhajanta, da kuma kungiyoyi ko kamfanonin sadarwa na duniya. Idan wani kamfani ya kirkiri wata Ka’ida da yake ganin zai taimaka wajen habbaka sadarwa a tsakanin kwamfutoci, sai ya mika ma wannan hukuma, ita kuma ta yi nazari. Da zaran an samu amincewa, sai ayi maza a sanar da kamfanoni masu kera kwamfutoci da karikitanta, da kuma masana ko magina babban manhajan kwamfuta (System Programmers), don su dauki wannan ka’ida don yin aiki da ita kan dukkan abinda zasu gina ko tsara mai alaka da kwamfuta, nan gaba. Su wadannan ka’idoji ginannun tsare-tsare ne da ake shigar da su cikin kwakwalwan kwamfuta, wanda muddin tana tunani, da zaran wani bukata wanda ya danganci wannan ka’ida ya iso gareta, nan da nan zata fahimta, ta kuma yi abinda ake son ta da yi ba tare da bata lokaci ba.

Matakan Sadarwa Tsakanin Kwamfutoci

Kamar yadda bayani ya gabata makon da ya wuce, kafin a samu sadarwa tsakanin kwamfuta, dole ne a samu kwamfutoci a kalla biyu; daya mai mikawa, dayan kuma mai karban bayanin. Ko kuma daya mai neman bayani, daya kuma mai bayarwa. Muka ce a kowane hali ake, wacce zata bayar da bayanai ita ake kira Remote Host, ko Server, ko Terminal ko kuma Workstation. Ita ce mai dauke da hanyoyin mika bayanai da taskance su. Dayar kuma, wacce ke neman a aiko mata, akan kira ta Client, a turancin Kwamfuta. Don haka, da zaran Remote Host ko Server ta aiko da sako zuwa wata kwamfutar, to akwai Matakai ko Zanguna guda bakwai da sakon zai bi. A duk zangon da ya zo, za a masa alama don a sheda shi a zangon da zai tarar a gaba, haka haka har ya isa zuwa kwamfutar da aka aika shi ba tare da samun matsala ba. Wannan tsari na lika ma bayanai ko sakonni alama, a hanyarsu ta zuwa inda aka aika su, shi ake kira Data Encapsulation a turancin Kwamfuta. Kwamfutar da ke aikawa da wannan sako, zata kacalcala sakon ne zuwa tsibi-tsibi, kowane tsibi (abinda masana kwamfuta suke kira Datagram, jam’insu shi ake kira Packet Switch) zata bashi alama, kamar yadda bayani ya gabata a sama. Sannan ta turo su ta wadannan zanguna guda bakwai, wadanda ake kira Layers a turance. Tsarin da ke kunshe da wadannan zanguna bakwai shine The Open Systems Interconnect Model, ko kace OSI a takaice. An kuma kirkiri wannan tsari ne cikin shekarar 1981. Amma kafin nan, tsarin TCP/IP Model ake amfani dashi, wanda ya kunshi zanguna hudu ne kacal, duk da yake akwai dukkan ka’idojin da ake bukata a ciki. To a wadannan matakai ne ake samun dukkan ka’idojin sadarwa tsakanin kwamfutoci, watau Networking Protocols ko kuma Standards. Ina ganin zai dace mu yi takaitaccen bayani kan dukkan matakan da galibin ka’idojin da kowanne ke kunshe dashi, don mai karatu ya fahimci yadda lamarin yake.

The Open Systems Interconnect Model (OSI)

Da zaran kana son aikawa da sako daga wata kwamfuta zuwa wata, zangon farko da sakon zai fara kasancewa ciki ko biyowa ta cikinsa, shine mataki na bakwai; Layer 7, watau Application Layer. Wannan shine matakin manhajan da kake son aikawa da sakon ta hanyarsa. A wannan mataki ne zaka shigar da sunan wanda kake son aika masa da sakon, ko sunan kwamfutar da kake son aika mata da sakon, da kuma matanin sakon. Application Layer ne ke da hakkin tabbatar da cewa sakonka ya samu wanda ka aika masa ta hanyar adireshin da ka shigar, domin wannan zango ne ke dauke da ka’idojin da ke wannan aiki. A wannan zango na Layer 7 akwai Ka’idoji irinsu: File Transfer Protocol (FTP) – ka’idar da ke taimakawa wajen sauko da jakunkunan bayanai daga wata kwamfutar zuwa ko daga wani gidan yanar sadarwa mai dauke da bayanai zuwa kan kwamfutar ka, ko kuwa dora bayanai a gidan yanar sadarwa. Wannan shine shahararren aikin ta, amma da bayyanar ka’idar Hypertext Transfer Protocol (HTTP), sai kasuwar FTP ta mace kurmus. Yanzu galibin aikin da ake yi da masarrafar FTP bai wuce dora jakunkunan bayanai zuwa gidajen yanar sadarwa ba, don masu lilo da tsallake-tsallake su rinka isa garesu. Duk bayanan da zaka ta cin karo dasu a gidajen yanar sadarwa, da ka’idar File Transfer Protocol ko FTP aka dora su cikin kwamfuta. Sai kuma ka’idar Trivial File Transfer Protocol (TFTP), wacce kanwar FTP ce. Daga cikin ka’idojin da ke wannan zango har wa yau akwai Domain Name Service (DNS), wacce ke taimakawa wajen nemo sunan kwamfutar da za a isar da sakon gareta, ta hanyar adireshin da ka bayar lokacin aikawa da sakon. Sai ka’idar Simple Mail Transfer Protocol (SMTP), wacce ke taimakawa wajen aikawa da sakonnin Imel daga kwamfutar da ka aika zuwa uwar garken da ke dauke da jakar wasikar wanda ka aika masa. Muhimman ka’idojin sadarwan da ke wannan zango kenan. Da zaran ka aika da sakon, sai Layer 6, watau Presentation Layer. Wannan zango ne zai juya sakonka daga haruffa ko bakaken da kayi amfani dasu zuwa yaren kwamfuta, wanda ba wanda zai iya fahimta, ko da kuwa wani ya tare sakon a hanya. Wannan aiki shi ake kira Encording. Daga nan kuma ya takura sakon (Compress) don kankanta shi. A wannan zango akwai ka’idoji irinsu Motion Picture Experts Group (MPEG), Joint Photographic Experts Group (JPEG), Tagged Image File Format (TIFF), wadanda ka’idoji ne na takura mizanin hotuna wajen aikawa dasu. Sai kuma ka’idar Hypertext Transfer Protocol (HTTP), wacce ke sadar da kwamfutar da kake kai da wacce ke dauke da gidan yanar sadarwan da kake son ziyarta, ta hanyar Rariyar Lilo (Browser). Sai kuma zango na gaba, Layer 5, ko Session Layer, wacce ke taimakawa wajen hada alaka tsakanin kwamfutar da ke aikawa da sakon da wacce zata karba. A wannan zango ne kwamfutarka ko wacce ke aikawa da sakon zuwa wata kwamfutar, zata san ko kwamfutar da ke karban sakon a shirye take ko a a. Wannan zangon ne ke tura sakon gaba, zuwa zangon gaba, bayan gama kintsa shi. Akwai ka’idar Structured Query Language (SQL), mai taimakawa wajen saukake neman bayanai daga rumbun kwamfutar da ke mikowa, ba tare da matsala ba. Daga nan sai Layer 5, watau Transport Layer, wanda ke gyatta sakon ka yadda suka zo kimtsi-kimtsi, wani na bin wani, don tabbatar da cewa wani bangare bai makale a zangon baya ba. Shahararriyar ka’idar da ke wannan zango ita ce ta Transmission Control Protocol (TCP), wacce ke sawwake mika sakonni, musamman ma shafukan yanar gizo, daga wata kwamfutar zuwa wata, cikin sauki. Sai kuma zangon gaba, Layer 3, watau Network Layer, zangon da ke lura da tsarin tsibin sakonnin da ke tafe, ya tabbatar babu wata mishikila cikin tsarin da aka masa a zangon baya, da kuma dora masa adireshin mai aikawa; mutum ne ko kwamfuta, don mai karban sakon ya san daga inda sakon ya fito. Nan ne ake da ka’idar Internet Protocol (IP), wanda zai damfara adireshin kwamfutar da ke aikowa da sakon. Adireshin kwamfuta shine lambobinta, wanda dashi ake iya sheda ta. Ana kiran sa IP Address, kuma da wadannan lambobi ne ake iya gane kowace kwamfuta a ko ina take. Ko da kuwa an juya wadannan lambobi ne zuwa adireshin gidan yanar sadarwa (misali a ce http://www.google.com), idan aka aiko sako daga wannan gidan yana, kafin ya fice, sai wannan zango na Network ya damfara lambobin kwamfutar a jikin sakon, don sanar da kwamfutar da ke karban sakon cewa “wance ce ta aiko wannan sako”, misali. Sai kuma Address Resolution Protocol (ARP), wacce aikinta ne ta tabbatar da cewa sakon ka ya isa zuwa adireshin da ka ayyana, ta hanyar tabbatar da lambobin kwamfutar da ke karban sakon, watau IP Address kenan. Sakon ka na wuce wannan zango sai Layer 2, watau Data Link Layer. Wannan shine zangon da zai karbi tsibe-tsiben sakon ka, tare da bayanan da ke like a jikinshi, ya kuma juya shi zuwa yanayin hasken lantarki, tunda ya wuce muhallin da zai ci gaba da zama a dabi’ar farko. Wannan yanayi na wutar lantarki kuwa shi ake kira Bits. Shahararren ka’idar da ke wannan zango kuwa ita ce Point-to-Point Protocol (PPP), wacce jaruma ce wajen mika sako daga wannan zango na kwamfutoci zuwa wannan ta hanyar wutar lantarki. To fa, sakon ka na wuce wannan zango sai zangon karshe, watau Layer 1, ko kace Physical Layer, wacce ke daukan wannan sako naka daga yanayin wuta ko hasken lantarki, ta bi dashi cikin wayoyin kebul da mai karatu ke gani a like a jikin kwamfuta, idan a tsarin gajeren zangon sadarwa ne, watau Local Area Network (LAN). Sai ya zarce zuwa na’urar Switch, wacce zata tura ma kwamfutar da aka aika mata. Idan kuma a tsarin faffadan zango ne, irin su Internet Connection ko kuma Wide Area Network (WAN), sai ta mika sakon ga na’urar Router, wanda zai dauke shi ta hanyar wayar iska a irin yanayin sakonnin rediyo, watau Radio Waves, don sadar dashi ga tauraron dan Adam (Satellite Dish ko Mast), ko kuma na’urar Wireless Frequency Radio (Wi-Fi). Da zaran ya iso nan, sai a mika ma wani na’uran Router da ke zangon da kwamfutar take, don ya cilla ma kwamfutar da aka aiko mata, ko ta bukata. Idan mai karban sakon na jiranka ne, nan take zai gani. Idan kuma bai ma sani ba, to duk lokacin da ya budo jakar Imel dinsa, ko ya budo kwamfutarsa, idan ba Imel bane, zai ga sakon, dauke da cikakkun bayananka, da lokacin da ka aiko da sauransu. To amma ta yaya hakan zai kasance, bayan an luguiguita sakon, an kacalcala shi zuwa wani yanayi a kwamfutar da ya fito?

Wannan abu ne mai sauki! Da zaran sakon ya bar kwamfutarka zuwa kwamfutar da aka aike shi, zai fara cin karo ne da zangon Physical Layer, wanda zai jujjaya shi, ya tabbatar garau sakon yake, sai ya cilla ma zangon Data Link Layer, yayi nashi. Sai zangon Network Layer, wanda zai tabbatar da ingancin lambar kwamfutar da ta aiko da sakon, in ba matsala, sai zangon Transport Layer. Da zaran ya wuce nan, sai zangon Session Layer, wanda zai lika ma sakon bayanan da zasu tabbatar da mazuwansa; watau adireshin mai aikowa, da na kwamfutar da ta aiko, da lokaci da sauransu. Sai zangon gaba, Presentation Layer, wanda idan mai karatu bai mance ba, munce a nan ne ake canza ma sako yanayi, tare da kacalcala shi tsibi-tsibi. To idan ya zo nan a wannan siffa, sai wannan zango ya mayar dashi zuwa cikakken sako, a irin yanayin da aka aiko shi. Idan hoto ne ko zane, zai mayar dashi zuwa yanayinsa na asali, in ma takura hoton yayi, zai bude shi ya bashi ‘yancinsa na asali. Ya shirya sakon dai tsaf, don mika ma zangon karshe, watau Application Layer. Wannan zango zai karbi sakon sai ya adana, idan mai karba ya budo, sai kawai ya samu sakon garau, kamar yadda aka aiko masa. To amma idan akwai matsala tsakanin lokacin da mai aikowa ta aiko kafin mai karba ta karba, da zaran sakon ya fara isa kwamfutar da zata karba, sai ayi masa birke mai kyau, a kuma mayar dashi zuwa inda ya fito. Babu kira, mai kuwa zai ci gawayi? A hanyarsa ta komawa ne, zangunan zasu lika masa bayanai na irin matsalar da ya samu a hanya. Allah Sarki Malam Muttaka, a koma gida, sai wani lokaci!

Kammalawa

Wannan a takaice shine abinda zamu iya kawowa. Ina kuma fatan mai karatu ya cizgi wani abu. Idan ma bai cizga ba, to duk kada ya damu. Komai da lokacinsa. A mako mai zuwa kuma zamu kawo bayani ne kan Manhajan Wasikar Hanyar Sadarwa (Imel), da dukkan ka’idojin da take tattare da su. In ma da hali, zamu kawo gajeren bayani kan shahararru daga cikin gidajen yanar sadarwa masu dauke da wannan manhaja, da irin siga ko tsarin da kowanne ke dashi. Ina mika sakon godiya da ban gajiya ga dukkan masu karatu. Allah Yai mana gam-da-katar cikin wannan wata mai alfarma, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa,

Garki II, Abuja. 08034592444

Fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

Monday, September 24, 2007

Tsarin Sadarwa A Tsakanin Kwamfutoci (Computer Networking) #1

Mukaddima

Makonni kusan hudu da suka gabata na sanar da masu karatu cewa akwai wasu tambayoyi da aka rubuto masu bukatar bincike don samun gamsassun amsoshi. A nan take nayi alkawarin samun lokaci do fayyace mana zare da abawa kan abinda ya shafi ire-iren wadannan tambayoyi. Cikin ire-iren tambayoyin da nake samu akwai wanda ya danganci tsarin da kwamfutoci ke “Magana” ko “mu’amala” da junansu wajen mikawa da kuma karban bayanai, musamman a gajeren zangon Intanet, watau Local Area Network (LAN), a takaice. To, maimakon gajarta bayani kan wannan tsari, sai na ga dacewan tsawaitawa, iya gwargwadon hali da lokaci da kuma shafi, don kawo gamammen tsarin da kwamfuta (da ma sauran karikitan sadarwa) ke sadar da bayanai a tsakaninsu. Wannan tsarin sadarwa kuma ba a kan bayanai na rubutu kawai ya tsaya ba, a a, har da abinda ya shafi sauti, da hotuna masu motsi da marasa motsi. Sai dai kafin mu shiga wannan fage, ina son ba mai karatu hakuri, domin kuwa zai ta cin karo ne da wasu bakin kalmomi, ya Allah na turanci ne ko na Hausa, wadanda na kawo su ne don saukake masa fahimta kan sakon da nake son isarwa a wannan mako da ma makonni biyu ko uku masu zuwa. A yau zamu yi bayani ne kan tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci, wanda ya shafi dukkan hanyoyin, kamar yadda mai karatu zai karanta a kasa. A mako mai zuwa kuma mu jero bayanai kan tsarin ka’idar manhajan wasikar hanyar sadarwa watau Imel, da yadda kwamfutoci ke aikawa da kuma karban rubutattun sakonnin da muke rubutawa muna aikawa. Sai a mako na sama kuma in muna raye, mu samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin wayoyin salula da na’urorin kamfanonin da ke sadar da masu wayoyin. Wadannan bayanai zasu taimaka mana gaya wajen sanin abubuwa da dama kan abinda ya shafi hanyoyin sadarwa na zamani. A yanzu zamu shiga filin daga:

“The Black Box Theory”

Kafin mu dukufa, yana da kyau mai karatu ya san wani abu dangane da tsarin da dukkan karikitai da hanyoyin sadarwa na zamani ke gudanuwa a kai. Wannan zai taimaka masa wajen rage yawan tambayoyin da ka iya haifuwa cikin kwakwalwan sa a yayin da yake karanta wannan bayani da ke tafe. Domin duk yadda na kai da fayyace bayanai, zai dan yi wahala mai karatu ya samu cikakkiyar gamsuwa ko fahimta, dangane da abinda ake Magana a kai. Don fahimta kam za a fahimta, iya gwargwado. Dalilai biyu ne suka haddasa haka; na farko shine ganin cewa da harshen Hausa bayanan ke zuwa, wanda kuma ba shi bane asalin harshen da na karanto ilimin daga gareshi. Na biyu kuma, ko da ma da turancin ne, wasu abubuwa ba zasu taba bayyana maka a fili ba, ko da kuwa wadannan na’urori a gabanka suke, ina maka bayani. Wannan tasa na kawo ka’idar “Black Box”, don rage mana wahalar neman cikakkiyar fahimta. Kuma ga abinda wannan ka’ida ke nufi.

Na tabbata masu karatu sun taba gani ko ma sun mallaki kayayyakin sadarwa irin su Talabijin ko Radiyo ko wayar tafi-da-gidanka (wayar salula) ko wayar tangaraho (landline) ko kuma kwamfuta ma a takaice. Idan bamu mallaki duka ba, to a takaice mun mallaki wasu ko wani daga cikinsu. In ma bamu taba mallakan kowanne ba, to a kalla dai mun taba sarrafa wani daga ciki. Wadannan kayayyakin sadarwa, muna sarrafa su ne ta hanyoyin da makerinsu ya tanada mana, mafi sauki; daga abin murdawa zuwa matsawa ko dannawa ko kuma turawa – sama ko kasa. Kuma galibi bamu damu da sanin tsarin yadda injin su yake ba. Idan ma mun sani, to bamu san me da me ke haduwa, abu kaza da kaza su kasance ba. Da zaran kana amfani da wayar salula sai ta lalace, ba abinda ya dame ka, daukawa zaka yi zuwa wajen mai gyara. Amma idan ba lalacewa tayi ba, ba ruwanka da cewa “me da me aka kera injin wannan na’ura dashi”; in har zaka kunna Talabijin ka ya kama Magana da nuna maka hoto, ko ka kunna rediyonka ya fara Magana har ka kama tashoshi, ko ka kunna kwamfutarka ta kama aiki, ba ruwanka da abu kaza ne ya kasantar da kaza, ko kadan. Kuma da zaka bude injin, ba abinda zaka gani sai wayoyi da sauran karikitai. Ba ruwanka da tambayar “ta yaya aka yi wadannan ‘yan kananan wayoyi ke jiyar da ni Magana daga wannan akwatin rediyo, ko ganar da ni hotuna daga wannan talabijin? Wannan tunani, mai sa damuwa da zahirin fasaha ko na’ura kadai, ba tare da sanin yadda na’urar ko fasahar ke sarrafa kanta ba a fasahance, shi ake kira “The Black Box Theory”. Kuma shine tunanin da ke kwakwalwan kusan dukkan mai amfani da kayayyaki ko na’urar sadarwa na zamani a yau. Kai dai a ci baure, amma ban da tona cikinsa. A iya tunani na, wannan shi ne Karin maganan da za a iya kwatanta shi da wannan ka’ida ta “Black Box”, a takaice.

To me yasa galibi ake da wannan irin tunani? Saboda alaka iri biyu ce tsakanin kowace irin na’ura da mai sarrafa ta. Alakar farko ita ce wacce ke tsakanin na’urar da karan kanta; ma’ana, tsakanin ruhin na’urar, wanda ke sarrafa gangar-jikin da mai mu’amala ke iya gani har take bashi sha’awa. Wannan tasa dukkan iliminsa na mu’amala ya takaita a nan. Sai alakar da ke tsakanin sa da na’urar, wanda ke nuna masa tana da lafiya ko babu. Idan na’urar na da lafiya, wannan shine abinda yake so. Amma da zaran ta fara zazzabi, to ilimin sa ya kare. Sai dai yayi kirdajen alamun da take nuna masa. Kuma shine abinda zai gaya ma mai gyara, don a binciko matsalar, don gyarawa. To a takaice dai irin wannan boyayyar alaka da ke tsakanin na’ura da gangar-jikinta, shine abinda yafi wahalar fahimta ga mai amfani da na’urar, domin kuwa ba wani abu bane da zai iya gani a bayyane. Wanda kuma kashi sittin cikin dari na alakar da ke tsakanin na’ura da ruhi ko masarrafan da ke sarrafa ta, alaka ce badiniyyah, wacce ba a iya gani. To kuma gashi a kan wannan alaka ne za mu kawo kusan dukkan bayanan da zasu biyo baya, in Allah Ya yarda. Wannan tasa nayi kandagarki a farko, don kada mai karatu yace ”Baban Sadiq yai mana kwange”. Kai dai a ci baure, amma kada a tona cikin sa.

Ma’anar “Computer Network”

A turancin kwamfuta idan aka ce “Networking”, ana nufin tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci (daga biyu zuwa sama), wajen mikawa da karban bayanai, ta hanyar wasu ka’idoji da kowace kwamfutur ke iya fahimta. Wannan tsari na daga cikin dalilan da suka haddasa ma kwamfuta shahara wajen tasirin yada ilimi da harkokin sadarwa a duniya gaba daya, ciki har da fasahar Intanet. Samuwar wannan tsari ya sawwake daman shiga wata kwamfutar daga wata, a cikin gida ne ko a ofis ko kuma a wata jiha ce daban. Kai a takaice dai kana iya shiga wata kwamfutar da ke wata kasar, kana zaune a dakinka ko ofishinka. Duk ta albarkacin wannan tsari na mikawa da karban bayanai a tsakanin kwamfutoci. Yadda kasan mutane na mu’amala a tsakaninsu, to haka ma kwamfuta ke yi. Af, to me ye abin mamakin? Mutum ne fa ya kirkira! Akwai abubuwa biyu da ke haddasa mu’amala tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar ‘yar uwanta. Abu na farko shine samuwar kwamfuta a kalla biyu, masu dauke da manyan manhajojin kwamfuta, watau Operating System, irinsu Windows ko Mac da dai sauransu. A cikin wannan babban manhaja ne ake da Jami’an Sadarwa watau Network Drivers, da kuma Katin Tsarin Sadarwa da ke cikin akwatin kwamfutar, mai suna Network Card. Abu na biyu kuma shine samuwar komatsen da ke sadar da kwamfutocin, a bayyane ko kuma ta wayan iska (Wireless).

Wadannan komatsen sun hada da wayoyin kebul irinsu Twisted Pair (IJ45), da Twisted Pair (IJ11), da Coaxial Cable da Fibre Optic Cable. Sai kuma na’urori irinsu Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), da Routers, da Switches da kuma Satellite Dish da dai sauran komatse. Da wadannan ake sadar da bayanai tsakanin kwamfuta da kwamfuta, kai har ma da wayar salula da Talabijin da rediyo. Bayanan da ke fita daga wannan kwamfuta zuwa wancan na yin hakan ne ta hanyar wutar lantarki da ke bi tsakanin waya da waya ko tsakanin na’ura da wayar iska. Abin sai a hankali. Wadannan su ne karikitai na zahiri da mai karatu zai iya gani a yayin da kwamfuta ko wani na’uran sadarwa ke sadar da bayanai zuwa wata ko kuma ga masu kallo ko sauraro.

Nau’uka

Tsarin sadarwa daga kwamfuta zuwa wata kwamfutar ‘yar uwan ta, na daukan nau’i uku. Akwai tsarin sadarwa ta zahiri da ke shiga tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar da ke cikin gida ko daki ko kuma ma’aikata daya, da ke bigire daya, ko da kuwa ba a hade ginin suke ba. Wannan tsarin shi ake kira Local Area Network (LAN), kuma yana da hanyoyin sadar da kwamfutoci iri biyu ne; hanyar amfani da wayoyi na zahiri, musamman wayoyin Twisted Pair (IJ45) ko Fire-optic Cables, da kuma Switch, musamman idan tsakanin wani gini ne da wani. Hanya ta biyu kuma it ace ta hanyar wayar iska, watau Wireless, wanda kuma ake iya yi ta amfani da na’urar Wireless Frequency (Wi-Fi), da sauran na’urori makamantan su. Wannan shine tsarin Local Area Network, ko kuma Gajeren Zangon Intanet, a Hausance. Nau’in sadarwa ta biyu kuma ita ce wacce ta fi wannan fadi; tsakanin gari da gari, ko jiha da jiha, ko kauye da wani kauyen. Wannan shi ake kira Wide Area Network, watau Faffadan Zangon Sadarwa. Galibin kamfanoni masu rassa a wasu wurare kamar jihohi ko birane, sun fi amfani da wannan tsari. Inda za a iya sadar da bayanai tsakanin dukkan rassan, ba tare da wata matsala ba. Wannan tsari shi galibinsa ta wayar iska ake yinsa, watau Wireless. A kan kuma yi amfani ne da na’urar sadar da kwamfuta na dogon zango, watau Router, don sadar da bayanai kala-kala a tsakanin zangunan ma’aikatar. Misali, idan cibiyar ma’aikata wacce ke wani gari, na da iyayen garke biyu; daya na sadarwan Intanet (Internet Server), dayan kuma na rumbun bayanai (Database Server), sai ayi amfani da na’urar Router da kuma tauraron dan Adam watau Mast, don banbance iyayen garken biyu. Wannan zai ba duk mai son shiga Intanet, da mai son amfani da bayanan da ke tsibe cikin uwar garken ma’aikatan daman yin hakan, ba tare da samun wata matsala ba. Sai nau’in sadarwa na uku, wanda ya fi kowanne fadi da ban mamaki, watau Intanet. Sadarwa ne tsakanin kwamfutoci da ke duniya gaba daya, ba ma wani bigire takaitacce ba. A tsarin Intanet, kwamfuta ce zata nemo bayanai daga wata kwamfutar da ke uwa duniya. Watakil shi kanshi mai nemo bayanan ma bai san inda uwar garken take ba, a a, adireshin kadai ya sani. Wannan hanyar sadarwa na yiwuwa ne ta hanyar wayar iska mafi girma, wanda ke samuwa ta hanyar tauraron dan Adam mai suna Earthlink a turance. Na tabbata mai karatu ya ma san wannan tsari tuni, don haka ba a bukatar tsawaita bayani a nan. Sai abu na gaba.

Tsarin Mikowa da Karban Bayanai

A kowane hali ya kasance, a kan tsamu bangare biyu ne wajen gudanar da wannan alaka ta mikawa da karban bayanai tsakanin kwamfutoci; a gari daya suke ko a garuruwa daban-daban; a jiha daya suke ko a jihohi daban-daban; a kasa daya suke ko a kasashe daban-daban, duk tsarin daya ne. Wannan bangaren shine bangaren da ke mika bayanan, wanda ake kira Host ko Server, ko Terminal, a turancin kwamfuta, ko kace Uwar Garke kawai ka huta. Wannan kwamfuta guda daya ce tinkwal, kuma aikinta shine mika bayanai da zaran wata kwamfuta ta bukaci tayi hakan, ta hanyar da ya dace. Ita wannan kwamfuta har wa yau, tana da manhajan da ke taimaka mata yin haka, ba wai kwamfuta ce irin kowace kwamfuta ba. A bangare daya kuma, sai wanda ke bukatar bayanan, wanda a turancin kwamfuta ake kira Client. Da zaran Client ta turo bukatun neman bayanai, sai Host ko Server ta duba dacewan hanyoyin da wannan bukata ya zo. Idan ingantacce ne, sai ta mika ta hanyar da aka biyo mata. Idan ba ingantacciyar bukata bace, ba ma zata iso gareta ba.

Kammalawa

Na tabbata har zuwa yanzu mai karatu na dai ji na ne kawai, ba tare da wata cikakkiyar fahimtar almaran da nake cusa masa a kwakwalwa ba. Kada ka damu, zuwa mako mai zuwa abubuwa zasu fara budo maka. Shi yasa nayi kandagarki a farkon makalar, don kada a zarge ni. A mako mai zuwa, zamu yi bayani ne kan ka’idar da kwamfutoci ke dashi wajen sadarwa a tsakaninsu. A nan ne kuma zamu san matakai ko masaukai guda bakwai da kowace kwamfuta ke da su, don sadarwa a tsakaninta da ‘yar uwanta. Wadannan matakai ko masaukai ne ke tattare da ka’idojin mika bayanai. Idan mai karatu bai sani ba, kwamfuta tafi kowane halitta tsaban kishi da bin ka’ida. Idan baka bi ka’idarta ba, to kai da samun abinda kake so har abada. Ba kamar mutum bane, wanda zaka yi ta masa magiya don yayi la’akari da uzurorinka. A duniyar kwamfuta, sai ka bushe a wurin. A biyo mu mako mai zuwa don samun karashen wannan makala. A karshe ina mika gaisuwata ga dukkan masu karatu. Ina nan tafe mako mai zuwa in Allah Ya yarda. A ci gaba da kasancewa tare damu!

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa,

Garki II, Abuja. 08034592444

Fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com

Wednesday, September 19, 2007

Dunkulallun Ka'idojin Mu'amala a Intanet (3)

Makon Jiya

Idan mai karatu na biye da mu makonni biyu da suka gabata, ya samu bayanai kan asali da wasu daga cikin dunkulallun ka’idojin mu’amala da zasu taimaka masa wajen gabatar da dukkan abinda yake son yi a Intanet. Hakan muka ce yana da matukar muhimmanci wajen samun ingantacciyar yanayin da mai lilo da tsallake-tsallake ke bukata. A makon da ya wuce mun kawo ka’idoji guda goma dunkulallu. A yau cikin yardan Ubangiji za mu kawo sauran ka’idoji sha daya da suka rage. Har wa yau, mun sanar da cewa wadannan ka’idoji dukulallu ba su kenan ba, kowa na iya kirkira, daidai fahimta da mahangar da yake dashi kan wannan fasaha. A yanzu zamu ci gaba:

Durkusa ma Wada, Ba Gajiyawa Bane

Sosai kuwa! Wannan ka’ida tana da muhimmanci wajen mu’amala da mutane a Majalisun Tattaunawa, watau Mailing Lists ko Discussion Group. Domin waje ne da kowa ke iya kawo fahimtarsa kan abinda ake tattaunawa ko ya faru. Kuma yadda dabi’ar dan Adam take, zai yi wahala a ce ga wani ra’ayi da dole ne kowa da kowa ya yarda dashi, sai in doka ce. Don haka zaka ji ana ta tafka muhawara, wanda hakan ke taimakawa wajen fitar da wasu nau’uka na ilimi da wani bai sani ba. Wannan tasa a galibin Majalisun Tattaunawa, musamman na Hausawa da ke Intanet, ba a cika hana muhawara ba, sai in akwai cin fuska da zage-zage a ciki. Banbance-banbancen ra’ayoyi ne ke kawo haka, kuma haka Allah Ya halicci mutane. Wannan tasa dole wasu lokuta ka saurara ma wasu ra’ayoyin ko da kuwa kana ganin ra’ayinka (in ma ka bayyana kenan) bai samu karbuwa ba. Domin yin hakan, baya nufin kana kan ra’ayin da yayi rinjaye kenan. A wasu lokuta ma shawarwari ne za a kawo, ana son wanda ya fi dacewa, sai kake ganin naka ne yafi, amma kuma aka dauki wanda kake ganin bai kai naka muhimmanci ba, sai ka hakura. Don me? Durkusa ma wada, har abada, ba gajiyawa bane.

In Ka Ki Ji, Ba Ka Ki Gani Ba

Wannan haka yake, kuma misalai kan haka na nan ko ina a Intanet, galibi a gidajen yanar sadarwa na wasu al’ummomi da al’adu ko akidu ko kuma tsarin rayuwarsu ta sha banban da naka. Gidajen yanar sadarwa masu tallata hajojin da suka sha banban da yanayin tunani da tsarin al’umma hatta wadanda suke ciki, zaka samu suna gargadin duk wanda ya shigo, ”a wannan gidan yanar sadarwa, kaza da kaza muke tallatawa, idan yayi maka, ka shigo, in kuwa ba ka bukata, ga hanyar ficewa nan”. Ka ga a nan, sun fita hakkinka. Wannan yafi shahara a gidajen yanar sadarwa na masu akidun “Ba Allah” (watau Atheists), da na masu tallata hajojin batsa da shashanci. Har wa yau, wasu lokuta kwamfutar ka zata sanar da kai cewa a wannan gidan yanar da ka shiga, akwai wasu abubuwa da zasu iya bata maka kwamfutar; ka amince in shigar da kai, ko ko zaka fice? Zata baka zabi; duk wanda ka dauka, shi zata zartar maka. Sauran bayanai kuma, kai ka jiyo, sautun mahaukaciya. Dole su sa wannan sanarwa a dokokin kasashen su, don ba kowa bane ke da mahanga da tunani irin nasu. A nan an sanar da kai cewa ga abinda zaka gani idan har ka shiga; kenan in baka so, sai kawai ka fice. Amma idan ka ki ji, to fa ka sani, ba ka ki gani ba.

Gaskiya Kujera Ce…

Wannan a fili yake. Idan gidan yanar sadarwa kake dashi, kayi mu’amala da mutane da gaskiya, musamman a wannan duniyar da karya da zamba ne ke da tasiri, jama zasu kaunace ka, su ci gaba da mu’amala da kai. Amma da zaran sun nemi gaskiyarka sun rasa, sai ka ga wayam, sunan wani mawaki. Haka ko Majalisun Tattaunawa, idan ka fadi gaskiya aka ki sauraranka, share. Muddin ana raye, in dai gaskiyar ake nema, to sai an dawo mata. Don me? Kujera ce, duk inda aka je aka dawo, za a same ta. Ba ta bin kowa, sai dai a bi ta.

Zama Lafiya, Ya Fi Zama Dan Sarki

Wa ke Magana kuwa! Ai ka zauna lafiya shi yafi a tara maka dukkan arzikin da ke duniyan nan, ba ma kudin da ke ciki kadai ba. Idan kana Majalisar Tattunawa, ka lazimci bakinka, muddin abinda zaka fada bai da muhimmanci. Amma in har yana da muhimmanci, ko da wasu basu so, ka iya fada. Illa dai hakan ya danganta da yanayin da ka fadi maganar ne. Amma idan mutum zai ta aiko da dukkan abinda kawai yaji zuciyar sa ta raya masa ne, to fa zai ga ko ji abinda baya son gani ko ji. Son zuciya, in ji Malam Bahaushe, bacin zuciya. Wannan tasa wasu ke yin shiru a Majalisun Tattaunawa, kai kace basu nan. A a, kawai abin fadi ne bai zo ba. Ko kuma munasabar Magana ne bai zo musu ba. Sai kawai su lake a bakin garka suna karanta sakonnin da ake aikowa. Wannan shi ake kira Lurking, a turancin Intanet. Don me? Zama lafiya, yafi zama dan Sarki.

Idan An Ciza, A Rinka Hurawa

Sosai kuwa, sai al’amura su tafi daidai. Wannan ka’ida na da muhimmanci wajen tarbiyya a Majlisun Tattaunawa. Galibin lokuta, yin sassauci shi ke sa a dade ana amfana da juna, ko kuma amfanuwa da wata hanya ta ci gaba. Idan jayayya tai yawa ko ta tsawaita, galibi takan haddasa gaba a tsakanin masu yi. Haka idan tsanantawa tai yawa wajen lura da dokoki, sai a samu kosawa wajen mabiya. Wannan tasa a wasu Majalisun Tattaunawa zaka samu ana rangwame wajen shigar da gaishe-gaishe da aiko da sakonnin neman aiki, da na zanen suna da daurin aure, wadanda watakil sun sha banban da manufar Majalisar. Ana haka ne, don jawo mutane a jika. Idan an ciza, to fa a rinka hurawa.

Taka-tsantsan, Ya Fi Bundun-bundun

Ai ko a rayuwar yau da kullum haka abin yake. Ko da kana da manufa wajen abinda kake son yi, kuma ka samu abinda kake so, to fa taka tsantsan na da muhimmanci, don daukan abinda kake son daukawa. Kada ka dauki abinda ba shi kake bukata ba, saboda gaugawa. Intanet wata duniya ce mai kama da kantin alawa; idan ka zama yaro wajen daukan irin alawar da kake so don ruwan ido, sai ka rude, ka dauki mara zaki, don yawan kyale-kyalen bawonta. Taka-tsantsan, ya fi bundun-bundun.

Kowa da Abokin Burminsa

A Intanet kowa da abokin burminsa; Jamila na tare ne da Jamilu; Danjuma na tare ne da Danjummai; Salihu na tare da Salaha; Doma na tare da Awai. Don me? Abokin biri, idan ka bi duddugi, zaka samu kare ne. Wannan na nufin kowa ya san inda zai samu mutanensa; wadanda dabi’arsa ko tunaninsa suka yi daidai. Wannan shine galibin abinda yafi shahara a Intanet, musamman ga wadanda suka saba shiga yau da kullum. Hatta a Majalisun Tattaunawa, inda ake da jama’a daya, Hausawa kuma Musulmai, a misali, zaka samu a tsakaninsu ma kowa da abokinsa, ko abokiyarsa. Wani baya karanta sakon kowa sai na wane. Wani baya goyon bayan rubutun kowa sai na wane ko wance. Wani kuma baya Magana, sai an taba wane ko wance. Kowa dai da mutanensa. Idan ka fahimci wannan, to ba abinda zai bata maka rai. Don daman a rayuwa Allah bai yi mutane su zama daya ba; kowa da abinda yake so ko sha’awa. Sai hali yai daidai ake abota.

Gyara Kayanka, Ba Ya Zama Sauke Mu Raba

Idan aka maka gyara kan abinda ka fada a Majlisun Tattaunawa misali, ka karba, kada ka bi son zuciyarka wajen ki, ko kuma ka daga hanci. Ko wani ne ya cutar da kai, aka taru wajen baka hakuri, to ka hakura. Kada ka dauka an yi haka ne don raunata muhimmancin ka ko na tunani ko ra’ayinka. A a, gyara kayanka ne, wanda kuma ba ya taba zama sauke mu raba.

In Baka Gayyaci Kowa Ba, Baka Ganin Kowa

Wannan yafi shahara a Wasikar Hanyar Sadarwa, watau Imel. Idan ka bude akwatin wasikar Imel, dole ka sanar da abokanai da ‘yan uwa da kake son ku rinka karban wasiku a tsakaninku. Idan ba haka ba, ba zaka samu wasikar kowa a jakar Imel dinka ba, sam. In kuwa ka samu, to dayan biyu; ko dai wanda masu manhajar Imel din da ka bude ne suka aiko maka don yi maka “barka da shigowa”, ko kuma sakonnin bogi ne, watau Spam. Haka idan gidan yanar sadarwa kake dashi, kana bukatar ka rinka tallata gidan, ta hanyar sanar da abokan hulda, ko ka aika ma gidajen yanar sadarwa masu manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine), irinsu Google, Yahoo, Altavista, Websearch da sauransu. Su zasu sa “dan aikensu” watau Robot, ya shiga gidan yanar don taskance irin kalmomin da ke ciki, yana zubawa a Uwayen Garken su. Da zaran masu neman bayanai sun yi amfani da kalmomi masu munasaba da wannan, sai su samo ki. In kuwa ba haka ba, to ba ka ganin kowa.

Mai Hakuri Yakan Dafa Dutse

Idan kana da hakuri wajen neman abinda kake nema, ko ba dade ko ba jima, zaka samu abinda kake so. Abinda ake bukata shine ka rike ka’idojinka a matsayin fitila. Wannan zai kai ka ga nasara. Idan ilimi kake nema, duk wahalarsa, muddin ka lazimci ka’idojin da ke da munasaba da wannan ilimi, ba abinda zai hana ka samun sa. Duk abinda kake koyo, zaka iya kwarewa a kai. Duk abinda kake nema, indai yana nan, ka ci gaba da nema. Zaka samu wataran. Idan littafi kake son rubutawa, duk zaka samu bayanai. Idan wani fasaha kake son koyo, duk zaka samu mabudai da hanyoyin cin nasara. Abinda kake bukata shine ka san abinda kake nema, da ka’idojin da ke tattare da shi, kada ka damu da tsawon lokacin da zai dauke ka. Domin idan zaka yi mu’amala da duk abinda ya shafi kwamfuta da Intanet, to fa kana bukatar hakuri da jajircewa. Su ne manyan fitilu masu haskaka maka hanya. Da su, sai ka dafa dutsenka, har ka shanye romonsa.

Kowace Ka’ida Da Kaidinta

Wannan ita ce ka’ida ta karshe, kuma ita ke nuna mana cewa duk wata ka’ida da dan Adam ya kawo maka ko ya sanya ma kansa, to fa tana da kaidinta. Wannan kaidi shi ke tsawaita amfaninta, da kuma nuna cewa idan al’amura suka cakude, kana ganin cewa amfanin ka’idar da kake kai ya zo karshe, sai a ce maka ga mafita karkashin wannan ka’ida. Dukkan ka’idojin da muka kawo a sama suna da kaidin da ke kayyadesu da wani yanayi ko lokaci ko muhalli. Idan ba haka ba, sai hikimar da ke tattare da ka’idar ta bace. Da aka ce kada mu ci mushe a musulunci, sai aka kayyade wannan hani da lokacin tsanani ko rashin abinci. Domin tsare ran dan Adam da lafiyar sa, shi yafi. Don sai kana da rai sannan za a yi tunanin dora maka wata doka. Haka sauran ka’idoji suke. Misali, muka ce Ko da me kazo an fi ka; sai kuma muka kayyade wannan ka’ida da cewa kogi ba ya kin dadi. Don kada ka dauka, tunda an ce duk abinda kaje dashi na ilii da fasaha, ai wani ya riga ni, don haka na fasa. A a, kogi ba ya kin dadi. Da dai sauran kaidin da aka sa ma sauran ka’idoji da mai karatu zai ci karo dasu.

Kammalawa

A nan zamu dakata sai wani mako. Ina fatan masu karatu sun samu hanya guda wajen kiyasta manufa ko dalilan da zasu taimaka musu wajen mu’amala da wannan fasaha. Duk abinda ba a fahimta ba a rubuto. Zuwa mako mai zuwa kuma zamu juya akala zuwa wani bangaren don dada fahimtar wannan fasaha mai tasiri. Ina kuma mika sakon gaisuwa ta musamman da shigowar mu wannan wata mai alfarma na Ramadana, Allah Ya karbi dukkan ayyukan mu gaba daya, amin. Sai mako mai zuwa.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa

Garki II, Abuja.

080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com

Saturday, September 8, 2007

Dunkulallun Ka'idojin Mu'amala a Intanet (2)

Matashiya:

A makon da ya gabata ne muka fara bayani kan Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet, inda muka yi bayani kan ma’ana da amfani da kuma tsarin da ke tattare da bin ka’ida wajen mu’amalar rayuwa gaba daya. Daga karshe kuma muka yi alkawarin fara jero wadannan ka’idoji da nace kirkirarru ko fararru ne daga gareni, duk da yake lafazinsu ba wasu sabbin abubuwa bane da bamu taba ji. A yau zamu ci gaba, in da masu karatu zasu samu Dunkulallun Ka’idoji kan mu’amala da wannan fasaha mai harshe biyu; amfani da illa. To, a halin yanzu ga wadannan ka’idoji nan:

In Kana Son Tsira, Shiga da Alwalanka

Wannan Magana haka take. Duk mai son tsira wajen samun abinda yake so ko kauce ma abinda yake ki a duniyar Intanet, to dole ne ya shiga da alwalansa, cikakkiya kuwa, ba mai lam’a ba. In kuwa ba haka ba, to zai ta walagigi ne, ba car ba ar, har dan abinda ya tanada ya kare. Watakil mai karatu yace: “af, Intanet din kuma ya zama sai kana da alwala zaka shiga?”, to ba asalin alwala ake nufi ba a nan. Abinda kalmar alwala ke nufi a nan itace: shiga da manufarka, na abinda kake son yi ko samu; shiga da iliminka, na abinda kake nema ko son yi; shiga da al’adanka mai kyau, don akwai al’adu masu dimbin yawa da zaka tarar. Idan ka kuskure ka shiga ba tare da alwala ba, to dayan biyu; ko dai ka sha wahala wajen yawo ba tare da ka tsinana komai ba, ko kuma sai ka sha dan Karen wahala kafin samun abinda kake nema. In ma ka samu, to dace ne. Amma idan ka shiga da ilimin cewa ga abinda kake son zuwa ka yi, cikin dan kankanin lokaci sai ka samu abinda kake so. Sauran lokutan da ka saya su zama maka rara. Haka idan da manufa kaje, duk wata manufar da ta saba ma naka, sai dai ka kura mata ido kawai. Haka zakai ma sauran al’adun da suka sha banban da naka. Me kake son yi da har ka sayi lokaci don yin lilo da tsallake-tsallake? Ina manufarka? Nemo a halin yanzu, idan baka da ita, don ita ce tsiranka. Har wa yau, shiga da alwalanka, in kana son tsira. Wannan ita ce ka’ida ta farko wacce ta fi kowacce muhimmanci cikin dunkulallun ka’idojin mu’amala a Intanet. To me yasa?

Ba Dukkan Fari Bane Fari. . .

Sosai kuwa! A duniyar Intanet ba dukkan abinda yai kama da gaskiya bane ke zama gaskiya, yanke. Yadda ka san cewa ba dukkan launin fari bane yake fari; wani farin akwai baki-baki a cikinsa, idan kana da yanar ido ba za ka taba sani ba ko da kuwa ka zo kusa dashi. Don haka bayan manufa ko ilimi da kayi tanadinsa, yana da kyau ka san cewa a Intanet akwai wasu abubuwa masu kama da juna, amma hakikaninsu ya sha banban, nesa ba kusa ba. Ba dukkan bayanai bane zaka dauka abin kafa hujja. Idan ba haka ba sai masana suyi ta maka dariya baka sani ba. Akwai bayanai kan fannoni da dama, amma kana bukatar sanin me kake nema, don kada ka dauki bayanan da basu da alaka da maudu’in da ake Magana a kai, ka cakuda su. Ko ka nemo bayanan da ba su malaminka ke so ba, ka cakuda masa aiki. Me kake nema? Ka tuna, ba dukkan fari bane fari.

Ko Cikin Gaskiya Akwai Karya. . .

Haka ma ko cikin karya akwai gaskiya. Wannan ka’ida ce mai zaman kanta. Kada mu dauka akwai warwara, babu ko kadan. Idan ka shigo da alwalanka, kuma ka fahimci cewa ba dukkan ilimi bane zaka dauka; akwai wanda ya cancance ka, da wanda bai cancanci abinda kake nema ba, haka kuma ka san cewa, wani nau’in bayanin da zaka dauka karya ne, to akwai kamshin gaskiya a cikinsa. Haka kuma wasu lokuta kana iya daukan wani abu a matsayin karya ne, amma idan ka bincika sosai sai ka ga ashe gaskiya ne abu kaza. Duk wadannan ka’idoji biyu na biye ne da ka’idar shiga da alwalanka, kuma zasu taimaka maka ne wajen neman bayanai a dukkan inda kake zaton samu.

Daji Mara Kofa, Shiganka Sai Da Hikima

Wannan haka yake. Intanet wani duniya ne wanda bai da takamaimen kofa, don haka shiga cikin sa da gudanar da mu’amala na bukatar cikakkiyar hikima, wacce zaka damfara ta da ilimi ko manufar da ka shigo da ita. Hikima wajen sarrafa lokacinka. Hikima wajen mu’amala da wadanda zaka hadu dasu a wurare da dama. Hikima wajen iya neman abinda kake so. Hikima wajen iya sadar da sakonnin neman alfarma. Ka tuna, a Intanet ba a san fuskanka ba; ba wanda ya san kalan jikinka, balle tsawonka. Me aka sani a Intanet? Rubutunka, mai dauke da manufarka, wacce ke bayyana hakikaninka. Don daji ne mara kyaure (Sakkwatawa ku gafarce ni), shigansa sai da hikima.

Ko Da Me Kazo, An Fi Ka

Ai ba birnin Dabo bane kadai da wannan kirari, sam ko kadan. A Intanet duk abinda kaje dashi, sai ka samu wanda ya fi ka. Duk iliminka, sai ka hadu da wanda ya shallake ka, nesa ba kusa ba. Duk kwarewarka, sai samu wanda zai karantar da kai. Duk iya tsiyanka, sai ka hadu da wanda zai maka darasi. Duk kamun kan ka, sai ka samu wanda ya fi ka rikewa. Duk hakurinka, sai ka samu wanda zai kure ka. Duk fushinka, sai ka samu wanda zai kwantar maka da hankali. A Intanet babu shugaba, balle a ce ga wanda yafi wane abu kaza, ko a ce wane ne kadai ya iya abu kaza. Idan aka ce yau kaine wanda ya iya abu kaza a duk duniuyar, to nan da mako guda sai ka samu wanda zai koya maka abinda kake tutiyar iyawa. Idan takamarka iya rufe gidan yanar ka ne da hanyoyin tsaro na fasaha, wani kallon gidan yake a bude, tsirara. A yau duk Intanet ana maganar Google wajen iya tsara manhajan neman bayanai na Matambayi Ba Ya Bata. Shekara mai zuwa sai kaji ana maganar wani. A da, kamfanin Microsoft ce ta rike wuta, a yanzu ba ita bace. Don me? Don duniya ce, wacce ko da me kazo, an fi ka. Idan yau kai ne, to gobe fa, wani ne; kana son sa ko baka son sa.

Kogi Ba Ya Kin Dadi

Duk da cewa Intanet duniya ne wanda da zaran ka shigo, to ko da me kazo an fi ka, yana da kyau mai karatu ya san cewa kogi fa ba ya kin dadi. Wannan tasa ake cewa nau’in ilimi dai-dai ne baza ka samu a Intanet ba. Don a kullum kawo sabbin abubuwa ake iya, gwargwadon yadda duniyar ta kai wajen wayewa kan ilimi a fannonin rayuwa daban-daban. Domin ba don makoyi ba, da gwanaye sun kare ai. Don haka kada ka dauka don an ce “ko da me ka zo an fi ka,” kace, “af, kenan bari in zauna kawai, tun da in ma naje ba wani sabon abu na kawo ba”, a a, duk abinda ka sani na ilimi, ko da kuwa akwai wasu da suka yi rubutu suka zuba, zai dace kaima ka zuba naka. Wannan zai ba mai neman bayanai zabi da kuma tantance banbance-banbancen da ke tsakanin naka bayanan da wanda wasu suka zuba. Don me, ba dukkan fari bane fari. Wannan a tsarin neman bayanai kenan, amma a wasu gidajen yanar sadarwa ko wasu majalisun tattaunawa, abin ba haka yake ba. Amma duk da mun san “kogi ba ya kin dadi”, zai dace mu kuma san cewa “teku kam yana kin dadi”. Wannan tasa da zaran an yi ruwan sama, zaka ga teku na ta ambaliya. Don me? Don nau’in ruwan da ke zubowa daga sama mai gardi ne, mai dadi, amma wanda ke cikinsa ruwan gishiri ne. Kuma tunda akwai shamaki tsakanin ruwan gishiri da na gardi ko dadi, dole a samu rashin jituwa. Abin nufi, ba dukkan majalisun Intanet bane zaka je ka kawo wani abu sabo, wanda ba a kanshi aka assasa majalisar ba; ba dukkan gidajen yanar sadarwa bane zaka je ka kawo musu wani abu sabo, sai wanda ya dace da abinda suke so; kowace majalisa na da nata maudu’i. Don haka mu sani, idan kogi ba ya kin dadi, to teku na ki, sosai kuwa.

Abincin ka, Guban Wani

Wannan shine dalili. A yayin da kake ganin wannan bayanin ko kuma wannan tsarin ko wannan Maganan ya kamata a fade ta don tana da fa’ida, to ka san cewa tana da muhallinta na musamman. Kowane irin ilimi na da muhallinsa. Idan wani abin yayi maka, to kada ka dauka dole ma ya yi ma kowa. Domin ba haka tsarin rayuwa take ba. Shi yasa idan ka shiga wasu gidajen yanar sadarwan, ka ga irin abubuwan da suke tallatarwa, sai mamaki ya kama ka. To ina ruwanka? Su a wajensu abu ne mai kyau, don watakil yayi daidai da al’adu ko addini ko tsarin rayuwarsu. A yayin da wasu ke shiga don neman bayanai kan abinda zai ciyar da su gaba, wasu na zuwa ne wasan kwamfuta kadai. A yayin da wasu ke zuwa don yada addini, wasu na zuwa ne don yada tsana da kiyayya a tsakanin al’adu ko addinai ko launin fata. A yayin da wani ke zuwa don zuba bayanai masu amfani, kuma kyauta, wani kuma fatansa shine ya cutar da wasu ta hanyar amfani da fasaha ko kwarewarsa. A yayin da wasu ke tallata hajoji masu amfani wajen habbaka rayuwa da tunanin dan Adam, wasu kuma assha suke yadawa. Gashi nan dai; kowa da inda ya dosa. Don me? Abincin ka, guban wani.

Araha Ba Ta Ado

Ko kadan kuwa! Da tana yi, da duniya ta cika da kwalliya. A Intanet akwai manhajojin kwamfuta (computer softwares) da ake bayar da su kyauta. Wadannan manhajoji ko masarrafai suna da muhimmanci sosai. Akwai wadanda za su taimaka maka gina gidajen yanar sadarwa. Akwai na wasannin kwamfuta. Akwai na kididdigan lokuta. Akwai na koyon harsunan duniya (Ingilishi da Faransanci da Jamusanci da Mandarin dsr). Akwai na koyon addini. Akwai na koyon rubutu da karatu. Akwai na koyon iya kwankwansa allon rubutun kwamfuta, watau Keyboard. Akwai na sauraran wakoki. Akwai na gyaran kwamfuta. Duk wadannan, in kana so, zaka same su kyauta, har ka diro dasu kan kwamfutarka, ka rinka amfani dasu. To amma ba a nan gizo ke sakan ba. Galibin ire-iren wadannan manhajoji da zaka ji ana kururuta su, zaka samu suna da wani mummunan tasiri a kwamfutarka. Idan ka loda su da yawa, zata fara zazzabi; domin masu gina manhajojin na yi ne da wata manufa ko dai manufar kasuwanci ko kuma manufar ta’addanci, ko kuma, a karo na karshe, a samu kuskuren tsari wajen fasahar gina manhajar (watau Bugs), wanda hakan na iya cutar da kwamfutarka. Idan baka yi sa a ba, a yayin da kake diro da wannan manhaja, lokacin kuma kake diro da gurbatattun bayanai masu rikita maka kwamfutar, watau Virus ko Spyware. Kuma kafin ka cire su, kana bukatar manhaja na musamman don yin haka. Ka ga anyi ba yi ba kenan. In ka kebe tarin bayanai da zaka samu ka karanta, galibin abubuwan da ake samun su kyauta a Intanet, na tattare da wani nau’i na amfani ga mai shi, ko da kuwa baka sani ba. To dole ka lura, ka kuma rike wannan ka’ida kam a hannunka, musamman idan kwamfutar taka ce. Ka san cewa: Araha fa, ba ta ado.

Akan Tsinci Dame A Kala

Eh, sosai kuwa! Duk da cewa a kan samu irin wannan cutarwa cikin galibin abubuwan da suke kyauta ne a Intanet, sau tari sai kayi dacen samun amfani sau bakwai kafin ka hadu da cutarwa daya (da sharadin kana rike da alwalanka, bata warware ba). In kuwa haka ne, to ashe akan tsinci dame a kala kenan. Wannan ka’ida ce mai kyau, kuma ya kamata a rike ta sosai. Muddin ka san abinda kake nema, to zaka yi arkizi sosai a Intanet. Amma idan ka sake ka shiga ba tare da sanin makama ko mashigi ba, zaka ji jiki kafin idanun ka su washe. Har wa yau dai, akan tsinci dame a kala.

Inda Ka Kwana, Nan Wani Ya Tashi

Wannan a fili yake! A Intanet za ka iya zubawa ko fadan duk abinda ka sani na ilimi ko kawo duk abinda ka sani na ilimin fasaha, amma kada ka taba riya cewa tunda kai ne farkon wanda ya kawa hakan, ilimi ya kare a wajen, sam. Ko a ka’idar rayuwar yau da kullum ma ba haka abin yake ba, balle a Intanet. A Intanet, inda ka kwana, to fa nan wani ya tashi. In da ka ajiye alkalaminka, nan wani ya tsoma nasa cikin kuttun tawada. Idan bamu mance ba, a kasidun baya mun ta ambaton sunayen wasu shahararrun mutane da suka kirkiri fasahohi da dama da manhajojin da suka taimaka wajen habbaka wannan fasaha ta Intanet, shekaru kusan ashirin da suka gabata ko kasa da haka. To amma a halin yanzu, su kansu sun san cewa jiya ba yau ba. Misali, wanda ya kirkiri ka’idar sadarwa ta World Wide Web (www) ko kuma Hypertext Transfer Protocol (http), watau Farfesa Tim Bernes-Lee (Baban Intanet), gwani ne sosai wajen ilimin kwamfuta da Intanet, amma a halin yanzu ya san cewa akwai wadanda suka sha gabansa. Don me? Don inda ya ajiye alkalaminsa a shekarun baya, tuni wasu suka tsoma nasu, don ci gaba. Wannan ka’ida na cikin dalilan da suka sa Intanet ya zama gagarau a yanzu; a kullum kara kasaita yake, sai kace bajimin sa. Don, inda wani ya kwana, tuni wani ya tashi, don ci gaba da al’amura.

Kammalawa

A halin yanzu zamu dakata a nan, don kauce ma tsawaitawa. Idan mai karatu bai mance kirgan ba, mun kawo ka’idoji ne guda goma a yau; 1) In kana son tsira, shiga da alwalanka; 2) Ba dukkan fari bane fari, kamar yadda ba dukkan baki bane baki; 3) Ko cikin gaskiya akwai karya; 4) Daji mara kofa, shiganka sai da hikima; 5) Ko da me kazo, an fi ka; 6) Kogi ba ya kin dadi; 7) Abincin ka guban wani; 8) Araha ba ta ado; 9) Akan tsinci dame a kala; 10) Inda ka kwana, nan wani ya tashi. Wadannan su ne goman farko, kuma mako mai zuwa za mu kawo cikon goma sha-dayan da suka rage. Kamar kullum, duk abinda ba a fahimta ba, a rubuto. Inda kuma aka samu kura-kurai, a tunatar damu. Muna kara mika godiyarmu ga Sashen Hausa na BBC, musamman ma’aikatanta da ke ofishin watsa shirye-shiryen su da ke nan Abuja. Har wa yau, wannan fili na mika godiya ga dukkan masu karatu, kuma da fatan ba za a gaji da rubutowa ba. A ci gaba da kasancewa tare da mu a kullum.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa
Garki II, Abuja.
080 34592444
fasaha2007@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com

Wednesday, September 5, 2007

Dunkulallun Ka'idojin Mu'amala a Intanet (1)

Gabatarwa:

Bayan makonni hudu da muka kwashe muna ta shan bayanai kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke kunshe cikin Intanet, a yau za mu juya akala don yin wata duniyar kuma. Makalarmu ta yau ta ta’allake ne kacokan kan Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet; watau hukunce-hukunce na rayuwa da suka lazimci dukkan mai son yin mu’amala a duniyar Intanet ba tare da matsala ba, muddin ya bi su sau-da-kafa. A lura, wadannan sun sha banban da ladubban mu’amala da muka kawo su a makalar Zauren Hira da Majalisun Tattaunawa. Su wadannan ka’idoji ne na tabbatar da wani abu ko kore yiwuwansa a Intanet. Sun fi ladubba fadin ma’ana, kuma a ko ina kana iya amfani da su, don a yanzu ma aro su muka yi daga ka’idar gamammiyar rayuwa ta yau da kullum. Mun yi haka ne saboda akwai kamaiceceniya ta asali tsakanin rayuwar yau da kullum da wacce ake gudanarwa a Intanet. Don haka in da hali, zai dace mai karatu ya haddace su. Shi yasa zamu daddatsa makalar zuwa kashi uku, in ta kama, don fadada bayanai iya gwargwadon hali. Hakan zai taimaka mana fahimtar wadannan ka’idoji. A halin yanzu ga mukaddima nan, kafin mu fara koro ka’idojin.

Ma’anar Ka’ida da Muhimmancin ta a Rayuwa:

Da farko, kalmar “ka’ida” dai kalma ce da ke da asali daga kalmar larabci, kuma tana nufin “asali” ko “matabbata” ko “mazauni” ko kuma “mizanin” tafiyar da wani aiki ko tsari. Amma Hausawa da suka aro kalmar, sai suka bata ma’anar karshe kawai, watau “mizani ko ma’aunin gabatar da wani aiki ko tsari.” Da wannan ma’anar ko mahangar za mu gabatar da wannan makala gaba daya. Amma Dunkulallun Ka’idoji na nufin “curarrun hunkunce-hukuncen da ke tabbatar da yadda wani tsari ke yiwuwa, ko gudanuwa, ko ake tafiyar da shi – ko kuma kore rashin yiwuwa, ko guanuwa ko yadda ake tafiyar da shi – a rayuwa ta al’ada ko addini ko wani fanni na ilimi. A matsayin mizani da tsari na tafiyar da al’amura, Dunkulallun Ka’idoji sun samu shahara a bakin masana harkokin rayuwa kan addini da al’adu/adabi da sana’o’i, da fannonin ilimi daban-daban. Ba don komai ba sai irin kebantacciyar amfanin da wannan tsari ke da ita wajen gabatar da abubuwa cikin sauki da tsarin da ya dace, don samun sakamako mai matukar muhimmanci, ba tare da wata wahala ba. Wannan ita ce dunkulalliyar manufa da amfanin da Dunkulallun Ka’idoji ke tattare da ita a dukkan fannoni na rayuwa. Da haka zamu samu malaman kiwon lafiya na da na su ka’idar, cewa hanya mafi sauki wajen kare cuta ita ce ta hanyar riga-kafi. Haka suka sake cewa dukkan wata cuta ana magance ta ne da kishiyarta. Shi yasa da zaran zazzabi ya kama mutum yana barin sanyi, suka ce a zuba masa ruwan sanyi, zafin jikin zai sauka nan take. Da dai sauran ka’idojin da suka tanada a wannan fanni nasu. Idan muka koma wajen adabi ko al’adar Malam Bahaushe, zamu samu shima ya tanadi nasa dunkulallun ka’idojin na tafiyar da rayuwarsa gaba daya, kamar sauran kabilu ko al’ummai. Wadannan dunkulallun ka’idoji suna kunshe ne cikin Karin Magana da yake rayuwa da su. Yakan ce: riga-kafi yafi magani; kowa ya daka rawar wani, sai ya rasa turmin daka tasa; sara da sassaka ba ya hana gamji tofo; in kaji gangami, da labari; a sa a baka, yafi a rataya. Da dai sauransu. Bayan nan, Malaman luggar larabci su ma fa ba a barsu a baya ba wajen tsara dunkulallun ka’idojin rayuwa ko koyon wannan harshe. Suka ce duk kalmar da ke nuna mai aiki (faa’il), dole ta kare da rufu’a; duk wacce ke nuna wanda aka yi aiki a kanshi, dole ne ta kare da fataha. Duk wadannan ka’idoji ne da ke nuna ma mai koyo hanya mafi sauki wajen sanin abinda yake son koyo, cikin sauki. Duk inda ya ga kalmar suna ta kare da rufu’a, ya san kai tsaye, sunan wanda yayi aiki ne. Haka idan muka nufo zauren malaman addinin musulunci, suma ba a bar su a baya ba; malaman fikihu na da nasu, abinda suke kira Al-kawaa’idul Fiqihiyyah. Haka Malaman Hadisi da tafsiri da dukkan fannonin ilimin addini, duk zaka samu suna da dunkulallun ka’idoji masu sawwake ma mai koyo hanyar tara karatu cikin ‘yan kananan kalmomi gajeru. Malaman fikihu suka ce; dukkan ayyukan shari’a, ana lura da su ne ta hanyar niyyar mai aikin; idan aka baka ajiya, sai kayan ya bace ko aka sace, ba zaka biya ba; shari’ar musulunci ta zo ne don gyara dan Adam; duk abinda aka haramta, don yana cutarwa ne; duk abinda aka halasta, akwai amfani tattare dashi; ba a yin ijtihadi idan akwai nassi kan abinda ake Magana a kai. Wadannan dunkulallun ka’idojin fikihu kenan. Idan muka ziyarci malaman mandiki kuwa, su ma ba a bar su a baya ba. Suka ce: duk wata halitta mai tafiya da kafan ko cikinta ta a doron kasa, to dabba ce; dan Adam dabba ne mai Magana. Da sauran ka’idojin da suma suka assasa. Da wannan, na tabbata mai karatu ya fara fahimtar inda muka dosa wannan mako. To amma wani na iya tunanin cewa ”wai me ya shafi Intanet, wajen muhimmanci, da har za a samar masa wasu ka’idoji dunkulallu? Wani amfani hakan ke da shi ga masu lilo da tsallake-tsallake a duniyar Intanet?”. Fahimtar amfanin da ke tattare da hakan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.

Duniyar Intanet da Ka’idojin Rayuwa:

Idan masu karatu basu mance ba kuma suna tare da wannan shafi, mun sha nuna cewa tsarin rayuwa a Intanet, kadan ya sha banban da tsarin rayuwa a zahiri. Shi yasa ma zaka samu a kusan dukkan kasashen Turai da bangaren Amurka, suna da dokoki na musamman kan wannan fasaha, wanda galibinsu kusan iri daya ne da wadanda ake da su a cikin kundin mulkin kasashen. Suna haka ne don kada wani ya dauka cewa akwai banbancin tsari tsakanin rayuwa ta zahiri da wacce ake yi a Intanet. Yadda zaka tafka laifi a zahiri a kai ka kotu, to haka idan ka aikata makamancin sa a duniyar Intanet, kuma aka kama ka, sai a zarce da kai kotu, don yanke maka hukuncin da ya kamata. Ba nan kadai ba, idan muka shiga gidajen yanar sadarwan fatawowi na musulunci, zamu ga kusan dukkan tambayoyin da ake aiko musu masu alaka da hukuncin da ya shafi mu’amala da/a Intanet, amsoshin daga tsarin mu’amalar zahirin yau da kullum ake ciro su, don kwatanta abinda ya shafi hukuncin, tare da bayar da fatawa. Wannan ya faru ne saboda dukkan nassoshin da ake kafa hujja da su, basu takaitu da wani zamani ko shekaru ko yankin mutane ban da wasu ba, a a, kawai mizani suke tattare dashi, wanda da zaran an auna aikin da aka yi, sai a san hukuncin, daga irin ka’idar da nassin ya bayar. Kenan, wannan ke nuna mana cewa akwai alaka mai karfi tsakanin rayuwa ta yau-da-kullum da kuma wacce ake gabatar da ita ta hanyar fasahar Intanet.

Daga bayanan da ke sama, a tabbace yake cewa akwai alaka tsakanin tsarin rayuwa a Intanet, da kuma rayuwa a zahiri. In kuwa haka ne, kenan da akwai bukatar ka’idoji da zasu taimaka ma dukkan mai rayuwa a wadannan duniyoyi biyu masu kama da kuma alaka da juna. Shi yasa ma muka ciro tsarin ka’idojin rayuwa dunkulallu a duniyar yau, don dora su a mizanin tsarin rayuwar Intanet. Banbancin kawai, shi ne na harshe da kuma al’ada. A nan, kusan dukkan ka’idojin Bahaushe ne muka dauko, kuma mun yi haka ne saboda samun cikakkiyar fahimta kan sakon da muke son isarwa. Wannan bai hana wani ya kirkiro irin wadannan dunkulallun ka’idoji da wani harshe daban ba, duk za su dauka. Duk wannan, don mai karatu ya samu tsira ne, in ya so, yayin da yake mu’amala da wannan fasaha a duk inda ya samu kansa. Riga-kafi, inji Hausawa, ya fi magani. Idan kuwa ya rasa wani abin da zai taimaka masa ganin hanya, to fa, duniyar Intanet wata duniya ce mai cakude da rikitattu da kuma natsattsun al’amura, idan baka da mizanin tantance su, zaka samu matsala. Wata duniya ce wacce hatta kofar shigarta (kwamfuta), na da wani kebantaccen tasiri ga kwakwalwan mai mu’amala. Kana bukatar dunkulallun ka’idojin da zasu kwaranye maka yanar da ke idanunka, don ganin hanya da kyau, kada ka yi ta cin karo da kaya da sauran su. Duniya ce da zaka yi mu’amala da dukkan nau’ukan mutanen da ka san suna duniyar zahiri, amma a wani yanayi da kimtsin day a sha banban da wanda kake kai yanzu. Kaga idan baka dauko ka’idar ka ta yau da kullum ka sa a gaba ba, ina rayuwa zata yi kyau? Duniya ce da akwai tabbacin sai alakar kasuwanci ta hada ka da wani ko wasu, wanda kuma dole ne ka yi wannan alaka. Kana bukatar mizani don tantance waye zaka iya ingantacciyar alaka da shi don samun abinda kake so. A duniyar Intanet, kusancin al’adu da cakuduwar su yafi kusancin da ke tsakanin mutane a zahiri, masu banbancin al’adu. Kana bukatar samun abinda zai haskaka maka don tsintar al’ada mai kyau da guje ma mara kyau. In kuwa ba haka ba, zaka jefar da naka mai kyau ka dauki wanda bai da kyau ko bai dace da kai ba, ba tare da ka sani ba. A halin yanzu, yana da kyau mai karatu ya lura, cakuduwar ka da mutanen wasu kasashe ta hanyar Intanet, shi yafi sauki fiye da a ce ka sadu dasu a bayyane; wani mutumin da zaka hadu dashi a Intanet, ta yiwu ma har duniya ta nade ba zaku sake haduwa ba, saboda irin tazaran da ke tsakanin kasashenku. Har wa yau, yadda ka san zaka bukaci abokiyar zama don kulla alakar aure a duniyar zahiri, haka galibin wasu suke yi ta hanyar Intanet. Makonni biyu da suka gabata, gidan talabijin tauraron dan Adam da ke Gabas-ta-tsakiya mai suna Al-Arabiyyah, tai hira da wani saurayi dan kasar Ingila da yace ya rasa yadda za a yi ya samu matar da zai aura, kuma duk abin ya ishe shi. Don haka sai kawai ya bude gidan yanar sadarwa (web site), inda yake shelan wacce zata zama matarsa. Ai kafin kace me, ya samu yan mata sama da talatin da tara, daga kasashe daban-daban, da hotunansu da kuma tarihin su. Wannan bai sa ya rude ya bi na kyaun hotuna ba, sai da ya samu mizani da ka’idar tantance wacce ta fi masa, duk da nisan da ke tsakanin kasarsa da na wannan budurwa, sannan ya dace. Kan ka ce me! Sai gashi sun kulla aure, bayan ya ziyarce ta, ya ga irin yanayin rayuwarta a can kasar Austiraliya (Australia). Na san wannan ba kowa bane zai iya yi a wannan bangaren duniya da muke ciki, saboda tsarin rayuwa da al’adun mu. To amma mu lura, me ya cece shi? Samun ka’ida mai kyau wacce tai masa, kafin zaban wacce zai aura. Duniyar Intanet na cike ne da miyagun akidu a bangare daya, da kuma nau’ukan ilmummuka masu amfani a daya bangaren, sai kuma aka cakuda su a muhalli daya. Idan ba ka da ka’idar rayuwa da mu’amala, gaya min yadda zaka yi wajen tantance su? Haka idan muka zo kan addini; ai mun sha jin labarin wadanda ke musulunta sanadiyyar karanta kasida ko makala dangane da tsarin musulunci, da ace bundun-bundun suka yi ta yi a gidajen yanar sadarwa, ai idan ba tsananin rabo ba, babu yadda za a yi su samu bayanan. To amma sun san abinda suke nema, da kuma in da zasu je su same shi. Kuma duk abinda ka basu, idan ba shi suke nema ba, zasu mayar maka da kayanka. Idan basu shiga da ka’idojin binciken da zasu yi ba, ta yaya zasu samu abinda suke so? Daga karshe, Intanet wata duniya ce wacce dan karamin aikin da zaka yi wajen matsa wani mashigi ko fita daga wani wuri, na iya tasiri wajen sauya rayuwarka gaba daya, kamar yadda wasu suka yi haka, suka samu farin ciki ko bakin ciki dawwamamme a rayuwarsu. Allah Yai mana jagora, amin. Duk wadannan, ishara ne nake mana na dalilan da suka sa dole mu samu dunkulallun ka’idojin da zasu taimaka mana gabatar da mu’amala a Intanet.

Kammalawa:

Daga karshe, zan so mai karatu ya san cewa wadannan ka’idoji nine na kirkire su a wannan tsari. Zai kuma yi wahala kaje wani littafi ko gidan yanar sadarwa ka same su a rubuce a jumlace. Na yi la’akari ne da irin tsarin da muke dashi a rayuwa ta al’ada da addini, na ga dacewar kawo mana su don samun makama a wannan duniya mai cakude da fari da baki. Bayan haka, asalin ka’idojin nan fa ba wasu sabbin kalamai bane wanda bamu taba jin su ba, a a, kari ko salon Magana ne da Bahaushe ke amfani da su a matsayin dunkulallun ka’idojin sa na rayuwar yau da kullum. Sai muka dora su a matsayi ko tsarin rayuwa ta Intanet, in da mai karatu zai kara sanin dangantar da ke tsakanin wadannan filayen rayuwa biyu; rayuwar zahiri da ta Intanet. A karkashin kowace ka’ida, akwai bayanai filla-filla kan yadda mai karatu zai sarrafa ta. Sannan wasu ka’idojin sun yi ma wasu ka’idojin kaidi, ma’ana akwai ka’idojin da ba dukkan lokuta zaka yi amfani dasu ba, suna da kayyadadden lokaci ko wuri ko yanayi, kamar yadda ka’idar masu shirya ka’ida ke cewa: kowace ka’ida da kaidinta. A mako mai zuwa za mu fara kawo wadannan dunkulallun ka’idoji da bayanan su. Ka’idojin guda ashirin da daya ne, kuma zamu kawo guda goma sha daya a mako mai zuwa, sauran kuma mu karasa su a makon sama. Sai a biyo mu don samun cikakkun bayanai. Idan da abinda ba a fahimta ba, sai a rubuto. Har wa yau, idan an samu kurkurai sai a sanar damu don gyara. Muna mika sakonnin gaisuwa da godiyar mu ga dukkan masu bugo waya ko rubuto sakonnin gaisuwa da ban gajiya. Allah bar zumunci, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa

Garki II, Abuja.

080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com