Mukaddima
Makonni kusan hudu da suka gabata na sanar da masu karatu cewa akwai wasu tambayoyi da aka rubuto masu bukatar bincike don samun gamsassun amsoshi. A nan take nayi alkawarin samun lokaci do fayyace mana zare da abawa
“The Black Box Theory”
Kafin mu dukufa, yana da kyau mai karatu ya san wani abu dangane da tsarin da dukkan karikitai da hanyoyin sadarwa na zamani ke gudanuwa a kai. Wannan zai taimaka masa wajen rage yawan tambayoyin da ka iya haifuwa cikin kwakwalwan sa a yayin da yake karanta wannan bayani da ke tafe. Domin duk yadda na kai da fayyace bayanai, zai dan yi wahala mai karatu ya samu cikakkiyar gamsuwa ko fahimta, dangane da abinda ake Magana a kai. Don fahimta kam za a fahimta, iya gwargwado. Dalilai biyu ne suka haddasa haka; na farko shine ganin cewa da harshen Hausa bayanan ke zuwa, wanda kuma ba shi bane asalin harshen da na karanto ilimin daga gareshi. Na biyu kuma, ko da ma da turancin ne, wasu abubuwa ba zasu taba bayyana maka a fili ba, ko da kuwa wadannan na’urori a gabanka suke, ina maka bayani. Wannan tasa na kawo ka’idar “Black Box”, don rage mana wahalar neman cikakkiyar fahimta. Kuma ga abinda wannan ka’ida ke nufi.
Na tabbata masu karatu sun taba gani ko ma sun mallaki kayayyakin sadarwa irin su Talabijin ko Radiyo ko wayar tafi-da-gidanka (wayar salula) ko wayar tangaraho (landline) ko kuma kwamfuta ma a takaice. Idan bamu mallaki duka ba, to a takaice mun mallaki wasu ko wani daga cikinsu. In ma bamu taba mallakan kowanne ba, to a kalla dai mun taba sarrafa wani daga ciki. Wadannan kayayyakin sadarwa, muna sarrafa su ne ta hanyoyin da makerinsu ya tanada mana, mafi sauki; daga abin murdawa zuwa matsawa ko dannawa ko kuma turawa – sama ko kasa. Kuma galibi bamu damu da sanin tsarin yadda injin su yake ba. Idan ma mun sani, to bamu san me da me ke haduwa, abu kaza da kaza su kasance ba. Da zaran kana amfani da wayar salula sai ta lalace, ba abinda ya dame ka, daukawa zaka yi zuwa wajen mai gyara. Amma idan ba lalacewa tayi ba, ba ruwanka da cewa “me da me aka kera injin wannan na’ura dashi”; in har zaka kunna Talabijin ka ya kama Magana da nuna maka hoto, ko ka kunna rediyonka ya fara Magana har ka kama tashoshi, ko ka kunna kwamfutarka ta kama aiki, ba ruwanka da abu kaza ne ya kasantar da kaza, ko kadan. Kuma da zaka bude injin, ba abinda zaka gani sai wayoyi da sauran karikitai. Ba ruwanka da tambayar “ta yaya aka yi wadannan ‘yan kananan wayoyi ke jiyar da ni Magana daga wannan akwatin rediyo, ko ganar da ni hotuna daga wannan talabijin? Wannan tunani, mai sa damuwa da zahirin fasaha ko na’ura kadai, ba tare da sanin yadda na’urar ko fasahar ke sarrafa kanta ba a fasahance, shi ake kira “The Black Box Theory”. Kuma shine tunanin da ke kwakwalwan kusan dukkan mai amfani da kayayyaki ko na’urar sadarwa na zamani a yau. Kai dai a ci baure, amma ban da tona cikinsa. A iya tunani na, wannan shi ne Karin maganan da za a iya kwatanta shi da wannan ka’ida ta “Black Box”, a takaice.
To me yasa galibi ake da wannan irin tunani? Saboda alaka iri biyu ce tsakanin kowace irin na’ura da mai sarrafa ta. Alakar farko ita ce wacce ke tsakanin na’urar da karan kanta; ma’ana, tsakanin ruhin na’urar, wanda ke sarrafa gangar-jikin da mai mu’amala ke iya gani har take bashi sha’awa. Wannan tasa dukkan iliminsa na mu’amala ya takaita a nan. Sai alakar da ke tsakanin sa da na’urar, wanda ke nuna masa tana da lafiya ko babu. Idan na’urar na da lafiya, wannan shine abinda yake so. Amma da zaran ta fara zazzabi, to ilimin sa ya kare. Sai dai yayi kirdajen alamun da take nuna masa. Kuma shine abinda zai
Ma’anar “Computer Network”
A turancin kwamfuta idan aka ce “Networking”, ana nufin tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci (daga biyu zuwa sama), wajen mikawa da karban bayanai, ta hanyar wasu ka’idoji da kowace kwamfutur ke iya fahimta. Wannan tsari na daga cikin dalilan da suka haddasa ma kwamfuta shahara wajen tasirin yada ilimi da harkokin sadarwa a duniya gaba daya, ciki har da fasahar Intanet. Samuwar wannan tsari ya sawwake daman shiga wata kwamfutar daga wata, a cikin gida ne ko a ofis ko kuma a wata jiha ce daban. Kai a takaice dai kana iya shiga wata kwamfutar da ke wata kasar, kana zaune a dakinka ko ofishinka. Duk ta albarkacin wannan tsari na mikawa da karban bayanai a tsakanin kwamfutoci. Yadda kasan mutane na mu’amala a tsakaninsu, to haka ma kwamfuta ke yi. Af, to me ye abin mamakin? Mutum ne fa ya kirkira! Akwai abubuwa biyu da ke haddasa mu’amala tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar ‘yar uwanta. Abu na farko shine samuwar kwamfuta a kalla biyu, masu dauke da manyan manhajojin kwamfuta, watau Operating System, irinsu Windows ko Mac da dai sauransu. A cikin wannan babban manhaja ne ake da Jami’an Sadarwa watau Network Drivers, da kuma Katin Tsarin Sadarwa da ke cikin akwatin kwamfutar, mai suna Network Card. Abu na biyu kuma shine samuwar komatsen da ke sadar da kwamfutocin, a bayyane ko kuma ta wayan iska (Wireless).
Wadannan komatsen sun hada da wayoyin kebul irinsu Twisted Pair (IJ45), da Twisted Pair (IJ11), da Coaxial Cable da Fibre Optic Cable. Sai kuma na’urori irinsu Wireless Frequency Radio (Wi-Fi), da Routers, da Switches da kuma Satellite Dish da dai sauran komatse. Da wadannan ake sadar da bayanai tsakanin kwamfuta da kwamfuta, kai har ma da wayar salula da Talabijin da rediyo. Bayanan da ke fita daga wannan kwamfuta zuwa wancan na yin hakan ne ta hanyar wutar lantarki da ke bi tsakanin waya da waya ko tsakanin na’ura da wayar iska. Abin sai a hankali. Wadannan su ne karikitai na zahiri da mai karatu zai iya gani a yayin da kwamfuta ko wani na’uran sadarwa ke sadar da bayanai zuwa wata ko kuma ga masu kallo ko sauraro.
Nau’uka
Tsarin sadarwa daga kwamfuta zuwa wata kwamfutar ‘yar uwan ta, na daukan nau’i uku. Akwai tsarin sadarwa ta zahiri da ke shiga tsakanin kwamfuta da wata kwamfutar da ke cikin gida ko daki ko kuma ma’aikata daya, da ke bigire daya, ko da kuwa ba a hade ginin suke ba. Wannan tsarin shi ake kira Local Area Network (LAN), kuma yana da hanyoyin sadar da kwamfutoci iri biyu ne; hanyar amfani da wayoyi na zahiri, musamman wayoyin Twisted Pair (IJ45) ko Fire-optic Cables, da kuma Switch, musamman idan tsakanin wani gini ne da wani. Hanya ta biyu kuma it ace ta hanyar wayar iska, watau Wireless, wanda kuma ake iya yi ta amfani da na’urar Wireless Frequency (Wi-Fi), da sauran na’urori makamantan su. Wannan shine tsarin Local Area Network, ko kuma Gajeren Zangon Intanet, a Hausance. Nau’in sadarwa ta biyu kuma ita ce wacce ta fi wannan fadi; tsakanin gari da gari, ko jiha da jiha, ko kauye da wani kauyen. Wannan shi ake kira Wide Area Network, watau Faffadan Zangon Sadarwa. Galibin kamfanoni masu rassa a wasu wurare kamar jihohi ko birane, sun fi amfani da wannan tsari. Inda za a iya sadar da bayanai tsakanin dukkan rassan, ba tare da wata matsala ba. Wannan tsari shi galibinsa ta wayar iska ake yinsa, watau Wireless. A
Tsarin Mikowa da Karban Bayanai
A kowane hali ya kasance, a
Kammalawa
Na tabbata har zuwa yanzu mai karatu na dai ji na ne kawai, ba tare da wata cikakkiyar fahimtar almaran da nake cusa masa a kwakwalwa ba. Kada ka damu, zuwa mako mai zuwa abubuwa zasu fara budo maka. Shi yasa nayi kandagarki a farkon makalar, don kada a zarge ni. A mako mai zuwa, zamu yi bayani ne
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off
Garki II,
http://fasahar-intanet.blogspot.com, http://babansadiq.blogspot.com
Gaskiya naji dadin wannan bayanan kuma sun temaka min gurin kara fahimtar Harkar sadarwar computer wato "networking" Allah ya karo basira. Amin
ReplyDeleteAbubakar Hassan Yahaya
ahykematious@yahoo.com