Ban Hakuri
Sabanin yadda nayi alkawri cikin shekarar da ta gabata cewa a duk mako zan rika buga sakonnin tes ko na Imel da masu karatu ke aikowa, tare da amsa su, hakan bai faru ba saboda shagala irin tawa. Da fatan za a min hakuri kan abinda ya wuce, kuma zan ci ga da ganin cewa na lazimci wannan dabi’a, don tafi sauki. A yau zan amsa dukkan sakonnin tes da kuka aiko a baya, sannan kuma a makonni masu zuwa in ci gaba da bin tsarin da nayi alkawari. Kamar kullum, muna mika godiyarmu ga dukkan masu aiko da sakonnin godiya da gamsuwa, da masu bugo waya don yin hakan su ma; musamman ganin cewa baza mu iya ambaton sunayensu ba, saboda yawa da kuma maimatuwan hakan a lokuta dabam-daban. Mun gode matuka.
Mu’amala da Intanet a Wayar Salula
Salamun Alaikum Baban Sadik, don Allah ko zan iya saukar da Opera Mini a cikin waya ta nau’in “Sagem My X-7”, don shiga Intanet a saukake? - Dalibinka, Abdu Maigyada, Jas: 07031297258.
Malam Abdu Maigyada sannu da kokari, kuma mun gode da wannan sako naka. Saukar da manhajar “Opera Mini” a wayar salula ba wani abu bane mai wahala. Sai kaje inda ake shigar da adireshin gidan yanar sadarwa a wayar, ka sanya wannan rariyar likau din: http://mini.opera.com. Idan shafin ya budo, sai ka zabi zubin (version) manhajar (“Version 4.2”), ka matsa. Nan take wayarka zata saukar da manhajar a cikinta, sannan ta tambayeka ko kana son a loda maka wannan manhaja ta yadda zaka iya amfani da ita. Idan ka amsa, sai ta loda maka. Daga nan sai kaje inda aka ajiye maka ita, don ci gaba da amfani da ita. A karshe, ka tabbata kana da rajista da kamfanin wayarka, in kuwa ba haka ba, to baza ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar ba. Da fatar ka gamsu.
Assalaamu Alaikum, don Allah ka taimaka min wajen samar da hanyar karanta jarida ta hanyar Intanet a waya ta. Wayar ita ce “TECNO 570”. - 07084085752
Bayanai kan yadda ake iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula sun sha maimaituwa a wannan shafi. Amma a gurguje, kayi rajista da kamfanin wayarka don samun damar iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, sannan ka tabbata akwai ka’idojin WAP da ke taimaka ma wayar salula yin hakan. Wadannan, a takaice, su ne muhimman hanyoyin. Idan ana tare damu cikin silsilar da muka faro kan Wayar Salula da dukkan tsare-tsarenta, za a samu cikakken bayani in Allah Ya so. Da fatan za a amfana da dan abinda ya samu yanzu. Mun gode.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan kana cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin. Don Allah ina son ka sanar dani game da yadda zanyi saitin fasahar Intanet a waya ta. Domin duk sadda na tashi don na ziyarci shafin yanar sadarwa, sai a ce dani: “GPRS Not Subscribed”. Da na tuntubi kamfanin layin wayar, sai su ce: “Cannot Send Setting to this Type of Phone, Please Visit www.mtnonline.com”. Idan na tuntube su, sai suce bazan samu damar tuntuba ko kuma “Subscribe” din “GPRS” ba. To ko akwai wata hanyar da zan bi ba tare da ita “General Packet Radio Service” ba? Da fatan za ka amsa min. - Mustafa Rabi’u, Kano: 08131904162
Malam Mustafa sannu da kokari. Lallai ka sha zagaye-zagaye. Kuma ga shi baka gaya mana nau’in wayar da kake amfani da ita ba. Domin ba kowace irin waya bace ke karba, tare da iya sarrafa sakonnin da kamfanin waya ke aiko mata. Abinda wannan ke nufi shine, sai an je an sanya maka dukkan ka’idoji da kuma kalmomin da ake bukata, da hannu, watau “manual configuration”. A ka’ida, kamata yayi ace da zarar kamfanin waya ya aiko sakon tes, wayar ta kalli sakon da ya aiko. Idan na mai wayar ce, sai ta adana masa, tare da sanar dashi cewa ya samu sako. Idan kuma sako ne irin wanda waya ke iya sarrafa shi nan take, za ta ajiye masa ne. Da zarar ya budo ya karanta, zai ga abinda ake bukatar yayi da sakon. Idan bai fahimci sakon ba, kuma yayi kokarin rufewa, wayar za ta sanar dashi abinda ya kamata yayi da sakon, ta hanyar tambayarsa. Wannan na yiwuwa ne a galibin wayoyin salula na zamani, kuma na asali. Akwai wasu wayoyin da ba a tarbiyyantar dasu yin hakan ba tun wajen kera su. Ire-iren su sune irin wayoyin da ke zuwa daga kasashen Asiya. Shawarata a nan ita ce, kaje wajen duk wani mai gyarar wayar salula da ka sani, kwararre (zan maimaita: kwararre), don ya maka saitin wayar da hannu. Allah sa a dace, amin.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina amfani da waya nau’in SonyEricsson Z520i, don Allah ina son a taimaka min da yadda zan rika aikawa da sakonni da bude su idan an aiko mani. - Ibn Fiqh, Saabiqus-Thabaty, Trikania, Nassarawa, Kaduna: 08131392572
Malam Saabiq barka da war haka, da fatan ana lafiya. Baka sanar damu ko a halin yanzu kana iya mu’amala da fasahar Intanet a wayarka ba. In kana iyawa, sai kaje inda ake shigar da adireshi a wayar, ka sanya: http://mobile.yahoo.com/mail/p Ga masu amfani da wayar salula nau’in “iPhone”, su shigar da: http://mobile.yahoo.com/mail/iPhone Wannan shine adireshin shiga manhajar Imel na kamfanin Yahoo! a wayar salula. Shafi zai budo inda zaka shigar da suna (username) da kalmomin shiga (password), sannan ka matsa inda aka rubuta “login” ko “enter”, don shiga. Idan ka shiga, za ka ga sakonninka, sai ka matsa duk wanda kake son karantawa. Idan kuma sako kake son aikawa, sai ka dubi sama a shafin, za ka ga alamar “compose”, sai ka matsa. Shafin allon rubutu zai budo maka, sai ka shigar da adireshin wanda kake son aika masa, ka gangaro kasa don shiga allon rubutun, in ka gama rubutawa kuma, sai ka gangaro kasa har wa yau, ka matsa alamar “Send”, don aikawa. Idan baka mu’amala da Intanet a wayar, sai ka nemi kamfanin wayarka ya aiko maka da tsarin da zai taimaka maka wajen yin hakan. Gamsassun bayanai kan wannan tsari na nan tafe a silsilar da muka faro kan wayar salula. Da fatar ka gamsu.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Bayan haka, wai shin don Allah me yasa idan kana lilo a Intanet ta wayar salula, baka samun shafin da ka ziyarta gaba dayansa, ba kamar yadda kake samu ba idan a kwamfuta ce, sai dai kawai a dan tsakuro maka wasu bayanai? - Ahmad M. Umar, Na’ibawa, Kano: 07068196146
Malam Ahmad barka da war haka. Ai “kama da wane, bata wane”. Ma’ana, babu yadda za a yi a samu daidai tsakanin shafin kwamfuta da na wayar salula wajen bayyana shafukan gidajen yanar sadarwa a wayar salula. Saboda girman shafukan da ke gidajen yanar sadarwar, baza su yi daidai da girman shafin da ke wayar salula ba. Abu na farko kenan. Abu na biyu kuma shine, a halin yanzu galibin gidajen yanar sadarwa suna kera shafuka na musamman da wayoyin salula ke iya shigansu ba tare da wata matsala ba. Zaka samu muhimman abinda kake bukata a shafin baki daya. Gidajen yanar sadarwa na manyan kamfanonin kwamfuta irinsu “Yahoo!”, da “Google” da “MSN” duk suna da irin wannan tsari. Don haka idan kana amfani da rariyar lilon da ke wayar ne (watau “Phone Brower”), wacce wayar ta zo dashi, to kana iya samun shafuka wadanda suka dace da yanayin wayarka. Da zarar ka shiga shafin, sai a loda maka wadannan shafukan na musamman da suka dace da wayar. Amma idan kana amfani ne da “Opera Mini”, misali, kana iya zuwa wajen “Settings”, ka tsara masarrafar ta yadda shafukan da ka shiga zasu rika budowa daidai da yanayin wayarka. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu Alaikum, don Allah me yasa wayoyin salula na kasar Sin (China) basu iya shiga Intanet? - Sa’idu Danjuma, Kawo, Kaduna: 08096420965
Malam Danjuma, ban taba amfani da wayoyin salula na kasar Sin ba, amma nakan ji jama’a na korafi kansu sosai. Tabbas na gansu, na kuma shiga cikinsu don ganin yanayi da tsarinsu a fasahance. Suna da nakasu sosai ta bangaren sadarwa da mu’amala da wata waya ‘yar uwanta. Don haka, matsalar rashin iya mu’amala da fasahar Intanet a wayoyin Sin na komawa ne zuwa ga dayan dalilai biyu: na farko, ko dai ya zama saboda yanayin kiransu ne – ma’ana basu da ingancin da zasu iya taimakawa wajen yin hakan ta dadi. Na biyu kuma yana iya zama saboda rashin samun sinadaran da zasu taimaka mata don yin haka daga mai wajen mai ita ne. Misali, dole ne a samu tsarin da ke taimaka wa waya daga kamfanin waya, watau “Configuration Settings” kenan, kuma ya zama wayar tana da ka’idar mu’amala da Intanet, watau “Wireless Application Protocol”, ko “WAP” a gajarce. Da fatan ka gamsu.
Salamu Alaikum, ina son na kwafi bayanai daga Mudawwanar “Fasahar-Intanet” zuwa waya ta, amma da zarar na fara, sai ta nuno min: “out of memory”. Ya lamarin yake ne? - Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07027275459
Idan haka ta kasance, hakan ke nuna cewa ma’adanar wayar salularka bata iya daukan yawan bayanan da kake son zuwa mata daga shafin da ka kwafo su. Don haka ka tabbata kana da wuri ko ma’adana mai yawa da zai iya karban mizanin bayanan da kake son kwafowa zuwa wayar. “out of Memory” na nufin mizanin ma’adanar wayarka yayi kadan ga bayanan da ka kwafo. Da fatan ka gamsu.
Kwayar Cutar Wayar Salula
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kai da abokan aiki kuna cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin. Shin da gaske ne wai kamar yadda na’ura mai kwakwalwa ke harbuwa da cuta (virus infection), haka ma wayar salula (irinsu Nokia E-Series da makamantansu) ke harbuwa da cutar? Kuma ko mutum zai iya sa wa wayarsa kariya, watau Anti-virus? - Uncle B. Bash, Jimeta, Yola: 07069045367
Dubun gaisuwa da fatan alheri ga Uncle Bash, da fatan ana cikin koshin lafiya. Tabbas haka ne; wayoyin salula na kamuwa da kwayoyin cuta kamar yadda kwamfutoci ma ke kamuwa. Domin kusan duk tsarinsu iri daya ne. Kai ba ma su kadai ba, hatta na’urorin janyo siginar tauraron dan Adam na zamani da muke amfani dasu wajen kallon tauraron dan Adam (watau “Satellite Receivers” ko “Decorders”), duk suna iya kamuwa da kwayoyin cutar. Babban dalili kuwa shine, saboda tsari da kimtsin ruhin da suke amfani dashi duk iri daya ne. Ana iya sanya wa wayar salula manhajar kariya da goge kwayoyin cuta, watau “Anti-virus”. Akwai manhajoji na musamman da aka gina don wannan aiki. Wasu kyauta ake samunsu. Wasu kuma sai da kudi. Yana da kyau mai karatu ya san cewa samun wadannan manhajoji kyauta a wajen masu sanya abubuwa a wayar salula da muke dasu a biranenmu, ba zai iya kare wayar daga kamuwa ba, sai ana kara wa manhajar tagomashi ta hanyar Intanet, don tabbatar da cewa ta haddace sunayen dukkan kwayoyin cutar da ke rayuwa a zamanin da take. Wannan shi ake kira “Virus Update”, kuma kana iya yin hakan ne ta hanyar manhajar, idan akwai ka’idar Intanet a wayar. Idan kaje inda ake yin “Update” din, ka matsa, za a shige da kai ne kai tsaye zuwa shafin kamfanin da ya kirkiri manhajar, don bai wa manhajar damar haddace sabbin sunayen kwayoyin cutar da bata sansu ba. In kuwa ba haka ba, to babu wani amfani da za a samu na kariya, wai don an sanya ma waya wannan manhaja. Da fatan ka gamsu.
Salam, don Allah ka taimaka min da inda zan yi da kwayar cutar kwamfuta a waya ta, watau Virus. Don suna tayar min da hankali. Ka huta lafiya! - 08023672341
Shawarar da zan bayar ita ce, aje a samu masu gyarar wayar salula don su duba wayar. Don a nan bazan iya sanin wasu dabi’u take nunawa ba balle in san shin kwayar cutar kwamfuta ce ta kama ta ko a a. Amma idan aka je wajen masu gyara, suna iya fahimtar hakan. Allah sa a dace.
Shawara kan Kwarewa a Ilmin Kwamfuta
Assalam Baban Sadik, Allah Ya kaddare ni da karanta kasidarka mai taken: “Hanyar Sadarwa ta Rediyo a Intanet”, wadda ka rubuta a jaridar AMINIYA tun watan Agustar bara (2008), kuma nayi murna musamman ma da na ga wanda ya rubuta ta musulmi ne. Bayan haka, nayi Difloma kan Ilmin Kwamfuta amma har yanzu ban samu kwarewa mai zurfi ba a fannin Intanet, amma wasu hanyoyi suka kamata na bi? Wassalam - 08063446395
Malam barka da war haka, kuma mun gode da wannan sako na neman shawara. Ya danganci abinda kake nema ko son kwarewa a kai. Idan so kake ka dauki fannin Intanet a matsayin fannin kwarewa da cin abinci, sai ka sake neman makarantun da ake koyar da ilmin kwamfuta, don yin nazari na musamman a kai. Idan kuma a matsayin fannin sha’awa ne kawai da motsa kwakwalwa, sai ka lazimci ziyartar gidajen yanar sadarwa don sabawa da fasahar. Kwarewa kan fasahar Intanet ba karatu bane tsantsa, a a, aikata abinda aka koyo ne lokacin karatu. Wannan, a takaice shine abinda zan iya cewa. Ina kuma rokon Allah ya baka juriya da kwazo da dagewa kan abin. Da fatar ka gamsu.
Girgidin Jirgi a Saman Tsauni
Malam Abdullahi nakan ji wasu suna cewa: idan jirgin sama yazo saitin tsaunuka, ana fahimtar jirgin yana girgiza. Me ye gaskiyar lamarin ne? - Khalil Nasir Kuriya, Kiru: 07069191677
Malam Khalil barka da kokari. Watau wannan Magana haka take: lallai jirgi kan girgiza idan yazo saman tsauni a halin tafiyarsa. Ba ma tsauni kadai ba, ko cikin hazo ya shiga akan samu irin wannan girgiza…kaji kamar a saman duwatsu kuke tafiya. Duk wanda ya taba hawa jirgin sama, zai tabbatar maka da hakan. Bayan wadannan wurare har wa yau, idan jirgi yazo saman teku ma, yana iya samun wannan cikas. Babban dalilin da ke haddasa wannan cikas da jirgi ke samu kuwa shine idan iskar da ke sama ta kara kiba da tumbatsa zuwa sama ko kasa ko kuma gefen dama da hagu, sanadiyyar wani abinda ya tare ta a halin tafiyarta. Misali, idan iskar da ke can sama na tafiya daga gabas ne zuwa yamma, a guje, da zarar taci karo da wani tsauni, nan take sai iskar ta takura wuri guda, tayi toroko zuwa sama, ko kasa, ko kuma gefen dama da hagu. To idan aka yi sa’a (ko rashin sa’a) jirgi yazo saman wannan tsauni a daidai lokacin da iskar taci karo dashi, sai ya fara girgiza, saboda sauyin yanayin iska da ya samu. Idan a baya yana tafiya ne lafiya lau, yanzu iskar da tsaunin ya kado zuwa sama, zai kara tunkuda jirgin sama ko kasa, ko kuma zuwa wani gefe daban. Haka abin yake idan jirgi ya shiga cikin hazo. Domin shigansa cikin hazon na sauya masa yanayin iskar da ya baro a kasa ko can sama ne. Wannan tsari na sauya wa jirgi yanayin tafiyarsa sanadiyyar sauyin yanayin iska da ke sama, shi ne Malaman Fiziya (Physics) ke kira “Turbulence”. Da fatan ka gamsu.
Tasirin Wayar “Fiber-Optics” Wajen Sadarwa
Salam, tare da fatan alheri, ina fatan dukkan makaranta wannan fili muna lafiya, amin. Baban Sadik, wai ita wannan waya da kamfanin MTN take sanyawa a kasa, mene ne amfaninta ga sadarwa? Kuma mutane suna cewa tana hade da sadarwa irin ta Intanet wajen sauri; meye gaskiyar al’amarin? - Ibrahim Yahaya Mai Ruwa Dan-hutu: 07080948888
Malam Ibrahim Dan-hutu lallai wannan tambaya ce mai muhimmanci ga harkar sadarwa kowane iri ne kuwa. Ina fatan Allah ya bamu lokaci na musamman don mu gabatar da doguwar kasida kan yadda wannan tsari ke aiki. Da farko dai abinda kaji ana fada na alakar da ke tsakanin wannan waya da ake binnewa a karkashin kasa da kuma sadarwa ta wayar tarho musamman, gaskiya ne ko shakka babu. Na biyu kuma, wannan waya da ake shimfidawa, ba waya bace kamar sauran wayoyi. Waya ce ta “kunun gilasai”, wadda aka tsattsaga gwargwadon kaurin silin gashin kai. Yadda abin yake shine, gilasai ake narkawa, ko damawa, kamar kunu, sannan a sandarar dashi, tare da yayyanka shi filla-filla, ko sille-sille, ko sili-sili, gwargwadon kaurin gashin kai, sannan a hada su wuri guda, a suturce su da gasassun robobi (plastics), sannan a maye samansu da dafaffiyar roba (rubber). Wannan nau’in waya ita ake kira “Fiber-Optics”, ko kuma “Optical Fiber Cables”. Kuma su ne wayoyin da suka fi saurin isar da sakonnin murya ko bayanai ko bidiyo, saboda suna tafiya ne a matsayin haske, cikin gaggawa ba bata lokaci. Idan kana son fahimtar yadda tsarin saurin isar da sako da wannan waya ke yi, ka dubi yadda haske ke saurin isa idan aka haska tocila daga bakin wani bututu, zuwa karshensa. Nan take zai isa. Idan ma bututun ba a saiti yake ba, sai ka dubi inda yake da kwana, ka sanya gilashi a wajen. Da zarar ka kara haskawa, dungun da ke dauke da gilashi zai cilla hasken zuwa gaba, har ya isa inda ake son yaje. To idan ka dubi wannan waya da aka kera da gilasai, sai ka ga cewa da zarar ballin haske ya sauka kan sillin waya guda daya, to duk zata haskaka sauran, tare da isar da hasken da ke dauke da bayanan cikin gaugawa. Wannan kuma ya shafi hasken da ke dauke da murya ne (Tarho da Rediyo), ko bayanai (Intanet), ko kuma hotuna masu motsi da daskararru (TV da Bidiyo), misali. Don haka kake ganin kamfanin MTN (da ma GLO) suna binne wannan waya, don inganta tsarin sadarwarsu tsakanin tashoshin sadarwarsu da suka game dukkan jihohin kasar nan. Kai ba nan kasar kadai ba, galibin manyan tekunan duniya na dauke ne da wadannan wayoyi a cikinsu, ko karkashinsu, wadanda kamfanonin sadarwa na kasashe dabam-daban ke binnewa don isar da sadarwa cikin gaugawa da sauki a duniya baki daya. Da fatan ka gamsu.
Sabuwar Mudawwana
Assalaamu Alaikum, Malam a duba min mudawwana ta da ke: http://munbarin-musulunci.blogspot.com, a Intanet. - Aliyu M. Sadisu: 08064022965
Malam Aliyu sannu da aiki. Lallai na shiga Mudawwanar “Munbarin Musulunci” da ka bude a Intanet, na kuma gamsu da irin sakonnin da kake isarwa na ciyar da al’umma gaba a Musulunce. Wannan aiki ne mai gwabin lada, kuma Allah Ya albarkaci wanann yunkuri taka, amin. Dangane da tsarin Mudawwanar kuma, ina ganin ba wata matsala. Domin kana shigar da kasidun yadda ya kamata. Illa dai abinda zan iya cewa shine, ka cire alamar ruwa biyu (watau :) da ka sanya a tsakanin “BARKA DA ZUWA” da kuma “MUNBARIN MUSULUNCI”. Kawai ka mayar dashi jumla guda, kamar haka: “Barka da Zuwa Munbarin Musulunci”. Allah sa mu dace baki daya, amin.
Manhajar Canja Murya a Wayar Salula
Salamu Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: tsarin canje-canjen sautin murya na wayar salula, watau Magic Voices; Malam karin bayani nake nema dangane da yadda tsarinsa yake? - Aliyu Muktar Sa’id (IT), Kano: 08034332200
Malam Aliyu sannu da aiki, kwana biyu bamu gaisa ba. Da fatan kana cikin koshin lafiya, amin. Tsarin “Magic Voices” a fannin sadarwar tarho ko wayar salula, shine tsarin da ke bai wa mai waya damar canja sautin muryarsa da aka sanshi da ita, zuwa wata murya dabam. Misali, kana iya canja muryarka ta koma ta mace, idan namiji ne kai, ko kuma ta zama siririya, idan babbar murya kake da ita. Hakan na faruwa ne cikin sauki a wayar salula sanadiyyar wata manhaja da aka kera wayar da ita. Sannan kana iya neman ire-iren wadannan manhajojin canjin murya ka sanya wa wayarka. Duk wanda ya kira ka, kafin ka amsa, kana iya canja muryarka. Maimakon ya ji asalin muryarka, sai yaji wata murya dabam. Sai dai kuma, idan ba tsananin bukata bace ta kama, bai dace a kullum mutum ya rika yaudarar mutane da wata murya ba: ko don ba ya son Magana dasu, ko don kauce musu. Yana da kyau a kullum mutum ya zama yana wakiltar kansa. Ire-iren wayoyin salular da ke zuwa da irin wannan tsari galibinsu daga kasar Sin (China) ake zuwa dasu. Da fatar ka gamsu.
Godiya da Yabo
“Yabon gwani ya zama dole”. A cikin duka shafukan AMINIYA, shafi na 16 (watau Shafin “Kimiyya da Fasaha”) shine gwani na, saboda ina karuwa dashi ainun, kasancewar ni mutum ne mai son mu’amala da na’urar kwamfuta da sauransu. Baban Sadik Allah ya kara maka basira a kan aikinka, amin. - Bashir (GZG964), Minna, Neja: 08034629830
Malam Bashir mun gode da wannan addu’a taka, kuma Allah ya mana jagora baki daya, kuma inda an ga kura-kurai cikin abinda muke ciyar da kwakwalen mutane, to don Allah a rika tunatar damu. Allah saka maka da alheri, amin.
Jakar “Recycle Bin” a Kwamfuta
Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: meye amfanin “Recycle Bin” a jikin kwamfuta? - Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200
Malam Aliyu amfanin jakar “Recycle Bin” da ke shafi ko fuskar kwamfuta, shine taskance dukkan bayanan da ka goge ko share daga kwamfutarka. Kamar kwandon zuba shara ce, ko bola. Duk sa’adda ka goge wasu bayanai (delete) daga kwamfutar, an tsara kwamfutar ne ta yadda za ta rika zuba su a cikin wannan Kwando ko burgamin adana bayanai. Hikimar yin hakan shine, idan ka canza ra’ayi daga baya kaji kana bukatar abinda ka share ko goge, to kana iya bude wannan jaka, ka matsa jakar bayanin da kake bukata, za a mayar maka da jakar bayanin zuwa inda aka dauko ta da farko. Har way au, kana iya share karikitan da ke cikin wannan jaka gaba daya. Sai dai kuma idan ka share shikenan. Baza ka taba samun abinda ka zuba ciki ba. A takaice dai, aikin “Recycle Bin” shine ajiye maka share da ka sharo daga cikin kwamfuta. Idan kana bukata, kana iya komawa ka nemo su. Amma idan ka share su duka daga cikin jakar, shikenan. Da fatan ka gamsu.
Tsarin “GPRS” a Wayar Salula
Assalaamu alaikum, Baban Sadik ina fatan kana lafiya. Bayan haka, tambaya ta a kan GPRS ne: wani lokaci alamar “G” na bayyana a waya, wani lokaci kuma alamar “E” ne ke bayyana. Ko hakan me yake nufi, dangane da bambancin da wadannan haruffan? - Muhammad Abbass, Lafiya, Nassarawa: 08036647666
Malam Muhammad Abbass barka da war haka. Babu wani bambanci dangane da abinda wadannan alamu guda biyu ke nunawa a shafin wayarka a yayin da kake lilo ko mu’amala da fasahar Intanet. Bayyanar hakan shi ke nuna cewa kana mu’amala da fasahar Intanet ne ta hanyar tsarin “GPRS” da kamfanin wayarka ke da ita. Don haka, idan ka ga alamar “G” ko “E”, to duk suna nufin tsarin “GPRS” ne, wanda ke amfani da tsarin nau’in sadarwa ta “2G”. A wayoyin salula na zamani masu amfani da tsari ko nau’in sadarwa ta “3G” ko “3.5G”, alamar “3.5G” suke nunawa. Don haka idan kaga “E” ko “G”, to duk tsarin “GPRS” ne. Duk da yake wasu masana sun tafi a kan cewa alamar “E” na ishara ne zuwa ga ingantacciyar tsarin “GPRS” mai suna “EGPRS” (watau “Enhanced General Packet Radio Service”), mai amfani da tsarin sadarwa nau’in “2.5G”. Da fatan ka gamsu.
Majalisun Yahoo Groups
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, wane irin alfanu Internet Groups, irinsu Yahoo Groups ke dauke da shi? Malam mai zai hana ka bude wa wannan filin nashi? - Ahmad Muhammad Amoeva, Kano: 08066038946
Malam Ahmad abinda ake nufi da “Yahoo Groups” shine “Majalisun Tattaunawa ta Intanet”. Matattara ce inda mutane ke haduwa don tattauna wasu al’amura na rayuwa da addini. Wasu sun ta’allaka ne kan abinci, ko abin sha, ko tufafi, ko motocin hawa, ko zamantakewa, ko addini da dai sauransu. Tattaunawar ana yin ta ne ta hanyar sakonnin Imel. Da zarar ka shiga cikin majalisar ta hanyar rajista, duk sa’adda wani mamba ya aiko da sako, akwai wata manhaja ko masarrafar kwamfuta mai suna “Listserver” da ke cilla sakon ga dukkan mambobi. Sai ya zama abinda Malam “A” ya gani, shine abinda Malam “B” zai gani a jakar Imel dinsa. Shahararrun Majalisun Tattaunawa na harshen Hausa su ne: Majalisar Fina_finan Hausa, da Majalisar Marubuta, da Majalisar Nurul-Islam (wacce nake lura da ita), da kuma Majalisar Hausa-da-Hausawa. Wannan shawara ce mai kyau, kuma zan duba yiwuwar hakan in gani. Abinda wannan tsari ke bukata shine hadin kai da kuma lazimtar majalisar, don amfanuwa da abinda ake tattaunawa a ciki. Idan ma har na bude, to zai zama wajen tattaunawa ce da neman agaji kai tsaye ga dukkan masu matsaloli, kamar dai yadda ake yi ta hanyar tes. Tun farko ban yi hakan bane don tunatin cewa wayar salula a halin yanzu ta rinjayi rayuwar mutane. An fi karkata wajen aiko da sakonni ta hanyar wayoyin salula da hanyar Intanet. Wannan tasa na dan ja da baya. Amma dai, kamar yadda nace a sama, zan duba yiwuwar hakan nan gaba. Mun gode.
Asalin Launuka
Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta ita ce: meye asalin launuka (colours) ne? – Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200
Malam Aliyu wannan tambaya ce mai muhimmanci, kuma kasancewar bayanai kan haka sun ta’allaka ne ga tsantsar Kimiyyar lissafi da halitta a lokaci guda, nake ba da hakuri cewa sai hali ya samu zamu yi zama na musamman, don gabatar da bincike na musamman kan haka. Amsa kan haka na bukatar gamsasshen bayani, wanda fili irin na amsa tambayoyi bazai iya bamu dama ba. Don haka nake neman afuwa sai zuwa wani lokaci. Na gode.
Tsarin ‘Yan Dandatsa (Hackers)
“Hackers” da “Botnets”: akwai wani bambanci ne a tsakaninsu, ko duk abu daya ne? Ka huta lafiya. - Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677
Ko kadan ba daya suke ba. A ilmin sadarwa ta kwamfuta, idan aka ce “Hackers”, ana nufin ‘yan Dandatsa kenan, masu amfani da kwarewarsu ta ilmin kwamfuta da dukkan hanyoyin sadarwa, wajen cutar da kwamfutocin mutane ko hukumomi ko kungiyoyi, a ko ina suke a duniya. Duk da yake wasu kan yi amfani da kalmar har wa yau wajen nufin kwararru kan ilmin kwamfuta da hanyoyin sadarwa a sake ba kaidi, su kuma yi amfani da kalmar “Crackers” ga nau’in kwararru na farko. Amma abinda yafi shahara a bakin mutane a duniya yanzu idan aka ambaci “Hackers”, shine kwararru masu ta’addanci ga kwamfuta. A daya bangaren kuma, kalmar “Botnets” kalma ce mai tagwayen asali. Daga kalmomin “Robot”, da kuma “Networks” aka tsago ta. A ilmin kwamfuta da tsarin sadarwa na zamani, idan aka ce “Botnets” ana nufin gungun kwamfutoci wadanda suka samo asali daga kasashe dabam-daban, da wasu ‘Yan Dandatsa suka mallake su ta hanyar miyagun masarrafan kwamfuta, kuma suke basu umarni don su darkake wasu kwamfutoci na musamman da ke wasu kasashe ko birane a duniya. Suna yin hakan ne ta hanyar amfani da kalmomi ko lambobin kwamfutocin da suke son darkakewa, watau “Internet Protocols” ko “IP Address” a turance. Don haka, Kalmar “Hackers” tana nufin masu yin dandatsanci. Ita kuma kalmar “Botnets” na nufin tsarin aikin ta’addancin da suke yi. Da fatar ka gamsu.
Aika Sakonnin Imel
Baban Sadik, tambaya ta ita ce: shin yaya zan yi in aika da sakon Imel ga mutane da yawa a lokaci guda? - Bashir, Minna, Naija: bashir.kasim@yahoo.com
Malam Bashir, aikawa da sakon Imel ga mutane masu yawa babu wahala. Idan ka budo allon rubutu, watau “Compose”, sai ka shigar da adireshin wadanda kake son aika musu a filin da aka rubuta “To”. Idan ka rubuta adireshin farko, sai ka sanya alamar wakafi (watau “comma” - , -), sannan ka sanya na biyu, ka sa wakafi, ka sanya na uku, ka sa wakafi…har sai ka sanya dukkan adireshin wadanda kake son aika musu. Wannan haka tsarin yake: a kwamfuta kake, ko a wayar salula. Da fatar ka gamsu.
Wayoyin Salula Masu Katin SIM Biyu
Salam Malam, sai naga layin MTN a wayar salula mai Katin SIM guda biyu, yana komawa “MNT”. A wata wayar kuma, layukan suna komawa lambobi maimakon sunan kamfanin wayar. - Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07027275459
Malam Khalil, ta yiwu akwai matsala tare da wayar. Don kusan dukkan wayoyin salula na zamani suna da manhajar da ke iya nuna sunan kamfanin wayar da aka sanyan musu katin SIM dinsa. Idan kaga wayar na nuna maka “MNT”, maimakon “MTN”, a iya cewa matsalar daga wayar ce, ba daga kamfanin wayan ba. In kuwa daga kamfani wayan ne, to bai kamata ya zama a wayarka ce kadai matsalar ba, musamman a bangaren da kake. Kamata yayi a ce dukkan masu amfani da katin MTN su ma nasu ta rika nuna “MNT”. A daya bangaren kuma, rashin nuna sunan kamfanin waya a fuskar waya kuma, ya danganci kirar wayar. In har wayar ‘yar asali ce (irin nau’in “Samsung” mai katin SIM guda biyu, ‘yar asali), ba irin kirar Sin ba, ya kamata ta nuna. Amma idan kirar Sin ce, ba matsala idan bata nunawa. Hakan na iya zama nakasa ce daga kamfanin da ya kera wayar; ma’ana bai tarbiyyantar da ita yin hakan ba. Da fatan ka gamsu.
Me Ke Cin Batir a Wayar Salula?
Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta dangane da wayar salula ce: shin da kira, da amsa kira, wanne ne yafi cin batirin waya ne? - Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200
Ya danganci tsarin mu’amala da wayar. Idan wayar salula tana ajiye a kunne, ba a amfani da ita, bata cin batir sosai. Kamar mota ce ka tayar da ita, ka barta tana diri (slow). Idan kana shiga wurare don shigar da lamba ko gogewa ko wani abu daban, cin batirinta yafi na lokacin da take ajiye babu komai. Idan kuma kana sauraron wakoki, ko kallon talabijin, ko sauraron rediyo, ko yin wasa (da “games”) da sauran makamantansu, cin batirinsa yafi na yanayin baya. A karshe, idan wayar tana mu’amala da wata wayar, ta hanyar aika sako ta Bluetooth ko Infra-red ko Kwamfuta, ko kuma tana halin kara sanadiyyar kira (ringing), ko yanayin amsa kira ko yin kira da Magana da abokin kira, ko neman balas, ko neman yanayin sadarwa (Network Search), wayar tafi cin batir sosai. A takaice dai, idan waya tana mu’amala da wata wayar (ta hanyar kira ko amsa kira ko karba ko aika bayanai), ko kuma tashar sadarwar kamfanin waya (Telecom Base Station), tafi cin batir sosai. Illa dai yanayin cin ya danganci tsawon lokacin da aka dauka ne ana kira ko amsa kiran, ko aikawa da sakonnin ko karbansu. Da fatan