Friday, February 16, 2007

Labaru Daga Intanet

Kasar Sin ta Rufe Gidajen Yanan Sadarwan Masu Satar Fasaha (http://australianit.news.com.au): A wani samame na ba-zata da ta kai kan shahararrun gidajen yanan sadarwan masu satar fasahan kwamfuta daga giajen yanan sadarwa na kasashen waje, kasar Sin ta rufe a kalla gidajen yanan sadarwa 205. Jami’an gwamnatin kasar suka ce tsakanin watan Satunban shekarar da ta gabata zuwa Janairun wannan shekara, gwamnati ta saurari kararraki sama da 436, kan abinda ya shafi satan fasaha, wanda ya kunshi kararraki 130 da kamfanonin kasashen waje suka shigar kan haka. ‘Yan kasar Sin dai sun yi kaurin suna wajen satan fasaha musamman na abinda ya shafi wakoki da fina-finan da ke da cikakkiyar hakkin mallaka (copyright) daga wasu kasashe. Hakan na faruwa ne saboda dan karen tsadan da ire-iren wadannan fasaha ke da su a can. Kasar Sin na da gidajen yanan sadarwa 843,000 da masu amfani da Intanet wanda adadinsu ya haura miliyan dari da arba’in, kwatankwacin yawan ‘yan Nijeriya kenan, a kidayar bana.

HP ta Shigo Kasuwan Wayar Tafi-da-Gidanka (http://www.pcworld.com): Shahararriyar kamfanin kwamfuta da karikitanta, watau Hewlett Packard ta shiga sahun kamfanoni masu kera wayoyin salula na tafi-da-gidanka. Ta bayyana hakan ne a babban taron baje-kolin wayoyin GSM da aka yi daga ranar litinin, zuwa alhamis din wannan mako, a birnin Bercelona dake kasar Andalus (Spain). Sabon wayan, wanda ta kira shi iPaq 500 Series, na cikin sahun siraran wayoyin tafi-da-gidanka da ake yayi yanzu, kuma yana dauke ne da hanyoyin kayatar da mai mu’amala, ciki har har manhajan windows, watau Windows Mobile 6. Daga cikin kayatattun hanyoyin sadarwan da iPaq 500 Series ke dauke dasu, kana iya sauraron sakonnin da aka aiko maka a rubuce, cikin sauti, ka kuma aika da jawabi cikin sauti, a samesu a rubuce. Duk da cewa ta kirkire shi ne don kamfanoni, HP tace nan gaba za ta mika ma dilolin da zasu sayar ma dukkan mai bukata, ba sai kamfani kadai ba. Idan haka ya faru, farashin ba ya kasa dalar Amurka dari uku da hamsin ($350), wajen naira dubu arba’in da biyar kenan.

Google da Vodafone sun Kulla Yarjejeniya (http://news.yahoo.com): Babban kamfanin sadarwa na wayar salula ta duniya, watau Vodafone Group Plc, ta kulla yarjejeniya da kamfanin Google Inc., don shigar da babban taswiran kasashen duniya cikin wayoyin masu amfani da wayoyin Vodafone. “Google Maps”, wanda taswira ne da ke dauke da kwatancen biranen duniya, gidan yanan sadarwan Google ce ta kirkire shi shekaru biyu da suka gabata don taimaka ma masu ziyara a kasashe daban-daban, sanin halin da wurin ke ciki. Idan har wannan yarjejeniya ya dore, masu dauke da wayoyin Vodafone a kasahen turai musamman, zasu iya amfani da wannan fasaha wajen neman kyakkyawan kwatancen biranen da suke son ziyarta cikin sauki.


Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Garki II

Abuja.

080 34592444

Absad143@yahoo.com, salihuabdu@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com


Dangantakar Intanet da Harkokin Rayuwa (1)

Mabudin Kunnuwa:

Ga wadanda suka ziyarci wannan shafi a makon da ya gabata, sun karanta irin ci gaba da yaren Hausawa ya samu wajen shigar dashi cikin sabon babban manhajan kwamfuta da kamfanin Microsoft ke son fitarwa nan ba da dadewa ba, watau Microsoft Vista Office. Wannan ba karamin ci gaba bane da wannan harshe ya samu. Kuma wannan ke dada nuna ma mai karatau cewa nan ba da dadewa ba, Intanet zai fara shafan rayuwar Hausawa, tun da hakan na daya daga cikin muhimman dirkokin da ake bukata wajen hakan, kamar yadda bayanai suka gabata a kasidun baya. Ina taya mu murnan samuwan wannan al’amari. Wannan zai dada kara yawan kwamfuta a cikin al’umma, wanda zai sa mutane su kara sha’awan fasahar Intanet. Daga karshe, yanda muke ta jin labarin tsarin kasuwanci ta hanyar Intanet a wasu kasashen duniya, za mu wayi gari ana damawa damu ta wannan fanni. Kafin nan, zan so in sanar da mu cewa a halin yanzu akwai wasu hanyoyi da zamu iya aiwatar da harkokin rayuwa na abinda ya shafi shiga makarantu, hulda da bankuna, neman aiki, zuba jari, kafin mu kai matakin aiwatar da saye da sayarwa ta Intanet, a Nijeriya. Wannan shine tsarin da a turance ake kira e-commerce a dunkule. Wannan makon zamu yi tsokaci kan matakan da mai karatu zai bi wajen yin hakan, da hanyoyin da zai kare kansa, wajen aiwatar da wadannan harkoki, sai mu karkare da kawo misalai daga wasu gidajen yanan sadarwa da ke nan Nijeriya, a makonnin da zasu biyo baya.

Harkokin Rayuwa a Intanet:

Na tabbata mai karatu ya karanta cewa gidan yanan sadarwa (Websites) na daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen tallata hajoji da ra’ayoyi da sauransu. A yau kusan duk abinda kake tunanin ana sayar da shi, ko da hidima ne (service) wanda wani zai maka ka biya shi, zaka tarar ya gina gidan yanan sadarwa, don tallata wannan sana’a nashi. Wannan ruwan dare ne a kasashen turai. Amma a kasashe masu tasowa irin kasashen Afirka, Asiya da wani bangaren Latin Amurka, sai daidai zaka samu suna da iirn wannan tsari. Sai dai hakan na wucin gadi ne, wannan tsari zai mamaye duniya gaba dayanta, ko ana so ko ba a so. Wannan tasa dole dan Adam ya zama yana tafiya da zamani, ta fannin abinda ya shafi ci gabansa da al’umman da yake rayuwa cikinta. Duk da yake a yanzu muna aiwatar da harkoki ne a fili, ga-ka-ga-abokin hulda, nan gaba matakin rayuwa zai zama galibin harkoki basu yiwuwa ta dadi sai an kai ga Intanet. Shiga makaranta sai da Intanet. Hulda da banki wajen ajiya ko canjin kudaden kasashen waje, sai da Intanet. Zuba jari sai da Intanet. Neman aiki sai ka iya kwamfuta, don ta Intanet zaka aika da duk abinda ake bukata daga gareka. Harkan ajiyan Fansho sai da Intanet. Wadannan harkoki ne na rayuwa wanda mai karatu ba ya iya rayuwa sai yayi a kalla daya daga cikinsu. Duk da yake kafin nan, al’umma ita kanta zata sadaukar da kanta ne ga tsarin da zamanin ya kawo. Don haka mallakan makami kafin zuwan yaki ba ya nufin kana fatan zuwan yaki ne, sam. Sai don kare kai da kuma gudanar da ingantacciyar rayuwa a fuskar da take gudanuwa. Don haka akwai matakai a kalla hudu daga bangaren masu kamfanoni ko hukuma, da kuma bangaren mai mu’amala da su, irinsu ni da kai kenan, mai karatu.

Matakai:

Aiwatar da harkokin rayuwa ta Intanet, musamman abinda ya shafi saye da sayarwa, na bukatar abubuwa da dama. Duk kamfani ko hukumar da ke son aiwatar da hakan, dole ne ta bi su. Abu na farko, wanda yafi komai muhimmanci shine samar da kankararren gidan yanan sadarwa mai dauke da hanyoyin mu’amala da abokin hulda mafi sauki. Galibin ire-iren wadannan gidajen yanan sadarwan zaka samu suna da manhajar wasikar hanyar sadarwa mai zaman kansa, wanda ke hade da rumbun adana bayanansu (Database). Duk mai hulda dasu zai samu adireshin Imel da kuma kalman iznin shiga wanda babu mai irinsa. Ta wannan hanya ne kadai za a rinka shaida abokin hulda da zaran ya shigo ko aiko da bayan da ake bukata ya aiko. A wasu lokuta kuma katin biya (scratch card) zaka saya, misali wajen biyan kudin makarata. Da ka shigo gidan yanan sadarwan, zaka samu inda aka tanada maka don shigar da kalmin da ke kunshe cikin katin. Dukkan wadannan bayanai da zaka aika, suna zuwa ne kai tsaye cikin uwar garken gidan yanan. Hanya ta biyu kuma it ace samar da cikakken bayani kan haja ko tsarin da ake son mai mu’amala ya bi. Idan haja ce, nawa ake sayarwa, kuma ta yaya mai saya zai samu riskuwa da abinda ya saya? Da dai sauran bayanai. Misali, dole ne a tanada ma mai mu’amala hanyoyin da zai bi wajen shigar da bayanai da nau’in bayanan da ake so ya shigar. Wannan zai taimaka masa wajen aiwatar da abinda ake so, ba tare da matsala ba. Idan banki ne, a taimaka maka da bayanai kan yadda zaka shigar da nambobin ajiyarka da sauran bayanai. Idan makaranta ce, a tanada maka bayanai kan yadda zaka cika fam, da irin bayanan da zaka bayar, da kuma lokacin da zaka samu sakamakon abinda kake nema da sauransu. Hanya ta uku kuma ita ce tsare sirrin abokin hulda, watau Privacy, a turance. Galibin gidajen yanan sadarwa a turai, su kan sayar da bayanan abokan huldansu, wanda suka tara sanadiyyar saye da sayarwa da suka gudanar a gidan yanansu. Wannan ta tilasta ma hukumomin wadannan kasashe tsara doka wanda ya zama dole a tsare ma masu mu’amala bayanansu. Mataki na karshe kuma shine tanada ma masu mu’amala sashin taimako, watau Help Section. Wannan zai taimaka ma mai mu’amala samun warware lalular da ya shiga wajen mika bayanai ko aiwatar da huldodinsa a gidan yanan sadarwan. Wadannan a takaice su ne matakan da duk wani kamfani mai mu’amala da kwamstomomi ta hanyar Intanet ke bukatar tabbatar dasu, don samun dorewa da amincewan abokin mu’amala.

A bangaren mai saye ko kuma mu’amala, yana bukatar matakai hudu shi ma, don samun saukin mu’amala wajen gabatar da harkokinsa. Na farko, ya tabbata cewa adireshin gidan yanan sadarwan da ka samu ingantacce ne, ban a bogi ba. Domin akwai wadanda suka shahara wajen tsara gidajen yanan sadarwan kamfanoni, musamman wadanda suka shahara a duniya wajen kasuwanci da hulda da jama’a, don kautar da masu hulda da kuma sace masu bayanan katin adashin bankinsu. Idan ba tsananin lura kayi ba, ba za ka gane banbancin da ke tsakanin adireshinsu da na asalin kamfanin ba. Idan ka shiga gidan yanan sadarwan kuwa, wayyo, ba wani banbanci. Don haka, ka samu ingantaccen adireshi. Idan banki ne, ka tabbata cewa adireshin daga bankin ka samu, ko kuma a jarida ka gani wanda su suka buga. Idan jami’ah ce, ka tabbata adireshin da ke jikin fam din ka yi amfani dashi. Idan ba haka ba, sai a sha ka misilla. Mataki na biyu, da zaran ka samu kanka a cikin gidan yanan sadarwan, sai ka natsu, ka karanta bayanan da ke da munasaba da abinda kaje yi. Ka tuna cewa, da zaran ka aika fa shi kenan. Ka kuma tabbata cewa bayanin da ake so ka bayar. Wasu jami’o’in suna da gidajen yanan sadarwa iri biyu ne, misali Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, gidan yanan sadarwa biyu suke dashi. Akwai wanda suka tanada musamman don dalibai masu yin rajista, akwai kuma na hukumar makaranta. Idan ka shiga na hukumar makaranta, zai kai ka inda zaka yi rajista, amma sai ka lura da bayanan da ke ciki, idan ba haka ba, sai ka bace. Mataki na uku shine ka lura da sashin taimako, watau Help ko kuma FAQs (Frequently Asked Questions). Wannan shine inda zaka dosa da zaran ka samu matsala. Mataki na karshe shine tsare bayananka. Duk da yake wannan ba ya cikin huruminka, zaka iya tabbatar da cewa bayanan da ka aika (nambobin ajiyanka, namban katin biya, kalmomin izinin shiga dsr) a tsare suke ko ba a tsare ba. Idan kana son gane haka, duk lokacin da ka shigar da ire-iren wadannan kalmomi, ka matsa “enter” ko “go”, ka lura da adireshin da ke “address bar”, zaka ga harafin “s” a gaban “http” da ke bayyana a farkon dukkan adireshin gidan yanan sadarwan. Maimakon ka ga http:// zaka ga https://. Idan ka ga haka, to bayananka sun shiga inda ake kira “secured location” kenan, ba matsala.

Wadannan, a takaice su ne matakan da ake bukata a dukkan bangarorin biyu. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, zamu ci gaba da kawo bayanai kan tsarin saye da sayarwa da kuma gabatar da harkokin rayuwa ta hanyar Intanet. Daga karshe, ina mika godiyata da dukkan wadanda suka rubuto ko bugo waya ko yi addu’a a boye ga mahaifiyata. Allah Ya saka muku da alheri, Ya kuma sa Aljannah ce makomar mu gaba daya, amin. Na gode, Allah bar zumunci.

Sanarwa:

Ina farin cikin sanar da masu karatu cewa na bude kundin sirri (Blog) ko mudawwana ta Intanet, inda nake zuba dukkan kasidun da aka buga a wannan shafi, da takaitattun labarai kan hanyoyin fasahar sadarwa. Kowa na iya ziyartan wannan kundin sirri nawa. Dalilin yin hakan shine don samun wurin ziyara. Ga adireshin nan kamar haka: http://fasahar-intanet.blogspot.com. Idan kana son yin sharhi kan bayanan da ke cikin kundin, sai ka matsa inda aka rubuta “comments” a kasan kowane kasida. Amma dole ya zama kana da Gmail. Har wa yau, akwai rariyar likau zuwa muhimman zaurorin hira da majalisun tattaunawa. Sai mun sadu a can!