Mabudin Kunnuwa:
Ga wadanda suka ziyarci wannan shafi a makon da ya gabata, sun karanta irin ci gaba da yaren Hausawa ya samu wajen shigar dashi cikin sabon babban manhajan kwamfuta da kamfanin Microsoft ke son fitarwa nan ba da dadewa ba, watau Microsoft Vista Office. Wannan ba karamin ci gaba bane da wannan harshe ya samu. Kuma wannan ke dada nuna ma mai karatau cewa nan ba da dadewa ba, Intanet zai fara shafan rayuwar Hausawa, tun da hakan na daya daga cikin muhimman dirkokin da ake bukata wajen hakan, kamar yadda bayanai suka gabata a kasidun baya. Ina taya mu murnan samuwan wannan al’amari. Wannan zai dada kara yawan kwamfuta a cikin al’umma, wanda zai sa mutane su kara sha’awan fasahar Intanet. Daga karshe, yanda muke ta jin labarin tsarin kasuwanci ta hanyar Intanet a wasu kasashen duniya, za mu wayi gari ana damawa damu ta wannan fanni. Kafin nan, zan so in sanar da mu cewa a halin yanzu akwai wasu hanyoyi da zamu iya aiwatar da harkokin rayuwa na abinda ya shafi shiga makarantu, hulda da bankuna, neman aiki, zuba jari, kafin mu kai matakin aiwatar da saye da sayarwa ta Intanet, a Nijeriya. Wannan shine tsarin da a turance ake kira e-commerce a dunkule. Wannan makon zamu yi tsokaci
Harkokin Rayuwa a Intanet:
Na tabbata mai karatu ya karanta cewa gidan yanan sadarwa (Websites) na daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen tallata hajoji da ra’ayoyi da sauransu. A yau kusan duk abinda kake tunanin ana sayar da shi, ko da hidima ne (service) wanda wani zai maka ka biya shi, zaka tarar ya gina gidan yanan sadarwa, don tallata wannan sana’a nashi. Wannan ruwan dare ne a kasashen turai. Amma a kasashe masu tasowa irin kasashen Afirka, Asiya da wani bangaren Latin Amurka, sai daidai zaka samu suna da iirn wannan tsari. Sai dai hakan na wucin gadi ne, wannan tsari zai mamaye duniya gaba dayanta, ko ana so ko ba a so. Wannan tasa dole dan Adam ya zama yana tafiya da zamani, ta fannin abinda ya shafi ci gabansa da al’umman da yake rayuwa cikinta. Duk da yake a yanzu muna aiwatar da harkoki ne a fili, ga-ka-ga-abokin hulda, nan gaba matakin rayuwa zai zama galibin harkoki basu yiwuwa ta dadi sai an kai ga Intanet. Shiga makaranta sai da Intanet. Hulda da banki wajen ajiya ko canjin kudaden kasashen waje, sai da Intanet. Zuba jari sai da Intanet.
Matakai:
Aiwatar da harkokin rayuwa ta Intanet, musamman abinda ya shafi saye da sayarwa, na bukatar abubuwa da dama. Duk kamfani ko hukumar da ke son aiwatar da hakan, dole ne ta bi su. Abu na farko, wanda yafi komai muhimmanci shine samar da kankararren gidan yanan sadarwa mai dauke da hanyoyin mu’amala da abokin hulda mafi sauki. Galibin ire-iren wadannan gidajen yanan sadarwan zaka samu suna da manhajar wasikar hanyar sadarwa mai zaman kansa, wanda ke hade da rumbun
A bangaren mai saye ko kuma mu’amala, yana bukatar matakai hudu shi ma, don samun saukin mu’amala wajen gabatar da harkokinsa. Na farko, ya tabbata cewa adireshin gidan yanan sadarwan da ka samu ingantacce ne, ban a bogi ba. Domin akwai wadanda suka shahara wajen tsara gidajen yanan sadarwan kamfanoni, musamman wadanda suka shahara a duniya wajen kasuwanci da hulda da jama’a, don kautar da masu hulda da kuma sace masu bayanan katin adashin bankinsu. Idan ba tsananin lura kayi ba, ba za ka gane banbancin da ke tsakanin adireshinsu da na asalin kamfanin ba. Idan ka shiga gidan yanan sadarwan kuwa, wayyo, ba wani banbanci. Don haka, ka samu ingantaccen adireshi. Idan banki ne, ka tabbata cewa adireshin daga bankin ka samu, ko kuma a jarida ka gani wanda su suka buga. Idan jami’ah ce, ka tabbata adireshin da ke jikin fam din ka yi amfani dashi. Idan ba haka ba, sai a sha ka misilla. Mataki na biyu, da zaran ka samu kanka a cikin gidan yanan sadarwan, sai ka natsu, ka karanta bayanan da ke da munasaba da abinda kaje yi. Ka tuna cewa, da zaran ka aika fa shi kenan. Ka kuma tabbata cewa bayanin da ake so ka bayar. Wasu jami’o’in suna da gidajen yanan sadarwa iri biyu ne, misali Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, gidan yanan sadarwa biyu suke dashi. Akwai wanda suka tanada musamman don dalibai masu yin rajista, akwai kuma na hukumar makaranta. Idan ka shiga na hukumar makaranta, zai kai ka inda zaka yi rajista, amma sai ka lura da bayanan da ke ciki, idan ba haka ba, sai ka bace. Mataki na uku shine ka lura da sashin taimako, watau Help ko kuma FAQs (Frequently Asked Questions). Wannan shine inda zaka dosa da zaran ka samu matsala. Mataki na karshe shine tsare bayananka. Duk da yake wannan ba ya cikin huruminka, zaka iya tabbatar da cewa bayanan da ka aika (nambobin ajiyanka, namban katin biya, kalmomin izinin shiga dsr) a tsare suke ko ba a tsare ba. Idan kana son gane haka, duk lokacin da ka shigar da ire-iren wadannan kalmomi, ka matsa “enter” ko “go”, ka lura da adireshin da ke “address bar”, zaka ga harafin “s” a gaban “http” da ke bayyana a farkon dukkan adireshin gidan yanan sadarwan. Maimakon ka ga http:// zaka ga https://. Idan ka ga haka, to bayananka sun shiga inda ake kira “secured location” kenan, ba matsala.
Wadannan, a takaice su ne matakan da ake bukata a dukkan bangarorin biyu. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, zamu ci gaba da kawo bayanai
Sanarwa:
Ina farin cikin sanar da masu karatu cewa na bude kundin sirri (Blog) ko mudawwana ta Intanet, inda nake zuba dukkan kasidun da aka buga a wannan shafi, da takaitattun labarai
No comments:
Post a Comment