Intanet da Rayuwar Hausawa:
Alal hakika samuwan daidaikun gidajen yanan sadarwa na harshen Hausa da kuma yawan mashakata tsallake-tsallake a biranen kasar Hausa ba shine ke nuna cewa fasahar Intanet ta shafi rayuwarsu ba, ko kadan. Duk da yake fasahar sadarwa ta Intanet na iya shafar rayuwar al’umman Hausawa ta bangarori da dama, amma samun hakan a halin yanzu na da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. A wannan kasida zamu dubi dalilan da suka sa hakan ba zai yiwu ba a yanzu, da kuma abinda ya kamata a yi don samuwar hakan Sai dai kafin nan, ga wata ‘yar gajeriyar shimfida don munasaba.
A kasida ta biyu cikin jerin kasidun da muka gabatar a wannan shafi, mun nuna amfanin Intanet ga kowace al’umma, musamman ga al’ummomin kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzik’in kasa, wadanda kuma ta nan ne Intanet ya samo asali da bunkasar da yake
Wadannan hanyoyi guda uku kuwa sune: samuwar haruffan wadannan harsuna (fonts) cikin masarrafan kwamfuta, da yawaitan gidajen yanan gizo na harkokin rayuwa – hajoji da sauransu – na wadannan harsuna cikin Intanet da kuma uwa uba samuwar babban manhajar kwamfuta cikin wadannan harsuna, wanda hakan ta sa suka zama kamar sune yaren Intanet (Web Browser) yayin da Intanet din ya habbaka. Yadda zaka shigar da kalmomin turanci cikin Intanet ka nemo bayanai masu dimbin yawa, haka zaka sanya haruffan Hindu don nemo bayanai. Har wa yau, a kasar Sin (China) bayanan baya bayan nan sun nuna cewa Sinawa (Chinese) sun fi amfani da haruffansu da kuma gidajen yanan neman bayanai na harshen Mandarin don neman bayanai da kuma saye da sayarwa da sauran huldodin rayuwa fiye da yadda suke amfani da kalmomi ko haruffan turanci don gabatar da irin wadannan huldodi ta hanyar gidajen yanan turanci irinsu Yahoo! da Google da Hotbot da sauransu. A sharhinta na ranar Asabar, 14 ga watan Janairun shekara ta 2005, tashar talabijin CCTV9 na kasar Sin, ta nuna cewa kashi arba’in da biyar cikin dari (45%) cikin Sinawa na amfani ne da gidajen yanan neman bayanai da saye da sayarwa na harshen Mandarin, yayin da gidajen yanan turanci irinsu Yahoo! da Google dsr suka kwashi sauran kason. Wannan, har wa yau, tasa gidajen yanan sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine) da saye da sayarwa irinsu Yahoo! da Google suka shahara, saboda suna da sashen harsuna da dama irinsu Mandarin da Hindu da Jamusanci dsr. A takaice dai, ba komai ya sa harkokin hada-hada suka yawaita cikin wadannan harsuna ba sai don samuwan wadannan abubuwa uku cikin masarrafan kwamfuta wanda ko dai sun samu ne ta hanyar kamfanin Microsoft (a matsayin babban manhajar kwamfuta - Operating System cikin wannan harshe) ko kuma ta gidajen yanan sadarwa na Yahoo! da Google na shafukan da suka kirkira cikin wadannan harsuna a Intanet.
Dangane da bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa yaduwan harshen Hausa a Intanet, bai da wani tasirin da za a iya gwama shi da sauran harsunan da muka kawo misalansu a sama. Wannan ya faru ne saboda harshen Hausa bai samu irin gatan da wadannan harsuna suka samu ta hanyoyin nan guda uku ba. Duk da yake akwai bayanai da shafukan yana na harshen Hausa cikin Intanet. To amma ba wasu shafuka bane da suka kai suka kawo. Tunda ba zaka iya saye da sayarwa ba cikin harshen Hausa a Intanet. Ba zaka iya samo bayanan Hausa ba zunzurutu ta amfani da haruffan Hausa cikin Intanet, kamar yadda zaka iya in da haruffan turanci kayi amfani. Duk wadannan na bukatan wanzuwar bakaken Hausa cikin masarrafan kwamfuta a karo na farko. Sai samuwar babban manhajar kwamfuta cikin harshen Hausa (operating system). A karo na uku kuma yawaitan gidajen yana ya Allah na saye da sayarwa ne ko na huldodin rayuwa kowace iri, cikin harshen Hausa. Wannan zai ba duk mai mu’amala da wannan harshe daman yin duk wata hulda na rayuwa cikin harshen Hausa a Intanet. Zaka nemi duk irin bayanan da kake so ta amfani da haruffan Hausa ka samu.
A kasidarsa mai take: Hausa and Information and Communication Technologies, wacce ya gabatar a taron kara ma juna sani kan adabi da al’adun Hausa, wacce Sashen Nazarin Harsunan Najeriya dake Jami’ar Bayero ta shirya daga 13 – 16 na watan Disamba, 2004, Farfesa Abdallah Uba Adamu yayi doguwar bita kan irin kokarin da suka yi ta yi wajen ganin harshen Hausa ya samu hawa wadannan martabobi guda uku, don samun yaduwa da bin sahun sauran harsunan duniya a duniyar Intanet. Duk da yake an samu ci gaba ta wasu bangarori, har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ma na abinda ya shafi yaduwar gidajen yanan gizo na hada-hadan kasuwanci da neman bayanai cikin harshen Hausa. Gidajen yanan da muke dasu cikin harshen Hausa a yanzu duk da karancinsu, na al’adu ne da adabi da kuma addini. Wasunsu ma masu su ba a nan Najeriya suke ba. Wasu kuma ma, kare da karau, masu su Turawa ne masu sha’awan harshen Hausa; malamai a Jami’o’in Turai da Amurka. A bangaren Majalisun Tattaunawa kuwa, cikin Majalisu sama da dubu daya da ake dasu a Yahoo!, wadanda al’umman Hausawa suka bude suke tattaunawa cikinsu duk basu wuce hamsin ba. Duk da haka ma, cikin kasa da hamsin din nan, wasu daga cikinsu da Turanci ake tattaunawa dasu ba da Hausa ba – duk da yake masu tattaunawan Hausawa ne galibinsu.
A bangaren dora harshen Hausa cikin babban manhajar kwamfuta (Operating System) kuwa, shima ba a kai ko ina ba. Duk da yake kamar yadda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya nuna ne cikin kasidarsa, cewa babbar matsalar da wannan aiki ke fuskanta shine na rashin tallafin kudi da kuma cikakkiyar mayar da hankali musamman a bangaren wadanda suke da halin yin hakan; ko dai saboda rashin kasancewarsu a nan gida Najeriya ko wasu dalilai na daban. Cikin shekaran 2004, wani bawan Allah mai suna Muhammad Alimu ya farkar da wani kokari da aka assasa tun shekarn 1994, na samar da allon rubutun kwamfuta cikin harshen Hausa wanda ya sanya ma suna HausaWord 1.6, wanda yayi amfani da iliminsa na manhajar kwamfuta, watau Computer Programming, wajen samar dashi. Kamar yadda shima Farfesan yayi nashi kokari wajen karasa ko dora haruffan Hausa (irinsu K’, B’, TS, D’ dsr) cikin tsarin masarrafan kwamfuta. A halin yanzu ya samar da wannan tsari wanda ya sanya ma suna Abdallah TTF (watau True Type Font). Ina daya daga cikin wadanda suke amfani da wannan tsari a halin yanzu. Har wa yau, kamfanin Microsoft ta fara aiki
Bayan samuwan wadannan kuma har wa yau akwai wani abu guda da ya kamata harshen Hausa ya samu, watau daidaito. Da akwai bukatan daidaita Hausa cikin Intanet kamar yadda aka yi a rubuce, don dukkan mai neman bayanai ya samesu a fuskar da suka kamata. Don haka ya zama dole a samu kungiyoyi da masana da kuma gwamnatocin Arewa su hada kansu wajen ganin cewa Hausa ya samu hayewa matakan da suka kamata don tabbata a duniyar Intanet. Don dukkan kokarin da na zayyana mana a baya, ko dai mutum daya ne ya zauna yayi ko kuma k’ungiya ce ta masana, kamar yadda su Farfesa Abdallah suka yi, wajen shigar da haruffan Hausa cikin masarrafan kwamfuta. Babu inda zamu je in har abin ya ci gaba da zama a haka. Dole sai an samu masu daukan nauyi da kudi da kuma wadanda zasu zage dantsensu wajen yi ma Hausa gata a wannan zamani da kowace al’umma ke kokarin ganin an santa ta kowace fuska. Duk da kokarin da kamfanoni irinsu Google da Microsoft da Wickipedia, duk da haka ina ganin bai kamata mu shantake ba da wannan. Don na farko, su wadannan kamfanoni suna kokarin yin hakan ne don habbaka kasuwancin hajojinsu, kuma ba lalai bane Hausa ya samu dukkan gatan da yake bukata, misali, na abinda ya shafi daidata lahaja, dole sai mun shigo ciki da dai sauran abubuwa da suka kamata mu yi ma kanmu. Babban misali ma shine
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Anguwar Hausawa,
P. O.
Garki 900001
080 34592444
It's a very interesting concept where you have to balance objects perfectly on the field which are provided to you. Obviously, there may be some changes in the images produced by the pre and production run 5DIIIs. The EOS 5D Mark II naturally characteristics a total-frame sensor, but the resolution enjoys a considerable increase through the 12.
ReplyDeletemy web site :: 5d mark iii
The question is - which platform provides the best viewing experience.
ReplyDeleteBlip - TV: Distributes 48,000 independently-produced Web shows.
Apple TV and Roku are two devices you can use to stream High Definition
(HD) Video, movies, TV Shows, photos, and more to your HD TV wirelessly and connect to your wireless environment and connect to the internet.
Feel free to surf to my website ... roku 2 xs
This will help you to alter the quantity of blur easily and allow
ReplyDeletecamera make other critical decisions when you are shooting.
A tripod or sturdy table is a must when holding any superzoom
camera steady. The D7000 just may be the best performing APS-C format
camera in the market today.
my site - d7100
The 8GB version is only being sold through Google's own store, rather than physical retailers - but online buyers appear to have shunned it, surprising Google, which had thought that the cheaper version, despite having only half as much storage, would sell better than it has. RM416-419,Sufa305 Building Huafabei Road, Futian District, Shenzhen, China. Moving on, this handset ships with Android Gingerbread for its OS but soon enough the famous Ice Cream Sandwich update will land on this phone.
ReplyDeletemy web site: google nexus 7
Its appearance is note-bookish and minimalistic having no front button.
ReplyDeleteIf you little bit understand technologies, you can easily root your Black - Berry.
These efforts are incredibly obvious when it comes to the Playbook's strengths as a traveling device.
my blog post ... blackberry playbook review
ina bada shawara https://www.penpaland.com harshen musayar tushen website
ReplyDeleteAndroid:http://app.appsgeyser.com/Penpaland