Wednesday, January 10, 2007

AMFANIN INTANET

Amfanin Intanet

A kasidar da ta gabata, nayi alkawari cewa zan turo bayanai kan yadda ake Gina Gidan Yanan Sadarwa (Web Designing) da kuma amfanin da ke tattare da Intanet. Amma hakan bazai yiwu ba a lokaci daya, saboda tsoron tsawaita kasidar. Don haka a wannan sati zamu ji bayani ne kan amfanin Intanet, in yaso a sati mai zuwa sai mu kawo bayanai kan yadda ake gina gidan yanan sadarwa, in Allah Ya yarda. Don haka a gafarceni!


Fasahar Intanet wata duniya ce mai zaman kanta. Babban hadafin kirkiro wannan fasaha a farkon al’amari shine don sadarwa tsakanin jama’a ko ma’aikatu, kamar yadda bayanai suka gabata a kasidar farko. Amma saboda tasirin wani yanayi da turawa ke kira Killer Application, Fasahar Intanet a yau ta zama gagarau. Domin bayan hanyoyin sadarwa, a Intanet idan bayanai kake so tsagwaronsu, zaka samu ta hanyoyi da dama; ko dai ta hanyar Matambayi Baya Bata, watau Search Engines – Yahoo!, Google, AltaVista, Lycos dsr – ko kuma ta Tsararrun Hanyoyin Neman Bayanai, watau Directories. Har wa yau akwai wasu nau’uka na bayanai wadanda suka shafi sauti, irin na wake ko muhadara ko kuma hotuna, duk zaka iya samunsu ta hanyar Intanet.

Idan haduwa da mutane kake son yi, duk abu ne mai sauki. Daga wadanda ka sani zuwa wadanda baka sansu ba, duk akwai hanyoyin da zaka iya haduwa dasu. Idan ma hira kake son yi da mutum, har kaji ga-ka-gashi, shima wannan ba matsala bane. Shiga Yahoo Messenger, ko MSN Messenger ko kuma ICQ Chat Messenger, muddin wanda kake son hira dashi yana da irin wadannan hanyoyi kuma ya bude su, yanzu zaku yi rubutacciyar hira. Kai in ma muryarsa kake son ji, akwai yanda zaka ji har ma ka ga hotonshi ya ga naka. Idan kuma mutane da dama kake son hira dasu a lokaci daya, duk zaka iya.

Dangane da ilimi kuwa, a Intanet samun digiri (Degree) har da digirgir (Masters) da dingirewa (Phd), ba wani matsala bane. Zaka iya shiga makaranta ka dauki darasi, ka nemi bayanai wurin malaminka, kayi jarabawa har ka samu sakamako. Babban jami’ar da ke cin karenta ba babbaka a duniyar Intanet, ita ce Jami’ar Phoenix, watau Phoenix University. A kalla ta yaye dalibai sama da dubu arba’in da biyar. Intanet har wa yau wata duniya ce ta ma’adana bayanai, watau Laburare. Mutum ya zauna da jahilcin wani abu, bayan ya iya rubutu da karatu - alhali ga Intanet - shi ya so. Duk bayanin da kake bukata a kan menene, zaka sameshi (muddin wani yayi rubutu a kansa). Idan takamarka karatun jarida ne, an gama! Dukkan wata jarida da ka san ta shahara a duniya – New York Times, Washington Post (Amurka), Financial Times, The Guardian (Ingila), China Daily (Sin), Frankfurt Zeitung (Jamus), Al-Watan, Ukaaz (Saudiyya), Ath Thaurah, Tishreen, Al Ba’th (Syria) – duk zaka samesu a Intanet. Idan ma jaridun Nijeriya kake son karantawa, shi yafi komai sauki; daga Weekly da Daily Trust, zuwa Guardian, This Day, Punch, Vanguard, Gaskiya Tafi Kwabo, duk akwai su. Sai ka karanta su ma kafin a fara sayar da su a biranen da ake bugawa ko yada su. Idan kana son karanta irin binciken da wasu masana suka yi kan wasu al’amura, duk samammu ne a Intanet. Dukkan wata kasa da ka sani zaka iya samun bayaninta a Intanet, ka karanta ko ka ma yi dukkan abinda ka ga daman yi dashi, ya rage naka.


In kuma abokiyar rayuwa kake so na aure, an gama. Ba mata kadai ba, har da maza suna nan; daga kowace kasa a duniyan nan, mai kowane irin matsayi – na addini, ilimi ko dukkan wani rabo na rayuwa – ga hotunansu nan birjik. In ma marasa hotuna kake bukuta duk suna nan.


Samun zaurukan hira da “Majalisun” Tattaunawa (Mailing Lists) kuma wannan wani abu ne da sai ka samu kanka a wurin. Zauruka na nan iri iri; akwai wadanda zaka shiga ko da baka da rajista dasu, ka karanta abinda kake so a zaurensu, watau Bulletin Board. Kashi na biyu shine wanda sai kana da rajista zaka iya shiga ka ga irin wainar da ake toyawa. A zauruka ko”Majalisu” irin wadannan, akwai kananan zauruka daban daban inda ake tattauna harkoki daban daban na rayuwa. Zaka ilmantu har sai ka ture karatu. Samun abokai maza da mata a irin wadannan zauruka ba bakon abu bane. Don a ciki zaka samu dan kasar Sin, da dan kasar Amurka, da wadanda suke dangi ne daga nan Afirka da sauran jihohin duniya baki daya. Har wa yau, zaka ci karo da dan Nijeriya, dan Arewa ko ma wanda garinku daya ne dashi.


A Intanet harkokin kasuwanci su suka fi yawa da bunkasa. Wannan a bayyane yake. Saye zaka yi ko sayarwa, duk kana da filin tallata hajarka. Zaka saya kuma ka sayar. Duk wani abinda ka san dan Adam na rayuwa dashi zaka sameshi ka saya a kasuwannin da ke duniyar Intanet. Duk da yake wannan ya fi shahara ne a kasashen Turai da sauran kasashen da suka ci gaba, a nan Najeriya ma an samu wani Gidan Yanan Sadarwa dake da shaguna da kantuna a Legas da sauran biranen Najeriya, inda zaka iya sayen kayayyaki, ka kuma biya da Naira, ba da Katin Adashin Banki ba, watau Credit Card. Zaka samu wannan Gidan Yanan Sadarwa a: www.shopforless.com. Daga kayayyakin masarufi, kayan ofis, kwamfuta, duk zaka iya zaba, ka aika da odarka, adireshin gida ko ofishinka, da kuma Lamban Adashin Bankinka, wayau Account Number da sunan bankin da kake ajiya. Kafin kace me? An aiko maka dasu duk inda kake a Nijeriya.


A bangaren addini ma ba a bar Intanet a baya ba. Wane mutum! Daga masallatai zuwa majami’ai (Churches), duk ba matsala bane saduwa da su. A kasashen da suka ci gaba, zaka samu kusan dukkan masallatai na da adireshin Wasikar Hanyar Sadarwa, watau E-mail. Zaka karanta Al-Kur’ani mai girma yadda kake so. In ma karatun ya ishe ka, zaka iya jona sifikan kwamfutarka don sauraro, kyauta! In kuma so kake ka rubuta kasida ko makala wanda a ciki akwai ayoyin Kur’ani, akwai Gidajen Yanan Sadarwa wadanda aikinsu shine kawai su taimaka maka neman kowace aya kake so, a kuma kowace Sura ta Kur’ani ayar take, tsaf! In lokutan Sallah kake bukata na kowane birni a duniyan nan, akwai. Kai! Ba ma lokutan Sallah kadai ba, in kana son jin kiran Sallah a bayyane, zaka iya diro (Downloading) dashi zuwa kwamfutarka, ka jona sifika don sauraro. Idan ma so kake ka karanta Baibul (Bible), duk akwai shi; daga na harshen Turanci, Hausa, Jamusanci, Faransanci, duk sai ka ture.


A fannin lafiya ma fa ba a bar duniyar Intanet a baya ba. Komai da ruwanka kenan! Zaka iya hira da likita, ka gaya masa matsalarka, ya kuma baka shawara. Abinda sai ka biya kudi in asibitin kaje. Zaka samu bayanai akan kowane irin magani kake sha na wani cuta da tasirinsa; idan ma akwai wani nau’in maganin da ya bayyana a lokacin da kake wannan bincike, duk zaka gani a rubuce.


Idan kafar yada furofaganda kake nema, to ka samu, da zaran ka shigo Giza-gizan sadarwa ta Intanet. Domin babu hanyar sadarwar da tafi Fasahar Intanet tasiri wajen yada manufa da furofaganda. Duk wasu kungiyoyin duniya da ka sani, suna da Gidajen Yanan Sadarwa wanda suka tanada don yada manufarsu. Daga kan kungiyar Hizbollah da ke kasar Lubnan, Eta dake kasar Andalus (Spain), Hamas da ke Palasdinu, IRA da ke kasar Ailand (Ireland), Tamil Tigers da ke kasar Philiphines, da sauran kungiyoyin duniya, duk suna yada manufofinsu ta hanyar Intanet. Kai a kasashen Turai da Amurka, galibin harkokin siyasa duk ta Intanet ake gabatar dasu. Zaka samu kowane dan takara ya tanadi Gidan Yanan Sadarwa don yin kamfen. Hatta jam’iyyun siyasa duk ba a barsu a baya ba. Wannan na faruwa ne saboda a duniyar Intanet kowa na da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa. Idan hakan yai maka zafi, sai ka zuba naka ra’ayin. Abu mai sauki!

Wani Hanzari. . .


Sai dai fa, idan ka hangi fari-fari daga nesa, inji Hausawa, da zaran ka matso kusa zaka ga baki-baki. A duniyar Intanet ma haka al’amarin yake. A hanyarka ta neman bayanai in baka yi hankali ba sai ka fada hannun miyagu! Barayi kuwa yadda ka san a kasuwan kauye kake. Gidajen Yanan Sadarwa na batsa da wasan kwamfuta (Computer Game) da Caca kuwa, ruwan dare ne. In har ka sake ka samu kanka a farfadan daya daga cikinsu, kafin ka fita sai kai da gaske. Wannan ya faru ne saboda miyagun na amfani ne da wata Masarrafa (Software) dake makure Dan Manunin Kwamfuta (Computer Mouse), watau Mouse- Trapping Software. Shafukan batanci ma na nan, birjik. Wasu shafukan don bata kadarin wani addini aka tsara su, wasu kuma don bata kadarin wata al’umma da dai sauransu. Hanyoyin koyar da hakikanin ta’addanci kuwa mai sauki ne a Intanet. Daga yanda ake koyar da yin bam da gurneti da sauran kayayyakin shedana, sai yanda ake shirya sharrurruka. Wasu Masana Manhajar Kwamfuta (Computer Programmers) kuma basu da wata manufa illa na bata ma al’umma kwamfutocinsu ta hanyar aiko da wasu Rikitattun Bayanai (Virus) masu haukatar dasu. Hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli shine ka san inda zaka tafi, kawai. Muddin ka san inda ka dosa, baka da matsala. Amma idan ka tsaya walagigi da gutsiri-tsoma, kai ka jiyo!

Siffofin Intanet


Duk wannan habbaka da Fasahar Intanet ta samu na da nasaba ne da wasu siffofi guda uku da suka banbanta ta da sauran hanyoyin sadarwa. Da farko dai zuwan Intanet ya haddasa kirkire kirkire da dama, na abinda ya shafi dukkan harkokin rayuwa. Na biyu, Intanet wata fasaha ce da ta game dukkan duniya baki daya, wata kasa ba zata iya kebance ma kanta ba. Na uku kuma yayin da ta bunkasa, duk sai ta lakume sauran fasahan sadarwa da ake dasu irin su wayan tarho, radiyo, jaridu da talabijin. Dukkan wadannan in kana son yin mu’amala dasu da zaran ka jona Intanet zaka same su ta hanya mafi sauki. A takaice dai ya saukaka ma al’umma hanyoyin mu’amala gaba daya.


A halin yanzu tunda mun ji bayanai kan ma’ana da yadda Intanet ke samuwa, da takaitaccen tarihin kirkirarsa, da kuma amfanin da ke tattare da wannan fasaha, a mako na gaba cikin yardan Allah, zan gabatar da bayanai kan yadda ake Gina Gidan Yanan Sadarwa (Web Desiging). Domin gidajen yanan sadarwan ne ake mu’amala dasu a duniyar Intanet. Duk mu’amalar da mai ziyara zai yi, dasu ko a cikinsu zai kare yawace-yawacensa.


A dakace ni!

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Securities and Exchange Commission (SEC),

Tower 421, Constitution Avenue,

Central Area, Garki – Abuja.

080 23788040

absad143@yahoo.com, salihuabdu@yahoo.com

4 comments:

  1. Only that he's doing the opposite of getting people fit. Not only are they located in Las Vegas the entertainment capital of the world. Kanye West – “Heartless” Mixed With Lady Gaga – “Lovegame”.

    My web blog ... daft punk random access memories flac free download

    ReplyDelete
  2. The momentum for Macklemore & Ryan Lewis' 'Thrift Shop' continues to rise, as the band sits atop the Ultimate Song Chart for a third straight week. 5, the Windows Marketplace is preloaded onto the phone allowing the ability to download apps from the phone itself without having to log onto a computer to download them. You should narrow down your potential list of schools based on your criteria, but you should still plan on visiting more than one to give you a sense of comparison.

    Here is my website; Weekly Top 20 Music

    ReplyDelete
  3. In addition, The Muscle Maximizer comes with a complete 9 week workout program for you to
    follow so you now have everything you need to get started right
    away and achieve the level of fitness you''.
    To find out if it is actually true and to understand better if Kyle
    Leon's system is generally for you or not, let's look into a few
    of the benefits and drawbacks of the product. Who is this Somanabolic Muscle Maximizer Training Software Designed For.


    My site: Muscle Maximizer Review

    ReplyDelete
  4. Somanabolic Muscle Maximizer program is optimized for the U.
    Check out this article instantly to determine for yourself.
    Whenever upgrades became ready you'll fully grasp this totally free no matter what quantity of money cost to establish them.

    my webpage - muscle maximizer Results

    ReplyDelete