Thursday, January 11, 2007

WAIWAYE ADON TAFIYA!

Waiwaye Adon Tafiya

Sakonnin Masu Karatu:

Masu karatu ku gafarce ni wannan mako. Ba mancewa nayi kan alkawarin da nayi ba, cewa zan kawo bayanai kan ”Yadda Ake Neman Bayanai a Yanar Gizo.” Ina sane. Babban abinda yasa na taka mana burki shine don muyi waiwaye, abinda Malam Bahaushe ya kira “adon tafiya.” Kada gabanku ya fadi, ku dauka ko karshen wannan shafi kenan. A a, zamu ci gaba da kwararo bayanai insha’Allah, sai inda karfi ko iliminmu ya kare.

Da farko dai ina so in mika godiyata ga masu rubuto sakonni ko bugo waya, ko aiko da gajeren sako ta wayar salula, watau text message. Hakika na kan ji dadi kuma kamar yadda a kullum nake cewa shine; babu wadanda suka cancanci wannan yabo irin Hukumar Media Trust, masu buga wannan jarida mai alabarka ta AMINIYA, musamman ma Edita, Hajiya Aishah, da kuma Malam Abubakar AbdurRahmaan, wanda aikinsa ne karbowa da kuma shirya wannan shafi da nake gabatarwa a duk mako. Hakika ta wadannan sakonni na fahimci abubuwa da dama. Wannan yasa na yanke shawaran kawo wadannan gajerun shawarwari, wadanda na tabbata zasu taimaka ma mai karatu a hanyarsa ta mu’amala da wannan bakuwar hanyar sadarwa. Da haka nima na fara, kuma duk da yake ba wani cikakkiyar kwarewa nake da ita ba kan wannan fasaha, a kalla zan iya bayar da shawarwari iya gwargwadon fahimta da sani na.

Kasidun da Suka Gabata:

Idan mai karatu bai mance ba, wanann shine mako na bakwai da muka fara aiko da wadannan makaloli. A kasidar farko mun yi gabatarwa kan ma’ana da tarihin Intanet, da nau’ukan Intanet. A makon da ke biye da shi kuma muka kwararo bayanai kan amfanin Intanet, da kebantattun siffofin wannan fasaha mai ban al’ajabi. A mako na uku mai karatu ya karanta bayanai kan yadda ake gina gidan yanan sadarwa, watau Web Designing. Daga nan muka turo bayani kan yadda ake lilo da tsallake-tsallake a wadannan shafuka ko gidajen yanan sadarwa. A mako na baiyar mai karatu ya karanta yadda ake budewa da kuma mu’amala da akwatin wasikar hanyar sadarwa, watau Imel. A mako na shida kuma sai kasidar Hira da Tattaunawa ta biyo baya. Ina da yakinin cewa masu karatu sun karu da wani abu, duk kankantansa. Domin a tabbace yake cewa mafi yawancin wadanda suka yi ta aiko da sakonni basu jima da fara amfani da wannan fasaha ba; wasu kuma ma sai ta wadannan kasidu suka san yadda ake mu’amala da ita. Tabbas akwai da dama da suka jima suna ta’ammali da fasahar Intanet, amma duk da haka, samun bayanai cikin harshen Hausa kan yadda ake sarrafa wannan fasaha shi kanshi wani ci gaba ne, ko da mutum ya jima yana lilo a giza-gizan sadarwa. A gaba zamu ci gaba da aiko kasidu, kuma zan yi iya kokari na wajen ganin na dada sassauka bayani cikin kasidun, don mai karatu ya samu fa’ida mai yawa, insha’Allah. Kafin nan, zan so mai karatu ya lura da wasu abubuwa masu mihimmanci dangane da mu’amala da Kwamfuta da kuma Fasahar Intanet, kamar haka:

Sha’awa:

Wannan shine babban garkuwa da mai karatu yake bukata. Sha’awar da nake nufi a nan ita ce abinda ake kira “Interest”, a turance. Ya zama kana son yin abin, kuma kana kulawa da irin ci gaban da kake samu lokaci lokaci. Domin idan baka da sha’awa, to babu yadda za a yi ka rinka kulawa da shiga Yanar Gizon, balle har ka samu fa’idojin da ke tattare da wannan fasaha. Kada ka damu cewa “ai ban taba mu’amala da kwamfuta ba”, duk wannan ba hujja bane. Idan kana da cikakkiyar sha’awa, nan da nan zaka koya. Shekaru shida da suka gabata, ko kusa da kwamfuta bana yi, saboda tsaban tsoro. Domin a kullum gani nake kamar idan na taba jikin kwamfutar, lalatata zan yi. Amma na fara gina sha’awa na ne lokacin da nake ta mu’amala da gidajen rediyon BBC da Deuschewelle dake Jamus, da irin su Voice of America. Nakan ji suna ambaton adireshin Imel dinsu, ni kuma ba a abinda na fi bukata a rayuwa illa in aika da sako, ya isa cikin gaggawa. Don haka wata rana sai na rubuta sako zuwa ga BBC Sashen Turanci (The Learning Zone), na samu wata baiwar Allah da ke sashin kwamfuta a ofishinmu ta aika musu. Sai ta dinga min yanga. Har sai da na harzuka. Daga lokacin na yanke shawaran koyan kwamfuta da shiga Intanet. Ba a dauki lokaci mai tsawo ba Allah Yai mani muwafaka. A yanzu bana iya kwana ba tare da nayi shaukin taba kwamfuta ko shiga Intanet ba. Ya zama kamar jinin jiki na. duk wannan ba komai ya kawo haka ba, sai tsaban sha’awa da nake dashi kan hakan. Ban taba zuwa makaranta don koyon ilimi da aiki da kwamfuta ba, balle yadda ake mu’amala da Intanet. Don haka, idan mai karatu ya gina sha’awarsa kan wannan fasaha, ina tabbatar masa cewa nan ba da jimawa ba zai samu bakin zaren.

Karatu da Aiki Da Shi:

Abinda ilimin kwamfuta da Fasahar Intanet ke bukata bayan sha’awa, shi ne aiki da abinda ka karanta. Domin idan baka aikata abubuwan da kake karantawa, to zai yi wahala ka iya komai a harkan. Domin shi wani fanni ne wanda karantunsa ke rataye da aiki. A wasu lokuta ma zaka samu aikin ya fi karatun yawa. Duk lokacin da ka karanta yadda ake mu’amala da gidan yanan sadarwa, dole ne ka samu Intanet, ka aikata wannan ilimi a aikace. Babu abinda zaka koya a harkan Kwamfuta da Intanet ba tare da kayi karatu ba; kuma baka iya komai, idan baka kwatanta abinda ka karanta ba. Don dole ne mai karatu ya rinka kwatanta ilmummukan da yake dauka cikin kasidun da muke aikawa mako-mako. Wannan ne zai bashi daman auna ilminsa kan abinda yake karantawa. Duk inda ya cije, sai yayi tambaya. Wannan tasa nake zaburar damu kan abinda ya shafi neman bayani cikin dukkan abinda mai karatu ya karanta amma bai fahimta ba. Ko ya koya, amma da yaje aikawa sai ya gab a haka abin yake ba. Yin tambaya ne kadai zai wayar maka da kai cikin abinda kake nema. Galibin abubuwan da na tara na ilimi da aiki kan wannan fasaha, ya ta’allaka da tambayoyin da nake kusan a kullum. Idan abubuwa suka cakude mani, na kan rubuta ma Farfesa Abdallah Uba Adamu dake Jami’ar Bayero sakon Imel, don neman Karin bayani. Wasu lokuta kuma sai in nemi bayani (Search) ta hanyar matambayi baya bata, watau Search Engine, wanda zamu kawo bayaninsa mako mai zuwa, in Allah Ya yarda. Don haka, mai karatu ya sa a cikin zuciyarsa cewa dole ne ya aikata abinda ya koya, kuma duk inda ya samu matsala, to yayi tambaya. Domin matambayi, inji Hausawa, baya bata – sai dai in bai yi tambayar daidai ba, ko kuma yadda ta dace.

Manufa:

Wannan ya kawo mu kan mataki na gaba, watau manufa. Kafin nan, yana da kyau mai karatu ya san cewa “kamar yadda ya san cewa zuwansa duniya na da manufa mai karfi,” to dole ne ya san cewa a duniyar gizo ma sai ya riki manufa kwakkwara, idan kuwa ba haka ba, sai ya bace. Wannan ya faru ne saboda duniyar Intanet wata irin duniya ce mara badala; babu kyaure, muddin a ciki kake. Kuma yadda kasashen duniya suka kasu kashi-kashi, to haka manufofi da ra’ayoyin mutane suke birjik. A duniya irin wannan, idan baka da manufa, sai ka narke cikin rubibi. Samun manufa ya kasu kashi-kashi; manufa wajen lilo da tsallake-tsallake. Wani irin gidan yanan sadarwa zaka ziyarta? Me kake bukata a ciki? Dole ne ka samu manufa a nan, idan ba haka ba, sai ka ci karo da miyagu. Manufa wajen hira da tattaunawa; su waye abokan huldanka a Intanet? Wani irin mu’amala kake dasu? Duk sai ka tantance. Har way au, yana da kyau ka san irin majalisar da zaka rinka shiga. Wannan na rataye ne da irin manufarka da kuma abokan da ka shaku dasu. Domin a duniyar Intanet, akwai wuraren da zaka iya ziyarta gaba gadi. Akwai wadanda zaka iya shiga da kyar. Akwai kuma wadanda duk tsiyarka baza ka iya shiga ba said a izni. Ya dai danganta da irin abinda ya kaika wajen. Kafin in karkare wannan bangare, yana da kyau mai karatu ya san cewa yadda dabi’un mutane suka karkasu a rayuwar yau da kullum, to haka ire-iren wadannan dabi’u suke a duniyar Intanet. Idan addini kake so akwai. Idan holewa kake so, akwai mazauninta. Idan neman kudi kake son yi, ta hanyar da ta dace da wacce bata dace ba, duk akwai su. Duk irin abinda kake bukata na dabi’u, baza ka rasa mazauni ba. Don haka nake karfafa Magana kan manufa. Me kaje yi?

Hakuri da Juriya:

Komai dan hakuri ne, musamman idan aka ce ya shafi neman ilmi da aiki da shi. Mu kwatanta rayuwarmu na addini mu gani mana; sau nawa muka ji wa’azi kan hani daga aikata zunubi, kuma sai nawa muka yi amfani da wannan hani? To balle Intanet, wacce a ciki babu wanda zai kwabe ka kan irin Gidan Yanan da zaka shiga, sai tsaban tarbiyyan da kake da ita. Hakuri ya kasu kashi biyu a Intnet; juriya wajen kamewa daga aikata alfasha. Da kuma juriya wajen dagewa da ganin ka koyi abinda zai amfaneka. Ba za ka san dimbin ilimin da ke makare a giza-gizan sadarwa ta Intanet ba sai ka fara mu’amala da ita. Kowane irin ilimi kake son koyo, zaka iya samunsa in Allah Ya yarda. Abinda kake bukata kawai shine sanin abinda kake nema, da kuma inda zaka je ka sameshi. Hakurin da ya fi kowanne shine wanda zaka yi wajen koyon ilimi; ilimin kwamfuta da Fasahar Intanet nake nufi. Domin wani fanni ne dake tsarinsa ke sauyawa kusan a dukkan dakika ko bugun agogo. Yana bukatar a kullum ka rinka mu’amala da shi don sanin irin sauye-sauyen da ke samuwa a kullu. Idan ba haka ba sai ka zama bakauye cikin kankanin lokaci. Domin ana kirkiro sabbin hanyoyin mu’amala da Intanet kusan a kullum. Wannan tasa dole mai karatu ya zama mai juriya da hakuri wajen lazimta da mu’amala da kowane irin bangare ne na wannan fasaha. Idan hakan ya zama maka jiki, ba zai rinka damunka ba, in Allah Ya yarda.

Kammalawa:

Dangane da bayanan da suka gabata, na tabbata mai karatu ya dauki mataki kan tsarin da zai bi wajen mu’amala da wannan fasaha. Kuma kamar yadda masu karatu suke yawaita bayar da shawara cewa mai zai hana in mayar da wadannan kasidu zuwa littafi mai zaman kansa. To ina son sanar dasu cewa a halin yanzu akwai wanann littafi a rubuce, amma saboda ayyuka da suka addabe ni a ofis, ban riga na dabba’a shi ko ba. Amma nan da wasu watanni masu zuwa insha’Allah zan sanar da ku halin da ake cika. Akwai gyare-gyare da kuma kare-kare da zan yi saboda tsawon lokacin da na dauka ban buga ba. Domin kusan dukkan kasidun da nake aikowa, da ka nake hararo su, ba da littafin nake amfani ba gaba daya yanzu. Daga karshe, ina kara sanar da masu karatu cewa samun lokaci, hajuri da juriya, manufa da kuma amfani da ilimi, sune manyan dirkokin da ake bukata wajen ci gaba da hulda da wannan fasaha. Duk abinda mai karatu bai gane ba, sai ya rubuto. Insha’Allah zan yi iya kokari na wajen ganin na taimaka.

Sai mun sadu mako mai zuwa!


Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Securities and Exhange Commission (SEC)
Tower 421, Constitution Avenue
Central Area, Garki – Abuja.
080 23788040
absad143@yahoo.com, salihuabdu@yahoo.com

No comments:

Post a Comment