Wednesday, January 10, 2007

Fasahar Intanet a Jiya, Yau da kuma Gobe!

As salaamu Alaikum!

Barka da isowa wannan dandali mai albarka. Sanin kowa ne cewa duniya na sauyawa dangane da tsarin sadarwa da harkokin rayuwa, a kusan kowane dakika guda a yau. Wannan tasa kowace al'umma ke kokarin ganin cewa ta zama gaba wajen samun shiga a wannan zamani. Wannan hali da duniya ta samu kanta a ciki a yau, na da nasaba da bunkasar sabbin fasahan hanyar sadarwa suka cika duniya. Shekaru saba'in da suka gabata, abu ne mai wahala a ce mutum ya samu labarin abinda ke faruwa a wasu kasashe cikin sauri da sauki. Mutane kan yi doguwar tafiya wajen neman ilimi, koyon sana'a, sadar da zumunci da kuma yawon bude ido. Amma a yanzu, cikin 'yan dakiku sai ka san me ke faruwa a kowace kasa ne, muddin ka san abinda kake nema.

Duk wannan ya samu ne sanadiyyar yaduwa ilimi kan bunkasar fasahar sadarwa, ciki har da fasahar Intanet, wacce a yau ta zama gama-gari, musamman a kasashen turai da Amurka. Wannan tasa na ga dacewar shigar da al'umman Hausawa wannan jirgi na zamani, don sanin abinda ke faruwa. A wannan dadali, mai karatu zai ci karo ne da kasidun da nake rubutawa cikin Jaridar Aminiya da ke fitowa mako-mako a Nijeriya.

A sha karat lafiya.

Baban Sadiq

No comments:

Post a Comment