Matashiya:
A cikin kasidar “Amfanin Intanet” da na “Waiwaye Adon Tafiya (1)”, mun gabatar da hanyoyin da mai karatu zai iya taimaka ma kan sa wajen mu’amala da na’urar kwamfuta wacce ke hade da Intanet, don samun saukin lilo da tsallake-tsallake da kuma saukin rayuwa, musamman wajen mu’amala da abokan da yake hulda da su. Sai dai wani abin da ba mu tabo ba tun fara kwararo wadannan kasidu a wannan shafi, shine tasiri ko dangantakar da ke tsakanin Fasahar Intanet da kuma kwakwalwar dan Adam. Shin wace irin dangantaka ke tsakanin fasahar Intanet da kwakwalwan dan Adam? Me irin wannan danganta ke haifarwa, kuma me da me ke haddasa hakan? Ta yaya za a yi kuma a shawo kan hakan, idan da akwai matsala tattare da ita? Wannan zai taimaka ma dukkan mai mu’amala da fasahar Intanet samun saukin rayuwa.
Tsani
Hakika a tabbace yake cewa tasirin akwatin talabijin (TV) ya zarce wanda akwatin rediyo ke da shi, wajen tsumar da mai mu’amala da su a lokuta daban-daban. Domin a yayin da mai sauraron rediyo ke jin sakonnin da ke zuwa daga akwatin rediyon sa, mai kallon akwatin talabijin na sauraro ne tare da ganin hotuna masu motsi. Wannan, a cewar Malaman dabi’a (Psychologists), shi ya fi hanyar farko tasiri wajen da mai mu’amala da shi. Idan mu ka dauki wannan a matsayin mizani, sai mu ga cewa tasirin fasahar Intanet ga kwakwalwan mai mu’amala da ita, ya zarce na rediyo da talabijin. Don me? Saboda tasirin ji, da gani, da kuma mu’amala, duk a lokaci daya. Wannan ta sa duk wani mai mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar kwamfuta, na shagala ne saboda wata dangantaka da ke tsakanin kwakwalwansa, da zuciya, masu sarrafa gabobin jikinsa (hannu, idanu da kunnuwa) don kulla alaka tsakaninsa da akwatin talabijin kwamfutar, wacce ke aikawa da sakonninsa zuwa wata tabbatacciyar duniya ta gaibu, mai kama da kawalwalniya. Dankari!
Watakil mai karatu yai tunanin mai ya kawo kalmar “kawalwalniya” cikin zancen, tun da an ce “tabbatacciyar duniya” ce? Domin kowa dai ya san cewa kawalwalniya wani irin yanayi ne a saman titin kwalta ko falallen dutse, wanda idan rana ta yi zafi ka na nesa, za ka rinka ganin alamar ruwa na walwala da malala a saman dutsen ko kwaltan. Idan ba zuwa in da abin yake ka yi ba, kai kace wata korama ce ko rafi na ruwa a saman kwaltan. Sai dai kuma da zaran ka nufi in da abin yake, sai ka iske sunan wani mawaki wai shi Wayam! Bahaushe kan yi amfani da wannan kalma wajen nuna rashin tabbacin abu, ko kuma wata siffa da abin ke da shi irin na rudi; babu tabbas! To mene ne alakar da ke tsakanin tabbaci da rashin tabbaci, a duniyar Intanet? Akwai alaka ko dangantaka. Idan kana mu’amala da fasahar Intanet da dukkan abinda ya shafe ta, kana sawwara wata irin duniya ce a kwakwalwarka, tsakaninka da abokin alakar ka ko manhajar da kake mu’amala da ita. Kuma karshen ta da za ka je in da yake, sai ka ga abin da ba shi bane kake sawwarawa. A wasu lokuta kuma, ga alakar kana yi, da abinda kake da tabbacin shi ne abin da kake alaka da shi, amma kuma idan aka nuna maka hakikaninsa, sai ka ga baya nan, kwata-kwata ma. To me yasa, bayan ga tabbaci ka samu da farko? Oho! Jama’a, ba almara muka zo yi ba wannan mako, ku fahimce ni sosai.
Musabbabai
Domin fahimtar wannan murdadden jawabi mai cike da rikitarwa, yana da kyau mu dubi musabbabai ko in ce ababen da ke haddasa samuwar irin wannan duniyar ko tabbaci mai kama da kawalwalniya, da kuma abin da hakan ke haifarwa ta fannin tunani sanadiyyar dadewar alaka da fasahar Intanet. Akwai dalilai da dama; za mu kawo shahararru ne kawai daga cikinsu, don samun mahanga kan wannan al’amari. Hanya ta farko ita ce ta hanyar Manhajar Hira ko Zauren Hira, wanda a turance muke kira Chatting ko kuma Chat Rooms. Ga mafi yawancin masu shiga Intanet don yin hira da abokanai ko kawayensu ko kuma wasu mutanen da a can za su hadu da su, Zauren Hira wani wuri ne mai wajen kebewa da mu’amala a wani siga da ya sha banban da duniyar zahiri da su ke ciki. Sanadiyyar haka sai ya zama sun samu wani wuri mai kima a zuciya da kwakwalwansu. Manhajojin da aka fi amfani da su wajen aiwatar da wannan hira su ne: Yahoo Messenger! (http://messenger.yahoo.com), ICQ Chat Messenger (http://www.icq.com), Windows Live Messenger (http://www.hotmail.com), da kuma American Online Chat Messenger (http://www.aol.com). Wannan hanya na da tasirin da haduwa fuska-da-fuska ba ta dashi ga masu saduwa. Misali, idan ka na hira da mutum ta hanyar Zauren Hira, akwai wasu maganganu da za ka iya gaya masa, wanda idan tare kuke a fili ba za ka iya ba. Har wa yau, dukkan manhajojin na da wasu alamu da za ka iya aika ma abokin hiranka, don sanar da shi halin da kake ciki na farin ciki (murmushi, dariya da kyacewa da bakin ciki) a lokacin da kuke tattaunawa. Wannan tasa zaurori irin wadannan suka zama wata matattara ta jama’a, wanda alakar da ke tsakaninsu a wannan wuri kan sha banban idan su ka hadu. Hanya ta biyu ita ce ta hanyar dandanli ko majalisun tattaunawa, watau Mailing Lists ko Bulletin Board; hanyoyin tattaunawa kan al’amuran rayuwa ta hanyar wasikar Imel, ko kuma ta hanyar gidan yanar sadarwa masu makalallun zaurorin hiran zo-ka-karanta-ka-tafi, watau Bulletin Board kenan. Yadda mutane ke taruwa su na hira da juna a zauren hira, haka suke tattaunawa a majalisun tattaunawa. Banbancin kawai hanyar farko ta fi tasiri wajen tabbatarwa da kuma dawwamar da alaka tsakanin masu mu’amala. Amma fa hanya ta biyun ita ma ba baya take ba wajen hada alaka mai karfi. Domin har aure a kan yi tsakanin masu mu’amala a majalisun tattaunawa. Kar ka kai abin da nisa; a nan Majalisar Tattaunawa ta Finafinan_Hausa (http://groups.yahoo.com/group/finafinan_hausa) ma an samu wadanda su ka kulla alakar aure a tsakaninsu sanadiyyar wannan hanya. Hakan ke nuna irin tasirin da wannan hanya ke da shi wajen shiryar da kwakwalwarsu da kautar da ita daga kebantuwa da duniyar zahiri kadai, wacce su ke cikinta a “jikince” (da gangar-jikinsu). Sai hanya ta gaba, wacce ke samuwa ta gidajen yanar sadarwa na wasannin kwamfuta, watau Computer Games ko Cartoon. A wadannan gidajen yanar sadarwa, in da mutum zai je ne ya kama mu’amala da wasu halittu ginannu a duniyar jiki ba rai ba, tasirin alaka dawwamammiya na dauke ma masu mu’amala hankali daga duniyar yau da gobe, zuwa wata duniya da mai hankalin ke surantawa a kwakwalwansa. A wadannan hanyoyin wasanni, za ka yi mu’amala ne da mahajojin wasannin kwamfuta (na lissafin wasa kwakwalwa, yake-yake, saye da sayarwa ta mutum-mutumi, dsr). Idan ka saba wasanni ta ire-iren wadannan manhajoji, tasirin hakan na iya sarrafa maka tunaninka zuwa wata duniya mai zaman kanta. Akwai kuma masu zuwa shiga Intanet don gudanar da binciken ilimi kan harkokin rayuwa daban-daban. Da dama cikinsu sun saba aiwatar da hakan, har suka wayi gari galibin bayanin da za su nema don gudanar da bincikensu dole ne ya zo daga Fasahar Intanet, idan ba haka ba, gani su ke bai cika ba wajen inganci. Ina da wani aboki yanzu haka, ko ma’anar kalma ce ta bace masa daga tunani, dole sai a Intanet zai nemo ta. Duk da cewa ga Kamus na turanci a aljihun teburinsa. Amma saboda fitinuwa da zazzabin alakar Intanet, ba ya iya hakurin dubawa. Sai kuma masu shiga Intanet don yin karatu; ya Allah makaranta suka shiga a ciki ko kuwa karanta labaru kawai su ke. Akwai jami’o’i da dama cikin Intanet; masu gudanar da karatu don samun shaidan ilimi kan fannoni daban-daban. Sau tari ko da dalibai ne, za ka samu tasirantuwansu da fasahar Intanet ya janye alakar da ke tsakaninsu da sauran dalibai a makaranta. Duk wani karatu da za su yi, idan ba ta wannan hanya bane, sai yai musu wani iri. Sai wadanda suka mayar da Intanet wata matattara ta karatun jaridu a kullum. Ba za ka ga sun taba sayan ko da shafi daya bane na jarida, amma duk labarin da za ka karanta a kowace jarida ce, za ka iske suna da bayani a kan shi. Masu wannan dabi’a basu sanin lokacin da hakan ke auran kwakwalwansu, har a wayi gari sun zama ‘yan makarantar Intanet. Na kusa da na karshe kuma su ne masu gudanar da saye da sayarwa ta hanyar Intanet, musamman a kasashen Turai da Amurka. Galibin su sai su yi kusan shekara (idan ba wata haja bace wacce ba a samunta a Intanet) ba ka gan su a kasuwa ba, sam sam! Hakan na da nashi tasiri wajen shirya musu wata tafkekiyar kasuwa a duniyar kwakwalwansu, wacce zai yi wahala su same ta a wani bigire na duniya, a zahirance. Sai hanya ta karshe, wacce ke rarake ma mai mu’amala sashen tunaninsa tabbatacce ya bar masa wata duniya kwakwalwantacciya a duniyar Intanet, shi ne ta hanyar abin da na kira Lilon Shirme! Lilon Shirme shi ne duk wani yawo da mutum zai yi a duniyar Intanet mara tabbatacciyar ma’ana da amfani da kuma manufa mai kyau a hankalce, ba ga al’umma kadai ba, a a, hatta ga mai yin ta. Wannan ya hada da yin lilo a gidajen yanar sadarwa na caca, da tambola da kuma shiga gidajen yanar sadarwan batsa da ashararanci. Sabawa da wannan irin lilo mara manufa da ma’ana na da nasa tasiri mai cike da munanan akidar barna da ke darsuwa a kwakwalwar mai yi. Dukkan wadannan hanyoyi na da tasiri daya ko biyu ko ma sama da haka, wajen samar da wata duniya tabbatacciya mai kama da kawalwalniya, a kwakwalwan mai yin lilo da tsallake-tsallake a duniyar Intanet. To a ina alakar ta ke, tsakanin tabbaci da rashinsa? Kuma me ye hakan ke haifarwa wajen sauya dabi’ar mai yi, bayan tsawon lokaci?
Alakar Tabbaci da Rashin sa
Kafin mu ci gaba, ina son mai karatu ya fahimci cewa, kasancewar dukkan hanyoyin da aka zayyana a sama na haddasa samuwar wata irin alaka mai wannan siffa, wacce ke darsuwa a kwakwalwan sa, ba shi ne abin zargi ba, dari bisa dari. A a, ishara ne kawai zuwa ga wani abin da zai iya kawo cutarwa ko jirkita dabi’a, ko kuma akasin sa, iya gwargwadon yadda mai yin hakan ya samu kansa a ciki. Dangane da abin da ya shafi alaka tsakanin tabbaci da rashin tabbaci kan abinda kwakwalwan mai mu’amala ke sawwarawa kuwa, abu ne mai saukin fahimta.
Ga wanda ya saba shiga zauren hira yana zance da budurwansa ko abokanansa (ya taba ganinsu ko bai taba ganinsu ba), dole ya rinka ganinsu, a cikin zuciyarsa ba ta gululun idonsa ba, a a, a kwakwalwance. Wannan kan sa ya rinka shaukinsu a ko da yaushe. Iya gwargwadon shakuwansa da su ko ita budurwan tasa ne zai iya nuna kadarin shagaltuwar tunaninsa da su ko ita. Kun ga a nan, yana sawwara abokansa ne a cikin zuciyarsa, tare da cikakken kalansu da nau’insu, kuma su na nan a tabbace. To amma abin ya zama kawalwalniya ne saboda a hakikanin asalinsu ba yadda su ke kwakwalwansa ke suranta masa su ba. Musamman ma idan bai taba ganinsu ba. Haka wanda ya saba shiga don wasan kwamfuta da Cartoons. A ko da yaushe hankalinsa na kan abinda ya saba wasa dasu ne, iya gwargwadon shakuwarsa da su, shi ma. Kuma ko da misali yake son bayarwa a wajen hira, zai samu kansa yana mai misali da su. Tabbas akwai manhajar da yake wasa da su a gidan yanar sadarwan. Wannan tabbaci kenan. Amma a hakikanin rayuwa ba su nan, ko kadan. Kuma ba zai gane hakan ba, sai lokacin da ya fita daga Intanet. Sai dai ya yi ta shaukin su, amma ba zai same su ba a zahirance. Haka wanda ya mayar da Intanet a matsayin makaranta, a kowane lokaci. Abinda zuciyar sa za ta rinka sawwara masa kenan: maranta cikakkiya. Kuma yana da tabbacin ta, a duk lokacin da ya shiga Intanet. Wannan tabbaci kenan. Amma da zaran ya fito hakikanin rayuwa fa? Sai dai shauki. Idan muka zo kan mai saye da sayarwa ma haka abin yake. Ya ki zuwa kasuwa ne watakil saboda ganin cewa abinda zai saya na samuwa ta hanyar Intanet. Da zaran ya saba da haka, sai ya ga ashe yana da kasuwa kebantacciya a kwakwalwansa, ba sai ya fita zuwa shagon da ke kofar gidansa ma ba, balle wata unguwa. A kullum ya tuna kasuwa, kwakwalwansa ba ta tuno masa da kasuwar unguwarsu, tabbacciya, a a, sai dai kasuwar Intanet, wacce zuciya ke sawwara masa ita. Tabbas akwai ta, tun da har gashi yana biya, ana kawo masa kayayyakin har gida. To amma a hakika ina kasuwar take? Ba ta, sam. Da zaran ya kashe kwamfutar ko ya rufe rariyar lilo da tsallake-tsallakensa shi kenan. Ko da kuwa gidan yanar sadarwan na da shago tabbatacce a zahira, idan ya je ba zai iya gudanar da komai ba, don ba don hakan aka yi shagon ba. An ajiye shagon ne don ajiyan hajojin. Idan ka saya ta hanyar Intanet, a dauka a kai maka gida ko ofis. Wannan shi ne hujjar alaka tsakanin tabbaci da rashin sa.
Kammalawa
Daga karshe, wadannan su ne hanyoyi da kuma tsarin alakar da ke tsakanin tunani ko kwakwalwan dan Adam mai sarrafa kwamfuta da Intanet, da kuma tabbacin abinda yake sawwara ma kansa ko rashinsa. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, za mu ji ko akwai wata illa da ke samuwa sanadiyyar hakan. Idan akwai, ina magani? Na san har zuwa yanzu mai karatu bai san in da wannan kasida ta sa gaba ba, saboda irin sarkakiyan da ke ciki. Kada ka damu, mako mai zuwa na ka ne. A biyo mu!
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Unguwar Hausawa,
Garki II, Abuja. 080 34592444
Fasaha2007@yahoo.com
http://babansadiq.blogspot.com, http://fasahar-intanet.blogspot.com
No comments:
Post a Comment