Sunday, July 29, 2007

Tasirin Fasahar Intanet ga Kwakwalwan Dan Adam (2)

Makon Jiya

A makon da ya gabata ne idan masu karatu ba su mance ba, mu ka fara jero bayanai kan irin tasirin da Fasahar Intanet ke yi ga kwakwalwan dan Adam, saboda irin mu’amalar da ya ke yi da wannan fasaha. Mun yi bayanin irin dalilan da ke haddasa tasirin, da kuma cewa lallai akwai alaka tabbatacciya mai kama da kawalwalniya, wacce ke samuwa tsakanin kwakwalwan dan Adam da kuma asalin duniyar da yake ciki. Mun nuna cewa wannan alaka na samuwa ne sanadiyyar tasirin wannan fasaha da kwakwalwan mai mu’amala. Daga karshe mu ka yi alkawarin kawo abin da hakan ke haifarwa, da yadda za a iya magance wata matsala idan akwai. Saboda yanayin tsarin da bayanan su ka zo, mun ce mai karatu ba zai fahimci in da aka dosa gaba daya ba, sai a wannan mako. Mu na kuma fatan hakan. Don haka yanzu za mu ci gaba.

Sakamakon Alaka

A hankalce duk abinda aka ce yana da wata tasiri kebantacciya sanadiyyar alakantuwansa da wani abu, to dole ne a samu sakamakon da ke haifuwa sanadiyyar alakar, bayan an ji dalilan da ke haddasa hakan kenan. In kuwa haka ne, to mene ne sakamakon tsananin shakuwa da fasahar intanet, mai tabbatar da wata duniya kwakwalwantacciya a cikin tunanin mai yin alakar? A takaice, mutumin da ya mayar da duniyar Intanet a matsayin wata makaranta wacce yake ji da ganin ta a cikin kogon zuciyarsa, kuma ta ke sake a bishiyar kwakwalwansa; da wanda budurwarsa ko abokiyar hirarsa ko abokanansa na samuwa ne kawai ta wannan fasaha; da wanda Intanet ce kasuwarsa, ba kuma ya tuna wata kasuwa ko da kuwa a kofar gidan sa take; da wanda a duk lokacin da yake jin nishadi, bai da wata matattara sai gidan yanar sadarwan wasannin kwamfuta ko Catoons; da mai Lilon Shirme, wajen lasa ma zuciyarsa irin zuman da take bukata duk da dacin da wannan zuma ke tattare da shi a hankali da tunani lafiyayye (ina nufin masu shiga caca da tambola da gidajen yanar sadarwan zinace-zinace da ashararanci), duk wadannan, me ye sakamakon yin hakan ga kwakwalwa da lafiyarsu? Mai karatu kana ina? In kana kusa, to mu dukufa!

Gaggawar Zuci: Tabbas, duk wanda ya saba mu’amala da fasahar Intanet, musamman ma wajen amfani da Imel da kuma Zauren Hira da Tattaunawa, lokacin da zai dabi’antu da Gaggawar Zuci, ba zai sani ba. Za ka wayi gari, duk wani sakon da za ka aika ko karba, idan ba ta wannan hanya bane, sai ka ga nawarsa. Wannan ya faru ne saboda a tunaninka (sabon tunanin Intanet), bai kamata a ce duk wani sako, ta kowace hanya za ka aika ko karba, ya gaza irin gaugawan karba da aikawa irin ta Intanet ba. Duk wani abin da zai sanar da kai cewa “ai komai da muhallinsa; wannan Intanet ne, kuma haka aka tsara shi. Wannan hanyar gidan waya ce, kuma haka aka tsara ta”, zai bace bat daga kwakwalwanka. Don haka komai aka ce za a aiko maka, sai kace sai ta Imel. Duk wata tattaunawa da aka ce za a yi da kai, kace sai ta Chat Room. Haka dai, ka zama wani Walkiya Sarkin gaggawa. Kwanakin baya wata ‘yar uwa ke tamabaya na “Baban Sadiq, wai me yasa aka kasa yin hanyar aikowa da abinci ne ta Intanet?” Sai na bushe dariya. Kin kamu! Watakil wasu lokaci ta kan so ta rinka aika ma aboki ko abokiyar hirarta ne dukkan abinda ta mallaka. Me ya jawo haka? Gaggawar Zuci. Shin wannan abin zargi ne? Za mu ji bayani nan gaba.

Tabbatacciyar Kadaici: Sosai kuwa! Duk wanda ya zama likau ga fasahar Intanet, sai ya lazimci Tabbatacciyar Kadaici. Shi ba hulwa ya shiga ba balle ya yi tsammanin kashfi ko samun lada! Masu karatu su lura da kalmomin: ba kadaici kadai na ce ba, a a, tabbatacciyar kadaici. Wannan ya fi kama masu yin awanni su na gabatar da wani aiki ko hira a kan Kwamfuta, musamman masu gina gidajen yanar sadarwa da kuma masana manhajojin kwamfuta, Computer Programmers. Wani kan yi awanni sama da goma yana kwankwashe-kwankwashe a kan kwamfuta. Ba ya son jin wata sauti, ko da kuwa ta faduwar allura ce. Me yasa? Saboda a cewarsa wannan na iya kawar masa da hankalinsa daga abin da ya ke yi. Bai san cewa wata kyakkyawar budurwa ce mai suna Kadaici ta aure shi ba. Galibin wanda ya saba mu’amala da kayayyakin wasannin kwamfuta ko Cartoons, da masu zuwa musamman don yi hira ko zance da ‘yan mata ko abokanansu, suna kamuwa da wannan cuta ta Tabbatacciyar Kadaici. Sai dai galibi ba su sani. Allah Sarki! Idan a cikin mutane milayan su ke zaune ana gudanar da wani abu, muddin ba su bane ke gudanarwa kai tsaye, yan saurare ne su, to gani suke kamar bata lokacin su kawai su ke. Za su kosa da barin wurin, don ji suke kamar a cikin kwalba su ke. Me yasa? Don duniyar da ke surance a kwakwalwansu kadai su ke kallo. Kuma idan ba a Intanet ba, ba ka da inda zaka samo musu gamsuwa ta hakika. Amma idan su kadai ne da kwamfuta a daki ko mashakatar tsallake-tsallake, wayyo, sai ka shigo har ka gama abinda ya kawo ka (muddin ka iya taku), ba su ma san wani ya shigo ba. Domin a nan kadai su ke samun natsuwa da debe kewa. Ba komai ya kama su ba illa zazzabin kadaici, wanda sauron da ke fitowa daga giza-gizan sadarwa ta Intanet ya cije su, ya kuma zuba musu guban sa cikin kogin jininsu. Ko shi ma wannan abin zargi ne? Za mu ji bayani nan gaba.

Shauki: Shauki fa! Ko ka ce tsananin bege. Ban san wace kalma ce ta fi dacewa ba. Jama’a ku agaza mini; ni Bahaushen (ko Gwarin) Abuja ne. Mene ne banbancin shauki da bege? Ni duk daya na dauke su, illa in ce ya danganta da abinda mutun ke yin abin don shi. Idan mutum ne, nake ganin zai fi dacewa mu ce “bege” - “Ai yana matukar begenta.” Misali. Amma shauki na iya shiga kowane irin abu. Kenan shauki shi ya fi fadi bisa kalmar bege. To shauki din, mu dauke shi. Wannan shi ne mafi girma da hadari daga cikin lalurorin da ke haifuwa sanadiyyar tsananin shakuwa ko sabo da Fasahar Intanet. Larabawa kan kira shi “Al-ishqu”. Amma a turancin Intanet, mu kan kira shi Internet Addiction. Watau tsananin alakantuwa da sabo ko jarabtuwa da Fasahar Intanet. Tabbas, lalurori biyun da su ka gabata duk nau’i ne na wannan addiction din, amma shauki shi yafi dacewa da a kira shi da kalmar. Domin ya kunshi dukkan biyun da ke sama. Shauki ne zai sa mutum ya dabi’antu da gaggawar zuci, don gani ko jin muryan wanda ko abinda yake so. Haka kuma, shi zai sa mutum ya ji cewa idan ba kadaituwa ya yi da abinda yake shauki ba, to ba zai samu cikakkiyar natsuwa tsakaninsa da abin bege ko shaukinsa ba. Ina fatan mun fahimta yanzu. Shi shauki na samuwa ne sanadiyyar tabbatacciyar dadewa ana amfani ko mu’amala da Fasahar Intanet. Ba wai ta yawan shekaru ake nufi ba, a a, yawan kasancewa tare da fasahar sanadiyyar himma da kuma muhimmancin abin da ake gudanarwa a kansa ne ke haddasa wannan illa. Wanda ya kamu da wannan matsala na iya kamuwa da hakikanin zazzabi idan bai samu mu’amala da Intanet ba. Kai wasu ma har sumewa suna yi, saboda tsaban shakuwa. A halin yanzu akwai mutane da dama da su ka samu matsololi irin na tunani da shauki saboda tsananin alakantuwa da wannan fasaha ta Intanet. Wasu sun haukace, wasu sun susuce, wasu kuma ga su nan dai; ba yabo ba fallasa. Ba dukkan masu shauki ne ke kamuwa da wannan matsala a lokaci guda ba; daraja-daraja ne abin. Akwai sabon-shiga, wadanda saboda Allah-Allah da su ke yi a ce sun saba da wannan Fasaha, sai su kasa mallakar hankalinsu. Duk safiyar Allah, su na kan kwamfuta. Duk yinin Allah, su na kan kwamfuta. Duk yammacin Ubangiji, su na kan kwamfuta. A kullum jin su suke a zabure, sai kace dawakan yaki. Duk in da su ka ga wani adireshin Imel ko gidan yanar sadarwa, sai sun kwafa, sun kuma yi mu’amala da mai su. Idan su ka mallaki kansu daga baya, za su rage, musamman idan su ka fahimci abinda su ke son fahimta. Amma idan su ka kasa mallakan hankalinsu waje daya kuma fa? To za su zarce mataki na biyu, wanda ke kunshe da tabbatacciyar kadaici. Mun yi bayanin sa a sama. A wannan mataki, su na baina-baina ne, in ji Larabawa. Tsakanin Gizo da Koki! Idan har yanzu ba su mallaki tunaninsu ba su ka tsara abin da su ke son yi da wanda ba su bukata, to sai matakin karshe, watau tozon shauki kenan. A wannan mataki kam, ko da sun fahimci abinda su ke son fahimta, daga baya ne, wai sadaka da bazawara. Rabuwa da Intanet zai musu wahala. Lokacin da na fara mu’amala da wannan fasaha shekaru kusan bakwai da su ka gabata, na kai mataki na biyu, amma Allah yai min gyadan dogo; kasa ‘yaya sama ‘yaya. A mataki na uku ne mu’amala da fasahar Intanet ke zama ma mutum farilla irin ta dabi’a; idan bai yi ba, gani yake kamar Allah zai tambaye gobe kiyama. Wannan shi ne matakin tsananin shauki da bege, wanda babu mai iya goge tasirinsa a zuciyar wanda ya kamu, sai a hankali. Wannan, ba sai mun je kasa ba, abin zargi ne kai tsaye. Domin da farko dai ya shafi lafiyarka kai tsaye, tun da har an fara kawowa ga sumewa. Yana kuma iya hana ka gabatar da duk abinda zai amfane ka, a wajen Intanet; musulmi ne kai ko ba musulmi ba. Bayan duk mun ji wannan, to ina mafita?

Mafita

Kamar yadda kowa ya sani ne, ba a kaddara cuta ba, sai da aka halicci maganinta. Ma’ana duk lakacin da ka ji an ce ga wata cuta, to maganinta ya riga ta isowa. Illa kawai ya danganta da darajar ilimin masu wannan zamani; sun gano maganin ko ba su gano ta ko ba. To wannan matsala da ke samuwa sanadiyyar zazzabin ciwon sauron giza-gizan sadarwa ta Intanet, na da na ta maganin. Ga wasu hanyoyi nan shahararru:

Tsara Lokaci: A gaskiya duk wanda ka ga ya kai mataki na karshe, musamman a wannan bangaren da muke ciki na duniya, to ba karamin sakaci yayi ba musamman wajen amfani da damar da ya samu, ya kume cinye lokacinsa a haka. A turai samun wannan ba abin mamaki bane, domin su na da ababe da ka iya jawo musu sha’awarsa sosai. Don kusan komai a Intanet a ke gabatar da shi. Shi ya sa a can wajensu su ke da likitoci masu bayar da shawarwari kan wannan cuta na musamman, masu suna: Cyber Counselors. Idan mutum ya iya tsara lokacin da yake dashi, ko da yana da kwamfuta a gidan sa mai hade da fasahar Intanet, ba zai samu kan sa cikin wannan matsala ba. Amma idan bai da tsari, komai nisan da mashakatar tsallake-tsallake ke da shi da gidansa, sai ya tafi. Lokacin da na fara kamuwa, sai in yi tafiyar kusan kilomita goma don yin lilo. Idan kuwa na yi tafiya doguwa zuwa Legas ko Bauchi ko Kano da makamantansu, abin farko da nake fara yi da zaran na sauka masauki shi ne, neman in da mashakatar tsallake-tsallake ta ke. A tsara lokacin shiga Intanet, jama’a.

Kyautata Manufa: Kyautata manufa a nan ba yana nufin zuwa da manufa mai kayau bane kadai, a a, me kake yi wanda zai amfane ka? Wannan zai sa ka shirya su iya gwargwadon lokutan da za ka amfana da su, ba tare da matsala ba. Misali, idan darasi ka ke dauka, ka sanya ma kanka lokaci, idan ba da malami kake ba. Idan gina gidan yanar sadarwa kake, ka sanya ma kanka lokaci iya yadda ka tsara aikin. Idan hira zaka je yi, ka san in da ka dosa. Karatun jarida kake zuwa yi, nan ma ka san ina ne zaka iya samun labaran a tare wuri daya? Domin iya gwargwadon yawonka wajen neman labarai, iya gwargwadon yawaitan tunaninka kan abin da ka gani. Shi yasa kwanakin baya muka kawo bayanai kan wasu gidajen yanar sadarwa kan haka. Mu kyauta manufa tare da tsara abin yi cikin lokacin da muke da shi. Sai mu tsira.

Kankanta Kaskantacce: Wata babbar matsala da masu yin lilo da tsallake-tsallake ba su cika lura da ita ba, ita ce: suna samun kansu cikin kambama wata matsala ko al’amari, wacce a zahirin hankali ba ta cancanci hakan ba. Misali, bai sai wuri ba wajen masifar Intanet, ka ji ana kiran sallah, ko a ce ana kiranka a gida ko wani wuri, wanda zuwanka ke da amfani ga al’umma ko karan kanka, amma saboda kana da wasu ‘yan mintoci kamar talatin da suka rage maka, ko wani abokin hira ya rike ka, kace “a a, bari in gama.” Lokacin da ka zarce, kana iya haduwa da wani ko wata, ko kuma wani abu ya darsu a cikin zuciyarka, wanda bai ma kai mintunan da za ka rufe ba balle abin da ake kiran ka a kai, sai kawai kaji kana bukatar kara lokaci, ba tare da ka tuna da abin da ake kiran ka kan sa ba, da farko. Ka ga nan, ba ka kaskantar da abin da ya cancanci kaskanci ba. Akasin sa ka yi. Ko kuma sai kawai kaji kana sha’awar shiga wuraren tsiyataku da shirme, ga wasu wurare masu amfani ba ka damu da su ba. Karshen ta ka na zuwa can, sai kawai a aure ka ba tare da ka sani ba. Wannan zai sa kusan kullum ka shigo, sai ka dangana da wajen. Alhali wannan wuri bai cancanci wannan muhimmanci da ka bashi ba. Dukkan wannan na cikin ababen da ke haddasa kamuwa da zazzabin cizon sauron giza-gizan sadarwa ta Intanet. Don me ba ka kankanta kaskantacce ba?

Shawarwari: Daga karshe, idan ya zama ka kai matakin karshe na shauki (Addiction), to sai addu’a da neman shawarwari. A wannan bangare na duniya ba mu da kwararrun da su ka wuce Malaman Addini da Dibbu (Likitoci). Domin duk abin da ya shafi kwakwalwa, to zancen ya wuce na shan kwaya ko kuma tsara lokaci. A turai su na da masu bayar da shawara ta hanyar Intanet. To amma a nan idan mutum ya kai matakin sumewa da zazzabi don kawai bai shiga Intanet ba, al’amarin yayi nisa kenan. Don haka sai neman shawarwari daga kwararrun masa kan dabi’a da halittan dan Adam. Allah Ya sawwake, amin.

Kammalawa

A yanzu kam na tabbata mai karatu ya fahimci in da na dosa a makon jiya, matukar fahimta, in ma bai fara tuhumar kan sa ba dangane da irin dabi’ar sa ta mu’amala da fasahar Intanet. Kamar yadda na sanar a makon jiya har wa yau, ina da tabbacin mun fahimci cewa, ba shiga Intanet din ba ne matsala (da an samu tufka-da-warwara kenan), a a, irin tsari da dabi’ar mai shiga ko mu’amalan ne ke sa ya kai wannan mummunan mataki. Don haka Intanet wata ala ce mai matukar muhimmanci, amma a matsayinta na abin aiki, dole ne tana da ka’ido’jin mu’amala. Haka kawai ba ka zuwa ka hau jirgin sama, don kawai ka karanta littafin kera jirgin, sai ka koyi yadda ake komai, tare da tarbiyyar da ke kumshe cikin sana’ar. A nan za mu dakata, sai zuwa wani mako. Duk abinda ba a fahimta ba, to a rubuto. Ina kuma mika godiya ta ga dukkan masu bugo waya ko rubuto sakonnin gaisuwa. A nan zan mika gaisuwa ta musamman ga Malama Habeebah Haroon da ke Jami’ar Jas, mace ta farko da ta fara nuna farin ciki da gamsuwanta ga wannan shafi. Na gode, Allah bar zumunci!

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Unguwar Hausawa,
Garki II, Abuja. 080 34592444
Fasaha2007@yahoo.com
http://babansadiq.blogspot.com, http://fasahar-intanet.blogspot.com


No comments:

Post a Comment