Tuesday, August 28, 2007

Nau'ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (4)

Matashiya

A makon da ya gabata idan masu karatu basu mance ba, mun kawo bayanai kan tsarin da masu tashoshin talabijin suke bi ne wajen yada shirye-shiryensu, da kuma nau’ukan shirye-shiryen da suke da su a shafukan Intanet. Wannan mako, kamar yadda muka yi alkawari, zamu dubi hanyar sadarwa ta jarida ce da mujallu da suka mamaye giza-gizan sadarwa ta Intanet, kamar wutar daji. Har wa yau, za mu dubi irin tsarin da suke bi wajen yada labarai da kasidu da makaloli. Idan shafuka basu mana halinsu ba, zamu kawo wasu daga cikin jaridun da ke da shafukan yanar gizo a Intanet.

Tsarin Yada Labaru

Da farko dai, yana da kyau masu karatu su san cewa hanyar sadarwa ta Jaridu da Mujallu na daga cikin dadaddun nau’in hanyar sadarwa da suka fara saduwa da wannan sabuwa kuma gamammiyar hanyar sadarwa mai suna Intanet. Wannan ya faru ne saboda tsananin tasirinsu wajen isar da sako cikin sauki da kuma gamewa. A halin yanzu, kusan kamfanonin yada labaru daidai ne a duniya basu mallaki gidan yanar sadarwa ta Intanet ba a duniya. Hanyoyin da suke bi wajen yada labaru a Intanet sun sha banban da sauran nau’ukan fasahar sadarwa da muka kawo bayanansu a baya.

Da zaran ka shigo gidajen yanar sadarwarsu, ba abinda zaka fara gani sai labaru, yadda ka san dai ka dauko jarida ce tabbatacciya. Za ka samu kanun labarai daki-daki, a tsarin rariyar likau (links), da zaran ka matsa, za a kaika inda cikakken labarin yake. Har wa yau, zaka samu babban labari (editorial) da rahotanni da kuma makaloli da masu aiko musu da rahotanni suke aiko musu.

Bayan haka, suna da rumbun adana kasidun baya (archives) in da zaka samu rahotannin baya da kuma kasidu da makaloli. A wasu gidajen yanar sadarwa na jaridun Turai ko Amurka misali, samun kasidu ko makalolin baya abu ne mai wuya, sai kayi rajista dasu, ko kuma ka saya, kamar dai yadda mai karatu ya ji tsarin sayar da wasu shirye-shirye na talabijin ko rediyo a makonnin da suka gabata. Idan kaje gidan yanar sadarwa ta jaridar The Washington Post (Amurka), ko na The New York Times (Amurka) ko kuma na Guardian Unlimited (Ingila) misali, duk zaka samu basu bayar da makalolin da ke gidajen yanar yanar sadarwansu, kyauta, sai ka saya. Wannan na faruwa ne saboda su can kusan komai sai da kudi. Wannan na daga cikin tsarin jari-hujjan da suke kai, a fannin tattalin arzikin kasa. Bayan haka, akwai labaru da rahotanni cikin hotuna masu motsi (video) da ma marasa motsi (images). Haka gidajen yanar sadarwa na jaridun Nijeriya, su ma haka tsarinsu yake. Sai dai dan abin da ba a rasa ba. Misali, galibin su basu da manyan rumbuna na adana kasidun baya, balle a ce maka sai ka saya. Don haka idan ka samu wani kasida sabo, yana da kyau ka buga (print) ko adana shi a kwamfutar ka (save) in kuwa ba haka ba, idan ka dawo ba za ka same shi ba.

Kamfanonin jarida na Intanet na samun kudaden shiga sosai ta hanyar tallace-tallace (advertisements). Idan ka shiga gidajen yanar sadarwansu zaka ga haka sosai. Har wa yau, wani abinda galibin su suka shahara dashi shine, duk lokacin da ka shiga gidajen yanar sadarwansu, zaka samu labarun lokacin da ake ciki, na kusa-kusa (latest news and reports). Wannan yafi yawa ga jaridun kasashen Turai, in da suke lura da dukkan abinda ke faruwa, kuma suke aiko da rahotanni kan haka, nan take. A jaridun Nijeriya ma akwai masu wannan kokari. Daga karshe, ga dukkan wanda ya mallaki hanyar saduwa ta fasahar Intanet, zai ji dadin samun labarai a dunkule wuri daya, kuma cikin sauki ba tare da ka kashe ko kwabonka ba. Matsalar dai daya ce ; ba za ka iya buga (print) dukkan labaran da kake so bane cikin dadi. Idan kuma kana bukatar binciko kasidun baya ne, duk zaka samu manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine) da zai taimaka maka yin hakan cikin sauki.

Neman Shafukan Jaridu a Intanet

Wannan shine abu mafi sauki, sabanin nau’ukan sadarwan da suka gabata. A Intanet akwai inda zaka samu adireshin dukkan jaridun da ke Nijeriya ko arewacinta, idan kana so. Idan ba a manta ba, mun yi wannan bayani a makalar Ziyartan Gidajen Yanar Sadarwa, in da muka zo bayani kan gidan yanar sadarwa ta Gamji.com. Wannan gidan yanar sadarwa mahada ce babba, wacce ta kumshi dukkan hanyar da za ta sadar da kai da gidajen yanar sadarwan jaridun da ke Intanet a duniya ma, ba Nijeriya ko arewacinta kadai ba. Duk labarun ko kanun labarum da ke wannan gidan yanar sadawa, ta tsarin rariyar likau, za su isar da kai ne zuwa asalin shafin jaridar da ke dauke da cikakken labarin, cikin sauki. Har wa yau, idan ka samu kusan dukkan jaridun da ke Nijeriya zaka samu adireshin su da ke giza-gizan sadarwa ta Intanet., hada har da mujallun da ake dasu. Wasu daga cikin su su ne: The Sun (http://www.sunnewsonline.com), Daily Trust (http://www.dailytrust.com), New Nigerian (http://www.newnigeriannews.com), Gaskiya Ta fi Kwabo (http://www.newnigeriannews.com/gaskiya/index.htm), Mujallar Fim (http://www.mujallar-fim.com). Har wa yau, idan na kasashen waje ne, ga su Guardian Unlimited (http://www.guardian.co.uk) da ke Landan, Ingila. Sai mujallar The Economist (http://www.economist.com). Ga kuma su The Washington Post (http://www.thewashingtonpost.com) na kasar Amurka. Da jaridar New York Times (http://www.nytimes.com), ita da ma da ke kasar Amurka. Idan muka koma kasashen Larabawa da ke Gabas-ta-Tsakiya, za mu samu jaridar Okaz (http://www.okaz.com.sa) shahararriyar jaridar da ke fitowa daga kasar Saudiyyah a duk mako. Sai irin su Tishreen (http://www.tishereen.info), wacce ke fitowa ita ma duk mako daga kasar Syria. A takaice dai, kusan dukkan jaridun da ke yada labarai zaka samu suna da gidajen yanar sadarwa mai zaman kansa. Wannan ya faru ne saboda saukin mu’amalar da wannan fasaha ta Intanet ke dauke da ita. Idan kana neman adireshin wani shafin jarida da kake tunanin tana da shafi a Intanet kuma baka san adireshi ko cikakken adireshi shafin ba, ko dai kaje Gamji.com, ko kuma ka gudanar da tambaya a Google.com, cikin sauki.

Tsarin Gidan Yanar Sadarwa

A gidajen yanar sadarwan yada labaru ta jaridu, akwai masarrafa ko manhajoji da ake amfani dasu wajen taskance labaru da kasidun da ake zubawa don masu ziyara da karantawa. Kusan dukkan gidajen, zaka samu suna da sassaukan hanyar yawo a cikin dakunan gidan, watau Navigational Tools. Suna da rumbuna wajen taskance bayanai, watau Archives. Sannan idan kana son labarun da suka shafi hotuna masu motsi (na bidiyo), sai kana da manhajan da zai taimaka maka, kamar yadda bayanai suka gabata a makonnin da suka gabata. Ire-iren wadannan manhajoji kuwa sun hada da Real Player, Macromedia Flash Player, Quick Time Player, ko kuma Media Player, a wasu lokutan. Bayanai kan yadda ake sarrafa su kuwa sun gabata a makonnin baya.

Kammalawa

A karshe, a tabbatace yake cewa nau’ukan sadarwa da ke Intanet sun samu wata sabuwar kasuwa ce ta yada labaru da shirye-shiryen su, kuma a ga dukkan alamu wacce ta fi kowacce shahara da samun nasibi a cikinsu it ace hanyar yada labaru ta jarida da mujallu. A mako mai zuwa za mu jula akala zuwa wani bangaren kuma na fasahar Intanet. Don Allah idan an samu kura-kurai kan tsari ko kuma sahihancin bayan da muke jefowa, a rinka tayar da mu. Duk dan Adam ajizi ne. Muna kuma mika sakon gaisuwarmu ga dukkan masu aiko sakonnin gaisuwa da ban gajiya. Allah Ya saka da alheri, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)

Off Lagos Crescent, Unguwar Hausawa,

Garki II, Abuja.

080 34592444 fasaha2007@yahoo.com

http://fasahar-intanet.blogspot.com

Friday, August 17, 2007

Nau'ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (3)

Matashiya

A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai kan tsarin da ke tattare da yada labarai da wakoki a gidajen yanar sadarwa na tashoshin rediyo da ake dasu a giza-gizan sadarwa ta duniya. Mun kuma nuna irin hanyoyin da su ke bi wajen taskance labaran musamman ga tashoshin FM masu sayar da wakoki ko kuma yada taskantattun shirye-shiryen su. Har wa yau, ba mu karkare wancan mako ba sai da muka tabbatar da cewa mun kawo bayanai kan dukkan makale-makalen da suka dace mai son sauraron labarai da shirye-shiryen tashoshin rediyo ta Intanet ke bukata kafin yayi hakan. A yau kuma cikin yardan Ubangiji za mu kama hanya in da zamu ji irin tsarin da masu tashoshin Talabijin ke bi a nasu harkan.

Hanyar Sadarwa ta Talabijin (Rediyo Mai Hoto)

Kamar yadda aka samu gidajen yanar sadarwa na yada shiryen-shiryen tashoshin rediyo a Intanet, to haka ake da gidajen yana na musamman in da ake yada shirye-shirye na Talabijin, kamar yadda ka ke kallo a talibijin gidan ka; banbancin kawai shine na irin hanyar da kake kallon shirin amma ba na hakikanin shirin ba. Galibin tashoshin talabijin da ke Intanet tashoshi ne masu yada shirye-shiryensu ta amfani da tauraron dan Adam, watau Satellite Channels kenan, a turance. Akwai su da yawa kuma suna da na su hanyar da suke watsa shirye-shiryensu. Su wadannan tashoshi, kamar na rediyo, sun kasu kashi-kashi su ma; akwai na kyauta zalla, in da zaka shiga ka kalli dukkan shirye-shiryensu kyauta ba tare da ka biya wasu kudade ba ta amfani da katin adashin banki (Credit Card). Wadannan tashoshi, har wa yau, sun sake kasuwa zuwa biyu; akwai wadanda za ka kalli shirye-shirye ne kai tsaye (live), daidai lokacin da ake yada su. Galibin wadannan tashoshi su ne manyan tashoshin yada labarai na duniya, irinsu Al-Jazeerah (Qatar), CNN (Amurka), CBS (Amurka), BBC (Ingila), Al-Alam (Iran), Al-Hurra (na Amurka ne, tana Dubai), Al-Majd (Saudiyyah) da dai sauransu. Dukkan wadannan tashoshi zaka same su kamar yadda mai DSTV ko NileSat ke samun su, ka kalla ba matsala. Akwai kuma kashi na biyu, wanda sai kana da kudi zaka iya kallon shirye-shiryen su. Galibin ire-iren tashoshin nan tashoshi ne masu gabatar da shirye-shirye na cikin gida (domestic programmes) a kasashen Turai ko Amurka ko wasu kasashe na Gabas-ta-tsakiya (Middle East). Akwai kuma wasu tashoshi masu nuna wasannin kwallo na Premier League da ya shafi kungiyoyin kwallon Ingila, da na Turai, duk su ma sai kana da kudi zaka iya kallon shirye-shiryen su. Bangare na biyu kuma shine wadanda ba kai tsaye suke watsa shirye-shiryen su ba. Tashoshi ne masu yada taskantattun shirye-shirye, kuma su ma sun kasu kashi biyu ne. Akwai na kyauta, da kuma na sayarwa. Watakil mai karatu zai yi mamakin jin cewa, “wai shirye-shiryen talabijin da na rediyo ma sai mutum ya saya?” Af, ai jari-hujjan kenan. Su a can wannan ya zama jiki a garesu. To wadannan su ne nau’ukan tashoshin talabijin da ke giza-gizan yanar sadarwa ta duniya. Saura kuma mu ji irin tsarin da suke bi wajen yada shirye-shiryen su.


Tsarin Gabatar da Shirye-shirye

Idan ka shiga gidajen yanar sadarwa na tashoshin talabijin, akwai abubuwa da dama da watakil ba za ka gan su a fili ba su ma, amma suna nan. Abubuwa ne da ke da nasaba da fasahar tsara gidajen yanar sadarwa. Da farko dai akwai jakunkunan bayanai na sauti da hotuna masu motsi, watau Video Files, wadanda ke dauke da shirye-shiryen da ake taskancewa. Wannan ya fi zama ruwan dare a tashoshin talabijin masu sayar da wakoki ko shirye-shiryen da suke gabatarwa masu kayatarwa. Domin sun riga sun tanadi dukkan wakoki ko shirye-shiryen da suke saidawa. Za ka ka samu hanyar kallon wadannan wakoki daga irin alamun da ke makale a gidan yanar, cikin sauki. Wadannan jakunkunan bayanai an gina su ne su ma a tsarin mp3, ko mp4, ko midi ko mov ko mpeg da dai sauran hanyoyin taskance bayanai masu sauti da hoto mai motsi a Intanet. Bayan haka, a kan girke su a rumbun adana bayanai na gidan yanar, watau Web Database. Duk lokacin da ka shigo, ka bukaci kallon shirye-shirye, Uwar Garken za ta miko maka su. Idan kuma gidajen talabijin na watsa shirye-shiryen su ne kai tsaye, to akwai manhaja ko masarrafa da suke amfani da ita, wacce ke baiwa kwamfutarka daman miko maka bayanan iya gwargwadon yadda take karban su daga Uwar Garken gidan gidan talabijin.

Yanayin Kallon Shirye-Shirye

Ga duk mai bukatar kallon shirye-shiryen gidajen talabijin da ke Intanet, yana bukatar wasu makale-makale a kwamfutar da yake amfani da ita, wadanda suke ta’allaka ne da rariyar lilo da tsallake-tsallakenta, watau Web Browser, idan ba haka ba, bazai iya sauraro ba. Da farko kana bukatar diro da wasu manhajoji na musamman wadanda za su taimaka maka wajen kallon shirye-shiryen. Akwai irin wadannan manhajoji da dama, wadanda a turancin Intanet a ke kiran su da suna Plug-Ins. Akwai su Real Player (www.real.co.uk), wanda galibi a gidajen yanar sadarwa shi aka fi amfani da shi, don yafi nuna hotunan bidiyo rau-rau, kai kace a talabijin din kake kallo. Sai kuma irin su Quick Time (
www.apple.com). Shi wanda ke zuwa cikin manhajar Windows, watau Media Player, shi ma yana da kyau. Na baya-bayan nan shi ne Media Player 11. A wasu tashoshin talabijin din kuma, za ka samu basu amfani da kowanne cikin wadanda muka ambata a sama ba, sai Macromedia Flash Player. Wannan manhaja na da wata maziyya wacce ke babanta ta da sauran, wajen saurin bayyana hotuna masu motsi da kuma taskance sauti. Idan haka ta kasance, sai kaje gidan yanarsa da ke http://www.macromedia.com, don ka diro da shi, kyauta. Idan ka samu wannan, sai kuma abin jin Magana, watau Speaker ko kuma Headphone. Duk wanda ka ke da shi yayi. Duk lokacin da ka matsa alama ko shirin da ka ke son kallo, wannan manhaja za ta karbo maka shi ta budo maka iya fadin shafin da zaka iya kallon shirin gaba daya. Idan shafin da aka budo maka yai maka kunci, duk akwai in da za ka iya fadada shi, ba tare da wata matsala ba. Su wadannan manhajoji na Plug-Ins, musamman aka gina su don jiyar da sauti da hotuna masu motsi na Video ko Animations a kwamfuta, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya. Idan manhajar ta jawo jakar bayanin, za ta bayyana a fuskar kwamfutarka, ta budo shirin, don fara nunawa (playing), sai kuma “jami’an” da aka tanade su don sadar da ruhin jikin kwamfuta da gangar-jikinta (Sound and Video Drivers), su hada manhajar da abin jin magananka, watau Speakers ko Headphone da ka jona ma kwamfutar. Haka zaka yi ta kallo tare da sauraro har sai shirin ya kare, ko kuma adadin mintuna ko sa’o’in da aka diba ma jakar sautin ya kai, idan taskantaccen shiri ne (recorded program). Idan ka sake ya katse, sai ka yi la’akari da dalilan da aka bayar a makon jiya, cewa; ko dai wayar kebul din ka ta cire, ko kuma yanayi ya sauya, ma’ana an fara ruwa ko kuma hadari ya hadu. Idan duk babu dayan biyun nan, to watakil jakar da ke dauke da shirin ce ta lalace, kuma wannan manhaja da ke da hakkin nuna maka shirin, zai sanar da kai irin matsalar. A wasu lokuta kuma zaka ga shafin manhajar ta dau lokaci kafin ta budo. Wannan bai rasa nasaba da abu biyu, na farko shine yawa ko girman mizanin jakar da ke dauke da shirin (File Size), wanda wannan din shi kan shi yana da alaka ne da yanayin saurin kwamfutar ka, wajen girman mizani. Idan kwamfutar mai sauri ce, zata gaggauta wajen budo shi, duk da yawansa. Idan kuma raguwa ce, sai kayi hakuri, sai sanda ta budo maka. Dalili na biyu kuma wannan dabi’a ce ta hanyar sadarwa a Intanet, cewa hotuna masu motsi su suka fi kowane irin bayani nawa wajen budowa, saboda girman su da kuma irin hanyar da suke bi kafin isowa kwamfutarka. A yanzu ne ake ta kokacin ganin an kyautata wannan dabi’a ta kwamfuta wajen saurin karba da kuma jiyarwa ko ganarwa.

Tashoshin Talabijin a Intanet

Wani abin da mai karatu ba zai ji dadin sa ba shine, babu tashoshin talabijin na Intanet da ke yada shirye-shiryen su da harshen Hausa a halin yanzu. Na san akwai shiri da gwamnatin Jigawa karkashin tsohon Gwamna Saminu Turaki ta fara yi, na samun tashar talabijin ta al’adun Hausa wacce zata rinka watsa labarai da sauran shirye-shirye kan al’adu da harshen Hausa. A karkashin wannan shiri, wannan tasha za ta kasance ne budaddiya; kowa na iya kallon shirye-shiryenta a dukkan bangarorin duniya ta hanyar tauraron dan Adam, watau Satellite. A halin yanzu ban san in da aka kwana ba. To tunani na a nan shine, da wannan tasha ta samu a halin yanzu ko a wancan lokaci, ina da yakinin za ai mata gidan yanar sadarwan ta na musamman, wanda kuma daga nan za ta iya watsa shirye-shiryenta ta hanyar Intanet. To amma haka bai kasance ba a halin yanzu. Don haka tashoshin talabijin da ke Intanet yanzu, sabanin na rediyo, babu na harshen Hausa. Daga turancin Ingilishi sai Jamusanci, sai Mandarin, da Sifaniyanci da sauran harsunan duniya. Don haka idan ka san irin harshen da kake son kallon shirye-shiryen su, za ka samu cikin sauki. Ga kuma takaitaccen bayani nan a kasa.


Neman Tashoshi a Intanet

A halin yanzu akwai gidan yanar sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da ke taimaka ma mai neman tashoshin talabijin don kallon shirye-shiryen da suke watsawa. Duk da yake gidan yanar sadarwan Yahoo! na da na ta (za a same shi a nan:
http://video.yahoo.com) Haka ma gidan yanar sadarwa ta Google, tana da gidan yanar sadarwa na watsa shirye-shiryen talabijin da kuma faya-fayan bidiyo daga ko ina ne a kasashen duniya (za a samu wannan shafi a http://video.google.com, ko kuma ka je http://www.youtube.com). Amma idan kana son samun tashoshi daga dukkan kasashen duniya, za ka iya samu in har tashoshin sun bude shafin yana na watsa shirye-shirye a kasar. Wannan shi ne ma hanya mafi sauki wajen neman tashoshi, kamar dai yadda bayani ya gabata a makon jiya, kuma zai taimaka wajen neman wata tasha wacce ka san kasar da ta ke, amma kuma kuma baka san adireshin gidan yanar sadarwan ta ba. Wannan gidan yana na neman tashoshin talabijin shi ake kira World Internet TV, kuma za a samu shafin gidan yanar a nan: http://www.wwitv.com. Wannan ita ce shahararriyar mahada da ke tattare da tashoshin talabijin sama da dubu biyu da dari biyar daga sassan duniya daban-daban. Wacce ke biye mata kuma ita ce World TV List, wacce ke samuwa a wannan adireshi: http://www.worldtvlist.com. Duk tashar da ka ke so, a kowace kasa take, muddin ta bude shafin yana tana watsa shirye-shiryen ta, za ka samu har ka kalli shirye-shiryen su. Sai dai kada mai karatu ya mance, wasu daga cikin tashoshin na kudi ne, sai kana da katin adashin banki za ka iya kallon su. Amma galibi dai, duk kyauta ne.

Kammalawa

Daga karshe kuma a mako mai zuwa, zamu kawo bayanai kan tsarin tsarin da kamfanonin gidajen jaridu da mujallu suke bi wajen nasu harkar. Kamar kullum, duk abin da ba a fahimta ba, a rubuto don neman Karin bayani. Na samu sakonni na neman Karin bayani kan Local Area Network da sauransu, zan samu lokaci don amsa su, in Allah Ya yarda. Ina mika godiya ta musamman ga Malam AbdurRahman Mamman Abdu, Malam Abdullahi Kyari, Umar Suleiman, Sanusi Imam, Sani Abubakar Jos, da kuma Malam Aminn bn Yusuf da ke tsangayar horar da malamai a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Mun gode, Allah bar zumunci, amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa
Garki II, Abuja. 080 34592444
Fasaha2007@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com

Friday, August 10, 2007

Nau'ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (2)

Matashiya

Mun fara kawo mukaddima a makon da ya gabata kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke giza-gizan sadarwa na Intanet. Inda muka fara da irin dalilan da suka haddasa yaduwar nau’ukan wadannan hanyoyin sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da nasu muhallin da su ke ta taka rawa shekaru kusan hamsin da suka gabata. A yau muka ce zamu ci gaba da koro bayanai kan ire-iren wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa, da tsarin da suke gudanuwa a kai da kuma yadda mai karatu zai iya amfana da wadannan hanyoyi ba tare da ya mallaki nau’urorin da ake sauraro ko saduwa da su ba. Bisimillah, wai an hada Malamai kokawa:

Hanyar Sadarwa ta Rediyo

Nau’in fasaha ko hanyar sadarwa da zamu fara bayani a kai ita ce hanyar sadarwa ta rediyo, wacce ke daga cikin tsoffin hanyoyin sadarwa a duniya. Alal hakika kowa ya san cewa dole ne a mallaki akwatin rediyo don sauraron shirye-shirye irin su labarum duniya da sauransu. Amma wani zai yi mamaki matuka idan ka ce masa akwai wani tsari a duniya in da zai iya sauraron shirye-shiryen gidajen rediyo ba tare da ya mallaki akwatin rediyo ba, musamman idan bai taba jin labarin fasahar sadarwa ta Intanet ba da irin yadda take gudanuwa. Akwai hanyoyi da dama da suke bi wajen yada labarai da shirye-shiryen yau da kullum. Kafin nan, gidajen rediyo masu yada shirye-shiryensu a Intanet sun kasu kashi-kashi. Kashin farko su ne gidajen rediyo masu tsarin FM, wadanda kuma galibi wake-wake su ke sanyawa ga dukkan masu sauraronsu. A gidajen yanar sadarwan su idan ka je, zaka samu hanyoyin sauraron wakoki iri biyu; na kyauta da kuma wadanda sai ka biya za ka samu isa zuwa gare su. Wadannan galibi basu cika damuwa da gabatar da wasu shirye-shirye ba, kuma wakokin na su duk taskantattun wakoki ne; ma’ana an riga an tanade su a gidan yanar sadarwan, ba wai kai tsaye (Live) ake watso su ba. Sai kuma bangaren masu yada labarai da sauran shirye-shirye a tsarin matsakaici da kuma gajeren zango, watau MW da kuma SW, watau manyan zangon yada shirye-shirye mafiya girma da shahara a duniya. A ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwa na rediyo, nau’ukan shirye-shirye kala biyu suke da su; akwai wadanda za ka saurare su ne kai tsaye, kamar yadda masu saurare daga akwatunan rediyon su suke sauraro su ma. Ire-iren wadannan shirye-shirye galibi labarun duniya ne da kuma shirye-shirye masu kebantattun ranaku da suka shafi hira da baki da ake gayyata zuwa gidajen rediyon. Sai kuma kalan shirye-shirye na biyu, wadanda taskantattu ne. Su wadannan sun hada da wakoki da wasu shirye-shirye maimatattu. A wasu lokuta kuma za ka samu dukkan shirye-shiryen da aka yi na baya an taskance su (archived) don masu ziyara. Wadannan su ne nau’ukan gidajen rediyon da ake da su a giza-gizan sadarwa ta Intanet. Abu na karshe da ya kamata mai karatu ya sani shi ne, wasu daga cikin shirye-shiryen da ke wadannan gidajen yanar sadarwa na rediyo za ka samu na saidawa ne (musamman a kasashen Turai da Amerika). Idan ka je ka biya sai a budo maka su ka saurara ko ka ma diro da su a kwamfutarka, don sauraro a wasu lokutan. Galibin gidajen yanar sadarwa na FM da ke Intanet duk sayar da wakokin su suke. Kamfanin Apple da ke Amurka ce gaba-gaba wajen wannan sana’a. Su wadannan gidajen rediyo ana kiran su Music On Demand Stations. Ma’ana, tashoshin rediyon sayar da wakoki. Akwai na kyauta tabbas, musamman gidajen rediyon BBC da VOA da DW Radio masu sashen harsunan kasashen waje, da kuma wasu gidajen yanar sadarwa na addinin musulunci masu zuba shirye-shiryen da’awa da ake watsawa a wasu gidajen rediyon Turai da sauran kasashen duniya, duk kyauta suke watsa shirye-shiryen su. Kafin mu kai ga ambato adireshin wasu daga cikin ire-iren wadannan gidajen rediyo da ke Intanet, zai dace mai karatu ya san tsarin da suke bi wajen yada shirye-shiryen su, da yadda zai iya mu’amala da gidajen yanar sadarwan su idan ya samu kan sa a can.

Tsarin Gabatar da Shirye-shirye

Idan ka shiga gidajen yanar sadarwa na gidan rediyo, akwai abubuwa da dama da watakil ba za ka gan su a fili ba, amma suna nan. Abubuwa ne da ke da nasaba da fasahar tsara gidajen yanar sadarwa. Da farko dai akwai jakunkunan bayanai na sauti, watau Sound Files, wadanda ke dauke da shirye-shiryen da ake taskancewa. Wannan ya fi zama ruwan dare a gidajen rediyon sayar da wakoki. Domin sun riga sun tanadi dukkan wakokin da suke saidawa. Za kuma ka samu hanyar sauraron wadannan wakoki daga irin alamun da ke makale a gidan yanar, cikin sauki. Wadannan jakunkunan bayanai an gina su ne a tsarin mp3 ko midi ko mov ko mpeg da dai sauran hanyoyin taskance bayanai masu sauti a Intanet. Bayan haka, a kan girke su a rumbun adana bayanai na gidan yanar, watau web database. Duk lokacin da ka shigo, ka bukaci sauraron shirye-shirye, Uwar Garken za ta miko maka su. Idan kuma gidajen rediyon na watsa shirye-shiryen su ne kai tsaye, to akwai manhaja ko masarrafa da suke amfani da ita, wacce ke baiwa kwamfutarka daman miko maka bayanan iya gwargwadon yadda take karban su daga Uwar Garken gidan rediyon. Shi yasa wasu lokuta zaka ji Mannir Dan Ali ko Alhaji Dauda Kulibali ko Aishatu Musa da ke sashen Hausa na Rediyon BBC suna cewa “. . .a yanzu za ku iya sauraron mu a mita na 41, da 26, da 49. Ko kuma kai tsaye ta hanyar sadarwa ta Intanet. . .”. Duk da wannan tsari su ke amfani.

Yanayin Sauraro

Ga duk mai bukatar sauraron shirye-shiryen gidajen rediyon da ke Intanet, yana bukatar wasu makale-makale a kwamfutar da yake amfani da ita, idan ba haka ba, bazai iya sauraro ba. Da farko kana bukatar diro da wasu manhajoji na musamman wadanda za su taimaka maka wajen sauraron shirye-shiryen. Duk da yake dukkan kwamfuta kan zo da irin wannan manhaja, amma galibin gidajen yanar sadarwa basu cika damuwa da na kamfanin Microsoft ba. Akwai irin wadannan manhaja da dama, wadanda a turancin Intanet a ke kiran su da suna Plug-Ins. Akwai su Real Player (www.real.co.uk), wanda galibi a gidajen yanar sadarwa shi aka fi amfani da shi. Sai kuma irin su Quick Time (
www.apple.com). Shi wanda ke zuwa cikin manhajar Windows, watau Media Player, shi ma yana da kyau, amma sau tari idan kaje wasu tashoshin za a ce maka sai kana da Real Player a kwamfutarka zaka iya sauraro. Idan haka ta kasance, sai kaje gidan yanarsa da ke http://www.real.co.uk, don ka diro da shi, kyauta. Idan ka samu wannan, sai kuma abin jin Magana, watau Speaker ko kuma Headphone. Duk wanda ka ke da shi yayi. Duk lokacin da ka matsa alama ko shirin da ka ke son sauraro, wannan manhaja za ta karbo maka shi ta kuma jiyar da kai dukkan abin da ke kumshe cikin sa. Su wadannan manhajoji na Plug-Ins, musamman aka gina su don jiyar da sauti da hotuna masu motsi na Video ko Animations a kwamfuta. Idan manhajar ta jawo jakar bayanin, za ta fara bugawa (playing), sai kuma “jami’an” da aka tanade su don sadar da ruhin jikin kwamfuta da gangar-jikinta (Drivers), su hada manhajar da abin jin magananka, watau Speakers ko Headphone da ka jona ma kwamfutar. Haka zaka yi ta sauraro har sai shirin ya kare, ko kuma adadin mintuna ko sa’o’in da aka diba ma jakar sautin ya kai. Idan ka sake ya katse, to dayan biyu; ko dai wayar kebul din ka ta cire, ko kuma yanayi ya sauya, ma’ana an fara ruwa ko kuma hadari ya hadu. Idan duk babu dayan biyun nan, to watakil jakar da ke dauke da shirin ta lalace, kuma wannan manhaja da ke da hakkin jiyar da kai shirin, zai sanar da kai irin matsalar.

Gidajen Rediyon Harshen Hausa a Intanet

Na tabbata galibin masu karatu a yanzu sun san cewa gidajen rediyo irin su BBC, Muryar Amurka (VOA), Muryar Jamus, da gidajen rediyo na kasar Sin da Faransa, duk ana iya sauraron su ta Intanet. Wannan na daga cikin ci gaban da aka samu a wannan bangaren fasahar sadarwa na zamani. Idan kana son sauraron labaru da shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC ko Muryar Amurka, ko Muryar Jamus, abu ne mai sauki, muddin ka cika ka’idojin da aka zayyana a sama. Za ka iya sauraron shirye-shiryen baya, da kuma wanda ake yi a lokacin da ake ciki (in har lokacin yin ne). Sai dai, kamar yadda bayani ya gabata a sama, idan siginar Intanet ta dauke, zaka ji shirin ya yi tsit. Wannan wata dama ce ga wadanda ba su iya samun sauraron shirye-shiryen a kan lokaci. Bayan haka, za ka iya sauraron wasu tashoshin BBC na turanci a wannan adireshi
http://www.bbc.co.uk/radio. Idan kuma na Sashen Hausa ka ke son sauraro, ka shiga nan: http://www.bbc.co.uk/hausa, sai ka nemi alamar da zata sadar da kai da shafin shirye-shiryen a sauti. Haka idan kana son sauraron na Muryar Amurka, watau Voice of America, za ka samesu a nan: http://www.voanews.com/hausa. Nan ma sai ka nemi alamar da za ta sadar da kai da shirye-shiryen cikin sauti. Har wa yau, za a samu na Muryar Jamus, watau Deustchewelle, shi kuma a wannan adireshin: http://www2.dw-world.de/hausa. Wadannan su ne shahararru cikin gidajen rediyon da ke shafin yana a Intanet cikin harshen Hausa. Idan mai karatu ya ziyarce su, zai samu bayanai kan yadda zai yi mu’amala da jakunkunan da ke dauke da dukkan shirye-shiryen.

Neman Tashoshi a Intanet

A halin yanzu akwai gidan yanar sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da ke taimaka ma mai neman tashoshin rediyo don sauraren shirye-shirye da dama. Duk da yake gidan yanar sadarwan Yahoo! na da na ta (za a same shi a nan:
http://music.yahoo.com), amma idan kana son samun tashoshi daga dukkan kasashen duniya, za ka iya samu in har akwai tashoshin da suka bude shafin yana na watsa shirye-shirye a kasar. Wannan shi ne ma hanya mafi sauki wajen neman tashoshi, kuma zai taimaka wajen neman wata tasha wacce ka san kasar da ta ke, amma kuma kuma baka san adireshin gidan yanar sadarwan ta ba. Wannan gidan yana na neman tashoshin rediyo shi ake kira Radio Locator, kuma za a samu shafin gidan yanar a nan: http://www.radio-locator.com. Duk tashar da ka ke so, a kowace kasa take, muddin ta bude shafin yana tana watsa shirye-shiryen ta, za ka samu har ka saurari shirye-shiryen su.

Kammalawa

Daga karshe, yaduwar hanyoyin kayatar da gidajen yanar sadarwa wajen yada bayanai da sadar da su, shi ya haddasa samuwar nau’ukan fasahar sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da na su muhallin tabbatacce. Wannan har wa yau ke nuna irin tasirin da wannna fasaha ta Intanet ke da shi, wanda ya shanye na sauran nau’ukan hanyoyin sadarwan. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, za mu ci gaba da kawo bayanai kan gidajen yanar sadarwa masu dauke da talabijin, ya Allah na cikin gida ne (local channels) ko kuma wadanda ake watsawa ta tauraron dan Adam, watau Satellite Channels. Ina mika godiyar wannan shafi ga dukkan masu rubuto sakonnin gaisuwa da ban gajiya ko kuma bugo waya don yin hakan. Allah Ya bar zumunci, amin summa amin.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa
Garki II, Abuja. 080 34592444
Fasaha2007@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com

Tuesday, August 7, 2007

Nau'ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (1)

Shimfida

Watakil mai karatu zai yi mamakin ganin taken wannan kasida na wannan mako, cewa “ah ah…shi Intanet din ba fasaha ba ne na sadarwa?”. Fasaha ce mai zaman kan ta, amma ta sha banban da sauran fasahohi ‘yan uwanta, saboda irin tsarin da aka gina ta a kai. Idan mu ka ce za mu yi Magana a kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke cikin Intanet, muna nufin dukkan wasu hanyoyi da ake amfani da su kafin ko bayan zuwan fasahar Intanet, wajen sadarwa a tsakanin al’umma da ke wannan duniya ta mu, wadanda kuma ake amfani da su wajen wajen sadarwa ta wannan hanya ta Intanet, a wannan zamani, saboda irin kyakkywan tsari da daman da Intanet din ya bayar. Wannan zai ba mu daman sanin irin gamewar da wannan fasaha ta Intanet ta yi ma duniya. Ta zama jakar magori. So nake mu dauki kowace hanya ta fasahar sadarwa daya-bayan-daya, don yin bayani kan samuwar ta a fasahar Intanet, da dukkan wani bayani da ya danganci yadda ake gabatar da sadarwa ta hanyar, duk da kasancewar ta a Intanet, ba tare da wata matsala ba. A takaice dai za mu dubi muhallin da kowanne ke gudanuwa ne a Intanet da tasirin hakan ko rashin sa, wajen dada yaduwar hanyoyin sadarwa na zamani a duniyar yau. Za mu yi kokarin takaita bayani kan kowanne, kamar yadda mu ka saba.

Kafin nan, zan so a yau mu dubi dalilan da suka kawo zuwan wadannan hanyoyin sadarwan kan giza-gizan sadarwa na Intanet. Ta yaya aka yi masu tafiyar da gidajen sadarwa ta rediyo suka fara tunanin zuwa kasuwar Intanet? Ina masu gidan talabijin? Me ya kai su can? Ai na hangi masu wayoyin salula ma suna ta cin duniyar su da tsinke. Me ya kai su can su ma? Wadannan tambayoyi da ma wasu, su ne za mu shagaltu da su a wannan mako. Daga karshe za mu kawo wasu tambayoyi da wani cikin masu karatu ya rubuto, don fayyace amsoshin su in Allah Ya yarda. A yanzu kam mu je zuwa, wai kwamfuta ta hau kura!

Musabbabai

Samun nau’ukan fasahar sadarwa a Intanet a yau ya samo asali ne saboda wasu dalilai kwarara guda uku, wadanda galibin kamfanonin wadannan sadarwa suke ganin dama ce ta samu wajen ci gaba da habbaka harkokin sadarwa wajen yada al’adu da tunani da ilmummuka daban-daban a duniya, kamar yadda su ka faro a baya. Wannan bai sa sun bar tafarkin yada labarun su da suka gada kaka da kakanni ba. Hasali ma dai galibin kamfanonin ma sabbi ne, wadanda wannan ita ce kadai hanyar da suka dauka don tafiyar da wannan harka. Wadannan dalilai dai ga su kamar haka:

“The DotCom Boom”:

Kamar yadda bayani ya sha gabata a wannan shafi cewa daga cikin dalilan da suka haddasa yaduwar fasahar Intanet wajen tasiri a duniya su ne samuwar ingantacciyar hanyar tsarawa da kuma kayatar da shafukan gidajen yanar sadarwa ta hanyar fasahar Hypertext Markup Language (HTML) da kuma ka’idar mika bayanai da ke dauke a shafin Intanet masu launi ko dauke da sauti ko hotuna, wanda kafin kirkiran wannan ka’ida da fasaha, hakan baya yiwuwa. Wannan ka’ida, kamar yadda muka sani, ita ce ka’idar Hypertext Transfer Protocol (HTTP), kuma Farfesa Tim Bernes-Lee, watau “Baban Intanet”, shi ya kirkiri wannan ka’ida tare da fasahar HTML a shekarar 1990. Wannan ci gaba da aka samu a tafarkin bunkasar Intanet ta dada kara jawo sanayya ga wannan fasaha, ta in da musamman ‘yan kasuwa suka ga dama ta samu wajen tallata hajojin su. Ana cikin haka kuma sai ga Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake (Web Browser) na kamfanin Microsoft mai suna “Internet Explorer” ta shigo. Mc Andreessen, masanin manhajar kwamfuta kuma mai kamfanin Netscape, shi ma ba a bar shi a baya ba, in da ya shiga dakin bincike don kirkiro tasa Rariyar Lilo da Tsallaken mai suna “Netscape Navigator”. Shi kenan, ai sai duniya ta game wajen aiwatar da hada-hada a giza-gizan sadarwa ta duniya. Maimakon malam jami’o’i da a farko su kadai ne ke cin Karen su ba babbaka wajen zuba bayanai da gudanar da bincike, sai ga ‘yan kasuwa da hajojin su, sun kwace fage. Wannan har wa yau ta sa aka samu ci gaba da samun kirkire-kirkiren manhajoji ko masarrafan kwamfuta da ake iya gabatar da kasuwanci ko Karin bincike da su. Wannan zamani ya faro ne daga farko-farkon shekarar 1990 zuwa 1999, kuma shi a ke ma lakabi da “The DotCom Boom”; watau zamanin yaduwar kamfanonin kasuwanci a giza-gizan sadarwa na duniya. Zamanin da kamfanoni masu tozon adireshin (.com) suka yawaita a Intanet. Babu shakka daidai wannan lokaci ne aka fara samun yaduwar sauran nau’ukan fasahar sadarwa a giza-gizan sadarwa ta Intanet. Don an samu manhajoji ko masarrafa na kwamfuta masu bayar da daman tsara shafin yanan gizo mai launi ko dauke da sauti ko hotuna masu motsi da ma marasa motsi, duk a Intanet. Har wa yau, duk a cikin wannan zamani ne aka samu masarrafa masu iya daukawa da kuma yada labarai ta hanyar Radio Transmitters. Da wannan ya zama abu ne mai sauki ka iya sauraran shirye-shiryen gidan rediyo a Intanet kamar yadda kake sauraro a akwatin rediyon ka. Wannan ita ce daili ta farko, kuma mafi karfi daga cikin dalilan da suka haddasa samuwar sauran nau’ukan fasahar sadarwa a Intanet.

Saurin Yaduwa

Bayan samuwar wannan zamani mai take “The DotCom Boom”, sai ya zama fasahar Intanet ta samu wani nau’i na yaduwa mai ban mamaki, wanda kusan duk inda dan Adam yake a duniya, muddin ya mallaki kwamfuta da hanyoyin hada shi, to zai sadu da wanda ke ko ina ne a gidajen yanar sadarwa ta duniya. Wannan sifa ta yaduwa da Intanet ya mallaka, ya kara karfafa samuwar nau’ukan sadarwa a Intanet. Wannan siffa har way au na daga cikin kebantattun siffofin fasahar Intanet. (Sabanin sauran nau’ukan fasahar sadarwa da sai an dauki tsawon lokaci kafin su yadu). Malama Helen Cairncross, a cikin littafinta mai suna The Death of Distance, ta nuna cewa hanyoyin sadarwa irin su Rediyo da Talabijin da jaridu da kuma hanyar aikawa da bayanai na Fax da kuma Telegram, duk sun dauki shekaru a kalla goma zuwa talatin kafin su zama ruwan dare a sauran kasashen duniya. Amma fasahar Intanet ta samu habbaka ne a tsawon lokacin da bai wuce shekaru ashirin ba ko kasa da haka. Don haka, wannan saurin yaduwa na daga cikin dalilan da suka haddasa samuwar sauran nau’ukan fasahan sadarwa a Intanet.

Saukin Mu’amala

Sai dalili na karshe, watau Saukin Mu’amala. A tabbace yake cewa duk abin da ya yadu a hannun jama’a, kuma suke amfani da shi a kullum don tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum, duk wahalan sa, wataran zai zama sassauka. Wannan mujarrabi ne na rayuwa, kuma abin da ya faru da fasahar Intanet kenan. Daidai lokacin da wannan fasaha ya yadu kuma mu’amala da shi ya sawwaka a hannun al’umman da ke rayuwa tare da shi, sai ya zama masu dillancin labaru da hanyoyin yada shi sun sake samun wata kafa ta saduwa da mutane cikin sauki da araha. Wannan ya kara musu kwarin guiwan kirkiran kafafen yada labarai da sadarwa a Intanet ta dukkan hanyoyi. Domin a tunaninsu wannan shi zai kara sa su samu karbuwa da yawan masu sauraro ko abokan mu’amala.

Kammalawa

Daga karshe za mu dakata a nan. Ina mika godiya ta ga dukkan masu aiko sakonnin text ko na Imel. Mun gode Allah saka da alheri. Har wa yau, duk abin da ba a fahimta ba, a rubuto don neman Karin bayani. Matambayi, in ji Malam Bahaushe, ba ya bata. Allah sa mu dace baki daya, amin. A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, za mu fara koro bayanai kan nau’ukan wadannan hanyoyin sadarwa da suke cin duniyarsu kuma suke cin wata a giza-gizan sadarwa ta Intanet. A dakace mu!
……………………………………………………………………………………………...

Wasu Tambayoyi

Wannan shafi ya samu tambayoyi guda uku daga wajen Malam Sanusi Sagir Tudun Murtala (
elnusy111@yahoo.com), daya daga cikin masu karatu, kuma ga abin da yake cewa:

Don Allah wasu tambayoyi nake so ayi mun bayani a kan su tambayoyin sune: Kamar yanda a internet cafe a ke sa lokaci kafin a iya amfani da kwamfuta, haka yake ma ga mai ita a gida? Sannan don Allah ya ake zuba bayanai a yanar gizo-gizo….Bayan haka, wai akwai security da ake sa wa bayanan? Na gode

Amsa:

Da farko dai, idan masu karatu basu mance ba, a kasidar “Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake (Cyber CafĂ©), mun sanar da cewa galibin kwamfutocin da ake amfani da su wajen shiga Intanet, a kulle su ke. Wannan kariya ne wajen tabbatar da cewa duk wanda ya sayi sa’a daya, to lallai sa’a dayan yayi. Da zaran ka samu dakiku sittin, kwamfutar za ta rufe kanta. Wannan shi ake kira “Cyber Lock” a turancin Intanet. To amma idan kwamfutar gida ce, sai in ka saya ka sanya mata da kanka, domin manhaja ne mai zaman kan sa, ba wai sayan kwamfutar ake yi da shi ba. In kana bukata sai ka saya ka sanya. Amma ni ina ganin tunda ba kasuwanci kake da kwamfutar ba, naka ne, ka iya barin ta haka.

Sai Magana kan yadda ake zuba bayanai a yanar gizo-gizo, watau gidan yanar sadarwa kenan, wanda wasu ke iya shiga don karantawa, in na fahimce ka. Zuba bayanai ya kasu kashi-kashi; akwai wanda za ka iya zubawa a matsayin dakunan gidan yanar sadarwa (Web Pages), a matsayinka na wanda ya mallaki wannan gidan yanar sadarwa. Sai kuma Mudawwana. Idan kana da Mudawwanar Intanet (Blog) nan ma za ka iya zuba ra’ayoyin ka wasu su karanta. Ko kuma ka aika da kasidu ko ra’ayoyin ka zuwa wasu gidajen yanar sadarwa irin su Gamji.com don su buga a gidan yanar sadarwan wasu su karanta. Duk wadannan hanyoyi ne na zuba bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet.

Sai tambayar karshe, wacce yake son sanin ko akwai wani Security da ake sa ma bayanan. Kalmar “Security”, wacce ke nufin hanyar tsaro ko wata kariya da ake sanya ma bayanai a giza-gizan sadarwa na duniya na bukatar bayani ne mai tsawo. A takaice abin da zan iya cewa shine “eh akwai kariya da ake sanya ma bayanai saboda kare su daga kwafowa ba tare da izni ba, ko kuma hana kwafansu ma gaba daya, ko da kuwa za ka ga bayanan, har ka karanta. A wasu lokutan kuma, ba za ka san da bayanan ba, idan ba ka da iznin ganin su.” Bayani kan wannan abu ne da zai cinye shafuka a nan. Zan dakata sai in munasaba ta sake kawo mu. Da fatan ka gamsu.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Garki II.
Abuja.
080 34592444.
fasaha2007@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com http://babansadiq.blogpsot.com