Matashiya
A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai kan tsarin da ke tattare da yada labarai da wakoki a gidajen yanar sadarwa na tashoshin rediyo da ake dasu a giza-gizan sadarwa ta duniya. Mun kuma nuna irin hanyoyin da su ke bi wajen taskance labaran musamman ga tashoshin FM masu sayar da wakoki ko kuma yada taskantattun shirye-shiryen su. Har wa yau, ba mu karkare wancan mako ba sai da muka tabbatar da cewa mun kawo bayanai kan dukkan makale-makalen da suka dace mai son sauraron labarai da shirye-shiryen tashoshin rediyo ta Intanet ke bukata kafin yayi hakan. A yau kuma cikin yardan Ubangiji za mu kama hanya in da zamu ji irin tsarin da masu tashoshin Talabijin ke bi a nasu harkan.
Hanyar Sadarwa ta Talabijin (Rediyo Mai Hoto)
Kamar yadda aka samu gidajen yanar sadarwa na yada shiryen-shiryen tashoshin rediyo a Intanet, to haka ake da gidajen yana na musamman in da ake yada shirye-shirye na Talabijin, kamar yadda ka ke kallo a talibijin gidan ka; banbancin kawai shine na irin hanyar da kake kallon shirin amma ba na hakikanin shirin ba. Galibin tashoshin talabijin da ke Intanet tashoshi ne masu yada shirye-shiryensu ta amfani da tauraron dan Adam, watau Satellite Channels kenan, a turance. Akwai su da yawa kuma suna da na su hanyar da suke watsa shirye-shiryensu. Su wadannan tashoshi, kamar na rediyo, sun kasu kashi-kashi su ma; akwai na kyauta zalla, in da zaka shiga ka kalli dukkan shirye-shiryensu kyauta ba tare da ka biya wasu kudade ba ta amfani da katin adashin banki (Credit Card). Wadannan tashoshi, har wa yau, sun sake kasuwa zuwa biyu; akwai wadanda za ka kalli shirye-shirye ne kai tsaye (live), daidai lokacin da ake yada su. Galibin wadannan tashoshi su ne manyan tashoshin yada labarai na duniya, irinsu Al-Jazeerah (Qatar), CNN (Amurka), CBS (Amurka), BBC (Ingila), Al-Alam (Iran), Al-Hurra (na Amurka ne, tana Dubai), Al-Majd (Saudiyyah) da dai sauransu. Dukkan wadannan tashoshi zaka same su kamar yadda mai DSTV ko NileSat ke samun su, ka kalla ba matsala. Akwai kuma kashi na biyu, wanda sai kana da kudi zaka iya kallon shirye-shiryen su. Galibin ire-iren tashoshin nan tashoshi ne masu gabatar da shirye-shirye na cikin gida (domestic programmes) a kasashen Turai ko Amurka ko wasu kasashe na Gabas-ta-tsakiya (Middle East). Akwai kuma wasu tashoshi masu nuna wasannin kwallo na Premier League da ya shafi kungiyoyin kwallon Ingila, da na Turai, duk su ma sai kana da kudi zaka iya kallon shirye-shiryen su. Bangare na biyu kuma shine wadanda ba kai tsaye suke watsa shirye-shiryen su ba. Tashoshi ne masu yada taskantattun shirye-shirye, kuma su ma sun kasu kashi biyu ne. Akwai na kyauta, da kuma na sayarwa. Watakil mai karatu zai yi mamakin jin cewa, “wai shirye-shiryen talabijin da na rediyo ma sai mutum ya saya?” Af, ai jari-hujjan kenan. Su a can wannan ya zama jiki a garesu. To wadannan su ne nau’ukan tashoshin talabijin da ke giza-gizan yanar sadarwa ta duniya. Saura kuma mu ji irin tsarin da suke bi wajen yada shirye-shiryen su.
Tsarin Gabatar da Shirye-shirye
Idan ka shiga gidajen yanar sadarwa na tashoshin talabijin, akwai abubuwa da dama da watakil ba za ka gan su a fili ba su ma, amma suna nan. Abubuwa ne da ke da nasaba da fasahar tsara gidajen yanar sadarwa. Da farko dai akwai jakunkunan bayanai na sauti da hotuna masu motsi, watau Video Files, wadanda ke dauke da shirye-shiryen da ake taskancewa. Wannan ya fi zama ruwan dare a tashoshin talabijin masu sayar da wakoki ko shirye-shiryen da suke gabatarwa masu kayatarwa. Domin sun riga sun tanadi dukkan wakoki ko shirye-shiryen da suke saidawa. Za ka ka samu hanyar kallon wadannan wakoki daga irin alamun da ke makale a gidan yanar, cikin sauki. Wadannan jakunkunan bayanai an gina su ne su ma a tsarin mp3, ko mp4, ko midi ko mov ko mpeg da dai sauran hanyoyin taskance bayanai masu sauti da hoto mai motsi a Intanet. Bayan haka, a kan girke su a rumbun adana bayanai na gidan yanar, watau Web Database. Duk lokacin da ka shigo, ka bukaci kallon shirye-shirye, Uwar Garken za ta miko maka su. Idan kuma gidajen talabijin na watsa shirye-shiryen su ne kai tsaye, to akwai manhaja ko masarrafa da suke amfani da ita, wacce ke baiwa kwamfutarka daman miko maka bayanan iya gwargwadon yadda take karban su daga Uwar Garken gidan gidan talabijin.
Yanayin Kallon Shirye-Shirye
Ga duk mai bukatar kallon shirye-shiryen gidajen talabijin da ke Intanet, yana bukatar wasu makale-makale a kwamfutar da yake amfani da ita, wadanda suke ta’allaka ne da rariyar lilo da tsallake-tsallakenta, watau Web Browser, idan ba haka ba, bazai iya sauraro ba. Da farko kana bukatar diro da wasu manhajoji na musamman wadanda za su taimaka maka wajen kallon shirye-shiryen. Akwai irin wadannan manhajoji da dama, wadanda a turancin Intanet a ke kiran su da suna Plug-Ins. Akwai su Real Player (www.real.co.uk), wanda galibi a gidajen yanar sadarwa shi aka fi amfani da shi, don yafi nuna hotunan bidiyo rau-rau, kai kace a talabijin din kake kallo. Sai kuma irin su Quick Time (www.apple.com). Shi wanda ke zuwa cikin manhajar Windows, watau Media Player, shi ma yana da kyau. Na baya-bayan nan shi ne Media Player 11. A wasu tashoshin talabijin din kuma, za ka samu basu amfani da kowanne cikin wadanda muka ambata a sama ba, sai Macromedia Flash Player. Wannan manhaja na da wata maziyya wacce ke babanta ta da sauran, wajen saurin bayyana hotuna masu motsi da kuma taskance sauti. Idan haka ta kasance, sai kaje gidan yanarsa da ke http://www.macromedia.com, don ka diro da shi, kyauta. Idan ka samu wannan, sai kuma abin jin Magana, watau Speaker ko kuma Headphone. Duk wanda ka ke da shi yayi. Duk lokacin da ka matsa alama ko shirin da ka ke son kallo, wannan manhaja za ta karbo maka shi ta budo maka iya fadin shafin da zaka iya kallon shirin gaba daya. Idan shafin da aka budo maka yai maka kunci, duk akwai in da za ka iya fadada shi, ba tare da wata matsala ba. Su wadannan manhajoji na Plug-Ins, musamman aka gina su don jiyar da sauti da hotuna masu motsi na Video ko Animations a kwamfuta, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya. Idan manhajar ta jawo jakar bayanin, za ta bayyana a fuskar kwamfutarka, ta budo shirin, don fara nunawa (playing), sai kuma “jami’an” da aka tanade su don sadar da ruhin jikin kwamfuta da gangar-jikinta (Sound and Video Drivers), su hada manhajar da abin jin magananka, watau Speakers ko Headphone da ka jona ma kwamfutar. Haka zaka yi ta kallo tare da sauraro har sai shirin ya kare, ko kuma adadin mintuna ko sa’o’in da aka diba ma jakar sautin ya kai, idan taskantaccen shiri ne (recorded program). Idan ka sake ya katse, sai ka yi la’akari da dalilan da aka bayar a makon jiya, cewa; ko dai wayar kebul din ka ta cire, ko kuma yanayi ya sauya, ma’ana an fara ruwa ko kuma hadari ya hadu. Idan duk babu dayan biyun nan, to watakil jakar da ke dauke da shirin ce ta lalace, kuma wannan manhaja da ke da hakkin nuna maka shirin, zai sanar da kai irin matsalar. A wasu lokuta kuma zaka ga shafin manhajar ta dau lokaci kafin ta budo. Wannan bai rasa nasaba da abu biyu, na farko shine yawa ko girman mizanin jakar da ke dauke da shirin (File Size), wanda wannan din shi kan shi yana da alaka ne da yanayin saurin kwamfutar ka, wajen girman mizani. Idan kwamfutar mai sauri ce, zata gaggauta wajen budo shi, duk da yawansa. Idan kuma raguwa ce, sai kayi hakuri, sai sanda ta budo maka. Dalili na biyu kuma wannan dabi’a ce ta hanyar sadarwa a Intanet, cewa hotuna masu motsi su suka fi kowane irin bayani nawa wajen budowa, saboda girman su da kuma irin hanyar da suke bi kafin isowa kwamfutarka. A yanzu ne ake ta kokacin ganin an kyautata wannan dabi’a ta kwamfuta wajen saurin karba da kuma jiyarwa ko ganarwa.
Tashoshin Talabijin a Intanet
Wani abin da mai karatu ba zai ji dadin sa ba shine, babu tashoshin talabijin na Intanet da ke yada shirye-shiryen su da harshen Hausa a halin yanzu. Na san akwai shiri da gwamnatin Jigawa karkashin tsohon Gwamna Saminu Turaki ta fara yi, na samun tashar talabijin ta al’adun Hausa wacce zata rinka watsa labarai da sauran shirye-shirye kan al’adu da harshen Hausa. A karkashin wannan shiri, wannan tasha za ta kasance ne budaddiya; kowa na iya kallon shirye-shiryenta a dukkan bangarorin duniya ta hanyar tauraron dan Adam, watau Satellite. A halin yanzu ban san in da aka kwana ba. To tunani na a nan shine, da wannan tasha ta samu a halin yanzu ko a wancan lokaci, ina da yakinin za ai mata gidan yanar sadarwan ta na musamman, wanda kuma daga nan za ta iya watsa shirye-shiryenta ta hanyar Intanet. To amma haka bai kasance ba a halin yanzu. Don haka tashoshin talabijin da ke Intanet yanzu, sabanin na rediyo, babu na harshen Hausa. Daga turancin Ingilishi sai Jamusanci, sai Mandarin, da Sifaniyanci da sauran harsunan duniya. Don haka idan ka san irin harshen da kake son kallon shirye-shiryen su, za ka samu cikin sauki. Ga kuma takaitaccen bayani nan a kasa.
Neman Tashoshi a Intanet
A halin yanzu akwai gidan yanar sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da ke taimaka ma mai neman tashoshin talabijin don kallon shirye-shiryen da suke watsawa. Duk da yake gidan yanar sadarwan Yahoo! na da na ta (za a same shi a nan: http://video.yahoo.com) Haka ma gidan yanar sadarwa ta Google, tana da gidan yanar sadarwa na watsa shirye-shiryen talabijin da kuma faya-fayan bidiyo daga ko ina ne a kasashen duniya (za a samu wannan shafi a http://video.google.com, ko kuma ka je http://www.youtube.com). Amma idan kana son samun tashoshi daga dukkan kasashen duniya, za ka iya samu in har tashoshin sun bude shafin yana na watsa shirye-shirye a kasar. Wannan shi ne ma hanya mafi sauki wajen neman tashoshi, kamar dai yadda bayani ya gabata a makon jiya, kuma zai taimaka wajen neman wata tasha wacce ka san kasar da ta ke, amma kuma kuma baka san adireshin gidan yanar sadarwan ta ba. Wannan gidan yana na neman tashoshin talabijin shi ake kira World Internet TV, kuma za a samu shafin gidan yanar a nan: http://www.wwitv.com. Wannan ita ce shahararriyar mahada da ke tattare da tashoshin talabijin sama da dubu biyu da dari biyar daga sassan duniya daban-daban. Wacce ke biye mata kuma ita ce World TV List, wacce ke samuwa a wannan adireshi: http://www.worldtvlist.com. Duk tashar da ka ke so, a kowace kasa take, muddin ta bude shafin yana tana watsa shirye-shiryen ta, za ka samu har ka kalli shirye-shiryen su. Sai dai kada mai karatu ya mance, wasu daga cikin tashoshin na kudi ne, sai kana da katin adashin banki za ka iya kallon su. Amma galibi dai, duk kyauta ne.
Kammalawa
Daga karshe kuma a mako mai zuwa, zamu kawo bayanai kan tsarin tsarin da kamfanonin gidajen jaridu da mujallu suke bi wajen nasu harkar. Kamar kullum, duk abin da ba a fahimta ba, a rubuto don neman Karin bayani. Na samu sakonni na neman Karin bayani kan Local Area Network da sauransu, zan samu lokaci don amsa su, in Allah Ya yarda. Ina mika godiya ta musamman ga Malam AbdurRahman Mamman Abdu, Malam Abdullahi Kyari, Umar Suleiman, Sanusi Imam, Sani Abubakar Jos, da kuma Malam Aminn bn Yusuf da ke tsangayar horar da malamai a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Mun gode, Allah bar zumunci, amin.
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq)
Off Lagos Crescent, Anguwar Hausawa
Garki II, Abuja. 080 34592444
Fasaha2007@yahoo.com
http://fasahar-intanet.blogspot.com

No comments:
Post a Comment