Friday, March 5, 2010

Ruhin Wayar Salula

Ruhin Wayar Salula

A daya bangaren kuma, akwai ruhi ko kace “masarrafa” ko “manhaja” da kowace wayar salula ke dauke da ita. Wannan ruhi, kamar yadda kowane dan Adam yake, ita ce ke sarrafa gangar-jikin da bayanansu ya gabata a makonnin baya. Kamar dai mutum ne; akwai bangaren gangar-jiki (kamar kafafu da hannaye da kai da yatsu da baki da idanu), sannan kuma akwai numfashi da dan Adam ke yi, wacce ke samuwa sanadiyyar rai ko ruhi da aka busa masa. Wadannan abubuwa guda biyu: watau gangar-jiki da kuma ruhi, tare suke mu’amala. Idan daya daga ciki ya samu tangarda, ana iya samun tangarda a aikin wayar baki daya. Matsalar da za a samu ya danganci iya girma da zurfin matsalar da aka samu wajen tangardan. A harshen turanci, idan kaji ance Software, to ana nufin ruhin wayar salula kenan.

Wannan ruhi na wayar salula ya kasu kashi biyu, ko ma uku. Bangaren farko shine wanda ake kira tabbataccen ruhi, ko Firmware a Turance. Wannan shine bangaren da ke rike da wayar, kuma tare da wayar ake kera su. Wannan bangare shine ruhin da ke samar wa wayar da nunfashin da take yi. Shine bangaren da ke rike gangar-jikin, ya kuma sawwake mata hanyoyin mu’amala da sauran masarrafan da ake sanya mata bayan an kera ta. Wannan bangare na ruhi ba a iya canza shi. Kuma ko da ka kashe wayarka, to yana nan yana aiki. Yadda ka san mutum ne ke bacci. Shi yasa ma da zarar ka sake kunna wayar, zaka samu saitin agogon wayar bai kauce ba. Domin wannan ruhi na waya ne ke rike dashi, ke kuma bashi wuta ko sinadaran lantarkin da yake bukata don ci gaba da aikinsa. Idan kuma ya samu matsala, to wayar za ta mace baki daya. Domin daga kamfani ake tsofa shi cikin wayar. Yadda ka san cewa kowane dan Adam ba shi da wani rai na musamman, to haka kowace wayar salula take; bata da wani rai idan wannan ya samu matsala. Da zarar ya mutu, to ita ma rayuwarta ya zo karshe kenan.

Bangaren ruhi na biyu kuma shine babbar manhajar wayar, watau Phone Operating System. Shine wanda ke dauke da sauran masarrafai masu taimakawa wajen sadar da kira da karbar kira da rubuta sakonnin tes da karanta su da dai sauran aikace-aikacen da zaka iya yi da wayar salula mai lafiya. Ita ce “dandali”, kuma da zarar ka kunna wayar salularka, ita ce zata farkar da ita, ta kuma kirawo maka dukkan masarrafar da kake son amfani da ita, nan take. Idan ka gama amfani da manhaja ko masarrafa, ka rufe, nan take zata kawar da dukkan bayanan wannan manhaja daga ma’adanar wucin-gadi (watau RAM) zuwa cikin tabbatacciyar ma’adana (watau Hard Disk). Wannan nau’i na manhaja ko masarrafar wayar salula suna nan kala-kala ne: ya danganci kamfani da nau’in wayar salular. Misali, akwai wadanda ake kira Series 40 (S40), wadanda ke dauke cikin galibin kananan wayoyin salular kamfanin Nokia Corporation ko na kamfanin Samsung Group. Sannan akwai wadanda ke kira Series 60 (S60), a dauke cikin galibin manyanan wayoyin salula na musamman, watau Smartphones – musamman nau’ukan Black-berry. Su S40 sun fi sauki da saurin karbar umarni, da kuma juriya da kauce wa yawan kamuwa da kwayoyin cutar wayar salula, watau Mobile Phone Virus. Sai dai kuma yadda ka saye su, haka zaka ta amfani dasu, baka iya canza babbar manhajar, ko kuma kirkirar sabbin masarrafai ko manhajoji ka sanya mata.

Amma nau’in S60 ba haka suke ba. Idan ka ga dama, kana iya kera wasu manhajojin wayar salula (irinsu abin wasa – games – da agogo, ko manhajojin da ke baiwa wayar umarni ta aikata wasu abubuwa idan aka kira ko ka kira, da dai sauransu), sannan kana iya canza wadanda tazo dasu. Ko kuma samo wadanda aka kera don sanya mata. Har wa yau, kusan dukkan wayoyi masu dauke da irin wannan nau’in manhaja suna amfani ne da tsarin sadarwa mai karfi nau’in “3G”, da kuma manhajojin mu’amala masu inganci, tare da kyawun sura wajen hoto ko bidiyo, da dai sauransu. Sai dai kuma matsalarta shine saurin kamuwa da kwayoyin cutar wayar salula, da kuma saibi, ko nawa, idan ka bata umarni. Tsarin babbar manhajar wayar salula nau’in S60 iri daya ne da na kwamfuta. Kuma kamfanin da ya fara kera su shine Symbian Group, wanda a halin yanzu kamfanin Nokia Corporation ya saye shi tun shekarar 2008. Wannan tasa galibin wayoyin salula masu amfani da wannan nau’in manhaja sune na kamfanin Nokia. Misali, dukkan ayarin wayoyin Nokia nau’in “N Series”, da “Nokia Communicator”, da kuma galibin nau’in “XpressMusic”, duk suna dauke ne da babbar manhaja nau’in Series 60 wanda kamfanin Symbian ya kera ko samar. Kana iya gane wayar salula mai dauke da wannan nau’in manhaja har wa yau daga irin fuskar wayar, kamar yadda zaka gani a hoton da ke manne a gefe. Kamar nau’in tabbataccen ruhi da bayaninsa ya gabata a sama, wayar salula bata iya rayuwa sai da babbar manhaja, ko kuma Operating System.

Nau’in manhaja ko ruhin wayar salula na uku kuma shine “ruhin wucin-gadi”, watau nau’in ruhi ko manhajar da ake iya sanya wa wayar salula don yin amfani da su wajen gabatar da wasu abubuwa. Misali, manhajar da ke sawwake maka rubuta sakonnin tes, sanya ta aka yi cikin wayar, bayan an sanya babbar manhaja. Manhajar da ke sawwake maka mu’mala da fasahar Intanet, ko fasahar Bluetooth, ko fasahar Infra-red, ko rediyo ko talabijin, duk sanya su aka yi. Ana iya kirkiran wasu ma a sanya. Wannan tasa zaka samu wayoyin salula na zuwa da ire-iren wadannan manhajoji ko masarrafai barkatai. Kowane kamfani na da irin manhajar da yake sanya wa wayoyin salularsa, masu taimakawa wajen tallata su.

Manhajoji ko masarrafai ko kuma “ruhin wucin-gadi” sun kasu kashi biyu ne. Akwai wadanda kowace wayar salula ke zuwa dasu. Ire-irensu sun hada da manhajar wasannni, watau games, da mahajar fasahar Intanet, da manhajar fasahar Bluetooth da kuma ka’idojinsu. Cikinsu har wa yau akwai manhajar sauraron wakoki da na kallace-kallace, da kuma manhajar rubuce-rubuce da lissafce-lissafce (irinsu word, da excel da dai sauransu). Akwai kuma manhajojin bude jakunkunan bayanai, irinsu acrobat reader (ko PDF), da na kallon fina-finai, irinsu flash, da na sauraron wakoki ko bude su, irinsu real player, da sauran ire-irensu. Galibin wayoyin salula kan zo da wadannan masarrafai ne a cikinsu. Da zarar ka saya, sai ka ta amfana dasu.

A daya bangaren kuma, idan Allah Ya hore maka hazaka da ilimin gina manhajar kwamfuta da na wayar salula, kana iya samun wayar salula mai dauke da babbar manhaja nau’in S60, ka sanya mata dukkan kayayyakin aikin da ake amfani dasu wajen gina manhaja ko masarrafa, (irinsu C++ Compilers, ko Phyton Mobile Interpreter), don ginawa, tare da gwaji da kuma loda wa wayarka duk irin masarrafar da kake son amfani dasu. Idan baka da irin wannan hazaka ko kwarewa, duk kada ka damu. Kana iya samun ire-irensu a Intanet ba tare da wata matsala ba. Misali, idan kana son rariyar lilo a Intanet irin ta wayar salula, watau Mobile Browser, kana iya saukar da Opera Mini zuwa cikin wayarka, ka loda mata, sai kaci gaba da amfani dashi. Haka ma kana iya samun manhajojin wasanni (watau games), da manhajojin karatun Kur’ani, da na Hadisai, da na koyon harsuna, da na koyon lissafi da dai sauransu. Dukkan wadannan ana samunsu yauta, ko kuma ka saya ka loda wa wayarka, don ci gaba da amfana dasu. Sai dai kuma kayi hankali, idan shafin da ka shiga a Intanet yake, kuma manhajar kyauta ce, kana iya cin karo da kwayoyin cutar wayar salula, watau Virus. Kuma kada ka mance, wayoyin salula masu tsarin S60 basu cika jure wa ire-iren kwayoyin cuta ba; nan take suke kamuwa dasu. Wannan tasa nan gaba kadan zamu kawo bayanai masu gamsarwa kan nau’ukan cututtukan da ke addabar wayar salula, da kuma yadda ake magance su, a aikace, in Allah Yaso.

Kammalawa

Wayoyin salula dai basu da bambanci da kwamfutoci ko kuma tsarin halittar dan Adam, wajen gangar-jiki da abinda ya shafi alaka tsakanin ruhi da gangar-jikin nake nufi. Akwai gangar-jiki mai dauke da dukkan abinda mai mu’amala da wayar ke amfani dasu wajen bata umarni. Da kuma ruhi, wanda aikinsa shine samar da kuzarin da ke taimakawa wajen aiwatar da dukkan umarnin da mai mu’amala ya bayar. Bayan tabbatacciyar ruhin da ke samar da rayuwa ta dindindin ga wayar, akwai kuma ruhi mai samar da shimfida ga dukkan masarrafan da mai wayar zai yi amfani dasu. Sai nau’in ruhi na uku, wanda ke taimaka wa mai wayar yin mu’amala da wayar kai tsaye – kamar yin kira, ko amsa kira, ko rubuta sakon tes, ko wasa don wasa kwakwalwa, ko sauraron wake, ko kallon hotuna da dai sauransu. Duk wayar salular da bata da ruhi, gwamma a yashe ta. Duk wayar salular da bata da babbar manhaja, gwamma rashinta da mallakanta. Ruhin wayar salula shine bangaren da yafi muhimmanci wajen amfani da wayar, domin ko da marfin wayar ya balle, ana iya amfani da wayar. Amma idan ruhin ya rikice, kunna wayar ma sai ya zama matsala.

No comments:

Post a Comment